wani abu da kike iya tunawa na rayuwarki ta baya?
-Eh, abinda kawai nake tunawa ranar da na bude ido na ganni a wannan kauyen sai sunana. Kuma babban tashin hankalin shine....
-Ina jinki meye?
-Inada ciki!
Da sauri Dauda ya mike, cikin tashin hankali yace
-Ciki?
Sunne kai Jinah tayi tana hawaye sannan tace
-Wallahi bansan ya aka yi hakan ta faru ba, inada aure ne ko kuwa, ban sani ba? Nasan mutane zasu ta min kallon yar iska, ita kuma Sarah suyi ta nunata. Na jawo mata abin kunya.
Hada kai da gwiwa tayi ta cigaba da rera kuka. Shi kuwa Dauda safa da marwa ya fara a wurin kafin yace
-Ni nasan yanda za'ayi!
Da sauri Jinah ta dago tace
-Ta yaya?
-Abu mai sauki, na aureki kinga mutane zasu yi tunanin dan nawa ne.
Duk da hawayen dake fuskar Jinah hakan bai hanata kyalkyata dariya ba tana yi tana cewa
-Daman na dade ina wannan tunanin, ba isashiyar lafiya gareka ba...
-Allah Jinah da gaske nake!
-Gaskiya bakada hankali, ni kaga tafiyata.
-Ki dakata Jinah, Allah da gaske nake, hakan ita kadai ce mafita.
-Kaga, bamu san juna ba kace kana sona, haka ka cigaba da bibiyata tin daga ranar da wannan abun ya faru, a duk lokacin da nazo cikin jeji ko bakin kogi sai na tarar da kai. Yanzu kuma nace maka inada ciki ba tareda nasan ta yaya na sameshi ba, kai kace zaka aureni. Fada mani wane mai hankali ne zai yin irin wannan?
-Kinada gaskiya Jinah, amma kin manta da cewa idan mutum ya kamu da soyayya, zaucewa yake yi. Saboda daga ranar ba kwalwa bace ke jagorantarsa, Zuciyarsa ce, zuciya Jinah!
-A dauka na amince, idan kuma aka je inada aure, kuma na tuna komai?
-Daga ranar babu aurenmu, na amince zan barki ki tafi.
-Ni fah bana sonka Dauda!
Duk da yaji maganar tata kamar saukar aradu, hakan bai hanashi cijewa yayi dariya ba.
-Kai abin dariya ma ya baka kenan?
-Ina dariya ne, dan zan aureki dan ina sonki duk da ke baki sona, amma zan zauna zaman jiran ranar da kema zaki bude baki kice kina sona.
-Gaskiya ba zan iya ba Dauda, kayi hakuri.
Ta juya ta tafi, ta barshi a tsaye kamar an dasashi, shi kanshi yayi mamakin kalamanta sai dai wannan itace mafitar da zai iya samun Jinah, don har cikin zuciyarshi yana sonta. Tun jiya da ya fada mata yana sonta, bai ga alamar amincewa a idonta ba, yasan taki fada masa ne dan kar yaji ba dadi.
Yanzu kuma yana cikin farin ciki ganin zai aureta, sai dai sam bai ji dadin jin tanada ciki ba. Amma yana tunanin komai zai zama daidai da ya aureta.
Jinah karasawa tayi gida da kuka, ita dai bata san me yasa rayuwa tazo mata a haka ba, duk da ta fara sabawa da cutar mantau din da yake damunta, sai dai yanzu abin ya dawo mata sabo sanadiyar wannan cikin. Abincinta Sarah ta kawo mata, sai dai bata cikin yanayin da zata iya cin abinci. Tunani ta fara
Yanzu idan na auri Dauda, mutane zasu dauka Dansa ne, kuma hakan ba zai taba mutuncin Sarah ba, ba zan iya ja mata abin kunya ba, dan tayi min halacci kwarai. Kuma Dauda mutumin kirki ne, nasan ba zai wulakantani ba...
Tana idar da tunaninta, ta duro daga kan gado ta nufi bakin kogi inda ta baro Dauda. Tarar dashi tayi a gurin zaune yana wasar jefa kananan duwatsu a ruwa. Wani dogon numfashi ta ja, kafin ta kira sunanshi.
-Dauda!
Ba tare da ya juyo ba yace
-Oh Allah, haukacewa zanyi, har muryarta nake ji alhali bata wajen.
