ace kai ka yanke wa talauci cibiya. Basa daga cikin irin waɗannan mutanen masu raina ƙarfin na ƙasa da su, don Allah kar ka ce za ka guje ni bayan sai da ka sanya igiyoyin sonka ka ɗaure mini raina dasu, wallahi zan sha baƙar wahala".
Tsaki mai dogon zango ya buga mini zai bar wajen na yi saurin riƙe rigarsa ya fincike. Ya fara tafiya ina bin sa a baya tare da yi masa roƙo da magiya ban damu da inda nake ba balle raguwar ɗalibai da suka yi mini farin sani suke bi na da na mujiya. Ban yi aune ba juyarwa da zai yi kawai na ji ya ɗauke ni da wani gigitaccen marin da sai na idanuna suka hango mini gilmawar baƙin duhu.
"Kashegin ƙarshe zan yi miki ƙi fita a harkata idan kin cika 'yar sunna a cikin iyayenki". Na buɗe baki da nufin bashi amsa idanuna suka sauƙa akan fuskar shugaban makarantar da Malam Saminu da suke kallon da dukkan alamo sun daɗe tsaye a wajen.
Wani tsaki ya kuma dokawa ya juya ya ɗauki hanyar ficewa daga makarantar, na sunkuyar da kaina ƙasa ina hawaye, in ban da so me zai haɗa ni da malam Suraj har ya yi mini wannan cin mutuncin a bainar nasi kuma na kasa ganin laifinsa.
Ofishinsa Shugaban makarantar ya ƙira ni tare da tambayata abinda ke faruwa, ban yi ƙwauron baki ba na feɗe masa biri har wutsiya tare da roƙonsa ya ba wa Malam Suraj haƙuri har ya rabu da ni. Kwantar mini da hankali ya yi sosai sannan ya ce na je gida tare da yi mini gargaɗin cewar kar na ƙara yin kuskuren bin saurayi inda yake.
Makaranta na wuce lokacin har sun fito daga gwajin, ina isa wajen hall ɗin na yanke jiki na faɗi sai buɗe ido na yi na gan ni kwance a asibiti ma'aikatan jinya tsaye a kaina. Tun su Momma da Hajiya da raguwar 'yan uwana suna yi mini faɗa da jin takaicin abinda na aikata har suka koma jin tausayina domin ko maƙiyina ne ya ganni dole ya yi mini ƙwalla.
Sai da Abban su yaya Sufyan ya tabbatar mini da cewar zai nema Suraj su zauna dashi sannan na ɗan dawo cikin hayyacina, bayan ya zo gidan mu da ƙyar da suɗin goshi ya bayyanawa su Abba cewar ko kyauta aka ba shi aure na ya yafe domin a cewar wai bani da kamun kan da yake buƙata daga wajen mace.
Na yi jinya tamkar ba zan cigaba da rayuwa ba, sai da na koma kamar mahaukaciya ba ni da aiki sai sumbatu ganin halin da nake ciki shi ke sanya su Abba ƙara tuntuɓar Suraj amma yana maimaita musu zance ɗaya. A lokacin yaya Sufyan da Yaya Sa'eed suka dawo bayan kammala karatun su na shekara biyu. Suka tarar da ni cikin wannan yanayin sun yi baƙin ciki matuƙa da kuma tausaya mini.
Ko makaranta bana iya zuwa dole na yi dipparing domin ba ni da nutsuwar yin komai. Bayan dawowar su da wata biyu yaya Sa'eed ya yi aure, ni kuma Anty Suwaiba ta ɗauke ni na kuma gidanta da zama sai da na yi watanni tara cur bana garin sannan na ciwon zuciyata ya soma warkewa. Yaya Sufyan ya sadaukar da lokacinsa wajen ba ni kulawa har na soma dawowa dai dai.
Ya hana ni na yi kaɗaici ya zamo abokin a gare ni kuma bangon da zan jingina a duk lokacin da nake tangal tangal. Ya wadata ni da komai kullum cikin rarrashin zuciyata yake yi.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam
LAMBA TA GOMA SHA TARA
Sai da aka ƙarar da zangon karatu cur bana nan ko jarabawa ban sama damar zanawa ba. Sai da daga bayan na dawo garin bayan na gama ciwon raunin dake ke cikin zuciyata da kullum yake ɗanye.
