kaga wani ya biyo, to bako ne cikin rashin sani.
Ana cikin wannan halin ne, sai mutanen da ke kauyukan, nan biyu suka rinka kaura, sai dagatan kauyukan byu abin ya dame su, don sun ga mutanensu sun kusa kauracewa su bar kauyukan, sai su ka hadu suka yi shawara, suka zartar da cewar, kada kowa ya yi tafiya, sai cikin ayari dauke da makamai, tun da sarkin yawa dai ya fi sarkin karfi, ko Kurya zai bullo dai, sa gabza da shi, kuma suka ce duk wanda ya yi dalilin Kurya ya zo hannu za'a bashi lada mai-yawa, kuma a dauke ma sa biyan haraji, in kuma mace ce, to mijinta ko iyayenta sun huta da biyan kudin kasa muddin ransu.
Wata rana sai samarin wannan kauyen suka tafi yawon tsarince a Tafi-da-kwarinka, sai wani saurayi daga cikin samarin ya sami wata budurwa a kauyen, akawala kyakkyawa, sai ya ce, yana sonta, sai ta ce, ita ma tana sonsa, ya tambayeta sunanta, ta ce masa sunata Ayashe, ta tambayeshi nashi sunan, ya ce mata Mazgau. Ayashe ta yi dariya, ta ce, wannan suna naka bai dace da kai ba, don ga alama dai sunan ya cancanta da masu karfi ne, to, amma kamar nan taka, wa za ka iya mazgewa? Hala dai sunan kakanni ne wannan. Mazgau ya amsa mata ya ce, "I" na yarda, tunda an ce alamar karfi tana ga mai kiba, toamma ba a dukkan lokaci ba, wani sai ki gan shi, ki raina, amma in wuri ya yi wuri sai ya baki mamaki, ya yi maki ba zata." Mazgau ya yi sallama da budurwarsa, ya tambayeta randa za ta zo kauyensu Kurya, ta ce masa za ta rinka zuwa a duk ran kasuwar kauyensu, don cin kasuwa, in ta kwana ta ci kasuwar, ta juyo, suka yi sallama ya tafi.
Ayashe ta rike alkawarin da ta yi masa, a duk ranar kasuwar kauyensu Mazgau, sai ta je masa tsarince, to a duk lokacin da ta je, in suna tadi na hirar saurayi da budurwa, sai ta kan ce masa, Shin me ya sa ne kai baka cika zuwa kauyenmu ba, sai ni ke zuwa naku, ko don barawon nan ne dan fashi da ke tare mutane? Mazgau ya amsa mata cikin ruba ya ce, "Shi din me, ya ma isa, ji kika yi an ce maza mata ne? Ayashe ta yi murmushi ta ce masa, haba ai ko a matan ma suna kadai suka tara, amma ai akwai munam mata, akwai mataye, akwai kuma mata, kai har ma da mateku. Ashe baka da labarin wata matar ta f namiji jarunta ba ? Don kuwa ta kowace hanya ya bi, ta damashi ta shanye a nan, sai Mazgau ya ce don Allah rufe mana baki, namijin banza ba ? In dai ban da baki, da me mata suka fi maza ? Ayashe takan ce to a bar wa ranar gwaji wann sani, sai randa ta zo.
Ayashe ta ci gaba da zuwa tsarance wurin Mazgau, har dai ta gaji, shi da rana daya bai taba zuwa mata can kauyen nasu ba, tun dai daga ranar da suka sadu, ashe dai shi a ransa tsoron gamuwa da dan-fashin nan ya ke yi, kuri ne kawai ya ke yi wa Ayashe ta ce masa, ko Kurya ke hana shi zuwa kauyensu ganinta.
To, ana haka, har sai Ayashe ta soma shan jinin jikinta ta ce, ko baya sonta ne, shi ya sa baya zuwa, rannan data je sai ta sake tambayarsa dalilin da ke hana shi zuwa, sai ya kawo mata wadansu dalilai marasa karfi ya ce, su ne suka hana masa samun sukunin zuwa, daga nan sai Ayashe ta ce, haba Mazgau, ku maza dai kun raina hankalin mata, alhali kuwa ba ku san bakan mukan yi maku ba, don mu ga iya gudun ruwanku, kai dai kawai matsoraci ne, Kurya ke hana maka zuwa kauyenmu, ni kuwa in fada maka yau, ni fa ba matar matsoraci ce ba, daga yau in baka je ba, ni ma na daina zuwa maka. Mazgau ya murtuke fuska, ya ce haba ki dubi duk tuli na ki ce da ni matsoraci ? Yo, duk duniya akwai wanda nike tsoro, in barnda wanda ya haliccemu.