Zaunawa kusa dashi Jinah tayi tareda cewa
-Ni din dai ce da gaske.
Har wata yar zabura Dauda yayi dan baiyi tunanin zata dawo ba.
Sunkuyar da kai tayi kafin tace
-Nayi tunani kuma na amince zan aureka.
Wani farin ciki ne ya lullube Dauda, ta yanda kasa fadin wani abu yayi. Ji yake tamkar a mafarki, wanda kuma ba zai so ya farka ba.
Kowannen su tunani ya fara ta yanda wannan al'amari zai kasance, sai dai basu yi tunanin me zai je ya dawo ba. Dauda yana matukar sonta, Sai dai bai san abinda zai sameshi ba idan ya auri JINAH matar aljani.
---------------------------
Madallah, a nan zan tsaya a yau, sai kuma idan Allah ya kaimu a wata sabuwar chapter.
Kada ku manta da fadar ra'ayinku na wannan labari...!π€
My watty : @El_Ashtar
π JINAH (Matar Aljani)π
by Malik al-Ashtar βοΈ
On wattpad π https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New β€οΈ Story
CHAPTER 5
Kalmomi sun yi kadan wajen fayyace maku irin farin cikin da Dauda yake ciki. Har yanzu ya kasa gasgata cewa Jinah ta yarda zata aureshi, ganin kin amincewa da tayi a baya.
Duk da wawanci ne auren mace da ciki, sai dai Dauda yana ma Jinah matsanancin son da idanunsa sun rufe ba zai iya ganin aibun da zai hanashi aurenta ba. Abinda yake ji game da ita kwarai ne, wanda shi kanshi ba zai iya fassarashi ba. Muna iya fadawa soyayyar wani a kowanne lokaci, ta dalilin haduwar farko ko kuma a kallon farko. Haka so yake.
-Yauwa ka bani labarinka.
Jinah ta fada tana mai kawo karshen zurfin tunanin da kowannensu ya fada.
-Da farko dai, anawa gidan mu lakabi da gidan Malam Shehu, inada 'yan uwa maza uku da mata biyar wanda muke uwa daya uba daya. akwai kuma yan uwa maza da mata wanda muke uba daya. Mamata itace mace ta biyu cikin su hudu a gun babana. Ke a takaice dai mu mun kasance babban dangi da muke zaune a gida daya...
-Kai kace babban gidane?
-Sosai ma kuwa ai sai kin shiga ciki zaki gani.
Murmushi Jinah tayi tana kallonsa. Cigaba yayi da bata labarin gidansu.
-Babana yanada babbar masana'antar sarrafa auduga, babban mutum ne kauyen mu. Ke dai sai kinje kin ganema idonki.
Jinah na murmushi tace
-Naji labarin gidanku, saura naka.
-Shekaruna 20 daidai, tun ina da shekaru goma na bar school na koma masana'antar babana da aiki. kinsan anan bamu baiwa karatu muhimmanci ba. Saura ke bani labarinki.
Kwalo ido Jinah tayi tace
-Amma wasa kake ko?
-Da aka yi me?
-Kai da na fada bana iya tuna komai...
Ta fada cikin yanayin damuwa.
-Oh yi hakuri, na manta.
-bari naje gida, na fadawa Sarah.
-Toh, amma ki shirya gobe zan zo muje ki gaida yan gidan mu.
-Ok, Allah ya kaimu.
Ta fada tana mikewa.
-Ameen, ki gaida yan gidan.
Koda Jinah tayi nisa, Dauda dan tsalle yayi tare da cewa "Yes!" rawa ya fara tika kamar mahaukaci. Gida ya nufa, mahaifiyarshi ce ta farko da ya fara ba labarin Jinah.
Yana yan tsalle tsalle, yana fadawa mamanshi
-Na samota Mama, mama na samota!
-Me ka samu dana?
Mamarshi ta fada tana kallon ikon Allah ganin yanda yake tikar rawa gabanta.
-Na samo matar aure mama! Inda kin ganta kamar aljana tsabar kyau, sai idan ma tayi magana mama, sai inji kamar tayi ta magana kar tayi shiru. Muryarta idan kika ji kamar algaita, murmushinta wayyoh.. hakorinta sai kice na karamin yaro.
