Share this page
Kaka take ta nanata Kamarin ta sa ta soma ingiza zuciyarta a kogin soyayyar sa ta soma yaudarar kanta, ta soma sawa'zuciyarta kwadayin auren mutumin‘da yafi karfin ajinta. Abu kamar wasa Karamar magana ta soma zama babba, saboda yanda soyayyar Abubakar ta soma girma a cikin zuciyar ruky, .musamman yanda '_takcme ganin yana daukar Wanka', dukkayan da ya saka sai sun masa kyau manyan kaya k0 qanana k0 shigar turawa suit, har kayan lndiyawa yake sanyawa Pakistan, suma suna masa kyau matuqa. ldan ka ganshi sai ka rantse da Allah bai san hanyar kauyc ba, saboda gogewa da haduwa amma ciki yake kwana ya tashi. Yanda zuciyar Rukayya take kwana ta tashi da qaunar sa yasa har ta kai ta kawo bata iya barci idan ba ta ji muryar sa ba k0 ta ganshi ko da tsawa ce yai mata sannan take samun nutsuwa. Abun har mamaki yake bata yanda ta tsinci kanta a soyayya, abinda bata taBa yi ba. Fatan ta dai Allah Yasa shima abinda kezuciyar sa kenan. ‘ **************** Suhaila ta kwaso a guje ta nufi falon _ mommy dinta wadda ke zaune kan lumtsimemiyar kujera 3 sitter tana gyaran wasu tulin takardu, Suhaila ta fada kanta gamida rungumeta cikin murna tana fadar "Mommy albishirin ki?" Hmmm lol llah RIKON KAKA CHAPTER9 Ta saketa ta zagayo ta zauna gefenta ta ce "Mommy Mansir ya dawo daga Brazil, ya kammala karatun sa" . ~. Mommy tai murmush1 kafin ta ce "Hmmm! Ke wa ya fada miki?"Ta ce "Yanzun nan Hanifa kanwar sa ta kira ni take fada min jiya ya dawo cikin dare‘ ’ Ta ce "Shi ya ce ta fada miki k0 k0. gaban kanta . ne‘? " Suhaila tace, "Kai mommy, kema dai wanda ‘ya dawo cikin dare hadmr ya isa yin wata hira?" Mommy ta tabe baki kafin ta ce, "Iska na 'wahalar da mai kayan kara, ni wallahi in bacin 'so‘_sone amma banga abin so ‘wurin wannan ‘yaron ba. ‘Yaro yana tafe yana faman doro sai kace‘ ,shugaban zabbi‘, mutane masu mutunci suna ‘sonki amma ki ka‘ zauna jiran wani Mansir shekara uku kamar daga kansa maza sun kare". Suhaila ta mike tana fadar,"Kai ni dai 'kinga tashina, mommy ke kullum ba ki gajiya da mita. Ai dai . .tunda ya dawo zan iyasa direba ya kaini in masa sannu da zuwa". Ko Mommy ta ce, "Da yake baki da magayi k0? Ai duk saurin unguwar zoma ta bari a haife, tunda bai fada miki ya dawo ba da bakinsaba sai ki saurara ya kira ki ko yasa a taho miki da Iefensa". Suhaila tace, "Kash! Mommy kina da (problem), wa ya fada miki zamanin ku da namu iri daya ne? Ai da mata ke Jawa maza aji, amma banda yanzu". ' Mommy ta ce "To aje a yubar da ajin tunda zamani ya canza". Suhaila ta fice tana gunguni, mommy ta bita da kallo harta fice, ta girgiza kai ta ci gaba da aikin gabanta. . Suhailat tana shiga dakinta (toilet) ta fada ta watso ruwa, ta jima tana wanke lungu " da sako na jikinta tamkar amaryar da sabon angonta zai zo gareta. Ta fito daga (toilet) din tana tsane jikinta da tawul. . ' Ta zauna bakin (mirrow) ta murzawa jikinta (cream) mai kamshin gaske yabi fatar jikinta yai (smooth) sannan ta shafa hoda ta kai kala hudu. Ta qawata fuskarta da kayan kwalliya irin na zamani, tai gwanin kyau. ' Ta