Share this page
Azee karaya, Allah sarki shikenan she lost him forever, bata san sanda hawaye suka shiga zarya a fuskarta ba.,, "Ganin irin kukan da take harda shesshek'a yasa sa tallafo fuskanta, kallonsa Ummi tayi gamida sunkuyar da kai, da sauri ya rik'e hannunta gam cikin nasa yana mai jin rad'ad'in zuban hawayen ta. "Banda surutan surkullen Laila da Hajiya baja jin komai... i zuwa lokacin takaicin su ya cika Azee, da sauru ta k'arasa gabansu tana hawaye take fad'in" Haba, haba ENOUGH of this, ta k'arashe maganar cikin kakkausar murya.. "Kaman an d'auke ruwa haka d'akin yayi d'if Karime da Laila suka yi tsit baka jin sautin komai sai na kukan Deejah da Ummi.. "A hankali ya k'arasa da wheelchair dinsa gaban gadonta, kallonta yayi yanda lokaci guda ta d'aid'aice, duniya tai mata juyin waina, hannu yasa gamida goge hawayen da suka zubo masa don kuwa ganin Karime ya tuno masa abubuwa da yawa ciki harda mutuwar matarsa masoyiyar sa Hindatu, da kuma mutuwar aminin sa Mumtaz. "Muryarsa ya gauraye cikin d'akin sanda yake fad'in"Karima ki sani ALLAH baya bacci, ki sani ita duniya ba waje ne na tabbata ba, snn duk abinda ka shuka shi zaka girbe, Karima hak'ik'a kinyi ta'addanci a doron k'asa kinyi fasadi mafi muni, kin aikata laifi mafi girma, Karima kin d'auki ran d'an adam ba abakin komai ba, duk a sabida Duniya.. Toh ki sani shi Allah ba azzalumin bayi bane, ya haramta ma kansa zalunci snn ya sanyata haramun a tsakanin bayi. "Fasali ya d'anja kafin ya goge fuskarsa yaci gaba da fad'in" Karima duk wani zalunci da ha'inci da kika min na yafe maki, tsakanin nida ke na yafe ki...."Muryarsa na rawa sanda yaci gaba da fad'in" Amma bayin Allahn da kika yanke masu rayuwa fah, wanda kika zab'i rabasu da rayuwarsu...."Shin su sun yafe ki, anya Karima kina tuna kwanciyar kabari," Kin rabani da Hindatu, kin rabani da Mumtaz, kin rabani da tilon 'yata da jikata ta hanyar haukatar da ita, Fatimah ta rayu babu d'iyarta, taa rayu cikin jinyar hauka, shin kinsan illan bawa ya haukata bawa..."Kuka ya kufce wa dattijo Baba Alhj.. "Da sauri Ummi ta tsuguna gamida rik'e hannayensa, d'agowa yayi yana murmushi yana dubanta still hawaye na kwaranya a fuskarsa, a hankali yaci gaba da fad'in" Alhmdulillah, Allah ya kuma had'ani dasu, Allah ya dawo min da Fateemah da d'iyarta cikin d'an sauran rayuwan da ya rage mun... "Karima yau ga Fateemah ga d'iyarta a tare dani...." "Idon Karime da Laila tsuru tsuru suke kallon Ummi da Deejah, babu alamun nadama a tattare dasu saima wani sharrin da suke shirin k'ullawa a zukatansu. "Maganganun Baba Alhj sun d'aure kan Azeeza, da sauri ta k'araso gabansa gamida durk'usawa tana hawaye take fad'in" Grandpa, ban gane ba, meyasa kake fad'in Ummi is ur only daughter? What about my mum, and Deejah ce kawai jikarka, what about me grandpa, are you going to deny me, nasan nayi kuskure mafi girma, but na gane laifi na, and na canza halayyata, i'll start a fresh....." Tausayin Azeeza ya cika zuciyarsu "Rik'o hannayenta yayi yana tuno kalan k'auna da soyayyar da ya nuna mata a