ke da Bukari baku ranci na kare ba ranar da kuka fara ganina.
Abin da Jinah ta fada ne yasa dariya ta kwacewa Sarah.
-Allah Sarah da gaske nake, mutumin da na fara gani, rokona yayi tayi akan dan Allah kar in cutar dashi in kyaleshi, ai kuwa ina bashi hanya ya fece kamar mashi.
Dariya Sarah take tace
-Ni kaina na so guduwa lokacin da na fara ganinki.
Cikin mamaki Jinah ta kalleta tace
-Me yasa?
Hannu Sarah ta dora akan fuskar Jinah tana shafawa tace
-Jinah, kina da wani masifaffen kyau ne, fuskarki har wani sheki take, ki duba ko ina a jikinki daidai ga gashin ki har ya wuce mazaunan ki. Gaskiya kyanki ba irin na mutane bane, sai dai ko na aljanu. Idan mutum ya fara ganinki dole yayi tunanin ke ba mutum ba ce, dan ko ni ban taba ganin mutum mai irin wannan kyau ba.
Cikin jin dadi Jinah tace
-Allah da gaske kike?
-Da gaske nake Jinah, ki bari duk randa kika je bakin kogi ki duba fuskanki a ruwa zaki gani.
-Kenan babu wani dalili da zan boye kaina?
-A'a, zo bari in gabatar da ke ga mutanen gidan nan ba tare da kin boye fuskarki ba, daman sun sha tambayata wai don me yasa kike boye fuskarki.
Kama hannun Jinah tayi suka fita zuwa tsakar gida, inda kowa sai aikin gaban sa yake. Ganin Jinah yasa kowa ya tsaya da abinda yake, suka zura mata na mujiya.
Ganin haka Sarah ta katse shirun da cewa
-Sunanta Jinah, itace yar kawata da ta bani riko.
Wurin shiru yayi, mutanen gidan na bin Jinah da kallon tsoro.
Sarah ta kara katse shirun da fahimtar dasu cewa Jinah mutum ce kamar su, kuma tana boye fuskarta ne dan ganin yanda mutane ke yawan kallonta da jin tsoronta.
Ajiyar zuciyoyi ne ke tashi a wajen, wasu da yawa tsoron su ya rage, amma wasu har yanzu suna ganin wannan kyau na Jinah yayi yawa. Wasu kuwa tasowa suka yi suna ta taba jikin Jinah, wasu kuma na shafa dogon gashinta suna al'ajabin wannan abu. Ganin Jinah duk ta tsargu yasa Sarah ta janyeta. Rungume Sarah Jinah tayi tana hawayen farin ciki, domin Sarah tanada kirki, gashi dai basu hada komai da Jinah ba amma ta dauketa tamkar wata yar uwarta. Tin daga ranar komai ya koma daidai tsakanin Jinah da Sarah, suka koma tamkar wasu shakikan kawaye, duk da Sarah zata fi Jinah da kusan fiye da shekaru 10, domin Jinah tana shirin shiga shekara ta 17 ne ita kuma Sarah tanada shekaru 33.
Kauye kowa ya dauka ana ta yadawa cewa ai gidan Lasaini akwai wata kyakyawar yarinya mai kama da aljanu. Mutane na ta tururuwar zuwa ganin Jinah, hakan ya dauki lokaci sosai, har ta kai idan Jinah ta fito a hanya mutane na kallonta har suna nunanta suna cewa ita ce mai kama da aljanu, har ya kai Jinah na tsarguwa da abinda suke mata. Shi yasa koda yaushe tafi son taje cen cikin jeji tayi ta wasa da dabbobi, kuma tafi jin dadin kwanciya kan reshen bishiya da kwanciya kan gado. Sai dai yanzu bata boye fuskarta kuma tana magana da mutane. 'Yan matan kauyen da dama kishi da ita suke, ganin samarin su nata rawar kafa gunta wasu har zuwa tambayar aurenta suke. Ita kuma Jinah ko a jikinta don wannan bai ma gabanta. Sarah ta fahimci hakan har wata rana take tambayar Jinah
-Me yasa baki kula samarin dake zuwa wajenki?
-Kawai haka nan, naji bana da ra'ayin soyayyar ne.
