da Amuncewa ta ba banyafe ba! Hhhhh mansur kenan Kai kadamu da wannan.! Shiru yayi yace Allah ya kyauta.!
Bayan kwana biyu zeenah tafara jin sauqi Amma duk ganin da zatayiwa umaima se tsikar jikin ta tashi dan ji take kamar Abun ne ze koma faruwa da itah gashi tana son tserewa to Amma Ina zata dosa idan ta tafi wace Rayuwar ce zata sake shiga? Wannan tambayoyin ne suka tsaya mata Azuciya. Alkhairan mansur na dayawa tare da itah tana cikin wannan thinking umaima tashigo!
Cikin tashin hankali tace bismillahi ! Umaima uhum tace tare da gyara zaman gilashinta, ke fad'a mun Alaqar ki da mansur Aure kukeyi ko yaudarar ki yayi ya maida ki karuwar sa!?
Cikin kuka tace wlh Ban San shiba se da Tsautsayi ya Afka mun. Ido tazare tace ke dubeni da kyau banda mutunci game da mijina, Wlh Aunty NAMIJI ko ya yake Na tsane shi bana San wata Alaqa ta Had'a mu bare Aure domin sanadin sane nake wannan muguwar Rayuwa.
Bana yadda da macce ko yau tazo duniya muddin shari'a bata haramta Auren ta da mansur ba! Shawara d'aya ce kibar gidannan tun Ahalin ki idan sungan ki zasu shaida ki! Tare da Jan hancin ta tace Umurni ne!
Wasu tears ne suka gangaro sannan yaran da ke cikin ta ya harba da fewa tayi tace ya Allah ka nema mun mafita duk rintsi da rikicewar Rayuwa Ina tare da kai.
Gefen Taheer yagama shirinsa tare da d'auko mutanen da zasu sace Abbah da mah ta hanyar garkuwa dasu cikin sa'a kuwa Suka sace miji da matarsa A Welcome to China communication d'aya daga reshen hada hadar kasuwancin Abbah da Akayi bikin ceka shekarun sa biyar da kafawa.
Azahiri hankalin taheer ya tashi domin sam baya iya magana da y'an jarida se de suna rubuta labrai da d'aukar sa photo domin yana cikin kad'uwa me zaman kanta... Kai tsaye labari yakarad'a ko inah satar Abbah yakad'a y'an boko da masu fad'a Aji...... Amma A wata majiya......
ASMEENAT ZEEYAN CE
[31/07 4:01 PM] YAYA HAYAT: *B.W.A*
*🥁BAKIN GANGA*🥁
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*Story, Written,*
*ASM££NAT Z££YAN*
↪2⃣2⃣
*Astagafurul lahal laazi la ilaha illahuwal hayyul qayum wa atubu ilahi*👏🏻
*Alhmdullah bini'imaty Ina taya y'ar uwa murna Ruqayya mua'axu ladan (Gimbiya) Akan Azirta ta dayayi da cika Rabin Addinin ta ta hanyar Aure to Ina roqon mabuwayin sarki yabada zama lafiya da keda Ango rabi'u muna missing d'inki by by*🖐🏼
↪
Amma a wata majiya..Y'an garkuwar sun kira number Alh. Ibrahim jabo.! inda suka buqaci zallar Naira millions dubu!!! hankali sa yatashi sosaiiiiii Ina xesanya kansa? d'an uwan sa tilo da yakeji dashi, Hawaye suka sirnano masa da yatuna cewa millions dubu fa ba wasa bane!? Sake kiran shi Akayi tare da shaida masa only 72 Awas ne yarage numfashin Abbah kuma ko qwandala bazasu rage ba.
Da kyar yace kar Ku kashe mini habibu shine nake kallo naji sanyi!!! Dariya Akayi babbah, sanan akace kud'i sune fansar ran d'an uwanka Ibrahim! dan haka ka kaimana su A inda muka buqata, Asirance .kuma idan wani yaji Aka harba bindiga. Tare da karamasa muryar habibu. cikin muryar kuka yace habibuna shima cikin da kiyar murya yace yaya karkayi kuka saqon Allah ne ba Wanda ze kautar dashi kuyi Haquri!
