,kika fi waya gaya miki ana haka .
Shiru ya Ibrahim yayi jin mu kawai ya keyi "Hajiya a bita a hankali don Allah kar ciwon ta ya tashi yanzu an ba mu dokoki wajen kulawa da lafiyan ta,kuyi haƙuri zai wuce wataran .
Duk kansu ficewa sukayi daga ɗakin waya ta na ɗauko naga mutane da yawa sun Kirani har da JB ko kiran shi banyi ba ina riƙe da wayar naga ya sake kira ɗauka nayi "don Allah ki ɗaure ki dawo yadda kike don ina cutuwa yau she kika je barno ko gaya mun ba kiyi ba ? Jiya na dawo sati na biyu a cen lafiya kuwa kake tambaya na me ya faru dole ne in zanyi tafiya sai na gaya maka me ya faru .
An kai saƙo gidan mu, sannan an ce daga damaturu yaran kuma sunce wata ce na tabbata kece don yanzu ko mai nawa kin sani shi yasa amma hidimar tayi yawa ga nawa har da na iyaye na sun gode wallahi da,ina nan babu wanda zai karba .
Fa shewa da kuka nayi yanzu shikenan hankalin ka, ya kwanta kenan zan yi aure kamar yadda ka faɗa a baya in na samu miji in yi aure jiran ka gaibu ne zan yi tunda haka ,kace sannan wanda zan aura ya haɗa duk wani abu da nake buƙata hankali nasaba kima daraja babu ,abun da bai haɗa ba daman na gaya maka wataran zakaji abun da zai tarwa tsa,maka tunani .
Jinayi ya ce na shiga uku Nusaiba wallahi ba zakiyi aure ki barni ina waje ba ban shirya rabuwa da ke ba ko da rai na zaifi ta,ki tausaya mun karki gujeni wallahi na dai na duk abun da nake yi kiyi mun afuwa kuka ya keyi kamar an aiko mishi da mutuwa .
Ikon Allah
Yau JB ne ke kuka ina gadaran ina rashin mutunci ,ina jiji da kanshi tabbas in naga ba,ayi auren nan ba to ɗayan mu ya mutu, taya zan yi rayuwa da mutumin da babu son shi a raina amma zan yi ko da zan mutu koda shine zai zama,abu mafi muni a gareni ban taɓa ganin fishin Hajiya ba sai a kan auren Ibrahim ya JB zai yi ya zai yi rayuwa ba tare da niba ban son wani hali yake ba a yanzu na nafi son yaga mata suna da mutunci kar ya mana kuɗin goro nafi so ko da rabuwa mukayi yaga wasu matan da mutunci yau sanadin ƙadddara ya raba mu.
Jinayi ya Ibrahim ya kira sunana "Nusy kiyi haƙuri karki zargeni wajen an gama ko mai dani wallahi bansan ko mai ba ,ni ce mun a kayi in ci gaba da shiri wallahi bansan ko mai ba tunda bake ƙauna na zanyi nesa da ke har sai kin koyi sona kafun zan bari a yi auren in kuma kika ce bake suna zan tayaki neman wanda kike so don naga a lama a kwai wani a ranki ".
Zanyi magana ya dakatar dani
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
©️Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam
Zaki sanya kuɗin ki ta 400 wannan asusun Amina maaji Accounts no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan ta wannan number no 08068748984
LAMBA NA ASHIRIN DA HUƊU
Kowa ya watse aka bar mu mu kaɗai. Duk wani lallashi, lallami gami da kwantar da muryar da ya yi wajen ban haƙuri bai sanya ni tsagaita da kukan da nake yi da dukkan ƙarfina ba.
Cikin zuciyata ji nake yi tamkar ana sanya tsinin bakin mashi ana caccaka mini saboda tsananin azabar zogin da yake yi mini.
"Duk wannan kukan na menene Surayya? Don Allah ki yi haƙuri ya isa hakan nan, kar ki jawa kanki wani ciwon na daban".
Yanda ya yi maganar kaɗai ya isa ya bayyanar da irin tsananin damuwa da tashin hankalin dake tattare a dunƙule a cikin ƙirjinsa. Ya zube akan gwiwoyinsa a gaba tare da haɗe dukkan hannayensa biyu waje guda alamar roƙo"ko don ni don Allah ki yi haƙuri ku tsagaita wannan kukan, wallahi duk wani ɗigon ruwan hawayen da ya zuba daga idonki. Ji nake yi tamkar tafashashshen ruwan dalma ake watsa min".