Jinah tace a takaice.
-Jinah ya kamata ace kina kulasu, dan idan da ta nice ba zan bari ki ma fara ba, domin aure shine babban kuskuren da na taba yi a Rayuwata. Amma sanin aure shine darajar kowacce mace, yasa nake son ki fidda gwani a cikin masu neman aurenki.
Cike da mamaki Jinah ta kalleta tace
-Amma me yasa? Ina mijinki yake? Sai yanzu wannan tunanin yazo min dan tinda nazo gidan nan ban taba ganin mijinki ba...
Sarah ta katseta da cewa
-Ke nifa kar ki sauya mana magana, ya maganar da muke yi amma ke kina so ki canja zancen ki kamo wani babi. Bansan daga inda kike ba amma mu nan a kauyen Mambila muna aurar da yarinya ne da wuri...
Ita ma Jinah katseta tayi da cewa
-Kece dai kike son canja maganar!
Ita ma ta kara musawa
-A'a ke dai kika canja maganar!
Musu ne ya barke a tsakanin su kafin daga bisani Sarah tace
-To shikenan wata rana zan fada maki.
Jinah tace
-Me zai hana ki fada yanzu?
Sarah tace
-Ke dai nace ba yanzu ba...
Mikewa Jinah tayi tana kakkabe zaninta tace
-To shikenan, ni dai na tafi cikin jeji.
Tabe baki Sarah tayi tace
-Aikin kenan!
Cikin shagwaba Jinah tace
-Ina jin dadin zaman ne a cen, kuma ko ba komai ina kallon yanda dabbobi ke kai kawo...
Kara tabe baki Sarah tayi tace
-Ina guje maki kar ki je wani aljani ya ganki, ya makale maki, kin ga sai ki dawo gida ki zauna.
Fita Jinah tayi daga gidan tana dariyar maganar Sarah.
Tana isa cikin jejin, kamar kullum bishiyar da take hawa tayi kwanciyarta ta dale, cikin zurfin tunani ta fada, tunani take ko zata iya tuna wani abu na rayuwarta ta baya, kamar kullum dai tana jin kewar wasu mutane da ta kasa gane su waye, tafi jin kewar wani wanda tana tunanin nata ne na kusa da ita sosai, da ta fara irin wanann sai zuciyarta ta rinka bugawa da sauri da sauri. Tana cikin wannan tunanin ne taji wata murya tana cewa
-Ni fa ba zan koma gida yanzu ba, kawai kuyi tafiyar ku!
Lekawan da Jinah zata yi sai ta ga wasu samari su uku ne a kasan bishiyar da take kwance.
Daya daga cikin samarin ne yace
-Ka dakata da taurin kan nan naka Dauda, dare fa ne ke shirin yi, kuma kaga nan jeji ne bamu san me yake dauke dashi ba na cutarwa.
Dayan saurayin kuma yace
-Musa fa na da gaskiya Dauda, bamu san meke akwai na hadari ba anan...
Dayan saurayin mai suna Dauda wanda yake ta yiwa yan uwan nashi taurin kan ba zai koma gida yanzu ba, ya katseshi da cewa
-Ku rabu da ni kuyi tafiyar ku! ku wane irin masu naci tsiya ne? na fada maku ni ba yanzu zan koma gida ba, ta yaya zamu fito farauta ko fara bamu kama ba, sannan mu koma gida haka hannu rabbana? Kuna tunanin wani abu zai same ni ne? Ai bansan cewa abokaina matsorata ne ba.
-To mu kaga tafiyar mu zaka iya tsayawa, ruwanka ne wannan. Muje Mahadi idan ya gaji ya iskemu gida.
Tafiya suka yi suka barshi anan, shi kuwa ko a jikinsa.