Habibu Ina zamu samu wannan kud'in? tare da sa yatsan sa yashare qwallar da ta gangaro dai dai hancinsa!Ina tsoron mutane nan kar su jima ciwo ! Yayansa yabashi tausayi yace kar kaji komai Allah natare damu! Hakane habibu Ina matarka? Basu Bari yayi magana ba suka qwace! Hello hello amma shiru Se ya fashe da kuka me sautiiiii! Ladidi ce tace haba baban taheer kuka be kamace ka ba Addu'a ce mafi Alkhairi!
Kuka yakamace ni hajiya! habibu shine b'argon jikina, yayi min taimako Alokackin da nake faqiri, ya maidani mutum Alokackin da na zauce! yau Ina zan saka raina, ga habibuna na Neman temako Na bani da komai se Rayuwa tabbas Rayuwa ta fansa ce ga d'an uwana. Domin Na tabbatar tashi Rayuwar itace mafi Alkhairi! Haba baban taheer kar ka yanke hukuncin da ubangiji be yanke ba kasani ba Rayuwar da tafi fifiko face wadda Allah yasanya ma tsoron sa.
Haka yakira Taheer cikin muryar kuka yace Yanxu ya Ake ciki? Na de sa gidan da nake kasuwa! Shima cikin kuka yace ai gida rufin Asirine ne baba da kabarshi! Maganar banza ne taheer xanyi farincikin ganin habibu koda zan mutu Ina cin qasa matsayin Abunci kasani duk duniya bani da tamkar sa.
Haka yake Abbah ka Kira khaleel bana iya gaya masa wannan ibti'lain! Nima bakina baya furta Abun Qi ga habibuna domin kuskure ne! Mubari muga. Katsewa sukayi. Baba yasadda Kai qasa yana tunanin mafita.
Yana haka kiran khaleel yashigo da kyar baba Ibrahim yad'aga cikin dake murya yace khalilu! Na'am baba! shiru ya ratsa wannan kuma ya tabbatar ma khaleel saqon da Aka turo A line sa na kar ta kwana gaskiya ne! Hawaye yaji yace baba shima cikin rawar murya yace khalilu! Da gaskeni Anyi garkuwa da su mah? Kuka yafi qarfin baba! Khaleel ne yace baba kadaina kuka dan Allah! Kaga in zakayi kuka muma karyewa zamuyi mu koma mata. Na Kira brother taheer yakasa d'auka Amma zan shigo NIGERIA yau da tsakiyar dare gobe se muga ya Allah ze tsara!
Thom khaleel se kazo! Allah yayi muku Albarka suka katse! Haqiqa idan khaleel sun kad'a sunyi mugun jah damuwa ta bayyana fall Afuskar shi hannu yakai ya share qwallah yace Allah gafurun rahim! yafara shirin Neman bixar gaggawa cikin sa'a yasamu. Yafara shirin tafiya. Khaleel sanye yake cikin riga da wando farare soul ,Amma kallo d'aya zaka masa kasan hankalin baya tare dashi.
Haka har yashiga jirgi misalin ukku da Rabi Na dare jirgi ya sauka mai makon murna se ya Aza kuka da ya tuna in yashigo NIGERIA yadda A hali ke tarbon sa Amma yau tun Ba Amutu ba ga Duniya lallai Budurwar wawa ce. Shi yasanya kataka sannu domin bakasan ya gobe za ta waye ba.
Haka ya jawo jakar sa yana tafiya da qafarsa yayi tafiya me nisan gaske kafun ya yada zango A wani qauye da ke garin sifawa tun Assuba ya bi motar kasuwa ta jabo...A can ma shirin da wowa Sokoto sukayi dan duba mafita...bayan sun shigo hankalin khaleel,baba, taheer ya tashi domin 75millions ne kawai a account d'in Abbah sannan millions dubu Ake buqata ya kenan?
