ya kasa cewa komai, shi ma zauna yayi a kasa, ita kuwa Jinah ta haɗe kai da gwiwa. Shuru wurin yayi kamar na wasu mintuna kafin Infa ya katse shurun da cewa :
-Bai zama dole sai ka koma wajen ta ba, ni da ƴan biyu zamu yi ƙokarin kare ka.
Kowa a wurin sai da yasa rai a kan plan din Infa kafin Dauda ya sare musu gwiwa da cewa :
-Tana controlling duk wani motsi na ne daga nesa, sau da yawa nasha kokarin guduwa, amma bansan ta yaya ba, sai na ga na kara komawa gare ta.
-Shedaniya! A hannun ta kake!
Cewar Infa.
-Lokacin da baba na ya mutu, ban ji wata damuwa ba domin nasan ina da kai, a gare ni, kafi baba na, kar ka tafi ka barmu baba.
Cewar Ayu, cikin yanayin nuna tsantsar kaunar da yake wa Dauda. Shi ma Dauda cikin bakin cikin zai rabu da su yake, amma ba yanda zai yi. Dauda rungume Ayu yayi, sannan yayi wa Aya nuni da ta taho. Ita ma kamar mahaifiyar ta, tashin hankalin da take ciki marar misaltuwa ne, ta yanda daƙyar ta iya buɗar bakin ta tace:
-Bana son ka tafi, kar ka barmu dan Allah.
Kara ƙanƙame su sosai Dauda yayi, shi kanshi baya son rabuwa da su.
-Jinah! Jinah! Jinah!
Suka yo kan Jinah gaba ɗayan su, ganin ta zube kasa bata motsi. Cak Dauda ya ɗauke ta, ya kwantar da ita kan gado, su kuwa yaran suka yi waje kiran Sarah da sauran.
Dubawa suka yi, suka ji tana numfashi. Kumatun ta ya dan tattaɓa, a hankali ta buɗe ido.
-Sannu Jinah, duk wannan mai wucewa ne wata rana. Nasan kin gaji, kin sha wahala sosai, amma ina son ki sani komai yana da karshe.
Dauda ke faɗa mata haka, yana mai shafar fuskar ta. Wahala ta rayuwa dai Jinah ta ganta, kuma fiye da haka na tafe.
*****
-A ina nake? Kuma ke wacece? Sannan ni waye?
Farkawa yayi, ganin wata mata da bai san ko wacece ba, Gashi shima kuma bai san ko waye shi ba.
-Ni shugabar ka!
Ta bashi amsa a taƙaice.
-Ina jin ƙishi!
Ya faɗa yana taɓa makoshin sa. Miƙo masa tandu biyu tayi, dayan ɗauke da ruwa, ɗayan kuma da jini a ciki domin ta tabbatarwa kanta a yanayin da ya tashi. Eh Fally ya dawo daga duniyar matattu, ƴan biyu sun ɗauka karfin su bai iya tayar dashi ba, amma ba haka bane, domin da sun ƙara hakuri na wani dan lokaci toh zai tashi a gaban su. Hindu kuwa tana laɓe lokacin da suke ƙoƙarin tayar dashi, kuma tasan sun iya, sai ta ƙyalesu, suna bada baya tazo, anan taga zuciyar sa na bugawa. Farin ciki ne fal a ranta. Idan aljani ya mutu, sannan aka yi kokarin tashe shi, toh fa yana tashi ne tamkar jariri, babu komai cikin kan sa, toh daga nan zai fara daukar sabbin abubuwa, walao sharri ko alkhairi.
Fally mika hannu yayi, ya karbi tandu mai dauke da jini, ya shanye a take. Hindu kuwa daɗi ne ya lulluɓe ta.
-Zamu je mu ɗauki fansa!
Hindu ta fada cikin karaji.
-Fansar wa?
-Ta makiyan mu, da suka cutar da mu, kuma dole su biya.
-Dole zasu biya!
Shi ma ya sake maimaitawa.
-Ina son ka san wani abu, ni shugabar ka ce, kuma dole ka bi umarni na.
-Yanda kike so Shugaba, zan iya samun ƙari?
Ya faɗa yana nuni da tandun jini.
-Zaka samu, kuma sai ya ishe ka, mu je lokaci na ƙurewa! Jinah da dangin ta zasu ji daɗin ganin mu.
