missing those moments da nakan dauke k gaban doki tun muna _Los Angeles_.......
"Irfan yasa hannunsa ya goge hawayen da suka zubo masa kafin yace" when mummy was still alive, "Engr ya juyo ya kalle sa take tausayin d'an nasa ya kamasa, sauk'owa yayi bisa dokin dama already sun iso wani park, kama dokin Irfan yayi ya taimaka masa ya sauko ya cire masa helmet din dake kansa shima ya cire nasa kafin suka k'arasa kan wani dogon kujera me daukan sama da mutum biyu suka zauna.
"Har lokacin Irfan na share fuskansa......" Engr ya rungumesa take shima yaji k'walla na nema ciko masa ido sabida tausayin d'an nasa, a hankali ya soma lallashinsa. " It's Ok Son, dukanmu munyi rashin Khadeejah Allah yayi mata rahama, she's in a better place right now.
"Daga kansa yayi kafin yace haka ne daddy I love you,.... I love you too son.
"Daddy meyasa 'yan uwan mummy tinda ta rasu basu tab'a zuwa Nigeria ko sau d'aya sun duba mu ba......." Take annurin fuskan Engr ya dauke cak..... Irfan ya sake maimaita masa tambayan da cewa" Daddy meyasa tun tasowarmu bamusan dangin mummyn mu ba, tun lokacin mummy na raye idan na mata maganar fada take min why daddy...." Mikewa Engr yayi kafin yace" Enough Irfan, zan gaya maka, but this is not the right time, we are here to talk based on another issue.
"Irfan bana son aurenka da Deejah, ka nemo wata yarinyar na aura maka........" Kaman sauk'an aradu haka Irfan yaji kalaman mahaifin nasa yayinda k'irjinsa ya koma tamkar an d'aura dutse.......ββββ
*Tofah masu karatu muje zuwa*
πΈπ»QueenSamyNovelsπππ....
[8/22, 14:46] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
46
*Na Sameena Aleeyou*
" K'irjinsa ne yaci gaba da dukan tara-tara sanda ya dago yaga fuskan Dad dinsa babu alamun wasa. Da k'yar Irfan ya iya lalub'o kalamai ya soma fad'in" Daddy pls don't do this to me, I love Deejah...... I love her with all of my heart. I can't bear loosing her...." Enough!!! Engr ya daka wa Irfan tsawan da yasa yin shiru babu shiri.... "
" Irfan na riga na gama magana, kaje ka samo wata na aura maka but Deejah,......"Daga haka Engr ya wuce ga dokinsa ya gyara linzamin ya soma tafiya....
"Tashin hankali wacce ba'a saka mata rana, jinsa yake tamkar a wata duniya..... da kyar ya iya mikewa dan barin wajen....
"Tunda Engr ya isa gida zuciyar sa ta shiga tuhumansa kan bai kyautawa Irfan ba, take kuma shawarin matarsa Laila ya fad'o masa" _Irfan shine danka na fari bai kamata ka barshi ya auri wacce batada asali ba, wata rana idan baka nan irfan shine magajinka, shin zaka so manyan mutane abokan ka suyi tattaki daga kasashe zuwa auren danka da matar da batada asali balle tushe_........ " Take ya toshe kunnuwansa dan kuwa gaba d'aya ji yayi bai son tuno kalaman Laila, kai duka wann abu marassa kyau da Laila ta fad'i gameda Deejah ko kad'an bai rage abunda Engr keji akanta ba, _Toh wai me Engr yake ji gameda Deejah ne_..... "Shi kansa Engr Nazif bashida wann amsar.
"Kaman wanda aka jefo shi haka Ammah ta gansa tsaye akanta...." Irfan lafiya meke faruwa, ta tambaya sanda ta k'arasa ta rik'o hannunsa....." Rungume Ammah yayi sanda yaji hawaye na k'ok'arin bin k'uncinsa" Ammahhhh ki fada mun meyasa Daddy baiso na auri Deejah pls Ammah..... yayi maganar cikin rawar murya.
