arzikin ka karka b'ata mun rananr da yafi ko wace rana muhimmaci a rayuwata, ka tausaya min Safwan kar ka rabanimda farin cikin rayuwata.,,....'"
"Murmushin mugunta yayi kafin yace" Deejah kenan. And what makes you think that I can change my mind?, na riga na gama magana ko kiyi yanda nace kokuma a wajen aurenki na aikata abinda na fad'a maki... sann idan baki sani ba ki sani, na hada fuskokinmu nida ke a wani video na blue film... kinga duk wanda yaga videos da pics na rawanki a club to kuwa babu ko shakka zasu yarda kin aikata wnn blue film din... So zabi na gateki, na dai gaya maki sharudai na wllhi kika yarda da auren Irfan ki kadda kin zama abin k'yamata a garesu... sai naji feed back... daga haka ya kashe wayar yana tuntsure dariya.,"
" Deejah tamkar gunki haka ta sandare a waje.... Zaro ido waje tayi wanda ya jik'e da hawaye dan bata zaci rashin imanin Safwan yakai haka ba, girgiza kai ta soma tana toshe bakinta da hannunta dan already taji ana knocking a k'ofar d'akinta.... "Kasa ko motsa k'afarta tayi balle ta iya bude k'ofar... "
"Nadiya ce ta shigo hannunta rik'e da laffayan da amarya zata saka yayinda Aunty Larai ke biyeda ita a baya hannunta rik'eda kayan manya wanda aka girkasu musamman don amarya.
"Knocking Nadiya keyi k'ofar bathroom tana kiran Deejah.." Dee pls ki fito ki shirya haka nan, time na tafiya for goodness sake.... "Deejah tana jin haka ta kuma matse idanunta wasu zafafan hawaye suna zubo mata yayinda zuciyarta ke barazanar tarwastewa...๐ช
"Fitowarsa kenan daga bathroom yana tsaye closet dinsa yana faman shiryawa, Ahidjo ne ya shigo ya sha gayu cikin jampa ruwan toka da bak'ar hula sai watsa k'amshi yake.
"Guy how far, cewan Irfan dake k'ok'arin saka babbar rigar fara k'al din jampan sa wanda yaji aiki irinta yayi.
"Everything is going perfect Mr Groom, Ahidjo ya basa amsa kafin ya zauna can gefe kan kujera, ciro wayar sa yayi ya fakaici Irfan ya tabbata hankalinsa na kan shiryawa... wata murmushin mugunta Ahidjo yayi kafin ya furta a zuciyarsa _You'll never be happy Irfan, Deejah ba Mallakin ka bace da sannu zamu san Deejah *Mallakin waye*_....
"Dago idonsa yayi ya hangi wayar Irfan dake gefe dashi kan kujera, wata murmushin ya kuma yi kafin ya ciro wata k'aramar nokia a aljihunsa, cikin mintuna k'alilan ya turawa Irfan tex din da tun jiya yake tura masa, kan kace me har ya kashe wayar ya cire sim ya jefa cikin aljihun sa....
"Irfan na d'aura agogo yaji k'aran shigowar text, k'irjinsa ne yayi mugun bugawa dan ko bai duba ba yasan bazai wuce d'an isakan nan bane da ya damesa... Amma yasha alwashin bazai saka ma ransa damuwa ba a ranar da yafi ko wace rana mahimmanci cikin rayuwarsa. Dan yau jinsa yake cikin wani irin farin ciki marass misaltuwa, Dee dinsa zata zama *Mallakin sa*
"Ai kuwa shid'in ne gajeren tsaki yayi gamida goge mssge din.... "Ahidjo daya maida hankali kan wayarsa dake faman dannawa ya saci kallon Irfan a sace.. Murmushi yayi kafin ya saita kansa, kallon Irfan yayi sosai kafin yace" Bro is anything the matter.
"Gorgiza kai Irfan yayi sanda yake kafa hularsa kafin yace" No Bro just forget about it, it's nothing serious, ya su Ashraf kuwa sun iso, ka kirasu pls kasansu basa abu on time. Ka kira Sadiq ma pls I don't know what took him so long, he supposed to be here by now, ka kirasa pls kaji ko lafia. Barinje I've to see Ammah.......