Dariya mamarshi ke yi, dan idan da sabo ta saba da shirmen dan autanta. Kawai gani take giyar soyayya ce take diban dan nata yake wannan sambatun. Yana gama shirmenshi ya nufi masana'anta ya tarar da mahaifin nashi. Daure fuska mahaifin nashi yayi, kafin yace
-Sai yau kayi niyyar zuwa? Yaushe rabonka da zuwa aiki?
-Ai Abbah, yanzu ma ba aikin bane ya kawoni, nazo ne na fada maka wani labari kuma sai kayi farin ciki da jinsa.
-Meye wannan da ya hana min yaro zuwa gurin aiki?
-Abbah, na samu mata, duk wannan lokacin da na dauka ina wajenta ne, dan in san halinta sosai, in san ko matar aure ce. Kuma Abba komai ta hada, kyau, hankali da komai ma.
Yanda Dauda ke ta zuba gaban mahaifin nashi zai tabbatar maka da shagwababbe ne sosai.
Cike da fara'a Mahaifin nashi yace
-Ah to madallah, dole kaki zuwa aiki, ashe ka fara zama mutum. Fada min yar gidan waye?
-Ba anan kauyen take ba, a Mambila take.
-Ah hakan yayi kyau, Allah yasa alheri.
-Ameen Abbah, gobe insha Allahu zan kawota ta gaisheku, jibi kuma sai kuje ku nema min aurenta...
-To ba damuwa, Allah ya kaimu lokacin.
-Ameen Abbah, bari naje na kama aikin.
-A'ah yau na yafe maka, kaje ka huta.
-toh nagode abbah!
Ya fada cike da zumudi ya nufi gurin abokinshi.
Ita kuwa Jinah zuwa tayi ta fadawa Sarah. Hakan ya girgiza Sarah, dan kasa cewa komai tayi.
-Dan Allah kice wani Abu Sarah!
-Ni..Ni bansan me ya kaiki yin wannan gangancin ba. Kin ga na farko baki san wannan mutumin ba, ke ba sonshi kike ba, kina tunanin aure wasa ne da zaki yanke wannan shawarar ba tareda kin fada min ba?
Kunya ce ta kama Jinah ta sunkuyar da kanta, dan wannan shine karon farko da taga ran Sarah ya baci. Kuma tasan Sarah tafi ta gaskiya.
-Dan Haka wannan aure ba yiwu ba, dan sam ni ban amince ba.
-Na fa riga nace masa na amince Sarah, kuma wannan ita kadai ce mafita, idan ba haka ba kema kinsan abinda zai faru.
Shiru Sarah tayi na wani lokaci kafin tace
-Wannan ba hujjah bace Jinah, ni dai ban amince ba, dan haka ki fidda wannan tunanin a ranki.
Fita tayi ta bar Jinah a gurin. Kuka kam Jinah tashashi, dan daren ranar kasa bacci tayi. Washe gari, Dauda yazo daukan Jinah, ranar, ranar hutu ce, kowa yana gida, har da Lasaini da yayi mamakin ganin Dauda. Koda Jinah ta ganshi kallon kayi hakuri tayi masa, shi kuwa yayi kamar bai gani ba. Bayan ya gama gaisawa da yan gidan, ya nemi da su kebe da Lasaini ganin shine babba a gidan.
Bayan sun kebe Lasaini yace
-Ya sunan malamin ma?
-Sunana Dauda Ibrahim.
-Madallah malam Dauda, ko me yake tafe da kai?
-Am.. Nazo ne daman na gabatar maku da kaina, ina son auren Jinah ne.
-Ikon Allah, amma ita Jinar ta sani?
-Eh ta sani, dan har ma ta amince.
-To madallah hakan yayi kyau, sai dai ni banida iko da ita, iyayenta ba anan suke ba, tana karkashin kulawar yar uwata ne, amma bari na kirata dan jin me zata ce.
Kiran Sarah Lasaini yayi, bayan wani dan lokaci ta zo.
-Sarah, wannan saurayin da kike gani yazo ne da maganar yana son Jinah, kasancewar tana karkashin kulawarki, kuma ke kika san iyayenta yasa na kiraki dan ki ji.
-Eh Jinah ta fada min, sai dai zan so muyi magana da shi, daga ni sai shi.
-Ok, ba damuwa, bari na baku waje.
Lasaini ya fada tareda mikewa ya tafi.
-Me kake so ne da wannan yarinyar?
Sarah ta fada fuska a tamke.