ASMEENAT ZEEYAN CE✏
[31/07 4:01 PM] YAYA HAYAT: *B.W.A*
*🥁BAKIN GANGA*🥁
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*Story, Written,*
*ASM££NAT Z££YAN*
↪2⃣3⃣
*Astagafurul lahal laazi la ilaha illahuwal hayyul qayum wa atubu ilahi*👏🏻
*Rana me Raba ma Rana Aiki! Brilliant writer's kenan Allah yaqara muku hazaqa da baseera da kareku da sharrin mugu da muguwa! Duka baqin mu da suka samu kasancewa damu Ina mai muku murna welcome*🥛
*Ina ganin comments inku akan taheer mudai jira muga domin munsan tabbas watarana Asirinsa ze tone mudai bi sannu inajin sweet*💋
↪
Sannan millions dubu Ake buqata ya kenan..?suna cikin haka wayar khaleel tayi qara tare da ta taheer lokaci d'aya!
kallon kallon suka hau kasancewar duka baqin number's ne sannan suka d'auka Araunane! Gefen khaleel dai angaya masa lokaci Na tafiya! Gefen Taheer kuma qarar dukan Abbah da mah yaji Tare da cemasa kuyi wani Abu! Cikin da firgici yace kubani Abbah dan Allah! Karamasa shi sukayi da gajin muryar sa kasan ya jigata Amma saboda karyasa su cikin tashin hankali yace taheer kuyi imani da qaddara inshallah ba Abunda xe samemu! wani shegen mari Aka Dallawa Abbah se da yace washhhh! Ganin taheer yakasa magana khaleel yakarb'a tare da cewa Abbah Ina mah!?
Yawu ya had'a yace tananan khaleel, kubi A sannu kajiya kubawa yaya Haquri nasan yana cikin kad'uwa! Cikin kasalalliyar murya yaceThom Abbah itafa zeenah!? Gaban Abbah yafad'i dan yasan khaleel be San komai ba tasalima yace tana gidan Abokin sa na kaduna, kasancewar bata karatu! Se yace tana da rauni kar Abari tasani kajiii kuma kasan tana kaduna. thomm Abbah nasa tallar kadarorin ka Akasuwa idan da Wanda bansani ba kasanar mu kuzasu ceto rayukan ku!
Khaleel duk Abunda zakuyi taheer yasan komai nawa kuyi! haka Allah yaso! Cikin rauni murya khaleel yace Abbah sadani da mah se kuma yaji wata muryar daban!!! Hhhhhhhh khaleel kujira idan kud'in sun shigo babarka zataci gaba da Rayuwa! Aka katse wayar! Kukan da bashiri yasirnano A idonsa! Ya qara imani wannan zamanin talakka ne me gata, domin ba Wanda ke hango sa bare ayi tunanin tar watsa Ahalin sa, wannan masifar da me tayi kama? A NIGERIA ba wani d'auki da hukuma ke kawowa sab'anin qasashen da suka cigaba! Taheer ne yad'ago khaleel yace brother bamu da lokacin kuka yanxu mu fara had'a kud'in lokacin Na tafiya.
Khaleel ne yace hakane taheer! kuma yace duk Abunda kasani mallakin sane Asiyar Agani ko zasu ceto ransu! Shiru taheer yayi me nuna tsantsar damuwa yace mun yadda da hukuncin Allah ! Sannan khaleel yazo yadafa baba Ibrahim yace haba baba kar kajawo wa kanka ciwo mana Ba Alkhairi zubar million Tear's A idon ka dan Allah kayi shiru!+ Qanqame khaleel yayi yace Nakanji sanyi ne idan natuna habibu da yadda mukayi Rayuwa cikin maraici da Rashin gata ,khaleel mun kasance Abun qyama da hantara A qauyen mu! Bansan kowa ba se habibu haka shima be San kowa ba se ni. Tayaya idanuwa Na zasu juri Rashin habibu A tare dasu! Haqiqa Baba yaba khaleel tausayi yace baba ka manta da wannan ya wuce!
Girgixa Kai yayi yace bazan tab'a mantawa ba khaleel! Bazai tab'a wucewa ba! Domin lokacin da mahaifiyar mu Na naqudar habibu ina kimanin shekaru ba kwai Aduniya! Mahaifin mu Na daji gurin Neman Mana Abuncin da mukaci mahaifiyata ta dinga shafa kaina ta riqe hannu Na ban san komai ba bare nagane wane hali take ciki.