Yaya Sufyan ya sanar da su Abba yana so na sun yi matuƙar farin ciki. Abbanmu har da kukan sa don murna domin a cewar sa tun bayan faruwar wannan lamarin kullum cikin fargaba yake, bai san wanda zan kuma faɗawa soyayya dashi ba don ya fahimci cewar ina da rauni sosai, idan ba a yi dace da na ƙwarai ba sai ya yi amfani da hakan ya cutar da ni.
Ba a nema jin daga gare ni ba balle tambaya ra'ayina ina son shi ko akasin hakan duk ba a bani damar faɗin hakan. Gadan gadan aka fara shirin biki dole na lallashi zuciyata ta ƙarfi da yaji na tusa Yaya Sufyan a cikinta, ba don komai saboda farin cikin iyayena da kuma irin halaccin da yaya Sufyan ya yi a gare ni a lokacin da nake cikin tsanani.
Babu wanda ya damu da me nake ji a cikin raina, kowa gwaɗa mini kyawawan halayyansa kawai yake yi da yi mini don albarka. Momma ta ƙara ninka soyayyar da take gwada mini sai nan da nan take yi da ni. Na canza layi na kuma goge duk wani abun da zai sanya ni tunawa da malam Suraj haka nan na dage da kai kuka ga Allah. Na koma makaranta na cigaba da karatuna bayan na ƙara kwasa-kwasan da na yi diparing ɗin su kafin na zo na jona su Sakina da a lokacin su na aji biyu a jami'ar.
Tabbas Yaya Sufyan ya cika cikakken masoyin da samun irin sa a Wannan zamani sai an tona, sai kuma mai da ce gami da sa'a. Babu shakka ya nuna mini tsantsar soyayya kuma tsaftacceyi, soyayyar da yake bani 'yanci na faɗi ra'ayina akan komai. Na sha jin ana cewar maza ba sa karɓan laifin su balle har su ba da haƙuri, amma yaya Sufyan ya sha bambam da da yawan mazaje.
Ya kan karɓa laifinsa da ma wanda ba nashi ba na kuma bada haƙuri, haƙurin da ya amsa sunan sa ba irin na izgilanci ba.
Ɓat hotunan abubuwan da suka wakana masu motsi suka ɓacewa ganina, na dafe kaina da nake jin tamkar zai rabe izuwa gida biyu tsabar sarawar da yake yi mini.
Na matse jikina wajen guda wasu hawayen masu ɗumi suna fareti akan kuncina tare da zarewa izuwa tudun wuyata. Na saki bayyananniyar ajiyar zuciya tare da buɗe rinannun idanuna na zubawa wayata. Har yanzun bai ajiye mini wani saƙon ba kuma ya ga rubutun gobe ɗaurin aurena da aika masa.
Figigi na dawo hayyacina tare da ɗauke idona daga kan wayar jin ana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin. Muryar Sakina ce na ji tana ƙiran sunana tare da ɗaurawa"lafiya kuwa?. Kina ji na?".
Sai da fesar da zazzafan iska daga bakina na ce"lafiya ƙalau". Na miƙe akan ƙafafuna da suke rawa na isa ga famfon da na buɗe yana zubar da ruwa na wanke fuskata sannan na ɗauro alawala na riƙo wayata na fito.
Tana tsaye a ƙofar banɗakin ta ba ni hanya na wuce har na shimfiɗa sallaya ba ta ce da ni komai ba. Wutar ɗakin yana kunne ɗaiɗaikun ƙawayenmu suna bacci yayin da masu wayar dare da samarin su kuwa suke ta fama.
Raka'ar farko kawai na iya yin ta a tsaye amma na biyu a zaune na yi shi saboda juwan dake shammatar ƙafafuna. A zuciyata na yi addu'ar domin na gaza samun haɗin kai daga bakina wajen furzo da zancen dake cikina.
Sakina ta zo ta zauna a gabana tare da kafe ni da ido"Surayya wai lafiya kike kuwa?". Na yi mata kallo ɗaya na ɗauke kaina gefe"ga alama kuwa kin ga ni".
Ta jijjiga kanta"duk alamomin da suka bayyana a gare ki ba na mai lafiya bane, don Allah ki sanar da ni me ke faru".
Sai na yi ɗan jim kafin na ce"ki taya ni da addu'a kawai Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar". Ina dasa aya nan na miƙe tare da zage hijabin kaina na je na kwanta sai dai gabaɗaya bacci ya gagari idanuna, duk motsin da zan yi sai na duba wayata ko zan ga saƙon Suraj amma shuru tamkar an shuka dusa.
