Share this page
dire, Abubakar da‘ ' jikinsa ya gama yin la'asar ya dubi Suhailat muryarsa a raunane, ya ce ”Am sorry (my love) kar ki damu da ‘ rigimar Kaka don Allah, kin san haka nake fama da ita, rigimammiya ce sosai" ~ Suhailat ta ja wani gajeren murmushi, tace"Ba komai (my dear) muje kada ranta ya Kara Baci . ‘ Abubakar ya ce "A‘a, kije kawal daki ki ‘ shirya, kar ki damu zan iya da ita" ' Suhailat tace, "Ahh. No my dear, muje na soma rallashinta tukunna, don ba xanso ta qara fusata dani ba". Abubakar ya ce “A"a kar ki damu kije ni zan ji da ita" ' Ta ce. ”A'a, kai gaban ka barni Dear". Cikin tsananin rudani Abubakar yai ta maza ya bata"rai Wai ya zamu zauna muyi ta gardama, ' nace kije kawai k0?" _ Suhailat ta kafa mashi idanuwa cikin tuhuma, kafin tace. . .' ‘ _ "Anya Dear ‘ba akwai abinda kake ‘kakkarcwa da baka son in sani ba? Meye?" 'Au wai nan zaka girkemu kamar gumaka?” ' Suka ji muryar. Kaka ta daki dodan kunnuwansu, bai iya bawa Suhailat amsa ba ya, nufi wurin kakar a hanzarce ya duqa gabanta cikin rudu yace. “ ”Don girman Allah Kaka kar ki fada :mata RuKayya mata tace wallahi mugun kishi ne da ita", ' Kaka tace "Ina ruwana yau sai dai ya kasheta, kishin karuwar banza. Ai wannan daga gani kasan ta zagaya .ina ganin idanuwannaN nasan tantiriyar' yar... _ Abubakar ya zabura ya dafe mata baki._ yace don 'Allah ki daina kaka, matata cefa kuma, kin san ko a Musulunci babu kyau Irin wannan Daga shigowar ki kita aibata min mata,ba kyau irin haka wallahi". Kaka ta ture mashi hannu. "Kai ni kyaleni kaji, ai dama idonka a rufe yake, ba zaka gane abinda nake fada ba tunda an riga an barbada maka kaci ka sha, kai wanka shi yasa. aka dauro maka aure da yarinya ka. .. . Abubakar yai saurin amshe zancen da ‘ fadar. "A'a Kaka, kar muyi haka don Allah don Annabi, ki rufa min wannan asirin" . Suhailat ta nufo su da murmushin karfin hali a. fuskarta, ta ce. ’ . "My Dear .kar ka damu, indai ta nice to kuwa k0 kadan babu ruwana da duk kalaman da Kaka zata fada akaina don inka lura ai tsohuwa ce. _ _ , Kaka ta dauki sallallami, idan ta dauki wannan kafin ta dire sai ta saki ta dauki wani. ' ' Cikin gigita ta soma fadar, "Yanzu sana'ar da ka soma kenan Hubu? Dama aikin da kake kenan a birnin siyar da giya? Me giya? giya fa Habu? Yau na shiga uku ni Salamatu"; Sai ta fashe da kuka. ‘ Abubakar ya dafe kai "Yau ni na shiga uku, Kaka ki fahimta mana, my dcar ta cc ba wai mai giya ba, kuma hakan yana .matsayin maigidana, k0 mijina, k0 sahibina, k0 me sona, to duk irin hakan ne shi ,ne ita kuma ta maida da turanci, amma'Kaka k0 giya nake saidawa ai ba zata rinka kirana da' me giyar kai tsaye ba k0?" .Kaka ta‘watsa mashi wani kallo, "Uhm! Kai dai. ka sani, ni dai ga matar, ka nan na kawo maka, idan ma kashe ka matar taka zata yi to. sai dai ta kashe ka yau,tunda dai ka zama sauna kira mana shashasha kar ta barka da rai"idan taga dama Rukayya ta dibi tsummokaran kayanta, tana fadin "Kaka tambaye' hi inane dakina naje na share? Suhailat tai saurin Waro ido waje tana kallon su daya bayan daya, kafin kace me idonta ya sauka tace 