Se naji tace Ibrahim kuyi Haquri da Rayuwa da kai da Abunda xan Haifa idan Allah yaso!
hawaye suka keta gefen idanuwan ta hankali Na ya tashi ganin Hawaye idon innarmu! Na kai hannu nadinga sharewa ba tare da nace komai ba! Tana haka naji tayi nisa tare da fad'owar Abu me kukan jarirai Naga jini ya wanke zanen ta! Zan gudu ta riqeni tace Ibrahim kuyi Haquri ta Aza hannuna dai dai kafad'ar ta tace je kakirawo babanka Amma idan kukayi sanya baza ku iskoni ba lokacina Na qaratowa. Ko Alama bansan mutuwa ba bare nagane zancen innata! Haka naje daji nakira baba! Bayan sa yad'oro ni yana gudu sosaiiiiii ko da muka zo muka kira inna rabulll izah yacika Umurnin sa!
Babana ya Aza kuka nima nayi habibu Na kwance yana qara sosaiiiiii! Aka kira dattijawa sukayi ma habibu da inna wanka ba wadda ta tausaya ta tafi dashi Aka miqo mun!
Baba duk ya kalli habibu to kuka ne haka muka dinga ba habibu nono saniya kullum ta lauci qaruwa yake muka kasance bamu da komai se gidan mu da saniyar mu. baba kullum faranta mana ya ke Aka tilasta masa Aure da bashida niya saboda yakare mutuncin mu ya yadda!
sadda Aka kawo Amarya Adaren tace bazata riqa mu ba! Baba yaci kuka yana roqon ta Amma taqi gashi idan ya saketa za'a qwace gidan da saniyar mu ,hankalin sa yakoma tashi daga qarshe yayanke Kai mu gidan marayu!
Besan ya Ake ba yazooo bakin get ya Ajiye mu yace ze dawo dawowar da har yanxu da girma yafara kawo jiki jiranta muke! Nan kuwa Aka qullah Baqin hadari muka sha kashin Ruwan da sukayi sanadin d'auke takardun da komai da baba yabamu kayan jikin mu sunjiqe muka had'e ni da d'an uwana se karkarwa mukeyi. Har baccci ya d'auke habibu ni kuma Ina zaune yunwa ma ta Adda bemu.
Muna haka me gadi yaganmu yace mu shigo ciki Na d'auko qanena mukayo ciki!ya tambayeni nace masa baban mu mukejira yabamu Abunci Na kalla Naga iya kacin sa Habibu Na Ajiye masa!
Kwanaki masu tsayi babu baba muka kasance cikin marayu! Muka fara aiki tuquru kamar yadda kowa keyi, ni biyu nakeyi da nawa da na habibu! Ko Ina Akwai shed'anu haka za'a dinga dukan sa Ina Rama masa Watarana Aka kulle ni a wani d'aki me duhuwa Aka fara sa Habibu aiki koda Na futo d'an uwana yarame se Naga cewa banyi ma innarmu halacci ba. Kuma Ashekarun habibu baya iya wannan aikin! Haka dai Rayuwa tacigaba da tafiya ranar wata laraba misalin ukkun dare gobara ta tashi ni dai naci nasarar tsirar da kaina da kuma habibu Amma taci yara da yawa!
Wannan yayi sanadiyar tarwatsewar gidan marayu !Aka kira masu kud'i akan suyi wani Abu kuma masu son yara su d'auka Ina riqe da habibu wani yace shi yakeso barazana da tashin hankali sukazo mun atare anfi qarfina Aka qwace shi nafara kukan da se da na shekara 25 nagama sa shine had'uwa ta da habibu ina tallaka me Neman temako! shikuma sun sa yayi karatun boko da na Na Islam mukayi kuka da farin ciki ya min gata da komai yayi mun Aure, sannan daga baya shi yayi yaso Na dawo Sokoto naqi Na haihu ya d'auko d'ana yana masa komai tayaya zan daina kuka ga yaron da nine uwarsa shikuma d'ana shin Na tambiye ku duk da ku ba iyaye bane mata! Amma ya uwa keji idan anrabata da d'anta? Sosaiiiiii suke kuka sannan khaleel yayi qarfin halin cewa Allah kad'ai yasani! Yace to kubari nayi kukana haka nake ji.
Taheer ne yayi qarfin halin cewa muje khaleel mugani saqwannin sayen kadarorin Na shigowa.....!
