Share this page
ta iya haka ta dawo gidan ba don zuciyarta ta gamsu _da bayanin Hajiya Maimuna ba sai don ba yanda ta iya, tai ' sa'a kuwa: babu kowa a falon don haka tai . wucewarta dakinta tai kwanciyarta zuciyarla ‘ cike da qunci bata fito ta dora girkin dareba sai bayan' sallar magaruba lokacin da taji . shigowarsa ya dawo daga salla masallaci. , Ta Zira takalminta mai madaidaicin tsini ta fito, ai kuwa tai sa'a suna baje cikin falo shi da 'yar mulkin matarsa, dukkansu suka rakata da idanuwa ' Sanye take da riga da :zani na sabuwar atamfarta super exculisive wadda aka matse ‘ akaiwa lafiyayyen riga da siket wanda suka zauna mata mata a jikinta, "Me kake kallo‘?” Muryar Suhaiiat ta katse Abubakar yai saurin maido hankalinshi’ da tunaninshi a wurinta, ya dan soshi Keya alamun rashin ’ gaskiya kafin ya ce. "Me kika 'gani?“ Suhailat ta watsa mashi harara ‘ "Ban gane wannan tambayar ba, ta mi na gani?" . "To gani nayi ka tsareta da idanuwa, ban gane wannan kallon ba to meye? meye ma 'anarsa?" Abubakar yai murmushi kafin Yace "To yanzu mc zan kalla a can wanda ban taBa kallonshi anan ba?" Yai wata shakakkiyar dariya yana fadar. . "Yanzu duk ki rasa da wacca za kiyi kishi sai da qanwata? Haba SUhaila, ai» k0 ana . ‘ Sara a tsallake icen kuka". ' Suhailat ta Kara Bata fuska tana facfar. . ,"A'a Wallahi, ai dan hakin da ka raina shi . yake tsokane maka idanuwa. Ni kuwa ban yarda ba, kai kace da mun dawo zaka mayar da ita, kauyen su, ni dai kawai ‘ ka maida ita kamar yanda kace din". Abubakar ya shafi kansa yana fadar. "K0 baki ce ba insha Allahu zan mayar “ da ita ta ma cigaba da karatunta a can" ' Suhailat ta tabe baki tana fadar. "Da dai yafi" Abubakar yai dariya yana girgiza kai cike da mamakin halin kishi irin na Suhailat na ,babu gaira babu dalili, lallai ashe akwai takaddama a gaba. Rukayya dake tsaye a kicin tana jiyo-duk abinda suke fada, ta lumshe idanuwanta _' wasu hawaye masu zafi suka biyo kuncinta, ashe dama ita ke haukanta a banza shi bai dauketa a matSayin mata ba? Ashe dama tuni ya warware auren nasa dake kanta. "Innalillahi wa'inna 'ilaihi raji'un!". Kalmar da bakinta ke iya maimaitawa kenan, inda ruwan hawaye ke ta faman' zarya a saman kuncinta‘. Yanzu ya zata yi kenan? Ya zata yi da dumbin soyayyar sa da ta mamaye mata zuciya? Ta rungume idanuwanta tana _ wani irin kuka marar sauti. Tabbas Abubakar ya Cika babban makiyinta, ya zalunccta, bai mata. adalci 'ba. Tabbas ya zame mata wajibi ta cire Sonshi a zuciyarta ta cike gurbin da tsanarsa da kuma kiyayyarsa ta sake rushewa da kuka mai sauti dole zata bar "gidan ba ma sai ya maida ta da kanshi, ba bata bukatar wani abu ya sake , hadata dashi, bata buqatar ganinsa har abada. ' Rukayya ,tai kuka har taji .kanta na .ciwo sannan ta saurarawa raywuarta ta kalleshi kanta' ta kunna gascookcr ta dora tukunya jellof din taliya ce tayi express babu k0 kifi ballantana ’ suci arzilqin nama. Ta juyeta a kula ta rufe k0 lemu bata hada ba sai dai ta dauko na‘kwali ta hada da robar ruwa ta jera akan tire ta dauka ta fito Tana ajiyewa akan table