To, yau in za ki koma har gida zan kai ki, in kuma dawo komai dare, kuma ta nan wajen sarkakiyar itatuwan kukkokin, inda yake labewa, ta nan za mu bi mu shige. Ayashe ta ce masa, to, in dai kai namiji ne sosai, sai ka bari sai dare ya yi tsaka, kana mu bi, mu tafi...
-Wa ke son yaji karshen labarin? Sarah ta tambayesu. Dukansu suka amsa da "Ni!"
-Toh, kuyi addu'a Allah ya nuna mamu gobe i warhaka lafiya, domin sai gobe zan karasa maku labarin.
Cewar Sarah kafin ita da Abdul su kyalkyace da dariya.
-Dan Allah Sarah ki karasa mana.
Cewar Jinah da Nafisa.
-A'a sai fa gobe, kunga har yan tagwaye sunyi bacci.
-Dan Allah...
-Nace a'a.
-Ba kyau haka fa aunty Sarah.
-Kuyi kamar ni kuyi imagine sauran labarin.
Abdul ya fada yana cigaba da dariya.
Harara Jinah da yar uwar tashi suka watsa masa. Shi kuwa kamar sun kara tunzurashi ya cigaba da dariya.
Fally da shima yake wurin yana sauraron labarin ba tare da sauran na ganinshi ba, ya radawa Jinah a kunne :
-Kinga muje mu kwanta, tanada gaskiya, dare yayi.
Hakura tayi akan ta jira gobe a karasa mata labarin. Daukar daya daga cikin yan tagwaye tayi ta nufi makwancinta, itama Sarah ta dauki dayan ta wuce. Nafi kuwa sai da ta gama guna guninta Abdul yana mata dariya kafin taje ta kwanta.
-So nake na gabatar da kai a wajensu.
Jinah ta fada bayan sun koma daki ita da Fally.
-Kina tunanin zasu yarda da ke? Ba zasu yi maki kallon mahaukaciya ba?
-Wata kila, amma zan gwada, na gaji da boyewa idan zan maka magana.
Murmushi yayi kafin yace :
-Yanzu dai kiyi bacci, kinsan dare mahutar bawa ne, gobe sai muyi maganar.
-Shikenan, ka tashi lafiya bugun zuciyata.
-Ki tashi lafiya sanyin idaniyata.
-Ka tashi lafiya masoyina.
-Ki tashi lafiya rabin raina.
-Ka tashi lafiya numfashina.
-Ki tashi lafiya tauraruwata.
Haka suka cigaba da yi, har sai da bacci barawo yayi awon gaba da Jinah.
Washe gari kamar Kullum Sarah ce ta fara tashi, tayi alwala sannan ta tada sauran domin suyi sallar asuba. Bayan sun gama, ta shiga hada abin karin kumallo. Tarar da ita Jinah tayi, tana janye da yan tagwaye.
-Ina son in tayaki aikin nan, amma wadannan masu kamar danko suna manne dani sunki su sakeni.
Dariya Sarah tayi tare da cewa :
-To ba dole ba, irin dadewar da suka yi da kewarki.
-Idan muka sakeki zaki fadi kuma ba zaki bude idanu ba.
Cewar Ayu, ita kuma Aya ta kara da cewa :
-Eh, ai idan muka rikeki haka, ba zaki fadi ba bare ki sake rufe ido.
Sosai Jinah da Sarah ke dariya, sai dai kuma lokaci guda suka shanye dariyar ganin Aya na kokowar neman numfashi, kamar an shaketa.
-Aya! Aya! Me ya sameki? Yimin magana...'yata...Sarah...ta..
-Yi sauri ki bata ruwa!
Jinah bata kai ga yin koda taku guda ba taga 'yarta ta zube kasa sumamma. Ba tare da shakkar komai ba, ta kwalawa Fally kira ta hanyar kiran sunanshi. Lokaci guda suka zo shi da su Abdul.
