wani namijin......
"Oh momy believe me I didn't want it happen either, is just thay I couldn't help it ne, ni dae yanzu asan abin yi shiyasa na kiraki....
"Tsaki Laila ta buga kafin tace" K'arama dake sai jaraban tsiya, toh ki bud'e kunnuwanki da kyau kijini, kina jina... Azee ta gyada kai baki a ture tamkar laila na ganinta, kafin Laila taci gaba da fad'in" kinsan har Niger nasa aka je min a sabidake, toh yanzu akwai sauran magungunan zan bawa Zulai ta kawo maki, wllhi saura ki sake mik'awa ma wani shegen kanki nida kene.
"Murna Azee ta soma harda daka tsallenta kafin tace " wa ai ansha ni na warke bazan kuma, ina jira momy... daga haka tayi hanging.
*Orphanage*
" Duk da ta wani koma sukuku da ita, babu me shiga sabganta itama bata shiga sabgan kowa, musamman dashike yanzu Aunty Larai bata Orphanage, rayuwa tayiwa Deejah d'aci, idan ka ganta saika tausaya mata, duk ta rame ta fita hayyacinta, a kullum bata da aiki sai tunanin Irfan da family dinsa sai kuwa kuka, son Irfan a jininta yake ita tasan da haka.
"Yauma kaman kullum, ta gama cin kukanta ta mik'e daga saman katifarta lokacin agogo ya nuna k'arfe biyar daidai na yamma, kai tsaye kitchen ta wuce dan neman abinci, dan yanzu bata isa ta shiga kitchen lokacin kowa na cin abinci ba, habaici a cin mutunci kawai sun isheta, bata da kowa yanzu a orphanage, babu Auntu Larai babu Yusra, saiko wad'anda suka k'i jininta tun a baya.
"A tunaninta tunda yanzu yamma ne, bazata sami kowa a kitchen ba, amma ga mamakinta sai gani tayi akwai mutane a kitchen d'in, daurewa tayi ta k'arasa babban food flask yanda ake zuba masu abinci, ta d'au plate tana k'ok'arin zubawa.
"Atika ta kalli Delu suka saka shewa da rangad'a gud'a, Atika tace " Oh k'awata ke da kika saba da abincin gidan masu kud'i ta ina zaki soma iya cin wnn abincin namu... "Delu ta kwashe da dariya kafin tace " kedai bari kawai ba dolena ba, tunda bani da zab'i sun k'ini sun koroni yaya na iya dole na dawo tushena gidan marayu.. "Atika ta kuma sa dariya kafin tace" toh meyasa kema baki tafi wajen uwarki data tsince ki ba, koda yake itama yanzu babu abinda zatayi dake tunda babu kudin da zaki kai mata ko kuma da kinbi k'awar taki kuka ci gaba da karuwancin ku ba tunda tare kuka faro.......
"Tunda suka soma magana Deejah bata tankasu ba, amma wann magana da Atika ta furta na k'arshe yayi mugun mata zafi, ... A hasale tayi jifa da playe din hannunta kafin ta k'araso gaban Atika tana nuna ta da yatsa take fad'in " Duk abunda zaku ce kuce amma kar wacce ta sake ce min karuwa cikin ki dan ni ba fasik'a bace..... "Dariya suka fashe dashi Delu ta mike tana shan d'ammara suka soma fad'in" Ke wllhi ki iya kanki yarinya dan yanzu uwar da take d'aure maki gindi bata nan, sai mulallasa maki dukan tsiya a nan.... an fad'a karuwa 'yar tsintuwa, mu da kika gani a nan kowa yasan iyayen mu da certificate aka kawo mu orphanage, ke kuwa fa, saidai a ce a zaizayan k'asa a tsince ki, wanda ko a tarihi bamusan da wann ba,..... "Kasa jure sauraron maganganun su tayi tuni ta fice a guje tana sharan kuka mai tsuma rai.... Allah sarki π°π.....
*Katsina*
_Daura_
"Hajja umma mahaifiyar Mamie ce zaune gefen Dada, bayan ta gama mata hayak'in magani, kallon Dad take ta soma samun lafiya ta rage ihu da koken da take ba kaman da ba, harta sunbatun da takeyi a da ta d'an rage yanzu, Alhamdulillah sauk'i nakan samuwa. Kallonta take xike da tausayawa duk ta fige gashin kanta wanda ada daga gani yana da tsananin yawa, sosai ta k'arewa Dada kallo, tabbas Dada kyakkyawan mace ce dukda tana cikin hauka kana iya gane hakan, Allah sarki Allah ya saka maki duk wanda ya maki haka cewar Hajja Umma....