tai gaba abinta ba tare _da ta kalli inda suke ba, saboda hawayen dake faman zubowa a cikin idanuwanta har a lokacin. Tana shiga Bangarenta ta maida kofar ta ' .ruga da gudu dakin baccinta ta fada akan gado ‘ ‘tare da rushewa da wani sabon kukan mai ban tausayi. Tana cikin baqin ciki tare da Jin haushin kanta da zuciyarta da har ta bari son Abubakar ya Shigeta, sai yanzu ne ta soma takaicin yanda' ta biyewa Aunty Maimuna akan wai dole Abubakar zai sota alhalin tafi kowa sanin irin tsanar da yai mata. . Tabbas itama zata kwatanta mashi kadan daga cikin irin kiyayyar. da yai mata, dole zata fatattaki soyayyarsa koda da qarfin tsiya ne daga. zuciyarta. Ta qara makalkale filo tare da rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi. . Washegari tunda Rukayya ta kammala sallar asuba bata sake komawa bacci ba, ta . shiga tattaro komatsanta tana zubawa cikin Katuwar jakar kayanta, sai data hada kan komi sannan ta zube qatuwar jakar ta dauko atamfarta ta‘ jiya ta saka, sannan ta saka hijabin _ sallarta, karfe bakwai daidai ta dauko jakar ta tai hanyar barin gidan. . Tun kafin ta ida isa bakin get ta soma tunanin irin qaryar da-zata shirgawa maigadi ta samu ta bar gidan, sai dai cikin ikon Allah tana zuwa ta samu qofar a bude da alama ya zagaya ne. Cikin farin ciki Rukayya ta sa kafa ta bar ~gidan jikinta na rawa, bakinta kuma na addu'ar Allah Yasa ta samu ficewa daga layin -ba tare da wani ya ganta ba, saboda unguwar tasu G,R,A CE ; k0 tsit yake k0 da yaushe zaka samu babu kowa. Don haka har ta samu ta iso bakin titi mutanen data gani basu wuce uku ba, suma amman babu wanda ta sani cikinsu. ta jima a bakin titi kafin ta samu mai keke napep ya dauketa daga nan zuwa Dandagoro naira dari biyar. Rukayya bata samu nutsuwa ba sai da taga sun fice daga‘unguwar gaba daya sannan ta samu sukuni Karfe takwas saura mintina shidda taiwa Rukayya a kofar gidan Kaka wanda rabonta dashi tun randa Kaka ta kaita gidan abubakar, sai yau data gudo da qafafuwanta haka rayuwa take. Rukayya ta biya mai keke napep sannan , ta dauki kayan nata duk da uban nauyi ta nufi cikin gidan na Kaka. tana Sallamar farko Kaka ta amsa tare da duban qofa, sukai ido hudu da Rukayya. Kaka :ta dau salati tana fardar Rukayya yau a gidan nan ko ko dai gizo idona ke mani?" :Rukayya ta sauke jikarta a gaban Kaka taja ;kujera 'yar tsuguno tana kokarin zama agaban tabarmar da kaka ke zaune, 'Kaka ta ‘tsarrta da idanuwa tun kafin ta zauna ta soma fadar. "Ke 'yar nan ya naga idanunki luhuluhu kamar wadda ta sha kuka? Wannan uwar jakar ma wai ' daga ina?“ Rukayya ta zauna tare da sa gefen hijjabinta tana share kwallar dake qokarin zubomata ' Kaka ta sake daukar salati saida takai aya ta ajiye sannan daga karshe ta furta. ', "Kada kice min yaji kika yo Kada " ki fada mani wannan bakar kalmar" ' Rukayya ta tsaya da sharar kwallar tana kallonta. Haushi ya fara kama Kaka, tace. ' "Ke nak saurare Jika, me ya fito dake ciki gidanki. Babu dai abinda kika nema kika rasa to akan wacce hujjar? . A wane dalilin?" ‘ Rukayya tacigaba da Sharar kwallarta, tabar ~. Kaka nata sababinta har sai da Lami mai aikin kaka ta fito daga cikin dan karamin dakinta ta iso inda suke' tana fadar. . "Haba Kaka. kin tasa ‘ya a gaba da sababi akan'abinda baki sani ba, sai‘ kace baki swn halin mazan nan na yanzu ba lalatattu, na kirkin cikinsu ragaggu ne". ' ”Kaka ta karkace kai tana fadar; "Shi ne kuma za'a rinka lullubo zani a taho yaji? Da kika ganni nan Lami shekarata arba'in da mijina ban taBa zuwa gida --. kararsa ba balle in rufa zani in tafi gida yaji ba kuma don baya saba min ba". ' Lami ta ce, "To k0 dai mene ne yanzu ai .kin tsaya kiji ta bakinta lukun sai ki yanke hukunci Kaka tace, "ai gata nan sai .ta gaya miki, ina saurare Lami ta juya kan Rukayya ta dafa kafadarta tana fadar. ‘ "Yi shiru mana haka nan Rukayy'a, kiyi hakuri ki fadi abinda ke faruwa sai a san ts inda za'a taro al'amarin Ai ke kinyi sa'a ma abin'duk na‘ gida. ne ba zai yi wahalar gyaruwa ba Sai 'da Lami ta bata lokaci wurin 'lallashin Rukayya kafin ta bude baki ta ~ Zayyano duk _'abinda ya faru tsakaninta da Abubakar har izuwa yanda Tun kaifin ta kai aya Kaka ta soma ‘sallallami tana rusawa Habu zagi, tana mmmmm. "Yanzu in wanke' yar in bashi shi ne zai zuba mata ido yana kallo saboda rashin mutunci da wulakanci? Ni habu zai nunawa iyakata?" . ' ' Rukayya na kaiwa qarshe Kaka ta rushe da kuka, k0 kalonta Rukayya bata tsaya tayi ba ta mike tai Cikin daki ta haye kan gadon Kaka taci gaba da kukanta. Tabbas abin ba qaramin bakin ciki yaiwa Kaka ba don yau tai mashi zagin da bata taba kwatanta yiwa wani irinshi ba don ma dai lami na‘gefe tana tausarta da ban san irin abinda za tai mashi ba Duk yanda Kaka taso ta lallashi Rukayya taqi saurarenta, ita ala dole fushi take da ita. ‘_ Kaka kuwa duk tabi ta damu, har suka kwanta ~dadaddare. . Kaka dai ta kasa daurewa don gaba daya baccin ma ya gagari idanuwanta, ta tashi zaune tana kiran Rukayya ya kai sau uku kafin ta amsa. ' Kaka ta ce "Tashi kiji abinda zan gaya miki". ‘ Rukayya ta ce, "Ni fa bacci nakc ji, ki fada kawai ina jinki". Kaka batai musu ba ta cigaba da fadar. "In har'dai ba habu bane autan maza a duniya to kin gama aurensa tunda har ya wulaqanta ki haka, ki barni dashi. K0 gaisuwa ban yafe ba idan ta hadaki da shi kinji abinda na fada' ‘ . miki". Rukayya dai bata tanka ba, _amma a zuciyarta gani take gaisuwar ma bazata qara hadasuba Mutumin da ya wulakanta ta, ya nunawa duniya ’ita da dan uwansa namiji amfaninsu daya wajensa, to gaisuwar mece ce zata hada su? Ai ba ma zata yarda ya sake ganinta ba. ****** ********** . Bangaren Abubakar kuwa tunda gari ya waye misalin qarfe bakwai ya gama shirinshi na tafia (ofiice) a matsayin shi na' sabon ma'aikacin da aka tura (curse) .su goma su uku ne kawai sukai nasarar fitowa da (result) mai kyau, don haka aka dauke su aiki, yau kuma ita . ce rana ta farko da zai fara zuwa (offlce) din. Suhailat na kwance akan katafaren gadonsu, tana ta sharbar barci, har ya kammala shiryawarsa. Bai yi tunanin tayar da ita ba saboda .bai ga amfanin hakan ba tunda babu . wani abu da zatai mashi yasa kai ya fice