-Me yake faruwa, innalillahi Aya! Cewar Nafisa.
-Fally, kayi wani abu, bata motsi!
Sauran kasa fahimtar ko da wa take magana suka yi, Abdul ne ya shiga rarrashinta tare da ce mata ta tashi suje asibiti.
-Me yasa kaki cewa komai? Kasan abinda ya sameta ne?
Cewar Jinah ba tare da ta damu da sauran basu ganin ko da wa take magana. Abdul fita yayi da gudu neman abun hawa.
-Mama ta mutu ne?
Cewar Ayu dake ta rizgar kuka, bayan yayi iya kokarinshi ganin ya tayar da yar uwar tashi.
-A'a na tabbatar bata mutu ba, kinga Jinah ki tashi mu tafi asibiti.
-Wai me kake nufi ne Fally, me yasa ba zaka yi komai ba?
-Kiyi hakuri ki yafe min Jinah. Sai a wannan karon Fally ya bude bakinsa.
-Hakurin me kake bani? Kayi wani abu mana!
Rungume diyarta tayi jikinta tana kuka. Ta kasa gane komai, amma tasan duk abinda Fally ya kasa to ko likitoci ma walaha ce zasu sha.
-Ki tashi kinji diyar mama... kada ki yiwa mama haka, dan Allah! Mama na sonki, kiyi magana Ayata.
Kasa jurewa Fally yayi, ya bace daga wurin. Bayan ya danyi nesa dasu, ya fashe da kuka yana mai dana sani da jin haushin kansa.
Kwanakin nan cike suke da jin dadi a gareshi ta yanda har ya manta meye silar samun farin cikin nashi.
Tunawa yayi da ranar, ranar da itace silar fadawar 'yarshi wannan halin. Ranar da itace yayi wannan mummunan zabin.
A lokacin da yake kwance kafin su samu lafiya shi da Jinah, yayi tunanin komai ya kare masa, rayuwarsa da ta Jinah, da kuma soyayyarsa... Babu wani sauran karfi da ya rage masa ta yanda ko idanu bai iya budewa. Wani abu yaji ya sokeshi, yayi tunanin ko mutuwa ce, amma sai yaji ana kiran sunansa :
-Fally ! Fally !
Haka yake ji ana fada cikin rada, sai da mai kiran nasa ya cigaba da maimaitawa kafin ya bude ido dakyar. Kara rufe idanunsa yayi ya sake budewa domin tabbatar da ko wacece a gabansa, ba kowa bace face Hindu. Murmushi tayi masa, daman tayi alkawarin zata dawo gashi yanzu ta cika.
Farawa tayi da fadin :
-Zan iya fitar da kai daga wannan halin.
Kokarin yin magana Fally yayi amma ya kasa.
Ganin haka ta kara da cewa :
-Nice kadai zan iya taimakonka.
Sake iya kokarinsa yayi ganin yayi magana, amma bakinsa ne kawai ya motsa, sauti bai fita har sai da Hindu ta tsikara masa wani abu kamar allura.
-Na..roke..ki...ki..taimake...ni.
Wata bahaguwar dariya tayi ta jin dadi, jin ana rokonta, tasan a duk lokacin da aka roketa, to zata samu abinda take nema a matsayin na fansa.
-Tabbas zan taimakeka, ina ce tsakanin aljanu akwai taimakekeniya?
Ta fada tana wani dage gira, sai dai Fally ya fahimci me take nufi, tana son ya bata wani abu a matsayin fansa.
-Kaga Fally, na sanka da wayo, kada kace min yanzu ka zama sakarai.
-Yan tagwaye.
-Yauwa ko kai fa?
-Ba..zan iya yin hakan ba.
-Kwarai kuwa zaka iya, kuma ai ba duka nake so, daya daga cikinsu nake so.
-Jinah ba zata taba yafe min ba.
-Ai zaku iya sake haihuwar wasu.
-Ke kinsan ba a cika samun irinsu su rayu ba.
-Ni wannan ba damuwata bace, bakuda lokaci mai yawa gara da sauri ka yanke abinda yafi.
-Ba zan iya yiwa 'ya'yana haka ba.
-Kana tunanin zasu yi tsawon rayuwa ne bayan mutuwarku?
-Me kike nufi?
