Share this page
idanuwan Rukayya don haka ta bar Ahubakar yana sassaka kayan firij ita kuma ta shige dakin baccinsu ta watso ruwa tasa rigar baccinta cikin ta daure gashin ta da ribon ya shigo. Ta madubi ta hango .shi ya iso inda take bata san yanda akai ba sai dai taji ya rungumeta ta buya ya miqa hannunshi guda y; diuko kwalbar turaren cool water ya rinqa fesa mata a jiki saidaya fesheta dashi sannan ya ajiye turaren sannan ya jasu sukn fada saman gadon dake bayan su, ya kashe wutar dakin yaja bargo ya lullubc su. Washegari ita ita takama Lahadi, ba aiki kamar jiya asabar, don haka suna idar da sallar asuba suka koma suka kwanta. Rukayya bata sake farkawa ba sai da Iaji tamkar ana yamutsa ta ta bude idanuwanta da kyar don ganin mai wannan aikin. Abubakar yaja muta hanci yana fadar. "A tashi haka nan ayi wanka a karya. ga ruwa can: na hada miki". ' .a toilet ta fara juye juye yace kinga wasa sai dai kiji ki cikin ruwan wankan'. Rukayya tai surin tashi zaune tana . ' kallonsa da idanuwanta duk bacci, Abubakar ya miqa hannu ya janyota ta sakko daga kan gadon, ya tisata gaba har sai da ta shiga (tOilet) din ta kullo sannan ya juya ya fice. ' Rukayya bata bata lokaci ba wurin .shiryaWa ta fito yau a tare suka karya don ta ‘soma sakin jiki dashi. Tarairaya da lallashi .tare da soyayyar da yake nuna mata ita tasa ta soma jin wata irin sabuWar qaunarsa na shiga zuciyarta. Yanda yake nuna tausayinta a fili abin har mamaki yake bata, wai yau yaya Abubakar ne ya abubakar ne ya koma' haka ya canza tamkar ba wannada yatsaneta, ya hantareta ba. : lallai Allah Ubangiji mai juya zuciya gashi yan'zu ya juyo mata da zuciyar abubakar gareta. Lallai a yanzu ta yarda'da maganar Aunty Maimuna da take cewa, mai haquri yana tare da ‘nasara aiko ita dai taga nasarar. don ma zuciya da taso ta rinjayeta daga farko lallai kuwa da tayi 'asarar da ya kamata azo mata jaje don rasa namiji kamar Abubakar ba karamin asara bace Da wannan tunanin har bacci ya dauketa a daren yau inda ta kwana da zummar‘ garin Allah na wayewa litinin zata riga Abubakar tashi, ita zata yi komai ba,hidimar gidan ta hutar dashi don harta . soma tausaya mashi. ' '_ _ Don haka tunda suka koma baccin asuba ita taqi ta koma tana ganin bacci ya dauke shitaja jikinta ta fice kai tsaye‘ ‘kicin ta Hula nufa ta dora ruwan zafi ta Zuba masu garin chitta‘da' na‘a-na‘a,. suna ' tafasa ta juye a flask din ruwan . Ta koma ta dayko dankalin turawa ta fere tasa a tukunya ta dafa shi sannan ta. ' tsame shi tamai bula bula ba koyon girki mukaxoba am sorry Dayan ta gama tsaf sannan ta dauki komi la jajjera su gwanin sha‘awa, sannan ta koma kicin din ta gyara shi ta hada ruwan omo ta wanke dukkanin abubuwan da tai amfani dasu ta kife ta share kicin din ta goge ko ina da tawul sannan ta janyo kicin ta kulle ta dawo falon tasa tsinlsiyar laushi ta share shi tun daga qasan kujeru har zuwa qarkashin sai da tabi ta share. Sannan ta dauki mopprr ta hada ruwa a bukiti ta goge tayils din tsab, k0 ina ya dauki sheki. Ta koma ta sa