why Dee do you hate me that much. Kiyi hak'uri kar ki sake risking life d'in ki haka, idan akan buk'atanki da kike nema daga gareni ne na yarda na amince da zaran mun koma Nigeria I'll do as you wish kinji, but for now kiyi hak'uri har na gama abinda ya kawo ni England I promise I won't bother you again kinji...."A zabure take kallonsa yanda yake maganar babu alamun wasa a tattare dashi, ji tayi zuciyarta ya tsinke hawaye suka ciko idanunta, did she just hear him right, Goodness she just couldn't believe it wai ya Irfan ke fad'in da zaran sun koma Nigeria zaiyi abinda ta umarce sa yayi, kenan zai rabu da ita yake nufi... tuni hawaye ya soma ambaliya a fuskarta...."Cike da tashin hankali yake fad'in" Com'on Dee kiyi hak'uri just couple of weeks zamu kara nasan kina son komawa Nigeria, but pls this is all I'm asking of you pls, matse hannunta ya kuma cikin nasa kafin yaci gaba da fad'in" Ganinki cikin farin ciki ya fiye mun komai a rayuwata zanyi abinda kike so sweetheart ya k'arashe maganar yana mai rungumota cikin jikinsa yana fad'in" Oya stop crying, ki daina min asaran hawayenki it hurts me alot...."luf ta kwanta cikin k'irjinsa sai ajiyan zuciya take, sonsa take ji kaman kar ya saketa daga rungumar da ta masa..."Kowa da nashi sak'e sak'en da yakeyi cikin zuciyoyin su.. Dr na zuwa yayi discharging nasu...
"Wani kulawa na musamman Irfan ke bata, da kansa yake bata abinci sann ya tabbatar tasha maganinta, dare yanayi kuwa mik'ewa yayi ya d'au pillow ya bud'e wardrobe ya ciro wani bedcover kafin ya k'araso wajenta gamida manna tama peck a goshinta yace" If you need anything ina parlor kinji princess daga haka bai kuma cewa komai ba ya d'au jakar laptop d'insanya wuce parlor......"Kallo Deejah ta bisa dashi har ya fice, ji take kaman tace masa ya dawo ta kwanta cikin jikinsa, tana son mijinta tana missing nasa, amma idan ta tuna abinda yayi mata wani takaici da haushinsa ne yake tokare mata mak'oshi, a hankali ta kwanta tana mai kukan zuci.....
"Kasa bacci tayi dan kuwa tunanin Irfan ya addabeta a hankali ta mik'e tana sand'a kaman wata b'arauniya ta shiga lek'ensa ta ramin k'ofa, "Yana zaune yana sipping coffe lokaci guda yana aiki bisa computer.... A guje ta koma ta kwanta gamida lumshe ido ganin ya taso ya nufo d'akin ashe wayarsa ya mance gefen bedside.....
"Kallonta yake kanyi sanda ya sunkuya don d'aukar wayarsa, kwad'ayin matarsa yake yana tsananin buk'atar ta burinsa bai wuce ya kwanta cikin jikinta ba amma yasan hakan ba mai yuwuwa bane a hankali ya sunkuyo gamida mata light kiss akan lips dinta kafin ya furta I luv you Dee pls don't leave me, I can't imagine life without you... daga haka ya fice ba tareda ya kuma yin komai ba..."Hawaye ne suka zubo daga idanunta anya batayi ganganci ba kuwa wata zuciya tace dad'in baki kawai yake maki dan yana son jikin ki, da sauri ta toshe kunnuwanta dan bata son tunanin ko kad'an.....
