Share this page
albashi ba. Don' haka Abubakar ya nemi aron Naira dubu wurin abokinsa, yana dawowa gida k0 dakinsa bai shiga ba ya nufi dakin Kaka. Tans zaune ita' da Rukayya suna cin abinci, Abubakar ya ce Yau dai'na fita Kaka, ga kudin dinkin wannan mummunar da ake ta yi min mita kullum, na huta da ciwon baki_ Kaka ta dauka tana fadar, “To ka kuwa kyauta, amma da har na fara tunanin k0 in siyar da dan maraqina in amso mata dinkin nata,dashine don ‘ na dauka baka da niyyar amso mata".‘ Abubakar yace Hmm! Kaka kenan, ai gashi nan na ranto nabada, na huta . ’ Ya wuce zaure abinsa ya shige dakinshi. Rukayya ta warci dubun tana tsallen' murna, tace. “Kaka baje na karbo?‘ Ta ce, “Jeki ki karb0 abinki kiyi sauri, ko Yan iskan yaran garin nan sun tsokane ki kar ki kula su“. Ta ce, “To kaka". Ta dauki hijabinta tana tsallen murna ta fice. Tana shawo kwanar gidansu ta hango yara sunyi dandazo ana ta kade kade jikin Rukayya har ciri yake ta nufi wurin, inda ake_ ta ihu, "Ga 'yan kura. ga 'yan kura masu wasa da kura)" sai a kwasa aguje ayi nan riii, ayi nan rii Rukayya ta samu abinda take so, ta ma ~"mance da aiken da akai mata, ta rufawa sauran yara baya suka shiga bin masu wasa da kura, sai da suka zagaye garin kaf. . Ita da aka aika tun wurin la'asar amma har duhun magariba ya keto babu ita babu labarinta. ' ‘Hankalin Kaka ya tash ta leqa dakin Abubakar ta kwalla mashi 'kira, ya fito yana fadar. "To wani abin ne kuma k0?" Kaka 'tace tunda fa na bawa Rukayya kudin dinkin nan taje ta karBo har yanzu bata dawo ba". . Ya ce”To sai me Kaka? Idan ta bata ba mun huta ba, kema kin zauna bakin ki ya huta". Cikin rikicewa ta ce, “a bakin ka ba mara mutunci me bakin tsiya, bari inje ni na nemota dukma indata shiga". _ Tai waje tana mita, Abubakar yai murmushi wanda iyakar sa saman laBBan sa, ya koma dakinsa ya sanyo rigar sa ya fita ya ja gidan ya nufi hanyar neman ta, duk inda ya ga dandazon yara sai ya je ya duba amma babu ita. Yana Shawo kwanar gidan Maigari ya hango dan- dazon yara suna bin ‘yan kura. 'Tabbas tana nan ciki". ‘ _Abinda zuciyar shi ta ce mashi kcnan, ya shiga kutsawa yana neman ta. Can gaba-gaba ya hangota ita da wata yarinya suna ta rabzar fada, sai qokarin raba su ake sunqi rabuwa, da alama ta sami 'yar masifa irinta. Abubakar ya kutsa ya riqo hannunta, tana ganinshi kuwa 'yan cikinta suka rikice, idanuwan nan suka yo war waje. Yanda ya riqo ta haka ya rinwa janta har" gida ya hankada ta tsakar gidan, Ya dauko igiyar guga ya shiga zabga .mata tana ihu. . Bai ji shigowar ta ba sai dai yaji kukanta. "Kashe ta zaka yi? Jama'a ku taimaka, zai kashe marainiyar Allah". Tana ganin kakar ta kwasa aguje ta rugungumeta tana ihu, kaka tace "Cewa naika kirata ka duke ta? Ba 'ccwa nayi ka nemo min ita ba?" ‘ Cikin takaici Abubakar ya cc, "Duk abinda yarinyar nan~ke yi duk laifin ki ne, ke ke lalata ta. Wallahi indai ni zan ci gaba da saka hannuna a cikin lamarin wannan to wallahi dole