Share this page
Ganin dare yayi nisa yasa kowace ta nemi makwancinta. Asuba ta gari! Safiya na wayewa, Sarah ta tafi kasuwa yin cefane, ita kuma Jinah wanka ta shiga, bayan ta fito ta zauna taci abin karinta. Tana idawa ta kwanta da niyyar komawa bacci, wata murya taji na rera wasu baituka masu dadi a kunnenta. Baituka ne kamar na mutumin da yayi kewar masoyiyarsa. Yanda Jinah ta kashe kunne, zai tabbatar maka da lallai tana jin dadin baitukan, tashi tayi ta leka ta window da niyyar ganin mai wannan dadaddiyar murya, sai dai kafin ta karasa lekawa taji sallama a bakin kofa. Amsawa tayi tareda tambayar waye. Dauda ne ya amsa da -Nine Dauda! Fitowa tayi ta tarar dashi bakin kofa. -Nazo nayi maki sai an jima, dan tafiya zan yi. Ba tare da Jinah ta kalleshi ba tace -To sai an jima.. Kallonta yayi yace -Sai kuma yaushe zamu sake haduwa? Zaro ido Jinah tayi tace -A'ah ba da ni ba? Dauda yace -Saboda me? Tace -So kake ka mutu a hannuna? kaje kawai nagode. Dariya Dauda yayi, abin dariya yake bashi ganin yadda Jinah ta kakkahe ita dagaske take. -Ai ki kwantar hankalinki ni da nake fatan mu kasance na har abada.. Ya fada yana kashe mata ido. Irin kallon sama da kasa Jinah tayi masa kafin tace -Ban fa gane ba! -Zaki gane nan gaba kadan, kyakyawar aljanata. Ya fada yana murmushi tare da juyawa zai tafi, Jinah kuwa kamewa tayi kamar an shukata, tana ta juya maganar tashi dan ita sam bata fahimta ba. Tunawa tayi da dadaddiyar muryar nan da taji, da saurinta taje ta leka windon dakin amma bata ga kowa ba. Tunani take a zuciyarta, waye wannan mai muryar, me yasa take jin wani abu a lokacin da yake rera baitukan kuma me yasa har yanzu muryarshi ke mata yawo a kwakwalwa? Da wannan tarin tambayoyin da batada amsar su, ta nufi jeji da muryarta mai dadi tana rera daya daga cikin wakokin Umar M. Shareef. Wa zani ba kaina? in ba ke ba a cikin yan mata Wa zani ba raina? kece dai nake kira yar gata Kaunar da nake miki ban yiwa kaina, kin riga kinyi rata Kowa yazo tanka mini kan kaunarki yanzu ma fafata In zaku yimin take, bani son wata sai ke Ga masara ga wake, ni dai nace sai ke... You can watch lyrics of this song by Umar M Shareef 👉 https://youtu.be/Q0tGz9DJ1Ck --------------------------- To fah wannan shine Chapter din mu na yau. Bayyana ra'ayin ku akan labarin yana karan karfin gwiwar cigaba. Zaku iya cigaba da bibiyar labarin a wattpad ta wannan link din 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 3 Kamar yanda yake a duniyar mutane haka yake a duniyar aljanu, idan har aljani ya taka daya daga cikin dokokin al'adarsu, ana yanke masa hukunci daidai da laifinsa. Abinda ya faru ga Fally kenan, ya rasa duk wani karfi nashi da iko irin na kowanne aljani. Idan kuwa haka ta kasance ga aljani, kwanaki kadan suke rage masa a maimakon dubannin shekarun da zai yi. Aljanun da sarki ya turo sun yi nasarar cafke Fally ne, lokacin da yake kokarin bin Mahaifiyarshi da Jinah. Sanadin abinda ya aikata aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari. -Me kayi aka kawo ka wannan wajen? Cewar wani aljani da suke daki daya da Fally a gidan yarin. Ba tare da Fally ya bashi amsa ba ya cigaba da cewa -An yanke mana hukuncin daurin rai da rai ne, kuma ko ba dade ko ba jima dole zamu mutu a bayan wannan kantar, dan