"Washe gari da safe farkawa tayi ta gansa yana shiryawa gaban dressing mirror, abun mamaki yau jampa ya saka sky blue harda hula dark blue zanna bukar ba k'aramin kyau yayi ba, ji tayi ta kasa d'aga idanunta daga barin kallonsa, ta jikin madubi yake kallonta yanda tai masa k'urillah sandanyake d'aura agogo, a hankali ya juyo gamida sakar mata murmushi kafin yace"Good morning baby...."Da sauri ta kawar da kanta gefe wai kar ya gane kallonsa take, murmushi ya kuma kafin yace" Ki tashi ki shirya we are going somewhere....." A zabure ta mik'e dan dama ta gaji da zama waje d'aya tunda tazo tana nanik'e waje guda, har bata san sanda murmushi ya subce mata ba, murmushin shima yayi kafin yace" Ina parlor idan kin gama daga haka ya fice zai baza k'amshi yake.... "Yana fita Deejah ta mik'e tana fad'in" Yes yeey yau zan fita nasha iska..."Irfan na lab'e yana kallonta harda wani tsalle da rawan ta, dariya sosai ta basa yanayin ta na burgesa....
"Yana zaune parlor yana kallon TV a lokaci guda yana sipping black tea Deejah ta fito cikin wani Arabian gown navy blue mai bak'ak'en duwatsu ta yane kanta da bk'in mayafi... "A hankali ya furta ya Salam, dif ya mance shan tea yake, tayi bala'in masa kyau...."Murmushinya sakar mata, ita kuwa duk sai tajita wani iri sabida irin kallon da yake mata, zo ki karya baby kar muyi latti muryansa ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, babu musu ta k'araso gamida zama duk jinta take a tak'ure hakanta karya, sabida mayen kallon da Irfan ke binya dashi...
"Duk yanda suka wuce kallonsu ake kaman wasu taurari, Irfan kuwa harda sakalo hannunta cikin nasa, sunyi kyau har sun gaji shakka babu sun dace da juna, Yanayin k'asar ya burgeta, ko ina tas tas gwanin ban sha'awa ga gini masu kyau da d'aukar hankali, a hankali take murmushi tana jin annashuwa cikin ranta, Shi kuwa Irfan sai murmushi yake yana son ganinta cikin farin ciki yana saka sa jin dad'i.....
"Ga mamakinta wani gida taga sunzo Irfan ya danna bell, wata baturiya ce tazo ta bud'e masu k'ofa gamida masu sannu da zuwa, haka kurum Deejah taji gabanta na fad'uwa tun zuwarsu Gidan, gabanta bai gama yankewa ba saida taga wata mata bak'ar fata ta fito tana ma Irfan sannu da zuwa cikin harcen hausa, toh su wacece wann a ina Irfan ya santa..."Gaisuwa da zolaya matar ta soma yima Irfan gaba d'aya bata lura da Deejah ba wacce ta kafe wani makeken hoton family picture d'in gidan Alhj Abdullah da idanunta, zuciyarta na harbawa haka kurum sanda take kallon hoton......
Sameena ceππΎ
[10/11, 10:05 PM] βͺ+234 803 864 9695β¬: ππππ *Mallakin Waye*
88
*Β©Sameena Aleeyou....βπ½*
_Queen Samy Novels Forum....ππ_
"Muryar Anty Bilki ne ya dawo da Deejah daga duniyar tunanin da ta tafi yanda take fad'in" Architect matar tamu kenan? Irfan ya murmusa yana kallon Deejah wacce ke k'ok'arin gaisar da Aunty Bilki,
"Itace Aunty na, musamman yau na kawo maki ita ta tayaki wuni kafin su Ayla su dawo daga school. Aunty Bilki ta fad'ad'a murmushinta kafin tace" Kai amma kuwa naji dad'i ya sunan nata. "Khadeejah Irfan ya bata amsa a tak'aice, agogon hannunsa ya duba kafin ya mik'e yana fad'in" Toh Aunty na I'm leaving nasan Mr Chairman yana jira na...,
"Mik'ewa Aunty Bilki tayi cikin sauri tana fad'in"
"Kallo Deejah ta bisa dashi alamun da gaske barinta zaiyi ita kad'ai tare da mutanen da bata sansu ba..."Muryan Aunty Bilki ya katse mata tunaninta sanda take fad'in" Irfan breakfast fah, pls ka tsaya ka sa wani abu a cikin ka, d'an girgiza kai yayi kafin yace" wllhi a k'oshe muke Aunty na, we already have our break.