mike ta nufi kan gadonta ta dauki kayan dake sama, sabon less né mai matukar kyau da tsada Wanda aka amso mata dinkin shi jiya daga shago ' , Ta saka dinkin riga da siket ne sun bi jikinta Sosai, ta dauki kalabin ta ta nufi gaban madubi ta , raba gashin kanta gida biyu, ta jawo shi ya hau 'saman bayanta sannan ta nade ‘ shi a'baya ta daure: Ta kafa daurin kallabinta mai“ kama da_rawani, ya dauru sosai, gashin kama ya zame mata tamkar acuci maza. ’ Dan kunne da sarwa duk na (gold) ne ta saka' ta hau Wata 'yar siririyar agogonta shima na gold ne Ta dauki siririn mayafinta ta,yafa saman kafadar ta ts saka takalminta’ mai tsinin gaske saboda bata ‘da .tsaWo sosai ta dauki 'yar Karamar jikar ta’ :ta hannu ta dauki manyan wayoyinta Suhaila kyakkya'wa ce ajin farko, fara ce ' . tas.har_ wani yalo-yalo take, gajeriya ce mai matsakaicin jiki, Allah Ya wadala ta da dirin jiki na daukar hankali. Tana da matsakaiciyar fuska mai daukeda daradaran idanuwa da dogon hanci, bakinta daidai misali. Suhailat tana da kyau matuKa, matsalar ‘ta kawai gajarta, itama gajartar ba a gane mata saboda duktakalman da lake amfani da su masu matukar tsini ne , . _ Suhailat ta wucc kai tSaye zuwa harabar gidan ba tare da ta bi ta sashin mommy dinta ba,tana fitowa harabar gidan direba ya kwaso da dan gudu-gudun sa ya bude mata gidan baya ta zauna, sannan ya tambaye ta. "Ina muka yi Hajiya?" . . . Ta ce, "Gidan Alhaji Maiwada zaka kaini, gidan su Hanifa" ' Dircba ya ce, "Oh,na gané" Sannan ya rufe mata kofar, ya zagaya ya shiga ya tashi motar suka fice daga harabar gidan, maigadi ya hangame musu gate suka fice Unguwar alkali suka nufa daidai saman sabon titin unguwar alkali, qaton gida ne wanda yake saman titi. Direban yai hon maigadi ya bude ya sa hancin motar'cikin get din gidan. Sai da ya‘ fara gaisawa da maigadin Sannan ya nufi harabar gidan kai tsaye ya faka motar Wurin da aka tanada don ajiye motoci, sannan Suhailat ta bude motar ta fito ta nufi gidan kai tsaye. Katon gida ne kai da ganinsa kasan a .gidan an zuba Naira, sai da Suhailat ta wuce faluka kusan hudu Sannan .ta shiga Wani Emwaton falo, tana yin sallama taji ihun qawarta Hanifa, ta kwaso aguje suka rungume juna suna dariyar murna suka shiga falon. . Hajiya Sadiya tana hakimce cikin kujera . tana lallatsa laptop, , ta dago tana kallon Suhailat har ta shigo falon ta zauna tana fadar. "Ina kwana Momcy“. Sannan Hajiya sadiya tai murmushi, "Lafiya lau Suhailat, ashé ana ganinki? Ai mu , tuni na riga nayi fushi, mu baza kizo ki Koxo“ ki ganmuba amma tunda hasken ranki ya dawo ai gashi kinxo Suhaila tai dariya ta dubi Hanifa cike da jin kunya, tace ”Ba haka bane momcy'. Hajiya Sadiya tace, 'To yayane? K0 kina nufin bakisan ya dawo bane Murmushi kawai tayi don bata: data cewa kuma. . Hajiya Sadiya ta miqe da laptop dinta a hannuma tana fadar. ”Ni kinga nama haye sama tunda dai nasan wannan :zuwan Mansir ne, idan kingama ganinsa kin biya mu gaisa. Dariyn kawai tayi, Hajiya Sadiya ta haye sama. Tana barin falon Suhailat ta ce, “Ke qawar ina Yaya Mansir