wani tsumma mai Iaushi ta goge duk wasu abubuwa masu daukar qura dake falon, sai data gama tsab sannan ta dauko boner har guda biyu daya ta zuba turaren wuta ta jona‘ a socket daya kuma ta kunna tsinsiyoyin kamshi masu kyan gaske ta tsilstsira a jiki ta koma ta dauko room freshner ta ruwa ta feshe dakin. Ai kafin kiftawa da bismillah dakin ya kaure da wani ni'imtacccn kamshi ta saki labulayen ta goge sannan ta qara qarfin A.C ta nufl sauran falukan suma duk ta gyara su kamar na farko, da turare su da kamshi. Karfe takwas dai-dai ta shiga (facin baccinta shima ta gyara shi, ya wanko toilet‘sannan ta watsa ruwa tana gamawa shima ta hada mashi sannan ta filo. _ Kwalliya tayi ba wata mai yawa ba, ta saka baqar jallabiyya mai hade da gyalenta, sannan ta nufl kan gadon da Abubakar ke kwance ta rasa ta yanda zata tayar dashi. can dabara ta fado mata ta dauki fIlo ta rinwa‘ buga mashi a kafa amma babu alamar Zai tashi. Rukayya ta rasa yanda zata yi dashi, can dai ta saduda ta hayo kan gadon tana dan bubbugar filon da yake kwance akai tare da kiran sunanshi Caraf ya yi da ita, sai dai taji ta cikin jikinshi ya kanannadeta da hannayenshi yana dariyaya ce ' . "Wato na ma zame miki tamkar wani. dodo. k0?" Rukayya ta girgiza kai tana’ Roqarin zamewa. ' ya Kara riqeta yana fadar. "Ki tsaya kada ki jiwa kanki ciwo. tambayar ki zanyi". ‘ Rukayya ta nuna mashi agogo tana Rukarin zillewa, karfe takwas da rabi agogon ya nuna. Ya yi saurin sakinta yana fadar, "Kai-kai loakcin (office) ya kusa yi".. Bai jirata ba ya Sauka‘da gudu-gudunsa ya fada (toilet) yana faman yarfa hannuwa wai ya shiga uku ya kusa makara. Rukayya ta zauna bakin ‘gadon tana mashi dariya har sai da ya shige sannan ta. mike ta yaye zanin gadon ta canza wani mai ‘laushin gaske, ta feshe Shi da (bed frcshncr) sannan ta bude (wardrop) ta cirowa Abubakar kayan da zai saka. Sannan ta flce abinta. 'A gaggauce Abbakar ya shirya yai break dinshi ya, bata wata sabuwar waya rantsatstsiya, a cikin kwalinta mai matuwar tsada, tsabar doki Rukayyabata san lokacin da ta Runkame shi ba tana murna. Abubakar ya lakace mata hanci yana mata dariya ya fice ya 'nufl wurin aiki‘abinshi. . Rukayya kuwa wuri ta samu ta rashe‘a' falo ta rinqa cskule-cakule a wayar tata tunda take a ' duniya bata taBa riqe waya ta kanta ba sai yanzu, lallai .Abubakar ya gama mata komai tunda ya hadata dawayar salula. Shi kuwa Abubakar tunda ya isa (office) din aiki kawai yake amma zuciyarsa na kanta, duk abinda yake qarfin hali ne kawai da jarumta, amma a yanzu yana ji a jikinsa qarfin halin nasa ya kusa qarewa. Yana son Rukayya so ba na wasa ba, haka kuma yana sha'awar komi nata. Yasa hannu ya tallabe kansa cike da damuwa, duk lokacin da ya kalli Rukayya yakan rasa hankalinshi gaba daya, sigarta kawai takan nemi ruguje‘ mashi lissafi. Lallai ya yi sa’a da kasaitacciyar mace, sai a yanzu ne yake mamakin kansa ta yanda har ya rinqa hantarar ta. Shin a lokacin meke damun kwakwalwarSa da idanuwansa da suka kasa ganin abinda ya dace da shi? Wai