Share this page
nayi farin cikin ganinka a raye, na tsorata sosai da na gano, yana wasa da tunanin mu ne. Cewar Aya kafin ta kara rungume baban nasu. Suna komawa gida, Fally yayi matukar mamaki da takaicin ganin Dauda, a ranar haka ya wuni sukuku. A ranshi ya raya, dole yayi wani abu ganin ya raba Jinah da wannan mutumin, zai bi ko ta halin yaya ganin Jinah ta tuna dashi da kuma soyayyarsu. Bayan yan tagwaye sun bashi labarin ta yanda suka gane makircin Zumana, turasu yayi su tambayi Dauda ko ya taba jin irin makamancin labarinsa a wurin kawunshi; dan Adam da ya kasa tuna soyayyarshi da aljani. Dauda amsa masu yayi da eh, kuma har da ma tagomashin sanin yanda ake dawo da tunanin. Ya basu labarin komai da yayi masu karyar kawunsa ya fada mashi. Ba tare da wani tunani ba, Fally ya yarda da maganganun Dauda, har ya yanke shawarar da marecen nan zai aikata abinda ya fada masa. A bangaren Sarah, sauyi sosai ta gani ga Abdul, sai dai tayi tunanin wata kila saboda Jinah bata bar gidan bane ya dan dameshi. Yanke shawarar zuwa ta fahimtar dashi tayi, daman kuma sosai tayi kewarshi, da dadewa kenan rabon da ta jita manne a jikinsa, da wannan tunanin mai cike da tsantsar kunya ta karasa dakinsa. Tarar dashi tayi zaune, ya kurawa bango ido, hankalinsa na wani gu, a hankali ta rugumoshi ta baya, yayi firgigit ya mike. -Subhanallahi, ah ke ce? Wallahi har kin tsorata ni. Abdul ya fada cike da tsoro, ba tare da ya fahimci abinda Sarah take nufi ba. Sai dai lokacin da ta matso kusa dashi ta dora labbanta akan nashi, fiddo ido yayi waje kamar zasu bar cikin kurminsu. -Meye...haka...saboda.. Tsabar firgici ya kasa hada kalaman da zai fada. -Na san ka damu ne saboda ta tsaya, amma kar ka damu ba zata kara takuraka ba, zamu iya yin soyayyarmu babu shamaki. -Baki da hankali ne? Fita daga dakina yanzu yanzu, kin manta ke matar babana ce? -Daman nasan wata rana zaka ce min haka domin ba sona kake ba, yanzu na tabbatar da wawancina da na yarda da kai. -Ki fita dan Allah! Kallonsa take cike da damuwa da da na sani, ba tare da ta hana hawaye wanke fuskarta ba ta fice daga dakin. Da na sani fal a ranta, tana jinta tamkar hankicin da aka yi anfani da shi aka jefar. Abinda bata sani ba, Abdul ba zai iya tuna komai ba da ya faru tsakanin ita da shi, ko kuma in ce tsakanin ita da gangar jikinsa. Shi kanshi ya kasa fahimtar komai, yana jinsa kamar wanda ya samu tabin kwakwalwa na wani dan lokaci ko kuma wanda ya dauki kwanaki masu tsawo yana bacci. Tashi yayi da niyyar zuwa wajen kanwarsa, domin yana son suyi magana. Tarar da ita yayi tare da Jinah, ya nemi guri kusa dasu ya zauna. Kallon da yaga suna binshi dashi yake jin kamar ya aikata wani abu da shi ma bai san meye ba. -Me yake faruwa? Irin wannan kallo kamar na aikata wani mummunan abu? -Tambaya ma kake? Mtssww. Cewar kanwarshi. -Me nayi? Ganin basuda niyyar bashi amsa, ya cigaba da cewa: -Ko ma dai meye na aikata, ina neman afuwarku har cikin zuciyata, ina sonku kuma kun sani, idan na cutar daku to ba da sanina bane. Ba tare da ya jira jin ta bakin daya daga cikinsu ba, ya bar wurin, tunaninsa a wannan lokacin kawai ya koma Nigeria zai fi, ya kasa fahimtar komai a