din yake ne? Ni fa qagare nake naga yanda ya koma‘ Hanifa tace, 'Amma kya bari a kawo Maki abubuwan motsa baki saunan k0?" , Suhaila tace'A‘a, idan na ganshi na dawa naci. Hanifa ta harare ta ce "Allah Sarki dadi ‘ ai nasanma k0 kinje yaxu bai farka daga barci' ba, ‘don Yaya Mansir sai ya kai dayan rana yana barci". Suhailat tace, "Eh naji, dai yana ina .inje in tayar da shi?" ‘ Hanifa ta ce, "Ai da yake kece nasan zai tashi, ba zai miki masifa ba. Kije yana dakinsa da kika sani" Suhailal ta mike da sauri tana dariyar murna ta nufi hanyar dakin nasa, sai da ta fita ' falon ta shiga wani sannan ta nufi bangaren sa, ta, tura kyauren dakin. ' A bude ta Same shi, don haka ta shiga da sallamar ta. Duk da ba a amsa mata ba hakan‘ bai hana ta sa kai ba cikin falon, qaton falo ne mai dauke da wasu kananan kujeru irin na‘ ma 'aikata, sai wasu kujeru biyu da katon tebir a‘ ‘tsakiya aka dira computer desktop a sama, a. gefe kuma, jikin bango aka sa kayan kallo ‘ ' Suhailat ta nufi dayar kofar ta tura ta ; shi ga, karamin falo ne babu abinda ke cikin sa .sai karamin gado da qatuWar wardrop da “sauran tarkacen kayan maza. Yana kwancc saman gadonsa a lullube da bargo yana faman sharar barcinsa hankalin sa a kwance Ta nufi kan gadon ta zauna. gefe idanuwanta na kansa. Ya qara haske da qiba har wani tumbi- tumbi ya ajiye, sai taga ‘ qibar tasa ta? rage masa kyau kok0 saboda sumar da ya kara ne oho. "Yaya Mansir mutancn Brazil" _ Suhailat ta furta tana murmushi tare da dan bubbugar kafafuwan sa. Ya motsa jikinsa kafin ya bude idanuwansa kadan yana kallon ta, kallon qurillah. Suhailat ta sakar masa murmushi _‘ wanda har ya bayyanar da haqoranta. Mansir ya yamutsa fuska ya tashi zaune suna qarewa juna. kallo, babu riga a jikinsa, daga shi sai dan gajeren wando na maza Cikin nitsatssiyar murya ta ce, "Sannu da zuwa Yaya Mansir ina‘ kwana?" Cikin rashin kulawa ya ce, "Suhailat ashe ba kiyi aure ba? Amma dai gaskiya kinyi jinkiri da Aini na zata tuni kin tSUfa gidan miji qila ma har da yara'‘ Kirjin Suhaila ya Shiga barazanar ‘ fashewa duk da A.c din dake dakin bai hana zufa kwararowa jikin Suhaila ba ta rinqa jin tamkar ana kada kalangun tashin hankali a ’kirjinta. Take idanunta suka ciko da kwalla Fashewa da kuka ‘tayi, tace, ".Yaya Mansir ba dai kana nufin harka mace da. alkawarin mu ba? Yaya Mansir kana nufin har ka mance da Suhailar ka, Wadda kake so take son ka, wadda ku kaiwa juna alkawarin soyayya da amana? Haba Yaya Mansir, kada ka cutar da ‘zuciyar da bata da tunanin cutar da kai ba, kar ka guje ni don Allah‘ ‘wallahi zuciyata ba za ta iya jure rashinka ba, (please) Yaya Mansir don Allah" Hawaye suka ciko gaba da bin kumatun ta ‘ tamkar an kunna famfo Mansir yai dariya kafin ya ce,"Suhailat kenan, har yanzu kina nan da halinki da na' sanki da shi" . Ya kara murmushi kafin ya ce, "Ke yanzu in banda abinki Suhailat ai kin min tsufa; ina ke ina ni me qananun shckaru? Yanxu haka fa shekarar ki biyu da gama digiri, inajin ma har kin soma aiki. . Haba Suhailat,‘idan za kimin adalci _ai kema kin san ba mu dace ba, yarinya nake ncma karama mai kananun shekaru, wadda bata wuce (lebcl '200) ba a jami'a, (please) Suhailat ki taimaka don Allah ki janye wannan xanccn tun wuri". Cikin firgici Suhailat ta ce, "Ban gane abinda» kake son fada ba Mansir dukaduka a nawane shekarun nawa‘? 