"Mik'ewa Aunty Bilki tayi tana fad'in " I know you Irfan baka son cin abinci har Chairman ma ya gane ka, so I'll make takeaway for you.... bata jira cewarsa ba tayi wucewarta ciki.
"Juyowa yayi yana kallon Dee wacce tayi shiru tamkar bata wajen, sunkuyowa yayi kafin ya d'an shafi gefen fuskarta yace" Baby I'm going, da zaran na gama da Office zanzo na d'auke ki, just feel at home kinji Aunty Bilki is like a sister to me though a nan na saba da ita, so if you need anything don't hesitate to talk to her, she's very friendly yanda baki tsammani, nasan na barki a safe hand, I love you....ya k'arashe maganar yana manna mata kiss a goshi. "D'ago ido kawai tayi tana kallonsa sai samun kanta tayi da gyad'a masa kai alum toh. Murmushi ya kuma kafin yace "Yauwa baby ta, shafa kanta yayi tamkar wata k'araman yarinya kafin ya fice, Deejah ta bisa da kallo har ya b'ace ma ganinta....."
"Fitowar Aunty Bilki kenan da basket a hannu ta tarar Irfan ya tafi, zama tayi gefen Deejah kafin tace Wai tafiyar yayi bai karb'i abincin ba, Deejah ta d'an murmusa kafin tace" Ai munci abinci kafin muka fito, murmushi kawai Bilki tayi kafin tace" just feel at home, Irfan ya zama d'an gida, mijina yaji dad'in aiki dashi, Khadeejah kinyi dacen miji mai gaskiya da rik'on amana and also very hard working, at his age samun matashi mai k'wazo da k'ok'arin aiki irin haka da kamar wuya..."Nan ma murmushi kawai Deejah tayi, Kallonta Aunty Bilki tayi tana nazarinta dan kuwa tsaf taga irin sallaman da sukayi da Irfan, shakka babu akwai matsala tattare da aurensu dukda kodaga gani suna tsananin son sunan su, idan da amana kuwa ya kamata ta taimaka wa Irfan ta gyara masa auratayyar sa, d'an murmushi tayi kafin tace" Khadeejah tashi mu shiga ciki, babu musu Deejah ta mik'e tabi bayanta tana mai fad'in" Toh Aunty...
"Kar ki damu Khadeejah ni wllhi na d'aukeki tamkar k'anwa bance ki fad'a mun sirrinki ba, amma ina so nasan shin kina son mijinki..."Dago ido Deejah tayi tana kallonta kafin ta gyad'a mata kai a hankali k'walla fal idanunta.
"Sauk'e ajiyan zuciya Anty Bee tayi ta rik'o hannayen Deejah kafin tace" Deejah inajin wani al'amari mai girma a tattare da ke dan Allah ki fad'a mun tarihin rayuwarki...."I zuwa lokacin hawaye sun soma bin..."Jikin Anty Bee ya kuma yin sanyi, bata san sanda ta rungumo Dee ba tana lallashinta, Deejah bata b'oye mata komai ba tun girmanta a Orphanage har zuwa yau.