ne in hukunta ta tunda dai ita haka Allah Ya yi ta bata jin magana k0 miskala . zarratin, kuma harda hadi da kin shagwaba ta, kinsa ta raina kowa, bata .ganin kowa da mutunm, to ni dole na hukunta ta wallahi" "Ina Naira ta dubu‘?!". ‘ ' Ya daka mata tsawa, tai saurin sakin kaka tana lalube-lalube a jikinta, har' da su kwance kallaba tana dubawa. Abubakar‘ yai murmushin takaici kafin ya ce, "Kin yar k0? Da kyau, kinwa kanki don wallahi tallahi sai dai kiyi sallar haka, fada kuma kar ki fasa, ki tayi, ban ce ki daina ba". ‘ Ya yar da igiyar gugan ya wuce dakinshi abinshi. Rukayya ta kara fashewa da kuka, "Na ' yar da kudin Kaka wurin kallon' yan kura, bari inje in dubo". ‘ Kaka ta ce, "Ya za ai ki gansu Jika? Ai ba za ki gansu ba, kiyi hakuri kawai in lallaBa shi ya Kara miki". . Cikin kuka ta ce, "Ai ba zai Kara min ba". . Kakata ce, "Ya. ma isa? Share hawayen ki, ki na_ zaune sai ya kara su k0 da ya rantse sai dai ya yi azumin kaffara". Rukayya ta share 'hawayénta tabi kaka dakinta tana fadar. "Dubi, inda ‘duk ya ji min ciwo, wallahi yana tafiya sai na rama a wurin ragunan sa". ‘ Kaka ta ce, "Shcgun ragunan ma da . kullum ke ke dawainiya da su amma bai gani, kullum ya kama ki yai ta duka. Wata rana sai na baSu shinkafar Beta sun Ci sun mutu inga ta tsiya, kema ki hula. Allah Ya 'soki ma an kusa kwashe su ki sami sauki" Rukayya ta ce"Shinkafar Bera ita ke kashe su Kaka?" Ta ce"Sosai ma, ai k0 ke kika ci sai kin . mutu ba raguna ba". * Rukayya tai shiru zuciyarta na saqa da warwara. Kaka tace, Tashi ki dauro alwala kiyi sallar magariba".' ' ‘ . “Bata ce Kala ba ta miqe ta nufi wurin da . ake ajiye butoci ta dauka ta nufi kewaye Ana gobe daren sallah Abubakar ya karbo dinkunan sa dana Kaka ya kawo mata yana nuna mata. Rukayya na kwance saman gado tana kallon su, dinkunan shi kala uku, na Kaka kala biyu. . Sai data gama ganin nata sannan ta ce. "Ina na Jika?" ‘ . Ya ce ”Wacce Jika Kaka? Ai na rantse tunda ta zubar da kudin wurin fada ba zan qara fitar da wasu in bata ba, wallahi sai dai tai sallar haka". _ ' Kaka ta jefa mashi nata, "Ai ko indai ba _zaka amsowa Jika nata ba to nima ban so, wallahi sai dai ka hada duka ka rike". ‘ Abubakar ya ninke kayan da ta jefa masa suka zube qasa, ya ce_ "Ba zan tafi da su ba, sai dai in kinji ' haushi ki kyasta masu ashana su qone, koki bada sadaka duk daya wai makafi sunyi dare, kinga tafiya ta". Ya wuce abinshi ya bar mata kayan Rukayya ta fashe da kuka tana harbeharbe da ta tabbatar ya tafi Kaka ta ce, "Ke yi shiru Jika, ai dama so yakc ya‘ sa ki_ kuka, idan kika yi ai kinga yai nasara Ki kyale shi dole ya amso miki dinkin Inma bai amso ba sai ki saka wadannan nawa Tana kukan Rukayya ta ce, "Wadanne zan saka? Wannan dinkin tsaffin su zan saka? Allah Ya sauwake" . ' Kaka ta ce, ”Ba sai ki ba da su a rage miki ba?" Ta ce, "Allah Ya sauwake ni dai ban son su, nawa nakeso". . Kaka ta ce, "To kiyi shiru haka nan muga iya gudun ruwan sa". Ta