Na ɗago rinannun idanuna na zube su akan fuskarsa da ya yi kalan tausayi, ya ɗaga mini kansa alamar tabbatar mini da gaskiyar kalaman da ya furta.
A bayyane na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina tausayin kaina da kuma hashashen irin rayuwar da zan yi a cikin gidan sa da soyayyar wani a cikin raina.
Dole na tsagaita don ganin irin damuwar da ya shiga, ya yi ta zabga mini addu'o'i da alƙawarin ƙawata rayuwata da farin ciki da jin daɗi.
Washe gari kafin na tashi na iske ya kammala komai, wanka kawai na yi na shirya don gabaɗaya bana jin daɗin jikina. Ya yi mana karin kumallo na ɗan cakala bisa takura mini da ya yi da marairaicewa.
Na zauna a falon shi kuma ya shiga yin wanka, ina ƙarewa tsarin falon kallo. Ya ƙawatu sosai domin irin design ɗin da ya turo mini na zaɓa shi aka yi kwabo da kwabo babu abinda aka canja.
Sai a lokacin na tuna da wayata da rabo na da ita tun ranar jiya, na tashi na koma ɗaki ina duba inda Sakina ta ajiye mini ita.
A cikin jakata na same ta na ɗauka na kunna, take saƙonni suka fara shigo da jerin ƙiraye ƙiraye da suka zama missed call ana bani bayanan su ta saƙo.
Ƙira bakwai rigis Suraj ya yi ga kuma saƙonsa da na latsa kansa na buɗe jikina yana rawa.
```"Na san ni har yanzu mai laifi ne a wajen ki. Amma na roƙe ki da girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara kar ji ba wa ko wani ɗa namiji damar kusantar ki Surayya. Wallahi ba zan iya jurewa domin zuciyata zata iya bugawa ki riƙe min amanar kanki, ko ba daɗe ko ba ji ma sai na cika alƙawarin da na yiwa kaina na auren ki".```
Take na ji gabaɗaya jikina ya soma rawa tamkar wacce ake jonawa wutar lantarki, zuffa ya fara tsatstsafowa daga jikina. Ganin ina gab da faɗuwa ya sanya ni yin zaman dirshan a ƙasa dafe da kaina da nake jin tamkar zai rabe gida biyu saboda tsananin sarawan da yake yi mini kwatankwacin irin bugun da maƙeri yake yiwa ƙarfe.
Na tsurawa saƙon kallon ina ƙara karantawa wasu hawaye suna zarya a bisa a kuncina. Tabbas so bai yi mini adalci ba domin ni a gare ni masifa da bala'i ya zame saɓanin wasu da yake zamowa silar farin ciki da annuri akan fuskokinsu.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u!".
Na furta a bayyane ina cije leɓena tare da lumshe idanuna, me ye mafita a gare ni? A ko yaushe Suraj zuciyata take hango mini a mahangar dacewa da ni ta kowacce fuska.
Jin kamar za a shigo ɗakin ya sa ni saurin miƙewa na mayar da wayar ciki jakar da na ɗauko ta, na nufi banɗaki na wanke fuskana na fito. Yana tsaye jikin ƙofar ɗakin ya haɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa tare da zubo mini idanu. Har na iso gabansa ni yake na yarfa hannuna a fuskar tare da ɗage masa idona ɗaya alamar lafiya.
Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana gyara tsayiwarsa"godewa kawai nake yi da ya mallaka min ke a matsayi mata, wallahi Surayya ina son ki irin son da babu wasu kalmomin da zasu wadatar wajen furta miki girman su ba. Na yi alƙawarin gusar miki da duk damuwarki ta hanyar ƙawata duniyarki da farin ciki marar yankewa".
Tun da ya fara maganar na yi ƙasa da kaina ban ɗago sai da na ji hannunsa a jikina. Ya tallafo fuskana idanunmu suka sarƙafe cikin na juna, tabbas na hangi tausayi da tsantsar soyayyata a cikin idanunsa sai dai soyayyar Suraj ta yi rassa a cikin zuciyata da tuge ta dai-dai yake da datse mini numfashina a duniya.
Ban ankara ba na ji hannunsa ya zame zuwa saman kafaɗata, da sauri na ture ina ɗan ja da baya.
Ya nufo inda nake gadan gadan ya jawo ni jikinsa yana shafa fuskata. Roƙon da Suraj ya yi mini akan na riƙe masa amanar kaina kar ba ba wa ko wani ɗa namiji damar kusanta ta, ya fara dawo mini cikin kwanyata tiryan tiryan.
