tazo zancen ta yi mini kenan na kasa daurewa har ka shigo ka ji ina furta mata idan sonka take yi ta aure ka tunda a idanunta babu mutumin kirki a kaf duniya nan kamar k....".
Tun kafin na dire zancen ya katse ni"innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Surayya kika faɗa mata haka"?.
Na gyaɗa masa kaina, ya cigaba da cewa"Sakina ta wuce haka a wajen ki, na tabbatar tana ɗaya daga cikin masoyanki masu ƙaunar ganin farin cikinki. Ta taimaka min sosai wajen samun soyayyarki bana tunanin idan tana yi min kallo so zata yi min wannan taimako. Surayya idan hankali ya gushe hankali ake sawa a nemo shi, shi harshe bashi da ƙashi amma yana da dafi sosai".
Sosai na fashe da wani irin kuka har jikina rawa yake yi.
"Subhallahi lafiya?".
"Kai ma kenan goyan bayan ta kake yi?".
Na faɗa ina ƙoƙarin miƙewa jirin da yake walagigi da na ya dawo da ni na zauna. Ya riƙo hannuna na fizge.
"Ba ina goyan bayan ta bane face ina sanar dake gaskiyar da idanunki suka makance suka kasa gano miki su. Kin san ina sonki wallahi ba zan taɓa fifita wata 'ya mace akan ki ba ki yi haƙuri kin ji?".
Banza na yi dashi, rashin kula shin da nayi bai sanya shi dakatawa daga furta mini kalaman ban haƙuri ba tamkar shi ya aikata mini laifin. Bai tsagaita ba har da ya yi nasarar sanya zuciyata da take tafasa lafawa.
A karo na farko a rayuwarta da na roƙo Allah idan son Suraj ba alkhairi bane a gare ni Allah ya cire mini shi har daga zuciyata gabaɗaya. Ban taɓan jin tausayin yaya Sufyan ba kamar yau domin da farko na yi tunanin cewar ya ji duk tattaunawar da muka yi da Sakina ashe har yanzu lalume yake yi a cikin duhu.
Har na fara fita makaranta ban nema Sakina ba kamar yanda ita ma bata nema ni, sannu kawai shi yake shiga tsakanina da ita ko mun haɗu a cikin makarantar.
Duk wasu abubuwan da muke yi tare bamu daina ba magana ce dai kawai bana yi, hakan ya sanya mutane da yawa basu gano taskaron da ya gifta a tsakanin amintar mu ba.
Wata ranar asabar bayan yaya Sufyan ya dawo daga lecture ɗin ƙarfe goma sha ɗayan da yake dashi ya ce na shirya zamu je gidan su Sakina. Direwa na yi akan babu inda za ni tun ita ma har yanzu ba ta tako tazo inda nake ba to ban ga dalilin da zai na kwashe ƙafafuna nake inda take ba.
Sai da na ya nuna mini ɓacin ran da ban taɓa gani akan fuskarsa ba sannan na shirya muka je.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam
Zaki sanya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984
LAMBA TA ASHIRIN DA BAKWAI
Yau Nusaiba ni kika mara sabo da kin tsane ni kaicun wannan ranan nasan nayi miki laifi ki yafe mun don girman Allah zan gyara kuskure na kiyi mun afuwa .
"Wallahi JB muddin baka fita daga rayuwa ta ba zan baka mamaki sannan kace zaka kashe mu ,duk kan mu sannan ka kashe kanka ina jiran wannan ranan fisge hijabi na nayi nafice ko wai-wayo wa banyi ba haka na nufi ɗaki na na kwanta ina fitar da numfashi mai wahala jin wani yanayi sai da gaba na ya faɗi nayi ƙoƙarin dai dai ta numfashi na amma ina bazan iya ba ido na yafara juyawa baki na yafara kumfa bugun numfashi na da sauri yake yi tsintar kaina nayi a asibiti a lokacin kwana na uku ina kwance wanda duk wani masoyi na ya fidda ran zan rayu duba wa nayi naga banga Hajiya ba sai ƙanwar Abba na takaici duk ya cika ni yanzu daman da gaske Hajiya take yi wani likita ne da ban ba doctor Ibrahim ba shima yanzu fushi yake dani kenan.