'Abubakar, ; cikin »wata irin rikitacciyar murya take fadar. ‘ ' ' .. Hmmmmmmm asha karatu lafiya naku har kullum A,I,S kecewa gobema da labarizallah RIKON KAKA CHAPTER14 ”Me kunnuwan suke jiyo min Abbakar? Da. gaska ne abinda kunnuwana keji Abubakar ya shiga dabur-dabur, ya rasa abin fada Suhailat ta dafe kai, ”Innalillahi wa inna ilaihi raji 'un‘! Ka cuce ni, wallahi ka cuce ni, ka yaudareni Abbakar, yanzu dama kasan kana da wannan qazamar a qauye kace mani baka taBa auree ba? Ashe dama kana da mata? Abbakar ka yaudare ni, kasa‘ na mallaka maka zuciyata kaina matsayina na mace ashe ban. sani ba kai daudacce ne'. ba T a fashe da wani irin kuka, "Ka cuce ni, ka cuce ni Abbakar". ' Ta kwasa da gudu ta nufi dakinta. * ' Jikin Abubakar yai sanyi matuqa, hankalinsa yai masifar tashi, yana matukar son Suhailat so irin wanda baki ba zai iya furtawa ba. ya runtse idanuwansa yana jin wani irin abu na tsirgawa a kirjinshi. ‘ . Kaka ta, mike ta dubi Rukayya, ”Taso muje in zaar miki dakinki kinji Jika?“ Abubakar ’ya bude jajayen idanuwansa ya dubeta. ”Kar muyi haka dake kaka don Allah, don Allah ki rufa min asiri kada kisa na rasa matakin... Cikin Bacin rai Kaka ta ce, ”Matsa daga nan Habu . Yandan yaga idanuwanta sun juye a dole ya matsa ya bata wuri, dakuna ‘ne birjik a gidan, kowanne an qawata shi da kayan more rayuwa na zamani. ' . Kaka ta ZaBar mata wani qaton falo mai hade da (bedroom) da (toilet) gaba daya an zuba mashi Naira, da ganin tsaruwar dakin matsayin dakin baki yake. Dadi ya kama Rukayya, sai rawar jiki take. Kaka ta ce. .’ . "Ki zamanki yarinya, babu uban da ya isa' ya takura miki a gidan nan. Ni zan tafi sai na dawo" Rukayya tace"To Kaka, kisa aje gidana na kauye a rufe, a bude na baro shi". kaka ta zabura a rufe kika barishi da gaske ? Rukayya ta daga mata kai tace uhm kinga tafiyata , Rukayya k0 rakiya batai mata ba tana zaune tana ta shafar tayil din dakin da’ katon kafet din dake baje a tsakiyar dakin, ‘ cikin farin ciki ta mike ta haye kan kujera tanata sukuwar murna ' ******* Tsananin tashin Hankalin da Abubakar' yake ciki baya misaltuwa, tunda ya fada kan kujera ya dafe kai bai sake dagowa ba sai bayan minti talatin a haka, kunnuwan shi sai rurin kukan Suhailat suke jiyo' mashi. Yai ta maza ya mike a kasale ya nufi falon da yaga ta nufa, nufa kofar a bude take don;haka ya tura da sallamar sa ya shiga ‘ Tana kwance saman makeken gadonta ‘dakin bakajin komai ciki, sai sautin kukanta. ya nufeta ya duqa gefen gadon gwiwoyinsa a qasa yan fadin "Suhailat don Allah ki dauro kima abinda zan fada miki kyakkyawan kallo da kuma kyakkyawar fahimta. Suhailat wallahi ba,,, ’Yi min shiru Munafiki, mayaudari, mai mummunar manufa. Hum! Ai dama tsiyar talaka kenan, duk yanda ka ganshi a rana yi kokarin kara turashi cikin ranar, inba haka ba kuwa ya sami dama: to kai zai jefa". Ta dan tsagaita tana share hawaye kafin tacigaba. ‘ 'Wallahi nayi nadamar saninka da nayi a duniya, ka tashi ka fice min daga daki, bana son sake. hada ido da wannan. mummunar .. fuskar tAka. tashi ka ficemin Ta maimaita a harzuqe Ran Abubakar yai mummunan