"Hawaye tuni ya wanke fuskan Aunty Bilki, dukansu biyu kuka suke, Aunty Bilki ta saita kanta kafin ta rik'o hannayen Deejah tace" Hak'ik'a Deejah kin had'u da sharrin 'yan adam, hak'ik'a rayuwarki akwai tarin darussa a ciki, amma Irfan baiyi Deserving haka daga gareki ba, duk abinda yayi, yayi ne out of love, yana sonki yana k'aunarki, kar ki kuskura ki *Mallaka* ma wata mijinki, auren Azeeza da yayi makirci ne kawai suka k'ulla ba wani abu ba, yanzu kinsan me nake so dake?..."Deejah ta girgiza kai alaman a'a. Aunty Bilki ta murmisa kafin tace" tashi muje kitchen muyi girki, babu musu Deejah ta mik'e ta ajiye mayafinta fuska fal fari'a tabi bayan Aunty Bilki dake rik'e da hannunta suka nufi makeken kitchen d'inta wanda turawa keta kaikomo a ciki,
"K'aramar tsuntsu ta ciro daga freezer da alama baru ne, wankewa ta kuma yi kafin aka d'aurata bisa wuta, wasu k'ullin kayan manya ta ciro aka soma had'i ma barun nan, Deejah dai sai kallonta take, suna had'a ido ta sakar mata murmushi kafin tace ta bud'e fridge ta ciro kankana da kwakwa da dibino sann ta nuna mata wata drawer tace ta d'auko mark'waila a wajen Deejah sai mamaki take ina ta sami wad'an nan abubuwan ita da take England, wata zuciya tace ba abun mamaki bane tunda a duniya take, nan da nan tayi duk abunda Aunty Bilki ta saka ta kan kace me sun had'a kayan sauk'ar wa macce ni'ima, Deejaj dai gaba d'aya kasa shan parpesun nan tayi dole dole Aunty Bilki ta sakata ta shanye tass, juice d'in kuma tace shi zata wuni tana sha, daga nan ta ciro wani k'ullin ta mik'a mata tace da zaran magrib tayi tayi tsarki dashi, Deejah tana d'an sunne kai ta karb'a Aunty Bilki ta murmusa tace, nifa yayarki ce so kima daina jin kunyata duk abinda ke damunki just let me know ta kashe mata ido guda tace hope kin gane....sosai ta bawa Deejah dariya gaskiya kirkinta ya zarce tunanin mutum, bud'e jakarta tayi da niyyan saka maganin ciki sai ganin kwalban turare tayi a ciki wanda ya sauk'ar mata da fad'uwar gaba....."Aunty Bee ta bita da kallo ganin yanayinta ya canza d'an tab'ata tayi kafin tace yaya dai Deejah.
"Deejah ta ciro turaren tace turare na gani cikin jakata, kuma ni a iya tunani na ba ni na saka ba, Aunty tayi shiru tana nazarin abin, Deejah ta ciro tana k'ok'arin bud'ewa da sauri Aunty ta karb'a kafin tace bazakiyi amfani dashi ba dan kina kewaye da mugaye zo muje, taja hannun Deejah suka fice, can ta baya suka je, Aunty tayi bisimillah ta buga kwalban nan a k'asa ya fad'i tuuuuiii, ai kuwa yana fashewa sai wani hayak'i da wari ne ya gauraye wajen, basu gama shan mamaki ba sai ganin tsutsosti sukayi suna fita daga cikin kwalban, cike da tashin hankali suke kallon juna Deejah ta rungume Aunty Bee tsam cikin jikinta sai b'ari jikin nata keyi, Aunty tace ki kwantar da hankalin ki kinfi k'arfin mugu zo muje muyi alwala muyi sallah raka'a biyu muyi addu'o'i babu musu Deejah ta amsa mata da toh Aunty......
*Abuja, Nigeria*
"Haka kurum Laila taji wani mugun fad'uwar gaba, da firgici kallon agogo tayi taga k'arfe 9:00pm, sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin tace Allah sa dai lafiya, a'a abu kaman wasa sai ganin wani ciwo tayi a tafin k'afarta wanda batama san taji ciwon ba, wani mugun zafi da zogi had'i da k'aik'ayi ciwon ke mata tuni ta soma sosa ciwon tana lailayasa da 'yannyatsun ta....