Cewar Hindu da sigar sheɗanu.
Kamar kyaftawar ido, suka bayyana a ƙofar gidan su Jinah. Sai dai basu shiga ba, suka tsaya bakin ƙofar, domin tasan ko su waye ƴan biyu. Don haka dole sai sun yi taka tsantsan.
-Infaaa! Infaaa!
Fally ya shiga ƙwalawa Infa kira bisa umarnin Hindu. Kiran kuwa ya isa kunnen Infa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya bayyana gaban su, ba tare da ya fahimci meke faruwa ba. Fally ne a gaban sa, bai gama mamakin ganin Fally ba, sai ya tsinkayi Hindu a bayan Fally, nan ya gama yankewa kansa wannan ba alamu bane mai kyau.
-Fally...am..amma ta..yaya..
-Kai Fally bamu da lokacin yi masa bayani ka kashe shi!
Hindu ta umarci Fally, murya cike da karaji. Ba tare da wani tunani ba ya cika umarnin ta. Infa bai samu lokacin maida martani ba, bare kuma ya kare kansa, sai lokacin da yaga jinin sa na zuba sannan ya fahimci meke faruwa, Hindu nada babban makami, kuma Fally ne makamin nata.
-Mun gama da wannan! Ɗauke gawar ka jefar, sannan ka dawo.
Cewar Hindu.
Ƴan biyu ne suka karaso wajen, ganin mahaifin su yasa suka kwaso a guje suka nufo shi, ba tare sun yi tunanin ta yaya mahaifin nasu ya tashi ba, har da Ayu da tuni mutuwar baban nashi ta fara taɓashi. kafin su karasa jikin sa, tuni Hindu ta tsikarawa kowannen su, wata allura a gadon baya, fadawa jikin baban nasu suka yi summamu.
-Yauwa! Yanzu ka shiga gidan, kaji daɗin ka, kayi yanda kake so da mutanen gidan, ka sha jini iya son ran ka.
Bata jira jin amsar shi ba ta ɓace da ƴan biyu.
Ɗaki na farko da Fally ya tarar shi ne na Jinah, tana kwance ita kaɗai bisa gado, idanun ta a rufe, da alama sauran sun fita ne sun barta domin ta huta.
Matsowa Fally yayi sosai kusa da Jinah, santin kyawun ta ya shiga yi, kasa motsawa yayi kamar bai taɓa ganin halitta mai kyau ba irin Jinah. Yatsun sa, ya tura cikin gashin kanta, sannan yabi tsawon gashin, tare da janye wani daga gashin da ya rufe mata fuska, anan ya kara shaida kyan da take da shi. Kasa controlling kan sa yayi na son taba jikin ta, anan ya shiga yawo da hannun sa kan fuskar ta. A hankali ta bude idanun ta, idanun ta cikin idanun sa, numfashin su ya hade, shuru ya mamaye ko'ina, ba tare da bata lokaci ba, Fally ya tsinci laɓɓan sa cikin na Jinah, ita ta fara sumbatar sa, kafin shi ma ya biye mata. A hankali sumbatar ta kara karfi, daga nan suka lula wata duniyar, sun sha soyayya kamar ba zasu dena ba. Duk wasu sassan jiki na Fally magana suke, yana jin tamkar ana saka masa lantarki. Bai fahimtar meke faruwa, amma yana jin abun da karfi sosai da haɗuwa iya haɗuwa, zuciyar sa na wani irin bugawa da za'a iya jiwowa daga nesa, numfashin sa na yin sama-sama. Yanayin ya dauke su wani dogon lokaci, dukan su biyun suna jin su tamkar a wata duniyar da su biyu kaɗai zasu iya rayuwa a ciki, kuma domin rayuwa a cikin ta, dole sai sun rayu tamkar a gangar jiki daya.
Ƙarar da Jinah ta kwalla ne ya kawo karshen yanayin da suke ciki, Fally ne ya gatsa mata wani cizo a gadon baya, ba da gangan ba. Jin ɗanɗanon jinin a bakin sa ya dawo dashi duniyar mu. Jinah tambayar kanta take :
-Me yasa nake jin zafi alhali mafarki nake?