haka kayi amfani da sauran lokacin da ya rage ma da wannan zaman tunanin da kake... tam duk da ka ki kayi magana, kuma nasan kana ji na, bari na baka labarina da dalilin zuwana wannan waje. Na kasance daya daga cikin aljanu masu tafiye tafiye daga wannan kasa zuwa wata kasa bisa umarnin sarki. Inada mata, na kan dade ban koma gida ba, hakan yasa matata take amfani da wannan damar tana kawo kwarata gida. Nasha kamata amma bansan wane mataki zan dauka ba, har dai wata rana da na kamasu zuciya ta debeni na cire masu kai ita da kwartan nata sannan na kona gawarsu. Wannan yasa aka yanke min hukuncin daurin rai da rai. Ko a cikin aljanu ko cikin mutane, cin amana mummunan abu ne, yana iya kasancewa ga mace ko ga namiji, wannan ya zama kamar ruwan dare. Cin amanar wanda muke so yanada ciwo. Ba zaka taba sanin zafin cin amana ba sai lokacin da wanda ka yarda dashi yaci amanarka. Sai dai daukar hukunci kamar yanda wannan aljanin yayi ba abinda zai rage maka na daga radadin zuciya. Har yanzu Fally bai da alamar yin magana, dan ba lalle bane ma yaji abinda aljanin yake fada. Hankalinsa yana cen a tunanin abar kaunarsa, yana cikin kewarta sosai kuma da fama ciwon rashinta a kusa dashi. Wani aljani daya daga cikin masu gadin gidan yarin ne, yazo ya sanar dashi, mahaifiyarshi ta kawo masa ziyara. Bayan yazo daidai inda mai kawo ziyara ke haduwa da fursuna, mahaifiyarsa ya gani, take ya ji zuciyarsa ta rage zafi. Ita ma ta ji dadin ganin danta duk da akwai shamaki tsakaninta dashi. -Yaya kake dana? Tace tana mai tausaya masa -Lafiya lau nake, ke fa yaya kike? -Lafiya nake, sai dai nayi kewarka sosai. -Nima haka, yaya baba? -Lafiya lau yake, shi ma zuwa an jima zai zo ganinka. Ta fada, yanayinta na nuna alamar damuwa. Fally ya fahimci bata zo da labari mai dadi ba. - Ba zasu sake ni ba koh mama? -A'a dana... -Haba! Mama kinsan fah kwanakina kidayayyi ne anan. -Na sani Fally, na sani, hakan shi ke kara tayar min da hankali, kusan zaucewa nake ganin na samu hanyar fitar da kai! -Na sani Mama, kawai ina jin tsoron ranar da zan... -Ranar da zaka mutu? Ka yarda da ni, mutuwa ba yanzu zaka yita ba, zan fitar da kai daga wannan guri koda kuwa zan rasa raina. Haka ta cigaba da kwantar masa da hankali tare da yi masa alkawarin zata fitar dashi koda kuwa hakan zai zama ajalinta. Uwa kenan, ta kan so ta wahala akan danta ya wahala, Uwa zata iya sadaukar da komai dan ganin murmushin danta. Ga uwa farin cikin danta shine gaba da komai. Bayan tafiyar mahaifiyarsa, damuwarsa ta rage, farin ciki fal a zuciyarsa, tabbas yasan mahaifiyarsa zata fitar dashi, abinda yafi sanyashi farin ciki shine idan ya fita zai ga sanyin idaniyarshi Jinah, wadda ta dalilin ta ya rasa duk wata kima tashi ta aljanu, wadda ba zai taba daina sonta ba har abada.. -Kana ganin Jinah ba zata manta da kai ba kuwa? Wani bangare na zuciyarsa ne ke fadar haka. -A'a ba yanda za'ayi ta manta da ni... Nan fa rikici ya barke tsakanin bangarorin zuciyarshi. -Kana da tabbaci ne? Tayi fa nisa da kai yanzu! -Nisa ba abinda zai iya a soyayyar mu. -Ka tuna, tana da masifaffen kyau, kuma ba wani namiji da zai ganta bai kyasa ba. Murmushi yayi. -Baka yarda ba kenan? -A'a abokina, ni da Jinah mun riga mun yi aure, tare da alkawarin zama na har abada. Duk namijin da