vaci, kalamanta sun qona mashi" zuciya, bai san lokacin da ya mike yana kallonta ba ya girgiza kai cike da bacin rai, ya ce "Suhailat kenan, ban yi mamakin fadar wadannan kalaman daga bakinki ba, saboda tun farko nima nayi tunanin'hakan. Amma ina so ki sani, Abubakar bai da matacciyar zuciya ' irin ta sauran maza da kike tunani, kuma idan baki sani ba yau ki sani, ba kudin mahaifinki sukasa na soki har na aure ki ba, asali ma mahaifinki bai da kudin da zai iya biyana. Na soki kuma na nuna miki irin soyayyar da nake miki, kuma ki sani a yanzu a shiryc nake zan iya ajiye duk wani abinda mahaifinki ya mallaka min, sannan na dauke ki na maida ke asalina cikin dangina da' yan uwana. Suhailat, duk da son na nake miki da irin halaccin da ku ka nuna min ke da iyayenki, ba zai sa inyi Karya ~ba don hangen wani abin hannunku.ba Abinda‘na fada miki ada shi zan kuma maimaita miki a yanzu, tunda nake ban taBa .aurc ba, ban taBa sanin wata diya mace ba sai akanki ‘ _ Rukayya Rmqanwata ce marainiya ce iyayenta sun rasu kamar yanda nawa suka rasu Kaka ita ta riqe ta tun tana jaririya cikin tsumma a lokacin nima ina wurin Kaka sa,in da mahaifina ya rasu Aurena da Rukayya Kaka ta qulla shi ta nace saidai in hada Rukayya dake in aura, ganin abin zai zama rigima yasa na amince. Tunda satin bikin nake tare dake ba tare dana leqa inda sukeba kuma bawai don basa buqatar ganinaba a'a sai don kawai naga na kasance da abinda nake so Suhailat idan kika ce don kudin mahaifinki nake zaune dake kin qaskatar da: kanki kin ragewa kanki (qualities) Na rantse miki da Allah Suhailat kin kai ajin da ba namijin da zai kalle ki bai yi sha awar ya mallakekiba, babu shi. Sai ‘” dai ina Son ki sani son da nake miki bazaisa in juri cin fuska daga gareki ba, don a. qarkashina kike ‘ “ Suhailat idan har zuciyar ki bata amince dani ba kada ki cutar da kanki, a shirye nake in miki dukkanin abinda kikc so. Ina saurarenki 2page is missing iya kula wata mace ne balle waccan qazamar?" ' Suhailat tace, "Ni dai zuciyar bata natsu bane Dear, kawai ni dai ka saketa ka maida ita kauyen in har kana so hankalina ya kwanta". Tana fadin sakin sai da gaban Abubakar ya fadi har yana maimaita. "Saki fa?" Suhailat ta daga kai, "Saki kuwa Abubakar, don ba zan iya zama da wata mace a matsayin kishiya ba" ’ ' _ Abubakar yai murmushi kafin ya ce "Suhailat kenan, wannan yarinyar ki dauketa a matsayin 'yar aiki, wannan yarinyar ki dauke ta ' a matsayi 'yar aikace-aikace, wannan yarinyar ki dauketa tamkar baiwa ba mata‘ ba Saboda k0 da Abubakar bai da ke ba zai iya kallonta a matsayin matar da zai yi rayuwar aure da ita ba". Suhailat ta rarrafa ta nufi jikin 'Abubakar ta kwanta, muryarta a sanyaye ta soma magana. "My Dear kai min alqawarin ba zaka taBa kulata ba, ba zaka taBa kusantar ta ba matsayin mace"ba. Abubakar yai murmushi, ya lakacc mata hanci yana fadar. "Nayi sarkin kishi". Suhailat tai murmushi cike da jin dadi, Abubakar ya yunkura ya mike da ita a jikinsa. Muje. mu karya kada yunwa ta kama mu". Suhailat dai batai magana ba sai dai murmushi. Rukayya ta gama duk dokin da' zata