Jin wani yayi mun magana "kin tashi sannu Allah ya baki lafiya irin wannan rashin lafiyar taki sai wanda zai,iya fatan mudai Allah ya baki lafiya tambaya na ina ne yake mun ciwo nace babu Anty mariya ce ta matso in da nake tayi mun sannu da jiki na amsa "Anty ina Hajiya ban ganta ba ?"kiyi haƙuri tayi fushi da ke a kan hakan ne ma suka samu matsala da Abban ki muma kan mu bamu ji daɗin hakan ba Allah ya baki lafiya ".
Kuka nakeyi sosai Anty mariya tabani haƙuri "amma taya Hajiya tana fushi da ni zan samu sauƙi a zuciya ta ya zanyi yadda na keji sai nake ganin kamar ba zan rayu ba fatana Hajiya ta yafe mun wallahi zan auri ya Ibrahim sannan zan zauna da shi ko dani nawa farin cikin zai dirƙushe ina son ganin Abba na don Allah a kira mun shi zamuyi magana jikin Anty mariya yayi sanyi kiran Abba tayi juyowar da zatayi ganin ina aman jini numfashi na ina ta kokuwa da shi ban ƙara sanin in da hankalina ya ke ba
Sai da nayi kwana hudu kafun na dawo hankalina karan nan har Abba na ya fitar da tsan mani zan rayu narame sati ɗaya nayi ina kwance kamar wata nayi ,karan nan Hajiya tazo duba ni amma an ce mun bata jima ba na gaya wa Abba a daura auren kawai ko da ina Asibiti da ya tambayi ya Ibrahim ya ce a dakata a bari sai na warke nasan fushi yayi don bai Kirani ba sannan bai zo ba sai da Abba na ya ce ya na son ganin shi kafun ya zo shi yaje du bani a asibiti ko minti talatin bai yi ba ya dawo .
Zuciya ta a tunku she take matsaloli sunyi mun yawa in na tina irin ƙaryan da JB yayi mun ji nake kamar in haɗiye rai na duniya yanzu ba yadda masoyi yaci amanar masoyiyar shi ƙawa taci amanar ƙawar ta duniya ke nan a ranan da za,a sallame ni a ranan ya Ibrahim ya bar damaturu .
Lokacin da zamu bar asibitin a lokacin naga doctor in badan na gan shi sannan mun haɗa ido hudu ba bai yi niyar ƙariso wa ba kunya yaji ya kari so "ya jikin har an sallame ku kenan ? "e doctor daman kana nan na ɗauka ba kanan ne shiya sa Allah sarki "Nusaiba ba na son in ƙarasa bata miki rai shine nace doctor Garba ya duba ki .
Kayi fushi dai kawai taya zakace baza ka duba ni ba tunda ka gaji nima bazamu ƙara zuwa asibitin nan ba wani zamu koma kallon da yake mun kallo ne na wasu abubuwa da ban nasan waye doctor tunda yace har sun samu saɓani da matar shi a kaina haƙiƙa so mungun abu ne na tabbata da son da doctor ya ke mun da na ya Ibrahim shine asalin so amma in a kace JB yazo a wata mahangar don son shi ya zame mun illa ya cutar ni sallama yayi man ko kallo na ba yason yi jan motar mu,mukayi muka bar asibitin .
Sati na ɗaya da warke wa,ina kwance naga sai kirana a ke da wani number naƙi dauƙa cen wani zuciyar ta bani umarni da in ɗauka na ɗauƙa bayan sallama da nayi a gigice a ka amsa "a kwai wani ne yayi hatsari a mota duka yan cikin motar Allah ya musu rasuwa sai shi ƙadai ne ya rage a hanyar su ta zuwa Biu wayar shi babu kati shine muka kiraki don number ki ne yafi yawa wajen kiranki ".