"Gyada kai Ahidjo yayi yana murmushi harda sara masa kafin yace yes boss, komai kace za'a yi right the way...is your day ai.. "Murmushi kawai Irfan yayi kafin ya fice yana sab'a babbar riga, kana ganinsa ba sai ance maka yau ya soma skawa ba... "Duk sai jinsa yake awkward ๐. Su ba saban ba...
"Babu yanda Aunty Larai batayi da Deejah dan ta stagaita kukan da take taci parpesun er shilan barun da aka mata amma Deeja ta kasa ko guda daya...
"Nadiya ta kuma shigowa taci gayu sosai cikin doguwar rigar atampa super yellow, tayi kyau sosai dama Nadiya gwanar gayu ce. "Dee pls ki saka lappayan na dauki hotonki na turawa ya Irfan, tun dazu sai damuna yake wai zaiga bride dinsa, nasan na kuma fita mukayi karo dashi ban dau pic din ba sai yayi ball dani, pls ki shirya na tura masa, wnn lappaya da kike gani tun mummy nada rai ta basa ya bawa duk matar da zai aura ranar aurensa tunkan ya Irfan yasan zai soma kula mace, kinga idan baki saka ba he'll get mad... " Ta juyo tana duban Aunty Larai da ta saka wa Deejah ido tana karantar yanayinta tace "Aunty pls ki sata tashirya barin kai abinci wa abokan ya Irfan.
"Juya lappayan ta rink'ayi a hannunta tana kallonsa, lokaci guda tausayin kanta ya kamata, Allah sarki lallai Irfan yana sonta so na hak'ik'a bai cancanci juya baya daga gareta ba,.. _"Yay zanyi ni Deejah??_ta fadi a zuciyanta gamida rumgume laffayan tana shesshekan kuka... Ido kawai Aunty Larai ta zuba mata tabbas akwai abinda ke faruwa.
" Tana rik'e da hamshak'an warmers wanda basai ance maka sunji tsada ba, ta nufi sashen Irfan.. Azee da Zulai suna rik'e da wasu suna take mata baya, burin Azee duk bai wuce taga farin cikinta Irfan ba.
"Kaman daga sama ta hangosa ya kafeta da idanu yana mata kallon dake tsunduma ta cikin kogin tunaninsa....."Karasawa yanda yake tayi tana murmushi, shima murmushin yayi gamida kulle motarsa ya k'araso, yayi kyau cikin jampa fara kal da hula, kaman ka suresa ka gudu dan kyau. "Sosai yake bin Nadiya da kallo dan bata tab'a masa kyau irin haka ba.
"Ruqayya da fitowanta kenan daga cikin mota ganin yanda Nadiya ta karaso wajen Sadiq yasa saurin ficewa ta nufi cikin gidan da sauri ko tsaywa batayi ba balle ta tanka Nadiya, Nadiya da Sadiq kam kula basuyi ba sunyi nisa cikin aika wa juna sakwanni ta idanu.
"Dole tasan yanda zatayi da Nadiya, she really needs to get rid of her, da wnn tunani ta shige cikin gida.
"Lil sis, kinyi kyau sosai, sai ina?
"Murmushi ta danyi kafin tace big bro kenn kaima kayi kyau sosai, dama abinci zamu kai maku.
"Zaro ido Sadiq yayi kafin yace" wait, a haka dinne zakije gaban abokan Irfan na US salon su kalle mun lil sis dina, com on bani abincin ni zan kai masu..... "Sosai Nadiya take dariya kafin tace kai big bro don't be ridiculous.
"Daga mata gira yayi kafin yace" what ever ya karbe kulan daga hannunta, a kunnenta ya rad'a mata, "you look gorgeous, daga haka ya wuce ya barta nan tsaye tana kallonsa cike da murmushi.....
"Agogo yayi clicking k'arfe 11:50 daidai, ya rage saura en mintoci a daura auren Irfan da kuma Deejah, Mutane sun soma cinkoso a k'ofar gidan Engr Nazif Mumtaz dake Babban birin tarayyan Nigeria Abuja unguwar Life camp.
"Engr. Nazif sai faman tarban bak'i yake wanda da yawa daga wata ka'sar sukayi tattaki, dan tun safiyar jiya jiragen sama suke sauk'a da tashi a babban filin jirgin saman Namdi Ezwikwe international airport Abuja.
"Kaman wacce aka zabura ta mik'e a guje tana ambaton Ammah!!!.......