Har aka ƙiran sallan assalatu idanuna ƙar wani zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, sai na sha magani sannan na ji ɗan ƙarfi a jikina. Wanka ma da ƙyar na yi shi na fito fuskata a kumbure bayan na gama cin kukana a cikin banɗakin tare da ƙara aikawa Suraj saƙon cewar ƙarfe goman safiyar yau za a ɗaura aurena.
Shadda na saka ɗinkin doguwar rigar da ya bi jikina aka ɗaura mini kallabin da ya zauna a kaina ya yi mini ɗas. Sashin Hajiya aka kai ni na gaishe da ita da kuma ƙawenta da sauran dangi. Yaƙe kawai nake yi amma ni kaɗai na san zafin da nake ji a cikin raina da balbalin wutar raɗaɗin da nake ji a cikin raina. Ƙarfi da yaji Sakina ta raba ni da wayata a cewar ta wai ita take ɗauke mini hankali don haka za ta ajiye ta a wajen ta.
A masallacin da ke jikin gidan mu za a ɗaura auren, ina zaune bayan na canja shiga ana gyara mini kwalliyar fuskata. Na ji sanarwar an ɗaura aurena da yaya Sufyan. Kwatankwacin yanda gero ke tashi yayin casarsa a cikin turmi ya yi tsalle haka zuciyata ta yi tsalle. Da hakan ya sanya ni numfashina sarƙafe babu shiri na ɓarke da wani matsanancin tari mai ƙarfi.
Duk sannu suke jeranta mini wani na bin wani tare da ba ni ruwa, kafa kaina na yi na soma shan ruwan babu ƙwauƙwatawa sai da na shan tas sannan na koma sakin ajiyar zuciya tare da dafe kaina.
"Lafiya kuwa Surayyan?".
Kaina kawai na iya ɗaga mata mai kwalliyar ta cigaba yi mini, ana ɗaura mini kallabi Sakina ta sanya mini wayata a kunnena kafin na tambaye waye ne. Muryarsa yaya Sufyan cikin tsantsar farin ciki da annashuwa yana faɗin"alhamdulillah an ɗaura yau dai kin zama mallakina Surayya. Mun zama ma'aurata wallahi na rasa yana zan falsata miki farin cikin da nake ciki a yau. Zan tabbatar miki da cewar ba ki yi zaɓen tunin dare ba zan wadaci da dukkanin abinda mace take da buƙata daga wajen ɗan miji."
Ihu da shewan da 'yan ɗakin suka saka a tare suna hasko ni da kemarurin wayoyinsu, shi ya ankarar da ni cewar wayar a amsa-kuwwa take duk abinda yake faɗa suna yi. Shima dariyar ya yi"ku shirya zamu shigo da abokinsa". Daga haka ya kashe wayar kwatattun hawayen da suka ciko mini idanuna suka zubo.
Duk a zaton su hawayen farin ciki ne da murnar ganin wannan ranar amma ni a gare ni abun ba haka yake ba. Mun sha hotuna da dangi da abokan arziki, shigowar yaya Sufyan ya abokansa ya sanya wata tsohuwa sakin goɗa ana shelantawa ga ango ga ango.
Hotuna aka yi mana dashi sosai da kuma abokansa a kunnena yake yi mini raɗar cewar shiga ta da kwalliyata sun burge ni. Sadda kaina ƙasa kawai na yi ban ce dashi komai ba. Sai da aka yi sallan magrib aka kai ni wajen su Abba suka yi mini nasiha sosai mai ratsa jiki da haifar da nutsuwa a dukkan sassan jiki.
Haka nan ma Hajiya da kuma su Anty Suwaiba sai sauran dangi da suke ta yi mini fatan alkhairi da addu'ar samun zaman lafiya a cikin auren mu.
Tamkar wacce aka ciro daga cikin ruwan sanyi za a tsoma ta cika wuta haka nake jin kaina yayin da aka fito da ni za a sanya ni cikin mota. Kuka nake yi bil haƙƙi da dukkan ƙarfina amma haka aka ɓamɓare ni daga jikin Hajiya aka sanya ni a cikin motar.
Har muka isa gidan ban tsagaita daga sakin hawayen da nake yi, Sakina da Anty Sadiya suka tsaye a gefen hagu da damana. Suka umarce ni da na shiga da addu'a da kuma ƙafar dama.