************************
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story
CHAPTER 27
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
Ganin Jinah da kuma yanayin da suka shiga a yanzu, yasa Fally ɗorawa kan sa wasu tambayoyi da ya kasa samun amsar su : "Me yasa nake jin damuwa akan wata halitta da ko sanin ta ban yi ba? Me yasa nake jin ina bukatar ta a kusa da ni? Me yasa zuciya ta ke jin zafi domin na cutar da wadda kasheta nazo zan yi? Me yasa bana jin sheɗancin dake jiki na domin ina kusa da ita? Me yasa lokacin da jikin mu ya haɗu, nake jin zuciya ta kamar zata fashe? Me yasa ganin hawayen ta, nake jin tamkar ana zuba min ruwan zafi a jiki?"
Zafin da Jinah take ji ne ya dawo da ita hayyacin ta, iya karfin ta tasa ta ture Fally, sannan ta jawo lullubi ta rufe jikin ta, zuciyar ta na wani irin bugu. Kallon kallo suka shiga yi, nan Jinah ta gasgatawa kan ta da ba mafarki take ba.
-Fally?
Cewar ita cike da mamaki. Shi kuwa bai bata amsa ba.
-Wai mafarki nake ne?
Ta sake maimaitawa.
-Ke wacece a gare ni?
Ya bata amsa da wata tambayar.
-F..Fa..
Wannan karon rawan tsoro take, domin ta gasgata Fally ne da kan shi, sai dai ya manta ko wacece ita. Nan kalaman Infa suka dawo mata : "Zai iya tashi a sheɗani." Tsoron ta kara daɗuwa yayi.
Fally rage dan nisan dake tsakanin su yayi, ita ta ƙwalla kara sosai, wadda ta janyo hankalin Sarah, ƴaƴan mijin ta da kuma Dauda. Ba tare da wani tunani ba, suka kwasa zuwa dakin Jinah, nan suka ganewa idanun su, wani ƙato na kokarin cutar da Jinah. Kafin suyi wani ƙwaƙwaran motsi, ya ɓace da Jinah akan idanun su, Sarah da Nafisa zubewa suka yi sumammu. Jinah da wannan mutumin da basu san ko waye sun bace a gaban idanun su. Shi kuwa Abdul kasa motsawa daga inda yake yayi. Dauda ne kawai, ya karasa daidai wurin, hankalin sa a tashe. Nan ya shiga dukan bangon, da sa ƙafa yana kutufo da duk abinda ke kusa da shi. Yau ne yake bakin cikin rashin karfin kwato Jinah, baida wata dabara ta sanin inda zai ga Jinah, babu wanda zai iya taimakon sa a yanzu. A take ya tuna da ƴan biyu su zasu iya taimakon sa, sai dai daga baya jikin sa yayi sanyi, domin yasan da ƴan biyu na cikin gidan da su zasu fara kawowa mahaifiyar su ɗauki, ko kuma Infa yana ina? Rashin ganin su, bai nuna masa alamu mai kyau.
Fita yayi daga ɗakin ya bar sauran cikin yanayin rudu. A bakin ƙofar gida, Dauda ya shiga dukan kan sa da hannayen sa. Idan ka gani zaka ɗauka mahaukaci ne sai dai shi yasan me yake yi, domin yanzu wannan hanyar ce kaɗai zata sa ya samu wata solution; yana son ya fitar da Jinah daga kan sa, domin aljanin dake jikin sa ya dawo aiki. Yasan akwai haɗari yin hakan amma wannan ita kaɗai ce damar sa. Sai dai hakan ba sauki gare shi ba domin ya kasa fitar da hoton aljanin da ya gudu da Jinah daga cikin kan sa.
Daga karshe cuisine (kitchen) ya nufa, ya ɗauki wata ƴar ƙaramar wuƙa, ya saita daidai hannun sa, ya rufe idanu tare da cije hakoran sa, sannan ya cakawa hannun sa wuƙar. Wani ihun wahala ya saki, sai dai ya ci nasarar abinda yake son yi, zafin da yaji na dan lokaci yasa ya manta da Jinah, a take aljanin jikin sa ya ɗau aiki. A nan yaji babu alamar aljani cikin gidan. Babu Infa, babu ƴan biyu a cikin yankin gaba ɗaya. Tunanin sa na farko ya kai kan Hindu, ba ɓata lokaci, sai gashi ya bayyana a maɓoyar ta. Bai yi mamakin ganin ƴan biyu kwance a wurin, ba a hayyacin su ba. Ƙoƙarin zuwa yayi inda suke, Hindu ta daka masa wata tsawa :
-Me kake yi a nan?