yana daura tsadadden agogonsa a hannu. Ya so ya biya ta sashin Rukayya yaga yata kwana? Sai daisaurin da yake ba zai barshi ba don haka inda so‘ samu ne ya dan karya 'da " lafiyayyen girkin Rukayyar kafin ya tafi To hakan ba zata samu ba, saboda qarfe bakwai dinma harta dan gota Hmmmmm kaka dai tace indai habu ba autan maza bane a duniya ba to ba habu ba ruky lol muje zuwa wai mahaukaci yahau kura admin is back RIKON KAKA CHAPTER23 aka ce tai musu a can don haka bai tsaya Bata lokaci ba ya dau motarsa a gaggauce ya tafi. ‘ Tunda suka isa wurin aiki shi da sabbin da aka dauka irinShl basu samu sun shiga (office) ba sai qarfe sha biyu tunda ya shiga (office) din nashi sallar azahar da la'asar ce kadai ta fiddo dashi, k0 abinci bai iya fitowa ya nema ba sai ruwan (tea) kawai da yake ta faman kwarara ma cikinsa, amma duk da haka har qarfeshidda bai samu ya gama (clearing) din komi ba, a dole ya taho gida saboda lokacin tashi ya riga yayi. ' ‘ . Bai taho gidan ba sai da ya biya ta crepcy ya kwaso tarkacen su (snacks) ice cream da lemuka yayo leda biyu na Suhailal da kuma Rukayya sannan ya nufo gida. Tunda ya shigo falon bai nuti Bangaren kowacce ba, kai taye wurin teburin cin abinci ya nufa saboda wata irin yunwa da yake‘ji tana neman kayar dashi. Sai dai da mamakinsa ya iske tcburin wayam ji yayi gabanshi yai wata irin faduwa wani irin masifaffen Bacin rai ya shige shi, ya 'juya a zafafe ya nufi Bangaren RuKayya tamkar ita kadai ce a matsayin matar shi a gidan. Ya tura kyauren falon, kai‘ tsaye yasa kai a cikin falon nata yana kwala mata kira. Jin da_ yayi babu alamar za'a amsa, yasa shi ‘sa kai cikin‘ dakin baccin 'ta sai dai mamakinsa, nan ma wayam babu kowa a ciki. Ya maida kallonsa akan qofar toilet din wadda ke a'bude. Gaban Abubakar .yai wata mummunar bugawa, ya juyo a firgice yayo waje. Dakin Suhailat ya nufa, tana tsaye gaban (home theater recorder) tana ta tikar rawa da wakar Adam Zango ta gayu komai na mata ne. Takaici ya kama Abubakar ganin bata ma san ya shigo ba har sai da yaje ya kashe wakar sannan ta waigo a tsorace sukai ido hudu dashi, ta yamutSa fuska a gajiye tana fadar. ' "Am sorry, wallahi banji shigowar ka ba". . _ ._ . Abubakar yaja tsaki kafin ya ce. "Ai dama ba‘zaki ji shigowata ba tunda kin qure volume kina ta tikar rawa sai kace "yar nanaye. lna Rukayya ta tafi ne?" Suhailat ta bata tuaka tana kallonshi kafin tace. , "Rukayya kuma? Akan wanc dalilin zaka lambayeni inda take? Ka bani ajiyarta ne?" Abubakar ya hade girar samadata qasa kafin yace ‘ "Ban gane na baki ajiyar taba? Ya zan lafi in barki da yariya a gida in dawo kuma in tarar bata nan in maki magana kuma kice na baki ajiyarta? Jinan Suhailat, ban son rainin wayo kinji?" itama ranta ya soma Baci, a ganinta ma in ba ya rainata ba ya za'ai yai mata wannan tambayar? ’ Ta dauke kai tana fadar, "To na koreta ‘daga gidan tunda ba gidan ubanta bane, ko nima zaka’ koreni ' ' ne‘?" Ran Abubakar ya yi wani masifar baci, wai har 'Suhailat tayi bakin da zata xagi 'yar uwarsa‘? Lallai shi ya bata fuska, don haka cikin matukar