Har cikin uwar ɗaka suka shiga da ni tare da ɗaura ni akan gadon da Abban su yaya Sufyan ya saya mini. Nasiha suka ƙara yi mini sosai tare da nusar da ni cewar na bi wa mijina biyayya akan dukkan komai matuƙar komai ɗin bai kaucewa komai daga cikin tsarin Allah da dokokinsa ba.
Alfarmar Anty Sadiya na nema akan ta bamu waje ina son ganawa da Sakina, kasancewar mai fahimta da sauƙin hali ba ta kawo komai a ranta ba ta tashi ta koma falo wajen su Anty Suwaiba da raguwar dangi da ƙawayena.
"Don Allah me yake damun ki?, shin kin gani cewar yaya Sufyan yana da wani mummunan hali ne da yake ɓoyewa ko kuma menene?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a sannan na yaye laffayar dake kaina na ce"maganar Suraj ne". Na yi mini wani kallo fuskarta ɗauke da mamaki ta ke faɗin"Suraj kuma?. Na yi tunanin su mun gama wannan maganar dake. Don Allah ne yasa kike son ɗaurawa kanki damuwar wanda bai damu dake bane. Wanda ya yi fatali dake a lokacin da kike tsananin buƙatarsa. Wallahi Surayya ina guje miki faɗawa cikin fushin Allah domin yanzu fa ke matar aure ce ".
"Son gujewa kaina ɗaukar zunubi shiyasa tun farko na zuciyata ta ke yi mini huɗubar na ce na fasa wannan aur.....". Kafin na ƙarisa ta yi saurin kai takufan hannunta ta rufe mini bakina"kar ki ƙara faɗin hakan kuskure ne, na roƙo ki don Allah kar ki sake ki yi maganar nan da wani ba don ni ba ki duba ko don soyayyar da yaya Sufyan yake yi miki shi da iyayensa ki manta da Suraj".
Tamkar ta ɗaba mini mashi haka na ji zafin zancenta na ƙarshe na kasa cewa komai, har izuwa lokacin da Anty Sadiya ta dawo cikin ɗakin tare da cewar na gyara ga ango nan da abokansa zasu shigo.
A falo muka zauna muka ƙara yi mana nasihohi tare da damƙa amanata gare shi, abokansa suka biya kuɗin sayan bakin sannan aka buɗe mini fuskata. Duk suka watse domin su Abba sun ce babu kwana a gidan amarya.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani
LAMBA NA ASHIRIN DA ƊAYA
Kai tsaye zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun 400 Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta nombobin 08068748984
Kai na ciwo yake yi mun ba na kaɗan ba haka na daure ba na son kwanciya nasan ya Ibrahim zai shiga wani hali sosai.
Anty Nusaiba ina son gaya miki wani magana amma bansan ya zaki ɗauki maganar ba sannan ina jin tsoron ya Ibrahim daga ya ganmu tare sai yace muna takura miki"karki da mu zo muyi maganar amma lafiya kuwa meyafaru?.
Ya kuke da wanda muka je shagon shi siyan kayan ɗinki ,a ina kika sanshi ya alaƙar ku ya ke da shi saurayin ƙawata ne Aisha Salisu Sharif sunyi soyayya da shi ,ada ya sota ,ita ma tayi mishi wani kalan soyayya a kanshi tafara soyayya wani abu da yake zuwa mata da shi wanda ta gagara gane hakan kullum sai yace sai ta tura mishi sufffan jikin ta,tun bata yadda tafara tura mishi gashi ba halayyar ta ba ce unguwar su ɗaya da shi nikuma tare mukayi secondary school da ita aminiya tane bata boye mun komai a haka.
sukayi shekara ɗaya da rabi da shi wannan shine aikin shi yanzu basa tare da shi sun rabu taga zuciyar shi babu Allah kinga gemun nan duk ta banza ne ,rana ɗaya in iskancin ya tashi ajiye ta yake matsalan a lokacin da yake neman ta ko shagon ba shida shi abubuwa dayawa a kanshi wani rana da ya tura mata photon jikin shi,a lokacin ƙanin ta ya ɗauki wayar kaman za,a kashe ta,a gida sai dai fuskar shi bai fito ba da,a sirin shi ya tonu mungu ne fuska biyu ne gare shi wallahi Allah sai ya sakawa Aisha na tsane shi gashi ya yaro ne sai zuciyar banza .