-Ban fahimta ba, me kike nufi?
-Wanne namiji ne zai yarda ya auri yarinya tana cikin wannan halin, ba tare da ita kanta tasan ya aka yi hakan ta faru ba?
-Nasan kina son Jinah, kuma ba zaki so wani abu ya sameta ba, ina mai tabbatar maki ba wani abu nake so ga Jinah ba, face farin cikinta. Ina sonta har cikin zuciyata, duk da nasan ita bata sona kamar yanda nake sonta. Kuma ke kin sani, duk yawancin auren da ake yi cikin kauyen nan, auren hadi ne, daga karshe bayan aure ya juye zuwa na soyayya. Nayi maki alkawarin zan saka Jinah farin ciki, kuma ba zan taba cutar da ita ba. Nayi maki wannan alkawarin.
Jin abinda Dauda ya fada yasa jikin Sarah yayi sanyi. Tayi shiru na wani dan lokaci kafin tace
-Amma kasan ba'a yin aure da ciki ko? Kuma ya zaku yi da darenku na farko? dan kasan ba budurwa bace.
-Kar ki damu, ke dai a daura auren, nayi maki alkawarin babu wata matsala da za'a samu.
Kiran Lasaini Sarah tayi.
-Lasaini, iyayen Jinah sun bani ita ne, tareda bani duk wani iko akanta, ganin ni mace ce ba zan iya bada aurenta ba, yasa nace zan baka ramagar komai, kuma kaga kai ne babba a nan.
-Idan haka ne, babu damuwa, kai Dauda ka turo min magabatanka domin mu tsaida magana. Kuma a gaskiya naji dadi da zata yi aure dan na gaji da ganin samarin da ke min sintiri a kofar gida.
-Naji dadin jin wannan kuma insha Allahu idan na koma gida zan turo magabatana. Amma yanzu ina son ku yimin izini muje da ita don ta gaishe da mahaifiyata.
-Wannan ba matsala bace.
Cewar Lasaini.
-Shikenan bari nayi mata magana.
Sarah ta fada tana mikewa. Dakinta ta nufa ta tarar da Jinah zaune ta kurawa window ido.
-Tashi ki shirya zaku je ki gaida iyayen mijinki na gobe.
Tsalle Jinah tayi bisa gado tare da cewa
-Wai kin amince!?
-Eh, munyi magana dashi kuma naga tsantsar sonki a idonshi. Nasan ba zai cutar dake ba.
Da sauri Jinah ta shirya, ta nufi gun Dauda da ya hangota yake ta watse hakora. A tare suka fito daga gidan. Wani kyakkywan doki Jina ta gani a bakin kofa.
-Kai dokin waye wannan mai kyau? Ina matukar kaunar dawakai!
Ta fada tana karasawa kusan dokin tare da shafa kanshi.
-Nawa ne!
Cewar Dauda.
-Dagaske? amma me yasa ban taba ganinka dashi ba?
-Ya dan yi rashin lafiya ne, shi yasa na barshi ya dan huta.
-Mace ce ma ko? meye sunanta?
-Ashanti sunanta!
-Suna mai dadi! Zan iya hawa?
-Me zai hana? tsaya ki gani.
Hawa ya fara yi sanann itama Jinah tayi kamar yanda yayi ta hau. Kada kan ashanti yayi, Sai da suka yi tafiya mai nisa kafin su kawo gidan. Jinah tayi mamakin ganin gidan, dan babban gida ne. Gabatar da ita ya fara yi ga mahaifiyarshi wadda tayi mutuwar zaune dan bata taba zaton maganar da danta ya fada gameda kyan Jinah gaskiya ne ba. Ta yaba da hankalin Jinah kuma taji tana sonta. Sauran yan gidan ya gabatar ma da Jinah, tsabar yawansu kasa rike duka sunayen su tayi. Gida ya dauka "Matar Dauda, kamar aljana."
Washe gari, iyayen Dauda suka je gidan su Jinah neman aurenta, ba wata-wata aka tsaida maganar aure, domin mahaifin Dauda babban mutum ne da duk kauyukan dake yankin an sanshi.