baya, a matsayinta na jikarsa k'wara d'aya, " a hankali ya soma fad'in" Azeeza kiyi hak'uri, har gobe ke jikata ce, keda Deejah bazan banbance ku ba, Azeeza ur grandma cheated on me,.."muryarsa ya soma rawa don baya son tunawa take yaji heart dinsa ya soma masa nayi,.."A zabure Azee ta mik'e gamida k'arasawa wajen Karime, kallon wulak'anci ta soma mata kafin tace" "Tell me the truth, ki fad'a mun gasky nace.... ta k'arashe maganar cikin d'aga murya.,"Karime ido yayi tsuru tsuru.. Baki na rawa ta soma fad'in" Azeeza babu yanda na iya ne, Hindatu zata cinye gida dole na nemo mafita, dole na bada kaina wa boka na...."Ai bata gama rufe baki ba Azee ta sulale a k'asa tana hawaye, sautin kukan ma bai fita..." "Laila cike da makirci ta soma kuka tana fad'in" Hajiya kin cuce mu nida 'yata, waann duk munanan ayyukanki ne, ashe Fateemah ba yayata bace, ashe zamu iya kasancewa KISHIYOYIN JUNA, Anty Fatee, y'ar uwata, dan Allah kar ki bari mijina ya sake, don ba yin kaina bane that i turn to be baster ... hawaye ya soma kwarara mata, tuni zuciyar Ummi ya karaya, hannayen Laila ta rik'e tana tunosu a da lokacin da suke a matsayin yaya da k'anwa.. Ana cikin wann yanayi Sukaji an banko k'ofa an shigo.... "Ba kowa bace illa Yusrah. Kan ubanchan! K'irjin Laila ya shiga dukan tara tara, sikenan wnn tsinanniyar Yarinyar tazo tarwatsa mata rayuwa. Tuni zufa ya shiga keto mata tako ta ina,,, ."Kallonsu ta shiga yi one by one, hango Deejah tayi rungume jikin Irfan da sauri ta k'arasa gamida rik'o hannunta." Sai snn Deejah ta d'ago suna hada ido suka rungume juna.., sosai suke kuka su duka biyu.. "Cikin kuka Yusrah ke fad'in" Ki yafeni Deejah, naci amanarki, na cutar dake, duk wani sharri da tuggu da suka k'ulla maki da taimako na ne, ki yafe mun k'awata, na sani hakkin ki shike bibiyata, gashi na auri wanda nake so din amma ban huta ba, sabida na ci amanarki,.."Kuka yaci k'arfinta. "Kasa furta komai Deejah tayi sai hawaye dake ambaliya a fuskarta, da k'yar ta iya furta" Yusrah ban tab'a ruk'eki ba, you always be d Yussy i knw, the one we always had that beautiful moments together, Allah ya yafe mu gaba d'aya.. "Yussy ta d'ago tanai mata godiya caraf idanunta ya sauk'a kan Azee dake durk'ushe a k'asa, k'arasawa tayi yanda Azee ke kife da kanta tana hawaye. Dago fuskan Azee tayi tana kallonta, Azeen ma ita take kallo. "Yussy tace Azeeza yau zan fad'a maki sirrin da aka b'oye maki shekara da shekaru.... "Jar ubanchan! Cikeda masifa Laila take fad'in" Ke munafukar Allah me zaki fad'a mata, aki wuce ki fice tunda Deejah ta yafe ki duk irin cin amanarta da kikayi, ki fice ki bar family dinmu in peace... "Mikewa Yussy tayi tana murmushi kafin tace" Kiyi hak'uri my husband mistress i won't take much of ur time, sak'o nazo badawa. "My husband mistress" Abunda suke nanatawa kenan a zukatansu. Laila kuwa sai faman kumfan baki take. "Enough mummy! I'm insists to hear what Yusrah's about to say.. Azee ta fadi a hasale. "Murmushi Yusrah tayi kafin ta soma fad'in" Azeeza kin tab'a sanin wanene ainihin mahaifinki.,,"Kutuman