Share this page
ta kawo cat gidan, "Wayansa ya dauka ya shiga neman layin Nadiya, duk sunyi tsuru tsuru sun b'oye kenwan 'krkashin drawer, take Nadiya ta shiga nunawa Deejah screen din wayan," my goodness ya Irfan is calling, me zance masa, am sure allergy dinsa ya tashi, Deejah tace" a'a kai haba dai, ni ban taba jin wai dan kenwa na waje ba sai mutum yayi ciwo, kodayake bn sani ba, amma ki dauka ta yuyu wan7 abin zai tambayeki tinda ma ga kenwar a nan. " 'Kirjin Nadiya na dukan tara tara ta d'aga wayan da k'yar,..... "Tun kafin tayi magana a hsale yace mata" To my Closet right now" dag hak ya katse kiran. "Cikin 'dakinsa ta samesa a Closet dinsa wanda yake tamkar na wani celebrity, komai is arranged in an orderly manner, wajen suite daban, wajen shirts daban wajen neck ties daban, wajen jeans daban, wajen jampas daban, idan ka dawo tsakiyan closet din wanda yake glass ne zalla wajen , wristwatches da links ne jere a wajen ko wanne ya amsa sunan sa, daga can gefe kuwa takalma ne a jere gwanin ban sh'awa.... "A rakub'e Nadiya ta tsaya tana wulli wulli da idanu, take jikinta ya sona b'ari dan tsoro ganin yanda jikin Irfan ya turning to red, Fuska a tamke ya soma fad'in, " Who the heck brought cat into this house, Sa basa amsa tayi sai zare ido takeyi, " tsaki yayi gamida d'aga murya yace" am I not talking to a being, huh?, nace waye ya kawo cat gidan nan, despite the fact that am allergic to it," Dama dama wlhi ni ban sani ba yaya. "Jawo hanunta Irfan yayi suka fice zuwa sashensu, ta window Aziza ta hangosu a sittin ta fito itama ta biyo bayansu. "Duk sunyi tsuru tsuru a parlor, Irfan ya ci gaba da fa'din now can someone tell me who the heck brought cat into this very house? "Yakai dubansa gasu Amir da Aiman, daga gani ksan basu da gaskiya, Irfan ya hade gira sama kafin yace " yaya bamu bane, Nilam ta matso kusa da Deeejah, s hankali take kiran sunanta, Deeja ta dan sunkuyo tace yes precious, Nilam tace, yamzu ya Irfan zai buge ni idansu Aiman suka ce pussy cat dina ne. Girgiza kai Deejah tayi "no bazai nai komai ba....." Suna ta magana wa juna a hankali, basu san idon kowa na kansu ba harda Irfan da ya murtuk'e fuska, "Mastowa Irfan yayi kusa dasu kafin yace" ku gama whispering dinku and tell me the exact truth. "Girgizq kai Nilam ta soma, Irfan ya tsareta da ido kafin yace" Angel were you the one, ..... Kan tayi magana Deejah tayi caraf tace" ni ce, ni kawo kenwar.. " Kallonta kwai Irfan keyi babu ko kyafta ido. Aziza dake tsaye gefe kaman ta mutu dan haushi, she couldn't have a single chance to talk to Irfan, ga wann banzan so called Nanny din sai shishige masa takeyi. "Kallonsu kwai su Nadiya keyi, yanda suka b'ace da kallon juna, shi na mata kallon I can't disgrace you here in front of my siblings, cos I do luv you now. "Ita kuwa Deejah kallon" tausaya masa take yanda jikinsa yayi jazur, inama ciwon ya dawo jikinta, Oh master you be adjeboter, even cat irritates you..... Ihun da Aziza ta saa ne ya dawo dasu daga duniyan da suka lula.... A guj tayi bayan Irfan ta shiga ri'ke rigarsa sakamakon ganin kenwan datayi tana saukowa daga stirs. "Cike da tikaici Irfan ke binta da kallon mamaki, " He's like toh itakuma wnn wacece, tsaki yayi gamida daka mata tsawa, wani kallon da ya watsa mata yasata nustuwa babu shiri. Nadiya me zatayi banda dariya, Deejah kuwa kishin Aziza ne taji ya dirar mata. "Nan Irfan ya soma attishawa sosai, hannun Deejah ya jawo suka fice daga