har ya fifita Suhailat akan Rukayya, yarinyar da in bacin kyan fuska babu mamora a jikinta. Lallai shi ya gama wautar kanshi. “Ya' ja tsaki mtsw! Kafin ya mike yasa hannu ya lalubo wayarshi dake kan tebirs ya lallatsa lambar wayarta ya danna mata kira. (Ringing) daya, biyu na uku aka dauka. Rukayya ta: mike a saman doguwar kujera (three seater) ta danno mashi siririyar sallama a cikin dodon kunne, sai da Abubakar’ yayi murmushin jin dadi don har ’ 'tsakiyar kwanyar' kanshi maganar ta ratsa. Ya kwantar da kanshi a saman makarin kujerar da yake zaune, ya cigaba da jujjuyawa da kujerar yana fadar. "Ruky Darling, kinyi kewata kuwa?" Rukayya tai murmushitare da lumshe ido ta _ bude, kafin ta ce. -"Sosai ma Yaya Abbakar, duk gidan sai ya yi shiru da baka nan Abubakar jinshi yayi tamkar a saman gajiimare tsabar shauki, ya bude baki da kyar yana fadar. "To me za ki shirya mana kafin na dawo?" Murmushi tayi wanda har ya jiyo sautinshi a cikin wayar, ta ce. "Wani spccial girki ne Yaya Abbakar me ‘ motsa ' kunne" Dariya yayi sosaikafin ya ce"Sai kuma me qanwata? K0 shi kenan?" ‘ sai da tai wani fari da idanuwa irin na mai neman mafita kafin ta ce ' "To ai ban 'san sauran abinda kake so ba Abubakar ya ce "KeCe sauran, ke nake so Rukayya, k0 ba zaki bani ba?" ‘ Ta ce "To ai kariga daka samu yaya Abbakar, me kuma ya yi saura?" Abbaakar ya ja numfashi kafin ya ce ' "Ai baki so na Rukayya, guduna kike shi yasa". Tai saurin rufe baki tana dariya, ta ce "Kai Yaya, tun yaushe na daina?" ‘ ‘ Shima dariyar ya yi kafin ya ce"Da gaske kike mata ta.? Ta jinjina kai tare da fadar, "Da gaske nake mana, Ya ce "To shi kenan, kice yau inzo gida da kwarin gwiwa kenan matata tana maraba . dani. To' amma ai min irin kwalliyar jiya a shafa min janbaki da jan ido ta yanda da na shigo zan yarda da lallai abinda aka fada min yanzu da gaskene". RuKayya tana dariya ta ce, "Insha Allah Yaya, sai ka dawo". ' Ya ce"To qanwata, me kikc so inyo miki . tsaraba?" ., Ta danyi jim kafin ta ce, "K0 dami ma ka taho ina so". ' Ya ce "To Shi kenan, sai na dawo“. Sukai sallama sannan kowa ya ajiye ta kalli wayar _ Tsabar murna Rukayya ta rasa irin . shirin da zatai na tarbar Abubakar, tunda ' tayi la' asa: bata sake samun zama ba, ita ce shiga kicin ta hau shirya abincin da tasan zai yi farin ciki dashi. Abubuwa ne ta hada mashi sun kai kala hudu, ‘ sannan daga qarshe ta hada mashi (juice) din gwanda da karas. ' ‘ Ana kiran sallar magaruba ta gama komi ta nufi (toilet) ta sharto wanka ta tare da alwala ta fito, sai da tai sallah tana zaune tana lazimi Abubakar ya shigo gidan. A gajiye yake don ya sha aiki a (office), ya turo qofar bedroom din nata ya shigo da sallamarsa, Rukayya ta dago kai tana kallonsa bakinta dauke da murmushi. ’ Abubakar ya durkusa a gabanta ya dora hannayensa akan jikinta yana fadar. "Na gaji da yawa Ruky na, don Allah k0 zaki . taimaka mani da wanka?" .. Rukayya tai saurin rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana dariya. Shima dariyar yayi ya mike yana fadar. ‘Shi