25ycars nefa only, meye tsufan da nai wa saurayi me shckara talatin da wani abu? Kai dai kawai ka fadi. wani abin amma ba dai‘ wannan ba,‘ kawai kaCe kai dai ka daina sona, ka sami wadda ta fini kyau da komi amma ba kaita yimin zagaye zagayeba, ka filo kafito kawai kacc ka daina so na" ' Yanda take magana cikin daukar zafi yasa Mansir ya lahimci ta soma shaqa don haka ya kara kular da ita da cewa "Suhailat, duk yanda kika dauka haka nake nufi shiyasa: kike birge ni wani lokacin, saboda kinada saurin ganewa. Ai dama na taba gaya miki Shi so tamkar tsuntsu yake yakan tashi a duk lokacin dayaso ya canja bishiya. Kiyi hakuri Suhailat in har so cuta ne hakuri, ma magani''''''''' ' "Ya isa Mansir! Wadannan jahilan kalaman naka sun ishe ni haka" . Ta mike ta bar dakin gudu gudu sauri sauri ta bar masa falon Yana kallonta k0 a jikin sa don dama hakan yake bukata. yai murmushi ya ‘ koma ya kwanta abinsa yaCi gaba da barcinsa ' hankalin sa kwance Suhailat tana fitowa daga sashin sa kai ' tsaye ta bar gidan, direba na tambayar ta lafiya‘! Amma bata kula shi ba a dole yai shiru gida suka nufa kai tsaye : Kuka take sosai tamkar wadda " aka . aikawa uwarta da ubanta sun rasu ‘gaba daya har suka isa gidan tana abu guda, jikin direban yai sanyi. Yanda yaga ta bude murfin motar Cikin tashin hankali Lol soyayyah kenan Mu kwana lfy zallah RIKON KAKA CHAPTER10 Fice tana shasshekar kuka ya bita da kallo, sai dai bai da ikon da zai bata baki sai yaji duk jikinsa yayi sanyi dole ya tsaya inda aka ajiye shi Suhailat na shigowa falon gidan k0 gani bata yi har karo take da tebir din dake tsakiyar falon, mommy ta ce "Ke meye haka da za ki shigowa mutane ~ . k0 sallama babu?" . Ba ta tankaba ta nufi - bangarenta tana ' , faman kukanta, jikin’ mommy din yai sanyi ganin irin kukan da Suhailat din take tamkar ta , share ta, sai dai ba zata iya ba, a_ dole ta daure 'ta mike ta nufi sashin nata. Tana kwance saman gadonta tana faman ‘ ~ rera kuka, k0 takalman ta bata cire ba. ~ ' ' ‘ Mommy ta zauna gefenta ‘cikin tausassar‘ murya ta ce: "Lafiya Suhailat? Me ya faru?" ‘ ‘ Ta gaza magaba sai dai kuka, mommy "tai juyin duni'ya amma Suhailat taqi magana, sai dai kuka har ta'gaji ta tashi ta barta‘ Ta nufi falo ta dauki wayar ta, ta kira Hajiya Sadiya , taji k0 sun san abinda akai mata? Hajiya Sadiya ta ce'ai bata ma'san tafiyar taba, tace bari ta kira Hanifa taji abinda ke faruwa. " Mommy ta Ce, "To" ' _, Wasa-wasa har yamma Suhailat na abu -' daya, k0 abincin da aka kawo. mata taki. ci sai ; . dai kuka kawai take, kuma taqi? magana. , ' Ana idar da sallar isha'i Alhajin: su ya dawo, tana falo Hajlyar ta tare shi, ta ce.., . "Babu fa lafiya a gidan yau Aihaji, Suha’ilat tun safe take kuka har yanzu, taqici. taqi sha sai kuka". Alhaji ya