Share this page
for any girl......." shiru na d'an sakwanni sai bugun zuciyoyi kawai wanda harda Aziza dake lab'e bayan window wacce da kyar idan k'afanta zai iya d'aukanta.... "Irfan yaci gaba da fad'in" Deeee na jima ina avoiding dinki ina k'aryata abunda nake ji gameda ke, but I just couldn't help it anymore, I must admit it. Deeejah I fell for you from the very time I saw you. I love you Deejah with all of my heart, and am ready to give you the care and love a lady desires most. Tell me Deee do you feel the same for me????? "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un...."kaman a mafarki haka Aziza ke kallon wnn al'amari, dama mafarki ne dayafiye mata sauk'i, shikenan itakam ta shiga uku ta mutu ta lalace, da kyar da jan k'afa ta wuce d'akinta ta shia tattara kayanta tana zubawa a akwati........ "Deejah kuwa kasa motsa koda d'an yatsan tayi sabida wani irin shocked da bata tab'a experiencing ba. Take tunanin nasihan da Anty Larai ta mata kan ta fara aiki gidan Engr ya fad'o mata..... _" Ki kula sosai da kanki, musamman idan gidane me samaruka, so tari yaran masu kud'in nan sukan d'auki ma'aikata a matsayin 'yan iska, idan sunga ba layinki bane su b'ullo maki ta hanyar soyayya su yaudareki da kalmomi su samu abinda zasu samu daga gareki daga baya kiji ana zai auri 'yar gidan wane abokin mahaifinsa, ki tsaya a yanda aka umarceki. Ita rayuwa daidai ruwane daidai gari_....... Da sauri ta fizge hannunta daga rik'on da irfan yayi mata, ta soma girgiza kai kwalla na shirin ciko idanunta take fad'in." Bana sonka..... bana sonka master, aiki nazoyi gidan nan dan Allah kayi hak'uri dan ina ganin girmanka........ daga haka tasa kai ta wuce hawayen dabata so su zubo suka shiga zarya a fuskanta......" Kallo Irfan yabita dashi har ta haye sama...... πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„.......... [8/28, 13:56] Umar Dalha: πŸŒ—πŸŒ—πŸŒ˜πŸŒ˜ *Mallakin Waye* 38 *I Sincerely dedicated this Spectacular Chapter to All my Adorable Fans around the Universe........ 😍😘 #Allah bar Zumunci#πŸ’—* "Kasa motsawa Irfan yayi sabida wani irin shock da ya ziyarci illahirin jikinsa, haka yabiya da kallo har ta b'ace masa, gaba d'aya ya kasa gasgata abinda ya faru abinda kunnuwansa da idaniyansa suka gane masa " Wai shi Irfan har akwai yarinyar da zata kalli tsaban idonsa tace bata sonsa, in the first place meyasa ya fara yarda da wnn ridiculous thing so called love din,..... "Dafe kansa daya masa nauyi yayi yana so ya daina tuno kalman "Bana sonka da Deejah ta fad'i masa amma ya kasa, kalman sai yawi take masa a kunnuwansa da kwanyansa. Why all this, meyasa na yarda da zancen Sadiq cewa Deejah sona take, Oh my Goodness yarinyar nan shikenan ta rainani.... jifa da remote yayi yana firta " Shitt dammnn everything!!!.... Jiki a mace ya mik'e ya nufi sashensa... "Deejah kuwa tana fad'awa d'aki kwanciya tayi ta soma kuka da gaske, banda son Irfan dake azalzalanta babu abunda take ji musamman da ya furta mata kalman so a yanzu, anya tayi daidai ma kanta, anya bata tafka babban kuskure ba, meyasa tak'i amince ma buk'atan Irfan.... take ta soma furta innalillahi wa inna'ilaihirraji'un.... da taimakon Allah ta sami sauk'i cikin zuciyanta, wata zuciyan twce" Abinda kikayi kinyi daidai dan kuwa Irfan ba daidai ke bane, take maganganun Nadiya suoa dawo mata _Ke da ya Irfan kuna son junanku_ toh ko da gaske Irfan sonta yake, take wata b'angare na zuciyanta tace" yanzu ne zaki gane idan yana