uban chan "Laila ta fad'i a zuciyarta, mikewa ta soma yi tana fad'in" Azeeza kar ki yarda da duk abinda makiran nan zata fad'a maki, dangwala k'afarta da zatayi taji Azaban zafi, ihu ta sake tana rik'e k'afar. "Azee na kallon Yussy cikin wani irin yanayi, a hankali tace" Eh na sani ya rasu shekaru biyu da suka wuce.. "Yusra ta murmusa kafin tace" *No ba shine asalin Dad dinki ba, your uncle Safwan kwarton mahaifiyarki tun na d'an shekaru sha shida a duniya shine mahaifinki*... "Zukataansu suka girgiza, innalillahi wa inna'ilaihirraj'iun, anya Karime da Laila mutane ne.. "No that can't be, is just can't be, uncle Safwan is my only uncle, he can't be my father..." kaman zautacciya haka Azeeza ta koma, hannu Yusrah tasa cikin bakin zaninta kafin ta ciro wata takarda ta mik'a wa Azee, take this, this is d proof "Kallon takardan tayi kafin ta kalli Yusrah, hannunta na rawa ta amsa, DNA result ne wanda yake tabbatar da cewa Safwan shine real biological father dinta.... "Wani ihu Azeeza ta sake gamida d'aura hannu aka ta zube k'asa, kuka take tamkar ranta zai fita,.. "Kaman wacce aka zabura tayi kan Laila gamida cakumo wuyarta tana fad'in" Laila ki fad'a mun da bakinki, Safwan shine Biological father na, ki fad'a mun Lailaaaaaa....! Daidai nan Safwan ya banko k'ofa ya shigo tamkar wanda aka koro.., "Had'a idon da sukayi da Irfan ya gane Safwan, a hasale yayi kansa yana fad'in" How dare you blackmail my wife.. naushi ya kai mai a hanci saida ya fashe, ya shiga kai mai naushi ta ko ina, da sauri Deejah tayi kansa tana rikosa, Daddy na k'ok'arin k'watan Safwan don kuwa yaji jiki hannun Irfan.. Kuka Deejah take tana fad'in" Pls let him be, kaji my love, Engr ma gyada masa kai yayi alamun yabi maganar Deejah.. kallonsu Irfan yayi bazai iya kin bin umarninsu ba coz he lubs them, a hankali ya rik'o hannun Deejah kafin ya furta" Lets get out of here baby i can't stand them anymore, daga haka suka fice hannun su sakale cikin na juna. "Da k'yar Ummi ta k'waci Laila a hannun Azeeza, Azee na kuka take fad'in" Ummi ki barni na kashe wann bitch din bata da wani amfani, she ruined my life.."Ummi bata saduda ba sai faman lallashin Azee take. D'agi idon da zatayi ta sauk'e su kan Safwan, wani tsallen ta kuma yi kafin ta k'arasa ta rik'o kwalan rigarsa da iya k'arfinta..." "Is it true, tell me, is it true???? "Safwan cike da tashin hankali yake fad'in" Azeeza ki saurareni pls swethrt, yeah it is truem yku are my flesher blood, i'm your dad that's why i can do anything for you, koda zan rasa raina ne, "But believe me my dear, babu laifina alaifin momyn ki ne, she forced me since from the very beginning, ita tayita samu aikata wann mummunan aiki, snn har bayan mutuwar mijinta my brother bamu daina, har ta auri Engr Nazif bamu daina ba,,,"Ya dan kai kallonsa ga Engr wanda fuskarsa ta koma jazur... A hankali ya k'arasa gabansa zaiyi magana Engr ya d'aga masa hannu kafin yace" She's all yours, you can have her, banida sauran alak'a da ita, shes not longer my wife... Daga haka yaja hannun matarsa ya