*England*
_Manchester_
"Ayla da Afnan sai kuka suke suna fad'in saidai a kaisu Fatherland dinsu wato Nigeria suga k'asarsu, tumda aka haifesu a turai suke basu san k'asar iyayensu ba, yanzu da suka gane daddyn su will never take them back to Nigeria sai suka tada rikici sosai a gidan. Ba yanda mum dinsu batayi ba tayi convincing nasu suyi hakuri amma abu ya gagara duk da karancin shekarunsu...
"Da kyar bayan ta lallab'a su sunyi bacci ta dawo study room din mijinta yanda ta samesa zaune yana aikin tunani, zama tayi gefensa kafin tace" My dear pls let's go back to Nigeria ko don yaran nan, dago kai yayi yana kallonta kafin yace" Never, Never Bilkisu, I can't bazan iya ba Bilkisu you perfectly well know that, they should learn how to be patience, dole susan bazasu tab'a zuwa k'asarsu ba, England shime k'asar su.
"Shiru Bilkisu tayi na d'an lkaci kafin tace" what about business venture danaji kana magann zakayi da wani company a Nigeria.
"Shima d'in shiru yayi tamkar me nazari kafin yace" bana tunanin zan iya dukda d'unbin alkhairin da za'a samu, amma I'll think about it, koda zanyi saidai su biyo ni nan England don nikam alk'awari ne bazan je Nigeria.... Shiru Bilkisu tayi tana jimamin lamarin na mijin nata.
*Nigeria*
_Abuja_
"Shiryawa tayi cikin wasu matsatstun kaya wanda komai na jikinta ma iya cewa a bayyane yake, heavy makeup sosai tayi a fuskanta, rabin k'irjinta kuwa a bud'e yake, turarruka iri da kala ta feshe jikinta dashi, ta d'au alwashin yau kam saitaja hankalin Irfan sai tayi amfani da matantakan ta ta jawo hankalinsa gareta a matsayinsa na d'a namiji..... Tanajin k'arar tsayuwan motar sa k'irjinta yabada rass kallon kanta ta kuma a Consul din dake mak'ale a parlorn kafin ta isa jikin k'ofa........
*Tooh fah muje zuwa readers*
QueenSamy ce ππ½.........
[8/28, 14:11] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
66
*Β©Sameena Aleeyou.......βπ½*
_Queen Samy Novels Forum.....ππ_
*"Hi Sweethearts, da fatan duk kuna cikin k'oshin lafia, kuyi hak'uri da d'an mishkilan da aka samu a previous chapter, I was a bit exhausted lokacin da nayi typing ko editing bansamu nayi ba, that's why kuka ga ko numbering ban yi ba, afuwan pls for the little mistake, but still labarin daidai ne babu abinda ya canza" Keep on following me.... Luv you all π*
"Kallon Aunty Larai tayi zatayi magana Aunty larai tace , maza jekiji kiran nasa, babu musu ta d'au hijabinta ta saka, zuciyarta na ci gaba da bugawa da sauri da sauri,
"Daga can gefe ta hango Range Rover d'in Engr Nazif a pake, cikin nutsuwa ta k'arasa wajen, Engr yana ganin ya fito daga motar fuskansa babu alamun wasa.
"Duk jinta take ba'a sake ba, gaba d'aya gani take itakam bata kyauta ba abinda tayi, har k'asa ta tsuguna ta gaidashi, kafin ta d'ago tana wasa da 'yan yatsun hanunta take fad'in" Daddy ka shigo ciki mana.
"Girgiza kai Engr yayi kafin yace" No Deejah basai na shigo ba, Nilam ta aikoni wajenki,..
"Jin ya ambato Nilam yasa Deejah saurin d'ago kai, k'warjininsa ya hanata kallon cikin idonsa dan har yau kallon surki take masa.
"Cikin in...inaa take fad'in" Yayasu Nilam.
"Shiru yayi na d'an lokaci yana nazarin irin ramar da tayi kafin yace" duk suna lafia.
"Khadeejah meyasa kika tafi ba tareda sanina ba? Ya jefo mata tambayar da take ta faman tsoron kar Allah sa ya tambayeta.