sonki, he'll surely comeback to you,..... A hankali ta kwanta gamida runtse ido dan kuwa ko kad'an bata jin baccin mai zuwa ne....... "A b'angaren Azee kuwa sosai take kuka take had'a kayan cikin akwati itakam bazata iya tsayuwa bak'in ciki ya kasheta a nan ba, gwara ta koma gidan Hajiya kawai abin zaifi mata sauk'i....... "Da wnn tunani ta kwanta ta ci gaba da aikin kuka..... "Cikin wnn dare ma iya cewa mutane ukun nan basu runtsa ba, Irfan Deejah da kuma Aziza......! "Washe gari sassafe Laila ta tarar Azee tayi waya wa Safwan yazo ya d'auketa, sosai Laila ke lallashinta da ky'ar da yarda ta amimce bazata tafi ba, Safwan na isowa saida yasha tambayoyi wajen securities snn sukayi waya da Laila ta sanar dasu ko da yaushe yazo a bude masa gate uncle din 'yarta ne.... "A parlor Safwan ya sami Laila sai bin gidan da kallo yake, ya d'aga gira sama yana fad'in "Mansion Indeed" Laila zatayi magana yayi saurin cafko ta ya shiga kissing dinta yana juyata..... "Da kyar ta kwaci kanta hanun Safwan kafin ta soma fad'in "Lafiyanka Safwan kanka d'aya, cikin gidan Engr fa muke snn Aziza na gidan nan fah someone might see us ai. "Murmushi Safwan yayi yana shafa hab'a kafin yace" rabona dake tun yaushe kinsan nayi ko'kari.... ya kuma mastowa yana k'kok'aro cafkota.... matsawa baya tayi kana tace" kaga mijina na gida be tafi office ba, yanzu haka ma yana gab da fitowa dan ya gama shiryawa, dan Allah ka saita kanka. "Safwan yayi Murmushi kafin yace" toh me miji naji yanzu rubuta check din ki bani tunda Azee baby ta fasa tafiya. " A gurguje Laila ta zaro check din 200,000 ta b'alle ta mik'a masa.... daidai nan Engr ya shigo parlorn da sallama. "Take suka sha jinin jikinsu.... Safwan yayi saurin rusunawa yana gaida Engr......" haka kawai Engr yaji Safwan be kwanta masa ba... "Laila tayi saurin fad'in har ka fito..... "Karasawa ciki yayi be amsata ba saida ya shige cikin d'akinta, nan itama ta biyo bayansa, kallonta Engr yake kafin yace" Wanene wancan kuma a parlor.... "Take Laila ta soma had'o kalmomi tana fad'in" Dama k'anin baban Aziza ce, toh kasan na fada maka batada lafiya shine yazo dubata. "Engr yayi shiru kaman bazaice komai ba sai kuma yace" Next time idan yazo ya tsaya a parlorn bak'i dan bana so Maza suna shigewa kan iyalina kin gane...... "Da sauri ta gyada kai ta soma gyara masa links dinsa gamida kissing dinsa tana wani manne masa, a hankali Engr ya d'agata daga jikinsa kafin yace" na makara ina sauri, yaya jikin Azizan... sai ku shirya driver ya kaita asibiti. Laila ta dan marairaice fuska twce wai da ni zanyi driving. Girgiza kai Engr yayi kafin yace" how many times do I have to tell you, bana so kina driving, driver ya kaiku period.... daga haka yasakai ya fito dan ransa ya gama b'aci sakamakon ganin Safwan da yayi a parlorn matarsa danma dai k'anin baban Aziza ne da yau ya gane kurensa. Ta biyoshi har waje tana masa sallama daidai lokacin da escort dinsa ke bude masa marfin mota, juyowa yayi kana yace" yaron can ya dawo parlorn bak'i su gana da 'yar shi kinjini da kyau... gyada kanya tai tana mamakin dama haka Engr yakeda kishi... "Tana dawowa Safwan ya tsareta da ido yanda duk ta birkice, dariya yayi kafin ywce" wnn tsoho naki akwai kishi,... zama tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin tace "Safwan bana son duk wani abin da zai kawo mishkila tsakanin aurena da Engr...... sai faman magana take bata ankara ba sai ganin Safwan tay7 yana rage belt d'in jikinsa.... mikewa