kenan, bari intafi ‘sashina inyi tunda' ‘ ba‘ zaki min anan din ba". RuKayya dai na jinsa amma bata dago din ba ‘ har ya fice, sannan' ta mike ta nufi gaban madubi ta zauna ta soma kwalliyarta cikin saurisauri ta samu ta gama, ta ciro kayan da zata saka riga da wando ne blue din ’ jeans sai sky blue din riga irin ta Pakistan mai' adon pink sama da kasa, ta kawo mata kusa’ da gaiwa, tana da tSaga a gefe da gefenta. ‘ Rukayya ta dauki siririn gyalen rigar kalar pink ta daura akanta,'sannan ta saka dan kunne kalar rigar Tayi kyau ba ma kadan ba, don haka ta dauki hijabi ta saka tai sallar isha‘i, , sannan ta cire ta saka flat din takalminta ta; fito falon . A kishingide ta same shi saman kajera” yana waya, don haka bata bi ta kanshi ba ta , wuce wurin (dinning table) ta rinka kwaso kayan abincin .tana maido su akan carpet har ta kammala'bai gama wa‘yar ba wadda*'ta fahimci ba da kowa bane ba face Suhailat don daga karshe taji yana fadar... ' ‘“ "Kinga Suhailat ina da ababuWan yi masu yawa a gabana, sai anjima" Ya kashe wayar. ' ' Ya sauko kusa da Rukayya ya zauna tare da dafo kafadana, ya ce “Ya dai madam? Kin san kuwa ina jin Yunwa?" Rukayya tai murmushi kafin ta soma zuzzuba musu abincin. ‘ ‘ Lallai kam Abubakar ya kawo yunwa, don narkar abincin kawai yake kamar ba gobe, sai faman zuba santi yake Rukayya na Sheqa mashi dariya Aka murda qofar falon aka turo tareda sallama, su duka suka bi qofar da kallo don ganin mai shigowar. : Oga Mahmud ne ya shigo tare da Kaka, mamaki ya kama Rukayya, ai bata san lokacin da ta tashi ta nufi kaka zata rungumetaba . Kaka ta tureta tana fadar ‘ “Ke ni kauce ki bani wuri, shashashar banza da wofi, shi ne kika sa qafa kika biyo shi, wato ni ban isa in yanke hukunci a kanki ba k0? . To na gode. Rukayya ta rike hannun Kakar ta Iangabe kai tana fadar. ' "To ai kaka shi ya matsa sai da ya taho dani". , Kaka ta fisge hannuwanta tana fadar. "Ke gafara can sakarai, ya dai laye ki ' da dadin bakinshi, amma k0 da ihu da cizo baki guduwa? Meye amfanin zama da azzalumin mutum irin shi? Sai ki juya yanzu mu“ tafi" . . Ta kamo hannun kukayyar za ta jata, tai sautin turjewa tana fadar. A'a Kaka, bari in dauko mayafina mana". Ta ce, "To jeki maaza ki dauko, ina nan ina jiranki" , Mahmud dake tsaye yana kallon su yai murmushi kafin ya ce. "Anyi haka kuwa Kaka? Ki shiga mana ‘ ki fara zama tukun". kaka ta dalla mashi hararar da har saida yaji yan hanjinshi sun motsa kafin tace Wohoho su kaka manya jama,a anya kaka zata bar wadannan ma,auratan su huta kuwa Hmmm muje zuwa RIKON KAKA CHAPTER 28 Abubakar ya mike ya nufo inda ‘suke yana fadar; ' "D0n Allah Oga ta yaya ka taho mani da wadannan kayan rigimar?" ‘ ' Kaka ta ja tsaki, "Ai k0 bai kawo ni ba ' wallahi ban barin garin nan k0 da zan mutu . .sai na gano gidan nan, marar mutunci kawai" Abubakar ya ce, "Ai k0 da na sanya' maigadi ya hadaki da kare ya raka ki har gida Kaka ta ida rikice masu, "Eh, dama , iskancin ka ai ya wuce haka Habu, ‘rashin imaninka da rashin tausayinka ya zarce