"Shiru tayi ta kasa furta komai,
"Gyara tsayuwarsa Engr yayi kafin yace" Deejah bai kamata ki tafi ba sabida abinda ya faru tsakaninki da Irfan, you perfectly know how Important you are to my family, kin shiga rayuwar yarana suna sonki yanda baki tsammani, ever since you left bamu samu kwanciyar hankali a gidan ba, Nilam tana son kasancewa dake, you shouldn't have left Khadeejah, ko ban isa uba a gareki ba ni inajinki tamkar jini na tamkar d'iyar da na haifa, I deserves some respect from you......
"Innalillahi wa inna'ilaihirra'ji'un " wayyo Allahn ta tamkar kasa ya tsage ta shige haka taji, shikenan Daddy kallon maras kunya yake mata, take taji hawaye sun ciko idanunta,
"Durk'usawa tayi ta soma bama Engr hak'uri, da sauri ya furta "No Khadija, tashi daga k'asan nan ba na fad'a maki bane don naji haushi saidai raina ya b'aci sosai when I found out that you left the house, kin zama member na family d'inmu Deejah, you're one of us koda baki auri Irfan ba. Pls kiyi hak'uri ko baki dawo sabida mu ba ki dawo ko don Nilam.....
"Jiki a sanyaye ta mik'e tana goge ragowar hawayen, kafin tace daddy dan Allah ka daina rok'ona kafi k'arfin haka a wajena nice ya kamata na baku hak'uri sabida abinda nayi ban kyauta ba"
Sosai tabawa Engr tausayi daga gani kasan wani babban al'amari na damunta,
"Daddy kayi hak'uri, I didn't mean it, insha Allah zan dawo gida na ci gaba da zama cikinsu Nilam, amma kafin nan inaso nayi magana da Aunty Larai saita maidani.
"Murmushi Engr yayi kafin yace" Allah maki Albarka Deejah.... wayansa aka kira ana nemansa urgent sunada meeting da shareholders.
"Daga kan closet d'in ya hango motan Daddynsa, Ahidjo dake ta faman tambayrsa yaya akayi motarsa ta b'aci me ya sameta? Nan yaji hankalin Irfan baya taredashi kallonsa yayi yanda idanunsa suka kad'a sukayi jazur flesh dinsa tayi turning to red, kafin ya kalli yanda ya k'urama ido, nan ya hango abinda Irfan ya hango, sosai shima ya razana da abinda ya gani, kai no no way, this can't be possible. Da sauri Ahidjo ya karya kan mota da niyyan barin wajen.
"Cikin dakekkiyar murya Irfan yace wa Ahidjo" Stop the car, Ahidjo yace "No Irfan don't do something stupid, you can't talk right now.
"Starry din motar ya kama da k'arfi kafin yace "I said stop the dammn car idiot. Dole Ahidjo yaja burki badon yaso ba,
"Kallonsu kawai Irfan yake" So it was really true, Deejah son Daddy take, they made a fool out of him, Zuciyarsa ta shiga masa zafi, his very own father zaiyi soyayya da macen da he was about to marry her, what the heck is all this, never over his death body....
"Engr ya dubi Deejah bayan ya gama amsa wayar kafin yace" naso na shiga nayi magana da Larai d'in but sauri nake, anyway idan kun gama shiryawa driver zaizo ya d'aukeku ko.
"Murmushi tayi kafin tac toh daddy mun gode, Allah ya taimaka Allah ya tsare, Engr ya amsa da amin kafin Cimon ya fito ya bud'e masa marfin mota suka wuce....
"Deejah tabi motan da kallo tana murmushi, Allah sarki lallai family din Engr suna sonta, she can't wait to see Nilam and twins again, gabanta ne yayi mugun fad'uwa sakamakon tunowa da Irfan datayi, da sauri ta juya da niyyan shiga gida, caraf taji an cafko ta...
"Juyowan da zatayi sukayi ido hud'u dashi fuskan nan nasa tamkar bai tab'a murmushi ba, idanunsa sun kad'a sunyi jazur haka fatar fuskansa, kallon juna suka shiga yi na lokuta, bugun k'irjinta ya k'aru,...
"Kan ta ankara saiji tayi Irfan ya zura bakinsa cikin nata, kissing nata ya shiga yi da k'arfin gaske babu k'ak'k'autawa, ....