samu da kyar tai shiru,“ amma zuciyarta na mata sake-sake kala-kala. . ' ' ‘ Cikin dare duk sun‘ kwanta barci amma Rukayya ta kasa barci saboda tunanin rashin kayam sallah, ta tashi zaune tana tunanin abinda zata yi itama ta‘ guma masa. Can ta tuno'da shinkafar bera da Kaka ke ajiya a karkashin gado saboda Beran dake matsa masu. Ta lallaBa ta dauko ta tamkar wata munafuka, tai sadaf-sadaf ta fita waje ta sami kwano ta zuba shinkafar ta zuba 'ruwa ta lallaba ta nufi wurin ragunanshi. Duk sun ma yi bacci,‘ ta girgiza gudayana motsawa .ta miqa mashi. Kamar jira yake ya kafa kai ya sha sosai.‘ Ta nufo gudan tana girgiza shi, yai kuka "Beyyy!‘ tai mugun tsorata ta zubar da ruwan. ‘ ta ruga daki aguje ta kudun dine saman gado. K0 minti biyar batai da kwanciya ba taji ragon ya soma dire. dire, Abubakar ya fito daga . .dakin shi hankalin shi tashe, ya kwance ragon yana duba shi. ' Ragon ya fadi yana harbe-harbe, Abubakar ya rude yai dakin Kaka aguje ya tayar da ita yana fada mata rago ba lafiya, ta rude sukai waje. . A lokacin har jikin ragon ya saki, sai kumfa da ke fitowa daga bakinsa. Kaka ta ce, "Maza dauko wuqa ka yanka shi, gazawa zai yi". Abubakar ya juya ragon ya kalli gabas, ya ce "Bismillahi, Allahu Akbar". Sannan ya yanka. , Jikin Abubakar ya mutu saboda gazawar ragon nasa, duk cikin ragunan yafi kowanne girma, Naira dubu hamsin sukai cinikin sa gobe za a zo a dauka. Don haka babu wani kuzari a jikinsa ya tafi daki ya kwanta, sai dai batun barci babu‘ labarinsa, ita kanta Kaka sai data dau lokaci kafin baccin ya dauke ta. Rukayya k0 dadi ne dankare a zuciyarta, tana labe tana kallon su. Yanda ta ga Abubakar ya rude sai yai nan aguje ya dawo nan aguje dariya kawai take masa har da rike cike, ta rufe' baki don kar wani yaji ta. Tunda sanyin safiya Abubakar ya tashi ya tafi, ya kira mahauci don 'siyar masa, gashi ranar sallah. ' Tare suka dawo da mahaucin, ya duba ragon yai masa kudi dubu ishirin. Babu yanda ya iya haka ya ce ya bayar, a take ya kirga kudin ya bayar sannan Abubakar ya tafi dakin Kaka ya fada mata yanda aka siya Kaka ta ce ”Anya Habu ragon nan bai mutu ba aka yanka?" . Abubakar ya ce, ”Kai Kaka, Allah Ya sauwake, sai kace dai ba Musulmi ba zan yanka mushc? To ko da na yanka shi sai da ya harba, yanzu inda gabansa kika fadi wannan ai kinga ba zai siya ba". . Kaka tace, 'A'a, ai nidama ban sone ka aikata abinda Ubangiji zai yi fushi da kai ne' . Abubakar ya ce, “To bai mutu ba na yanka, yanzu ma buhu zaki ara mana zai fede anan. Kaka ta ce, "To bari in duba maka” . Rukayya ta mike simi-simi ta raba Abubakar ta wuce tamkar wata tsohuwar munafuka, ta nufi wurin mahaucin tace masa ‘ "Baba ragon nan sai da ya mutu aka ‘ yanka shi, kar ka siya". Mutumin ya zaro ido yana mamaki, kamin yai magana tai saurin rugawa daki abinta ta haye kan gado“ Kaka ta zakullowa Abubakar buhu a Qarqashin gado ta bashi, ya fito. "Yauwa ga buhun Baba Halliru". Da yake haka ake kiransa a