haka shi yasa Kafata kafar jikata, bata yin zaman auren k0 dole ne? Rukayya dake tsaye taiwaAbubakar nuni da hannu alamar yai shiru, sannan ta kamo hannun Kaka tana fadar. "Zo mu shiga daga ciki Kaka kada ki biye mashi ranki ‘ ya Baci" . , Rukayya ta jata sukai dakin baccinta. -. Abubakar .ya dubi Oga Mahmud yana fadar. . . ' "Ai fa yau na bani". _ Oga Mahmud ya ce, "'Haka yau na wuni. ‘ ina rigima da ita ni da Madam dana gaji da lallashin ta ne na ce ba zan kawota ba, amma ta dasa mani kuka dole na kawo maka ,ita don haka sai ka samu ka lalabata da kalamai ka “samu ku rabu lafiya"; , ‘ . Abubakar ya ce "An gama YallaBai". . ’“ Sun ’dan jima suna hira‘ kafin 'Oga' , Mahmud ya tafi bayan Abubakar‘ yai mashi rakiya ya dawo kai tsaye dakin baccin . Rukayya yai tsinke. ' A zaune ya .samesu Saman Carpet da .alama‘wata rigimar ce suke yi da Ruqayya. .Abubakar 'ya‘ durqusa har qasa ya gaishe da Kaka, Kaka ta dauke kai tana fadar: kai"Ni ba gaisuwar kace ta kawo ni ba : kaji" Abubakar ya saSsauta murya yana fadar. "Allah Ya‘ huci zuciyar ki kuma sai kika yo tafiyar dare haka maimakon ki kirani nazo da kaina na daukoki?” . Kaka ta» hayayyaqo mashi, "Motar banza gareka ‘motar wofi, da ka dauke ni da motarka ai gara na taho‘ a qasa tunda kai ba mutumin kwarai bane". ' Ruqayyar tai saurin kallonta tare da Bata fuska alamarbata jin dadin abinda take yi mashi, Kaka ta banka mata harara "Kike wani Bata fuska shegiya don ina kwatar miki' yanci shi ne kike Bata rai? To ba : zan fasa ba". Ruqayya ta mike tana fadar, "To shi kenan, ki cigaba‘ bari injr in hado maki abinci". ‘ ‘ Bata saurari abinda zata ce ba ta fice ta bar Abubakar da rigimar ta. _ Kicin ta shiga ta jajjaga kayan miya sannan ta kunna cookcr‘ gas ta dora tukunya ' Farfesun 'yan ciki ne tai mata wanda yaji kayan yaji, sannan ta soya‘ mata indomie_ da kwai, ta koma ta tafasa mata ruwan zafi a ‘ 'flask ~ta dauka ta nufo . falonta Da mamakinta sai ta iske Kaka ta Saki, Abubakar na ta zuba' mata uban“ dimi' tana dariya. Rukayya ta KaraSo‘ cikin falon ta ajiyeWa ' Kaka abincin. Labarin "tafiyar Suhailat gidansu ne Abubakar ke bawa Kaka. " a' Abin mamaki ta saki lokaci daya har da ‘su dariya, Rukayya taja ta zauna tana fadar. "Ga abinci nan kici kaka, kada ki biye mashi yai sanyi". _ Kaka ta ja farantin ta soma ci ana hira, sai aunawa Suhailat zagi take tana ‘roKon Abubakar kada ya sake ya maida‘ ita. Shi‘ . kuwa ya samu yanda yake so, ya shawo ‘kan ‘kaka don. haka ya saki baki sai sheka uban dimi yake, da wanda ma akai da Wanda ba ‘ai' . ba., . -' Ganin babu dama yasa Rukayya ta mike tana fadar. "Ni kam sai da safenka, bacci nakc ji" Abubakar yace "Au ban gane ba, kina nufin don Kaka tazo sai ki kyaleni na kwanta ni kadai Rukayya ta dauke kanta tana fadar. "Sosai ma kuwa". Ya‘ kada kai yana fadar, "Ashe kuwa zamu kwana a gado guda". , Kaka ta dauki salati cikin daga murya tana radar ‘ "Dawa zaka kwanan tsohon marar kunya to Allah Ya tsare ni yin kwai ban tanadi zakara ba. Kaji na gaya maka ba dani ba Jika