"Jikin Ruqayya yayi tsanani, tana rik'e da hannun Nadiya da Sadiq a hankali take fad'in" Ku yafe mun, ku rok'a min Allah ya yafe mun koda bayan raina ne, snn dan Allah kuce wa Mamie da Umma Hajja su yafe mun...."Nadiya cikin kuka take girgiza kai tana fad'in" Ruqayya ki daina fad'in haka, you are not going to die, you are a fighter, keep fighting kinji Ruqayya.... "Girgiza kai Ruqayya tayi kafin tace" Nadiya lokaci na yayi bazan wuce lokaci na ba, na gode wa Allah da yasa nayi nadaman abubuwan da nayi tun ina da sauran numfashi tun lokaci bai k'ure min ba, Ba hali na bane *Muguwar k'awa* da kuma son zuciya irin tawa ta kaini ga halaka.."Allah yasa wannan ya zama ishara ga masu hali da son zuciya irin tawa, Ya Sadiq ka rik'e Nadiya amana hak'ik'a matar zama ce, Allah ya baku zuri'a d'ayyiba, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku...."Kasa cewa komai sukayi Nadiya kam sosai take kuka, Shima Sadiq tuni yaji hawaye na k'ok'arin wanke masa fuska, salati Ruqayya ta soma kan kace me rai yayi halinsa..."Innalillahi wa inna'ilaihirraji un, ko wace rai sai ta d'and'ani mutuwa...."Kuka mai k'arfi Nadiya ta sake gamida durk'ushewa k'asa, shikuwa Sadiq addu'a yayi ya shafe mata idanunta da suke a bud'e, sosai ya rungumeta cikin jikinsa.....
Sameena ce ππΎ
[10/11, 10:05 PM] βͺ+234 803 864 9695β¬: ππππ *Mallakin Waye*
89
*Sameena Aleeyou.....βπ½*
_Queen Samy Novels Forum....ππ_
"Iyaka dauriya Sadiq yayishi dan neman kukan ma yayi ya rasa, he needs to be very strong, nan likitoci suka shigo suka soma duba gawar Ruqayya, Sadiq kuwa haka yayita lallashin Nadiya yana nuna mata mahimmancin hak'uri a lokacin da aka maka babban rashi irin haka,.. "Kan wasu awanni su Mamie sunji labarin mutuwar, Kuka baizo wa Sadiq ba saida yaga shigowar Mamie rayuwarsu na baya ya dawo wa Sadiq, shikenan da gaske Ruqayyar sa ta rasu ta barsu, take hawaye ta soma wanke fuskar Sadiq, Allah sarki rayuwar duniya maras tabbas, Haka Mamie ta had'e Sadiq da Ruqayya tana faman basu baki dukda itama dauriyar kawai take, dukda b'acin ran da Ruqayya ta sakata ciki, Mamie ta tausaya mata snn ta yafeta duniya da lahira, tasan Ruqayya yarinyar arziki ce had'uwa da lalatattun k'awayene kawai yaso gurb'ata ta, Allah Sarki d'iyar k'aninta, a tare suka bi gadon da ake turota da kallo, Mamie batasn sanda kuka ya kubce mata ba, a fili ta furta Allah maki rahama Ruqayya ta, Allah sa Aljannahtul firdausi ya zama masauk'in ki nanhar abada. Sadiq kuwa durk'usawa yayi a wajen yana kuka mai tsuma zuciya...
*Manchester, England*
"Koda su twins suka dawo suka tarar da Deejah ba k'aramin dad'i sukaji ba, dashike Deejah akwai son yara nan da sai suka saba, haka kurum taji son yaran ya shigeta tamkar k'annenta wanda suka had'a jini haka take jin sonsu har cikin b'argomda tsokanta, Aunty Bilki kuwa a tare ranan suka shiga kitchen ita da Deejah suka dafa dinner.