sakar mata murmushi kafin yace" Lets get out of here Hayatee.." Dan kallonsa tayi fuska cike da damuwa zata yi magana, ya dora mata yatsa a baki gamida cewa shiii, let's go. Kwanto da ita yayi kan k'irjinsa kafin suka fice, jikinta a sanyaye. Ya rage saura yasu yasu don dama tuni an fita da Baba Alhj an kaisa dak'in hutu, sabida heart dinsa yayi weak, "Tsugunawa Azee tayi wajen tana kuka mai tsuma zuciya, why is this happening, why, meyasa rayuwa ta kasance haka, her own mother is a baster, and now she also turn ti be baster, her so called uncle turn to be her real biological father... "Safwan zai durk'usa gaban Azee kenan Yakumbo ta shigo bayan biye da polisawa har guda uku., kuka take tana nuna Safwan da yatsa, cikin kuka take furta, oficer ku kamasa gashi nan, shi ya kashe mun d'anaa.. "Safwan cike da tashin hankali yake fad'in" Yakumbo nine fah, nine Safwan dinki, meyasa zaki min haka.."Oficer ya tallafo keyarsa kafin yace sajent arrest him. Nan akayi arresting Safwan aka tasa k'eyarsa... Da gudu Azee ta k'arasa ta rungume Yaakumbo, tana kuka take fad'in" Ki yafe mun kaka ta, ki yafeni...."Share hawayen idon Azee Yakumbo tayi kafin tace" Na yafe ki Azeeza, Allah ya yafmu gaba daya,...."Ganin Yakumbo zata fice da Azee yasa Karime fad'in "Ina zaki kaimin jika mayya, zuriyan aljanai, basu ko tanka ta ba suka fice suna rungume da huna,. "Daki ya rage saura masu shi wato Karime da laila, haba nan suka kaure kowa na tsine ma kowa cikinsu, abu kaman wasa ihu suke sosai kaman mahaukata nan suka shiga fincikan naman jikin juna suna sunbatai wanda har saida yaja hankalin likitoci. "Suna haraban asibiti suna k'ok'arin shigewa motocin su aka fito za a wuce da Safwan.... "Kallon Deejah ba tare da yace komai ba, oficer ya kwade kafarsa gamida fad'in " Move..! "Juyows Deejah tayi tana kallon Irfan murmushi ya sakar mata kafin ya bud'e mata marfin mota yace" let's go Mrs Irfan Mumtaz... murmushi ta sakar masa kafin ta shige cikin motar.. "A kan idon Azee komai ya faru, sun burgeta, A hankali ta rik'o hannun Yakumbo sosai suka fice neman adaidaita. "Sauk'arsu kenan a airport, ko a mafarki bata tab'a zaton Daddyn twins zaizo Nigeria bam yau sai ga shinan a birnin tarayya Abuja, wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Irfan..... *Kudai k'ara min uzuri masoyana, jiki da sauk'i sosai, na gode k'warai da kulawarku, da wanda suka turo sak'o da wad'an da suka kira harma wanda suka min addu'a a zukatansu, na gode k'warai, Allah bar k'auna.. #1Luv😍😘* Sameena ceπŸ‘ŒπŸΎ πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ *Mallakin Waye* 102 *Β©Sameena Aleeyou... ✍🏾* _Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_ "Ajiye Deejah Irfan ya soma can family house nasu kafin ya wuce airport d'aukosu Alhj Abdullah, "Tunda Engr ya sanar wa Ummi batun zuwan abokin kasuwancin nasa hankalinta ya gaza kwanciya. Haka kurum take jin matsanancin fad'uwar gaba wanda ta rasa dalilinsa.. "Deejah da Nadiya sai faman zirga zirga suke tsakanin parlor da kitchen. Motsi ksd'an idan Nadiya tayi Ummi