cikin wannan rayuwar, tunani yake ma idan ya zauna da wanne irin ido zai kalli matar babanshi, bordel rungumarsa fa tayi. Da marece, ya fara tattara kayansa, ya kuma ce da yar uwarshi ita ma ta hada nata. -Dan Allah Abdul, mu kara ko sati ne. Kar muyi irin wannan tafiyar ta farat daya. -A'a. Ya kamata mu tafi, kuma kinga an kusa komawa school. -Babu baba babu Mama a cen, ko ba komai nan munada yan uwa, dan haka nidai zan zauna anan. Ta fada da yar hayaniya. -Dan Allah Abdul, ku kara wasu kwanaki mana. Cewar Jinah da ta shigo. -To naji naji, kar ki wage mana wannan bakin naki. Cewar Abdul ga kanwarsa da yaga tana shirin fara kuka, tsalle tayi ta kankameshi tana murna. -Yauwa yayana na kaina, irin wanda ba kowacce kanwa ke da irinshi ba. -Eh ai na jima da sanin haka. -Banda dai girman kai. -Ai ba sai nayi ba, tuni kambun sauratana ya riga da ya mayar min shi katoto. Dariya su duka suka yi, dukansu ukun suna cikin farin ciki, matan a yanzu suka tabbatar da Abdul din da suka sani a baya ya dawo, mai raha da barkwanci. Zuwan Yan tagwaye yasa Jinah ta bar Abdul da Nafi, taja yaranta da niyyar zuwa su kwanta. Bayan ta kwantar da yaran, ta nufi hanyar zuwa wajen mijinta dake daki, sai dai akan hanyar taci karo da Sarah zaune ita kadai, ta buga uban tagumi, da yanayin damuwa a fuskarta, taso yi mata magana amma ta fasa. -Me yasa kazo ka tsabbace anan? Jinah ta tambayi mijinta. -Ba komai kawai yar gajiya ce. Dauda ya bata amsa, da murmushin tabbatarwa akan labbansa. Canja kaya Jinah tayi sannan ta kwanta kusa da mijinta, taga sauyi sosai a tattare dashi, amma hakan bai dameta ba ko ba komai yana kusa da ita. Bata jima ba tana tunani bacci yayi awon gaba da ita, wani mafarki ta fara yi mai firgitarwa. -A'a, a'a! Kar ka tabani a'aaa! Wayyooh, ka sakeni, dan Allah ka daina. Ihu da take yi kenan, a tsorace take, na ganin wannan mutumin da yake yawan tsoratata yayi mata fyade a cikin mafarkin, kuka take yi iya karfinta amma babu mai iya jinta. Ta kai har ta jika zanin gadon da zufar da take yi. Firgigit tayi ta farka, ganin duk halin da take ciki da murkususun da tayi ta yi bai iya tada Dauda daga nauyayyen baccin da yake ba, yasa ta gama kai da gwiwa, haka ta kasance har wayewar gari. Wannan tsoron kin sakinta yayi tsawon ranar. Wani lokacin ma sai ta dinga jin ana mata rada a kunne ba tare da ganin mai yi ba, wani lokacin kuma mutum take gani yana bayyanar mata yana bacewa akan idonta. Ayyanawa tayi a ranta idan haka ta cigaba da kasancewa to zata haukace. (....) -Fada min yaya plan namu yake tafiya? -Komai yana tafiya daidai! Zumana ya dade da fita daga filin tseren, shi kuwa wannan sakaran Fally tuni ya fada tarkona. Hahahah, bai san cewa yana haka kabarinsa bane. -Hahahahahaha!, ina alfahari da kaina! Zaka iya komawa, ka cigaba da aikinka. -Kar ki damu shugaba, wadannan tagwayen da ma duk wani karfinsu nan da ba da jimawa ba zasu zama mallakinmu. -A'a! Mallakina! Mallakina dai! Na kagu naga cikar burina!!!!!!!! *****************************""**** After un long moment! J'suis enfin de retour mes vrais 🤗 Ya hakurin jira? Fatan dai ba'a yi fushi da yawa dani ba? ©El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 