-Suna rayuwa ne, dalilin alakar dake tsakaninka kai da Jinah, kuma wannan alakar ta rushe, kai da Jinah zaku mutu, bayan wasu kwanaki su ma su biku.
-Ni ban yarda ba, hakan ba zai yiwu ba.
-Yarda dani wannan ruwanka ne, amma ka sani zaka yi nadama.
Wata kila Hindu karya take masa, domin irinsu a shirye suke suyi komai domin cimma burinsu, ko ma dai ta yaya, Fally ya yarda da maganarta, amma kuma cikin zuciyarsa yana jin kada ya yarda da wannan matar. Sai dai sonshi da yaga ya dawo da Jinah yafi komai karfi. Rufe idanunsa yayi na wani lokaci hawaye masu zafi suka zubo masa kafin yace :
-Na amince.
Wani murmushin keta Hindu tayi sannan tace :
-Abinda ya dace kayi kenan, Jinah ba zata ki yafe maka ba.
-Me ya kamata nayi yanzu?
-Zaka jawo daya daga cikin yan tagwayen anan sai ka bashi wannan ruwan yasha. Ta fada tana miko masa wata yar karamar kwalba da wasu ruwa a ciki. Kasan yanda za'a yi yasha wannan ruwan ba tare da wata tilastawa ba. Zai daukeshi sa'o'i 48 kafin ya fara aiki a jikinsa.
-Daga nan kuma me zai faru?
-Dena hanzari, zaka gani.
Ta bashi amsa da wani makirin murmushi a fuskarta. Karawa tayi da cewa :
-Kuma sai kayi sauri, domin abinda nayi maka yanzu domin ya kara maka karfi ba mai dadewa bane, dole sai ka hanzarta kafin ya kare, ni zan tafi kuma idan kayi abinda nace maka ba zaka kara ganina ba.
-Tsaya ki tafi da wannan fatalwar taki.
Fally ya fada yana kallon Dauda.
-Daina kishi, Jinah kai kadai take so. Ta fada tana dariya.
-Bana son kara ganinshi, domin bansan me zanyi masa ba.
-Kar ka damu, zan tafi dashi kuma ba zai kara dawowa ba bare ya kawo maka cikas tsakaninka da Jinah.
Tunani Fally yake ko wannan itace mafita gareshi. Sai dai wata murya cikin kanshi na kara tabbatar mashi. "Ko ba komai Jinah zata dawo gareka, kuma komai zai koma kamar a ranarku ta farko, zata yafe maka domin zata fahimta."
Kamar yanda Hindu tace, karfin jikinsa ne ya fara janyewa a hankali. A take ya rufe idanunsa, tunanin Aya yayi ta yanda har ita taji babanta yana son ganinta. Cikin kankanin lokaci sai gata ta bayyana a wurin.
-Baba! Ka tashi? Nayi tunanin ko kuskure ne aka samu naji kana nemana. Yi hakuri na barka kai daya, muna tare da mama ne a asibiti yanzu muka dawo gida.
-Kar ki damu 'yata, ya mama taku take?
-Ba sauki, ko motsi ma bata yi.
Ta fada tana kokarin yin kuka.
-Kar kiyi kuka 'yata, komai zai wuce.
-Ta yaya? Bamu san meye abun yi ba yanzu. A ina zamu sa kanmu idan kun tafi? Kada ku tafi dan Allah!
-Zo nan. Kwantar da ita yayi bisa kirjinsa tare da kankameta, a hankali ya fara kuka. Fally har ya riga da yayi zabi, kuma Aya ya zaba ita zai sadaukar. Kuna tunanin to me yasa bai zabi Ayu ba ko? Fally yasan abun ba zai zo da sauki ba idan Ayu ne, dubban tambayoyi ne zai yi ta yi masa kuma zai ce sai ya karanci tunaninsa ko kuma ya tilastashi sai ya fada mashi gaskiya daga nan ya gano dalilin da yasa zai yi haka. Ita kuwa Aya tanada banbanci da dan uwanta.
-Karbi sha wannan!
Ya umarceta tare da miko mata kwalbar.
-Meye shi baba?
-Ki sha dan Allah.