tayi tana fadin "a a meye haka kuma Safwan.... "Bai tsaya saurarenta ba ya janyota jikinsa ya shiga sarrafa sassan jikinta..... Laila tayi missing Safwan dan kuwa Safwan gwanine wajen Sarrafa mace... dole ta biye masa sukw fada dakinta suka aikata masha'ansu..... "Har Safwan ya bar gidan Aziza batasan yazo ba....! "Yau Deejaj kowa ya ganta yasan ba daidai take ba, gashi Irfan ya fice office bata gansa ba, bata tsammanin ya shigo yayi breakfast dui saita tsinci kanta da rashin jin da'din haka, ta sami kanta tana me d'aura laifin rashin karyawanshi ma kanta. Haka ta wuni sukuki, harta su Ammah da Hajja saida abin ya damesu, juyin duniya tq fad'i meke damunta tak'i fad'i.... "Shima a b'angaren Irfan kasa tab'uka komai yayi a office, duk yanda yayi ya cire tunanin Deejah a ransa abu ya faskara, shin wann wata irin yarinyace, gaba daya regretting dawowansa Nigeria yake..... yana zaune yana aikin tunani Sadiq ya shigo da sallama, ko kadan Irfan beji shigowar Sadiq ba har saida ya zauna. "Kallo d'aya Irfan ya masa ya watsar, Sadiq ya masa k'uri yana son gano wani abu. Can dai ganin Irfan bashida niyyan masa magana yasa sa cewa " Architect wai lafiya, meke damunka. "This is all your fault Sadiq, na gaya maka I don't wanna engage my self into such stupid so called love stuff, kayi influencing dina I should propose yo her, toh gashi nan she let me down, ta kallo tsaban idona ta fada bata sona, na fada maka dama ba sona take but you keep insisting, for goodness sake yanzu raini ma ya shiga tsakanina da ita........" Dariya sosai Sadiq ya shiga yi har yana sunkuyawa..... "Mugun kallo Kawai Irfan ke watsa masa kafin yace" you making a fun of me, good ya maka kyau Sadiq, barin fice na bar maka office din idan ka gama dariyan saika kirani. "Riko hanumsa Sadiq yayi yana ci gaba da dariya kafin yace" haba Architect take it easy, bani na kar zomon ba fah rataya aka bani... "Irfan ya tab'e baki kafin yace "there you go again with this hausa quotes, mtsw am serious fah Sadiq, I don't know what to do fah now that I fell for her.... "Sadiq yayi k'ok'arin saita kamsa kafin yace" my point exactly, neman solution za'ayi bawai kace shikenan yanzu ta rainaka ba, Architect shifa love babu ruwansa da status na mutum kawai shiga yake, ka ajiye all those girman kanka nan kayi facing reality, kar ka bari macen da kake so ta kufce maka, yeah na sani kana da komai da zakayi yanga wa mace son ranka, shiyasa ma nake ga babu macn da zaka ce kana sonta tak'i Irfan, kawai dai sai sun d'anja ajin nan ne da suka saba... amma ka sani su mata 'yan lallab'i ne dole ka sauk'e kanka ku zama level d'aya. "Tsaki Irfan yayi kafin yace" To hell with jan ajin nasu, all that I've shown to her, kana nufin saina bita fiye da haka,,,,, kai no never. Yanzu haka ma regretting abinda na mata nake, kai ni dama na rik'e son nata a zuciyana wllhi da yafi mun, kasanni I don't tolerates shitss wllhi. "Sadiq ya murmusa yana mamakin hali irin na Irfan, koda yake ya cika na mijin da zaiyi haka.... "Koda ya tashi a office me ba gida ya wuce ba, gidansu Ahidjo ya nufa direct dan kuwa tin bayan daukosa da yayi a club bai kuma ji daga garesa ba........ *Toh 'yan uwa a daidai nan zan dakata da rubuta wann littafi nawa harsai Allah yakai mu bayan sallah...... Inama kowa fata na Alkhairi, Allah yasa muyi azumi lafiya yasanya mu cikin 'yantattun bayinsa, Allah yasa ayi sallah lafiya.....QueenSamy ke maku happy Ramadan Mubarak in advance😍* πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ‘„........ [8/28, 14:01] Umar Dalha: πŸŒ“πŸŒ”πŸŒ—πŸŒ˜ *Mallakin Waye* 39 _Barka da Sallah to all my fans around the world 😍😘..... #Always 2geda ✌🏼_ "Kallo daya Ahidjo yayi ma Irfan ya gane wani abu na damunsa dan kuwa tin shigowansa bai cema Ahidjo kanzil ba sai zama da yayi ya soma buga game PS5, da ganin yanda yake danna pat din zaka gane something is definitely wrong, Ahidjo ya zauna gamida jawo pat daya shima suka soma game din a tare, yanda Irfan yake buga game din da zuci abun har ya bawa Ahidjo dariya, ganin dai tabbas Irfan lost his mind yasa shi ajiye pat din kafin yace" Guy wai meke damunka ne? "Irfan ya dago kai yana kallonsa galala kafin yace" what sort of question is this, I just came here to get some fresh air, look I don't want disturbance kar ka dameni pls. "Ahidjo yayi murmushi yana kallon abokin nasa dan idan da sabo to babu shakka ya saba da miskilancin Irfan tun ba yau ba, daga haka be kuma ce masa komai ba ya ciro wayarsa ya shiga dannawa. " _Bana sonka bana sonka bana sonka master_!!! Kalaman Deejah suka shiga dawo masa kwanyansa, meyasa ya kasa cireta a zuciyansa meyasa yakeji kaman wutan sonta dad'a ruruwa yake a zuciyarsa,..... "NOOO!!! ya furta da k'arfi gamida jifa da pat din dake a hanunsa, toshe kunnuwansa yayi tamkar zararre yake fad'in " you can't take me down, you cannot do this to me Deeee, I know you love me too, just say it, say you love Deee....... "Tamakar TV haka Ahidjo ke kallon irfan se yanzu ya gane dalilin shigan Irfan wani yanayi.... " _Tabdijam ko a mafarki be tab'a zaton akwai macen da Irfan zai zare akanta ba, kai ko zamansu a US babu kalan en matan da basu kawo kansu ma Irfan ba amma fir bae kula kowa bai da lokacin kowa yau ga Irfan dying for a mere girl, yarinya me law class irin Deejah lallai kuwa Deejah ta ciri tuta, duk wnn tunani a ransa Ahidjo keyi, sai yanzu ya kuma jin sha'awan Deejah na dad'a tsargarsa, kai dole ma Irfan yasota dan kuwa koda ace ba wani kyaun fuska bane da ita akwaita da diri wanda duk na miji mai isheshen lafiya yayi tozali da ita sai yaji abu ya tsargar masa, kai dole yasan yanda zaiyi ya sami Deejah kata halin k'a'ka_.. "Take it easy pls Irfan, comfort your self and spell everything, Ahidjo ya fadi sanda ya tsare Irfan da ido. " Gajeren tsaki Irfan yayi gamida mikewa ya nufi d'an madaidaicin fridge din dake a parlorn Ahido, wani karin abin takaici shine fridge din babu komai a ciki sai tarin alcohol masu dan karan tsada iri daban daban harma da magungunan mura na yara, tsaki ya kumayi sanda ya juyo yanama Ahidjo mugun kallo, kauda kansa gefe Ahidjo yayi dan yasan yanzu zasu haura da Irfan balle dama already ransa a b'ace yake. "Meye kake wani juyar da fuska, Ahidjo you'll never change will you? By the time alcohol ya saka maka wani ciwon ko ya maidaka mental nan ne zaka gane shan barasa ba abin burgewa bane, for goodness sake baka tsaya kan wines ba harda drugs kake sha abinda ka sani haukatar da mutum yake, ya kuma yin gajeren tsaki kafin ya suri car keys dinsa zai fice. "Har ya kai door yaji muryan Ahidjo yana fadin" baka gaya mun ba wa ya bata maka rai har kake sunbatu kai kadai, "Ba tareda ya juyo ba yace" is non of your business malam. Ahidjo ya murmusa kafin yace " koda baka fada mun ba na riga na sani kan wnn yarinyar kake wahalar da kanka, for goodness kaje ka nemi level dinka Irfan, kafi k'arfin wnn yarinya by far, of all people ka rasa wace zaka so sai wnn mere girl of a thing din........ " A zuciye Irfan ya juyo yayiyo kan Ahidjo na huci yake fad'in" how dear you called Deejah a thing, idan ban fada maka ba barin fada maka yanzu" I love her with all of my heart ka gane, I don't care what's her status in life, I loves her for who she's..... "Daga haka ya fice zuciyansa na ci gaba da zogi yanda yaji son Deejah na neman zautar dashi, ko da wasa aka ce masa zai so wata haka zai musa sai gashi yanzu ya rasa mind dinsa kan wata yarinya. A tsaitsaye ya shiga ya gaida Ammi mahaifiyar Ahidjo kafin ya fito yanda yayi parking motarsa, nan ya tarar Ahidjo na tsaye jikin motar na jiransa, ko kallo be ishi Irfan ba ya bude motar sa ya fizgeta da k'arfin gaske. "Ahidjo ya bisa da kallo yana mamakin irin son da Irfan ke ma Deejah, tunanin yanda zai raba Irfan da Deejah ya soma dan kuwa sha'awarta dad'a ruruwa yake a zuciyarsa mussaman yanzu da yaga yanda Irfan ya haukace kanta shed'an sai ya da'da k'awata masa sururar Deejah, wani murmushi yayi gamida shafa sajensa kafin ya shige sashen Amminsa..... "Sosai hankalin Deejah ya tashi jin gaba d'aya mutanen Orphanage babu wanda yasan yanda Yusra ke rayuwa a yanzu, k'walla suka ciko idanunta a hankali ta mik'e jiki babu kwari ta dubi su iya Delu tai masu sallama gamida barin sak'on gaisuwanta zuwaga Aunty Larai... "Gudu yaken falfalwa bisa titin Aso Drive, can ya hangi wata kamar ita tana neman abin hawa, so yake ya wuceta amma inaa zuciyarsa ta hanasa aikata hakan, dole yaja wata birki a gabanta wanda saida ya razanata.....! "A firgice ta d'ago idanunta da suke rikirkita Irfan tana duban sa, ta razana da ganin yanayin da taga Irfan, huci yake idanunsa naga kan titi, bae cemata komai ba sai horn da ya soma mata, fuska a turmuk'e tasa kai zata wuce duk da da'di da farin cikin ganinsa da tayi, "Irfan yabita da kallon mamaki ganin yanda ta wucesa abinta, a zuciye ya bude marfin mota ya nufota, ba tareda yace mata komai ba ya shiga fizgo hanunta ya nufi mota da ita. "Malam lafiya kar ka sake tab'a min jiki ni ba er iska bace, ta fadi tana k'ok'arin fizge hanunta, ko kad'an Irfan beji mamakin kalamanta ba dan yasan Deejah akwai kamun kai, saida ya jefa ta cikin motar kafin ya soma tuki tamkar me shirin tashi sama...... "Sosai abin yabawa Deejah mamaki, idanunta ya sauk'a kan fararen hannayen Irfan wanda jijiyon sukayi green shar suka tashi...... burkin da zaiyi kuwa Deejah ta hantsalo cikin jikinsa..... _Kuyi hak'uri da wnn babu yawa...... luv you all 😘_ πŸ‘ΈπŸ»QueenSamy........πŸ˜πŸ’„πŸ‘„ πŸŒ˜πŸŒ˜πŸŒ”πŸŒ” *Mallakin Waye* 40 *Na Sameena Aliyu* "Wani irin wawan birki yaja qiiiiiiiiiiiiiittttt a tsakiyar titi dan kuwa ba zata yaji fad'owan Deejah cikin jikinsa, sa'ansu guda babu mota dab dasu, Kallon Deejah yake babu ko kyafta ido, cikin azama ta mik'e tana k'ok'arin gyara zamanta. "Bece mata komai ba yaci gaba da zabga race bisa titi bai staya ko ina ba sai wani wajen shak'atawa da yake a cike flowers...... " Kallon mamaki Deejah tabisa dashi, gani tayi fuskan nan nasa tamau sai d'an pink lips dinsa dake kan shinning uwa ya shafa jan baki saurin kawarda idonta tayi dan bata iya juran kallon k'urilla wa Irfan, da kyarta iya furta "ina ka kawoni.... "bece komai ba sai parking motarsa da yayi, cike da miskilanci ya furta" ki sauk'o muyi magana, daga haka ya fice ya nufi kan grass carpet ya zauna gamida crossing legs dinsa ya daura hannayensa bisa gwiwoyinsa. "Tana zaune gaban mota take