18 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp Cikin kankanin lokaci, Jinah duk tabi ta lalace, ko ina a jikinta kasusuwa ake gani, rama ta ban tausayi tayi ba tare da tasan wace irin cuta ke damunta ba, eh cuta mana me zuwa ba tare da sanarwa ba ko dalili, abar da kullum muke takatsantsan wajen ganin mun kare kan mu daga kamuwa da ita. Cuta bata bamu zabi. Muna iya wayar gari lafiya amma mu kwanta da ciwo, mu dinga jin wani yanayi da zafi da ba zamu iya misultashi ba wanda hakan zai sa muje asibiti domin a fada mana abinda ke damunmu. Sai dai ita tata cutar Jinah, har likitocin sun kasa ganota, sakamakon ganin abu yaki ci yaki cinyewa Sarah ta dauketa zuwa asibiti sedai an kasa gane sahihin abinda ke damunta. Gashi dai a jikinta da ka gani kasan batada lafiya, amma kuma sanin ciwon nata ya gagara. Ganin haka likitocin suka bata shawarar kawai taje birni domin a kara dubata amma taki a cewarta idan har likitoci sun kasa gane abinda ke damunta wata kila ciwo ne mai wucewa, ba babba ba. Sedai kuma kullum ciwon nata kara ta'azzara yake, wannan ma ne yayi sanadin jinkirin tafiyar su Abdul. Halin da take ciki ya tayarwa da kowa hankali ba kamar ma yan tagwaye da suka kasa yin komai har da karfin tsafinsu, a tsorace suke sosai. -Me kake tunanin shine sanadin rashin lafiyar mama? Aya ta tambayi dan uwanta. -Ina tunanin baba ne! -Me? Hakan ba zai yiwu ba, baka ga shima ya damu sosai ba, kuma shima yana iya kokarinshi ganin Mama ta warke. -Eh, amma idan fa shine sila ba tare da ya sani ba, baki lura ba hakan ta fara faruwa tun lokacin da ya fara abinda tonton Dauda ya fada mashi zai yi domin mama ta tuna dashi. Shuru yar uwar tashi tayi alamar tunani kafin tace: -Kuma fa kanada gaskiya. -Ya kamata muyi masa magana. -hakan za'a yi. Neman mahaifin nasu suka shiga amma basu ganshi ba, yanke shawara su jirashi suka yi. Kafin nan suka wuce wajen mahaifiyarsu. -Nan da ba da jimawa ba zaki warke mama. Cewar Aya. -Nayi kewar fadanki. Cewar Ayu. -Karya ne, Mama bata yi mana fada. -Eh gaskiya ne, Tanti Sarah ce ke yi mana fada. -Amma ita mama idan muka yi laifi, kawai zata ce : a'a rabin raina, ba kyau abinda kuke yi, ku daina kunji kuma kar ku kara sakewa. -Sannan sai ta kara da ina sonku sosai, kyawawan diyana. -Kuma abinda zamu yi matsayin hukunci, shine mu rungumeta. -Kuma ba zamu saketa ba har sai taso hakan. -Muna sonki mamamu ! Duk da halin da jinah take ciki, sai da ta jawosu jikinta ta kankamesu, sosai kalamansu suka tabata ta yadda hawaye suka kasa tsaya mata. Zuwa cen kuma ta fashe da kuka, sedai kukan nata kuma da nashi dalili, ba komai ba ta tuna face yanzu idan ta mutu a wanne hali zata bar 'ya'yanta, duk da ta tuna hakan hankalinta na matukar tashi ganin irin shakuwar dake tsakaninsu. Jinah bata daina kuka ba har lokacin da Dauda ya shigo dakin. Tagwayen fita suka yi suka barta daga ita sai mijinta. -Ni fa wannan koke koken naki sun fara isata! Cewar Dauda a fusace, idanu Jinah ta fiddo cike da mamaki. -Gaskiya na fara gajiya. -Me.. Me yake damunka? Tsawa fa kake min? Jinah ta fada tare da kara fashewa da kuka, ko sau daya mijinta bai taba yi mata haka ba. -Kiyi hakuri, ki