Kwanci tashi asarar mai rai, yau an daura auren Jinah da Dauda. Farin cikin Jinah kasa boyuwa yayi, har wani zumudi take. Bayan ta fito daga wanka, Sarah ta kunce mata kitso, sake mata wani tayi saidai bai kai na farkon ba, dan irin simple din nan ne tayi mata, ta dunkule gashin duka, yayi mata tozo a tsakiyar kai. Zuwa karfe goma, gidan ya cika da mutane, makada da maraya sai cashewa ake. Kasancewar abin yazo da gaggawa babu abinda Sarah ta dinkawa Jinah, sai Wani leshi madaidaici da kuma wata doguwar riga tata da bata taba sakawa ba. Da leshin tayi yinin ranar, da dare kuma Sarah ta bata doguwar rigar ta saka. Rigar tayi mata bala'in kyau.
-Wow, gaskiya wannan riga ba dai kyau ba!
Jinah ta fada tana juyi dan ganin yanda rigar take a jikinta.
-Eh ta jima gareni, amma ban taba son sakata ba, gashi yanzu tayi rana.
Rungumeta Jinah tayi, dan nuna godiyarta. Zuwa karfe tara na dare kafin a dauki Jinah zuwa gidan su Dauda, Sarah ta zaunar da ita a daki dan yi mata huduba.
-Toh Sarah, yau Allah gashi yayi kin yi aure. Mijinki yayi min alkawarin babu wata matsala akan maganar budurci, kuma ina fatan hakan. Dama tsorona dangin mijinki. Dan Allah ki kasance mai yiwa mijinki biyayya, duk da nasan baki sonshi amma kuma babu wanda ya takuraki da sai kin aureshi dan haka dole kiyi masa biyayya. Kuma gashi kinyi sa'ar miji mai hankali, duk da hakan nima nayi tsammani a aurena. Dan Maza sai ana yi ana taka tsantsan dasu. Ina son dan Allah kiyi masa biyayya kamar yanda kike min, yi nayi, bari na bari. Sannan kiyi hankali da danginshi wasu zasu soki wasu kuma a'a, duk da haka ki zauna dasu lafiya. Ina son ki dauki Mahaifiyarshi da kishiyoyinta tamkar mahaifiyarki, mahaifinshi tamkar mahaifinki, 'ya'yan yan uwanshi tamkar 'ya'yanki. Sannan kuma kiyi hankali da yan uwanshi maza, dan kinsan namiji ba ruwanshi da ke sirika ce ko akasin haka, bare kuma ke ga yanda kike masha Allah. Ki tarairayi mijinki tamkar jinjiri... Tashi muje yanzu wata rayuwar na jiranki.
Kuka Jinah ta fashe dashi. Dan har ga Allah taji bata son rabuwa da Sarah to amma ya zata yi. Rakata Sarah tayi har gurin yan daukar amarya. Suka tafi ana guda, wasu na waka wasu na raye raye. Bayan sun kaita kowa ya watse banda Sarah da zata kwana a gidan dan ta zama shaida idan Jinah budurwa ce. Sanin Jinah ba budurwa bace yasa hankalinta ya kasa kwanciya, bata san wace dabara Dauda zai yi ba gobe.
Jinah ce zaune a tsakiyar gado ita kadai cikin wani babban daki. Ganin Dauda shuru babu alamun Dauda tayi niyyar kinshigidawa sai gashi ya shigo. A hankali ta mike zaune. Ajiye ledar hannunshi yayi tare da tambayarta gajiyar biki.
Bakar ledar da ya shigo da ita ya janyo ya bude, dakwalan kaji ne guda biyu. Tashi yayi ya dauko faranti ya fiddo kaza guda ya babbaleta sannan yayi mata bisimillah. Nokewa tayi, akan ita a koshe take. Da naci da lallashi yasa ta dan ci kadan. Tashi tayi ta wanke bakinta sannan ta dawo ta kwanta. Bayan shima ya gama ci, ya tattare yaje yayi brushing. Fira ya fara janta sama sama tana biye mashi, har bacci ya dauketa, shima ganin tayi bacci ya kwanta.
Da safe karar bugun kofa ne ya tashesu.
Dauda yaja dan guntun tsaki kafin yace
-Waye?
-Sarah ce!
Wani bugawa zuciyarshi tayi, dan shi sam ya manta da wani farin zanin gadon da ya kamata yan uwanshi su ga jinin budurcin Jinah, gashi bai yi tunanin yin wata dabara tun jiya da dare ba. Tsoro ne ya kamashi, dan bai san wane kallo mutane zasu yiwa Jinah ba. Karin bugun kofar ne ya karu, muryoyin biyu daga cikin aunties dinshi yaji. Cike da tashin hankali ya fara Safa da Marwa a cikin dakin yana tunanin mafita.