yayi kuskuren kusantarta, to fah jikinsa zai zama tamkar kifin da aka fiddo awa daya daga cikin ruwa. Mutuwa zata tabbata ga mutumin da yayi kuskuren yin hakan. Eh, Jinah tawa ce ni kadai har abada! A bangaren su Jinah Sarah ce ta shinfida tabarma, Jinah ta zauna. Dauko matajin kai da Man kwakwa Sarah tayi sannan ta zauna a bayan Jinah. -Bari muga yanda za'a yima wannan gashin naki, ki rage yawo dashi haka buzuzu. Sarah ta fada tana yamutsa gashin Jinah da mataji. Sarah sai da ta fara da nasanin farawa Jinah kitso, dan gashinta ba dai yawa ba, ga kuma santsi. Lura tayi da wani tabon haihuwa a bayan wuyan Jinah, tsayawa tayi, dan ta tuna mijinta yanada irinshi komai da komai shima kuma daidai da inda na Jinah yake. Abin daureta mata kai yayi, amma sai ta barshi a zuciyarta kafin ta maida hankalin ga yi mata kitson. Duk lokacin da ta kamo gashin da niyyar kitsawa sai Jinah tayi ta murkususu tana fadin "da zafi." tana turo baki. Sarah bata tanka mata ba, da abin Jinah ya isheta sai tayi mata rankwashi a tsakar ka ita kuma Jinah ta fasa kara. Haka suka cigaba da yi abin gwanin ban sha'awa. -To an kare! Sarah ta fada, mikewa jinah tayi tana ajiyar zuciya tace -Haba kin ji yanda mazaunaina suka yi kamar zasu kama da wuta. -Je ki duba madubi, zaki ga yanda na gyara maki shi, sai kin min godiya.. Dariya suka yi kafin Jinah taje ta duba a madubi, gashin yayi kamar an zatse kwarya, shi ba babba ba shi ba karami ba. Koda Jinah ta gani kasa motsawa tayi dan yayi bala'in kyau. Manyan zane ne Sarah tayi mata a tsakiyar kai tare da game jelar gashin ta dunkule waje daya ya sauka a gadon bayanta, kasancewar Jinah fara, haka fatar gashinta fara ce yasa zanen kitson ya fito da kyau. -Sarah kinyi gaskiya, yayi kyau sosai wallahi, nagode. -To idan kika tashi kwanceshi, zan sake maki wanda yafi wannan. -A'a gaskiya ba zan iya kara irin wannan zaman ba, ai sai duwawuna su fashe.. Dube dube Sarah take tana neman abinda zata jefi Jinah dashi, fahimtar abinda zata yi yasa Jinah tayi waje da gudu. -Shakiyiya! Sarah ta fada tana dariya. Bayan wasu yan mintuna suna zaune cikin daki, suka ji Bukari yana ta kwada sallama. Sarah ce ta amsa sannan tace masa ya shigo. -Wai kai Bukari, ba nasha fada maka idan kayi sallama biyu ta isa, sai ka jira a amsa ba? Cewar Jinah. -Babu banbanci idan biyu nayi ma tayi, idan kuma shida nayi ma tayi ko Tanti Sarah? Bukari ya fada cikin muryarshi ta yarinta. -Da gaskiyarka Bukari.. Sarah ta fada tana dariya, ita dai tana son Bukari, tana jinsa kamar danta. Bata samu sa'ar samun haihuwa ba gashi kuma ita mai son 'ya'ya ce. Sai dai ta dalilin Jinah da Bukari tana jinta tamkar Uwa kuma hakan yana mata dadi. -Jinah! kitsonki yayi kyau! Bukari ya fada yana kallon kitson Jinah. -Hmm nagode, Sarah ce tayi min. -Tanti Sarah kin iya kitso, fada mani kudinshi koda dubu dubu ne yanzu na biya.. Cewar Bukari, shi a dole dagaske yake, kallon juna matan suka yi. Barkoncin Bukari yasa yake da saurin shiga rai. Yaron yanada hankali da wayo, yana da cikin yaran kauyen masu zuwa school. Kwada masa kira yaji ana yi, ya amsa. -La'ilah, na manta! Tanti Sarah, Jinah mama tace na kirawoku kuci abinci. Sannan ya juya ya fita da gudu. -Duk wannan surutun da yake yi, ashe aikoshi aka yi kinji sai yanzu ya tuna. Cewar