yafe min, ba a son raina ba, ki yafe min dan Allah. Kinsan ina sonki fiye da komai. Mamaki ya kara dabaibaye Jinah ganin yanda ya koma yana bata hakuri. Zuwa cen Dauda kamar an bangajeshi yayi baya ya bugu da bango, yanayin fuskarshi ya fara canjawa, da ta nuna suffar mugun mutum sai kuma ta sauya zuwa ta nutsatsen mutum. Jinah bata ankara ba taji Dauda ya shaketa kamar zai kasheta, kokowar kwatar numfashi ta shiga yi, zuwa cen kuma ya saketa sannan ya rugumeta yana kissing dinta. Sosai Jinah ta tsorata da lamarin Dauda. Mikewa Dauda yayi, sannan ya fara buga kanshi jikin bango yana fadin : -Ka mutu ! Eh amma kuma gangar jikina ce ! Ni kuma ruhina ne ! Ba zan barka ka cutar da ita ba ! Ni ban damu da ita ba !... Juyawa Dauda yayi wajen Jinah sannan ya shiga juya kanshi hagu da dama, kuma duk lokacin da yayi hakan sai kamannin fuskarsa sun canja daga ta salihi zuwa ta mugu. Daga karshe dai ta muguntar ce tayi nasarar tsayawa, cike da mugunta ya dunfari Jinah kafin ya nausa mata wani naushin da yayi sanadin sumanta. A wancen ranar Aljana Hindu da mataimakinta makabarta suka je, sunje da niyyar kawo karshen rayuwar wannan aljanin ne domin taso da Dauda. Tayi anfani da ruhin aljanin a gangar jikin Dauda. Hakan yasa aljanin ya koma mutum ba tare da ya manta da tunaninsa na aljanu ba. Hindu tasan idan ta aika aljanin directly, tagwayen zasu iya halakashi. Amma yanzu wannan hadin da tayi shine kadai hanyar da zata iya samun cikar burinta ba tare da wata matsala ba, sedai kuma wata barazana da zasu fuskanta a yanzu shine, tsananin soyayyar da Dauda yake wa Jinah, da kuma zaman gangar jikinsa a kusa da ita, yasa kwalwar asalin Dauda ta fara aiki, a hankali a hankali yana dawowa Dauda. Gangar jikin ta fara kokowa da ruhin, da ganin ta hanashi yin duk wani abu da bai dace ba. A yanzu haka dai Aljanin ne ya dauki control din jikin ta yanda har ya sumar da Jinah, yanke shawarar zuwa ya samu uwar gijiyarsa yayi sai kuma ya tuna da yanda Hindu take ba zata yi jinkirin kasheshi ba domin bata son duk wani abu da zaya kawo mata cikas a cikar burinta. Bayan wasu lokuta Jinah ta farfado taga Dauda kwance a gefenta yana ta sharar bacci, a tunaninta mafarki tayi, ajiyar tayi tare da cewa : wannan wane irin mummunan mafarki ne nayi. (.....) Sarah ce ta shigo gidan a kasalance, Nafisa da gudunta tazo ta taimaka mata ta zauna kan tabarmar dake shinfide a tsakar gidan, dan kishigidawa Sarah tayi. -A ina kika je aunty Sarah ina nan duk na damu ? Nafisa ta fada cike da nuna kulawa. Tsantsar nuna kulawar da Sarah ke yi masu yasa a kullum take kara sonta, kuma tana damuwa idan ta ganta cikin wani hali. -Ganin likitoci sun kasa yin komai game da rashin lafiyar Jinah, shine na tafi neman mai maganin gargajiya. Sarah ta fada da muryar damuwa. -Kuma shine zaki tafi cikin wannan ranar, kema bakya tsoron wata rashin lafiyar ta kamaki ? Abdul ne ya karaso wajensu, ba tare da ya yarda ya hada ido da matar babanshi ba. Duk da abinda ke faruwa tsakaninshi da ita ba zai so ganinta cikin wani hali ba. Yar uwar tashi ce tayi masa bayanin inda Sarah taje, shiga yayi cikin kayansa ya dauko magani doliprane, da taimakon Nafisa Sarah