ce "Dama nasan hakan zata‘ faru". ‘ Ya‘ mika mata jakar hannunsa, yace "Haumin da ita sama,‘ sai ki kirawo min ita , Suhailat din".ta‘ Dole mommy ta janye tambayoyin da ' suka Cika’mata zuciya, ta wuce ta_hau benen da ' ' zai kaita sashin Alhajin. ‘ Tana; fitowa ‘ta nufi ‘ Bangaren Suhailat din, a kwance ta ' same ta tana kukan nata kamir'wata karamar yarinya; Mommy ta tsaya daga bakin qofa, ta ce ,"Kije inji Alhaji yana falo yana jiran ki". ‘ Bata ji ma abinda za ta fada ba tajuya ta fice.‘ ‘ ‘ Suhaiiat ta yunkura ta mike jikinta a mace ' ta ja kallabinta ta daure gashin nata wanda duk ya yamutse,sannan ta sauko daga .kan gadon ta nufi falon. ‘ . Muryar ta a shake tamkar mai mura, tai ‘ sallama ta shiga falon, Alhaji ya kafa mata idanuwa har ta zauna. Rana daya kacal harta zabge, ta lalacc, sai kace wadda tai ciwon ’ shekara. . Alhaji yace, "Suhailat, dazu Alhaji Maiwada ya sameni kamfani yazo min da wani zance Wanda ga dukkan alamu kema kin . sami labari , to abinda nake so Suhailat ki sawa . ,zuciyar ki haquri don Allah ki ‘mance da , Mansir da labarinsa', tunda bashi kadai bane namiji a " duniya ‘ Suhailat ta Kara fashewa da kuka kafin tace ‘ "Ba zan iya ba Alhaji, wallahi ba zan iya ' ”Zancen banza kenan Suhailat, ai ya zame miki wajibi ki mance da shi tunda mahaifinsane ya same ni ya sanar dani sun janye ' wannan maganar tsakanin Suhailat da Mansir tuni dama ai ba wata magana mai qarfi ta shiga tsakanin ku ba, ke kika Kara karfafa abin har kika Bata lokacin ki akan sa. , Mahaifinsa ya sanar dani dansu ya kawo masu yariyar da yake so a yanzu, kuma babu yanda: za suyi da shi tunda ba zasu yiwa dansu , auren dole ba duk wadda ya kawo ya ce ita yake so ita za su ba shi. . Don haka kiyi hakuri Suhailat, nima a matsayina na mahaifinki tun. a dazu da mahaifin Mansir ya zomin da wannan zancen nima na Samar maki nawa. Zan hadaki da wani yaro dake aiki a kamfanina mai suna Abubakar Dandagoro, shi da kakarsa suke iyayen sa sun mutu, nai miki sha'awar auren‘ sa tunda yaron kirkine, yana da mUtunci da nutsuwa. _-Mahaifinsa a lokacin yana rayé shi ya . kawo min shi a kamfani na muka dauke shi aiki da N.C.E dinsa; yana cikin aikin ya jona yai digiri dinsa, na tabbatar yaron zai miki saboda yaron bai da makusa. Nai mashi magana kuna ya amince gobe zai zo ya ganki ki ganshi ku gaisa kiga idan ya yi maki Suhailat ta ce, "Yanzu Alhaji har nayi girman da za ace ana talla na? Alhaji yanzu ban da kyan da zan iya samarwa kaina mijin da ya cancanta dani? Wayyo Allah na" Sai ta sa kuka ' Alhaji ya ce, "Kinji wani zancen banza Hajiya, kinji wani sakarci. Ai' maki miji ya amince zai aure ki ai arziki ne, kuma shi kanshi idan yazo ya ganki ai yasan ba rasa mijin aure kikai ba, ban son sakarcin banza kinji, tashi ki ban wuri, ki shirya kuma gobe zai zo" ‘ Suhailat ta mike ta Kara sa‘kuka ta nufi falonta, jikin momy ya qara yin sanyi liqis, 'tace . "Amma Alhaji naji . kace yaron .kamfaninka ne, anya ya dace da Suhailat “kUWa? Alhaji yace, "Ai idan dai har ya yi mata ” babu abinda bazan iya yi masa