ASMEENAT ZEEYAN CE✏
[31/07 4:01 PM] YAYA HAYAT: *B.W.A*
*🥁BAKIN GANGA*🥁
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*Story, Written,*
*ASM££NAT Z££YAN*
↪2⃣4⃣
*Astagafurul lahal laazi la ilaha illahuwal hayyul qayum wa atubu ilahi*👏🏻
↪
Muje.. haka aka dinga sayen kayan Arha da kyar Aka samu 900, millions Naira! an sayarda komai har gidan da suke ciki amma fafur sukace se ancika kud'in,taheer ne yakarb'i wayar hannun khaleel yafara magiya! shiru sukayi can kuma sukace sun Amince!
Godiya ga Allah sukayi tare da shirya kud'in tsaf shida khaleel suka nufi wani qungurumin daji da ba komai se duhun bishiyoyi sunyi tafiya me nisa sannan akace su Ajiye kud'in bayan dutseee su fita Abbah da mah za'a kawo su kamar yadda Aka d'auke su!
Amma fafur taheer yace se sungansu zasu bada kud'in! Khaleel yace taheer kud'i basuda wani muhimmanci garemu mu basu kawai! Nisa yayi suka Ajiye!
Haka suka cika duk wani umurni, suka juya bayan wasu Awas da suka share suna tafiya sukayi karo da Abbah da mah d'aure A wata bishiya jikin Abbah duk duka ne manya Abayan sa! Har tsikar jikin khaleel ketashi da yakai kallon sa ga mah! Durqushewa yayi qasa yace mah Abbah wane mafi girman Axxalumi ne ya zalince ku? Taheer ne ya miqe dan kwance su yanayi yana kuka takaici da baqin ciki ganin halin da Abbah yake ciki, qasan zuciyar sa kuma everything are fine.!
Bayan yaqare ne Abban da duk jikin sa shayin jinine yace kuyi Haquri kunji yarana tare da shafa kan taheer! suka banye mah! Cike da tashin hankali suka qanqame junan su duka, Abbah ne yasake mgn ta hanyar cewa khaleel Ina babanku?
Taheer ne yayi mgn khaleel yakasa domin yafara thinking yaya xe basu care duk Ahalin su ba mai qwandala ansiyar! Innalillahi wa innalillahi raji'un itace kawai yake nanata wa Azuciyar sa ji yake kamar yayi ta qwallah Ihuuuu sbd tashin hankali shikenan su duniya tashi d'aya ta musu! Allahu Akbar duniya makaranta inji Abbah ganin yadda suke tafiya da qafarsu bayan Ajigace suke!
Tafe suke mah Na fad'uwa qasa saboda ita tagama rikicewa bakin ma babushi se dai tera's khaleel ya lura da hakan! cikin zafin nama yaduqa ya Goya mahaifiyar sa suka ci gaba da tafiya har suka Kai cikin gari!
Bayan isane y'an jaridu suka cika guri da tambaya Amma Abu d'aya Abbah yace muqqadari ne! Wani gida me d'aki biyu wani maqaucin Abbah yabada yace su shiga! Haqiqa suna cikin yanayi da ba me cewa kowa ko qalah! Sannan dukansu sunyi imani kuka Na d'aya daga jerin manyan ni'imomin ubangiji lokacin daka shiga yanayi yazooo ma to sanyi ne ga zuciya.k kayi gaggawar gode ma ubangijin Muh'd!
Bayan kwana biyu Rayuwar da tasaba da Arziki !ta dawo me Neman temako, Abunda zataci ma bare ayi maganar hutawa wannan shine damuwar ko wanne su !Domin talauci baya ma Rayuwar da batasan wahala ba da kyau domin dukan su sunrame sun tsotse ba komai Azukatan su se tausayin junan su!
Khaleel ne zaune waje gashin kansa duk ya hargitse ,rigar da yazo da ita har yanxu be canza ba gashi besa ba dazama gida ba kuma yatuna qanwar sa me d'ebe masa kewa in yana cikin damuwa+ zumbur ya miqe yaje gaban Abbah da yakifa kansa da guiwa yace Abbahna yaqarin Haquri?
Qwallah ya maida yadda d'ansa ba ze ganeba yace Alhmdullah khalill sumar kansa ya Sosa yace Abbah yakamata zeenah tasan halin da muke ciki! tunda kullum jikin mah tsanani yake ba Asan ya Allah zeyi hukuncin sa ba! Kuma ita wayarta Na hannun ta se Asiyar akai mah hospital!!!