Jinah tana mikewa. Bayan sun ci abinci, kowa ya shige dakinsa, Jinah ta tarar da Lasaini dan uwan Sarah zaune tsakiyar gida. Yau tsawon kwanaki kenan tana son yi masa magana, sai dai bata samu dama ba dan bai cika zama gida ba. -Ina wuni? Ta fada, dago kai yayi ya kalleta, suka hada ido kafin ya amsa gaisuwarta. -Zamu iya magana? -Ina saurarenki. Zaunawa tayi bisa benci dake kusa dashi. -Magana ce nake son muyi akan Sarah. Yamutsa fuska yayi kafin yace -Kinga yarinya, ina mai baki shawara da kar ki shiga abinda ba ruwanki, dan baki san komai ba. -Ta bani labarin komai. -Wannan ba abinda ya dameki ba ne, dan haka ki fita daga wannan maganar kuma ki je ki kwanta dare yayi. -Ba'a gyara wata matsalar da kunno kan wata matsalar. Dakatar da ita yaso yi, amma ta rokeshi da ya saurareta. -Yanzu kamar kai, idan rana tsaka aka ce ka rabu da matarka, zaka iya?... ko kuma idan aka ce ita ta barka, ya zaka ji? Sunne kai Lasaini yayi alamar yana tunani. -Lasaini, Sarah tana son wannan mutumin sosai, ta yanda lokaci daya a nuna mata wani aibu nashi ba zata yarda ba. Wani lokacin soyayya tana hana mu ganin aibun masoyi. Ka dan yi tunanin ace kai ne ita na wani dan lokaci kaji. Tana cutuwa da irin rashin ko in kula da kake yi mata, wanda har ta kasa boye hakan, batada iyaye, batada 'ya'ya, kai ne komai nata a halin yanzu. Har zuwa wane lokaci zaka bar cutar da ita? Har zuwa wane lokaci zaka dawo yayanta na da? 'yar uwarka ce fah, kuma wajibinka ne ka kula da ita. Shiru Jinah tayi sannan ta mike da niyyar tafiya, itama tana jin tayi gangancin fadama mutumin da ya girme mata irin wadannan maganganun amma kuma tasan gaskiya ta fada. -Jinah! Kiran sunanta yayi, ta juyo tana fuskantarsa. - Wai nace shekarunki nawa? Idanu ta fiddo, tana mamakin me ya kawo kuma wannan tambayar? -Kawai naji kamar mahaifiyata ce a gabana... Ba tare da ta bashi amsa ba ta juya tana murmushi, cikin ziciyarta tace "Ashe dai maganganuna sunyi tasiri cikin dan karamin kanshi! Ai kuwa, safiyar ranar, Lasaini yaje har gun kanwarsa ya nemi gafagarta. Sarah kasa gasgata hakan tayi, dan ranar tasha kuka, tayi ta yiwa Jinah buhu buhun godiya, gashi ta sanadinta ta shirya rashin jituwar dake tsakanin yan uwa. Fita Jinah tayi, ta barsu. Ta nufi bakin kogi. Rage kayan jikinta tayi ta fada cikin kogin. Cen taji ance -Kyanki ya kara fitowa, da kika yi kitso. Sauri tayi ta fito, ta saka kayanta sanin ta gane mai muryar. -Sarkin naci! Ta fada kasa da murya. -Sunana dai Dauda ba sarkin naci ba. Ya fada yana mai nuna mata alamar ya ji abinda ta fada. Kunya ce ta kamata. -A'a ai da kin cigaba da wankanki, kiyi kamar bana wajen. Ya fada ganin ta juya zata tafi. -A'a dama na kare. -Toh, dan Allah kar ki tafi, daman yau tsawon kwanaki kenan nake ta son na ganki. -Ni kuma? -Eh -Saboda me? -Ai na fada maki, kin riga kin fada komata. -Ni kuma ai na fada maka, bansan me kake nufi da hakan ba! -Zo ki zauna dan Allah, sai na fada maki ma'anar hakan. Haka dai ta hakura ganin magiyar da yake ta yi mata. Zaunawa suka yi bisa wan dutse. -Toh ina sauraronka? Cikin wata marainiyar murya ya fara fadin -Jinaaaaah, tuuuuun lokaaacin... Dakatar dashi tayi, tace -Dauda bafa waka nace ka yimin ba. -Jinah, bana ganin komai a duk lokacin da na ganki, bana tunanin komai a