๐ธ๐ปQueensamy ce ๐
[8/28, 14:09] Umar Dalha: ๐๐๐๐ *Mallakin Waye*
59
*ยฉSameena Aleeyou*
_Queen Samy Novels Forum.....๐๐_
"Daddy pls people are waiting, what took you so long...... muryansa ne ya carke...
"Cak ya tsaya ganin sunyi cirko cirko ga hawaye kwance saman fuskokinsu.
"Ganin Deejah durk'ushe a k'asa itama kukan take da sauri Irfan ya k'arasa ya d'agota yana fad'in" Baby what's the matter, what's happening?
"Kuka take tamkar ranta zai fita ba tare da ta iya furta komai ba, da sauri ya rungumeta cikin k'irjinsa, fuska babu alamun wasa ya d'ago yana bin mutanen parlorn da kallo d'aya bayan d'aya kafin yace" Now can someone tell me what exactly is goin on here??
"Engr ne ya k'arasa yana k'ok'arin d'ago Irfan Son let's talk outside ok....."Girgiza kai Irfan yayi har lokacin na rungume da Deejah cikin k'irjinsa kafin yace" No daddy I need know why is my Dee crying, daddy me aka mata.
"Laila ce tayi caraf tace" Irfan saidai kayi hak'uri but can't get married today.
"Whattt!!!! Ya furta gamida d'agowa yana watsawa Laila mugun kallo. D'aga giranta Laila tayi gamida gyad'a masa kai. Wani mugun kallo Engr ya watsa mata tuni ta kauda kai gefe.
"Jijjiga Deejah Irfan ya soma yana fad'in" Dee me ya sameki why are you crying, you I can't help seeing you in tears. Shiru Deejah bata amsa sa ba sai kukan da yatsananta.
"Irfan ya d'ago yana kallon Ammah kafin yace" Granny what's going on here, pls explain to me, I don't get it, ban gane komai ba, why all this.
"Girgiza kai kawai Ammah tayi dan wani sabon kukan ne ya taso mata.
"Kankace me Fuskar sa tayi jajazur haka idanunsa ma, hular kansa ta zame baya. Jijiyoyin kansa sunyi rad'a rad'a.
"Lailace tayi gyaran murya zata soma magana da sauri Deejah ta d'ago kai tana kallon Irfan kafin tace
"Master forgive me pls, pls forgive me, ka yafe mun I don't deserve you. I can't get married to you........" Kasa fahimtar komai yayi cikin kwanyarsa, he just couldn't believe it. Sadiq ma ya zama lost abin ya juye masu tamkar a film.
"No Dee I know you're kidding me right? You can't be serious, this is our day, ranar da yafi ko wace rana mahimmanci a rayuwar mu, Deejah I luv you n I konw you luv me too. I know you must be nervous dear, but I promise you I do all my best to make you happy ever, you won't regret marrying me. Ina sonki Deejah with all of my heart......." Girgiza kai take har lokacin hawaye na bin k'uncinta take da kyar take fad'ain " Master ka yafe mun idan na aureka muyuwa zanyi, pls let me beee....."
"Irfan ji yake tamkar zuciyarsa zata fito waje, tunda uwarsa ta haifesa bai tab'a shiga tashin hankali irinta yau ba, tun bayan mutuwar mummynsa, girgiza kai ya soma har lokacin hannayensa yana rik'e da kafad'un Deejah sosai ya damk'eta kana iya ganin jijiyoyin hannayensa. "No this can't be possible, come on tell me you're kidding me, just tell me karya kike yi Deejaaah!!! Ya karashe maganar cikin d'aga murya.
"Kowa dake parlorn tausayin Irfan ya rufesu, babu kaman Sadiq wanda k'afafunsa suke barazanar kasa d'aukansa.
"Irfan yaci gana da jijjiga Deejah da iya k'arfinsa yana fad'in" Why Why Deejah, why now why today. I don't deserve this, meyasa zaki min haka, meyasa zaki cutar da zuciyan da bata nufeki da komai ba face alkhairi, meyasa zaki cutar da zuciyan da take tsananin k'aunarki,.... "Hawaye ne suka shiga zirya a fuskan Irfan, Da k'arfi yace" Dago idonki ki kalleni Deejah, I said look into my eyes and tell me you don't love me.