Nan take Aya ta karanta tunanin mahaifin nata, sai dai bata kai ga yin wani nisa ba ganin cewa ya bata ne domin ya cecesu gaba daya, wannan ma kawai ya isheta ba sai ta kara sanin wani abu ba, domin ita ba mai son sanin sirrin wasu ba ce. Bata yi wata wata ba ta karba ta shanye. Hannu tasa ta goge hawayen da babanta ke zubarwa ba tare da tasan dalilinsu ba. Haka suka zauna shuru suna jiran sakamako.
Kamar walkiya Fally yaji wani karfi na shiga jikinsa, kowanne bangare na jikinsa na komawa kamar sabo.
Ihu Aya tayi tana kiran sunan babanta :
-Baba!
Sakamakon bace mata da yayi bata ganinsa, tana cikin wannan dube duben taji ya kira sunanta :
-Aya!
Babanta ta gani tsaye cikin koshin lafiya a bayanta, tsalle tayi ta rungumeshi tana murna.
-Ka...warke, baba ka warke!
Wata muryar suka ji a bayansu.
-Aya! Aya! Mama ta tashi! Ta...
Cak Ayu ya tsaya ganin mahaifinsu a tsaye. Da gudunsa ya fada jikinsa yana murna. Ita kuma Aya ta ruga domin ganin mahaifiyarsu....
Wata sabuwa kara da Jinah ta saki ita tayi sanadin dawo dashi daga tunanin da yake, da gudunsa ya karaso wurin, kasa daukarshi kafafuwansa suka yi, tsabar rudin da ya shiga.
Yanzu ba wai Aya bace kadai kwance da alamun babu rai, har da Ayu. Sai kuma Jinah da ta fara wani abu kamar zautatta. Nan fa, shi kanshi ya kasa fahimta.
--------------------------------------
G day readers, ina fata yanzu masu tambayar : "Ta yaya suka farfado ba tare da Aya ta samu cikon abu na uku ba?" da kuma "Wanne irin laifi ne Fally ya yiwa Jinah?" sun samu amsoshinsu?
Ganin comments dinku, ke sa na gane ko labarin yana shiga...😊
©Al_Ashtar
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story
CHAPTER 23
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
Fally ganin duka 'ya'yanshi kwance ba a hayyacinsu ba, ji yayi kasa ta kasa daukanshi, ya kasa yin numfashi da kyau, iskar shaka na neman ta gagareshi. Ya amince da wadda sam bai kamata ya yarda da ita ba. A cikin ransa yace ta yaya na yarda da wannan matar, matar da ita tayi sanadin mutuwar mahaifiyata. A yanzu ya gane irin kuskuren da ya tabka.
A daidai lokacin ne suka dunguma zuwa asibitin kauyen, Jinah bata daina kuka ba, duk tabi ta firgice, suna zuwa likitoci suka sanar dasu yaran suna numfashi.
Kallon Fally Jinah tayi anan ta tuna da hakurin da yake bata dazu.
-Fally me ka aikata ne?
Ta tambayeshi da alamun tuhuma.
-Ina son ki dawo gareni ne, mu sake raya soyayyar mu, ina son mu koma kamar da ne.
-Fally ka fada min, me ka aikata? Wannan karon muryar Jinah cike take da zafi da kuma rashin tsoro.
-Dole mu hakura da daya daga cikin su, Hindu....
-Innalillahi Fally! Me yasa ita? Ta yaya kayi hakan? Ka maido min da yarana Fally! Ba ruwana da koma me zaka yi, ni yarana kawai nake so!
Jinah ta fada kafin ta sake fashewa da wani sabon kukan. Kokarin rungumeta Fally yayi amma ta goce tareda furta :
-Ka tafi, kada ka kara sako kafar ka anan, ba tare da ka dawo min da yarana ba! Bana kaunar ganin ka kafin nan!
Bai yi wata-wata ba ya bace daga wurin, zuciyarshi na kuna ganin zai rasa daya daga cikin 'ya'yansa gashi kuma zai rasa wadda yake yaruwa domin ta, bayan duk wasu wahalhalu da yasha a baya da sadaukarwar da yayi. Yanke shawarar yaje yaga Hindu yayi, sai dai wata matsalar bai ma san ko ta yaya zai ganinta ba. Koma dai meye zai yi iya kokarinsa yaga ya nemota ta karya abinda tayi. To kuma idan yayi hakan su zasu rayu ne? Tambayar da yayi wa kanshi kenan. Koma dai meye zai je ya nemi Hindu ta san abinda zata yi.