Bacin rai ya shiga fadar "Kin koreta kin kyauta, amma kamar yanda kika ce ba gidan ubanta vane to nima ai ba gidan uban babe hakaxalika tunda har gori ya fara shigowa ciki nima zan bar gidan yau kamar yanda itama ta barshi. Nine ke aurenki Suhailat bake ke aurena ba, don haka na baki zaBi k0 ki koma sabon gidan da na gida da kudina kiyi zaman aure, k0 kuma ki zauna anan, .zaBi ya rage naki". Yana gama maganar ya fada dakin barcinsu. Suhailat ta bishi da bala'i tana fadar. "Yo aurenka din banza, Abubakar kai har kayi kudin da zaka gina gidan da zaka sakani a Ciki‘.’ Ai dama tun kafin mu dawo qasar nan“ na gane take-takenka, ka ajiye aikin kamfanin mahaifina ne kanemi wani .aikin don kaji dadin'cin zarafina, to baka isa ba, wallahi kayi tsururu. In banda ma qaddara ai kasan nafi kariin ajin'. aurenka, ita wadda kakewa rawar jikin dama can ita ce ajinka ita ce dai dai kai ba __ ' ni ba" wohoho mata kaiiii muje zuwa Duk abin nan da take Abubakar na tsaye gaban (wardrop) yana hada kayanshi a cikin akwati, bai sake kallonta ba ballantana ya kulata. haka ya hada duk ‘wani abu mai muhimmanci a cikin akwatinshi ya gama zuge abarsa yaja hannun akwatinsa ya fice daga gidan. Har ya fice Suhailat ta raka shi da sababi, bai sake kulata ba ya saka akwatinsa a bayan mota ya fice ya zagaya gidan direba ya shiga yaiwa motar; (key) yai gaba abinsa, ya barta nan. Da Wauta kuma yana ficewa daga gidan sai. kuma ta rushe da kuka cikin tashin hankali ' sai' kace ba ita bace yanzu ke zazzaga masifa ‘ba har baki ’na kumfa. . ' Kai tsaye Abubakar gidan Haj. Maimuna ya fara tsayawa, yai sa'a kuwa ya samu, oga mahmud a gida, don haka suka baje a falo inda Hajiya Maimuna ta qawata masu tebur da kayan abinci da soye-soye kala-kala. ' Abubakar ya ' kasa taBa komi saboda tsananin damuwa da yake ciki Mahmud ya tsura mashi idanuwa yana fadar. "Lafiyar ka dai Abubakar naga kamar baka .da lafiya?" Abubakar ya jingina da makarin kujerar da yake zaune yana kallon Mahmud da jajayen idanuwansa cikin matukar damuwa ya soma fadar ' "Lafiya qalau Oga, damuwa ce kawai". ,Haj. Maimuna dake tsiyaya masu lemu a glass cup ta dago ta dan dube shi tana fadar "Wallahi naga alama, don ni har na danji tsoro don ban taBa ganika cikin irin wannan yanayin ba" . Abubakar ya shaki numfashi yana fadar. "Ni ' kaina ina tausayin‘ _kaina Hajiya Maimuna Suhailat ta. kOri yarinyar nan Rukayya - ina' (office) ban san ina ta ina zan fara 'nemanta ba, na' tabbatar matukar taje wurin kaka ka'shina ya bushe". ' . ’ .Haj. Maimuna dake duke ta_ koma da baya ta zauna 'akan kujera tana fadar. "ta kori Rukayya yaushe?" "‘Dazu". Abuhakar ya bata amsa. Haj Maimuna ta dafe kai cikin matuqar mamaki tana fadar “Ikon Allah, kuma har Rukayya ta baro gidan ba tare data biyo tanan ba?" Mahmud ya dubi Abubakar yana_ fadar. "To kai tayaya ka sakarwa mace haka harta iya korar wanda ka dauko ka kawo cikin gidanka baka nan?" _ Kafin yai qokarin fadar wani abu Haj. Maimuna ta karbe zancen da' '. "Ai Honarable duk abinda yake faruwa a cikin gidansa ba laifin kowa bane laifin sa