prlon... Aziza t bisu da kallo har suka fice, Nadiya ta watsa mata hrara gamida jan guntun tsaki tace" Don't deceive your self, coz yaya Irfan will never set his eyes on you, daga haka tayi hayewanta sama. Sosai abin ya ta'ba zuciyan Azee tabi Nadiya da kallo kawai hr ta b'ace mata.... "Irfan kuwa suna fita sashensa suka wuce, basu tsaya ko inaba sai naken bedroom dinsa, hanunta ta fincike daga ri'kon da ya mata, tana masa mugun kallo tace" let go of my hand,... "harara ya watsa mata kafin yace" don't think otherwise, closet dinsa ya nuna mata kafin yace" clear that mess, "Yatsina fuska tayi hfin tace mefah, ba tare da ya klleta ba yace" ki shiga mana zaki gani, daga haka ya fada toilet dan yin wanka. "Dariya sosai Deejah tayi ganin yanda kenwan nan t tulawa Irfan kashi a closet dinsa, closet din da ya amsa sunansa closet. Tsaf ta wanke wajen ta gyara, tana fitowa 'kasa ta nufo da niyyan fita amma me gimm taji kofan alamun rufe, ta duba key babu a jikin kofan, ta'be baki ta danyi ta shiga zagaye parlorn dan sosai parlorn ke mata kyau, wani dan kofa ta hango daga can gefe ta nufi wajen ko zata sami exit, kallon wajen ta tsaya yi wani 'karamin parlor ne an cikasa da Design Works, ga penti iri iri colours daban daban sosai wajen ya mata kyau, ga hoton wata mata wacce daga gani balarabiya ce an zana yayi kyau anyi k'aton enlargement, dan ksan hoton an rubuta" LOVE" da manyan harrufa, 'kirjinta ne ya shiga dukan tara tara, a fili take furta " kai noway, this can't be, ashe dama yanda budurwansa, mtsww ko kyauma batayi ba, farin fatane kawai, harda wani rubuta Luv.... ta kuma jan tsuka a karo na biyu....." juyowan da zatayi sukayi ido hu'du da Irfan yana sanye cikin english wears as usual, tamke fusja yayi yana kallonta, ya shiga matsowa kusa da ita, take Dejah ta soma matsawa da baya tana fa'din" dan Allah master kayi hakuri, wllhi ban zage budurwanka ba, ..... bai daina matsowan ba bai kuma ce komai ba, hr saida Deejah ta mannu da hoton, kirjinta na bugawa da sauri da sauri, ta shiga juya ido tana addu'an Allah sa kar yace sai ya mata kiss..... "runtse ido tayi tana jiran ta Allah ya sameta... " Wani sautin dariya me da'di taji yaba tashi, a sittin ta bu'de idonta ta sauke su tsaf kan Irfan, yanda yake dariya hankali kwance, a ranta tace kai dama master na dariya haka... Shikuwa Irfan dama abinda yake son gani kenan, idan taji tsoro abin na burgesa shiyasa sa dariya. "Take kuma ya gimtse yasha mur sosai kafin yace" ki juya kiyi apologizing ma pic din nan idan baki son nayi stealing a kiss from you, "Ta hade rai a zuciya take fa'din" tabb I should apologies to the pic, tsaban son budurwansa da yakeyi..... " Zakiyi yanda nace kokuwa ya soma matsowa..... A tamanin Deejah ta juya harda ha'de hannaye alamun ban ha'kuri tana duban pic din..... mamaki ne ya isheta ganin pic din ya canu hr yanzu mace daya ne, saidai wnn karan ta 'dan data fiye da hoton farkon wanda 'kuruciya ya nuna a fuskanta, wnn karan 'kasan hoton an rubuta" You were my Inspiration, I luv you Mum. "Da sauri ta juyo taba duban Irfan, sai kuma ta sunkuyar da kanta k'asa dan kuwa sosai ta samu kanta da jin kunya. Jiki a sanyaye ta soma fa'din" dan Allah kayi hakuri, I didn't know she was your mum.... am so sorry... "Murmushi Irfan ya sakar mata kafin yace" nasan baki sani ba, is ok ya wuce,. "Amma meyasa kikaji haushi lokacin da kikayi zaton budurwata ce.... " Dariyan ya'ke ta soma cikin zuciyanta kuwa cewa take, wane