Jinah ce zaune kan benci dake madakatar jiran likita kamar jaririn da yake jiran a haifeshi haka take. Taci kuka iya kuka ta yanda har idanun nata sun kafe babu ko digon hawaye. Duk dakikar da zata shude,sai taji wani abu ya soki zuciyarta.
-Zasu tashi.
Abinda Sarah da su Abdul ke ta maimaita mata kenan, domin likitoci sun tabbatar masu da yan biyu ba mutuwa suka yi ba, sun fita hayyacinsu ne, kuma likitocin na sa ran cetonsu. Ita kuwa Jinah tasan ba zasu iya yin komai ba domin ba kamar kowanne irin ciwo bane.
Kamar an tsikareta ta mike tare da fita daga asibitin. Da gudu Sarah tabi bayanta, ta tsayar da ita.
-Ina zaki je ne?
-Kar ki damu Sarah, yanzu na dawo, kawai ina son na samu natsuwa ne.
-Bari na rakaki.
-A'a dan Allah, ni kadai nake son tafiya.
-Amma...
-Dan Allah...
-Shikenan kar ki dade.
Sarah na nan tsaye har Jinah ta soma yin nisa, bata so ta barta ta tafi ba, amma kuma tana ganin hakan shi zai sa Jinah ta samu dan sukuni.
Jinah tafiya take yi ba tare da tasan inda zata je ba, har wani dishi-dishi take gani tsabar wahala. Ganin jiri na dibanta ta samu wani gindin bishiyar kuka ta zauna. Hada kai da gwiwa tayi. Ta kai tsawon wasu mintuna a haka, kafin ta dago kai taga wani a gabanta. Da ganinshi ta tabbatarwa kanta aljani ne. Kura masa ido tayi, shi kuma sai kallonta yake da mamaki dan ganin ko motsawa bata yi ba.
-Kina ganina ne?
Aljanin ya tambayeta, cike da mamakin ganin yanda Jinah ke kallonsa da alama tana ganinshi ne.
-Ta yaya kike iya ganina, alhali ke bil'adama ce?
Jinah bata ce masa kala ba.
-Gashi kuma kinada kyau irin na aljanu, zan so naji labarinki.
Har yanzu dai bata amsa mashi ba.
-Zan iya sanin sunanki?
Sai da tayi kamar ba zata amsa mashi ba, kafin tace :
-Jinah!
-Eh na san kin san ni aljani ne kuma da mamaki yanda baki ji tsorona ba, kuma nasan ke ba jinsin mu bace, sunanki nake tambaya.
-Sunana Jinah!
-Abin dariya, na taba sanin wata bil'adama mai irin wannan sunan, tana rayuwa ne cikin aljanu, Jinah a cikin "jinni"...
Shuru yayi yana kallonta kafin yace :
-Jinah! Jinah ta Fally kece?
Fiddo ido Jinah tayi, tana tunanin shi kuwa wannan ina ya santa. Kafin ta karasa tunaninta taji ya rungumeta.
-Jinah nine, INFA! Dan Narama da Gausu! Kin tuna ni?
-Infa! Kai ne?
Jinah ta fada da alamun ta ganeshi, murna ce fal cikin ranta da kuma hawayen jin dadin ganin wanda ta dade bata gani ba.
-Amma me kike yi anan? Ke kadai kuma ma ina Fally, da iyayenku? Yaya suke? Me ya faru duk tsayin wannan lokacin?
-Abubuwa da dama sun faru Infa.
Jinah ta fada yanayin fuskarta ya sauya zuwa damuwa.
-Ina jinki bani labari.
Ta fara da cewa :
-Iyayen mu sun mutu.
-Mene? yaushe? Ta yaya? Shi kuma Fally yana ina?
Tambayarshi ta karshe tasa fuskar Jinah tayi ja na tsana jin ya tuna mata da Fally.
-Shi, ban kaunar jin sunanshi, idan har bai dawo mun da 'ya'yana ba...
-'Ya'yanki? Yaya ne wannan labarin yake?...