"Dad din su Ayla da Irfan basu dawo ba sai wajajen k'arfe 8:pm lokacin Aunty Bilki nantsaye dining area tana jera plates twins suna parlor suna kallon wani Animation ai kuwa suna jin muryan daddyn su suka nufosa a guje suna d'alewa jikinsa, ganin Irfan yasa su fad'awa jikinsa a guje shima suna fad'in" Uncle Architect munga Aunty Dee your wife, murmushi kawai Irfan yayi ya shiga d'aga su sama yana masu wasa, haka suka d'unguma gaba d'aya suka shige ciki, Aunty Bilki ta k'araso tana masu sannu da zuwa, fitowar Deejah kenan daga kitchen hannunta rik'e food warmer sai ganin mutane tayi fal parlorn...."Caknta tsaya sanda idanunta ya sauk'a kan mutumin da hankalinta ya fi tafiya gareshi a family picture d'insu, shima kallonta yake haka kurum yaji fad'uwar gaba mai tsanani tareda abunda bazai iya fassarawa ba, Aunty Bilki ta k'araso ta karbi Warmer din kafin tace" Deejah ga daddyn su Ayla ku gaisa, da sauri ta saki murmushi gamida durk'usawa har k'asa ta gaishesa, shima cike da fari'a yake amsa mata mik'ewa tayi cike da kunya ta koma kitchen d'in ta sami Aunty Bilki,
"Haka kurum yaji yarinyar ta burgesa, juyowa yayi ya kalli Irfan kafin yace" Architec barin shiga ciki, ku fara dinner dinnkafin na fito, Irfan ya murmusa yace" Ok Mr Chairman a fito lafia. Haka daddyn su Ayla ya shige ciki yana mai tunanin Deejah shakka babu ganinta ya tuno masa Fatimah, yana jin wani al'amari da baisan yamda zai fassara ba.
"Aunty Bilki da Irfan sai hira suke twins suna k'wab'a masu shirme Irfan kuwa na biyesu yayinda Aunty Bilki ke faman k'wab'an su, Deejah kam banda juya spoon cikin plate bata iya komai, ganin mutumin nan a zahiri ya haifar mata da mummunar fad'uwar gaba, haka kurum taji tana alla alla su tafi, bata son mutumin ya kuma fitowa suyi arba,..
"Irfan na hankalce da ita gaba d'aya baison abinda zai tak'urata dan haka shima atsaitsaiye yaci abinci suka soma shirin tafiya, Aunty Bilki da twins basu tafiyar Deejah da Irfan ba, ta cika Deejah da goma na arziki tare da shawarwari na *Mallakn miji*.
"A b'angaren Alhj Abdullah kuwa tunda ya shiga d'aki ya kasa katab'us ganin fuskar tsohuwar matarsa yayi a tattare da Deejah, wainshin meke faruwa dashi ne, haka a wann dare Aunty Bilki ta kasa fahimtar mijin nata gaba d'aya.
"Nazarinta yake kan yi yanda gaba d'aya yanayinta ya canza, bai ce mata komai ba dan baison matsa mata ta kuma attempting guduwa, d'aukan abin sallah yayi kafin ya k'araso kusa da ita, zaunawa yayi gefenta gamida rik'o hannayenta, a hankali ta d'ago tana dubansa, abubuwa da dama sun tsaya mata a zuciya, na farko turaren da ta tsinta cikin jakarta na biyu ganin wann mutumin...." Murmushi Irfan ya sakar mata ba tareda yace komai ba, sun d'an jima a haka kafin yace" Kina son wani abu ne, "Da sauri ta girgiza masa kai alaman a'a, matse yatsun hannunta ya kuma cikin nasa kafin yace" You looking so dull baby ko dai bakiso zuwa gidan Aunty Bilki bane, ko an maki wani abu ne..."Nan ma da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a kafin ta bud'e baki ta soma fad'in" She was nice to me, naji dad'in kasancewa da ita.."Irfan ya murmusa yace that's good,kafin mu bar Manchester zamu sake ziyaransu.."Murmushi Deejah tayi wanda har saida fararen hak'waranta suka bayyana, rabonsa da ya ga wann murmushin nata tun kan ya aureta. Kiss ya manna mata a goshi kafin ya d'au pillow yace "sai da safe baby...."Har ya kai k'ofa yaji ta rungumesa ta baya tana hawaye..."Da sauri ya juyo yana dubanta, ganin hawaye