"Innalillahi meke faruwa da ita, abun da bata tab'a yi ko a mafarki, da k'arfin gaske ta shiga kokawa da Irfan tana turesa daga jikinta amma ta kasa, saida yayi kissin nata mai isansa kafin ya saketa yana huci..... "Dagowa tayi idanunta sunyi jazur dan ta nemi kukan ma ta rasa gohe bakinta ta shiga yi suna ma juna mugun kallo " Deejah ta tofar da yawu kafin tace" Allah ya isana idan dama k'udirinka akaina kenan toh ka sani bazan tab'a aurn fasik'i ba. Mugu azzalumi kawai
"Matsowa yayi daf da ita da sauri tayi hanyar wucewa amma kan tayi wani katab'us ya kuma rik'ota, matseta yayi sosai jikin garu suna iya jiyo sautin numfashin juna kowa fuskan sa a tamke tamkar masu shirin kashe junan su.
"Daf da fuskanta yake fad'in" Wann kad'an kenan daga cikin irin abubuwan dana tanadar maki muddin kikayi yunk'urin aurensa, ba kiss kawai ba zan maki abinda yafi kiss kinga daga nan babu yanda za'ayi ku biyu ku kasance a tare...... "Hawaye ya soma fita daga idanunsa har lokacin fuskarsa a murtuk'e take gaja da ya k'arayi kai kace alagy dinsa ne ya tashi. A haka yaci gaba da fad'in" Kin bani mamaki, was it was true, you were using me, saboda me kika playing my feelings, you've no idea how you ruined my life. I hate you Deejah, kin cika macuciua maci amana, muguwa azzaluman soyayya.
"Cikeda tsawa ta furta Enough! Hawaye na bin kumatunta take fad'in" bansan magan da kake ba, amma ko kadan abinda nayi nayi ne sabida sonka, nayi ne sabida tsananin sonka da nakeyi, amma abunda kayi yau ya nuna mun true color dinka Irfan, dama kai cikekken d'an iska ne, toh ka sani Allah baya had'a me kyau da gurb'atecce, na gode ma Allah da ban aurek...... "Kan tayi shiru ya kuma matseta jikin garu saiji tayi ya k'ara saka bakinsa cikin nata, sosai yake kissin nata... Hawaye na bin kumatunta tana kiciniyar turesa ta kasa, da k'arfi ta take kafafunsa, nan yayi sauri cika ta.... kan ya ankara saiji yayi ta sauk'e masa mari tasss! 'Dagowa yayi yana mata mugun kallo, itama d'in mugun kallo na kyama take masa.... "How dere you... 'dago hannu yayi zai kai mata mari, kaman wanda akace kar yayi sai kuma ya fasa.
"Tana hawaye take fad'in" Allah ya isa tsakani na da kai, bazan tab'a yafe maka ba... kuka take sosai ta shige gida a guje tana ci gana da kuka.
"Irfan da shima hawayen ne suke bin kumatunsa kallo yabita dashi har ta b'ace masa....
_Kuyi hak'uri da wann babu yawa, zakujini lter insha Allah ππ_
Queen samy ce ππ½
[8/28, 14:12] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
67
*Β©Sameena Aleeyou....βπ½*
_Queen Samy Novels Forum.....ππ_
"Da kyar ta samu ta saita kanta har lokacin bata daina tuno abinda ya faru tsakaninta da Irfan ba, a lokaci guda tana jin bakinsa cikin nata, stigan jikinta ne ya tashi dan kuwa abune da ko a mafarki bata tab'a yinsa ba, yau sai gashi a reality tayishi.. Runtse idanunta tayi da sauri wani haushi da takaici na Irfan na mamaye illahirin zuciyarta.
"A hankali ya shafi gefen fuskansa yanda ta maresa, mirmushi yayi mai cike da ma'anoni kafin ya shafi leb'en bakinsa yana tuno kiss din daya mata, for sure ya sani bai kyauta ba, amma babu yanda ya iya he just couldn't help it, akan daddynsa Dee tak'isa, dole ya nemo mafita he can't stand this.
"Ahidjo ne ya k'araso da mota yad'an masa horn, juyowa yayi ya k'arasa jikin motar ya bude ya shige, Ahidjo ya dubesa da kyau yace" Guy yaya akayi. Shiru Irfan yayi tamkar me tunani kafin yace" Ahidjo akwai abinda nake so ka mun.
"Da mamaki Ahidjo ke kallonsa kafin yace what's that buddy.
"Irfan da har lokacin idanunsa na kallon wani gefe guda yace" So nake kayi dating Deejah.