A gigice nace malam ka gaya mun sunan shi da number wayar yace mun bai san ya zai yi ba ba kati a wayar gaya mishi wasu number da zai sa number mai shi zai fito a lokacin da yake gaya mun number na gigice ba kowa bane illa JB sake kiran mutumin nayi nace ya duba zai ga an rubuta my mum ya kira yace mun baya shiga ,na rasa wazan kira A'isha na kira nace bata da number abokin JB ko dai na yan gidan su tace bata da shi amma bari taje shagon shi ko zata,ga wani a shagon nace tayi sauri don babu nisa tsakanin su.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam
LAMBA NA ASHIRIN DA TAKWAS
Jiran kiran Aisha nakeyi ina ta zullumi sai naga kiranta ya shigo waya ta da sauri na ɗauƙa take sanar mun babu kowa a shagon ita kuma tana tsoron ta gayawa wani tunda babu komai a tsakaninsu yanzu tambayar ta nayi wata gani a bakin shagon tace wani makwabcin shine mai sai da magani nace ta bashi wayar sanar da shi nayi sannan nace ya faɗa a gidan su an kira number mahaifiyar shi a kashe ya ce to .
Godiya nayi a Aisha da irin taimakon da tayi mun har zan kashe wayar naji tace "Anty in tambaye ki daman tunda kin sanshi ne ya alaƙar ku take da shi ne naga kin damu wallahi in zanga JB mota yabi ta kanshi wucewa zanyi ".
Haba Aisha Musulmi ne don uwanki ki yafe mi shi babu komai a tsakanin mu sai mutunci lokacin da nazo gidan ku, ina son sani wani abu ne game da shi karki damu ba komai Allah ya bashi lafiya shiru tayi banji tace Amin ba mukayi sallama .
Mutumin na kira nace ya jikin nasu yake sanar dani an kawo su damaturu suna TH in zo suna neman taimako tunda babu wanda ya sani gashi wayar shima ta mutu tashin hankali ba,a sa mishi rana da sauri na canja kaya na nace a Hajiya zan fita wani ne bashida lafiya zanje duba shi kafun yan uwan shi suzo,fatan samun sauƙi tayi mun na fita a lokacin da na ƙarisa da sauri na kira wanda ya Kirani yamun kwatance na tausaya mishi sosai yaji ciwo a hannu da fuska da ƙafar shi cikin ci ya bugu bai san waye a kanshi ba A'isha ne ta Kirani wai zata bada number na a yan uwan shi sunzo karɓa nace ta basu duk wani abu da ake buƙata duk na siya komai tinanin wanda zai kwana ,a gunshi nakeyi narasa wani ma,aikaci nagani yana shirin tafiya gida daga ganin ya gama aikin shi na yau naji yana sallama da sauran ma,aikatan shan gaban shi nayi "malam don Allah ina son muyi magana tun da nazo na yaba da hankalin ka ina da mara lafiya ne sannan yan uwan shi yan barno ne basu,iso ba ina son wanda zai kwana tare da shi zan biya shi nima gobe zanzo ƙarfe bakwai Kozaka taimaka mun ku kwana zan baka 10k".