ni da kai Irfan, we are not from the same level nida kai...." am asking you, muryan Irfan ya kayse mata tunani, "Da sauri ta shiga girgiza kai duk ta wani daburce ta soma fa'din" ni kuma haushi no no, ba haa bane emmm emm..... "Murmushi Irfan ya danyi kafin ya karasa shigowa cikin prlorn.... πŸ‘ΈπŸ» Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹ .......... πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ—πŸŒ— *Mallkin Waye* 33 *Shout out to all readers of Mallakin Waye... ILYSM* "Ganin irin kallon da Irfan ke mata yasata sauke nata idon, murmushi yake wanda ke k'unshe da ma'anoni, har gabanta ya tako sann ya tsaya yayinda k'irjin Deejah keta faman lugude, cikin muryan da bata tab'a ji daga gareshi ba taji yana fad'in" Deeejah there is something I wanna discuss with you, d'ago ido Deejah tayi tana dubansa jin sigan da ya mata magana dashi, murmushi ta gani kwance saman kyakyawan fuskan Irfan.... gani tayi sakare tana kallonsa yasa sa yin 'dan gyaran murya kafin ya karasa kan Couch ya zauna, take taji kunya ya mamayeta dan Irfan yaga irin kallon da take masa, Couch din dake gefen wanda ya zauna yayi mata nuni dashi kana yace" Please seat down, kasa masa musu tayi ta sami kanta da bin umarninsa. "K'irjin Deejah yaci gaba da lugude tana jira taji wani irin magana yau Master yakeso suyi.... "Shima a b'angaren Irfan d'in kasa cewa komai yayi, dan kuwa he just couldn't believe it wai shi Irfan yau ke soyayya kuma soyayyan ma da er Nigeria low class maid servant kaman Deejah, ya nemi kalma guda dazai soma mata dashi ya rasa, kallonta yayi sanda take kan wasa da en yatsun hannunta, tuno moments din da suka kacen tare yake lokacin da aka rubbering dinsu, a hankali ya sauk'e wata sassanyar murmushi....gyaran muryan da zaiyi wayarsa ta soma ringing wanda bashi ba harda Deejah saida ta d'an firgita, " Kallonta yayi kafin ya d'an daga mata yatsa guda yana me duban screen din yace" sorry let me receive this call pls. "Gyada masa kai tayi tana mai murmushin jin dad'i cikin ranta, farincikin da batasan dalilinsa ba ya mamaye mata ruhi..... muryansa tajiyo yana receiving call din. "What haba dai Ahidjo, do you really realize what kind of trouble you got your self into, you shouldn't have done that guy, nan fah ba America bane,..... "Daga daya b'angaren Ahidjo yace" So what Irfan, are you also blaming me, in the first place I didn't force her tayi gasan shan drug dani,....." Mikewa Irfan yayi ya dan fice daga wajen dan bayaso Deejah ta gane me suke cewa da Ahidjo, kafin yaci gaba da fadin" Ahidjo wai har yaushe zaka daina shan drugs for goodness sake, I thought ka jima da dainawa tun a America, yanzu gashi kaje kasa 'yar mutane tasha abunda yafi karfinta, what if she died me zaka ce wa iyayenta. "Ahidjo ya share zufan data zubo masa kafin yace" guy pls ka taimaka kazo ka dauke nasan yanda zanyi da yarinyar nan, I don't know what to do, pls kazo kafin corps su iso, kasan dad dina zaiyi contesting senator up coming election idan yaji abunda nayi he'll be definitely mad at me, Irfan do something pls. "Gajeren tsaki Irfan yayi kafin yace" just text your location daga haka yayi hanging up ya bar Ahidjo nata faman godiya... "Tsaye ya sami Deejah sai faman kallon Awards dinsa tun na sch da kuma na wasu ayyukan da yayi take, hadi da pics dinsu na sch da na family, komai na Irfan gwanin sha'awa ne, komai ya burgeta. Kallonta yake baison rabuwa da ita kona second ne,... jikinta