Shiru yayi can kuma yace qyaleta khaleel ba y'a tabace! Hawaye zar A idanun khaleel bakinsa ya tona Asirin zuciyar sa tahanyar cewa da me zanji haukacewar Abbah ko kuma talauci da Rashin lafiyar ummahna!
Dafa shi Abbah yayi yace haqiqa ban haukace ba khaleel? Da sauri yad'ago ya kalli Abbah Alamar tuhuma! Eh ban haukace ba sannan zeenah Na fiddata daga jerin yarana kamar yadda ta mantani mtsayin ubah!
Da zaune yadinga jah baya rigar jikin sa se nauyi take qarawa gumi keto masa yakeyi ko inah kukan ma cak yatsaya ya tsare Abbah da idan sa!
Abbah ne yayi qarfin halin miqewa jikin sa na karkarwa yace khaleel ka nutsu Abunda zeenah ta Aikata mana tabbas ko kare bazai shin shina ba! Khaleel duk ya rikice gashi kunnuwan sa na Aika saqo ba dai dai ba yadda zuciyar sa ke gaya masa kenan!
Se ga taheer da sauri khaleel ya riqo shi har seda yafirgita Abu ga marar gaskiya! sannan yace brother ka taimaka min Na haukace kunnuwa Na basa fahimta Ina y'ar uwar mu zeenah!? Shima qwallar yaji Tare da cewa khaleel kullum kwanan duniya Neman ta nake Amma narasa Ina zan ganta! Ko yanxu daga Neman ta Na futo
Kuka yafashe dashi tare da cewa me kuke nufi? Dan Allah kusanar kafun zuciyar ta Ida tarwatsewa! Taheer ne yace zeenah tsautsayi ya Afka mata Akan saurayin ta Anwar ya mata ciki!!!!!
Cikin wata murya kakkausa yace what! qaryane taheer ba de zeenah ba ,waye Anwar? Waye ubansa? Waya d'aura masa gindi A Nigeria!? Haqiqa yayi kuskure mafi muni Arayuwar sa! Ina yakai qanwata bayan ciki!? Duka tare yake maganar! Cikin kuka taheer yace nayi iya qoqari Na Amma nakasa. Ina bazai tab'a yuyuwa ba! Ina Anwar d'in ?yana koto! Da qarfi ze fita Abbah yace dakata khaleel! Be juyo ba yace kayi Haquri Abbah duk duniya Allah kad'ai ze dakatar dani daga fuskantar Anwar!!dan Na nemo y'ar uwa ta daga qarshe yayi kukan da ba iyaka Aidansa domin bazan tab'a bashi mutuwa me sauqi ba! koda kuwa ita ke Neman sa bashi yake Neman ta ba! Taheer ne yace haba brother kada kayi kisa!
Wani mugun murmushi yayi yace ba kisa zan yi ba! To mezakayi khaleel?
ASMEENAT ZEEYAN CE✏
[31/07 4:01 PM] YAYA HAYAT: *B.W.A*
*🥁BAKIN GANGA*🥁
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*Story, Written,*
*ASM££NAT Z££YAN*
↪2⃣5⃣
*Astagafurul lahal laazi la ilaha illahuwal hayyul qayum wa atubu ilahi*👏🏻
💋💋💋💋
↪
To mezakayi khaleel!?...kabarni kawai brother nagwada sa'a ta! Gaban taheer yafad'i Amma yadake tare da cewa fatan Nasara brother! Suka had'a hannu Aqasan zuciyar taheer mafi Alkhairi ga Rayuwar sa shine yaraba khaleel da Rayuwar sa. Haka yafita izuwa koton dan ganin Anwar ko da tsiya! Shikuwa taheer Aleenah hotel ya wuce yasamu shisha yana sha yana huro hayaqi da sauri ko zuciyar sa zata rage zogi sam ba ze jure kallon khaleel A duniya ba!
Gefen zeenah kwance take kasancewar yau Assabar Dr.mansur nanan shi yasanya takasa leqowa dan tasan halin umaima, idan yafita duka za ta sha! Kad'an kad'an take cije bakinta yusura Na ta surutu Amma bata gane komai, "I" kawai ke had'a su. Abun dataga yafi qarfin ta ne tafara salati tana Neman temakon Allah!