----------------------------
Dauda a cikin tsaka mai wuya, yanada kyau ku bashi shawarar abinda zai yi Fans ko dan ku ceci Jinah abar kaunarsa. π
Sai mun hadu a wani chapterπ€
My Watty : @El_Ashtar
π JINAH (Matar Aljani)π
by Malik al-Ashtar βοΈ
On wattpad π https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New β€οΈ Story
CHAPTER 6
Sintirin da Dauda ke yi a tsakiyan daki, kamar zakin da aka kulle a keji. Tunani kawai yake ko zai samu mafita. A jiya sam ya manta da alkawarin da yayi wa Sarah, dan shi hankalinsa ya karkata ne a zumudin son cikar mafarkinsa na ganin abar kaunarsa a gidansa.
-Me yake faruwa ne?
Jinah ta fada cikin muryar bacci. Tausayinta ne ya lullube Dauda, yayi mata irin kallon kiyi hakuri.
-Me yake faruwa ne Dauda, kayi magana?
Ta sake tambayarshi, amma wannan karon muryarta ram take ganin yanda mijin nata ke safa da marwa yasa dole baccin ya gudu.
-Sune a waje!
Ba sai yayi mata wani karin bayani ba, ta fahimci yan uwanshi ne dan Sarah tayi mata bayani. Amma ganin halin da mijin nata yake ciki ya tabbatar mata da ba wani shiri da yayi. Rawa jikinta ya fara, tsoro duk ya mamayeta. Toshe bakinta tayi kafin ta fashe da kuka. Ita ba kanta take tausayawa ba, Sarah dake waje, dan tasan tabbas sai tasha kunya ganin ita ce ta tsaya tayi sheda.
-A'a kar kiyi kuka dan Allah, zamu nemi mafita!
-Wace irin mafita?
Ta fada hankali a tashe. Tunani Dauda yayi na wani dan lokaci kafin yace
-Ko zakara nake samu na yanka sai mu zuba jinin a zanin gadon?
-Me? Hauka kake yi? Kana fa fita su zasu shigo kuma ma me zaka ce masu idan suka ganka da zakara?
Dafe kai yayi dan mafitar da kadai ya iya samu kenan.
-Me zai hana muyi abinda suke so?
Jinah ta fada tana kallon Dauda.
-Toh me hakan zai samar, ai a budurwa kadai ake samun abinda suke so.
Haka kowanensu yayi ta kawo shawarwari wanda ba zasu fiddasu ba. Ana cikin haka Dauda ya nufi wata yar karamar wuka da ya gani bisa dressing table ajiye.
-Me zaka yi da ita Dau...?
Kafin ta karasa tambayarsa, ya bude tafin hannunshi na hagu ya yanka. Zuwa yayi ya tara bisa zanin gadon a take jini ya fara zuba.
-Wayyo Allah...!
Cike da tsoro Jinah ta fada tana toshe bakinta da hannuwanta.
-Ke, ba fa wani abu bane, kawai dan karamin ciwo ne kuma bada jimawa ba zai warke.
Ya fada dan ya kwantar mata da hankali. Ganin jinin ya tsaya yasa ya goge hannunsa. Sannan yace mata ta kwanta, yaje ya bude kofa. Kusan kadashi aunties din nashi suka yi, shigowa dakin sukayi Sarah na biye dasu a baya fuska a dame.
-Ka wani garkame daki kai ga mai mata ko, baka son kowa ya shigo.
Daya daga cikin aunties din nashi ce ta fadi haka.
-Ai ba laifina bane, kusan kasheni fah tayi...
Dauda ya fada cikin rada yana wani murmushi.
-Kai jah cen ko kunyar mu baka ji...
Dariya suka yi, sannan suka karaso kusan amarya dake dunkule. Jan abu suka gani ga zanin gadon. Nan fa matan biyu suka hau guda. Daya daga cikinsu ce tayi kokarin daukar zanin gadon amma Dauda ya hana.
-Wannan kuma ba zai yiwu ba! Nine zan ajiyeshi, dan zai zama abin tunawa na karamcin da matata ta yimin, na bani wannan kyautar.