yi, ' tana zaune bacCi barawo ya sureta ba ita ta iya farkawa ba sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar.' Ta mike tana faman murza idanuwa, tasha ,bacci matuka. Wata irin yunwa ta bijiro mata saboda bata karya ba, a dole tayo .falon gidan Suhailat ‘ da Abubakar 'suna baje a tsakiyar falon saman kafet ‘Abubakar na kwancc ya tada kansa “da da filon kujera suhailat na kwancee kanta a saman qirjinsa suna kallon (laptop) Gaban Rukayya ya yi wata mumnunar faduwa har ta kusa faduwa saboda tsoro, ta datse bakinta saboda ihun da ya nemi kufce mata. Su duka suka zubo mata idanuwa sai faman makyarkyata take. Abubakar ya yunkura ya tashi zaune, ya daka mata tsawa "Ke Uwar me kika fito yi kika zo kika tasa mu gaba kamar kin sami talabijin? Me kike kallo?“ ~ Rukayya. ta hau rawar murya, "Um.“ Dama...dama... yunwa nake ji ne shi yasa abinci zanci". . ‘ Suhailat ta ce, "Abinci, ki ka bamu ajiya? Tantiriyar mara'kunya, k0 dai kinzo kigag. abinda muke tunda laben da kike bai miki ba?" Abubakar ya ce, “To sai kizo ki wuce ga Sauran. abinci can saman (table) kici, kuma idan kin gama ki kwashe kayan ki kaisu kicin ki wanke ai dai kina jina ko?" Rukayya ta daga kai alamar ce, sannan 'ta wuce simi-simi ta gefensu, Suhailat ta watsa mata harara har da jan tsaki, tace Sakarya, bakauya kawai. Allah wannan da ganinta za tai iyayi". Abubakar dai bai ce komai ba, ya koma ya kwanta ya ci gaba da abinda yakeyi Rukayya taje gaban (table) tana mazurai, shin zata zauna ne koko zatA diba ne ta wuce? Bata da amsa, don haka ta 'dauki filet da cokali ta dibu-iya yanda zata iya cinyewa ta zauna a qasa tanaci sai kace wacce aka tsare sai faman tutturawa take hannu baka hannu kwarya. Abubakar dake kwance ya; hangota dirshan a kasa kamar wata almajira ya tabe baki ya dauke kansa. Tana gama cin abincin.ta mike ta kama tattara wurin, sai data gama sannan ta dauka ta nufi hanyar fita. Abubakar ya ‘ watso mata kira, "Ke mahaukaciya! 'Gidan wa zaki kai?" Rukayya ta tsaya tana mazurai, sai da ya sake maimaita mata tambayar sannan ta ce ' "Fita zanyi in wanke" . Ya ce," Ke, zo ki wuce dallah nazo nuna miki". Rukayya ta dawo ta tsaya sai faman walqita idanuwa take, sai da ya nutsa yasha iska tamkar ba zai tashi ba, nauyi ya ishi ‘Rukayya saboda‘kayan dake hannunta, sannan ya tashi ya nufi hanyar kicin ba tare da ya tanka mata ba. Sai da ya shiga kicins din yana tsaye yana jiranta yaji shiru, sannan ya leqo. "Ke uwar me kike anan tsaye?" 'Rukayya tai saurin binshi, bai ce ta sauke*' kayan hannuntaba, ita kuma tana tsoron ta. saukc tai laifi “haka-ya shiga nunnuna mata yanda ake amfani da kayayyakin na‘urorin dake kicin din gaba daya, sannan ya ce "Muje'kuma (toilet) in nuna miki". Da kayan ta bishi Abubakar ya watsa mata wani irin kallo. _ "Ke wai me yasa har yau ba zaki hankali ba, wai kullum'kina girma kina 'cin qasa? ajiye tiren kwanikan muje”. Rukayya ta ajiyc sannan ta bishi, duk wani abin da yasan bata sanshi ba sai daya nuna mata, sannan ya dawo da ita kicin din tai wanke-wanke. . Har ya nufi hanyar fita ya waiwayo, "Au . na manta ban miki kashedi