garin. Ya ce "Riqe shi nan wurinka Abubakar, bani kudina". Gaban Abubakar yai wata irin faduwa, ya ce "Saboda me Baba?" ~ Ya ce "Saboda ni ba mutumin banza bane irinka da zan siyi mushe in saida wa al'ummar Musulmai. Ba "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Baba wallahi ba mushe bane, ni na yanka shi da hannu na wallahi". ' Ya ce”Kai kaga ni dai ba abokin wasanka bane, ka bani kudina kawai ban siye na fasa Kanwar ka da bakinta ta fada mini mushe ne ka yanka. wato ga mutumin banza ko Idan bakwason wannan littafin kuyi magana mu canja zallah shared a profile . RIKON KAKA CHAPTER5 zaka siyar mawa, to ban siye, ka bani kudina kawai". ‘ Sunan qanwarsa da ya ambata shiya bugewa Abubakar 'dukkanin gaBoBin jiki, jikinsa a sanyaye ya sa hannu ya Ciro kudin a gaban aljihunsa ya mika masa. Ya amsa yana fadar, "Mutanen banza kawai gaku Musulmai amma kuna aikata aikin kafurai, marasa tsoron Allah kawai". Abubakar dai bai tanka, masa ba. har ya fice banda zafi da:. Kuna babu abinda zUciyarsa keyi, yaji ya tsani ragon, bai son ma gaminsa Yajasa ya fita waje ya sa yaro yai masa sallama da makwabcin su malam Bala talaka ne . Yana fitowa suka gaisa da Abubakar sannan ya ce ' "Baba, dama ragona ne zai gaza, nasan kana jinmu ma wata kila jiya. To shine na yanka, yau na kira mahauci ya taya min shi yanda nake jin ba zan iya siyarWa ba, gara ma na ba da shi sadaka na San ladan tawa tana wurin Ubangiji tunda mu ma za muyi layya shi yasa na ce bari inzo in maka magana ka aika a dauko maka". Malam bala ya shiga godiya yana zabgawa Abubakar addu'a, shi dai bai ce komai ba ya wucc ya koma gida, Malam Lado ya turo yara suka daukar masa ragon. Abubakar ya dauki buhun ya maidawa Kaka, ya ce ”Ga buhun ki". Kaka ta ce ,"Yo ya fasa fedewar ne?” Abubakar ya ce, "Hmm! Idan kun bari ba Kaka ta ce, "Kamar yaya kuma in mun bari?" Ya ce, "Kamar yanda kika kitsa mata taje ta sanar da mahaucin mushe ne na yanka”. Kaka ta dauki Salati da sallallami, kafin Ta hau rantse-rantsen ba ita tasa ta ba". Ta ce "Ke Jika, wannan kuma wacce dabi'a ce za ki tsiro mana da ita ne?” Abubakar ya ce, "Wadda ki ka' koya mata, duk abinda fitinanniyar yarinyar nan ke Keyi kaka daurin gindinki ne take samu. Amma ba komai, ni nasan maganinta, ba zai yiwu yarinyar nan ta sangarce ta lalace ba, tunda har ta iya wannan gaba ban san abinda zata yi ba, idan ta Kara girma a haka to abin kuma sai yafi haka. Don haka makarantar boko zan saka ta, taje can ta koyi tarbiyya". Kaka da dauki Sallallami, "Wa za ka kai makarantar Abubakar? Jikar? Baka isa ba, wallahi babu inda za ka kaita a lalata marainiyar Allah. Ka kai ta makaranlar boko ta koyi tarbiyya k0 ta koyo iskanci?" Abubakar ya ce,"'Oho dai, ni dai na fada miki, k0 kina so k0 ba kya so sai na kaita". . ‘ Ya juya ranshi na suya ya ’bar‘ dakin, . yana jin Kaka na rantse-rantsen babu me kai mata jika makaranta. Anci sallah lafiya, Kaka tayi layya ta yanka dan marakinta, Abubakar