ba, zan bashi qaton gidan da k0 shi Mansir din iyakar shi zai gina mata, zan bashi mota kuma in ‘samar mashi aiki irin warida zai iya riKeta da Shi Mommy ta ce, "To hakan ya yi, kuma'; Alhaji Allah Ya taimaka Ya Kara budi". ’ Ya ce, "Amin" Ya mike ya nufi sama, Hajiya ta bishi a baya. ‘ ‘ . A daki Suhailat kukanta yafi nada karuwa, saboda a yanzu ta tabbatar da ta rasa; 'Mansir, gashi yanzu bata San ko waye Alhaji , ya zaba mata ba, bata san ya yake ba. Yau dai ; " tai kuka har ta godewa Allah, batun barci kuwa babu shi a wannan ranar. , Suhailat ta shiga tsananin damuwa da tashin hankali, ta riga ta sadakar data rasa Mansir, . , haka har‘ girin Allah “Ya waye tana abu guda, sai da mommy dinta tai da gaske sannan ta " samu tai break, shima ba wani da yawa ta ci ba. ' . Karfe hudu saura nayamma mommy ta tiSa Suhailat gaba sai da tai wanka ta tsareta ta shirya cikin wata doguwar riga baqa mai hawa - hawa, rigar tai mata kyau, musamman kasancewarta na farar fata. Ta nada dan qaramin gyalensa saman kanta. Tai kyau sai kace balarabiya, sannan mommy ta kyaleta ta tafl, ta sa masu aiki su gyara sashin da ake saukar baqi. . ‘ ***************** Haka nan Abubakar-ya sami kanshi da damuwa tun Iokacin da Alhaji Halliru ya kira shi ya sanar da shi buqatar sa yake jin tsananin damuwa. Sai dai babu yanda za ai ya watsa mashi qasa a ido, ya ce baya son kyaular da yai masa, saboda irin halaccin da yai masa a rayuwa. Kuma duk jama’ar dake kamfanin bai, zabi kowa ba sai shi, saboda yana ganin shi xai iya rufa masa wannan asirin, bai kamala ace ya watsa masa qasa a idanuwa' ba, kuma tunda shi ba wata tsayayyar budurwa ke gareshi' ba. ’ yasan yana da 'yan mata amma, duk irin sha ka '. tafi dinnan ne. Ya dade a gaban (mirrow) yana juya hular hannun sa kafin yai ta maza ya dora ta a kansa, ya dauki siririn farin gilas din ya dora a fuskar shi. " ‘ Ya tsaya yana karewa kanshi kallo shi dai yasan ba wani kyakkyawa bane na azo a gani,ba to amma yasan bai da muni. Yanada daidai nasa kyan na misali. Kuma inda yake kara birge kansa indai _ zaisa kaya sai sun masa kyau a jiki tamkar don . ' shi akayisu . don haka wata (light brown) din ’ shadda Ce. mai haske a jikinsa, an mata dinkin : Hannu. {dark brown) din zare akasa mai cizziWa,‘ ’ takalminsa sawu ciki da hular sa duk kalar shaddar ne. . . ' yai kyau sosai, ya dauki turaren sa 24 hour ya feshe bangarorin jikinsa sannan ya dauki makullin dakinsa ya fito ya kulle, ya jefa ‘ key din a aljihun wandon sa ya nufi dakin Kaka . , A kwance ya sameta sai Rukayya dake zaune tana kwance Kitson daya gaji da_ dauda har ya daddale dakyar take iya kwanceshi saboda kitson ya harhade sai warin dauda kan yake Abubakar ya tsaya daga bakin kofa ya tsugunna. "Ni zan fita Kaka. xan shiga can cikin birni, gidan ubangidana, ina tunanin wurin magaruba zan dawo . Kaka tace, "Me zaa kayi gidan nasa kuma? Ni kasan ban son kana shisshigewa masu kudin nan Habu, saboda yawancin su duk matsafane ajc a sai da kai a banza, . ' Abubakar ya cé, "Dadina da ke tsohuwar nan tsoro, saboda' ni kawai