"Kalaman Irfan sunyi matuk'ar bawa Ammah mamaki, yanda take ganin Engr ya rik'e Deejah tamakar 'yar da haifa batayi tunanin za'a sami mishkila daga garesa ba, mussaman duba da yanayi na hankali da nutsuwa da Deejah keda shi. "Ammah ta rik'o hanunsa suka zauna bakin gado, ta rik'e hannayensa sosai cikin nata kafin tace" Irfan ta yuwu Daddynka ya hango wani abu damu bamu hango ba, child kayi hakuri........" bata gama rufe baki ba Irfan ya mik'e idanunsa sun kad'a sunyi jajur haka fatar jikinsa tamkar jan gauta haka ta koma....., kallon Ammah yake yana girgiza kai kafin ya soma fad'in" So you don't want my happiness too, you want me to live a miserable life.... Granny I thought you loved me, I thought you'll be by my side, I thought I could feel presence of my mum with you... ashe ba haka bane, I was wrong all this while danayi tunanin kinfi kowa understanding dina, how I wish my was here or even her own mother or maybe her relatives nasan su zasu fahimce ni bazsu taking side din daddy ba,......" Shut up Irfan Ammah ta katse sa!!!!
"Irfan ya d'ago ido yana kallonta tun tasowar sa bata tab'a mas irin wnn tsawan ba. "Yana huci siririyar hawaye take bin idanun sa guda d'aya. " Gyada kansa yayi yana murmushin takaici kafin yace" Na dauka idanazo maku da batun aure zaku saurare ni and you'll be happy, but I was wrong.
"Yasa bayan hanunsa ya goge hawayen da ys sauk'o masa kafin yace" Zan tafi zan koma loss Angeles, I can't stay here any long...." Zai fice Ammah tayi saurin rik'osa hawaye na k'ok'arin kufce mata take fad'in" No Irfan dan Allah kr kuma tafiya ka barmu, bansan meyasa Daddynka bai son aurenka da Deejah ba,,,, she's not the only girl ka nemi wata koma er gidan waye I assure you zansa ya aura maka ita.....
"Girgiza kai ya soma yana k'ok'arin fizge hanunsa yake fad'in " Granny I LOVE ONLY DEEJAH....... JUST HER ONLY HER. Can't you understand, zan tafi zan nemi 'yan uwan mummy na duk yanda suka shiga I know they will support me. Daga hak ya fincike hanunsa daga rik'on da Ammah ta masa cikin sarsarfa ya isa k'ofa tana kiransa ko tsayawa beyi ba,.
"Daga yanda suka lab'e sun gama ganin komai, Lail ta shek'e da dariya tace ashede maganin malamin nan aiki.... Azee da damuwa ya d'an nuna a face dinta tace" momy what if he leaves yaya zanyi na shiga uku, kinga yanda ya koma tamkr damisa anya zaiji lllashi ya yarda ya zauna, karfa ya tafi American. ?......" Murmushi Laila tayi ta shafi kan Azee tace" yaro dai yaro ne, Azeeza ki kwantar da hankalinki malam na kan buzu ya tabbatar mana babu yanda Irfan zaije, haka dai zasu gama fadace fadacensu da iyayensa har ya sauko tinda ya ksance yaro mai biyayya dukda kafiya da taurin kan da yake dashi.... Azee ta sauke ajiysn zuciya... ganin Ammah da Engr sun nufi sashen Irfan hankai a tashe yasa su saurin juyawa da niyyan barin wajen, saiji sukayi Azee ta buge tukunyar da Malam na kan buzu ya basu, yana isa k'asa kuwa ya fashe tushhhhhh!!!! Wani ihu Azee ta sake Laila tayi k'arfin halin toshe bakinta dukda itama masifan tashin hankaline ya ziyarceta, dan kuwa na kan buzu ya sanar dasu kwaskwan nan tana fashewa to babu abinda zai hana auren Irfan da Deejah......
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
"Da k'arfi Engr ya shiga doka k'ofan Irfan yana kiran sunansa," Irfan!...Irfan!! Son open this door........
"Jifa da kayans yaci gaba da yi daga cikin sip yana cusawa cikin trolley... " kome ya tuna kuma sai gani nayi ya nufi k'ofan jiki a sab'ule.... ysna budewa ya koma cikin dakin
"Ammah da Engr sukabi d'akin da kallo yanda duk ya haustina yayi fashe fashe. Bai ce masu komai ba sai kobawa da yayi yaci gabs da hada kayansa......" Irfan will you stop this nonsense and listen to me!!!!"" Engr ya fadi cikin daka tsawa.