Duk abinda ke faruwa Jinah na saman bishiya tana kallon su. Wata dabara ce ta fado mata, tace bari na koyama wannan dan rainin wayon hankali. Shi kuwa Dauda zaunawa yayi karkashin bishiya ya dauko Kwari da bakanshi yana gyarawa. Koda ya ida tashi yayi wai da niyyar kama wata kurciya da ya gani. Cikin Sanda Jinah ta bishi a baya ba tare da ya sani ba, boye fuskarta tayi da gashinta sannan ta dira gaban Dauda, Dauda kamewa yayi guri daya ya kasa motsi, ita kuma Jinah ta kara nufoshi... Ganin haka Dauda ya fara kyarmar tsoro yana cewa
-Dan Al..lah ki..yi hakuri ki kya..leni kar ki cutar dani... Mamata zata damu sosai idan na mutu, nine dan autanta. Kiyi min rai!
Dariya ta so kwacewa Jinah, kamar ba shi bane yake ta cika baki dazun. Dauda kokarin guduwa yayi ai kuwa sai ga maciji kuma gabanshi, kasa motsi yayi ya fasa ihu
-Wayyo Allah! yau lokacina ne yayi!! wayyo!!
Taku daya Jinah tayi gaban macijin, ta durkusa tana kallon macijin cikin ido, koda macijin ya hada ido da ita sululu ya juya ya koma daga inda ya fito. Duk wannan dramar da ake yi Dauda yana tsaye a kame yana kallon ikon Allah, dan yau ya tabbata tashi ta kare. Jinah kasa rike dariyarta tayi, ai kuwa tayi ta dariya har ta gaji dan kanta ta dena, amma har yanzu Dauda ko motsi shi kawai gani yake tashi ta kare. Jinah ta matso kusa dashi tana mai dauke gashin da ke kan fuskarta tace
-Ni ba aljana bace, mutum ce kamar ka.
Har yanzu shiru Dauda yayi yana kallon ikon Allah. Jinah ta kara cewa
-Kamar ba kai bane kake ta kurari dazu ba, wai duk ina jarumtar taka?
Kallo dai kawai Dauda ke bin Jinah dashi. Abin ya fara ba Jinah haushi tace
-Tsaya da yimin wannan kallon, na fada maka nima mutum ce!
Ajiyar zuciya Dauda ya sauke tare da cewa
-Na kasa yarda ne...
Jinah tace mashi cikin zolaya
-To kayi hakuri da tsoratar da kai da nayi, kawai ina son na gwada jarumtar ka ce, ganin yanda kake ta cika ma abokanka baki dazun.
Juyawa tayi da niyyar tafiya. Dauda ya dan dawo cikin hayyacinsa, tsoronshi ya ragu. Cikin zuciyarsa yace "Kuma da ita Aljana ce ba yanda za'a yi ta ceceni a hannun wannan macijin, kuma ba yanda za'a yi ta kyaleni tayi tafiyarta." Tsayawa yayi yana kallon Jinah da tayi nisa, yana kallon irin halittar da Allah yayi mata kamar wata aljana. Kuma da ya tuna yanda tayi ta kori macijin nan sai ya kasa yarda cewa ita mutum ce. Dauda bai san lokacin da ya fara bin Jinah a baya ba, lokacin da Jinah ta fahimci ana binta a baya, tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi tace
-To kuma yanzu me kake so? Ka dakata da bina.
-Nima..nima bansan me yasa nake binki ba, kawai dai ina son nayi maki godiya akan cetona da kika yi, kuma ina son nasan sunanki...
A tsawace Jinah tace
-Wannan kuma ba zai yiwu ba, maganar godiya kuma ni nayi haka ne dan nishadi, shikenan zaka iya tafiya.
Juyawa tayi da sauri da niyyar tafiya, tuntube tayi ta fadi kasa, da gudu Dauda ya nufeta da niyyar taimaka mata
-Sannu ba kiji ciwo ba?
Kwalla a idonta tace
-Wayyo Allah zafi!
Anan Dauda yaga ya kara tabbatar ma kanshi lallai wannan mutum ce kuma akwai kurciya a tattare da ita. Lokacin da yazo da niyyar tabata, da sauri Jinah taja baya dan bata so ya tabata. Kuma me yasa zata yi haka alhali taimakonta zai yi? itama kanta bata san dalili ba.
Dauda ya dan ji ba dadi yace
-Kawai ina son ganin inda kika ji ciwo ne.
Da sauri Jinah tace
-A'a kar ka tabani!
Dauda bai tsaya saurarenta ba ya kama kafar tata, dole ta kyaleshi, kaya ce yaga ta taka a kafarta ta hagu.