"Kasa komai tayi banda kuka.
"You tore my heart into pieces Deejah, on my wedding day, why did you ruin my life just like that why Deejah why, why did you set your eyes on me,..... burki yaja kaman wanda ya tuna abu, hawaye na bin fuskarsa yake murmushin takaici yake fad'in" now I get it, so it's true you love him, you were just using me to get close to him. Meyasa kikayi amfani dani Deejah,....
"Mikewa yayi gamida cire babbar rigar jikinsa yayi jifa dashi har ya juya zai fice ya kuma dawowa gabanta yana mata kallon tsana kafin yace" nayi nadaman saninki Deejah, you are my worse nightmare, you turn my life to a horrible disaster, I hate you, I hate you Deejah. ?....
"Snn shi wanda kike so ya zama *Mallakin ki* he'll never be yours, you gonna pay for what you did. Daga haka ya fice cikin sauri..... "Engr da Ammah na kiran sunansa inaaa ko tsayawa beyi ba, Ammaj ta dubi Sadiq da sauri tace" Sadiq yi sauri kabi bayansa, Engr ma ficewa yayi Laila ta take masa baya.
"Kasancewar hankalin mutane naga gaisawa da junan su yasa basu kula da ditowan Irfan ba sai Ahidjo,
"Kai tsaye waje ya fice dama already motarsa na pake a waje, Sadiq na masa magana ko kulasa beyi ba ya shige yayi key ma motar ya bar haraban wajen.
"Cikin sauri Sadiq ya shiga neman mashin.
"Mikewa Ahidjo yayi ya shiga neman layin Azee.
"Can cikin bedroom dinsa Engr ya shige zuciyarsa na masa zafi, tuni ya kwab'e babbar rigarsa ya shiga kaikomo a tsakiyar makeken d'akin.
"Laila ce ta k'araso da ruwa a cup ta mik'a masa kafin tace" My Engr pls take things easy, stop stressing your self kar wani ciwon ya kamaka, kaga naga aya akan baba Alhaji, saka damuwa a rai shi haifar masa da shanyewar jiki, I don't want to loose you my husband kaji mijina.
"Kallon Laila yayi kafin yace" Laila how could you expect me to calm down, can't you see what's happening,da wani ido zan fice na sallami d'unbin mutanen dana tara for goodness sake, ta yaya zan soma da wani bakin zan soma.
"Mastowa Laila tayi ta rungumesa ta baya cikin murya mai taushi ta soma fad'in" My Engr kar ka damu I'm here for you, together we will go through this horrible tragedy, bazan barka by your self ba, you know I love you and I'm ever ready to do everything for you dear... Fasali ta danja saida ta wani juya idanu kafin taci gaba da fad'in" Emm kaga tunda abun ya kasance haka why not, a daura auren da Azeeza!!
"Juyowa Engr yayi yana fuskantanta kafin yace" Azeeza kuma?
"Kai Laila ta gyda kafin tace" yes Azeeza kaga dai you can't go out ka sanar da illahirin mutanen nan babu aure, your shear holders employees da sauran manyan mutane, snn kai kanada iko akan Azeeza, pls na rok'eka my dear ayi auren nan, dan amfanin matan kenan a rufa asirin juna.
"Shiru Engr yayi yana nazarin kalaman Laila.....