maza ki bishi ku tafi sashenku sai da safenku". ‘ Shi Abubakar ma dariya Kaka ta bashi, 'yanda ta zage tana ta soko zance ta inda take ' '. shiga ba tanan take fita ba. Rukayya kuwa , haushi ne ya Rumeta don a yau burinta ta kwana tarc da Kaka susha hirar su, don haka tun da suka fito Abubakar ya tsaya jawa Kaka kofa bata jirashi ba tai gaba abinta tana ta faman gunguni Bai shigo ba saids ta zira doguwar rigar baccinta da ta gani ajiye a gefen gado sabuwa kar alamar ya shiryawa, zuwan nata bangaren ' nashi a ya‘u. taa haye kan gadon ta ja bargo ta luliuBejikinta. . Abubakar bai shigo ba saida.yajé yai', , sallama da‘maigadi sannan ya nufo Bangaren nasa. Bai 'yi mamakin ganinta da yai a * kwance duk da yana da yakinin ba bacci take ba, don haka hankalinshi kwance ya sauya kayan jikinshi zuwa doguwar rigar bacci ya dauki turarensa ya fcsata kowacce gaBa ta jikinsa sannan ya hayo kan gadonYa kashe wutar dakin kafin ya kwanta tsawon lokaci ya dauka yana faman saka da warwara a . zuciyarsa kafin daga karshe ya kira‘ sunanta. '” "Rukayya". Ta amsa a shaqe saboda haushi da kuma kuma bacCin da ya fara kamata Abubakar ya miqa hannu ya yaye lulluBin da tayi yana fadar. ' "Barci fa kike koqarin yi, k0 kin manta ' da alkawarin. da kikai min?" Rukayya ta bude idanuwanta wadanda suka faraja, ta cr ' "Alkawari kuma na me?" Abubakar ya mirgina daf da ita ya sa hannuwansa ya tallabo qeyarta sukaiwa juna zuru na 'yan daqiqu, kafin ya ce "Yanzukina nufin har kin. manta da alqawarin da kikai min za ki bani kanki? Haba Rukayya ‘na soma tagayyara, plcasc ki ‘ taimakeni ki tausaya min haka nan". ' Gaban Rukayya ya yi wata mummunar faduwa, ta fahimci abinda yake nufi don haka tai wani saurin janye jikinta tare da juya mashi baya tana fadar. » "Ni dai bahaka nake nufl ba, ka kyaleni kawai inyi baccina". Abubakar yai sukuti yana kallonta, ta ja ,bargo ta lulluBa‘bai da yanda zaiyi haka ya kuma da ,baya ya kwanta. Bai da-burin ya' takuraWa yarinyar k0 kadan, yana jin tausayinta don haka ba zai iya yi mata komi ba sai da yardarta. Sai dai duk yanda'yake zaton al'amarin ya wuce nan, don gaba daya bacci ya qauracewa‘idanu wansa ya rinqa juye-juye har dare ya .raba idanuwansa kyam, don haka' ' ya mike ya fada (toilet) ya dauro alwala ya fito ya soma jera nafilfili na neman sauki a wurin Ubangiji. Washegari tunda sukai sallar auba Abubakar ya koma ya kwanta yana ta faman ramuwar bacci, 'ita kuwa Rukayya tsam ta miqe ta dauri zaninta saman rigar baccinta ta fito ta dawo Bangarenta Bata shiga dakin baccinta ba kicin ta nufa ta soma diminiyar hada abin karyawa Doya Ce ta soya da kwai sai tai masu yam ball sannan ta dama kunun tsamiya. Sai data gama tsab sannan ta gyara falukan gidan k0 ina da ina‘; hatta na sashen Abubakar din wanda keta faman ramuwar bacci. Karfe kawas da yan mintina Rukayya ta kammala komai ta nufi dakin baccinta ta ~ 'zaune ta samu Kaka da ‘zurmemiyar casbaharta tana ta ja. Rukayya ta waro ido tana tadar ., . . . .