Jin laushin kafarta da Dauda yaji yace
-Masha Allah, gaskiya kinada fata mai laushi da dadin tabawa... oh yi hakuri.
Kafarta kawai Dauda ya taba yana wannan sambatun ina ga...
Wata bishiya Jinah ta nuna mashi tace ya debo kunnuwanta, dan ta canja maganar, dan ta fara lura dan saurayin ya fara fita hayyacinshi.
Dauda yace
-Shit, barni nayi aikina, ba abinda zaki nuna min dan nima haihuwar kauye ne.
Cikin shagwaba Jinah tace
-To kayi a hankali.
Murmushi Dauda yayi yace
-Kinga shi yasa raina mutane baida kyau, ki duba yanda kika nemi kasheni da tsoro kema gashi yanzu Allah ya saka min.
Kallonsa Jinah tayi tace
-Kana nufin dan na tsorata ka ne yasa naji ciwo?
Dauda ya kara yin murmushi yace
-Ni dai ban ce ba..
Turo baki Jinah tayi a shagwabe tace
-Haka kake nufi ba gashi da bakinka kake fadi ba..
Fashewa da dariya Dauda yayi, kafin daga bisani wajen yayi shiru. Ciro ganyen bishiyar Dauda yayi sannan ya nika ganyen da taimakon wasu duwatsu biyu sannan ya saka dadai inda Jinah ta taka kayar. Keta zaninta tayi kadan ta bashi ya daure mata ciwon. Kamata Dauda yayi da niyyar taimaka mata ta mike, wani zafi ne yaji ya sauka a jikinsa kamar an kunna masa wuta. Ihu Dauda ya fasa kafin ya fadi sumamme ko matacce.
---------------------------
To Fans ku biyo mu domin jin abin da zai faru da Dauda sanadin taba Jinah da yayi.
---------------------------
Please comments dinku suna da matukar anfani domin suna karawa Marubuci karfin gwiwa...
Ga link sabon Group da zaku rinka samun updates na wannan sabon labari : https://chat.whatsapp.com/JGjb07Du5N45rzy8gfOCOV
Note : Amma fa ku sani Group ne wanda admin ne kawai zai iya posting, dan bamu son wani labari in ba na wannan labarin ba.
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story
CHAPTER 2
Mambila, cikin wannan kauyen mai nisa a kasar Nijar, duk da rana ta fadi, dare yayi, hakan bai hana farin wata haska kauyen ba. Kowane mutum a kauyen ya aje aikin da yake yi ya nufi gidanshi don an ce dare Mahutar bawa. Saidai ba haka yake ba a bangaren Jinah dake durkushe tsakiyar jeji da mutum kwance baya motsi, kamar babu rai a jikinsa. Tsoro da firgici ne kwance a fuskarta, haka ta cigaba da kokarin tasheshi, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Cikin kuka take fadin
-Dan Allah ka tashi, bawan Allah nasan baka mutu ba.
Kuka Jinah ta cigaba da yi, wata kakkausar murya taji ana cewa
-Idan har kika cigaba da tabashi, to ba zai taba tashi ba!
A tsorace Jinah take ta dube dube dan ganin mai magana amma bata ga kowa ba, tunani tayi wata kila kunnuwanta ne ke zaginta. Cigaba tayi da jijiga Dauda, amma ba alamar zai motsa, tsoronta ne ya karu. Ganin hakan ba zai fisheta ba, ta tashi a guje ta nufi hanyar gida domin nemo agaji.
-Sarah! Sarah! Sarah!
Jinah take fada, da alama har ta fara fita hayyacinta. Kusan karo suka yi da Sarah.
A tsorace Sarah tace
-Me ya faru kike wannan uban gudun da yimin irin wannan kiran?
Jinah na haki tace tana kama hannun Sarah
-Sarah zo ki gani, yaki tashi! Zo ki gani dan Allah!
-Kwantar da hankalin ki, kar ki tashe da mutanen gidan, fada mani me ke faruwa?
-Fa..du..wa ya..yi, faduwa yayi kasa, na tasheshi, na tasheshi amma yaki tashi. Sarah ina gudun ya mutu, wayyo Allah na...