_I know this episode zai tab'a maku rai, wasu suji haushi, but don't worry guys I'll make it up for you....๐_
*Muje zuwa๐*
Queensamy ce ๐
[8/28, 14:09] Umar Dalha: ๐๐๐๐ *Mallakin Waye*
60
*ยฉSameena Aleeyou*
_Queen Samy Novels Forum.......๐๐_
*"Assalamu'alaikum dear love ones". Zan d'anyi tsokaci gameda maganganun da nike kan ji akan littafin nan, wasu sunacewa Irfan should marry Deejah not Azeeza, kar ku mance Deejah itace tauraruwan book din nan no matter how Irfan will never end up with Azeeza, dalili shine duk auren da aka ginasa kan k'arya to kuwa bai tasiriri, Ai "A DADE ANA YI SAI GASKIYA*..... *So please you guys should bear with me and follow me Bumper to Bumper dan jin yanda labarin zata kaya.... Taku har kullum QueenSamy๐๐*
_Meena Aleee kanwata ta kaina I dash you this.......๐๐
_
"Girgiza kai Engr ya soma kafin yace" No Laila bazai yuwu a aura ma yarinya wanda bata so ba, shi dai Irfan yayi hak'uri nasa k'addaran kenan. Kar garin gyara mu kuma jawo wani lik'in"
"Fuska cike da nuna damuwa Laila ta soma fad'in" haba My Engr kar kayi magana haka, idan har ka isa dani toh wllhi babu ko shakka ka isa da abinda na haifa, ballantana kaine uban Azee, tun bayan mutuwan mahaifinta batasan gata da das'i na wani mahaifi ba sai naka, kayi mata sutura ka daukota ka had'ata da naka yaran, bazamu tab'a zama butulu ba, wllhi koda bana aurenka kai ka isa da Azeeza,.... ta d'an ja fasali kafin ta durk'usa kan gwiwoyinta ta ci gaba da fad'in" My Engr idan har ka aminta dani a matsayina na matarka toh ka aura wa Irfan Azeeza wllhi na maka alk'awari zaka sameta tana mai yi maka biyayya, Saidai kuma idan jinina ne baka so. Ta k'arashe maganar tamkar zatayi kuka....
"Zuciyan Engr mai taushi ne tuni Laila ta krya masa zuciya, kafad'unta ya kama ya d'agota kafin ya rungumeta yana fad'in" No Laila don't talk like that, kinada mahimmanci a rayuwata, kinada tarbiyan da kowani mahaluk'i zaiso had'a iri dake, besides idan da bana son had'a jini dake da ban auroki ba in the first place. So kar na sake jin magana makamancin haka daga gareki Irfan, Deejah da Azeeza su duka 'ya'ya na ne, kawai dai ina duba lamarin ne,
"Wani k'atutun bak'in ciki ne ya tokare mak'oshin laila jin Engr ya ambaci Deejah, wai wani irin so suke mata ne duk abinda ta masu bazasu cireta a ransu ba ( ni kuwa samy nace haka Allah kan jefa soyayyan wanda yaso a zuciyar da yaso).... "Muryan Engr ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin da ta tafi yanda yaci gaba da fad'in " kinsan d'an yau aka masa abinda baiso toh fah dole kaga consequences. Kaman yanda a addinance a barsu su auri wanda suke so shiyasa nikega kaman da an bar zancen da yafi.
"Laila ta kuma marairaice fuska tace" haba my Engr this doesn't matter, kar ka mance Governors senators ministers ne waje suke jiranka,harma da abokan huld'anka na kasuwanci daga k'asashen duniya, yaya kake ganin mutane zasu kalleka, hakan ka iya janyo sanadiyan daina business dinka da wasu mutane muddin suka gane ba magana d'aya kake yi ba, ka gayyace su sun bar komai nasu sunyi attending snn a ce babu aure, ai inaga hakan will affect your dignity, you know how important you are to people, you're so worthy pls my Engr don't let that affect you.... "Idan dan yaran ne da sannu zasu soma son junansu da zaran anyi auren, Allah yaga zuciyanmu na kyakkyawan kudiri, snn abinda babba ya hanga yaro ko ya hau tsauni bazai hango ba.
"Murmushi Engr yayi kafin ya manna ma Laila kiss a goshi yace " thank you Laila thank you for always being there for me, hak'ik'a shigowarki wann family alkhairi ne, bazan tab'a mance halaccin da kika min ba. Rungumesa tayi sosai cikin jikin tana murmushi mai cike da ma'anoni da fassarari.
"A hankali ta furta tsakani na da kai babu godiya mijina daddyn twins daddyn Irfan daddyn Nilam da Nadiya. Go ahead kaje a d'aura aure your guest are waiting.
"Saida laila ta kuma shiryasa ta feshe shi da turarruka kafin ya fice zuwa filin d'aurin aure.......
"Hello sweet baby ya kayai, Ahidjo ya fad'i murna fal ransa, wani dariya Azee ta fashe dashi kafin tace " ai komai ma anyi kai kam. Dariyan Ahidjo ma yayi kafin yace" ina amaryar mu nasan by now zuciyarda yayi exploding....." Azee ta kuma fashewa da dariya kafin tace" Hidjo guy baka da dama, tana can d'aki ta kulle kanta wayasani ma ko tayi suicide. Dariya sukayi gaba dayansu kafin yace " ki fito ta backdoor akwai maganar da zamuyi, babu musu Azee tace gani nan right the way, dan wani irin farin ciki takeji a ranta maras misaltuwa.