Take na fara kiciniyar raba jikina da nashi, ya riƙe ni gam na kasa ƙwacan kaina. Dole na sadadu ina sakin hawayen takaicin da ya turnuƙe mini raina.
Ya ɗago kaina yana kallon fuskana da hawaye ya gama ɓata shi"lafiya? Wannan kukan fa na menene?". Ban iya cewa dashi komai ba, ba samu na zame jikina daga nashi, na koma gefe ina sakin wasu sabbin hawayen.
"Don Allah ki sanar da ni wai me yake faruwa ne?".
Na shiga saƙe saƙen abinda zan faɗa masa domin ba kaɗan ba ya yi matuƙar kiɗimewa. Ganin yana matsowa inda nake kuma na tabbatar inda ya iso ni dole sai ya taɓa ni abinda na tsana kenan a yanzu fiye da komai.
Na yi saurin faɗin"tsoro nake ji".
"Tsoron meye?".
"Tsoron gidan ba zan iya zama a cikinsa ni ɗaya ba". Ya yi dariya"to ai ba ke ɗaya za ki zauna ba. Ba ga ni ba tare zamu zauna" . Na yi masa shuru da akan ya bashi damar ɗaurawa"ki daina damuwa za ki saba kin ji? Kema makaranta nan da ɗan kwanaki za ki fara fita, zamu fita tare mu kuma ce dawo tare kin ga ba ke ɗaya za ki zauna ba".
Kaina kawai na sama damar ɗaga masa muka fito falo, gabaɗaya a takure nake domin ya kasa motsawa ko nan da can daga inda nake zaune.
Sai wajajen ƙarfe goma sha ɗaya su Anty Safiya, ƙawayena da sauran dangi suka zo. Na ji daɗin zuwan su ba don komai sai don gajiyan da nayi dashi.
Tare muka wuni dasu har sai magrib ba sannan suka tafi bayan su ƙara yi mini nasiha da bani wasu shawarwarin da zai taimaki duk wasu ma'aurata. Wajen gudanar da zamantakewar aurensu ciki lafiya baka lafiya, sai dai a gare ni abun ya sha bambam domin idan ya shiga ta wannan kunnen babu ɓata lokaci yake ficewa ta ɗayan.
Sosai Sakina ta yi ta kwantar mini da hankali da karanto min tari kyawawan halayyan yaya Sufyan da ni gabaɗaya yanzu bana ganin su. Ban sanar da ita komai game da saƙon da Suraj ta aiko mini ba, domin a wannan karon na zaɓi na kashi a cikina ko da kuwa ba zai yi mini maganin yunwa ba .
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam
LAMBA NA ASHIRIN DA BIYAR
Har na cika sati guda cif a cikin gidan Suraj bai taɓa kuskurewa wata rana ɗaya bai turo mini saƙon ba. Tsaf nake karanta su sannan na zauna na yi zaman haddan su daki-daki a cikin kwanyata.
Tun da aka kawo ni cikin gidan bamu taɓa kwana ɗaki ɗaya da yaya Sufyan ba balle mu haɗa shimfiɗa. Yana ɗakinsa ina nawa, domin na roƙi alfarmar masa kan cewar ban saba kwana da mutum ba ko a gida shima ya san hakan, kuma yanzu bani da tsarki don haka sai na sama tsarki sannan zan sanar dashi.
Bai nuna mini komai a fuskarsa ba amma na san tabbas sai ya yi jinyar zuciyarsa. Kafin na tashi ya kammala karin kumallo tsaf wanka kawai zan yi na ci, ya shirya ya fice makaranta idan yana da lecture ɗin safe da zai yi, idan kuwa babu sam baya gusawa daga inda nake.
Zaune muke a falo a zahiri idanuna suna akan akwatin talabijin ɗin da yake aiki, amma a baɗili na yi zurfi cikin tafkin tunanin da na faɗa.
"Madam lafiya?".
Ya faɗa yana ɗage mini ido ɗaya, na yi gefe da kaina"lafiya ƙalau".
"Sati za ki fara fita makaranta, zan kai ki sannan kuma na ɗauko ki. Za ki zame min garkuwa ga 'yan matan da suke kawo min hari".
Na yi saurin kallonsa ya sakar mini da laulansan murmushi, na taɓe baki game da faɗin"har wani hari 'yan mata suke kawo maka?".
"Ƙwarai kuwa kuma har da ƙawayenki na cikin makarantar".