-Muje ki nuna min inda yake.
Jinah kaita tayi inda Dauda yake, har yanzu dai yana nan kwance kamar gawa. Karasawa Sarah tayi kusa dashi, tana shirin tabashi suka jiwo ana cewa
-Me kuke a nan?
Lasaini ne, dan uwan Sarah.
Karasowa yayi yana fadin
-Me ya faru?
Ganin mutum a kwance kusa da su. Bai jira jin amsar su ba, ya sunkuci Dauda a kafadarshi, ya nufi gida dashi. bai dire dashi ko'ina ba sai bisa gado, sannan yace a samo masa ruwa. Jinah a guje taje ta debo ruwan, ta kawo masa. Zuba masa ruwan yayi a fuska amma shuru bai farka ba.
-Ya mutu ko?
Jinah tace zuciyarta na bugawa.
-A'a yana numfashi.
Lasaini ya bata amsa.
-To me yasa bai farka ba, gashi kuma ko motsi baya yi.
-Ki kwantar da hankalinki Jinah Cewar Sarah.
Wani mari Lasaini ya gaura masa, sai suka ga ya motsa. Ajiyar zuciyoyi Sarah da Jinah suka yi. A hankali Dauda ya bude idonshi yana binsu da kallo, kafin ya tambaya a ina yake.
Basu bashi amsa ba, Lasaini ya tambayeshi
-Kai dan wane kauye ne?
Dafe kai Dauda yayi kafin yace
-Ni dan kauyen NA GAMA ne!
-Ko zaka iya tuna abinda ya faru da kai?
Daga idanu yayi ya kalli inda Jinah take, sannan yace
-Gamo nayi da aljana ta rikida zuwa mutum ko kuma mutum ce ban sani ba...
Sarah ce tayi dariya, kafin su hada ido da Lasaini ta gimtse dariyarta.
-Zaka kwana anan kafin safiya, tinda yanzu dare ya riga yayi.
Cewar Lasaini kafin ya mike tareda cewa su Sarah su ma su je su kwanta.
Sarah ce ta juyo tareda kiran dan uwan nata
-Lasaini!
A fusace ya juyo yace
-Ya aka yi ne!
Sunne kai Sarah tayi cikin i'ina tace
-ah daman... daman.. so nake.. ba komai ma sai da safe.
Tsaki yaja bai kara bi ta kanta ba, yayi gaba. Kwalla ne suka zubo mata, ta rasa sai yaushe tsakaninta da dan uwanta zai daidaita. Tana fata watara ya yafe mata, su koma kamar yanda suke da.
Kama hannunta Jinah tayi ba tare da tace mata wani abu ba, suka wuce daki.
Suna shiga dakin kowace ta nufi makwancinta, Sai dai bacci ya kasa daukansu.
Jinah ce ta sauko daga nata gadon tana fuskantar Sarah tace
-Sarah, kin san dalilin da yasa yayi kamar ya mutu? Alhali bai san abinda ya faru dashi ba, kawai fasa ihu ne fa yayi ya fadi. Daman ana irin wannan ciwon ko kuwa?
Sarah ta kalleta tace
-Ba wani ciwo a yanda yace ya ganki, yayi tunanin aljana ce ba dole ya tsorata ya suma ba. Ai yayi kokari ma da bai hade zuciya ba tsabar tsoro.
Dariya dukansu suka yi, kafin Jinah tace
-Tinda baki jin bacci, ki bani labarin ki, da abinda ke tsakanin ki da dan uwanki, naga baku cika magana ba, kuma na lura duk lokacin da zai yi maki magana fuskarsa a daure take. Dazun ma naga haka, kece babba ko shi ne?
Ajiyar zuciya Sarah tayi kafin tace
-Yayana ne, shekara daya ce a tsakanin mu.
Tabe baki Jinah tayi, tace
-Shekara daya ya baki, shi ne ya rainaki har haka?
-Haba, ai kuwa sai na fada masa.
Zaro ido Jinah tayi tace
-Lah rufa min asiri da wasa nake, ai mutumin kirki ne.
Ganin yanda Jinah take zaro ido ya baiwa Sarah dariya.