"Kaman a mafarki haka Ahidjo yaji zancen, girgiza kai ya soma kafin yace" No Irfan you must be kidding, why, what for. Kai no I can't do that Irfan.
"Juyowa Irfan yayi yana kallonsa idanunsa sunyi jazur kafin yace" Ahidjo I want you to do this for me, am I asking for too much.
"Girgiza kai Ahidjo yayi kafin yace" Irfan nasan yanda kake son Deejah dan wani k'addara ya gifta tsakaninku bakuyi aure ba doesn't mean ka daina sonta kenan, na sani kana sonta har kwanan gobe.
"Enough ahidjo! Irfan ya daka masa tsawa kafin yaci gaba da fad'in" Pls Ahidjo do this for me, we are talking about my dad here, baba na ne fah yake yunk'urin soyayya da yarinyar da I was about to marry her, ko a zamanin da bana jin ana irin haka balle a yanzu. What are friends forz? Pls buddy help me do that. Ba ina nufin ka aureta bane, no just date her and dump her ka gane.
"Kallonsa Ahidjo yayi, wani farin ciki na mamaye zuciyarsa, tabbas burinsa na *Mallakan* Deejah ya kusa cika a sauk'i, sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yace" Friend I know exactly how you're feeling, babu komai zan jarabba, amma kai kana ganin she'll love me back...
"Murmushin k'arfin hali Irfan yayi kafin yace" thank you, ko bazata soka ba, ka dai rabata da daddy that's all I want.
"Ahidjo ya murmusa sanda yake karya starryn mota kafin yace" I'll do thay for you buddy... daga haka suka d'au hanya...
"Gaba daya Aunty Larai bata gane mata ba, har Idi driber yazo ya dauke su, Aunty larai duk ta dangana hakan da tunanin komawa gidan Engr da take ciki.
"Idi ya gama zuba kayanta a mota kafin suma suka shige bayan sunyi sallama da mutanen orphanage. Su Atika sai zinde suka suna cewa sai ina kuma oho.
"Ahidjo ya gama parking a haraban gidan, a tare suka nufo cikin gidan shida Irfan, daga window din dakinta ta hangosu, da sauri ta d'auko sallaya da hijabi ta nufo downstairs, a parlor ta baza sallayan ta saka hijabi ta zauna bisa sallayan kaman wacce take lazimi.
"Da mugun mamaki Irfan ke kallonta, bai zaci tanada ibada haka ba, bayan haka rabonsa da yasata a idonsa ya mance sai yau, Ahidjo ya murmusa yace" a'a mutumina kace mun amaryar taka ustaziya ne.
"Irfan baice komai ba sai kallon Azee da yayi dan shima bai zaci haka ba.
"Shafa addu'a tayi kafin ta k'araso ta rusuna ta gaida su. Ahidjo da sakin fuska ya amsa nan yaja Azee da hira tamkar basu san juna ba irinta aboki da matar aboki.
"Da sauri ta wuce kitchen ta kawo masu drinks. Ahidjo ya murmusa yace sannu amarya, tan sunne kai tayi ta amsa tamkar me kunya.
"Mikewa Irfan yayi zai wuce upstairs da sauri tasa hannu ta karbi briefcase dinsa tace sannu da dawowa.
"Yanayin da ya tarar da ita yasa yaji nauyin gwaleta, sake mata briefcase din yayi ba tareda ya amsata ba, Azee kuwa wani dadi ne ya mamayeta, yau wace rana Irfan bai gwaleta ba. Da sauri ta wuce tayi hanyar upstairs, Irfan da har lokacin tunanin abinda ya faru tsakaninsa da Deejah yake nan yabi bayanta.
"Suna isa kofar dakinsa yace" bani jakata, fuska babau walwala, babau musu ta mik'a masa, sum sum ta dawo parlor, shi kuwa ya shige ciki.
"Tana isowa parlor, ta fad'a kan Ahidjo tana kissin nata, harda wani tsallenta kafin tace" yau mutuminka bai gwaleni ba, oya labarta mun plan dinmu tayi aiki.
"Dariya Ahidjo ya kwashe dashi a hankali kafin yace" keda kika sani, ai bamusa abu a gaba aga gazawar mu. Komai ya tafi normal, ya gama zata Daddynsa na son Deejah, ya riga ya gama yarda duk wani evidence da zai tabbatar masa da hakan ya samu, maganar da nike maki yanzu ya sallama mun Deejah, yace na neme ta, daddynsa ya nemeta gwara abokinsa...