Can kuma bayanta yayi damm da ciwo kamar Ana tsagawa da rezor gumi Na tafito mata! Amma dai batayi kuka ba domin yusura datagane zataje ta gayawa dadynta mamy Na kuka! Idon ta sun kad'a sosaiiiiii! Shikuwa mansur jiran fitowar ta yake Amma shiru aransa se Ayyana ta yake har misalin 9:00am shiru!
D'agowa yayi yakai kallon sa ga umaima da tayi d'aya d'aya da qafafunta tana chat da wayarta da fad'inta yazarta 5.4 tana wani silent smile ba ko shakka Duniya Na mata dad'i! girgixa kansa kawai yayi tare da takaicin Rashin mata tagari da Allah ya fauwallah masa idan kuma ya tashi yasan jahilcin ta ze motsa dan haka ya haqura yagani har in wannan hour ta shud'e zeenah bata fito ba.
Zeenah ta dake ,ta dake , Amma Ina bakin rijiya ba gurin wasar yaro bane! garin d'a nisa ne dashi cikin wata murya tace yusura riqeni! Kallon ta tayi tace mamy baki da lafiya ne!?
Hannun yusura ta riqo tace mutuwa zanyi yusura! Ai kuwa da gudu yusura tafita tace dady mamyna mutuwa zatayi! bashiri ya miqe tare da cewa Subuhanallah! Itama umaima miqewa tayi tace ke dan ubanki zonan! jikin ta har Kar karwa yake tace momy dan Allah kiyi Haquri kar ki dakeni! Kunnen ta tamtse tace bana rabaki da shiga harkar ta ba! Cikin b'arin jiki tace nadaina momy kar ki dakeni kinji! Bazan dakeki ba Amma kisani bata sanki kashe ki takeso tayi muguwa ce kinji kice zeenatu dan ba u'war ki bace nan nice mamanki kinji ko!? Mommy meyasa zata kasheni? D'aukar yusura tayi tace mayya ce kinji! Tabata chocolate!
Ganin halin da zeenah ke ciki mansur yadafe Kai, dabarar sa tab'ace ganin yake Kamar be kyauta ba idan yace ze mata V.E (Vagina Examination) Dr. Ruqayya yakira Amma tace tanada case Na haihuwa da yawa! Cije baki yayi sannan ya fara mata Aiki kamar bayaso Amma hankalin sa yatashi domin Abunda ke cikin ta qafafuwan sa ne qasa me makon Kai!
Gashi tana had'e qafafuwan tana washhhh! Shi ko sannu yakasa yimata kamar ba Dr. ba.haka dai yafara Aiki tuquru ya sadda kansa qasa baya kallon private part d'inta dayake mazaunar ko wane hallita akansa take! Ita ko zeenah se Jan jikin ta takeyi da kyar yayi qarfin halin cewa dakata kar naji mik ciwoooi dan Allah! Yana haka har yayi nasarar gyarashi dai dai! Sannan yace ta d'an bud'e qafafuwan ta ganin tana rintse Ido tana washhhh ya gyara mata zaman su yakuma shafa mata baby oil wurin Vagina yadda Abun ze zo da sauqi!.
Normal s/line ya samata tare da bata Oxt. Injection yana bata Haquri koda yafitooo waje duk ya jiqe kamar shine me haiuwar ga mamakin sa umaima bata gidan ko Ina tayi oho! Assemble d'in kaya yayi kamar yadda doka ta tanada domin yadad'e da siya koda haihuwar taxoooo Amma shiru ba tahaihu ba gashi qarfin zeenah baya yake jah kuma yanxu ne haihuwar take 6cm....
Ita kuwa umaima gidan nadeey ta nufa dan yaune zasu gurin mlm kuwa sukayi marmeenat tace shegiya macce mutuwa ce kishiyar ki ko kinchnza!
Hummm chab akan kishiya ai gara qasa ta nitse dani kutashi muje haka suka shiga motar marmeenat....
ASMEENAT ZEEYAN CE✏
[31/07 4:01 PM] YAYA HAYAT: *B.W.A*
*🥁BAKIN GANGA*🥁
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*Story, Written,*
*ASM££NAT Z££YAN*
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12