-"Kai kaka, ba dai wai har kin tashi ba‘?" , Kaka ta ce"A'a ban tashi ba, sai yunwa ‘ta kashe ni. Kuje ku kwashe wuri kuyi ta narkar bacci, wato ni kuma da yinwa za'a horar ‘ dani ko?" . Rukayya ta rike baki tana dariya, ta ce..“Wacc ni da daura zani uwar miji-na yawo xindir? Wallahi banyi tunanin kin farka ba, don tun dazu nagama hada abincin karin na tsaya na tsaya gyare gyare". ‘ Kaka tace To naji, kawo-mani nawa sarkin . aiki". “Rukayya ta ce"A'a bari dai na hada maki ruwan wanka ki fara watsawa tukunna ., Kaka tace "Wanka’kuma tun uwar safiyar nan 'sai kace wadda janaba ta hau. jika? To ban iya wannan bidi'ar ba,kawo mani abincin idan naci na koshi rana tayi nayi wankan". ' Rukayya ta fice tana murmushi, rigimar ,kakakam aisai ita. I . A kicin ta shirya kayan abincin gaba" daya a .saman qaton faranti ta kawo mata, ' _ Kaka ta sauko saman carpet tana faman mita an barta yunWa zata kasheta. ‘ ' ' Rukayya dai na. jinta ta share ta zuzzuba mata kOmai ta tura mata, Kaka ta dubeta ' "To keba zaki karya bane Rukayya‘. ’" . Tai munnu‘shi kafin ta ce "Sai goma ,_ tayi ke dai ki fara karyawar ki". Kaka ta tabe baki ta soma karyawa tana fadar . . "Ai ku .dai kuka sani indai kayan gulma ne ku biyewa yahudu da nasara suyi ta . sauwwara rayuwar ku Yanzu In ba haka ba da kinyi kyan gani don wallahi duk macen dake zama da kwarzabar miji indai bata Ci _ tana koshi to yanzu ta lalace Rukayya ta ce "To wai kewa ya ce miki bana cin abinci.?_ Ta cE? "K3 tashi can, k0 baki zauna tarr dani ba ina gani. Kin san Allah ki kula da kanki kar ki sake kiyi wasa da cin abinci tunda dai mijinki bai rageki da komai ba to karki sake ki’bari ki .lalace, don irinsu Abubakar ne kesa mace duk ta fita ' ‘hayyacinta, don haka ki dage. Sai kuma kina yi kina gyara kanki, don dake wata ce ki aika a siyo miki. kaza da kaza da kaza da kaza lol « Rukayya nadai sauraron Kaka har ta gama zayyano mata zancen sannan tai murmushi tana fadar. “ "Lallai Kaka, kice abubuwan suna da yawa" _ Kaka ta ce, "Kadan ma kika Ji Jika, don akwai saura ba ka_dan ba, irinsu sa maza kuwwa, gumbar maza.. .ke da dai sauranSu". . Kaka ta datSe zancen saboda shigowar Abubakar cikin dakiri . Yana shirye cikin kayan tafiya (office) ‘ sai da ya durqusa ya gaishr da Kaka kafin ya gefe ya zauna yana hararar Ru‘kayya wadda keta faman gaishe shi.’ Rukayya ta zaro ido tana fadar, “To ni kuma me nai maka yaya Abbakar kake. hararata?" . Ya~ce, "Au, baki ma san abinda kikai mani ba kenan? kina jinta fa Kaka? Bayan bata tayar dani ba ta barni ina'ta sharar barci har na , kusa makara wurin aiki, sannan bata hada mani . k0 ruwan wanka ba' ballantana ta ciro mani kayan da zan saka, amma wai batai min laifi ba". Kaka ta watsa mashi .kallo tana fadar. "Eh lallai yai maka dadi, wato ka hanata barci da-daddare kuma da safe kace duk ita ce zataimaka wannan bautar? Lallai samun wurin :naka ma yayi yawa": . '. Abubakar yai dariya 'yana kallon Rukayya wadda ta dauke idanuwanta daga kansa, ya ce . , "Yanzu ita ce ta gaya miki na hanata ’ barcin k0 kuwa?" ' Kaka ta ce "Ban sani ba, marar