duk lokacin da nake tunaninki! -Ni fah ban gane komai ba a cikin wannan waken naka, ka yimin gwari gwari. -A takaice kin fada komata ne! -Oh Allah, wai Dauda wannan kalamin naka ba fahimtarshi nake ba. -Yi hakuri, to "ay gaba ni Jinah" -Da Hausa! -Ina sonki Jinah, ina matukar kaunarki, kuma ina son ki kasance matata. Tuni ta dade da harbo jirginshi, kawai dai tana so taji daga bakinshi ne. Sai dai bata so yaji ba dadi, dan tasan amsar da zata bashi ba zata yi masa dadi ba. Itama tana son Dauda, gashi hadadde, sai dai ta bashi zuciyarta wannan ba mai yiyuwa bane. Shuru dukansu suka yi, kafin ita ta mike da niyyar tafiya gida. jiri ne ya debeta ta koma ta zauna. -Bana jin dadi Dauda! Ta fada tana dafe kai. -Sannu, me yake damunki? tashi muje na rakaki gida. Mikewa tayi yana mata sannu, suka kama hanyar gida, sai dai ba wanda ke yiwa wani magana har suka karaso kofar gida. -Yauwa ya isa nan, Dauda zaka iya tafiya nagode. Ta fada tana rike da kanta. -Kin tabbata? Ya tambayeta da alamar damuwa a fuskarshi. -Eh kar ka damu! nagode Ta juya da niyyar shiga gida, ya kira sunanta -Jinah! Waiwayowa tayi, yace -Ina jiran amsarki. Bai jira jin me zata ce ba, ya juya ya tafi. Jinah tarar da Sarah tayi ita kadai cikin daki, Sarah ta damu ganin halin da Jinah take ciki. Kwantar da ita Sarah tayi, ta kura mata ido kafin tace -Jinah, amma kwanan nan kina jin tashin zuciya ko? -Eh ina jin haka dan wani lokacin sai naji kamar nayi amai. -Tinda kika zo gidan nan, ko kin taba ganin al'adarki? -A'ah ban taba ba. -Innalillahi, Jinah kar dai ciki ne da ke? --------------------------------------- Bon, zan dakata nan a yau. Sai kuma zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Fatan dai wannan chapter ta burge ku? To ku fada min abinda kuke tunani, i want to know hahaha. 😂 Muje zuwa a wata sabuwar chapter, kuma kar ku manta da yin comment domin shi nafi bukata. 🤗 Watty : @El_Ashtar 💞 JINAH (Matar Aljani)💞 by Malik al-Ashtar ✒️ On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5 You'd like this New ❤️ Story CHAPTER 4 Asubar fari na yi, Sarah da Jinah suka fito da shirin zuwa asibitin dake kauyen. Suna fitowa, suka ga Safiya ce matar Lasaini kadai ta tashi, sauran har yanzu bacci suke. Bakin murhu take tana kokarin kunna wutar dumama tuwan karin kumallo. -"Mat arango Safiya?" Ina kwana Safiya? Sarah da Jinah ne suka gaisheta da yaren zabarmanci, ko kuma dai nace Sarah, dan Jinah tana cikin tashin hankalin da magana ma wahala take mata. -"Samaï day no. Mat ni kani bani?" Lafiya lau, an tashi lafiya? Safiya ta amsa masu gaisuwar. -"Samaï day no wallah." Lafiya lau wallahi. Sarah ta fada kafin tace -"Jinah sigama inga gahamo kani, aygo ga dum loktoru koira." Jinah bata jin dadi, shine zan raka asibiti. -"Ayyah! Irkoy madi ase, ma konda aran bani." Ayyah! Allah ya koro sauki, sai kun dawo. -"Aminna, kala tonton." Amin sai mun dawo. Hanyar asibiti suka dauka. Jinah har yanzu shiru babu alamar magana, duk tsoro da fargaba sun mamayeta. Bayan yar doguwar tafiyar da suka yi suka karaso asibitin, ba wata babbar asibiti bace kasancewar kauyuka irin Mambila sun fi ganewa yin maganin gargajiya akan na bature. Bayan sun je sun ciri tikitin ganin doctor. Kusa da Jinah Sarah ta zauna, ita kuma sai ta dora kanta bisa