"A hankali ya dago kansa wasu hawayen na k'ok'arin zubo masa yake fad'in" Daddy I need to go and find my mum's relatives tinda ku kunk'i gaya mana yanda suke, idan zan iya tunawa lojacin mummy tana raye ta tab'a cemun ita er asalin Lebanon ne, garin Berut, zan je na neme su,... su nema mun auren tinda ku....."Marin d Engr ya kifa masa ne ya hanasa k'arasa maganar, da sauri Ammah ta k'araso ta rungume Irfan......."Ya isa haka, ya isa Nazif, kar ka sake tab'asa, idan baso kake yayi irin rayuwar da kayi a baya ba toh ka aura masa wacce yake so,,.... " Cikin kunan rai Engr yake fadin " bazan aurawa d'ana yarinyar da bamusan salinta ba, Ammah pls kar ki biye Irfan har yanzu yaro ne....."Kasacewa komai Irfan yayi sai kallon mamaki da ysbi daddy dashi, watarana idan daddynsa yayi wani abu tamkar bashi ba.....
"Cikin zafin rai Ammah take fad'in " idan har Khadeejan yanzu batada asali ka fada mun shin khadeejah ta farko kasan asalinta? Shin kasan iyayenta ne har ka yarda ka aureta.....Kasa karasawa Ammmah tayi dan kuka dake shirin kufce mata, da sauri ta fice daga dakin Irfan.
"Engr ya dago yana kallon Irfan duk shima jikinsa yayi sanyi, kirjinsa na dukan uku da kyar ya iya furta, "Irfan.........." Irfan yayi saurin katsesa da girgiza kai kifin ya soma fadin cikin rawar murya irinta me kuka"
"Daddy dama mahaifiyar mu batada asali..... daddy dama wann ne dalilin da yasa muka kasa sanin dangin mahaifiyarmu tun tana raye.... daddy dama wnn ne dalilinku na b'oye mana......
"Girgiza kai Engr ya soma cikin rawar murya yake fad'in" Irfan mahaifiyar ku tanada asali, mahaifiyar ku tanada asali. Da kyar ya k'araso yanda Irfan yake su duka biyun suna kuka.
"Hannun Irfan ya rik'o suka zauna bisa sofa kafin ya soma fad'in " Son yau zan baka labarin sirrin da muka birne maku ya goge hawayen idonsa kafin ya soma fad'in"
" Tunda nake da mum dinku ban tab'a sonta ba, macen da na so a rayuwata guda d'aya ce tak, kuma tunda na rasata ban kuma son wata ba, d'iyar Baba Alhjai 'yar uwar Laila FATEEMAH itace macen danaso da duka zuciyata,
"Mahaifiyar ku....... Sai kuma ya danja fasali hawaye na k'o'karin ciko idonsa. Irfan ya bude idanunsa sosai yana sauraren me Daddy zaice.
"Engr ya share hawayen idonsa kafin yaci gaba da fad'in " Mahaifiyar ku aiki take a wani resturant dake cikin makrantar mu a lokacin, kullum idan naje sayan abinci ita ke kawo mun, nasha mamaki ganin ita kdaice musulma cikin masu aikin wajen, kullum zaka ganta cikin yalwateccen kaya snn gashinta a rufe ba kaman sauran ma'aikatan ba,
"Toh ana nan wata rana na shigo cin abinci sai na tarar shugan wajen wato me rusturant din yana faman cin zarafinta..... yana k'o'arin rabata da suturunta wai bata kawo masa customers, ma'ana bata zan ra'ayin masu zuwa cin abinci.
"A ranar nayi duka ma baturen nan dan kuwa duk yanda naga za'aci zarafin mace tofah sai yanda k'arfina ya k'are..... a takaice dai na kwaci yarinyar nan a wann rana. Na kafa masa doka kan cewa duk randa ya takurata tofah zan hada sa da hukuma. Kasan bature idan
Kwai abinda yake tsoro tofah hukuma ne. Da wnn yarjejinya muka rabu.
"Bayan wasu kwanki naje wann resturant har sau kusan biyar bani ganinta, koda na tambayi wata daga cikin ma'aikatan sai cemun tayi ai an koreta. Ban kwo komai ba a lokacin nace yamafi mata sauki..
"Toh bayan kaman sati na ganta a ksan gada tana kwance dashike watarana da kfa nse shiga cikin schl dan gidanmu babu nisa da sch.