Na gwalalo idanuna waje"tab ai kuwa iska yana wahalar da mai kayan kara". Murmushi mai sauti ya saka kafin ya furta"ke ko irin kishin nan na mata akan mazajen su bakya yi?".
Cike da ƙosawa da jin zantukan sa na ce"akan me zan yi kishi akan kan, bayan na san ka ɗin mijin mace huɗu ne. Ai abunda ake so shi ake kishinsa kai kuwa na sa.....".
Tun kafin na ƙarisa dire zancen da na ɗauko, ya dakatar da ni ta hanyar ɗaura yatsarsa akan leɓena yana faɗin"shit!. Ko da addini ya bani damar auren mata huɗu, to ni ɗin mijinki ne ke kaɗai daga ke na rufe ƙofa. Wallahi ba zan taɓa haɗa soyayyarki da na wata ba a cikin zuciyata ke kaɗai ce kuma da ke kaɗai zan rayu".
Na kasa cewa komai illa ƙasa da kaina da na yi, kunyar ɗagowa na haɗa ido dashi nake yi saboda takaicin zancen da na furta da nake yi. Tabbas baki ba zai gajiya wajen furta cewar yaya Sufyan ya fita daban a cikin ragowar jinsinsa maza ba, ya daɗe yana nuna mini tsantsar soyayyar da babu tsirki a cikin ta. Yana nuna mini kulawa matuƙar da ban zan iya butulce masa ba. Sai dai haƙiƙa na ƙara yarda cewar duk wanda ya yi nisa a soyayya bata jin ƙirji domin tamkar kifiyar ajali ce da tsilke baya tare ta.
"Ka yi haƙuri".
Ya sa hannunsa ya tallafo haɓata"ba ki aikata min laifin komai ba 'yan matana". Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya da nufin furta maganar dake baki, ya tari numfashina tare da sauya akalan zancen gabaɗaya ya koma wani daban.
Na yi artabu da zuciya ta hanyar amfani da ƙarfi wajen tusa soyayya yaya Sufyan a cikin ta, amma a banza wai an muntsine kakkaura. Ina son na ga nima ina nuna masa kulawa, taraiyaya da kuma soyayya kamar yanda yake nuna mini amma bana iya yin hakan.
Da zaran na yi ƙudurin kyautata masa sai na tuna da Suraj da kuma roƙon da ya yi mini, bai damu da auren da na yi ba shi dai kawai burinsa na riƙe masa mutuncina. Tare da tabbatar mini cewar zai cika alƙawarin mallaka ta komai daren daɗewa.
Bani da aiki da zaran yaya Sufyan ya fita face ɗaukar wayata ina karanta saƙon Suraj, duk da ban taɓa mayar masa da amsa ba amma kalamansa suna yin tasiri da cikin jikina.
Ina jin ɗumin hawayen da suka bin kuncina, ban yi wani yunƙurin kawar da su ba domin a yanzu fitar su ne kawai ke samar mini da nutsuwa a sashin ruhina.
"Surayya".
Na ji an furta kalmar sunana tare da fizge wayar dake hannuna. Na ɗago kaina da sauri cike da zaƙuwar son ganin wanda ya aikata hakan a gare ni.
Sakina ce tsaye a kaina ta tsura mini idanu. Ban damu da yanayin fuskarta ba kamar yanda ban ji ɗar da ganin ta ba na ce"me ye haka? Ba ni wayata malama".
Na ƙarkare zancen ina miƙewa tsaye.
"Me ye haka? Daman abinda kike aikatawa kenan da auren ki Surayya?". Ban tanka mata ba na miƙa hannuna na kuma cewa"ba ni wayata".
"Ba zan bayar ba, ba zan bayar ba. Har sai kin sanar da ni yaushe kika yi wannan lalacewar?. Ina hankali da tunaninki suka yi ƙaura suka tare da kike aikata wannan jahilcin da aurenk?".
Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina koma na zauna daga inda na tashi, na fashe da wani matsanancin kuka mai taɓa zuciya da kai tsaye yake fitowa daga ƙasan raina.
Sai da ta zauna kusa da ni kana ta cigaba da"sai yaushe za ki mance da Suraj? Sai yaushe za ki bambamce tsakanin masoyin ƙwarai da kuma wanda yake buƙatar a lokacin da yake nashi buƙatatun suka taso? . Sai yaushe za ki gane cewar Allah ya yi miki babbar kyauta da ya mallaka miki mutum irin yaya Sufyan, wallahi Surayya na rantse miki har da Sarkin da bashi da abokin tarayya, wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. A zamanin da muke cikinsa yanzu ire-iren su yaya Sufyan ƙalilan ne sukar rage, kuma ke kin sama ɗaya daga cikin su amma kuma nema yin wasa da damar ki".