Karki damu ba komai zan zauna da shi amma zanje gida in dawo Zangaya wa iyayena kiyi haƙuri ba nisa yanzu zan dawo in sha Allahu "shikenan ina jiran ka sai ka dawo zan tafi "
Bai jima ba ya dawo na ɗauki kuɗin shi na ba shi da wasu kuɗin kar za,a buƙaci wani abu bayan bananan komai sai da na tanadar kafun na tafi gida ina shiga gida Abba na shigowa sannu da zuwa nayi mishi na na shiga ciki numfashi naja rayuwar nan babu komai a cikin ta sai rudun duniya duk abun da JB yayi mun yanzu Allah yasa ni zan taimake shi duniya kenan tausayi yake bani yanzu babu wani so a zuciya ta har ƙarfe tara na dare yaron da yake kulawa da shi ya Kirani a kan ya farka nace ya gaishe shi gashi na taho da wayar shi zansa mishi chargi
Ƙarfe sha ɗaya na kunna wayar na dare kira yata shigowa kiran mahaifiyar shine ya shigo da bazan ɗauka ba na ɗauka bayan mun gaisa da taji murya ta ta ,tambaye ni, ina mai wayar bayani nayi mata tayi mun godiya a kan ƙanin shi da yayan shi zasu shigo gobe da safe nace to bana son kashe wayar karsu sa wani abu a ransu na barshi a kunne da safe nida kaina na shiga kitchen na haɗa komai da mota na nafita bana son wani abu ya biyo baya ƙarfe bakwai ina bakin get .
Ɓangaren in da suke na nufa na samu yana kwance idon shi a rufe godiya nayi wa, Usman ya bani kuɗin yace ba,a buƙaci komai ba bai san anjima ba ko zasu buƙaci wani abu godiya nayi mishi sosai nace muje in kaishi gida yace ba komai in barshi babu nisa tsakanin su zai wuce kawai fita nayi daga ɗakin har nafice bai farka ba naje siyo wasu abu ne nadawo zama nayi a kujerar gefen gadon sai cen ya farka ganina a kusa da shi duk ya firgita zare ido yayi tambayan shi nayi ya jikin ya amsa kiran mahaifin shine ya shigo wayar shi nuna mishi nayi yace in ɗauka kwatance nayi musu sannan na tashi naje don shigowa da su .
Kanin shi da yaga halin da yake ciki sai ya fashe da kuka mahaifin shi ya tausaya mishi dana ga yan uwan shi sunzo sai na fice daga ɗakin na shiga cikin mota na zauna nasha ruwa fita nayi don ƙara duba shi tun da na shigo ya zuba mun ido da wani kumburarren fuska mahaifin shine yayi mun godiya da hidimar da nayi musu nace ga abinci suci tunda jikin da sauƙi sosai godiya yayi mun sallama nayi musu nafice zan dawo gida ina fita muka haɗu da doctor Ibrahim muka gaisa "lafiya kuwa ? e lafiya nazo duba mara lafiya ne jiya sunyi hatsari a hanyar biu wani kallo yayi mun "muje na duba shi haka na ƙara komawa ya duba shi tare da tambayan ya jikin shi .
Bayan mun fito naga bakin shi yana ta motsi ",ya jikin ki kema don kema mara lafiyar ce?"ka damu da lafiya ta ne yanzu tunda kace bazaka ƙara duba niba da sauƙi sosai .
Allah ya baki lafiya kizo na kaiki "na gode da mota nazo "ya batun magana na kuma Nusaiba ina kan baka na har yanzu ban fidda ran zamuyi aure ba ki karɓi tayi na mana "babu komai a zuciya ta doctor kayi haƙuri bana son jefa ka cikin wani hali nasan yadda so yake "babu ruwan ki da halin da zan shiga tunda bake tausayi na kibarni kawai zaifi.
Ikon Allah !
naga ya ɗau zafi na tafi daga gun na barshi shiga mota nayi amma na kasa jan motar duk mutuwar Muhammad ne ya jawo mun komai da yanzu ina gidan shi ƙaddaran haɗuwa da JB bata shigo ba da ya Ibrahim zaici gaba da ɗauka na a matsayin ƙanwar shi doctor zaici gaba da kallona a matsayin mara lafiya na daɗe kafun na tafi .