"Duk yanda Sadiq yayi dan ya cimma Irfan abu yaci tura, gudu kawai Irfan yake bisa kwalta, lokaci guda abubuwan da suka faru suka shiga dawo masa, meyasa rayuwa ta koma haka, meyasa Deejah ta masa haka, shin wai shi bashida sa'a ne a rayuwarsa, meyasa ma ya soma yarda da ridiculous thing so called love.... "Buga starry yayi da k'arfi yana furta " I hate you Dee I hate my self...... " Daidaia wajen 'yan black market yaja burki petur ya saya a galan kafin yaci gaba da tafiya..... isowar Sadiq wajen Irfan ya bar wajen, nan masu black market din suka fada masa abinda Irfan ya saya.
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un kawai Sadiq ke ambato, " oh Irfan what are you doing, my goodness.... da sauri ya haye mashin din yace malam dan Allah kar ka bari ya bace mana am quite sure he gonna kill him self. Da sauri 'an achab'an ya shiga falla gudu bisa titi.....
"Irfan bai tsaya ko inaba sai gidansa da ya gina masu shida Dee dinsa, ma'aikata masu k'arasa sauran gini da masu gadi tuni suka k'araso dan kwasan gaisuwa, ganin yanayin Boss d'in nasu ya tabbatar masu da babu lafia,
"Daya daga cikin maginan ya k'araso yana fad'in "Architect akwai abin da kake so a canza ne.... "Kala Irfan baice ba sai bin gidan yake da kallo, ya tuna ranar da ya kawo Deejah taga gidan, ya tuna good times d'in da suka kasance shida ita, wani sabon k'unci ya tokare masa k'irji.... da sauri ya k'arasa ya bud'e bayan motarsa ya ciro petur din,"
"Sir, menene wnn, architect lafia meke faruwa, cewan shugan ma'aikatan, kallonsa Irfan yayi kafin yace" Engr ka tattari yaranka ku tafi.... " Engr Sabo yace" but Architect akwai sauran aiki kadan kayi hak'uri wllhi Oga ne yasamu kai kayyaki Kaduna jiya, aikin company mukayi jiya da tuni mun gama...." Harara Irfan ya b'alla masa kafin yace cikin d'aga murya wanda har saida ya jawo attention din sauran ma'aikatan " I said get the hell out of here, ko baka ji bane Engr, idan kuma baka son ranka fine you kan stay... "Da sauri Engr Sabo ya shiga basa hak'uri alama yayi ma sauran ma'aikatan da su fice, gaba daya suka soma ficewa....
"Kallon gidan yake yana tuna tun ranar da ya soma ganin Deejah tun ranar ya soma zanen gidan, a halin yanzu ya tsane gidan baijin zai iya zaman gidan, k'ona gidan shi yafi masa a'ala... "Kaman wanda aka zabura ya shiga watsa petur ta ko ina, .......
*#FFF* Fuck Fake Friends๐๐ฝ
๐ธ๐ปQueensamy ce๐
[8/28, 14:09] Umar Dalha: ๐๐๐๐ *Mallakin Waye*
61
*ยฉSameena Aleeyou*
_Queen Samy Novels Forum........๐๐_
"Tun d'an achab'an bai gama parking ba Sadiq ya sauk'o daga mashin din, a guje ya fada gidan Irfan, masu gadi suna ganinsa suka k'arasa wajensa da sauri suna fad'in" yauwa yallab'ai gwara da ka iso, Oga yana ciki ya bule gidan da warin petur......" Ai Sadiq bai gama jin me suke fad'a ba ya shige gidan a guje.... "Daidai lokacin Irfan na k'ok'arin kunna lighter, fizgewa Sadiq yayi cikeda b'acin rai yake fad'in" What the heck are you doing Irfan, are you insane or what, haba Irfan you need to calm down....
"Mugun kallo Irfan ke watsa wa Sadiq da rinannun idanunsa kafin yace" Kaine babban maras hankali daka hanani aiwatar da abinda nayi niyya, and let tell you nothing is wrong with my sanity, me zanyi da gidan nan, na tsani ganin gidan.
"This is my wedding day,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 40