kafafun Sarah, Hankalin Jinah a matukar tashe yake tun jiya da Sarah ta tambayeta ko ciki ne da ita. Lallai idan dai ya tabbata ciki ne da ita, ta shiga uku dan bata san waye uban yaron ba, shin ta yaya ta samu cikin kuma wanne lokaci ne hakan ta faru. Addu'a ta cigaba da yi Allah yasa ba ciki bane, duk da tasan yanayinta yana nuna mai alamar mai ciki ne. Juyar da kanta tayi jin hawaye na son zubo mata. Hankalinta ne ya kai kan maganganun wata mata da bata zata wuce shekaru 50 ba da wata matashiyar budurwa da ba zata wuce 17 ba duke tana rizgar kuka. -Me kike so na fada ma ubanki? Kin bani kunya Nana! -Wallahi Mama ki yarda da ni, ba abinda nayi! -"Ah to Nudu gunde par magie?" Ah kina nufin a ruwa kika shashi ko me? Kin bani kunya Nana, yanzu da wane ido zan kalli mutanen kauyen nan? Shikenan kin ja mutanen kauye su zageni suce na sakeki kin je kin yi ciki. To sai ki sani inda dare yayi maki dan yau kam ba dai a gidana ba, ni kinga tafiyata! Juyawa matar tayi ta tafi cike da damuwa, ta bar yarinyar durkushe tana kuka. Mutane sai kallonta suke amma ita ko a jikinta. -Bari naje na samo mana abin kari. Cewar Sarah tana mikewa, gyada mata kai kawai Jinah tayi. Bayan tafiyar Sarah, Jinah matsawa tayi kusan yarinyar dake kuka. -Yi shiru ki daina kuka, kar ki sawa kanki wani ciwon. Jinah ta fada cikin sigar lallashi, ba tare da ta dago kai taga mai lallashinta ba, ta fara ba Jinah labarin abinda ya faru. Haka na kasancewa ga kowa, idan muna cikin damuwa mu kan so mu bayyanawa wani ita ko da ba zai iya yi mana maganinta ba kawai dai hakan nasa muji damuwar ta ragu. -Na rantse da Allah ban yi komai ba, ni ban ma taba sanin yaya gaban namiji yake ba indai ba na yaro karami ba, ni ko saurayi banidashi, ba abinda na sani in ba karatu ba, ba anan kauyen nake ba, ina karatu ne a Niamey (babban birnin kasar Nijar). Nazo nan hutu ne, gashi yanzu wai nice da ciki, to wa yayi min shi? Yanda take bada labarin da yanayinta zai tabbatar maka ita iya gaskiyarta take fada, hakan ya zama ruwan dare a kauyuka ba dama yarinya tazo daga birni, abin kamar maita. Haka saurayi zai je ma yarinya da sigar yana sonta, daga nan zai yaudareta, yayi mata ciki, in ma da saninta, ko kuma yayi mata asiri, ko kuma ya zuba mata wani abu a abin sha ta sha, daga nan ya gudu ya barta da taraddadi. Shikenan fa rayuwar yarinya ta lalace, haka zaka ga wasu sun zama karuwai, wasu su kashe kansu, wasu kuma ana samun maza masu tawakkali da dogon ilimi su auresu. Allah ya kyauta! Hankalin Jinah kara tashi yayi jin labarin yarinyar gashi yana kamanceceniya da nata, sai dai ita tana ganin Sarah bata koreta bane, ganin ba a tabbatar da nata cikin ba. Lokacin da layi yazo kanta, lokacin yarinya mai kuka ta tafi, Sarah ta dawo har sun karya. Wani bugawa zuciyar Jinah ke yi da sauri sauri dan da tafiyar hawainiya ta shiga ofishin doctor. Yana zaune yana duba wasu takardu, ba tare da ya dago kai ba yayi masu izini da zasu zauna, tareda cewa -Ku dan jira yanzu abokin aikina yazo ya duba marar lafiyar. Ganin har lokaci ya dan ja, abokin aikin nasa bai zo ba, ya dago kai yace -Tinda har yanzu bai zo ba, bari ni na dubaku. Yanzu fada min me yake damunki? Ya fada yana kallon agogo. Sarah tace -Kwanan nan ne take fama da zazzabi da tashin zuciya, shine muke