Shuru na dan lokaci ya biyo baya, kafin Jinah tace
-To meye musabbabin abinda ya hada ku?
Shuru Sarah tayi kafin ta fara ba Jinah labarin
-Hakan ya fara faruwa ne lokacin da na fara soyayya. Ni da dan uwana mun kasance tamkar jini da hanta, kullum muna tare bama rabuwa, duk inda za'a ga keyata to ki tabbata za'a ga tashi...
Murmushi Sarah tayi tare da kwalla na tuno alakarta da dan uwanta a baya. Ta cigaba
-Na fada soyayya...
Kara matsowa Jinah tayi, cikin zumudin jin labarin soyayyar Sarah.
-Na fada soyayya ne da babban makiyin yayana mai suna Kimba. Kimba kyakyawa ne ajin farko ga kuma kudi, bai cika zama a kauyen nan ba saboda mutum ne mai yawan tafiye-tafiye. Yayana ya tsani Kimba kamar rai da ajali, lokacin da ya gane muna soyayya, sai da ya share kusan sati bai min magana kuma haka shi ne ya fara zama silar wargajewar alakarmu. Yayi kokarin ganin ya datse alakata da Kimba, amma fir na kiya, na nuna masa nifa ina son Kimba. Yana yawan fada mani, Kimba ba mutumin kirki bane, yaudarata kawai zai yi. Amma ina ni soyayya ta rufe min ido. Kimba ya turo yan uwanshi neman aurena, iyayen mu suka bashi, kowa na dangi na murna da auren mu amma banda yayana. Ana gobe daurin auren mu, da yawan samarin kauyen suka yi wata tafiya zuwa wani kauye dan nesa da mu mai suna Kumana. Hankalina bai kwanta ba dan tafiyar har da Kimba da yayana a ciki. Ina tsoron kar yayana yaje yayi wa Kimba wani abu. Saidai cikin ikon Allah suka dawo kowa lafiya lau. Sai dai Yayana yazo min da wani labari wanda shi yayi sanadin datse alakar dake tsakanin mu. Ya bani labarin cewa lokacin da suka isa kauyen Kumana, Kimba yayi shaye shaye ya bugu, ya shiga cikin jeji lokacin da ya dawo sai yaji yana ba abokinshi labari wai ya samu wata yarinya a jeji ya kore kishirwarshi, wato yayi lalata da yarinyar. Bansan lokacin da na wanke yayana da mari ba, ba zan taba manta abinda yayi ta nanata min ba "Yanzu Sarah ni zaki mara akan wannan dan iskan? To ki sani daga yau babu ke babu ni, kuma ba zan kara shiga tsakanin ki da wannan dan iskan ba!" Wadannan kalaman har yanzu suna min yawo a cikin kwakwalwa, amma ko kala ban ce masa ba dan nima a lokacin haushin sa nake ji, dan kazafin da yayi wa Kimba.
Da safe aka daura auren mu, shiru ban ga alamar yayana ba har aka daukeni zuwa gidan Kimba, tun daga ranar ban kara ganin yayana ba. A farkon auren mu, na kasance cikin farin ciki, na irin soyayyar da Kimba yake nuna min, duk abinda nake so Kimba yana yimin. Bayan wasu watanni Kimba ya nemi da na bishi garin da yake kasuwanci, hakan na damu sosai dan bana son nayi nisa da yan uwana, bare ma yayana, ina son na rinka ganinshi kullum koda kuwa baya min magana. Ba yanda zan yi dole na bishi, saboda mijina ne dole nayi masa biyayya.
Tafiya mai nisa muka yi kafin mu kai kauyen tsakiyar dare lokacin kowa yayi bacci banda wata mata wadda da alama zata fini shekaru kadan. Bayan mun aje kayan mu, matar tazo tace min naje ga ruwa cen ban daki nayi wanka. Bayan na gama, na kwanta baccin gajiya.
Hawaye ne suka zubo daga idon Sarah, shuru tayi dan ba zata iya cigaba da ba Jinah labarin ba, domin tana jin kamar yanzu ne abun yake faruwa. Rokonta Jinah tayi ta yi akan dan Allah ta cigaba. Share hawayen da suka zubo mata tayi kafin ta cigaba.