tasha maganin, kafin wani dan lokaci taje tayi wanka, sannan Nafisa ta danyi mata massage kafin ta kyaleta tayi bacci. Haka gidan ya kasance tsit, kowa yayi bacci banda yan tagwaye dake jiran dawowar babansu. Bayan tsawon wasu awanni sai gashi ya dawo. -Ina ka tafi baba ? -Ina tunanin ai zaku iya sani. -Ai ka hanamu anfani da tsafinmu ga mutanen dake cikin gidan nan, idan ba ya zama dole ba. -Hakane. Yau tsawon watanni kenan Fally yake son ko ta yaya yaga ya dawo da matarshi, yanzu kuma da ya samu hanyar ance masa duk cikin aikin ne matar take fama da wannan ciwon. -Idan mama ta cigaba da rashin lafiya, ba zan taba yafe maka ba. Ayu ke fadawa mahaifinsu da alamar kashedi, kafin ya bar wajen yar uwar ta rufa masa baya. Shi Fally a tunaninsa ciwon nata na wani dan lokaci ne daga nan komai zai koma masu daidai. Abinda Dauda yace masa yayi shine : Sake yin wani alkwarin aure tsakaninsa da Jinah kamar a baya «Wata yar karamar wuka Fally ya dauko tareda yanka babban yatsanshi, itama haka Jinah tayi, sannnan suka hada yankakkakun yatsun nasu gu daya inda jinin nasu ya garwaya. Bayan sunyi hakan sannan Fally ya dauko wata kwarya mai dauke da wasu koren ruwa, ya fara sha sannan ya ba Jinah itama tasha. Jinah cire zanin dake daure kugunta tayi, sannan ta kara cire wanda yake daure a kirjinta. Kwantawa tayi akan wani jan kyalle dake shinfide a gurin babu komai a jikinta. Shima Fally dama wani gajeren wando kadai a jikinshi ya fiddashi, sannan ya zuba wasu ruwa a jikin Jinah, bayan wani dan lokaci sai ga wani maciji ya bayanna a hannunshi, sakin wannan maciji yayi yanata bin jikin Jinah, ita kuwa ko a jikinta, dan ta san wannan yana daga cikin siddabarun alkawarin nasu, kuma daman ta iya sarrafa dabbobi kamar sauran aljanu, kuma kasancewar kyawun dake gareta irin na aljanu yasa tana iya yin wasu abubuwa sosai wanda cikakken dan mutum ba zai iya ba. Macijin ya bace bayan wasu yan lokuta. Bayan wannan, cikin farin ciki Fally suka raya wannan rana kamar kowanne ango da amarya. Hakan zai nuna sun dau alkawarin zama na har abada a tare.» Wannan shine abinda ya faru ranar aurensu, ranar alkawarinsu. Sai dai yanzu da yake son ya sake yin haka a cikin mafarkin Jinah, komai sai ya jagule, domin ita Jinah, ta kasa fahimtar komai, ta tsorata da ganin wannan mutumin yana tursasata shan wani abu da bata san ko meye ba, da kuma yanda taga maciji na tafiya a jikinta, kuma ta firgita sosai na ganin mutumin nan ta karfi yana yi mata fyade. Komai da ya kamata suyi cikin soyayya ita gani take ta karfi ne yake mata. Shi kuma ganin yake komai zai daidaita daga baya zasu zamo a tare kuma hakan shine muradinsa. Sam ya kasa bude ido ya farka ya kwaci kansa daga tarkon aka yi masa, ya gane wannan ba soyayya bace yake nunawa Jinah, kawai yana cutar da ita ne. Dadi da kari ma, kusan kullum sai ya bayyana akan idanunta sannan kuma ya bace, hakan ma bai san dab yake da haukatata ba. A zahirance Fally bai san hakikanin abinda yake kokarin yi ba, bai san yana sanya rayuwarsa, ta Jinah da kuma ta 'ya'yansa a hadari bane. Yayi nisan da ba zai iya gane abinda Dauda ya fada masa zai kaishi ga rasa duk wani farin ciki nasa, kuma a hakan