Numfashi na ja,yanzu wannan shine halayyar JB kenan shine yamun ƙarya tarabu da shi a she shine mungun Allah ya bimiki hakkin ki ya saka miki Aisha mata yawancin yadda da,amana da suke yi da saurin yadda da mutum shine babban kuskuren da sukeyi"ba komai laifi yayi shiyasa na nuna mishi ni nafishi wayo "ko dai kuɗin ki ya ƙarɓa ne bai biya kiba?"aa ba kuɗi bane abun da, nake so da ke shine don Allah karki gayawa ƙawarki munje shagon shi zaki rakani gidan su Aishan da yamma muje mu gaisa da iyayen ta bakince ke ƙawar ta bace zamuje ki shirya anjima kinji .
Duk yadda Aisha tayi tasan meke tsakanin mu da JB ban bata wani ƙofa ba illah kawai nuna mata nayi zan taimake shi da yamma muka shirya muka je gidan su Aishan yarinyar kekkewa da ita gata da fara,a sai Aishan ne ta nunani ga Anty na ku gaisa ƙaragaishe ni tayi "ni kuwa A'isha ya labarin ɗan iskan nan ne JB ya nanan makuwa?"ya nanan , bani da lokacin shi yaje duniya ce wanda bai zoba ma tana jiran shi ,ƙarya ce kawai yanzu in ance ya turo kuɗin gaisuwa gidan su budurwa ba shida shi abun da JB yayi mun har yanzu mama fishi take da ni duk da nace bansan wanda ya turo ba .
Allah ya kyau ta !
Bari mutafi duk abun da tafaɗa nayi recoding da zamu tafi har ɗaukan photo mukayi saboda tina ranan kash JB wannan in shine halin ka ,baka samu hali mai kyau ba in sha Allah macen banza ne zata zama matar ka yaudara da cin amanar soyayya sun zama ruwan dare naji takaicin yadda iyayen A'isha sukayi mata shi kuma ko a jikin shi gashi ta rufa mishi asiri taƙi bayyana siffofin shi ina son in ga ina kuka amma hawayen yaƙi zuba ban san dalili ba .
Muna zuwa ƙofar gida muka tarar da ya Ibrahim tsayawa nayi a kusa da shi a jikin mota shi kuma yana ta danna wayar shi "kunje unguwa ne "?
e munje unguwa gobe ki shirya zamuje gun likitan ki shirya da wuri ya tura miki number baki kira ba sai da nakira meyasa kike wasa da lafiyar ki ne haba Nusy ?
"Ina so ka bani labarin rayuwar ku da Fiddausi nasan ka yaudare ta ne kawai nasan kufa maza kuɗin ne sai a hankali" ba wani labarin da zan baki ina ruwan ki ,ne ke kin fi son abun da zai ɗaga miki hankali kenan bazan bayar ba ki shiga gida maza karsu kalle mun ke kinga sai kallon ki suke tayi .
Numfashi naja nayi kamar bada ni yake ba .
Ina ganin JB yana ta kirana ko ɗauka banyi ba haɗa ido nayi da shi ya Ibrahim naga ya wani daka mun harara kira ne ya shigo wayar tawa mum Muhammad ce ta Kirani bayan mungaisa "ya gida ina su Hajiya daman yayan kune matar shi ta haihu yau suna an samu Muhammad shine nace bari na gaya miki ".murna nayi tare da yiwa yaron addu,a Allah yasa ya biyo halin mai sunan shi na sanar mata bana gari amma ina dawowa zanzo in Sha Allah nayi godiya sai na tsinci kai na da farin ciki Allah sarki nima akwai takwara n ka a ciki na Muhammad ina son halayyar ka sosai
Buɗe Whatsapp nayi naga an tura mun hoton yaron take na ɗaura a status mutane da yawa, suka buɗe har da JB .
Suka tayiwa yaron addu,a Allah ya raya shi ya sha addu,a wasu cewa suke har yana kama da mai sunan shi rayuwa kenan.
Buɗe saƙon JB nayi
Yau she kika zo barno ya,akayi kika gane unguwar mu,ya akayi kikasan shago na wannan ya nuna kinsan ko mai agareni kenan ko kula shi banyi ba tun daga ranan JB ya daina wannan rawan kan irin na yan bana bakwai .