ne da sakacinsa. Dama k0 da Suhailat bata kori Rukayya ba itama Rukayyar ta soma tunanin guduwa ta bar maka gidanka. _ . , Abubakar ka ajiye mata biyu a cikin gida amma ka tauye faya akan daya saboda wani son zuciya can ~ naka. Shin ita Rukayyar ba matarka' bace? Ko ita ba mace bacc? K0 kana tunanin bata buqatarka? Amma ka' biyema “mace ka tauye yarinya, ka mayar da ita 'yar aikin gidanka ba' wai matarka ba, ku ka dinka ' wahalar da.ita'don kawai an aura maka ita ba . , . don kana so ba. Shin kana ganin Ubangiji zai barka ne k0 kana ganin kana da wani makari da zaka iya kare kanka a wurin Ubangiji? Dama ni jiranka nake kawai ka dawo in hadaka da Honarable yai maka nasiha tunda kuma an koreta ai shi kenan, dama abinda kake so kenan tatafi ta baku wuri ta yunkura ta mike a zafafe tai falonta zuciya ta kawo mata wuya kamar zata fashe saboda bakin ciki, ita a ganinta Abubakar ya cancanta a kirashi azzalumi mai bautar dana qasa da shi. oga Mahmud ya dubi Abubakar yana fadar. "To kai ta yaya duk wadannan abubuwan ~suka faru haka Kana aikin me?". ' ' ‘ Abubakar ya kasa magana, ya rasa abinda ke mashi dadi daga yanda yaga Hajiya Maimuna ta hau yasan zai iske dubun haka a wurin Kaka. _ . Oga Mahmud Yace"Kaifa nake saurare Abubakar kayi shiru Abubakar ya sauke numfashi kafin ya soma magana. "Wallahi Mahmud duk aikin zuciyane kasan Rukayya ba sonta nake ba kakace tasa dole“: na aureta, tasa dole na hada su da suhailat Gashi gidan da nake zaune mahaifin Suhailat din ne ya bamu aronshi kafin nayi nawa, gashi kuma ba son Rukayyar nake ba, wannan ne ye ‘taimaka wurin tauye mata haqqinta. Amma da taflya tai tafiya ni da kaina naji hakan bai kamata ba, hakan ne yasa na harhada kudi masu yawan gaske nasai qaton fili a Batagarawa low cost don a ganina idanna ce zan bawa Rukayya matsayi na mata a ‘wurina a cikin gidan uban Suhailat duk abinda akai mana ni na ja. ‘ Ban fara ginin ba na samu tafiya qasar nan yin wannan (course) din, na dauki Suhaila muka lafi kudin alawus din da aka rinqa biyanmu daSu na gina filina, daga can qasar na turo da zanen gida da nake so muna dawowa aikina na ajiye a ciki a kamfanin mahaifin Suhailat tunda nayi nasara akan (course) din da aka tura mu yai mana murna sosai Tun kafinmu iso gidanmu na sanar da Suhailat a gidana zamu_ sauka, amma ta qiya a dole muka dawo gidan mahaifin nata. Ni don da yanda naso in fara ajiyeta a gidan nawa sannan in dawo in dauki Rukayya itama na kaita gidan. Sashi uku ne iri daya nawa da na RuKayya da kuma na Suhailat to sai ta Kiya a dole na kyaleta, amma dai na sakawa raina zan dauki ita Rukayyar da sunan na kaita' qauye sai in kaita can gidan nawa indai data matsayinsu na matana sannan da na dawo in sanar da Suhailat gidana na kaita na bata irin matsayin da itama na bata nasan Suhailat tana matuqar sona zata haqura idan ma bata yarda ' ba to sai ayi duk yanda za'ayi tunda ni dai nasan inda .na dosa sai gashi ta koreta ban sa yanda zanyi ba nasan da wuya' idan kaka zata saurareni ballantana har ta fahimce ni". ‘ *Oga Mahmud yajinjina kai kafin yace. "Ai