"Wani tsalle Azee tayi tana fad'in dan Allah, wayyo this calls for a celebration, Ahidjo yayi saurin jawota ta fad'o jikinsa kafin yace" kin manta bamu kadaine a gidan ba, Ohhh na mance amma karan tv bazai bari yaji komai ba ta fadi tana fari da idanu.
"Mikewa tsaye tayi kafin tace" tabbas yanzu ne kowa zai san zuciyar Irfan *Mallakin Waye* ne. Zanyi komai dan na siye zuciyarsa. Ahidjo ya mik'e yana murmushi kafin yace tied your belt patner. Daga haka ta wuce kitchen yanka masu fruits.
"Jim kadan Irfan ya fito cikin k'anan kaya marassa nauyi, ya dubi Ahidjo yace Guy na gode da company dinka, daidai nan Azee ta dawo da tray na fruits a hannunta tamkar mutumiyar arziki. Kallon Irfan take yanda yayi kyau kaman ta hadiyesa. Ahidjo ya kashe mata ido guda kafin yace" Aah amarya baki gajjiya, already kin cika mun tummy dina, am okay saidai ki zauna ki bawa darling dinki a baki dan shine baici komai ba, Azee dai sai murmushi take, Ahidjo ya jiyo da dubansa ga Irfan wanda yake dauke wuta gaba daya kafin yace" mutumina gaskiya kayi dacen mata fah, haka akeson mace me kula da gida, da dukkan alamu gidanka bazai mutu ba.
"Gajeren tsaki Irfan yayi kafin yace" let's talk outside, Ahidjo ya mike yana murmishi kafin ya juyo ya dubi Azee yace" toh amarya na gode fah sai anjima.
"Azee ta murmusa tace toh sai anjima, mun gode fah.
"Tunda su Deejah suka shigo gidan annurin Laila ya d'auke, su Nilam kuwa sai murna suke, harta su Ammah dasu Hajja murnan su a bayyane yake, Nadiya ma da ta danyi fushi da Dee ta sake, ta dan dunguri keyarta tace zaki sani Letures sun taru sunyi yawa ki gama ganin mutanen kizo ki karb'i handouts, murmushi kawai Deejah tayi Nilam na zaune saman cinyarta.
"Saida Aunty larai ta danyi kusan yini kafin tayi masu sallama, ta karabawa su Ammah hak'uri snn ta tafi.
Misalin k'arfe 9:30pm yana zaune parlor gaban computer dinsa yana aiki lokaci guda suna waya da Sadiq yana fadawa Sadiq shidai bai yarda da sabon ma'aikacin nan Safwan ba, ya kamata su tsananta binkice akansa dan kaman yayi poisoning zuciyar Enhr baya ganin Laifinsa.
"Azee dake lab'e saman bene taji komai, a hankali ta juya d'akinta tana mai tunanin me su Uncle dinta suke kullawa dan bazata bari su cutar da Irfan ba, tana shiga cire kayan jikinta ta d'aura towel daidai gwiwa da k'arfin tsiya ta tak'ark'are ta k'walla wani irin ihu.......
"Sosai hankalin Irfan ya tashi dajin irin k'aran da Azee ta k'walla, da sauri ya mik'e ta cikin wayan yacewa Sadiq, I'll call you back... daga haka ya nufi stirs da sauri....
QueenSamy ceππ½
[8/28, 14:12] Umar Dalha: ππππ *Mallakin Waye*
68
*Β©Sameena Aleeyou.....βπ½*
_Queen Samy Novels Forum.....ππ_
"Azee bata fasa k'walla ihun da take ba, da sauri Irfan ya shiga bugun k'ofarta yana fad'in" Ke lafia meke faruwa. Inaa Azee bata sarara ba sai ihu take kaman ana yanka naman jikinta, Da k'arfin gaske Irfan ya daki k'ofar ta bud'e, tana tsaye can k'uryan d'akin jikin garu ta tak'ure waje guda, da gudu ta yo kan Irfan ta rungumesa sosai cikin jikinta.
"Wani irin yanayi yaji ya ziyarce sa dan kuwa sosai Azee ta manne a jikinsa, jin jikinsa yayi lk'awas tamkar babu laka yasata k'ara manne masa k'irjinta tana wani cukuikuyesa, cikin muryan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 40