zai cigaba ba tare da yasan wadda yafi tsana a duniya wato Aljana Hindu yake taimakawa da kokarin cika mata burinta ba. ---------------------------------------------- Domin sanin abinda zai biyo baya kan abinda Fally yayi. Mu hade a Chapter na gaba. Fatan wannan chapter ta kayatar daku ? Zan yi farin cikin ganin ra'ayinku. Sannan ina bada hakuri akan kuskuren typing. *©El_Ashtar* Allez à la prochaine Readers 💪 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 19 ~*Wilaya Writers association of Nigeria*~ (Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦 Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp A wurin mutane soyayya ba wani dogon nutsatsen kogi bane a'a, a wurin mutane soyayya dogon kogi ne mai cike da igiyoyin ruwa masu saka kogin yayi sama yayi kasa. Haka a wurin aljanu, banbancin ba mai yawa bane, sai dai akwai muhimmanci mai tsauri a soyayyarsu, suna tsananin yarda akan wanda suke so, ta yanda zasu iya sadaukar da komai akan wanda suke so, nuna kulawa da muntuntawa da gujewa duk wani abu da zai cutar dashi, wannan kenan a cikin soyayyar aljanu. Amma kuma idan aka samu akasin haka daya daga cikin masoyan wani ya cutar da dayan, alakar dake tsakaninsu zata wargaje kuma dukansu biyun da wanda aka cutar da wanda ya cutar kowanne zai biya bisa laifin dan uwan nasa. Hukuncin kuwa ba komai bane face mutuwa. Abinda Fally yayi kenan, bayan yayi magana da 'ya'yanshi, ya gano rashin lafiyar Jinah shine sila amma sai yace ai abu ne mai kyau domin dan ya gyara gobenshi ne. Bai san abinda yake aikatawa ba, a hankali yana wargaza muhimmiyar alakar dake tsakaninshi da Jinah ne kuma idan har ya cigaba dukansu zasu rasa rayukansu. Hindu tana sane da hakan, kuma wannan shine plan dinta, da kanta ta tsara komai daki-daki, kuma abinda zaifi kayatar da ita shine yayin da Fally da Jinah suka mutu haka zai sa yan tagwaye suyi rauni, ta yanda ba zasu iya anfani da karfinsu ba. Daga nan zata sa a kamosu ta barka kirjinsu ta ciro zuciyoyinsu ta cinyesu danyu. Daga wannan lokaci babu wanda zai iya kwatanta karfinsa da nata, karfinta zai karu, kuma zai mayar da ita gagara badau ki mutuwa (Immortelle). (...........) A gidansu Sarah, alfigir ya keto, duka mutanen gidan idanunsu biyu tun awowi 3 da suka shude, suna kan Jinah, sakamakon farkawa da tayi da kara, ciwo mai tsanani da kuma sambatu, wanda yayi sanadin taso Sarah, diyan mijinta da kuma yan tagwaye. Kowannensu cikin tashin hankali yake, basu san me zasu yi ba, su kaita likita? Sun riga da sun san abinda likitoci zasu ce. Sarah bayan tayi iya kokarinta na ganin ta rarrashi Jinah. Da gudunta taje ta jiko ganyen maganin da wani mai maganin gargajiya ya bata, lokacin da ta bata ta sha, Aya da dan uwanta ta dalilin karfinsu, suka saka uwar tasu bacci, su kuwa sauran sai suka dauka ganyen maganin ne yayi aiki. Fita suka yi suka barta ita kadai domin ta samu hutu. Yan tagwaye wajen babansu suka je, suka ce ya dakatar da abinda yake. Ce masu yayi, zata warke ne kawai idan ta tuna dani, a yanda na kusa cimma burina, ba zai yiwu na dakatar ba. Abinda ya fadawa yaran kenan. -Ka cika son kai baba. Cewar Ayu, kafin yaja hannun yar uwarshi su bar