-Ba ni nayi miki alƙawarin zan kawo miki su ba?!
-Na samu wata hanyar da tafi take. Wai ya ma aka yi bai kawar min da kai ba?
Waro idanu Dauda yayi, da mamaki.
-Wa kenan? Wani kika tura ya kashe ni?!
-A'a ya kashe ku dai! Domin baka da wani sauran amfani gare ni.
-Kenan shi ne ya ɗauke Jinah? Waye wannan?
-Hahah, sheɗani na, Fally!
-M..me? Bai mutu ba?
-Eh, amma kai yanzu zaka mutu.
Wani irin bugu zuciyar Dauda tayi. Tunani ya fara : A'a ba zan bari ta kashe ni ba, wa zai ceci Jinah da yaran ta? Hindu zata haɗa musibu da dama idan har tayi nasarar mallakar karfin ƴan biyu. Hannu yasa ya danna ciwon da ya jiwa kan shi dazu, take zafi yasa ya manta da Jinah, aljanin ya sake dawowa, Dauda ya ɓace daga wurin, sai dai cikin rashin sa'a yana dira inda yake tunanin ya gujewa Hindu, sai gata itama ta dira a wurin.
-Na roƙe ki kar ki kashe ni!
-Na ƙyale ka, kaje ka aikata wani abun a bayan ido na ko, ai nasan yanda ka damu da Jinah da ƴaƴanta.
-Zan fitar da su daga tunani na, sai aljanin dake jiki na ya dawo aiki, kuma kinsan irin biyayyar da yake miki.
-Bari nayi tunani...
Jim tayi kaɗan kafin tace "A'a!". Yatsu kawai ta ƙyasta sai gasu sun dawo maɓoyar ta. Tattaɓa jikin sa Dauda ya shiga yi, domin ya ɗauka ko har ta gama dashi ne.
-Kar ka damu, zaka jira na dan lokaci, zan ji da kai daga baya, yanzu zan ji da waɗancen ƴan biyun, domin gubar da na basu ba mai daɗewa bace.
Cewar Hindu. Kokarin motsawa Dauda yayi, amma yaji kamar an riƙe masa ƙafafuwa, nan ya fahimci tayi hakan dan kar ya sake wani yunkuri.
Wani jan ƙyalle Hindu ta shimfiɗa a kasa, sannan ta zuba wasu ruwa dake cikin wata kwalba da ta bayyana a hannun ta. Matsawa tayi kusan ƴan biyun, sannan ta dauko Ayu. Roƙon ta Dauda ya shiga yi da kar tayi, amma kamar ma yana zuga ta. Kwantar da Ayu tayi kan jan ƙyallen. Sannan ta shiga karanto wasu kalaman tsafi, wanda dakyar na iya gano kalmar : "Uwar gijiyar sammai da kassai!"
-Ki dakata Hindu, ki daina na roƙe ki! Dauda bai yi kasa a gwiwa ba, yana cigaba da roƙon ta, yana kuka kamar jinjiri sabon haihuwa dake jin yunwa. Duk da namiji ne shi, amma bai damu da irin kukan da yake ba, domin zafin biyu ya zamar masa, na farko saboda shi, yana ganin za'a kashe masa ɗa, sai kuma Jinah, wayyo Allah, idan aka fada mata ɗanta ya mutu, ba lallai bane ta iya jurewa ba.
Da taga ya fara isarta da raki. Wani surkulle Hindu tayi bakin Dauda ya rufe, ta mayar dashi kurma, babu abinda ya iya yi yanzu face hawaye. Wata ƙar karamar sanda ta ɗauko, wadda take da tsini kamar mashi. Hannun ta ta kai kan tsinin, nan take ya soketa sai ga jini. Wata mahaukaciyar dariya tayi. Da wannan karamar sandar ta zana croix (cross) bisa kirjin Ayu, kafin ƙyaftawar ido ta cakata a tsakiyar cross din dake kirjin Ayu. Ba ɓata lokaci sai ga wani bakin hayaki na fitowa daga ƙirjin Ayu zuwa jikin Hindu da ta ɗaga hannuwa sama cike da jin dadi.