takance maza ta bar aikin nan taje ta huta.... Dukda ita kanta Deejahn ma bata jin dad'in jikinta, k'ok'ari kawai take don bata so a gane batada lafia, Tasan idan Irfan ya sani he won't let her work n zai kaita asibiti a mata allura abinda take matuk'ar tsoro.... "Ammah ta share k'wallan da suka zubo mata sanda Engr ya gama labarta mata halin da suka baro Laila da Karime, tabbass duniya makaranta ce , Allah yasa hakan ya zame wa masu hali irin nasu ishara Ameen... "Gidan ya gauraye da k'amshi kala Kala, dishes kala daban daban suka girka, kama daga kan na k'asashen k'etere u want namu na gargajiya. Da taimakon Ummi da Hajja suka kammala komai.. " "farin cikin da Ammah ke ciki bai misaltuwa, burinta Allh ya cika mata shi, Family d'inta ya had'u gwanin ban Sha'awa, Nazif da Fatima Sun cika burin marigaya Ma'aruf da Hindatu. Alhamdulillah..... "Babu yanda Mr chairman baiyiba kan Irfan ya fara biyawa dasu masauk'i firr Irfan yak'i amincewa, Afnan da Ayla ma sunyi insisting a soma zuwa wajen Aunty Dee, haka Aunty bilki ma. Babu yanda Mr chairman ya iya dole ya hak'ura a soma zuwa gidansu Irfan.... "Shi kuwa Mr chairman ba wai baison zuwa bane, Allah kad'ai yasan abinda yake ji k'asan zuciyarsa. Shakka babu wani babban Al'amari na shirin faruwa dashi... "Haka suka d'unguma suka nufi gidan Engr Nazif Mumtaz wanda ke a unguwar lifecamp. "K'irjinsa ya tsananta fad'uwa sanda Irfan ya gama parking a haraban gidan.... "har suka gama ficewa daga cikin motar Alhj Abdullah bai sani ba... "Kallon gidan yake kanyi tunaninta ya fad'o zuciyarsa... "Tabbas yana jin presence d'in Fatima yana jin k'amshinta.... "Hannusa da Ayla ta rik'o me tana fad'in" Dady let's go the house is huge, I love Nigeria.... Wannn maganganu na Ayla shi ya katse masa tunaninsa, Irfan yayi masu iso... "Da gudu yaran suka tafi suka rungume Deejah, farin ciki maras misaltuwa suka tsinci kawunansu.... Deejah ta k'arasa ta rungume Aunty Bilki cike da murna, tarba sosai su Ammah da Ummi suka mash. "Alhj Abdullah kam tuni Irfan ya masa masauk'i a babban parlorn Engr, sai firan kasuwanci dana siyasa suke abunka da manyan mutane masu hannu da shuni...... "Tunda tayi tozali da matar hankalinta ya gaza kwanciya, tabbas fuskar matar yana tsananin kama da tsohuwar matar mijinta, saidai wannan ta nuna mata shekaru. Duk wani mostin da Ummi zatayi tofah idon Aunty Bilki na kanta, gaba d'aya jikinta yayi sanyi.. Duk labaran da su Deejah keta janta dashi amsasu kawai take amma ko kad'an ta gaza samun sukuni deep down a b'angaren Ummi ma wani bak'on yanayi takeji wanda bazata iya misaltawa ba, Mikewa Deejah tayi ta nufi kitchen cikin Sauri don ta baro barbeque a wuta. "Aikuwa nan ta samu ya soma k'onewa "Oh shit, cikin sauri ta kashe stand din tana kwalla kirawa ma'aikatan..... "Kaman daga sama ta jiyo hannun mutum Ya zagaye kunkuminta gamida kwanto da kansa yana shak'an k'amshinta, murmushi tayi kafin ta juyo suna facing Juna, take to soma jin kummali don gaba d'aya ji tayi bata son k'amshin turaren Irfan, "Irfan kuwa dad's matsota cikin