wurin. Shiga dakin mahaifiyar tasu suka yi, suka tarar har yanzu tana bacci. A bangare daya kuma na dakin, Dauda ne zaune a kasa hannuwansa dafe da kanshi. Matsawa suka yi kusa dashi, anan suka ji yana ta wasu sambatu. Aje hankalinsu suka yi domin fahimtar abinda yake fada. Anan suka ji yana fadar : -Ba zan iya cutar da ita ba! Me yasa nake yin haka? Amma kuma ba ni bane! Zan yi fada domin ta! Ta dalilina ne ka dawo, zan fadawa shugaba, zata batar da kai har abada! Daga nan kuma wannan karamin ahalin naka zai biyo baya. Ba zan barka ka aikata hakan ba! Ba zan barka ka cutar da... Maimata kalamansa na karshe yayi ta yi kafin ya fadi sumamme. Kallon juna yan tagwayen suka yi, ba tare da dayansu yace kala ba. Ayu ne ya saka hannunsa cikin rigar Dauda tareda dora hannun daidai kan zuciyar Dauda, shuru yayi na dan lokaci bayan ya janye hannunsa kafin yace : -Bansan ko menene shi ba. -Kamar yaya? Yar uwar tashi ta tambayeshi da mamaki. -Ban sani ba ko shi mutum ne ko aljani. -Me kake fada ne? Mutum ne mana! -Eh, da gani mutum ne, amma jin bugun zuciyarshi zai tabbatar maki da ta mutum ce kuma ta aljani ce. Kasa yarda yar uwar tashi tayi, sai da itama tayi da kanta ta tabbatar. Dukansu cikin rudu suka fada. Kokarin tayar da Dauda suka yi domin yayi masu bayanin meke faruwa dashi amma kuma yaki tashi. Kalaman Dauda ne ke ta lugude a kwakwalan yan tagwaye, kafin dukansu tunaninsu ya basu aljani ne ya shiga jikinshi. Daukar Dauda suka yi suka bace daga dakin nasu. Anan suka shiga bin duk wata hanyar da Dauda zai farfado, sai dai basu suka samu nasara ba sai da sanyin safiya. Kokarin karantar tunaninsa suka yi amma hakan ya faskara, wannan ya tabbatar masu shi ba aljani bane kuma shi ba mutum bane. -A zahirance kai waye? Ayu ne ya fara magana. -Ruhina aljani ne, gangar jikina mutum. -Ta yaya haka zai yiwu? Cewar Aya. -Ta karfin tsafin shugabata Hindu. -Wacece Hindu kuma meye dalilinta? -Hatsabibiya ce ita, Aljana mai karfin tsafi marar misaltuwa, kuma tana son kara zama gagarabadau ta hanyar samun naku karfin. -Me? Ta yaya? -Ta riga da ta fara, kuma sai ta karasa. -Tanada alaka da ciwon mahaifiyarmu? -Eh. -Kuma da abinda babanmu ke yi? -Eh. Zai yi sau 10 ne, a dare goma, daren jiya shine na dare na karshe. Zuciyoyin yaran ne suka buga duum. -Me zai faru bayan hakan? -Iyayenku zasu fada doguwar sumar da zata dauke su tsawon wasu kwankaki kafin su mutu. Kuma da hakan ta kasance zata juyo kanku. Zaku fara yin rauni, ku kasa amfani da karfinku, daga nan zata kamaku ta ciro zuciyoyinku ta cinye. Da gudu Aya ta nufi wajen iyayenta domin tabbatar da abinda Dauda yake fada, sai dai kuma da zuwanta ta tarar dasu sumammu, wurin mahaifiyarta ta durkusa ta fashe da wani azabataccen kuka wanda yayi sanadin jawo hankalin Nafisa, Abdul da Sarah. Ganin Jinah taki farkawa kuma bugun zuciyarta kadan kadan yake yi, yasa suka nufi asibiti da ita duk sun san ba lallai bane likitoci su iya yin wani abu. Shi kuwa Ayu tsayawa yayi wurin Dauda domin sanin yadda zai iya wargaza plan din Hindu. -Amma ta yaya zamu dakatar da ita? -Ba zaku iya ba, amma akwai hanyoyi biyu da zaka iya daidaita wannan matsalar. -Wanne

Chapter 12 of 19