ake'jira'daga zuwa sai a kama tsafe ni gasu sarakan tsafi Ai ni ‘naman jikina ya haramta ga duk wani aljani ballantana bil'Adama. ‘ ‘ Kaka tace, "Kai tashi can sai shegrn cika _ bakin tsiya, ai sai wanda ya girka kanshi da aYOyin Allah yake irin wannan ikirarin, wanda ya sha kuma yai wanka". Abubakar ya ce "to ai abun sirri ne Kaka tunda ba ki nemu mani ba ni da kaina nake nemowa kaina". Kaka tace, "Hmm! Dama dai wata wata furar amman bata gero ba". Abubakar ya mike yana fadar, "Kai bari in tashi kinji, idan na biye maki sai mu kai magaribar anan ban tafi inda zani ba abubakar ya dubi rukky yace kai mai hali dai bai canja halinsa amman wannan kan nasan ko tantama babu .ba a rasa kwarkwata acikin sa , " Kaka tace,"inma da kwarkwatan ina ruwanka? Kanka ne k0 nata‘? K0 dakin ka aka shiga , ana. kwantar?" Abubakar yace, "Ko daya, sai na daWo". Tace , "A dawo lafiya". ' Yasa kai ya fice abinsa. ********* ************* Suhailat tana kwance a falo saman duguwar kujera zuciyarta ta lula duniyar tunani,kana kallonta kasan tana cikin damuwa Sai admin yacemu tara donjin yaddah haduwar abubakar da suhailat zata kasance Naku har kullum A, I, S ke cewa asha karatu lafiya zallah shared a profile . RIKON KAKA CHAPTER11 end of book1 Mommy dinta ta shigo falon ta dan bubbugata‘ "tashi kinji ga bakon can ya iso tun Dazu na sa masu aiki sun kai masa abubuwan motsa baki"Suhailat ta yunkura ta mike ta Sako ‘ qafafuwanta daga saman kujerar, ta saka takalmantata mike; mommy tace . "A'a Suhaiial ai kya dai Kara gyara fuskar mana, kin tafi haka fuska duk a yamutse Suhailal ta Cinkuno baki, "Ni dai ki barni ‘ mommy kaWai, ina ruwana "? . ‘ Mommy taja hannunta har gaban madubi ta dauki hodar da kanta ta Kara shafa. . mata', ta dauki turaren bb ta fesa mata a , dukkann gab0bin jikinta,dakin ya dauki , _ kamshi sannan taja hannunta suka fice har bakin kofar dakin ta kaita. Sai dataga Shigarta sannan ta juyo ta koma tana roqon allah Yasa yai mata itama ita tai masa ta samu ta aurar da yar tilon.’ yar tata kwara daya Sai Yayanta Wanda yanzu haka yana . qasar Misra yana karatu \ Suhailal ta Shiga falon da sallama idonta na saman fuskar AbUbakar wadda take mannevda siririn farin gilas ' Gaban Abubakar , yai mummunar faduwa, tsantsar kyan da ya gani kWancc a ', fuskar Suhaiiat ya rudar da shi. ~ "Anya wannan itace kuwa‘?" ' ' tambayar da yaiwa kansa wadda bai da .mai amsa mashi ita. ' " kenan. , Suhaillat ta karaso cikin falon ta zauna .saman kujerar dakr fuskar tasa, taci gaba da .wasa da yatsun hannunta ba_ tare data furta masa qala ha. ' Wani irin abu ne mai kamar iska wanda ke tafiyarda dukkanin bakin .ciki da damuwa Suhailat taji yana kewaye' zuciyarta ha bata'san,“ lokacin da bakinta ke bayyanarda Wani kyakkyawan murmushi ba, abinda ya nutsar da ’ Zuciyar Abubakar kenan daga tsananin bugun' ‘ da take harya samu yai karfin halin fadin ' " "Sannu da, zuwa Hajiya ,Suhailat, barka Da isowa yake wannan kyakkyawar halittar Shiru ta dan ratsa wurin xuciyar' Abubakar taCi gaba da harbawa saboda tsananin tsoron da