Tun daga ranan ban ƙara zuwa asibiti ba amma kullum sau uku zan aika musu da abinci yan uwan shi sunzo duba shi suka tambaye ni mahaifin shi yace sauɗaya ya ganni amma bai san ko lafiya ba ga dai number na su Kirani ina zaune naga kira ya shigo ɗauka nayi jin mahaifiyar JB ce sai da gaba na ya faɗi "lafiya kuwa kin daina zuwa asibiti ko dai laifi a kayi miki ne "ba banajin daɗi ne shiyasa ya jikin na shi Allah ya bashi lafiya .
Ta buƙaci in mata kwatancen unguwar mu nayi musu Hajiya ce ta ,karɓe su hannu biyu naji daɗin zuwan su "yauwa Nusaiba kardai kece kika bada saƙo a kawo mun ranan a barno ? Shiru nayi tayi mun godiya sosai tace a lama tagani tagane hakan nida kaina na mayar da su asibitin na duba JB nayi mishi sannu da jiki yace da sauƙi" naji duk kan hidimar da kikayi mun nagode sosai nasan kin daina zuwa asibiti ne don bake son ganina kin tsaneni bake son tarayya ta dake kefa macece wanda babu wanda tarayya zai haɗaku ya watsar da ke ki yafe mun yanzu kam komai ya ƙare Allah yasa ta dalilin hatsarin nan zaki san iyayena suma su sanki zan bayya na musu ke nake so
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
MARUBUTAN JAHAR YOBE
Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam
Zaki sanya kuɗin ki 400 ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984
LAMBA NA GOMA SHA SHIDA
Bana son tafiya da ya Ibrahim gudu ne da shi gashi ba ka,isa kayi mishi magana ba kamar zuga shi kake yi ,ga yadda hanyar take shiru nayi na shirya mana kayan mu ,nida Fatima ƙarfe goma muka bar damaturu mun kama hanyar barno ban gayawa Inna ina hanya ba sai dai ta ganni . In da ace zuciya ta zata ,a mince min da ta zaɓi mutumin da yake da kima da daraja agun kowa ina mamakin yadda ya Ibrahim yake nuna mun kulawa fiye da kanshi a lokacin da Muhammad ya rasu tamkar ɗan uwan shi tare muka wuce bauchi da shi sunyi sabo da mutune agun zaman makokin Muhammad .
Muhammad yana da zafin kishi, amma ban taɓa ganin ya nuna wa ya Ibrahim ba .
Tinani natayi da yawa a cikin motar shi kuma ƙaratu ya kunna yana taji Fatima tayi bacci a cikin tunanin da nakeyi har na tino in da zamuje bauchi da Muhammad muka tsaya a darazo yace mu tsaya mu gaisa da wata batada lafiya haɗe rai nayi nace wata kuma ni bazan jeba ya je ina cikin mota lokacin da muka je duba mara lafiyan a she na miji ne zolaya ta yake yi nikuwa kishi ya rufe mun ido wajen samun lada.
Babban mutum ne a she sunan shi TY wajen aikin su ɗaya naji kunya da yazo ya sameni a cikin mota ya gaishe ni abun da naji ,ya faɗs"Madam kin ɗauka wata ne ko shiyasa kikaƙi zuwa a hakan ma nagode sosai Allah ya bar zumunci na gode ".
Abubuwan da Muhammad ya bar mun suna dayawa a rayuwa ta a kan alkairi zan ta, tina shi irin su JB ko da mutuwa sukayi babu abu mafi daraja da zan tina shi da shi sai jin maganar ya Ibrahim nayi yace "in kin shiga kicewa Inna na wuce gun aiki wannan key ɗin ɗaki nane ki share mun ɗan Allah ga kayan nan ku shiga da shi ".mai shara kamayar,dani ba zanyi ba in kadawo zakayi kayan ka ,kana da ƙanne kawani sani aiki sai kace wata matar ka kama hannun Fatima nayi muka ƙarisa ciki Inna nata rar tana tsaye ganina da tayi tace oyoyo uwata kece tafe babu waya kuma ?.
e Inna nice bazata zanyi miki shiyasa kika ganni .