"Tunda ta ganni naga t soma murna, toh nan dai ta bani labarin itama zuwa tayi illegally ma'ana ba ta amintecciyar hanya take zaune a US ba, koda na tambayeta dalili sai ta fashe mun da kuka, haa nayita lalashinta, krshe har ta hakura ta bani kabarin knta, yanda ta sanar dani iyayen mahaifiyarta sun kasance masu kudi sann ita kadai Allah ya basu, sun rasu sun bar mata tarin dukiya, tanda masoyi wanda ashe dan kudinta yake sonta, yan uwanta basuso aurenba amma kasancewar ita tanaso dan haka suka aura mata shi, koda ta haifi Khadeejah suka hade baki suka kasheta shida matarsa dama batasan yanada wata mata ba, nan sukayita gallazawa khadija azaba har kawo girmanta yanda mahaifinta da kishiyar uwarta suka tassama kasheta ta tsere ta biyo jirgin ruwa ta taho US......labarin gallazawan da wad'an nan bayin Allah sukayi wa Khadjia babu dadin maimaitasa. Na tausaya mata sosai, dan kuwa taga rayuwa.
"Da kaina na kawota gida wajen Ammah, na bata kabarin ta, Ammah ta tausaya mata snn ta riketa tamkar 'yar da ta haifa, toh ana a haka Ammah ta matsa sai na auri Khadeejah ganin yanda take bala'in sona, ni kuwa a da nayi kudirin nida aure har abada tunda ban samu Fateemah ba, da matsi da naci dai har na yarda na aureta... tunda muke tare ban tab'a fada mata kalman so ba koda daidai da rana guda ne, tayfarkin hakan ta ksance yafi sau babu adadi amma hakan bata kasance ba, Khadeejah tana mun son da bansan adadinsa ba, a haka har taifa min ku, yanda ta rok'eni kar na nunawa yaranta bsna sonta, na kuma mata wann alk'awari. Toh har bayan ta haifi Nilam randa zata bar duniya saida taso na fada mata kalman so "amma ban fad'a mata ba dan ban kawo mutuwa zatsyi ba......... " kuka me k'arfi ya kufce wa Engr...... "Irfan wanda shima hawayenne ya wanke masa fuska da sauri ya rungume dad dinsa yana kuka, saida sukayi mai isarsu babu me iya lallashin kowa kafin Engr yaci gsba da fad'in " Khadeejah ta mutu bataji wann kalma na so a bakina ba, nayi kukan rashinta nayi kuka sau babu adadi. Shiyasa nayi alk'awarin son abinda ta haifa ta bari da iya abinda na *Mallaka* shiyasa na dauki son duniya na daurawa 'ya'yanta shiyasa nayi devoting my entire life to her children...... "Shiru sukayi na dan lokaci yayinda kowa a cikinsu ke sharan kuka.
"Ammah dake zaune a parlor ta gama jinsu, ta share hawayen da ya wanke mata fuska, hakika yau mutuwan khadeeja ya zame mata sabuwa, yarinyar arziki wacce a iya zamansu bata tab'a sab'a umarninta ba koda da rana guda. A haka Ammah ta shigo ta zauna a tsakiyan Engrr da Irfan ta dafe kafad'unsu.
"Da kyar ta daidaita kanta kafin ta soma lallashinsu. Gaba daya suka rungume juna.
"Addu'a sosai Ammah tayiwa mummyn su irfan gaba daya suka amsa da ameen Ammah.
"Engr na kallon Irfan yana murmushi shi kadai yake ayyanawa a zuciyarsa _"koda ace son Deejah yake toh kuwa hak'ik'a zaiyi yak'i da zuciyarsa ya kalleta a matsayin d'iya danta kasance da Irfan, hak'ik'a farin cikin y'a'yan sa shine nasa_.
"Dafa kafadan Irfan yayi kafin yace" Son na amince ka auri Khadija na amince Son...... "
"Kallon Engr Irfan yake full of surprise kafin ya mike yana fadin " Really daddy, you mean ka amince na kasance da farin cikin rayuwata. Gyada masa kai Engr yayi yana murmushi kafin yace" yes Irfan na amince zan cikawa Khadeejah burinta na sanya yaranta cikin farin ciki ko yaushe, forgive me Son akan abunda na maka earlier I lost my mind ne that's why, I don't know why did that......... "Irfan kam baisan sanda ya rungume Engr ba yana masa godiya"
"Ammah ta goge hawayen idonta tana kallonsu cike da si kauna, kaikace yaya ne da k'ani.