Shuru na yi mata hakan ya bata damar cigaba da faɗin"yanzu ke fa matar aure ce kin san hukuncin macen da take da aure kuma tana tunanin wani a cikin ranta. Ki cire Suraj a cikin ranki ki sanya yaya Sufyan wallahi na tabbatar miki sai ya maida ke sauraniya a dukkan nahiya".
"Abinda nake ƙoƙarin yi kenan Sakina".
"Ba ki ɗauko hanyar yin hakan ba sam. Da kin ƙudurce a cikin ranki za ki hakan da ba zo na iske ki kin kafa waya a gaba kina karanta banzayen saƙonninsa masu cike da kalaman ƙarya da yaudara ki na kuka ba. Allah ya gani na yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na jawo ki daga faɗawa halakan da kike son jefa kanki".
Wasu hawayen masu zafi suka kwaranyo mini"ba za ki gane bane. Ba za ki gane yanda nake ji a cikin raina bane. A tunaninki a son raina nake yi wannan abun?. Ko kina tunanin nima bana son na yi rayuwar aure kamar ko wacce mace cikin kwanciyar hankali da mijinta da son farantawa juna?".
Sai da na numfasa na ɗaura da"nima da akwai zuciya a cikin ƙirjina, ni na da mutum ce mai 'yancin zaɓar abinda nake ganin ya dace da rayuwata. An tauye mini haƙƙina ta hanyar fifita dacewar yaya Sufyan da ni ba tare da koda da rana ɗaya an tuntunɓe da suna jin ta bakina ko ina son shi ko akasin hakan ba".
Na lura ta fara fusata domin zance kaɗan wani lokacin yake sanya ta tunzura, a lokuta da dama na fita haƙuri da kawar da kai ga wasu abubuwan.
"An tauye miki haƙƙi fa kika ce?. Sai yanzu na tabbatar da cewar lalle Surayya ba ki da hankali wallahi kin zauce. Ba zan ƙara yi magana akan wannan lamarin ba ki yi duk abinda kike ganin ya dace Allah ya ba ki sa'a. Amma ina tabbatar miki da cewar idan kika yi ganganci kika rasa yaya Sufyan za ki nadama mai tarin yawa a rayuwarki".
A kufule na ce"ko yaushe zancen ki idan na rasa shi zan yi nadama zan yi nadama. Shin ko sau ɗaya ba ki taɓa yin tunanin jin yanda nake ji a cikin raina ba?. Zafi da zogi nake ji suna sukar zuciyata. Na zaɓi na rasa komai da kowa akan wannan lamarin, in yaso ke sai ki auri yaya Sufyan ɗin tunda a idanunki babu mutumin kirki a kaf duniyar nan kamar sa".
Duk muka miƙe tsaye ni da ita muna kallon juna, har yanzu hawaye yana zuba daga idona. Na bude baki da nufin cigaba da amayar da zancen da yake kartan zuciyata, na hangi yaya Sufyan tsaye a ƙofar falon ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa tare da kafe mu da idanu.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam
LAMBA NA ASHIRIN DA SHIDA
Ina wani irin huci na juya na shige ɗaki tare da murza key a ƙofar, na bar su tsaye a wajen. Ba damuwata yaya Sufyan ya ji ya abinda na furta ba domin ba shi ne a gabana ba a halin yanzu.
Ina shiga na zube akan gado ina sakin wani gigitaccen kuka mai matuƙar ƙarfi, ina yi ina taune naman bakina tamkar ba jikina ba.
Sosai da na yi kukan sai da na ji jikina gabaɗaya ya mutu ga wani zazzaɓin da ya rufe ni sannan na tsagaita. Ba domin na ci sauƙin zogin da nake ji a cikin zuciyata ba.
A hankali kunnuwana suke jiyo mini ana bubbuga ƙofar ɗakin tare da ƙiran sunana. Jin muryan yaya Sufyan ne ya sanya ni tsintar kaina cikin faɗuwar gaban da ban san dalilinsa.
Na san ko takardan saki ya damƙa mini ba ni da damuwa, to amma menene dalilin tsintar kaina a cikin wannan yanayi?. Take zuciyata da take bugawa a raunane ta bani amsa da faɗin Surayya wani fuskar ya fi ƙarfin mari.
