Share this page
ta gano mutumin kirki ne, kuma sosai ƴaƴan shi suka shaƙu da ita. Suna jin daɗin kasancewa tare da ita, ba kamar idan Aya na gida suyi ta wasa. Wata rana, Fally da Jinah su kaɗai a zaune suna fira, Jinah ta kawo zancen da Fally ya tsani jin sa. -Zan mutu kafin kai. Ni kaga mutum ce, kiyasin shekarun da zan yi ba zasu wuce saba'in ba, wata kila tamanin, nayi masu yawa nayi ɗari. Kai kuma dubunnai ne a gaban ka. Wace kalar mace zaka sake a madadi na? Jinah tayi masa wannan tambayar domin ayi dariya, sai dai tuni taga yanayin Fally ya canja. -Ah habiby da wasa fa nake. -Toh bana son irin wannan wasa, ina shiga damuwa idan na tuna haka Jinah. -Toh yi hakuri na daina daga yau. Ta faɗa tare da shigewa jikin sa. Fally ya tsani ayi masa irin wannan zancen, domin yasan dole wata rana haka zata faru, shi yasa yake shiga damuwa sosai. Duk inda ke da rayuwa, akwai mutuwa, kaddara ce da babu mai iya guje mata. Sau tari, mu matasa, bamu cika tunawa da ita ba, mun fi tunanin tafi daukan tsofaffi. Abin dariyar ma, muna ganin yanda take ɗaukan matasa, yara kanana, hatta da jarirai, amma mu kullum tunanin mu mutuwa ta tsofaffi ce, har mamaki muke idan aka ce ta ɗauki matashi wane. Ya kamata mu daina yaudaran kan mu, mutuwa ba ruwanta da matashi, tsoho, talaka, mai kudi, mai kyau ko mai muni ne. Tana ɗaukan mu ne a lokacin da ta so ko a yanda ta so. Abinda da Sarah da wannan ahali nata suka fahimta kenan. A wata yammar litinin, dukan su suna gidan Ahmad, gidan da a yanzu Sarah take ciki tun bayan auren ta da Ahmad. Fally, Jinah, ƴarsu, Nafisa da kuma ɗan uwanta da ya daɗe da dawowa bayan wasu shekaru. Sun haɗu domin taya Jinah murnar cika shekaru 27. Suna cikin fira, cikin nishadi, lokaci guda suka bar jin muryar ta, bayan mintuna da yawa, alhali da ita ake ta surutu. Fally ne ya kai hankalin sa gare ta, mamaki yayi da ya ganta da alamun tana bacci, wani irin bugu zuciyar sa tayi. Aya dake waje tare da ƴaƴan Ahmad, ta shigo falon a gigice, da shigowar ta ta durkushe kasa, ta riga da taji a jikinta tun kafin ta shigo falon. Sauran mamaki ne a fuskokin su ganin halin da Aya take, har zuwa lokacin da suka ga Dauda na kokarin tashe da Jinah ya kasa. Falon yayi tsit, suna tunanin ta yaya hakan zai yiwu. Eh tabbas, Jinah rai yayi halin sa, Fally mikewa yayi tare da ɗaukan ta. Sauran basu fahimci komai ba, sai dai jikin su yayi sanyi duk da sun kasa gasgata abinda suke tunanin shi ya samu Jinah, sautin kukan Aya kawai ke tashi a falon. Fally nufa yayi da Jinah gidan su da ba nisa da na su Sarah, yana shiga ya kaita ɗakin su, ya kwantar da ita bisa gado. Shi ma kwantawa yayi kusa da ita, a take shi ma rai yayi halin sa. Amma kafin ruhin sa ya karasa fita daga jikin sa baki daya, yace : -Me kike tunani Jinah, dubunnan shekarun da suka rage min na rayu ba tare da ke ba, ba zai yiwu ba. Nima dole na mutu, yayin da nasan kema baki duniyar. Zuciya ta tana bugawa ne a tare da taki, babu abinda zan yi a wannan duniyar babu ke, ni da ke mun haɗu mun zama ɗaya, kuma ɗaya bata taɓa bada biyu ba. Sai mun haɗu a duniyar matattu, Habibty. Jinah was, is, kuma forever will be matar aljani. ----------------------------------------- ALHAMDULILLAHI, c'est fini lol. Bye bye matar Aljani. Ina fata kun faɗakartu, nishanɗantu, kun kuma ilmantu da wannan dogon labarin nawa. Sannan ina mika sakon gaisuwa ta ga masoya wanda suka jima suna bibiyar wannan labari. Allah ya bar hannu da kaifin ido. Ameen ya Allah An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 19 of 19