ba, nasan halinki da tsinanniyar amsifa da fadan tsiya, to wallahi tallahi duk randa ki ka sake gigi ya kaiki kika takali mata ta k0 kikai mata rashin kunya, kin san halina sarai yarinya, zan iya abinda yafi haka ma. Sannan batun aikin gida, ki tabbatar da garin Allah yana wayewa duk abinda kike ki saki ki hau gyaran gidan nan, da kuma kuku ya shiga kicin ki bishi kina kakkama mashi ayyuka da safe, rana da kuma dare, ina fatan kin gane" Rukayya ta daga mashi kai, sannan yaja kwafa ya wuce. Ta raka shi da kallo har ya bace, ‘sannan ta dawo da kallonta akan tilin kayan 'wanke-wanken dake gabanta, taja wata . nannau‘yar' ajiyar zuciya ta duqa ta soma wanke wankcn. Tana cikin goge-goge a kicin din Kuku ya shigo ya dora abincin . dare, saurayi ne dan kimanin 'Shekaru talatin da fan wani abu, Bayerabe ne amma Musulmi yaji Hausa sosai. ' Suna hada ido da Rukayya ya sakar mata murmushi. . ' "Sannu 'yan mata, ashe na samu abokiyar aiki, yaushe aka kawo ki gidan nan ne?" Rukayya tamkar ba zatai magaba ba, ta ce. ' "Dazu". Ya waro ido, "Daga zuwanki kuma ba za ki huta ba har Zaki _ soma aiki?" Rukayya tai Shiru ba tare da tayi magana ba, . don haka shima kukun ya cigaba da abinda ke gabansa. ' . RuKayya ta gama wanke-wanken, sannan ta dauki doyar da kuku ya bata ta feraye masa, ta cigaba da fira. Tana gama feran doyar ya miko mata yanke-yanke, tana yi ba ita ta samu 'tabar kicin din ba sai da ya gama girkin tsaf. ' Abun ya‘zama jiki, kullum in zai yi girki sai ya kira ta, duk wani aiki mai wahala ita yake bawa tai masa, sannan idan an gama duk lol rukayyah dai ta zama yar aiki karfi da yaji naku har kullum A,I,S KE cewa asha karatu lafiya sannan a dinga comment RIKON KAKA CHAPTER15 abinda akai amfani dashi ita yake barwa ta wanke ta goge kicin din, safe, 'rana da daddare. Tun Rukayya na jin wahala har ya kal‘ ga ta saba. ‘ Tund da asuba Rukayya ta farka tai alwala tai sallah, sannan ta koma baCCin asuba kamar yanda ta saba a. kullum. Cikin barci taji an maka mata wani uban duka a jiki tamkara mafarki, ta zabura ta mike a gigice tamkar mai shirin fita hayyacinta. ‘ .Suhailat ce tsaye a, bakin gadon tana" cikin shiga ta alfarma, tai kyau har ta gaji, gashin kan nan nata yasha gyara, yana zube > saman kafadunta. Duguwar riga ce a: jikinta (miik colour ) mai adon duwarwatsu bakake tun daga sama har kasa sai daukar ido suke. Dan 'qaramin bakin ya sha janbaki sai daukar ido yake. ‘ . Ta. nuna Rukayya da siririn farin danystsanta wanda yasha bakin lallr 'cikin tsawa tace ‘ ”Tashi ki fita munafuka kije ki gyara min falulluka'na, wato ke har wani bacci koma saboda samun Wuri. T0 idan ma kina _ tunanin barci kika zo yi gidan nan to ki, gaggawar: sauya tunaninki, don ko' yan aikin .