"Don Allah ki buɗe ƙofar nan na roƙe ki".
Ya furta muryarsa a sanyaye, ko motsawa daga inda nake kwance ban yi ba. Ya cigaba da faɗin"ina son magana ki taimaka ki buɗe ƙofar nan".
Shuru na yi tamkar bana jin abinda yake faɗi. Ina da tabbacin idan ba ni na tashi na buɗe ƙofar ba babu ta yanda zai iya shigowa ɗakin. Irin ƙofar da idan aka rufe ta ta cikin to ba za a iya buɗe ta ta waje ba.
"Surayyaaaa".
Ya furta kalmar sunan cikin wani irin muryar da sam ban san ya mallake ta ba. Wani yar na ji a jikina da hakan ya tilasta mini runtse idanuna da ƙarfi wasu hawaye suna gangarowa daga koramar idanuna.
Babu irin magiya da roƙon da bai yi gare ni ba, ƙiran wayata kuwa ya yi yafi a irga amma na kasa cewa dashi komai. Haka har aka yi ƙiran sallan zuhr na miƙe ina jin wani jiri ya ɗeba ta na shiga banɗaki na yi alwala, a zaune na yi sallan saboda rashin ƙarfin da nake ji bani dashi ba.
Na kasa furta komai yayin da na ɗaga hannayena sama, illa hawayen da nake yi. Na tabbatar da cewar ubangijina shi kaɗai ka san irin radaɗin da nake ji a cikin ƙalbina kuma shi kaɗai zai iya kawo mini sauƙi da mafita daga tsaka mai wuyar da na faɗa ba.
Ina shafa addu'ar na ji yaya Sufyan yana buga ƙofar, yanda ya kwantar da murya ya sa naji kifiyar tausayinta ta caki ƙirjina. Ina tafiya ina dafe bango hakan na miƙe na buɗe masa ƙofar.
Ban yarda na ga inda yake ba na juya ya yi saurin riƙo ni na faɗa jikinsa.
"Me yake faru? Me yake faruwa Surayya ki sanar da ni. Sakina ta tafi bata ce min komai ba".
Ya ƙare zancen yana jijjiga na matse idanuna gam. Cikin sarƙafewa harshe na furta"babu abinda ya faru face abinda ka ji".
"Me ye kike nufi?".
Sai a lokacin na yi nasarar kwace kaina daga riƙon da ya yi mini, na koma cikin ɗakin na zauna a ƙasa dirshan.
Ya tako ya zauna a gabana kamar mai ɗaukar karatu ya kafe ni da ido"tun kuna ƙanana ku ke tare da Sakina, babu wanda bai san ku a matsayi ƙawaye ba daga danginmu har na ta, kowa ya shaida irin yanda kuke kulawa da juna da ɗaukar matsala da damuwar ɗaya tamkar ta ɗayan. Na yi mamakin ganin kuna cacar baki da ita a yau me ya faru?".
Na ɗago idanuna da suka kumbura tsimtim na ce"kana nufin bata sanar da kai komai ba har ta bar cikin gidan nan?".
"Ƙwarai kuwa".
Na sauƙe ɓoyayyiyar ajiyar zuciya tare da faɗawan tunanin dalilin da ya hana Sakina sanar dashi komai duk da fusatan da tayi game da lamarin. Sautin muryarsa da suka yi dirar mikiya a na'urar jiyo mini sauti ya katse mini zancen zucin da nake yi.
"Me yake faruwa? Don na yi imanin ba ƙaramin abu bane zai sanya ku mayarwa irin wannan martanin da zafafan kalamai ".
Na kasa cewa komai sai da ya ƙara maimaita tambayar a karo na biyu. Haka siddan na tsinci kaina da sakin wasu hawayen da na kasa tantance dalilin zubar su. Shin na halaccin da Sakina ta yi mini wajen ganin ta ƙara zuba ƙasa a ramin da na haƙa na ɓoye sirrina bane, ko kuma na takaicin ƙaryar da zuciyata take shirya mini ne na gaza ganewa.
Cikin rawar murya na furta"zuciyata ce ta kasa daurewa na kuma gaza jure zantukan da take yi mini a kanka. Na ga take taken ta kamar sonka take yi domin kullum cikin yi mini zancenka take yi da kuma yabon kyawawan halayenka tare da addu'ar Allah ya mallaka mata miji irin ka. Ko yau ma da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 13