kwance kan fuskar ta ya tada hankalin Irfan, cike da damuwa yake fad'in baby lafia what's wrong...."Jiyo muryarta yayi tana fad'in" am sorry ya Irfan, am truly sorry pls forgive me for what I've done to you....."Rungumeta tsam yayi cikin jikinsa kafin ya masu masauk'i kan gado, a hankali ya shiga saka harshensa yana lashe hawayen nata, fad'i yake" Baby bakimin komai ba, ni yafi cancanta na baki hak'uri, ko me kikayi kinyi daidai, ko wani irin punishment kika yanke min I deserved it, so pls ki daina min asaran wann hawayen naki masu tsada...."Kallonsa take cikin ido tsantsan gaskiya da soyayyarta take hanhowa a idanun nasa, a hankali ta soma fad'in" I was stupid tun daga fari da ban fad'a maka komai ba da haka bata kasance ba, ya Irfan ina sonka ina k'aunarka pls kar ka rabu dani...." Rungumeta tsam yayi cikin jikinsa kafin yace" Deejah you're my life my inspiration, I'll never ever leave you, koda nace maki ma idan mun koma Nigeria zan yi as you saboda sonki na fad'a haka, amma rabuwa dake na daidai da rasa rayuwata, d'ago kai tayi tana murmushi tana kallonsa a hankali ta furta ka yafe mun, hancinta ya d'anja kafin yace" na yafe maki my Baby, nima ki yafe mun..."Bai ankara ba saiji yayi ta rungumesa sosai cikin jikinta, a kunnenta yake rad'a mata sai kin fad'a min dalilinki na k'in aurena a wancan lokacin. "Dago kai tai tana kallonsa ko kadan bata son tunowa amma ya zama dole ta fad'a masa komai, daga yanzu babu wani b'oye b'oye atsakaninsu.
"Deejaj ta fad'awa Irfan komai har dalilinta na fara zuwa club ta fada masa, da irin razanata da Safwan yayi kan auren Irfan, duk saboda Azeeza ta *Mallake sa*, bata rage komai ba bata k'ara komao ba....."Kan kace me fuskar Irfan yayi jazur, haka nan idanunsa.
"Cikin kakkausar murya yake fad'in" That Imbecile owes me alot, dama ni tunda daddy yayi employing dinsa nake da bad feelings akansa, so he was the reason da bamu kasance tare tuntuni ba, you shouldn't have kept quite Deejah, I'm pretty sure that jerk was the one who sent me those ridiculous texts, I'll make him pay for his damn crimes, I'll make him suffer, sann Niece din tashi da suka lik'a min zan sake ta da zaran na koma Nigeria...."Da sauri Deejah ta shiga girgiza kai tana fad'in" Pls ya Irfan kar kayi haka, Allah baya son saki, snn Azee bata da laifi ko kad'an Safwan shine mai laifi dan Allah kar ka hukunta ta da laifin da bata da hannu ciki, ka tuna tana d'auke da babyn ka, ko dan wann kar ka saketa pls...."Kallon Deejah kawai yake idanunsa sun kad'a sunyi jazur shi kad'ai yake jin abunda yake ji cikin zuciyarsa, baya tunanin zai iya yafewa Safwan, har had'a fuskan Deejahn sa da blue film yayi, tabbas idonsa idon Safwan na lahira sainya fisa jin dad'in..."Ganin damuwa ya nuna sosai a fuskar Deejah yasa saussauta ma kansa, a hankali ya kamo kunkuminta gamida mannata cikin jikinsa, abu guda ne zai mantar dashi bak'in cikinnda yake ciki anyanzu, shine kuwa ya kasance da Deejah, a hankali ya tallafo kanta gamida sakala bakinsa cikin nata, hannayensa suna rawa ya sauk'e su kan k'irjinta abunda yafi komai tafiya da Irfan a jikin Deejah, tun tana jin tsoro har ta samu kanta da biye masa suka ci gaba da aika sak'wanni wa juna,, "A hankali yake maganar cikin sigan rad'a yake fad'in" Baby muje muyi sallah mu gode wa Allah da ya *mallaka* mana junanmu k'ark'ashin inuwa guda a matsayin ma'aurata despite all the obstacles we've been gone through.
"A hankali ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 40