ne ya bata ana kallonta juyowan da zatayi sukayi ido hudu, tayi saurin ajiye pic dinsa data dauka yana sanye cikin graduation gown hannunsa rike da kyaututtukan da ya samu. Baki na b'ari ta soma fadin sorrrry Master I shouldn't have touched your stuffs. "Murmushi Irfan yayi dan kuwa idan taji tsoro tafi masa kyau, kina son pic din ne, ya tambaya yana saka wayansa a aljihu, murmushi kawai tayi ba tareda tace komai ba, dan kuwa Irfan ya tsareta da idanuwansa masu sata fad'uwan gaba. "Dan murmushi yayi ya girgiza kansa kafin yace" am sorry ban samu munyi maganan ba, abokina ya kirani he needs my assistant, we should talk next time kinji... "Gyada masa kai tayi har zata fice sai kuma tace" toh abinci fah gani nayi yanzu ka dawo, girgiza mata kai yayi kafin yace am Ok karki damu, kawai abinda nake so tjat cat ta bar gidan nan pls kinji. "Gyada kai tayi tana me dubansa.... Sauri sauri ya haye samansa ya dauko car keys dinsa, ga mamakinsa Deejah na nan tsaye a parlornsa bata fice ba, Far da ido ya mata kafin yace ya dai, "Wani kunya ne ya kamata, shikenan Irfan zaice ta kasa fita masa daga sashe tsaban tana son ganinsa, da sauri dabara ya fado mata tace.... dama dama naga bakada lafiya ne so I was thinking ko zaka iya driving a haka. "Murmushi ya danyi kafin ya dubi jikinsa yaga jan ya dan ragu kana yace" ai nasha magani, I'll be fine in some hours, haka yake mun normally idan na zauna waje daya da cat. That's why I don't like cats. Orbit chewing gum ya dauka saman center table dinsa ya balli daya ya jefa a baki ya mike ma Deejah ma snn yace have some, girgiza kai tayi alamun a'a.... tsareta da ido yayi kafin yace" see you banson kauyamnci oya karbi kici, bata kuma masa musu ba ta karba ta saka a bakinta. Daidai nan text ya shigo wayarsa Ahidjo ne ya turo masa location din da yake, kallon Deejah yayi ya dan rage murya yana mata wani murmushi hadi da kashe ido kafin yace" Pls acompany me miss Deejah.... Baki sake Deejah ke kallon wnn sabon lamari da Irfan ya bullo dashi, zatayi magana yace "I say please. Itakam bata iya masa musu... ganin tayi shiru yasa Irfan yin wani murmushi kafin yace" Ladies first, murmushi Deejah ma ta danyi kafin ta fice zuwa waje. Irfan na biye da ita suka nufi parking lot, "Shi Irfan gaba 'daya ya mance da wani hali Ahidjo ke ciki yasa ya dauko Deejah tareda shi giyan soyayya ya dibesa, itama a b'angaren Deejah ko kadan ta mance bata fad'awa kowa a gidan ba ta biyo Irfan itama dai giyar soyayyar ce ta dibeta, saida sukayi nisa bisa titi "abinda ya faru dasu kwanakin baya ya fado mata, the same Ahidjo ne yayi waya yana neman taimakon Irfan..... "Kirjinta ya shiga dukan tarara kar fa a maimaita abinda ya faru.... πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„ [8/28, 13:54] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye* 34 "Can 'kasa da club din Irfan yayi parking, ya dan juyo ya kalli Deejah kafin yace ki jirani a nan ina zuwa idan na fita ki danna security lock dan gaskiya am not comfortable with the people around this place. "Har ya saka k'afa zai fice sai kuma ya juyo yana kallonta ita din shi take kallo, marfin motan gefenta ya d'an rank'wafo zai bude mata jikinsu ya d'an goga na juna, Deejah kam k'irjinta ne ya shiga dukan uku uku dama tunda suka baro gida k'irjinta ke fad'uwa ga wann shock da ya sameta, shi kuwa Irfan kasa komai yayi dan kuwa sosai yaji a jikinsa, da sauri ya bud'e marfin motan murya can k'asa yace" am sorry, sa