-Da safe, motsin yara ne dake wasa da kuma matan gidan da ke daka ya tayar dani, dubawa nayi gefena amma ban ga Kimba ba. Fitowata daga dakin naci karo da matar jiya da dare, bayan mun gaisa nake tambayarta ko taga mijina Kimba. Budar bakinta sai tace min wai "Ya tafi wajen daya daga cikin matansa, ni sunana Mariya nice matarsa ta biyu ke kuma kece matarsa ta biyar." Jiri naji ya fara dibana, a take maganar yayana ta fado min. Sai dai ba zan yi saurin yarda da maganar wannan matar ba. Nuna mata nayi da ban fahimci me take nufi ba. Anan take bani labarin cewa ai Kimba yanada mata da yawa da 'ya'ya a wurare daban daban, wannan ma shine karon farko da ya hade matan sa biyu waje daya. Bayan ta gama bani labari komawa nayi daki nasha kukana, shine abu mafi muni da nake ganin ya faru a Rayuwata. Ban taba tunanin Kimba zai min haka ba, dan yasha fada min "Kece matata ta farko kuma kece ta karshe." Bai taba fada min cewa yanada wasu matan ba. Kuma wani bangaren na zuciyata kasa gasgata maganar matar yayi, dole Kimba ne zai fada min gaskiyar abinda ke faruwa, haka na bar abin a zuciyata na zauna jiran dawowar Kimba. Kwanaki da yawa sun shude, babu labarin Kimba, nan na fara gasgata maganar yayana tabbas Kimba mayaudari ne. Bai tashi dawowa ba sai bayan wata daya, da zuwanshi na haushi da masifa da kuka akan ni sai ya sakeni na koma gidan mu, babu tausayi ya lakada min dan banzan duka, naci kuka da neman taimako amma babu wanda yazo ya kwaceni, saka Mariya yayi ta tattara 'ya'yanta suka tafi, bansan ina ya turata ba. Kashedi yayi min akan idan har ina son zaman lafiya to dole inyi masa biyayya. Haka dan zaman da Kimba yayi na kwana biyu ya mayar dani tamkar jaka, dukan safe daban na rana daban. Gashi ya hanani zuwa ko ganin gida, idan ya tashi zuwa wajen sauran matanshi, haka zai barni ni kadai a gida gashi babu damar naje gida, dan mu a al'adar mu idan aka yi aure ko yaji ba'a yi bare saki, da kin ga aure ya mutu to ki tabbata daya ne ya mutu ya bar daya. Haka gidan Kimba ya zame mani tamkar gidan yari...
Kuka ne yaci karfin ta, lallashinta Jinah kawai take yi, dan sosai ita ma ta tausaya mata.
Share hawaye tayi ta cigaba
-Na dauki shekaru masu yawa gidan Kimba babu wani sauyi, lokacin da ya aureni inada shekaru 18, yanzu kuma shekaruna 32. Bayan wani lokaci naji labarin matarshi ta farko a Nigeria take, kuma yafi dadewa a cen dan wani lokacin yana kwashe har shekaru 2 wajenta. Kuma yanzu cen ne zai je, ganin hakan yasa na rokeshi da ya barni naje ganin gida daga karshe ya amince amma da sharadin kafin ya dawo yana son ya tarar dani na dawo. A haka na amince akan zan zo naga dangina uwa uba yayana dan yau kimanin shekaru 5 da rasuwar Abban mu, ita kuma umman mu shekaru 3 kenan. Har lokacin yayana baya min magana, ranar da nazo, na durkusa har kasa nayi ta rokonshi akan ya yafe mani, amma ko kallon banza bai min ba. Nasan har yanzu yana sona, dan duk wata kulawa yana bani ne ta hanyar matarshi, ban rasa komai ba anan, ko ba komai ina jin dadin ganina kusa da yayana dan shi kadai ne ya rage min a dangi, gashi ban taba haihuwa ba.
A wannan karon har Jinah kuka take yi, dan Sarah ta bata tausayi ba kadan ba. Bayan sun ci kukan su sun gaji, Jinah tayi mata alkawari da zata daidaita tsakanin ta da yayan ta. Hakan yayi wa Sarah dadi kuma tana fatan haka.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 19