*****
-Ka taimake ni, ni kuma zan amsa maka duk wasu tambayoyin ka.
Cewar Jinah. Mamaki ne ya kama Fally, tambayar kan sa yayi, ko dai karanta tunanin sa tayi. Sai dai ba haka bane, Jinah ta yiwa Fally farin sani, tasan idan har Fally yana da tambayoyin da ya kasa samun amsar su, ya kan yawaita motsa yatsun sa kamar mai jan carbi. Duk da yanzu alaƙar dake tsakanin su ta rushe, amma akwai wata alakar da tun kafin su je suyi aure akwai ta. Sun so junan su kafin aure, ya kula da ita tun kafin ta iya rarrafe, shi ya taimaka mata ta iya rarrafe, ya taimaka mata ta iya tafiya, ya kula da ita, ya saka kan sa a haɗari domin ta, ya sadaukar domin ta, ba sau ɗaya ba. Yanzu ya manta da ita, amma kuma zuciyar sa da ruhin sa sun san ita ko wacece. Akwai alaƙa mai girma tsakanin Jinah da Fally kuma babu abinda zai canja hakan.
-Ta yaya kike son na taimake ki?
-ƴaƴana, kafin ka shiga ɗaki na, nayi mafarkin suna cikin haɗari. Gashi yanzu ina tunani, kuma ina jin tsoron abi..abinda zai same su.
-ƴaƴan ki?
-ƴaƴan mu, ƴan biyu, Aya da Ayu!
-Su..suna tare da shugaba ta, Hindu.
-Mene? A'a! Ka cece su, nayi maka alƙawarin, zaka samu amsoshin tambayoyin ka. Hindu tana amfani da kai ne, kada ka yarda da wannan sheɗaniyar.
-Ke ma ba zan yarda da ke ba.
-Kalle ni cikin ido Fally, ka yarda da ni, dan Allah.
Dan jim Fally yayi kafin yace :
-Shikenan!
Da falar haka, ba'a dau wani lokaci ba, sai gasu sun bayyana a maɓoyar Hindu. Da isar su wurin, kasa ta fara girgiza, sama tayi jawur. Duk da wannan bai tayar da hankalin Jinah ba, dalilin tsinkayo ɗanta da tayi a kwance, jini na zuba, ga kuma wani mashi soke a daidai zuciyar shi. Numfashi ne ya fara gagarar Jinah, yin ƙarar ma ta kasa, lokaci guda ta koma tamkar marar baki. Ɗanta ya mutu, bata gasgata hakan ba, sai da taga ya koma normal yaro, da ba zai wuce shekaru uku ba. Idan jin zafi yana kashe mutum a take, toh da tuni Jinah ta jima da mutuwa domin zafin da take ji, ya wuce na misali.
Dauda yana nan a wurin, yana kallon ta, ba tare da ya iya matsowa kusa da ita ba, bare ya rungume ta, ya tayata bakin ciki, domin kafafuwan sa tamkar an saka siminti. Ba kuma zai iya faɗa mata : Kada kiyi kuka Jinah, kwantar da hankalin ki, kiyi juriya, Allah yana tare da ke, komai zai wuce, ke jaruma ce... saboda babu murya.
Shi kuwa Fally, ba tare da sanin dalili ba, wata shawara ta zo masa a kai, ya kashe wannan Hindun, abinda bai sani ba, shi ne : Karfin ta ya karu, ta yanda lokacin da yayi ƙoƙarin kai mata farmaki, naushi ɗaya tayi masa, sai gashi ya bugu da bango, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake kai mata wani farmakin. Wannan karon, a daidai ƙafafuwan Jinah ta jefo shi.
-Ki bar nan! Ni zan ji da ita! Ki gudu!
Cewar Fally, kafin ya sake miƙewa; Aya! Jinah ta shiga kiran sunan ƴarta, idanu ta shiga rarrabawa, cen ta hango ƴar tata a kwance. Wani karfi ne yazo mata, ta ɗauka a guje ta nufi wajen ƴarta, ɗaukan ta tayi ta rungume.