k'fq tayi ta fice daga motan shima ya fito, ganin yanayin mutanen dake kewaye da wajen yasa Irfan saurin rik'o hannun Deejah suka nufi club din.... "A zuciyanta take fad'in na shiga uku me Irfan zaiyi a club, k'irjinta yaci gaba da lugude.... "Duhu ne ya gauraye cikin club din sai irin party light dinnan bakajin komai sai k'aran music da turnik'in hayak'i da warin kayan maye..... "Duk k'warewan Deejah a zuwa Club bata ta'ba zuwa irin wnn ba, abin ya bata tsoro ganin 'yan mata dangin tsirara..... "Sosai Irfan ya k'an'kame hannunta kaman me tsoron kar a kwaceta, sai faman toshe hanci suke sabida hayak'i da warin kayan maye. Dube duben ta ina zasu hango Ahidjo suka soma, daga bayansu Deejah taji wani na janye hannunta, wani k'ara ta sake gamida k'ank'ame hannun Irfan, ai kuwa juyowan da zaiyi ya kai ma mutumin wata naushi a fuska... Nan hayaniya ya kacame dan kuwa yaron yayi niyyan ramawa Irfan yayi masa lilis. Abin da ya jawo hankalin Ahidji kenan har ya gane Irfan ya iso, daga dan cikin wani daki yanda ya ajiye budurwan ya fito yana fa'din " Irfan gani nan ta nan..... "wani tsaki Irfan yaja yana watsa wa Ahidjo mugun kallo, shi besaba zuwa places like nan wajen ba, shidai yana social life amma ko kad'an baya watsewa da mata da shaye shaye. "Ahidjo kam tuni ya makare a kallon Deejah ko yaushe ya ganta jin k'ara sonta yake, wutan sonta na da'da ruruwa a zuciyarsa, ita kuwa Deejah gaba daya taji ta wasa Ahidjo, ko kallonsa bata sonyi... bata gama jin shock ba saida suka shiga d'akin Yusrah ta gani kwance, Ahidjo ya gama watsewarsa da ita, daga ita sai d'an wata k'aramar riga wanda take tamkar shimi, ga kumfa nata faman fita ta bakinta alamun ta sha abinda yafi k'arfinta. Take jikin Deejah ya soma b'ari dan kuwa bata san zuwa club din Yusra har yakai haka ba, hawayene ya soma zuba a idonta yaushe Yusra ta fara zuwa Dirty club irin wnn, yaushe ta wulakanta rayuwarta haka, Deejah bata ta'ba nadaman zuwa cluns din da tayu a baya ba irin ta yau. "Guy temaka mun mu kaita motarka, cewan Ahidjo dake faman tangad'i...... "Idanuwan Irfan sun kad'a sunyi jajazur, fatansa fuskansa ma haka tayi jazur sabida b'acin rai, bai k'ara jin ya wasa Nude life ba irin ta yau, ji yake ya wasa mace me zuwa club komin yaya ne, ya wasa watsestiyar rayuwa irinta Ahidjo....., "pls mana Irfan Ahidjo ya sake fad'i. "Cikin zafin rai Irfan yake fad'in" You must be idiot, wnn karuwar ce kake cewa a sakata motata, Allah ya sauke mun karuwa me yawon club ta shigar min mota, wnn ai ta shiga motata a sai an mata wankan tsarki, Ahidjo bansan abin naka yakai haka ba, haba haba you are human meyasa zaka maida kanaka as if you're Animal. This is pure madness Ahidjo, wllhi da nasan zinan ka kazo kayi a nan da banzo ba, da ban dauko *matar da nake son aura nazo da ita nan ba*..." Take Deejah ta dago ido tana duban Irfan, _Matar da nake son aura_ ta maimaita a ranta. Shima Ahidjo shock ne ya ziyarce sa kenan Irfan son Deejah yake kenan bazai sameta ba, kai ina wllhi bazata saku ba, dole yasan abinyi... "Irfan ya juyo yana duban Deejah hawaye ya gani kwance kan kumatunta, a hankali ya saka d'an yatsar sa ya shiga share mata, murya can k'asa ya furta "am sorry pls, I didn't want you to get involved, muje na maidaki gida. Daga haka Irfan ya soma tafiya,,,, Deejah tayi karfin halin cewa "Master" juyowa yayi yana dubanta, a hankali ta furta" pls let get them out of this place, you can't leave them here, kar ka fasa