bai yi ba don gaba daya ya sai da ragunan sa,. ya ce kuma ya gama kiwon. Jika kuwa kayan Naira biyar bai siya mata ba, haka tai sallar da tsofafin kayan ta, shi ya saka ma ko kofar gida bata leqa ba _ Ana gama hutun sallah Abubakar ya je yai wa Rukayya takardar; haihuwa, washegari ranar Monday tun da sanyin saflya ya sa tai wanka ta sauya kayan jikinta, sannan ya tisa ta gaba suka tafi. Kaka tace, "Wai gidan uban wa zaka kaita ne Habu? Na fada maka kar ka sake ka kaita makarantar bokon nan, ban son ta”. Abubakar ya ce, ”Ai ko sai dai kar ki so . ta, amma makaranta na kaita na gama". Ta sa kuka, yana jinta ya tisa‘ Rukayya gaba suka ficce, can tsakiyar garin makarantar take Sha ruwa Primary School, suka dauke-ta aka kaita a‘ji uku, saboda ta wuce dauka. Suna dawowa yaje ya yanko mata (uniform) ya sai mata jakar makaranla da takalmi, sannan ya sai mata littattafai. . washe gari da kanshi ya tayar da ita ta: shirya ya tisa ta gaba har kofar makarantar, ya bata Naira ishirin kudin tara; sannan ya wuce wurin aikinsa. Rukayya 'yan makaranta, karfe sha biyu aka taso su daga makarantar, amma idan ka ganta ba zaka ce ita ce tajc makarantar da sabbin kaya ba, tai musu budu-budu, farar abayar har ta fita daga kamannin ta. ‘Tana dawowa gida ta fada jikin kaka tana murna, Kaka ta ce "Oh Jika da tsiya dai Habu sai daya kai ki makarantar nan don yasan ba yanda zan yiko?" Rukayya ta ce "Kuma Kaka sai da aka buge ni, dubi baya na". Ta cire abayar ta nuna mata, wurin yayi ,rudu-rudu da zanen bulala. ‘ Kaka ta ce, ”Wane dan iskan marar imanin ne yai miki wannan dukan? Shi yasa na ga fuskar ki ‘ da zanen hawaye". Rukayya ta ce "Wani malami ne, wai daga muna fada ya ka mani yai ta bugu ni kadai”. ‘ Kaka ta ce, ”Matsiyaci, ya kama ki yai ta duka, to Allah Ya isa, tsinanne lnsha Allah bai gamawa lafiya, kawai ka kama 'yar marainiyar Allah kai ta bugu kumar ka sami mandiri. Bari Habu din ya dawo Jika, wallahi ba ki komawa makarantar, sai dai yai duk abinda zaiyi, dauko furar ki gata can ki sha". Rukayya ta mike ta dauko kwanon furar tana sha, ta ce. _ "Kuma Kaka har Turanci aka koya mana da waka, amma wai (This is a boll, These is our Apple, That is your watch)". Kaka ta tintsire da dariya har saida sashinta ya fito saboda bakin ba haqora, ta ce. ' "Kai amma abun da dadi, duk can aka koya maku?“ ' Rukayya ta ce, "Eh Kaka". Ta cc, “Ai don dai azzalumin mutumin nan da kin Kara zuwa". . . Rukayya tace. "Ai ban Kara zuwa nima tunda buguna ake". . Da yamma likis Abubakar ya dawo gidan .ya iske Rukayya da kayan makarantar duk ta: musu duwan-duwan, takaici ya cika Shi Duk inda wata qazamar yarinya ta kai rukayyah Tafita: Kazanta , daga cikin abubuwan da sukesa yake qara tsanarta. Ya watsa mata idanu babu sauqi a fuskarshi,yace 'Wuce kije ki cire kayan ki kawo su wurin maguji'. Ta mike a tsorace ta nufi dakin nasu'. Ya tsai da ita, 'Tsaya ki tattaro dukkanin kayan daudarki kawomani'. Rukayya ta daga kai