Labarin komai Jinah ta bashi, abinda ya faru tun daga tafiyar Infa har zuwa yanzu da 'ya'yanta suke cikin wannan halin. Shi kuwa tun lokacin da yaji ta ambaci sunan Hindu, zuciyarsa ke tafarfasa na bakin ciki, tsana, da kuma son daukar fansa a gurin me wannan sunan. Shi ma Infa yana daga cikin wanda Hindu ta zalunta, lokacin da yake karami, shi ma yana rayuwa a cikin kauye daya da su Jinah, shine yaro daya bayan Fally mai son Jinah, yana shige mata fada idan wasu yaran aljanun suna son cutar da ita. Haka suke shakikan abokai, har ana masu lakabi da yan uku, duk da ya girmema Fally da Jinah na shekaru biyar. Komai yana tafiyar masa daidai har wata rana da ya dawo gida ya tarar iyayenshi da kanwarshi sun mutu, anan yaji ga makotansu cewar aikin Hindu ne, kuma idan shima bai gudu ba zata dawo ta hada dashi. Nan da taimakon mahaifiyar Fally ya gudu. Kuma har yanzu bai san dalilin da yasa Hindu ta kashe masa dangi ba.
Yanzu da ya girma, ya dawo da niyyar daukar fansa, duk da cikin ranshi yasan ba zai iya galaba a kanta ba, amma duk da haka zai yi iya kokarinsa.
-gaskiya nayi mamaki sosai, na kasa yarda, wai yan biyu kuma ruwa biyu. Kuma gaskiya Fally bai kyauta ba, amma kuma...
-A'a Infa, kar ma ka fara nemar masa wata afuwa!
-Ina tunanin a wannan karon, mu zamu yi nasara!
cewar Infa cike da jin dadi.
-Ban gane ba, akan me kake magana?
-Yaushe yan biyu suka shiga wannan halin?
-Yau da safe.
-Akwai sa ran ceto yaranki!
-Da gaske kake? Toh ta yaya?
-Kin tuna babana yana yawan son bamu labarin kakanin mu?
-Eh.
-Toh wani lokacin ko daga ni sai shi ne, yana bani labarin sirrukan duniyarmu da abubuwa da dama. Kuma har da labarin yan biyu ruwa biyu yana bani.
-Me yace?
-Abubuwa da yawa, amma ki sani, zamu iya ceto yaranki a yanzu, domin ita ma Hindu tana cikin irin halin da suke, domin haka aikin yake idan tana son ta janye duk wani karfi nasu.
Idan har aikin ya ida, yan biyu zasu mutu ita kuma karfinta zai karu. Sa'o'i sha biyu suka rage mana mu nemo Hindu mu kasheta domin a yanzu ne damarmu take ta yanda ba zata iya kare kanta ba.
Jinah taji dadi sosai da Infa yazo mata da hanyar ceton 'ya'yanta, sai dai matsalar a yanzu basu san inda zasu nemo Hindu ba, nemo aljani a cikin duniyar nan ba abu ne mai wahala, amma yafi ga irin su Hindu, domin sun san a halin yanzu sai da ta boye kanta kafin ta shiga wannan halin, dan gudun kar wani ya cutar da ita.
-Ya kamata mu nemo inda take.
Cewar Jinah.
-Nafi ki son mu nemota ko dan ta girbe abinda ta shuka na kashe min iyaye kuma ta fada min dalili.
-Bamu da lokacin bata lokaci!
-Mu fara daga wajenku inda taje cen wajen Fally.
-Toh, amma mu fara biyawa asibiti domin na sanar da dangina.
Shuru tayi kafin ta sake maimaitawa "dangina". Wannan ne karon farko da ta fadi hakan da nufin cewa Sarah da su Abdul.
Suna zuwa asibitin ta sanar da Sarah zata tafi wani waje, kuma ba zata dade ba zata dawo. Nan suka fita ita da Infa neman Hindu.
Sun bincika kasa da sama, suna yi suna tambayar duk wani aljani da suka hadu dashi, wasu ma basu amsa masu idan suka ji sun ambaci sunan Hindu. Kuma babu wani da yake da niyyar taimakonsu, amma duk da haka basu karaya ba.
Abin tashin hankalin garesu, yau ce rana ta karshe da aikin Hindu zai kammala. Sa'o'i kadan ne suka rage.
-Kiyi hakuri Jinah!
Cewar Infa.
-Koda dakiku ne suka rage mana,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 19