Photon mu nasa nida Aisha shine na uku da yagani ya ta,kira na sosai yakira yafi sau a shirin ko,in kula shi yayi mun magana ƙarshe har da muryan kuka karkisa nima nawa zuciyar ta fashe me ya haɗaki da Aisha meye a laƙar ku,da ita ? rubuta mishi nayi yar uwa ta ce..
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
MARUBUTAN JAHAR YOBE
Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam
Zaki sanya kuɗin ki 400 ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984
LAMBA NA A SHIRIN
Ya zama dole in bishi tunda Hajiya ta sa baki ga shi mai sunan mahaifin ta ne bata ganin laifin shi ko kaɗan .
bana son tafiya da ya Ibrahim gudu ne da shi ba ka,isa kayi mishi magana ba kamar zuga shi kake yi ,ga yadda hanyar take shiru nayi na shirya mana kayan mu ,nida Fatima ƙarfe goma muka bar damaturu mun kama hanyar barno ban gayawa Inna ina hanya ba sai dai ta ganni . In da zuciya ta zata ,amince da ta zaɓi mutumin da yake da kima da daraja agun kowa kash sai dai ita so duk ba ruwan ta da wannan,ina mamakin yadda ya Ibrahim yake nuna mun kulawa fiye da kanshi a lokacin da Muhammad ya rasu tamkar ɗan uwan shi tare muka wuce bauchi da shi sunyi sabo da mutune agun zaman makokin Muhammad .
Muhammad yana da zafin kishi, amma ban taɓa ganin ya nuna wa ya Ibrahim ba .
Tinani natayi da yawa a cikin motar shi kuma ƙaratu ya kunna yana taji Fatima tayi bacci a cikin tunanin da nakeyi har na tino in da zamuje bauchi da Muhammad muka tsaya a darazo yace mu tsaya mu gaisa da wata batada lafiya haɗe rai nayi nace wata kuma ni bazan jeba ya je ina cikin mota lokacin da muka je duba mara lafiyan a she na miji ne zolaya ta yake yi nikuwa kishi ya rufe mun ido wajen samun lada.
Babban mutum ne a she sunan shi TY wajen aikin su ɗaya naji kunya da yazo ya sameni a cikin mota ya gaishe ni abun da naji ,yace"Madam kin ɗauka wata ne ko shiyasa kikaƙi zuwa a hakan ma nagode sosai Allah ya bar zumunci na gode ".
A bubuwan masu matuƙar rikitarwa da ruɗani da zullumi Muhammad ya bar mun suna dayawa a rayuwa ta a kan alkairi zan ta, tina shi irin su JB ko da mutuwa sukayi babu abu mafi daraja da zan tina shi da shi sai jin maganar ya Ibrahim nayi yace "in kin shiga kicewa Inna na wuce gun aiki wannan key ɗin ɗaki nane ki share mun ɗan Allah ga kayan nan ku shiga da shi ".mai shara kamayar,dani ?ba zanyi ba in kadawo zakayi kayan ka ,kana da ƙanne kawani sani aiki sai kace wata matar ka kama hannun Fatima nayi muka ƙarisa ciki Inna nata rar tana tsaye ganina da tayi tace oyoyo uwata kece tafe babu waya kuma ?.
e Inna nice bazata zanyi miki shiyasa kika ganni .
Sannun da zuwa shiga ciki nayi na huta nací abinci nayi sallah har bacci ya ɗauke ni banga kiran JB ba tun safe a waya ta sannan bance ina garin suba akwai abun da nake son shirya mishi zan bashi mamaki kuwa sai ƙarfe takwas na dare ya Ibrahim ya shigo bayan na bada key ɗin ɗakin na shi a gyara mishi abun ka da mai tsafta komai a gyare ya ke kawai dai in da sabo ne an saba .
Sai kusan mangari ba kafun ya dawo duk muna falo muna ta shan hira yau sai naji damuwar da nake ciki a cikin kashi ɗari hamsin ya bar raina .
"Inna kiyi mun afuwa nawuce gun aiki ban shigo ba sauri nakeyi shiya sa ki yafe mun kinji" babu komai karka da mu hakan ma yayi tunda ka,kawo mun uwata kana kulawa da ita sosai ina godiya Allah yayi albarka .
"Amin ya rabbi ".
Washe gari da safe
Misalin ƙarfe goma na safe 10am bayan ya Ibrahim ya fita wajen aiki nima na shirya hijabin nan me rufe fuska da ko,ina na sanya na rufe fuska ta , yadda ko kasan ni ba lalle
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13