duk da haka Abubakar kayi matuqar wauta, amma ni a ganina shiryawa kawai zaka yi ka tafi biko da sunan kai baka ma san yanda akai ta taho ba, a can ne za'a fada maka kishiya . ce ta korota, kaga daga nan sai kasan sauran "‘ bayanin da zaka yi ka samu a baka matarka ku taho. ' Abubakar yayi murmushi cikin matukar jin dadi yana fadar ”Aiko ka ba da shawara yanzun nan zan je don banga abinda nake jira ba". Oga Mahmud ya ce, 'Amma kafin ka tafi din ya kamala ka fara biyawa ta gidansu Suhailat din ka sanar da mahaifinta duk abinda ya faru tsakaninka da Suhaila! din don kada ta rigaka zuwataje tai maka 'yan qulle-qulle'. Abubakar ya ce, 'Yanzu fa barima ka gani Ya mike tare da miqawa Mahmud hannu suka Kara yin musabiha sannan sukai sallama ya tafi ‘Abubakar ya isa gidan su Suhailat yai sa'a kuwa mahaifinta yana nan' don ‘haka a falonsa akai mashi masauki, sai dai Abubakar bai san yanda ake kai qara ba tunda bai tababa gashi yana matukar Jin nauyin sirikin nasa hakan ne yasa sai da yai tA 'yan zagaye zagaye kafin ya iya zayyanowa mahaifin Suhailat din abinda ke faruwa tun daga aurensa da Rukayya har izuwa yanzu.’ Alhaji ya jinjina kai yana fadar; lkon Allah, yanzu wuyan .Suhailat har yayi kwaridn da'zata dubi mijin aurenta tai .mashi wannan rashin mutuncin? To ba‘komai, kada ka damu, kayi haquri gida dai nawa ne don haka tunda Allah Ya buda maka kayi naka to nima na karbi nawa kuma bance ka dawo gidan nan bikonta ba, yanda kace ta koma naku gidan tasa Kafa ta shure to haka zata kwaso qafar dai nata taje ta iske ka Ka'bani , dan lokacu ln banda sukarcinta ai shi aure nufi ne na Allah, idan Allah Ya nufi mutum da shi babu Wanda ya isa ya hana Don haka Abubakar kaje ka maido da matarka, kada ka bari mace tayi rinjaye akanka“. Hmmmm lol an kammala da iyayen suhailat sauran mai ran qarfe hajia kaka koya zasu kwasota da abubakar oho naku har kullum A,I,S ke cewa mu tara donjin ci gaba da yaddah zataci gaba da kasancewa cont it RIKON KAKA CHAPTER 24 Abubakar ya amsa da, "Insha Allahu". Sannan sukai sallama da Alhaji ya tafi abinsa cike da qarrfin gwiwa ya dauki mota ya nufi Dandagoro zuciyarsa cike da addu'a tare da fatan samun kan Kaka ta bashi matarsa k0 ya samu natsuwar zuciyarshi. Karfe tara na dare ya iso qofar gidan Kaka, ya faka motarshi ya’fito ya kukkulle' qofar motar, sannan ya ‘nufi .cikin gidan ”zuciyarshi cike da fargaba ya . soma jera sallama. Daga daki ya jiyo muryar Kaka na amsawa, don haka ya nufi dakin kai tsaye yana ta faman addu‘a a zuciyarshi. Ya yaye labulen‘ dakin ya shiga Kaka na daga kwance da hasken wutan lantarki Ya durqusa daga bakin qofa yana gaishe daKaka cikin girmamawa-, tamkar babu abinda. ya faru, ta amsa mashi cikin sakin fuska, abinda ya fara bashi mamaki kenan wanda ya. sashi tantamar anya kuWa Rukayya tana gidan‘.’ ' Gabanshi ya yanke ya fadi,yaja daga tsugun0n da yayi ya zauna yana kallon Kaka ya ce ‘ "Harkun kwanta kenan?" Kaka ta ce, "To me muke jira?" Ya danyi jim yana ta sakesake a .zuciyarshi, so yake kawai Kaka ta tare shi da maganar Rukayyar amma tai burus ta share shi, abinda ya Kara sashi cikin rudani kenan, ya rinka waige-waige cikin dakin, babu ta inda ya hangi alamarta. ' Wata zufa ce ta soma keto mashi da yaga ya share fiye da minti talatin a zaune, ita Kaka ma tuni har ta soma barcinta. Ba yanda ya. iya shima haka ya mike ya fice jikinsa a kasale bai ‘xo da Shirin kWana garin ba, amma kuma yanzu baiga ta tafiya ba ina zai sa kanshi yanzu ’ idan aka ce Rukayya ta Bace? Sai da ya leka (toilet) yaga babu kowa a _ciki sannan ya wuce‘ tsohon dakinsa ya budc ya shigé ya kwanta akah katifarsa, babu alamar barci a cikin idanuwansa haka yaita juyi shi kadai a cikin daki daga qarshe kuma ya mike yaje‘ya ‘dauro alwala ya dawo dakinsa yaita . jero nafilfili: yana addu'ar Allah Ya bayyana mashi ruky Bangaren Rukayya kuwa tunda ta jiyo muryar Abubakar yana sallama ta wantsara ta. fada bayan gado tai kwanciyarta, tana jinshi ya qaraci zamansa har ya fice sannan ta mike ta haye kan gadon tai kwanciyarta. Washegari misalin qarfe. takwas Abubakar ya gama shirin tafiya (office) ya shiga dakin 'Kaka da niyyar yai ma Kaka sallama,‘ akai sa'a Rukayya tana kewaye tana watsa ruwa, saboda wankan safen da ya riga ya kama mata jiki, don haka har ya gama yiwa ‘ ,Kaka sallama ya filo ya hau motatsa ya tafi bata sani ba. ~ A moto Abubakar ya rasa abinda ke mashi dadi, ya shiga cikin matukar damuwa da tashin hankali Tabbas ya sani Rukayya bata gidan Kaka, to ina ta tafi? To kuma idan har bata 'zo gidan ba ya akai Kaka bata tambaye shi .yaya Jika ba? Sannan bata tambaye shi yaushe ya dawo daga tafiyar shekara daya da rabin daya tafi ba, da kuma bata daure mashi ba ta ‘ :karbe shifaran-faran anya kuwa babu wata maqarqashiyar da Kaka ta :shirya masa‘? ldan kuma akwai ta yaya zai iya ganewa tunda bata bashi fuskar hakan ba? Da wannan tunae tunanen har ya iso (office) dinsa zuciyarsa babu dadi duk ya fita hayyacinsa. Shi ji ma yake tamkar bai da lafiya, saboda da qyar yake iya jan qafafuwansa, sai kace mai ciwon lakka kwatakwata bai da kuzari a jikinsa. Cikin kwana uku duk inda Abubakar yasan Rukayya zata iya zuwa sai da yaje ya nemota, amma bai sa meta ba gaba daya ya zabge ya fita hayyacinsa, shi baima san zuciyarshi ta kamu da son Rukayyar ba sai *yanzu data kufce mashi, don haka washegardi safiyar.juma'a yana tashi. daga (office). Karfe hudu ya nufo dandagoro gidan Kaka, ya yanke :‘shawarar zai sanar da ita kawai tunda barin kashi a ciki baya maganin yunwa. . ‘ Da sallamarsa ya shiga cikin gidan babu kowa a. tsakar gidan sai Lami mai aiki tana “wanke a’laiyyahu a bakin famfo sai da ya gaisa da ita sannan ya wuce dakin Kaka kai tsaye inda yake jiyo sautin redio wanda ya karade gidan da wakar mutanen Niger wadda aka sako a gidan radio, Abubakar ya yaye Labule cike da mamakin 'yau. Kuma Kaka kida ake sha ‘ kenan, ita da take fada idan wani ya kunna'ta . ce xa'a cika mata kunne. Ya yaye labulen dskin tare ‘ da sallamarsa, sai dai wa zai gani? Rukayya ce kwance akan gadon da radio a kusa‘da ita daga' ita sai farin dogon siket irin 'budadden nan, sai 'yar Bingilar

Chapter 10 of 13