"Ya karaso ya rungume Ammah kafin yace" Ammah I'll be with her forever...... Murmushi Ammah tayi ta shafi kansa kafin tace " farinckinku shine namu Irfan.
"Engr yana kallonsu yana murmushi ya k'araso ya dafa kafadun Irfan yace" suna hada ido Irfan yaji kunya ya dan suke kansa k'asa yana sosa k'eya.
"Murmushi Engr yayi kafin yace zamuyi maganar ranar auren da Granny dinka kaji, for now ka mayar da kayanka mazauninsu.
"Rungume Engr Irfan ya kuma yi yanai masa godiya.
"Ammah ta jawo kunnesa tana fadin " ko kunyata bakaji ko oya wuce bathroom kayi wanka ka hau doki...... zaiyi magana ta mika masa towel ta jefa sa cikin toilet. Tana murmushi sanda ta jiyo shi yana fad'in " I'mmmmmmmmmmm in looooooooooveee.
"Murmushi kawai tayi ta shiga tattara masa dakin tana fadin "Silly boy hadi da girgiza kai......
πΈπ»QueenSamyNovelsπππ...........
[8/22, 14:47] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
47
*Β©Sameena Aleeyou*
"Na shiga uku momy yanzu inaji ina gani shegiyar yarinyar nan zata auri Irfan..... gaskiya momy bazata saku ba, ni danaga auren Irfan da wata ai gwara naga mutuwata.. cewan Azee da damuwa ya nuna k'arara a fuskarta.
"Murmushi Laila tayi kafin ta dafe kafa'dun Azee tace" yaro dai yaro ne, idan banda abinki ina kika tab'a ganin anja damu, ki daina sarewa kinaba dani Azee saikace ba d'iyar Laila jikan Hajiya Karime kike ba, ki kwantar da hankalinki, idan sunsan wata basu san wata ba, idan mun b'ulla masu ta sihiri da asiri baiyi aiki ba sai mu b'ulla masu ta makirci kissa da kisisina...." shiru tayi na d'an lokaci kafin ta d'ago tana duban Azee tace " yawwa ina abokin Irfan da kwanaki ya amshe pride d'inki na d'iya mace.
"Azee ta d'an tab'e fuska kafin tace " wai Ahidjo tabb niko me zanyi dashi...
"Laila tayi murmushi kafin tace" ai kuwa dole yanzu yayu mana aiki tinda dama kince son Deejah yake...." tsalle Azee ta daka kafin tace " ai kuwa nama tuna momy turn dinsa yazo dole ya bani something in return na abinda na basa kwanaki, dole yasan yanda za'a k'ulla sharri wa jarabebbiyar Nanny din nan.
"Dariya Laila tayi tana kallon d'iyar tata yanda farin ciki ya mamayeta kafin tace" Oh Azee bansan wani irin so kike wa Irfan ba... "Azee ta murmusa kafin tace" Wllhi momy ina masa son da bana maki yanzu dai I should get rid of that so called nanny din dan ita taimin cikass....." Laila kam dae baki sake take kallon Azee cikeda mamaki( _Wai tafi son shi akan uwar data haifeta... what a mess π_)...
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
β
*"Two weeks later*
"Zaune suke a Cafeteria suna cin snacks fitowarsu kenan daga Enxamz yau sukayi last paper gaba d'aya jinsu suke cikin farin ciki dan kuwa zasu samu hutun zangon karatu na farko wato first semester.
"Nadiya sai faman nunawa Deejah pics din brides take wai ta zab'i shigar da zatayi a bridal shower dinta.... "Azee kam gaba d'aya ji take tamkar zuciyarta zai tarwatse dan tsananin tashin hankali, gaba d'aya k'arfin hali take tana dannewa musamman da yanzu aka tsaida maganar auren Irfan da Deejah.
"Shigowan su Mus'ab Turaki course mates dinsu cikin Caf din ne ya katse masu hiran da suke... Take Deejah ta had'e rai dan kuwa ko kad'an bata son yanda su Mus'ab dasu Nadiya ke shaking hannaye tamkar ba yaran musulmai ba, ko tai masu magana cemata suke ai sch life ne so let's be social, gwarama Nadiya zata iya cewa tashin Turai ne har yanzu a jikinta amma Azee kam zunzurutun son wasa da maza ne kawai snn itake dad'a influencing Nadee. Dan haka nema ko kadan Deejah bata sake masu Mus'ab.