Ta shige dakin, shi kuma ya wuce Washegari yana tashi ya nufi dakin Kaka ya tashi rukayyah tai shirin makaranta Kaka tace kai babu inda zataje donka jini nan jiya suka kamata sukaita bugu kamar jaka don haka bata komawa Abubakar yace,'ldanta zauna nan me zatai miki? Nan makarantar allo ce kikai kane kane kika hanata zuwa wao bugunta ake , sannan kuma itama makarantar bokon sai ki hana? To wallahi .ko kasheta za a rinka yi tana dawowa sai taje har makarantar allon sai ta koma“. Kaka ta ce "Tunda dama ba qaunar ta kake ba ai dole ka kaita inda za a kashe ta saboda mugunta, haka kawai ka dauki karan tsana ka dorawa yarinya, ka kaita a kashe ta don Allah, idan an tashi a aiko mani da kai da qafarta gida". Abubakar ya finciko Rukayyar dake kan gado ya jata suka nufi kofa YANA FADAR. ’ ”Ba za, a kashe taba amma fa za ta daku kamar ikon Allah”. Bai ji abinda take fada ba don har ya kai bakin kewaye, ya zuba mata ruwa a bokiti ya bata ta shiga wanka. Tana fitowa ya mika mata kayan makarantar ta saka, ya ba ta mai ta murza ya zaro Naira hamsin ya bata, ya ce. Maza ki wuce ki tafi, kuma zan biyo bayanki yanzu, ki tsaya wasa k0 da labe ne kiga ' yanda zanyi da ke. Kina dawowa daga makaranta ki ka ci abinci ki ka hula, ana kiran sallar azahar kiyi sallah ki wucc makarantar allo idan ba haka ba wallahi kika bari na samu labarin baki zuwa na lahira sai ya fiki jin dadi wuce ki tafi. ‘ Simi-simi ta wuce, daga daki Kaka tace. ”Yanzu baka barin tai kalaci haka za~ ta wuce ta tafi?” , Ya‘ce, "Bata yi, ga Naira hamsin nan na . bata ta siyi abinci ta ci". ' -Kaka tace, "Indai mugunta ce irin taka ai ta wucc da haka Habu, yanzu haka zaka kora , min ita bata ci komai ba salon tai karo da mayya k0 maye su lashe mini ita?” » ‘ Abubakar ya e, ”Su hadiye ta idan ta tafi". ‘ , “ " Kaka ta cc, ”Ba bakin ka ba, me mugun baki. Insha Allahu aniyar ka sai ta bika". . Bai tanka mata ba ya wucc dakinsa yai nasa shirin ya fice ya tafi wurin aikin sa, amma 'yana can sai da aka kawo mashi kashcdi wai Rukayya tayi fada da wani yaro har ta cije shi a hannu ya fasa. Ya basu hawuri sannan yaje “Tana dawowa daga makarantar tana hutawa akai sallar azahar ta fito zata tafi makarantar allo Kaka tace, 'Yanzu zuwa za: kiyi k0? Mugun yaron nan ya hanaki zama lafiya, duk indayasan za a zalunceki saiya turaki Allah Ya saka miki'. . Jika Haka ta wuce makaran allon,.a can sukai sallar la‘asar, Sai biyar na yamma aka tasosu Tana dawowa tasamu Abubakar na gyaran cefane cefane ta giftashi zata wuce ya ce‘ .. ’Kezonan'. , ta dawo gabansa ta durkusa ya dubeta sosai kafin yace ,‘Wato saboda bakeke wankinba shi ,yasa idan kika dawo makarantar baki canja kayan sune na zaman gida kuma sune na Yawo cikin gari ko?