ya cika ta, duk da yasan Ba wannan bane lokaci na farko da ya saba zuwa wurin budurwa tadi ba" Tsawon wasu daqiqu sannan Suhailat ta . iya danne tsananin farin cikin da ya dabaibaye" Ta ta dube shi‘ "Sannu da zuwa YallaBai, -barka da zuwa ', Abubakar yace' "(Am sorry) Hajiya Suhailat, sunana Abubakar Saddiq ai Yallabai yana Kofar soro Suhailat tai wani lakaitaccen murmushi " kafin tace "Na so ace ka karBi qarin ginnan da ka samu daga wurin Hajiya Suhailat, amma tunda ka noqe ba komi". Abubakar ya ce “K0 kusa ba haka nake nufiba, naga dai kowane turmi da taBaryar data Dace da shi ne shi yasa". Suhailat ta cr, "Karka damu Abbakar, indai Suhailat ce zaka same ta a yanda kake ’“ Kake buKata, burina guda daya a rayuwa In auri Wanda yakr so na nake son shi, ba wai wanda yake sona ni kuma bana son shi ba". Abubakar ya dan yi jim, kafin ya ce, "Suhailat zan fada miki wasu maganganu na gaskiya da gaskiya, don Allah ki wa maganganun nawa kyakkyawan kallo da kuma kyakkyawar fahimta. Wallahi tunda na dora idona akan ki zuciyala ta amince da cewar ke ce kadai wadda, . zuciyata ke ncma, take yi min hasashen samu a matsayin matar aurcna. . Suhailat ki amince min na kasancc a tare dake duk rintsi mu kasancc da juna. Soyayyar ki ta garzayo a gare ni tunda na dora idona akanki Zuciyata ta'darsu da qaunar ki, gangar jikina na maki lale marhabin da zuwan sabuwar rayuwa zan kasance cikin farin ciki da jin dadi idan har na kalli kaina a matsayin mijin da aka kawo miki Suhailat ki dauka ni na ganki ina so, son da idan har muka kasance_ ma aurata zan'nuna miki shi irin wanda babu macen data taba samun irinsa a wurin masoyinta. ’ Ki amince min Suhailat mu gina wata kyakkyawar alaka mai cike da soyayya irin wadda k0 bayan ranmu za a dade ana tunawa da mu Suhailat, please". Suhailat lai wani kyakkyawan murmushi, wani irin shauki ya rinqa ratsa 'zuciyarta, ta bishi da kyawawan idanunta kafin ta ce . ' . "Abubakar idan soyayyar Suhailat kake nema to ka' riga ka samu, in baccin' ma ina tsoron halin ku na‘ maza~ ai dana ce kamar yanda na baka' Soyayyata Abubakar haka na baka kaina gaba daya, to ku din ne maza ‘ lamarin ku sai Allah". ‘ Wani dadi ya kama Abubakar don tunda ‘ yakcmr bai‘ taba tunanin zai samu soyayyar ' “kyakkyawar mace irin wannan ba, ya ce. "insha “Allah Suhailat zaki same ni mutum mai riqon amana da kuma alkawari". Suhailat ta ce, "Allah Yasa Abbakar". . Hira sukc a hankali a hankali har suka ‘ cinye lokaci, basu ankara ba sai dai suka ji ana’ kiran sallar magariba. Abubakar yai saurin ' " kallon Suhailat da murmushi a fuskar sa, ya ce. "Wasa-wasa mun cinye loka¢i fa".'~ Suhailat ta dan hatare shi da wasa, kafin"ta ce' "To da ba zaka yanxu ba kcnan?" _ Abubakar yai dariya, "Tuba nake gimbiya Suhailat, ~aimin afuwa, garin namu kauye ne dole zan wuce. Gashi ba abin hawa nazo da shi ba Ran Suhailat bai Soba,banda abinsa ma nan da garin Dandagoro, amma don kar tacika bayar da kanta ta sa ta ce ’ "To shi kenan, muje ka gaishe da mommy sai na sa direba ya mai da kai gida". Abubakar

Chapter 4 of 13