"Table din gefe suka k'arasa suka zaune, Mus'ab ya d'an tab'a k'afar Sudais gamida kashe masa ido d'aya alamun kar ya spoiling masa mission dinsa.
"Murmushi Sudais yayi kafin ya d'aga masa gira d'aya ya mik'e ya nufi table d'in su Deejah.
"Guys you're all invited to the farewell party of MUS'AB TURAKI (VICE PRESIDENT SON) As you all know that he's living the country tomorrow.
"Cikeda masifa Deejah tace" and who cares, kaga mun maka kama da masu zuwa party ne..." da sauri Azee ta katse ta da fad'in " Aaa haba Deejah zamuje mana, miye a ciki dan zamu partyn ban kwana da d'an ajinmu.
"Murmushi Sudais yayi kafin yace" Your presence is very important must especially you Arab girl.... yayi nuni da Nadiya da tun tsayuwarsa take faman danna wayarta. Sai snn Nadiya ta d'ago tana dubansa. Nuni tayi zuwa k'irjinta da phon dinta tace "Mee!! Surprisingly!
"Sudais ya gyad'a kansa kafin yace" yeah the vice president son have a surprise for you, anyway idan kun gama deciding ku samemu wajen cars dinmu sai kuji venue din. Daga haka Sudais ya juya ya wuce wajen zamansu..
"Deejah ta gallawa Azee harara tace" haba Azee meyasa kika biyesa ya maidamu 'yan iska ne masu zuwa party.... " kai Deejah meye iskanci a ciki dan munje farewell party din Mus'ab, kina gani mu kadai suke kulawa dukda ji da kai da 'yan click dinsu sukeda.... "Ringing din da wayar Deejah tayi ne yasata tashi ta nufi restroom ganin Sahibinta ne me kiranta,...
"Haka Azee tayita zuga Nadiya wai she's special tunda har Mus'ab na shirin bata surprise duk fadin Nile, nan kuwa Nadiya ta biyeta tana jin yes kenan duk tafi sauran 'yan matan sch din haduwa, mikewa sukayi suka nufi yanda Su Mus'ab suka pake Luxurious Cars dinsu.
"Suna isa wayan Azee dake cikin jaka ya soma ringing tana ganin Ahidjo ne tace wa Nadiya bari taje amsa wayan Hajiya, hajiya ke kiranta, nan Ahidjo ya sanar da ita su had'u a guest house dinsa urgent.
"Sudais ne ya bud'e wa Nadiya bayan Range Rover din Mus'ab take ta soma jin jiri bata san yaya akayi ba sai shigewa cikin motan da tayi...
"Sadiq da shigowarsa Nile kenan ya hangi wata kaman Nadiya ta shige bayan range rover da wasu maza take yaji k'irjinsa na dukan uku uku, sauri sauri ya ajiye Mamie wajen aikinta wato Cafeteria ya juya da kan motarsa nan ya tarar motan da Nadiya ta shige na k'ok'arin ficewa daga Nile, take ya soma binsu a baya cikin sauri dan kar su b'ace masa.
"Deejah tana dawowa Caf ta tarar babu su Nadiya, layinsu ta soma kira amma bai shiga, na Azee nema ya shiga sau d'aya ba'a d'aga nan tayi tunanin ko Department suka koma dan dama sunyi missing examz guda d'aya, tayi tunani ko sun koma yin complain ne. Ganin Mamie na shigowa da kaya yasata saurin k'arasawa ta amshi wasu kayan suka soma gaisawa.
"Yana shigowa cikin Nigerian Turkish Nile University ya shiga neman layinta, tana d'agawa yace gashi ya iso tana ta ina ne, nan ta sanar dashi tana Caf.
"Kai tsaye Irfan ya wuce Cafeteria, yana gama parking ya fito ya nufi cikin Caf din,
" Daga yanda take zaune ta hangosa... "Sanye yake cikin k'anan kaya Royak blue shirt wanda ya k'ara fito da hasken fatarsa yana sanye da wando ash chinos, gashin kan nan nasa sai shek'i yake as usual, idanunsa sanye cikin bak'in sunshade, yana hangota ya sakar mata murmushi nan itama ta maida masa martani, ganin yamda emmata kai harma da samarukan da suke zaune a caf din sun k'urawa Irfan ido wasu na faman fad'in "Woow handsome" yasa Deejah jin kishi sosai har
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 40