Gudu Jinah take iya karfin ta, ba tare da tasan inda take nufa ba, hawayen kuwa sun kasa daina zubo mata. Wata iriyar faɗuwa tayi, lokacin da Hindu ta dira gaban ta.
-Ita! Babu inda zata je!
A yanayin yanda Hindu tayi maganar, zai iya fasa kunnen mutum tsabar rashin dadi da tsoratarwa. Ita kan ta Jinah sai da taji zuciyar ta, ta canja bugu tamkar ana buga ganga. Fally ne ya bayyana a gurin tare da kaiwa Hindu wani mahaukacin naushi, a nan take su biyun suka bace, ita kuwa Jinah ta cigaba da gudun ta. Hakan ce tayi ta faruwa, kuma a ko da yaushe sai Jinah tayi tunanin tasu ta ƙare.
Fally ya gaji, kawai ya riƙe wuta ne, kuma kare kai kawai yake yi, domin ba zai iya hada ƙarfin sa da na Hindu ba, sake taso shi daga mutuwa, shi ya kara masa ƙarfi, sai dai ita Hindu nata ninkin ba ninkin nasa ne, domin cen dama ita mai ƙarfi ce, gashi kuma ta ƙara da na ɗaya daga cikin ƴan biyu, duk da ba duka ƙarfin Ayu ba ta kwashe, domin sai an ɗau lokaci kafin ta same shi baki ɗaya. Fally kam yayi ƙoƙari tunda har ya iya kai wannan lokaci yana gwabzawa da ita.
Amma yanzu, Karfin sa ya ƙare, ganin tsayuwa na shirin gagarar sa, ya shammaci Hindu, ya ɓace da Jinah, ya kaita gida. Sannan ya haɗa wata katangar tsafi a bakin kofar da ta hana Hindu shigowa.
-Gata nan zuwa! Gata nan tafe! Sheɗaniya!
Yo kan Jinah su Sarah suka yi, cike da ruɗu da farin cikin ganin ta, tuni suka dawo hayyacin su, sai dai yanzu kuma wani sabon tsoron ne ya shige su, jin abinda Jinah ta faɗa.
-Ku mu gudu daga nan, za.. Sauran kalaman nata suka tsaya a baki, ganin Fally ya faɗo daga sama a kan idon su. Kafin suyi wani yunƙuri tuni Surayya ta dira gaban su, cikin wata mummunar shiga. Jinah kara ƙanƙame ƴarta tayi cikin ƙirjin ta, Nafisa ta ɓoye bayan Sarah da Abdul.
Ita kuwa dan ta ƙara tsorata su, sai ta ɓacewa ganin su. Jinah ji tayi ana ƙoƙarin ƙwace mata ƴa ba tare da tana ganin ko waye ba, faɗa ta shiga yi iya ƙarfin ta domin ganin ƴarta tata bata bar jikin ta ba. Sake bayyana Hindu tayi rai a ɓace.
-Ya..ya aka yi na kasa raba ku?!
Hindu ta faɗa cike da ƙaraji da jin haushi.
-Ki bani ita, ni kuma zan rabu da ku!
Hindu ta sake faɗa, ita kuwa Jinah taƙi sakin ɗiyar. Hindu kallon Sarah kawai tayi, ita kuwa ta shiga kokowar ƙwatar numfashi kamar an shaƙe ta.
-Ki rabuta da ita, dan Allah!
Jinah ta shiga roƙon Hindu. Abdul ne ya taƙarƙare, ƙawadawa Hindu wani benci dake kusa da shi. Hakan da yayi kuwa, yayi nasar dawo da numfashin Sarah. Sai dai kuma hakan ya ƙara fusata Hindu, nuna hannu kawai tayi sai ga Abdul yayi sama, kanshi ya gauru da bango, ya faƙi sumamme.
-Abdul! Dukan su, suka kira sunan sa a tare. Da gudu yar uwar shi tayi kan sa tana jijjiga shi, tana kuka.
-Kin raba ni da ɗana, ki ƙyale min ƴata, ki bar min ita! Ki bar min ita!
-Ta kashe min dan uwa, mama!
Aya ta faɗa da wata ƙaramar murya, ta faɗi hakan ne ba tare da bakin ta ya buɗe ba. Da alama gubar ta fara raguwa.