hangosa, kai shikam komai nasa me kyau harta yanda ya zauna ya burgeta, tsan tsan son Irfan ne ke azalzalanta, runtse idanunta tayi k'irjinta na dumm dum haka ta fito ta k'araso yanda Irfan yake, can gefe dashi ta zauna sunfi minti biyar babu wanda yayi magana cikinsu..... " can ta tsinkayo killing voice dinsa yana fad'in" Khadija me yasa kika min k'arya, " d'ago idanunta tayi da sauri kafin tace k'arya kuma? Ni kuma?...,.. "Irfan ya karkato yana fuskanta ta kafin yace" Of course Deejah you lied to me, kince min baki sona bayan kuma ni na gani a kwayar idonki kina sona,. "A hankali Deejah ta sauk'e ajiyan zuciyadan duk a tunaninta Irfan yasan tayi yawon Club ne, girgiza kai ta soma tana fad'in " you've got this wrong bana son....,,, " Kafin ta k'arasa magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu" Don't you dear lie to me again, why can't you just admit it, you love me Deejah I can read your mind, na sani kina sona, just tell me why do you keep insisting sayin baki sona, you must have your reason for that. "Kasa cewa komai tayi sai kallon k'asa da takeyi..... "Irfan yayi gyaran murya kafin yaci gaba da fad'in" Deee ki yarda mun jima muna son juna tun sanda muka soma had'uwa, ki tuna those moments da mukayi a tare, ba komai muka nuna wa juna ba sai tsantsan soyayya, nikaina banyi realizing hakan ba sai yanzu da na tabbatar yess sonki nake, Dee a da can, da za'ace min ni Irfan zanso wata mace zan k'aryata, gashi yanzu ya faru da ni and I'm suffering for love. Dee ki fada min meyasa kika k'i yarda kina sona...... " Hawaye ya hango na digowa daga idanunta, da sauri ya matso kusa da ita ji yake tamkar ya rungumeta, cikin sanyin murya ya soma fad'in" Na tak'uraki ko, am sorry pls ki dena asaran wnn hawayen naki masu tsada, farin cikinki yafiye mun komai, idan de akan wnn maganar ne bazan sake ba, just stop shading those tear okay..... "Yanda yayi maganar yasata kuma jin tausayin kanta, A hankali Irfan ya furta tashi muje na maidaki gida. Har zai mike ya jiyo muryanta me cike da kuka a ciki tana fa'din" Ina sonka ina sonka master, saidai nida kai bamu dace ba ko kad'an....,," Tamakar a mafarki haka yaji batun Deejah. "Murmushin jin dad'i yayi kafin yace" Ni da ke munfi kowa dacewa....." Girgiza kai ta soma kafin taci gaba da fad'in " Kaid'an gata ne, ni kuwa er wahala ce, kai kyakkyawa ne, ni kuwa ban kaika ba, kai me kud'ine ni kuwa talaka ce, kai m...... " Enough of this Deee, Irfan ya katseta da fad'in haka, kar na sake jin wad'an nan kalamai daga bakinki, I don't care what your status, all I know is that I love you for who you're, na sani you're from Orphanage snn na sani kin rasa iyayenki ne sanadiyan zaizayan k'asa, Deee am ever ready to be your father your mother and husband a the same time. Bana so wnn maganar ya kuma damunki,and koda wasa kar ki sake furta haka a gabana, I love you for who you are. "Murmushi ta d'ago tanayi shi kuwa Irfan harda kashe mata ido d'aya, me keken ice cream yazo wucewa nan ya saya masu suna sha suna firan soyayya, Suna zaune suna sipping ice cream irfan na mata fira jefi jefi dan shima ba wai ya saba da surutu bane... can Deejah tace Ya Irfan, dagowa yayi yana duban cike da mamakin sunan da ta kirasa dashi dan bata tab'a ba, nan taci gaba da fadin " Alfarma daya nake so ka min, Irfan ya murmusa kafin yace" Ke kin wuce neman alfarma a wajen abinda kike so ayi kawai zaki fadi" Deejah ta dan sunne kai kafin tace " pls kar

Chapter 14 of 40