kunya Ni idan ba zaka karya ba tashi mujc ka maidani gida don na gaji da zaman gidan nan naka da babu tsiyar dake ciki sai rashin kunyar ka". Abubakar ya kada kai yana dariya kafin ya 'ce. . "To ai ke kika nema, haquri xaki yi ki bari sai anjima idan na dawo daga (office) sai na maida ke". , Kaka ta mike tana fadar, "Wah! Ai dolen ka ma ka maida ni yanzun nan, na gaji dai _ zaman gidan nan da nake don na lura baka da ta ido". ‘ Abubakar ya saki hannun Rukayya da ya fakaici idon Kaka ya rike ashe ta ankare, yaja tiren abinci gabansa ya soma ci yana fadar. "To ai k0 abincin ai mun haquri inci ‘tukunna ko~Kaka ta kyale shi ba tare da ta sake tankawa ba ya cigaba da.cin abincin amma gaba daya hankalinshi da Zuciyarshi suna ‘ wurin RUkayya sai a yanzu ya qare mata kallo a cikin rigar baccin dake jikinta lallai Rukayya ba qaramin kyakkyawa bace ' Tabbas ba ma kaka ba dake tsohuwa ba hatta Karamin yaro idan zai kalli irin' kallon da ‘Abubakar ke wurgawa Rukayya zai iya fassara . shi da ma'anoni da dama. Da kyar Abubakar ya gama karyaWar ya dauki Kaka suka tafi yana‘faman mitar zata makarar dashi. ' Suna tafiya rukayya ta fada (toilet) ta watso ruwa ta fito ko .mai._;bata shafa ba ta zira milk din doguwar riga marar nauyi komai bata shafa ba ta dauki turarenta mai sanyin kamshi ta fesa tabi lafiyar gado. '_ Misalin karfe shidda ' na yamma Abubakar yana zaune a (office)_dinshi hadari ya soma har haduwa da alama kuma idan har ruwan ya kaucewa mutum akan hanya to zai gane kurensa don da alama ruwan zai zuba bada wasa ba. . _ Abubakar ya qurawa sararin samaniya ido ta tagar (office) dinshi yana kallon yanda hadarin ke ta haduwa samaniyar tayi baKiKqirin-sai iska ke tashi tare da buji mai karfl. ‘ Abubakar daya tura kanshi a saman karfen tagar yanajin’ wani irin abu na tagaya . mashi. zuciya, son Rukayya 'ne‘ k0 kuma sha'awar kasancewa da ita ne oho. Shi dai abu daya ya sani shi ne 'idanuwanshi na bukatar’ ganinta hancinshi na bukatar shakar daddadan kamshin jikinta, burinshi kawai ya rungumeta da hannayensa ya hadata da jikinshi, shi k0 hakan kadai ya samu buKatarsa ta biya. ‘ Kamar Wanda aka tunzura yai baya da sauri ya soma harhada takardunsa da duk wasu komatsansa ya cusa a jaka 'ya zuge ya rataya ya . suri mukullin motarsa ya fice Da gudu-gudu ya nufi motarsa, yasa makulli ya bude‘ motar ya shige saboda ruwan da ya fara saukowa. A gurguje ya iso gidan nasa, a lokacin kuma ruwa ya kece kamar da bakin kwarya. Don haka lokacin da ya 'faka motarshi a harabar gidan da gudunsa yashige falon gidan hakan kuWa ya yi dai dai da‘ tahowar Rukayya , ~ da zummar ta zuge labulayen ”kofar sukai . karo da Abubakar wanda ya shigo da gudu,’ ' goshinta ya bugi kirjinshi. Tai saurin komawa da baya dafe da goshi tana fadar ' “Wayyo Allah na, kai Yaya". ‘ Abubakar yai saurin janyota jikinshi < yana fadar "Ayya, sorry baki‘ ji ciWo ba k0?" Rukayya ta shafo goshin nata da hannunta ta ‘ dubi Abubakar yai dariya yana fadar . “Saboda sharri wato har kirjin nawa ya

Chapter 12 of 13