-Ayu ya mutu mama, na sani, kuma naji a jiki na. Aya ta sake faɗa, har wa yau tana kwance jikin maman ta.
Hakan yasa Jinah ƙara shiga cikin ƙunci, kalamn ƴarta sun taɓa ta.
-Bani da lokaci! Ki bani ita yanzu kafin ta wartsake daga gubar, ko kuma na kashe su duka.
Hindu ta fada a fusace tana nuna su Sarah, Jinah kuka take iya ƙarfin ta, zaɓi tsakanin ƴarta ko Sarah, wadda ta zame mata kamar uwa, ƴar uwa, babbar aminiya... a taiƙace ita komai ce gareta. Sai kuma Abdul da Nafisa, mutanen nan biyu da take matuƙar so, waɗanda take jin kamar akwai wata alaƙa mai ƙarfi tsakanin su... Ta yaya zata iya wannan zaɓi.
-Ni ki ɗauke ni, ki rabu da su. Cewar Sarah. Wata mahaukaciyar dariya Hindu tayi.
-Babu wani amfani da zaki min!
-Mama, ki barta ta ɗauke ni. Cewar Aya, wadda maman ta ce kadai taji hakan, jin maman tata na shakku tace :
-Ki yarda da ni mama, komai zai tafi daidai.
-Ki ɗauke ta, amma kafin nan ki barsu su tafi, ki barsu su kai Abdul asibiti.
Cewar Jinah cike da dauriyar zuciya,tana mai miƙawa Hindu Aya. Ita kuwa Hindu tsabar murna, kamar ƙyaftawar ido, ta kai su Abdul asibiti, sannan ta dawo ba ɓata lokaci, ta ɗauki ƴar yarinya Aya, sai dai farin cikin nata bai wani ɗauki lokaci ba, domin Aya tuni ta ɓacewa ganin ta, daga kan hannayen ta.
-A'A! AHHHH!!! Hindu rai a ɓace, tayi wata kururuwa, ƙasa ta shiga girgiza, tuni guba aikin ta ya ƙare a jikin Aya, Hindu bata yi tsamanin abun ba zai mata sauki ba kamar yanda tayi fata. Ƙoƙarin kama Jinah take domin tayi garkuwa da ita, kafin Aya tayi wani yunƙuri, bata kai ga kudirin ta ba, taji wani abu na mata tafiya cikin jiki, kafin tayi ƙoƙarin kakkaɓe wannan abun, tuni har ya kai ga zuciyar ta. Wani masifaffen zafi ne taji da yabi kowanne sassa na jikin ta, razananniyar kara ta saki, kara mai bala'in karfi, karar da tafi wacce bokanya Karaba tayi, lokacin da Kiriku ya saka hakorin sa domin cire ƙayar dake a gadon bayan ta, wadda ta mayar da ita matsafiya.
Hindu durkushewa tayi kasa tana cigaba da ihun azaba, lokaci kaɗan Jinah ta hangi ƴarta, haƙoran ta datse kan ƙirjin Hindu, da take ta ihun neman taimako.
-Ki dakata Aya, cewar Jinah, sai dai bata da alamun dakatawa, kamar wani shedani ya shiga jikin ta. Da hakoran ta, ta yage duka fatar jikin Hindu, sannan ta saka hannun ta, ta fizgo zuciyar Hindu da tuni ta jima da mutuwa. Kuma Aya ta sani amma duk da haka bata dakata ba, kuma bata daina maimaita :"Ita ta kashe min dan uwa!" ba, hawaye na zubo mata. Ganin haka, Jinah ta taso ta janye ta, tare da rungume ta, tana lallashin ta.
-Jinah.
Dauda ne da ya karaso wajen ya kira sunan ta. Hannayen sa dauke da gawar Ayu.
-A'a, a'a, ba zan iya jure kallon sa, ba zan iya ba!
Jinah ta faɗa tana kuka, ganin gawar ɗanta. Ɗaki Dauda ya wuce, ya kwantar da shi. Sannan ya dawo da niyyar lallashin Jinah. Kukan Jinah ƙaruwa yayi da ta tsinkayi Fally a kwance dan nesa da ita, rarrafawa tayi wajen sa, ta shiga kokarin tashe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 19