jikinsa tuni idanunsa Sun k'ank'ance Sun canjza launi zuwa ja, tuni ya soma aika mata da ask'wanninsa masu wuyar d'auka.. "Tureshi ta somayi tana fad'in" what are you doing ya Irfan, someone might see us, kaga fah nan kitchen pls stop it..... Tana fad'i tana toshe hancinta sabida turarensa. "Cikin magana da yafi kama da rad'a yake fad'in" pld Baby don't say no, don't reject me, I can't help it anymore, rabona dake fah tun dawowar mu Nigeria, bakijin tausayi nane ai nayi k'okari. "D'an yamutsa fuska tayi ga yawun da ya cika mata baki, da sauri ta k'arasa washing base to zubar da yawun, Irfan ya bita da ido bai fahimci komai ba, matsowa daf da ita ya kuma ya shige jikinta har wani b'ari jikinsa keyi,... "Turesa ta shigayi tana fad'in" wai ka mance wani gida muke ne, and dakwai bak'i fah a gidan snn idan wani ya shigo ya ganmu a haka fah, fad'a fad'a take maganar nata.... "Kallonta kawai yake yanda duk ta canza lokaci guda, yatsun hannunta ya jawo yana d'an murzasu kafin yace, cikeda sigan shagwab'a" Baby kad'an fah kawai zanyi I promise, oya let's go to my room kinji Baby, ko na d'aukeki ne... . "Ynda yayi maganar ya bata tausayi amma ita harga Allah bama zallan turarensa bane sam bataso ya kusanceta balle yanzu data sami sauk'in jarabarsa... "Yana kokarin starts knn Ammah ta shigo kitchen d'in tana fad'in" Hajja wai meke k'onewane haka...... "Turus taja ta tsaya ganin mutane sunyi cirko cirko.... "Deejah duk kunya ya cikata sai kokarin kintsa kanta take yanda Irfan ya jagwalgwalata, sai faman gyara boobs d'inta take tana maidasu cikin riga.. "shi kuwa gogan shafa keyarsa ya d'anyi kana ganinsa kaga maras gaskets,. Tuni ya soma 'yan kame kame, Em my precious Granny mun kashe dama barbeque ne ke k'onewa... "sosai yaso bawa Ammah dariya, sarai ta gane me ya faru, ga kunyan da ya lullub'e Deejah..... "D'aure fuska tamau Ammah tayi kafin tace shine saika biyota har kitchen Oya fice ka bamu waje..... "Irfan yasa fuskan tausayi kafin yace "Ammah dama cin abinci nake shine nace takaimun ruwa "Right sweetheart" Ya k'arashe maganar yana kashe ma Deejah ido.... "Harara Deejah ta galla masa gamida turo baki gaba.... "Ammah ma hararan to wurga masa kafin tace" Oya d'auki ruwanka ka fice n ka barmu muyi aikinmu in peace.... "Irfan ya lashi leb'en bakinsa da k'yar kafin yayi kalan tausayi yace" Ammah pls let her bring the water pls mana Favorite Granny... Zaka fice kokuwa ta fad'i tana hararansa.... "Kallon Deejah ya kuma gani yayi tanai masa dariya k'asa k'asa harda gwalo.. "Kallon zamu had'u ya mata kafin ya fice daga kitchen d'in..... "Koda aka had'u gaba d'aya a parlor don cin abincin shareta yayi, tazo zatayi serving nasa ya basar. Sadiq da Nadiya sai satan kallonsu suke suna dariya k'asa. Don sunsan dawan garin... "Ummi Tana tashi ta nufi kitchen kenan Engr da Alhj Abdullah suka shigo. Gaba d'ya su Deejah suka soma gaishesu. Aunty Bilki ma ta gaida Engr gamida yin godiyan hidaiman da aka masu, cikeda fari'a Engr yace " a'a ai duk an zama d'aya Allah dai ya bar zumunci. Gaba d'aya suka amsa