son sanin ko... -Ko me? -Ina son sanin inada ciki ko a'a! Jinah ta fada dan ita ta matsu taji wanne hali take ciki. Bayan yan gwaje-gwaje da doctor yayi, ya tabbatar masu da Jinah tana da ciki. Doctor ya basu shawarar suna iya sake zuwa wani wajen ayi masu gwajin dan kara tabbatarwa sai dai ita Jinah batada wannan ra'ayin. Fita tayi daga asibitin da dan gudunta Sarah ta bita a baya. Sai dai Sarah bata yi nasarar cimmata ba sai da suka kai gida. -Kalleni nan Jinah. Sarah ta fada, cusa kanta tayi cikin katifa tana kuka. Ba wai tana kuka bane dan tanada ciki, a'a tunawa ne tayi matar nan ta dazu a asibiti dake hantarar yarta dan tayi ciki. Gani take itama haka Sarah zata yi mata, tasan itama haka mutanen garin zasu rinka nunenta suna zaginta. -Ki daina kuka Jinah, nasan ke ba irin wannan yaran bane masu kai kansu ga maza. -Kinada tabbacin haka Sarah? Idan fa saboda hakan ne aka koreni daga gida? Jinah ta fada tana fito da kanta daga cikin katifa. -Me kike cewa haka? kika sani ko kinada aure ne? -Ki duba fa samari nawa suka zo neman aurena, ai ba wanda aka taba fadawa inada aure. To yanzu kina tunanin akwai wanda zai yarda idan aka ce na taba aure ko inada aure? Yanzu wane kallo kike tunanin zasu yi maki keda kika bani mafaka? Ina ga zan yi tafiyata kafin mutanen kauyen nan su gane har na ja maki abin kunya... Kuka ne yaci karfinta. -Eh na sani dole zasu yi ta fada, dan kina karkashin kulawata ne, kuma hakan ba zai yimin dadi ba. Amma hakan kasheni zai yi? ko kwantar dani zai yi rashin lafiya? A'a ba fah abinda zai sameni. dan haka ki daina wannan kukan ki natsu muyi tunanin samun mafita. Mikewa Jinah tayi tana goge fuskarta tace zata je bakin kogi. Sarah bata hanata ba don tana ganin wata kila hakan zai ragewa Jinar damuwa. Da zuwanta bakin kogi ta zauna ta hade kai da gwiwa. Zuwa cen taji kamar kana kallonta, juyawa tayi taga Dauda ne, karasowa yayi ya zauna gefenta. -Yaya kike? -Lafiya lau. Ta bashi amsa a takaice. -Anya dai? Ya fada yana kare mata kallo, dan ya hangi damuwa a tattare da ita. -Na fada maka lafiya nake. Ta fada a dan tsawace. Duk da hakan bai hakura ba ya kara tambayarta. -Fada mun me yake damunki dan Allah? -Kaga ko na fada maka ba abinda zaka iya yi a kai, kuma wai wane sani ne nayi maka da har zan fada maka damuwata? Dan haka ka rabu dani. Duk wannan maganganun da ta fada mashi, basu hanashi yin dariya ba. -Abin dariya ma ya baka kenan? Dan Allah ka rabu dani. -Fushi baya maki kyau, kanki sai ya koma wani kala abin dariya. Ya fada yana dariya. Ganin so yake ya kara bata mata rai yasa ta mike da niyyar tafiya. Da sauri yace -Yi hakuri dawo ki zauna dan Allah, duk da bansan me yake damunki ba, amma na damu ganinki cikin wannan hali. Dawowa tayi ta zauna, sannan ta bashi hakuri akan daga masa murya da tayi dazun. Ya nuna mata ba komai. Cewa yayi ta fada masa abinda ke damunta, amma taki. Rokonta yayi ta yi akan sai ta fada mashi, ganin nacin da yake mata, kuma ita kanta taji tana son ta bashi labarinta. Dan yan kwanakin da suka yi a tare ta fahimci Dauda mutum ne mai tausayi da kuma barkwanci. Sai dai tana tsoron idan yaji tanada ciki ya kasa fahimtarta. Daga karshe dai yanke sharawar ta fada masa tayi, bayan ta gama bashi labarin yace -Yanzu kina nufin babu

Chapter 3 of 19