‘ Shiru ba amsa, ya ce "Tashi kije ki ciri kayan ki kawo mani". Haka ta mike ta ciro ta dawo da su a hannu, ya ce "Dauki bokiti gaya can da ruwa kisa ki wanke". Gaban‘ta ya fadi don tundatake bata taba wanki ba, shi ke yi mata da kanshi. Haka ‘ ta mike taje ta soma wankin kayan, yana kallonta har ta gama ya amsa ya shanya. . .. ’ Sannan ya ce "ki wanke hannunki ki , xo ki yanka mani alayyahun can da albasa". ‘ Rukayya ta dubi hannun nata babu abinda ya yi amma har sai ta wanke ya ce. ' "K0 baki ji ba?" , Haka ta wucc ta dauki buta ta wanke hannun nata sannan ta je ta zauna tana yankan alayyahun ya dora sanwar taliyar sa,tana gama yankan alaiyahun ya ce Jeki ki zuba" Ta tafi zata zuba cikin tukunyar .yai saurin daka mata tsawa. ‘ "Ke banza, haka za ki zuba shi? Barbada mashi gishin' ki sa ruwa ki wanke". ’ ‘ Ta dauki uban gishiri ta maka yana kallonta ya. ja tsaki ta zuba ruwa ta wanke ta tsane shi sannan ya ce ' "Je ki zuba". ' " Taje ta zuba ta rufe, ta dawo gabansa. "Na gama". Ya ce, "Jeki shi kenan". take ta nufl daki don kar ya qara saka ta wani aikin *** ******* *** Wata ranar Juma'a RuKayya tana . makaranta tai fada da (monitor) din ajinsu wai ta rubuta sunanta cikin 'yan surutu, malamin ya buge su.duka Shine fA yana fita ta ' kama monitar da kokawa' gata ba iya fada tai ' ba, tai mata, duka sosai. Akaje aka fadawa ' (headmaster) yazo da kansa da bulalar sa ya zane Rukayya: radau har tai fitsari saboda . .azaba. Yana fita ta dauki jikkarta ta gudo gida tana kuka, ta fadawa Kaka. Ta ce, "Ai k0 yau sai ya san ya debowa kansa masifa". Ta dauki mayafinta ta ce "Muje inga matsiyaci". ' Ta ja gida ta rufe suka dauki hanyar makarantar har office dinsa ta kaita, yana zaune saman kujerar dake gaban teburinsa sai . wani mutum dake daga can gefe suna magana. ' Kaka ta sawo kai cikin office din ba k0 sallama, ta dubi mutumin dske saman _kujerar gefe tace. ' "Malam wurinka nazo, zuwa nayi inji uban da yasa ka sa bulala ka rinka laftar mani jika kamar ka samu jakka, k0 k0 shi Habu din ' nc da ya kawo ta ya ce ka sa bulala kai ta bugunta harta ‘fita hayyacinta tai fitsari? To kotu zata rabani da kai, wallahi sai nayi shari'a da kai, sai ka bani labarin dalilin bugar mani 'ya babu gaira babu dalili". Mutumin yace Yi hakuri baiwar Allah, bani ne (headmaster) din ba, gashi nan, nima zuwa nayi“. Ta ce, "Karka sake ka zage ni’da turanci wallahi na gaya maka, nima ina da jika kamar ka dan makaranta" ~ Saurayin ya ce, "Ikon Allah, yi hakuri don Allah Hajiya" ‘ ' Ya mike ya bawa (headmaster) hannu sukai musabiha, ya ce. "Ni zan wuce Yallabai, zan kira ka a waya k0 mi kenan". _ Ya wuce abinsa ya bar (headmaster) da rigima. ‘ . Da yake kwararren dan boko ne sai ya mike daga kan kujerar da yake ya ce. "Hajiya zauna, bisimillah sannu da _ zuwa, bari akawo miki lemu". Kaka ta zauna tana fadar, "Karka kaWO mani komi, dan iskan da ya bugi Jika kawai nake nema, wallahi sai na rama mata ,kaji na fada maka Lol ran kakafa ya baci mai zai biyo baya mu tara later a zallah shared a profile . RIKON KAKA CHAPTER6 , Ya' kwantar da 'murya, "Ayi 'haquri Hajiya,ai duk abin bai kai na haka ba tunda ni da Jikar taki ai duka jikokin