Jinah ji tayi kamar ta nutse tsabar kunya. Fita matan sukayi, suna guda suna fadawa sauran mutanen gidan Jinah budurwa ce. Nan fah gida ya dauka "Matar Dauda danya ce kamar tuffa sabuwa fil a leda"....
Abinda basu sani ba, Dauda yaki basu zanin ne, dan kar suje wani dan konkonto ya gano ba jinin budurci bane.
Ajiyar zuciya Sarah tayi. Ta shiga ta tarar da Jinah, Rungumeta tayi ba tare da tace wani abu ba. Haka suka kasance rungume da juna na tsawon dan lokaci kafin Sarah ta rada mata a kunne.
-Nasan baku yi wani abu ba Jinah, amma ki shirya lokaci na zuwa. Dan Allah kiyi kwanciyarki daki, kar ki fita su fahimci wani abu. Kuma idan kina bukatar wani abu ki zo ki ganni zan baki, idan kin tuna da rayuwarki ta baya ki zo ki fadamin. Ki kula da kanki, zan kasance kullum domin ki kuma zan yi kewarki.
Gyada mata kai kawai Jinah tayi, tana hawaye, dan itama tasan zata yi kewar Sarar. A haka Dauda yazo ya tarar dasu, ya dade yana mamakin irin wannan shakuwa tasu, gashi basu hada komai ba, amma Sarah tana jin Jinah tamkar 'yar uwarta ko kuma 'yar da ta haifa.
Mikewa Sarah tayi, kafin ta tafi ta kara jaddadawa Dauda alkawarin da yayi mata na kulawa da Jinah.
Bayan ya raka Sarah, ya dawo daki wajen matarshi. Babban daki ne da makeken gado a tsakiya, a gefe kuma akwai dressing table da wardrobe, sannan bathroom madaidaici. Dakin ya kawatu sosai, har da gidan ma baki daya. Saboda idan ka shigo cikinsa zaka dauka a birni kake, duk da yanzu kauyuka da dama ana ta samun cigaba amma wannan ya banbata da sauran, dan a kauyen babu irinsa.
Bayan wani dan lokaci, Jinah ta fara jiwo wani sauti, wata murya, ba yau ba ne na farko da ta fara jiwo wannan sautin. Amma wannan karon taji kamar sautin kusa yake ba kamar da ba da take jiwoshi daga nesa. Shurun da tayi tana sauraran sautin ne yasa Dauda ya tambayeta.
-Me yake faruwa?
-Daga ina wannan sautin yake fitowa?
-Wane sauti kike magana?
-Saurara kaji.
Saurarawa Dauda yayi kafin ya fahimci me take nufi.
-Wannan kiran sallah ne!
-Kiran Sallah? me hakan ke nufi? A da ina jiwo sautin ne daga nesa amma yanzu kamar...
-Eh anan cikin gidan ne, muryar Buraima ce, yayana. Hakan yana nuna alamar lokacin sallah yayi.
Ya fada cikin yanayin damuwa, dan ya fahimci matarshi babu abinda ta sani game da musulunci, wata kila yana daga cikin matsalar mantau da ta samu ne. Ya fahimci hakan ne tun ranar da ya fada mata yana sonta. Duk da irin wannan ba wani abin mamaki bane a kauyuka. A kauye mutane na amsa sunan musulmai ne amma basa yin komai da ya danganci musuluncin, suna yawan fadar za suyi idan sun tsufa, su a tunaninsu addinin ana yinsa ne idan aka cimma kabari wato tsufa, akasarinsu matasa ne suka yi imani da wannan da'awar. Shi kanshi Dauda a baya yana fadar hakan har zuwa lokacin da yaje Maradi wajen wani kawunsa, anan yaga yaro dan shekara 7 bakwai yana sallah abin gwanin ban sha'awa. A ranar yaji kunya ba kadan ba, tun daga ranar ya shiga neman ilimin addini. Anan ya gano muhimmanci da kuma wajibi na gudanar da addini. Yana dawowa kauyensu yasa mahaifinsa ya gina masallaci a cikin gidansu kuma da taimakon wani malami a kauyen yayi nasarar jawo hankalin yan gidansu da ma makota suna zuwa sallah. Duk da har yanzu ba wani sani gareshi sosai a cikin addinin ba, amma yasan hakkoki da kuma gujewa duk wani sabon Allah. Duk da yan kwanakin nan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 19