‘dake cikin gidan nan sai sun fiki hutawa da Jin ‘ dadi kinji na fada miki Tashi muje ki gyara .min dakuna kinji na fada miki wani irin tsoro da fargaba suka kama 'Rukayya ta zabura ta fice daga falon, ' ‘ . Suhailat taja wani dogon tsaki tabi bayan‘ ‘ RUkayyar ta sameta tsaye a falon nata sai makyarkyata take suhailat ta wur’ga mata tsintSiya,ta daki fuskarta ta ce ' "Ki maza ki share ki kakkabe ki" ki goge,kiJe ki gyara min komai kamin kuku ya iso ku shiga kicin" ‘ .' Rukayya bata iya cewa komi ba har ” Suhailat ta wuce‘, sannan ta ja wata irin ajiyar zuciya wadda ke bayyanar da tsananin tsoron daya kama ta Rukayya kenan ko ina bakinta ya tafi da tsiwa da fada? Wadda rigima k0 ba tata 'bace 'shiga take ta siyi fadan tai ruwa tai tsaki; amma gashi yau babban fada ya' tunkarota tana‘ gocewa, k0 me yasa‘? K0 da yake Hausawa na cewa k0 Baba da Babansa ' Duk da rashin aiki irin na RuKayya da son‘jiki, amma yanzu duK babu su, ta Saki jiki tana ta faman aiki. Ta zama wata (Very silent), tai (cooling) sosai tamkar ba ita ce mai shegen surutu nan ba. Rayuwa kenan, duniya juyi~ juyi wai kwarto ya da. ya fada ruwan zafi yace, "Daminar bara ba irin ta bana bace". * Y‘au wata daya da zuwan rukayyah gidan Abubakar, kullum cikin wahala take, bata da zama sai cikin dare, don haka idan ta kwanta kamar matacciya, ana asuba kuma zata farka ta fara daga inda aka tsaya. Saboda wahalar datake gidan k0 Bangarenta bata iya gyarawa bata taba wanka ba, tun kayan da aka kawota dasu sune a jikinta har yanxu da take ‘duqe tama goge gogen na'urorin duke qaton falon gidan. Abubakar ya fito daga falonsa shi da Suhaiiat tana manne a jikinsa, yana sanye da kayan ma'aikata a jikinsa, Suhailat na rungume da jakarsa ta ma'aikata. Rukayya ta saci kallon . su tai sauri ta dauke kanta daga kansu. . Suhailat ta dubi Abubakar, "Au Dear, na manta don Allah ( just five minute)". Abubakar ya ce, "K0 minti daya 'kika qara sai dai ki dawo ki samu bana nan". Suhailat ta ce "Na yarda" ‘ Sannan ta kwasa da gudu gudunta ta nufi falon da suka fito Rukayya ta dauki bokitin da ta jiqa omo da mofa ta gifta Abubakar,muryarta a raunane ta ce "Ina kwana?" Sai da ya matsa yana kakkare hanci kamar wanda yaga wata Shara, fuskarshi a dagule ya ce "Subhanallahi! Kina da hankaii kuwa? Dubi kayan jikinki yanda sukai dakal-daqal, ke ko warin jikinki bakya ji sai kace mai kuli kuli? Mtsw!’ Allah Yai wadan wannan qazantar taki, sakarya wadda'bata san ciwon kunta ba. Wallahi kar ki sake na qara ganinki da wadannan kayan, (stupid) kawai, wuce daga nan dallah”. . . Rukayya ta, wuce simi~simi tana bin. jikinta da kallo, ita bata ga wata shahararriyar dauda da tai ba da har zai mata wannan cin fuska ba. , Hawaye suka ciko mata. a idanuwa, duk qazantar da take ma ai 'su suka ja mata, aikin ‘gidan kawai da take ai ba qaramin ' tashin hankali bane. Ta sa‘hannu ta ‘share hawayen da suka ' zubo mata, ta duqa tana zubar da ruwan Kamar kullum, yau ma tamkar marar lafiya Rukayya ta wuni, ana kiran sallar la’asar sannan ta samu lokacin shiga (toilet) ta samu tai wanka tana fitowa ta samu mai ta shafa sannan ta Ciro daya daga cikin Kullin kayanta ta saka, ta fito don tasan yanzu kuku yazo su dora . . abincin dare. _ . , Suhailat tana zaune saman daya daga cikin kujerun dake zube a falon, tana sanye da , . shigar shadda doguWar riga har kasa mai hade da zanenta, ta sha ai'ki tun daga sama har kasa sai daukar ido take, mai ruwan kasa-kasa da ganin shaddar