ki ne,kua zaki' iya‘ hukunta mu idan munyi laifi, ‘ musamman idan ki ka same mu da rashin gaskiya. Kiyi hauri kakata, ba a daki qanwa -ta saboda zalunci ba, ‘sai don laifin da tayi, ta ; kama shugabar ajinsu tai ta bugu Idan kika, ga bugun da tai mats sai kin tausaya matA . shi~yasa. Sanin da nai k0 ke ce kika ga haka sai» kin daki jikar. nan shi yasa‘ na hukunta ta saboda gaba amman kiyi haquri kaka Kalaman sa sun Shiga Kaka don haka ta ~sassauta fadan tace "Gaskiya kar a sake bugar min jika saboda wasu yara can, marainiyar Allah ce uwarta da ubanta duk sun mutu; ni kadai na rage mata. In bacin yaya'nta ma da ba mai jin magana bané ai daga yau bata Kara dawowa' ‘ makarantar". ' Ya ce, "A'a ayi hakuri, insha Allahu za a kiyaye" ta mike, "To sai anjima, Allah Ya _ taimnka". ' Ya ce "Amin Kaka" Ta tasa Rukayya suka ficc daga (ofiicc) din, (headmaster) ya koma ya zauna saman kujerar sa yana murmushi, ya ce. _ "Ho! Allah Ya raba ni da ke lafiya" (Duk wanda ya girmama tsohon wani shima ’za'a girmama nasa a gaban idonsa k0 bayan idonsa Da yamma bayan Abubakar ya dawo ~ daga wurin aikinsa yaji labarin zuwan kaka makaranta, yai ta fada ' "Haba Kaka, .yanzu in bacin kin hadu da dan mutunci ai da Allah kadai Yasan yanda za ayi. Haba! ki ta abu sai kace kanki farai jika? K0 ina sai kin fito da halin ki To, "To ubaba, zoka dakan sai in san kaji haushi: inba dukana kayi ba ai ban ssn kaji haushi ba Abubakar ya ce, "Ai burinki inji haushi in fitar da ita daga makarantar, kuma ba zan fitar da ita ba wallahi ta zo ta dami al'umma, gara ta zauna can duk wanda taimawa a zane ta". Kaka ta ce, "A daketa din ni kuma dukwanda ya bugar min jika idan naji sai naje na rama mata tabbas". _ ‘ Abubakar yace, “To shi kenan ki rama mata din, hukumar makaranta ta sa a kama ki, wallahi kuma k0 leke ba zan leka ba" Ta ce, "In ka tashi ka manta dani k0 kasa a rufeni har dan makullin ya bats" . ' Abubakar yai dariya ya ficce abinsa don yasan halinta idan ya cika ta yanzu ta sa masa kuka, ya tafi ya yo cefancn abinci ya_ dawo ya kira Rukayya, ya ce "Maza kisa tsintsiya ki share gidan nan, idan kin gama ki min magana ya wuce dakinsa ya barta tsaye". Ta sumBuro baki ta rasa dalili kwanan ‘ nan da yake takura mata ba yanda ta .iya, dolenta ta dauki tsintsiya.ta share gidan sannan taje ta sanar masa ta gama. -- Ya fito yace, "Hada itatuwa ki hura wuta, ai dai kinga yanda nake yi?" . Idanuwanta suka ciko da hawaye haka ta je ta hada itatuwan yana tsaye yana' kallonta ya ce.‘ ~ . ."To sa sabulu ki wanke hannunki ki . dauki tukunya ki dauraye ki~aza saman ’ wutar". Haka yai ta saka ta aiki daya bayan ' daya har sai da aka gama girka shinkafa' da miya k0 tsinke bai taBa da hannun‘ saba Yasa ta dibar masa nasa; sannan ya ce. "Daga yau aikin ki kenan a gidan nan kullum, don na gaji komai ni sai kace dan daudu a gida. _ Shekarar ki sha uku amma babu abinda kika iya a aikace-aikacen mata, jikin ki ma ba ki

Chapter 2 of 13