da ameen... "Ammah ce ta shigo hannunta rike da cazbaha da alama lazimi ta idda... Har k'asa Alhj Abdullah ya k'arasa ya gaisheta, cike da fari'a ta amsa harda d'an jansa da hira, akasarin hiran mahimmancin zama a k'asarmu da koyin al'adun mu take kan nuna masa, kasancewar itama ta zsuna a can turai d'in taga tasiri da illa da al'adun wasu yayi a rayuwar jikokinta a baya . "Alga Abdullah kuwa yaji dad'i sosai babu kaman Aunty Bilki wacce take son zaman k'asarta tunba yau be..... "Engr ya dubi Nilam da suke faman hayaniya ita dasu Ayla yace" Daddy's precious oya go Call your Ummi.. "Da gudu Nilam ta tafi kiran Ummi.... "Rik'e take da hannun Nilam sanda suke fitowa daga corridor din da zai sadaka tsakanin parlor da kitchen.... Sai faman biyewa Nilam take da surutan yarintan ta.......... " "Kasa d'auke idanunsa yayi daga dubanta, tabbas itace, shakka babu itace "Fateemah ce yau gashi ga Fatima...... "Kirjinsa bai bar bugawa da sauri ba haka idanunsa basu daina kallonta ba har ta k'araso cikin parlorn......... Sameena ceπŸ‘ŒπŸΎ πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’πŸŒ’ *Mallakin Waye* 103 *Β©Sameena Aleeyou....✍🏾* _Queen Samy Novels Forum.... πŸ“–πŸ“š_ *Bear with me for the spelling n typing errors plsπŸ˜…* "Cak taja ta tsaya sanda Engr ke fad'in "Fateema k'araso ku gaisa da Alhj Abdullah, chairman na *Abdullah Musa Construction Company*...... "Fuskar da tafi tsana a duniya yau shi ta kuma yin arba dashi, mutumin da ko a mafarkinta bata k'aunar su kuma had'uwa..... "Girgiza kai ta soma hawaye na shirin ambaliya a kumatunta, baki na rawa tana nunasa da d'an yatsa take furta " No, no, me wannan azzalumin bawan yake a nan,......."Shima Aljh Abdullah tuni hawaye sun soma kwarara masa, His whole life fatan sake gamuwa da ita yake, tabbas yasan hskan ne zata kasance, yasan bazata tab'a yafe masa ba, babban abunda yafi d'aga hankalinsa shine tayi aure bazata tab'a zama *Mallakin sa* ba..... "Kallon kallon illahirin mutanen dake parlorn suka soma yima juna..." "A hankali Engr ya k'arasa yana k'ok'arin jan Alhj Abdullah waje yana fad'in kayi hakuri Chairman bata jima da warkewa daga rashin lafiya ba.. I'm sorry pls..... Muryar Engr ne ya sarke sanda yaga hswaye saman fuskan Alhj Abdullah.... Cak suka tsaya su duka biyun... "Ummi bata daina kuka tana fad'in a fitar da wannan mugun ba... "Deejah Nadiya harma dasu Nilam suka k'arasa gamida rungumeta. Su Ayla kuwa jikin uwsrsu suka nufa suma wacce tuni itama idonta ya jike' da hawaye. Momy what's going on why u crying, aren't gonna be happy here..... Kasa amsa su Aunty Bilki sai hawaye..... "Fateemah nasan ban cancani yafiyarki ba amma bazan fasa rok 'onki gafara ba, ki yafe mun duk irin muna nan ayyukan da na aikata a baya, tuni na gane kuskurena na kuma gyara . Fatimah kece dalilina na k'in dawowa k'asata shekara da shekaru. Don Allah kimin aikin gafara, zuwan nan da nayi ma don nayi arresting Hajiya Karima ce wacce ta tilasta mun duk wani aikin da nayi a baya. Ko Bilkisu ban fa'da mata wann mission nawa ba

Chapter 38 of 40