zata yi tsada. Tun daga kunnenta har wuya har zuwa" ‘_ kafarta da yatsun hannunta gwala-gwalai ne, " . sai walkiya suke. Babu abinda yafl daukar . ' 'hankalin Rukayya sai daurin kallabin dataima kanta, ta dora kafarta daya kan daya da takalmi mai tsananin tsini a qafar tana ta karkadawa. ’ ‘“ ' Ta watsawa Rukayya wani irin kallo wanda ya .kusa ‘sata makyarkyata, Suhailat tace. . ke zonan gaban Rukayya yai wata mummunar '_ faduwa, ta nufi inda Suhailat take zaune ’ .. Bata ankara ba sai dai taji ta flsgota ta fadi qasa, ta sa hannu ta dauke la da Wani ' gigitaccen mari har sau biyu.. ' Rukayya tasa kuka tana faman rawar jiki, Suhailat cikin tsantsar masifa ta soma magana. "Uban waye ya koya miki yin wanka a cikin gidan nan? Wallahi sai kin fada min wanda ya kitsa miki wannan". ’ Ta janyo Rukayya ta shiga duka tako' ina, tun Rukayya na ihu har ta soma qokarin kwatar. kanta. Suhailal ta tsaya tana tafa hannuwa, "Lailaha illallahu, kokawa za kiyi dani iye? ' Kokawa za kiyi dani na ce? To bisimillah”. _Cikin kuka Rukayya ta ce "Wallahi -ba kokaWa xa muyi. ba, kiyi hakuri don Allah. Suhailal tace”Ai Allah yau sai kin fada min wanda ya koya miki yin wanka da sauya kaya a cikin gidan nan". ‘ Rukayya tace"Ai Yaya Abbakar ne ‘ Cikin kaduwa Suhailat= ta saketa tana maimaita. "Abbakar, wane Abbakar din?" "Yaya Abubakar, ai shi ne dazu zai fita ya...."tace me? Dakin ki ya shiga? Ku kai ‘ me? ' Me ya ‘ shiga ku kayi‘?“ Cikin rudani da kaduwa Suhailat ta jero mata tambayoyin da ita kanta bata san ma 'anarsu ba, sai ma tsoratar da Rukayyar da tayi da ganin yanayinta, ta rinka ja da baya cike da tsoro. ‘ ‘ ,Suhailat tace, “Dakata daga nan inda kike' ki bani“ , amsar 'tambaya ta“. Cikin ’rudani Rukaya ta ce, "Dazu da zai fita a _ falo ina goge-goge ya ganni yace in wuce inje in canja kaya, kar ya dawo ya sameni dasu a jikina". Suhailat taja wata nannauyar ajiyar zuciya mai karfi sannan tace ‘ ‘ ’ "Wuce muje ki tattaro min duka kayan da kika zo dasu gidan nan". Ta“ tisa Rukayya a gaba suka nufi sashinta jiki na rawa ta tattaro mata duka‘ yan komatsan da tazo dasu, Suhailat ta dauka ta zubesu a qasa ta bincike kayan, ta zaro mata 1page is missing taje ta kona kayan," sannan .ta wuce sashinta, kai. tsaye toilet ta fada ta sani (scptol) da ruwan xai .ta Wanke hannayenta , sannan ta fito abinta. Bayan sallar magaruba Rukayya na kwance saman makeken gadon dake dakinta tana. kallon t.v din dake manne jikin bangon . .dakin, idonta ne kawai saman tv din, amma gaba daya ilahirin hankalinta baya kai, xuciyarta ta lula duniyar tunani ' ’ A .hankali ta dago kanta tana kallon kofar”da taji an turo ,Suhailat ce ta shigo babu' ko sallama, rukayyah ta zabura ta tashi zaune sai rarraba idanuwa take . Suhailat taja ta tsaya riqe da kugu kafin ta kallii rukayyah ta tabe baki. ““ " tace lallai samun wuri wato anxo birni ansha jar miya har kinsan kixo ki miqe saman gado kina kallo ko , to daga yau kin gama shi, shegiya wayar dake hannunta ta lallatsa sannan ta kara a kunne hello sagir don allah kazo ” zaka cire min na'urorin kallon dake sashin bakine don Allah