kudirinka na khairi... "Cikin daka tsawa yace" I said ki wuce mu bar nan wajen bakiyi kama da wacce za'a gani ta fito daga nan ba. "Jiki a sanyaye ta karaso gabansa" cikin muryan sanyi tace" sunyi kuskure, but think of the girl pls, we can't leave her here..... nasanka da zuciya mai tausayi musamman mace, dan Allah let's get them out of this place. "Hararan Ahidjo kawai yake" kafin yace" am doing this for Deejah, sabida ita zanyi wnn, oya ka dauko wancan Trash din kazo mu tafi... ya karashe maganar yana nuna masa Yussy. "Deejah kuwa hawayene kawai ke bin fuskanta cike da tausayin aminiyarta Yusra, da kyar da tangadi Ahidjo ya jawo Yusra a kasa da sauri Deejah ta k'arasa ta rik'e masa gefen Yusra d'aya. Cikin sa'a suna barin wajen kuwa securities sukazo kame...... "Driving kawai yake amma kana ganinsa kasan ba daidai yake ba, yanzu ina zamu ajiyesu da kikace mu dauko su Irfan ya tambayi Deejah dake zaune gefensa mazaunin me zaman banza, dan su Ahidjo iam a back seat suke shida Yusra dukansu sunyi baccci ko muce sun sume...... " Tambayanki nake, kinsan dai muna zuwa gida a haka we're in trouble, Daddy and Ammah, sann gidansu Ahidjo mum dinsa bazata kula da wnn yrinyar ba, mukaje asibiti kuma it will become another issue su Ammah can even find out... Gwarama Ahidjo zamu iya ajiyesa gidansu, but wnn yarinyar da kika sa muka daukota ina zamu kaita. "Deejah ta sauke ajiyan zuciya kafin tace" I don't know master, gani nayi be kamata mu barta a wajen ba, tunaninta daya kar Irfan yasan da tana zuwa club tasan zai tsaneta har abada..... " wani tunani ne ya fado mata tace" yauwa mu kaita gidan Mamie. ?. "Mamie ya nanat.... shiru ya danyi ba tareda yace komai ba...... *Manage this Habibties babu yawa, if am less busy zakujini later... luv you all😘* πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„ [8/28, 13:54] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye* 35 "Banda kuka babu abinda Azee keyi, itakam she can't loose Irfan tanaji tana gani, Laila tayi rarrashin duniya amma Aziza ta kasa barin kukan da take, dagi kai tayi tana duban Laila ido sharkaf da hawaye ta soma fadin" Momy yaya kike so nayi, yaya kikeso nayi da tsananin son Irfan da nakeyi wanda besan inayi ba, can't you see it momy, he already fell for that witch, that common so called Nanny. Haba haba wllhimidan bakiyi komai a kinji na rantse barin gidan nan zanyi kuma naje na kshe kaina dan wlhi rasa Irfan na daida da rasa rayuwata ne..." Laila ta kafe Aiziza kawai tana dubanta totally speechless, bata zaci son Irfan Azee keyi har yakai haka ba, zama tayi daf da ita gamida dafa bayanta ta shiga lallashinta, sorry my baby, Azee you am doing all my best, du du yaushe kikazo gidan nan da har zaki daga hankalinki, ki dubi kanki farace ke tas gaki kyakyawa son ko wani namiji, kinfi that common rat dinan kyau nesa ba kusa ba, ninasan Irfan ba sonta yake ba, kila dai yana neman abinda zai samune ya kyaleta, dan so nawa 'ya'yan masu gida suke bin masu aiki, bada aure suke sonsu ba, kinsan samaruka yau duk yanda mace take toh fah idonsu na kanta ko yaya take, bacin haka me Irfan zaiyi da wnn yarinyar, banda ido babu komai a fuskanta, karki damu gobe goben nan zan daukeku keda Nadiya na kaiku shopping nasan daga haka Nadiya zata soma sakin jiki damu, sai na pamper ki ta yanda Irfan yana ganini zaiji baison kowa saike, maza tashi ki share wnn hawayen. "Aziza ta miketana ture turen baki dan itakam

Chapter 12 of 40