yau k0 gobe Ta danyi jim kafin ta ce"Okay, to Allah Ya kaimu". Ta kashe wayar, sannan ta ' dubi Rukayya. , ‘ . ‘ "To nayi maganin tsaffin idanuwa wanda duhun gona ya riga ya kashe sai inga ta iyayi kuma. Don na lura idan nai sake wata rana sai kin ce dani zaki goga, don haka ke da gogewa sai dai a lahira haka za ki qare cikin duhun'kai da‘ jahilci. Ki tashi ki flto falo kuma dan uwan naki na kira". "Mtsw!". ‘ Ta ja tsaki, ta balbadeta da harara Jikin Rukayya ya kara sanyi tamkar mai masassara, haka ta yunkura ta sauko daga kan. gadon ta nufo falon kamar marar lafiya . . Abubakar da Suihailat suna zaune saman kUJera mal zaman mutum biyu, Rukayya ta tsugunna a ..gabansu. tace gani Abubakar ya watsa mata, ‘ wani irin razanannen kallon daya motsa mata hanjin cikinta “Sannu, sannu marar kunya, wato kenan har jinki kike wata tantiriyar marar kunya Hmm! Rukayya kenan masu ilimi da wayewar kai ma sunyi sun gama ballantana ke dake fama da ciwon jahilci da duhun kai K0 da yake ai ance dogo da hankali dama dacene amma banyi tunanin ‘rashin hankalin naki har ya kai kice zaki kokawa da iyalina ba. ‘ Ashe wautar da sakarcin dake dankare cikin kanki sun‘wuce iya sanina Wato duk nasihar' danai miki ashe ta bayan kunnen ki tabi ta wuce bata shiga ciki ba kenan? ‘ Saboda kina ganin kamar ban iya daukar mataki akanki wato don na daina taba lafiyar jikinki ko to kisani 'akan matata wallahi zan iya jirkita miki kamanni in barki kwance kinji na rantse miki wannan girman jikin naki da kikai bazai hanani dinga jibgarki kaman allah ya aikon ba lol su abubakar manya asha karatu lafiyaa zallah RIKON KAKA CHAPTER16 yace wannan ya zamo na farko kuma “na Karshe, wallahi k0 kallon banza. kika sake kika Kara yi mata na lahira saiya fiki jin dadi. Tashi ki bani wuri!". ? Ya daka mata tsawar da batasan sandata zabura ta rufta aguje tai hanyar sashintaba, yaja tsaki. "Mtsw! Zokalar banza zokalar wofl“. -. Ya dan ja numfashi kafin ya maida kallonsa akan Suhailat. ‘ "Kiyi hakuri’ don.Allah, ki qara daddaure mata, saBoda‘ yarinyar bata da wayau ko kadan, k0 can haka take da shegen fadan tsiya, ga shegen karfi kamar namiji, sai ‘ kace -ba mace ba. kibita a hankali, ' kinga 'mahaukaciya ce, kar ta'zo ta kayar min dake a” banza". suhailat ta watsa 'masa wani kallo mai kama da: harara, cikin sigar zulaya tace ”Oh! Wato ni raguwa kakr dauka ta kenan ko?," ‘ Abubakar yai dariya kafin ya ce' ”zaki hada karfin mutumin kauye Wanda ya saba da cin‘dawa da masara da na mutumin birni, wanda bai da abinci sai biredi da - indomie?” Suhailat ta ce, “Allah k0?“ Ya ce, 'Da gaske idan kuma baki yarda . ba na kirata tazo ku gwada naga wanda za'a kayar". Suhailal tai murmushi kawai ta mike ta janyo“wayarts dake ta faman ruri akantebir din dake , gabansu. Rukayya na shiga sashinta ta fada kan ‘ gado ta soma rera kuka mai tsuma zuciya, kalaman Abubakar sukai mata tsaye a makogoro' _ tamkar .mashi, ji. take tamkar zata hadiye zuciya saboda tsabar bacin rai da bakin ciki. ‘ Ada bata damuwa da duk wulaqancin da Abubakar ke , mata amman to amman yanzu mai yasa abin

Chapter 6 of 13