Sannun da zuwa shiga ciki nayi na huta nací abinci nayi sallah har bacci ya ɗauke ni banga kiran JB ba tun safe a waya ta sannan bance ina garin suba akwai abun da nake son shirya mishi zan bashi mamaki kuwa sai ƙarfe takwas ya Ibrahim ya shigo bayan na bada key ɗin ɗakin na shi a gyara mishi abun ka da mai tsafta komai a gyare ya ke kawai dai in da sabo ne an saba .
Sai kusan mangari ba kafun ya dawo duk muna falo muna ta shan hira yau sai naji damuwar da nake ciki a cikin kashi ɗari hamsin ta bar raina .
"Inna kiyi mun afuwa nawuce gun aiki ban shigo ba sauri nakeyi shiya sa ki yafe mun kinji" babu komai karka da mu hakan ma yayi tunda ka,kawo mun uwata kana kulawa da ita sosai ina godiya Allah yayi albarka .
"Amin ya rabbi ".
Washe gari da safe
Misalin ƙarfe goma na safe bayan ya Ibrahim ya fita wajen aiki nima na shirya na rufe fuska ta ,ta yadda ko kasan ni ba lalle ne ka gane niba na ɗauki A'isha nace muje ta rakani unguwa amma karta faɗa fa tace to unguwar su JB na nufa ban tsaya shan wahala ba na tambayi shagon shi da zumar nazo siyan kayan ɗinki na samu shagon bada waya ta nayi a A'isha ta yadda zata ɗauka mun photo in naje shagon na samu wasu yara sunzo siyan zare da zip nikuma rubuta wa nayi da naje na ba,shi ya faɗa mun kuɗin na ba shi naga ya rame sosai ya ƙara duhu tsayin nan dai tana nan bai damu da yasan ko wa ye ba sana,ar shi yasa a gaba na duba shagon sosai abun duk ya bani mamaki bayan taho wata daga shagon karɓan wayar nayi A'isha ta burgeni har wajen da nake ba shi kuɗi sai da ta ɗauka da lokacin da yake bani kayan da nasiya munji ma,kafun muka tafi daga unguwar har gidan su ,sai da a ka nuna mun nagani .
Sai naji sanyi a raina bansan da wanake tare ba ina, gudun wani abu kar ya faru batare da nasan komai a tattare da shi ba wasu na samu suna bakin shagon ɗayan na gane shi wani abokin shine bansan ya ,suke ba a hoton da ya tura mun har da shi tabbas shima yaron ne JB yana cika ido abokin shi kuwa asalin yaron ne dan ga,a lama suna tashan rake a bakin shagon oh ni Nusaiba.
Bayan mun dawo gida ne na buɗe waya ta don muna hanya na kashe ina buɗe wa yana kira muka gaisa sosai"kiyi haƙuri na samu kuɗin gobe zanje "ka zauna kayan ka, bance ka nemi kuɗi a ro saboda nawa buƙatan ba baka da shi sannan koda kaje gun Abba ba shida amfani don ga abun da iyayen ka suka ce .
"Me yasa kike haka ne kinsan abun da Allah zai yi ya,kamata ki gane masoyi ba ya taɓa zama maƙiyi a rayuwa .
Nuna mishi nayi bana gari nayi tafiya amma in zaizo yayi mun magana in gaya mishi "wani kalan zuwa zanyi bayan bake nan kibari sai kin dawo kafun na shirya sai in je da to na bishi banyi musu ba amma a jiki na nakeji bazai jeba kawai ya faɗa ne .
Nayi kwana uku a barno babu komai JB yayi blocking ɗina a Whatspp ban bita, kan shi ba na ci gaba da,abun da nake yi duk wani abu na shi a waya ta duk na goge su wani photon da wasu abubuwa wanda suke a laƙa da soyayyar mu duk na fitar da su daga raina nagoge ban bar komai ba nagoge a nawa tinanin ban gaya mishi magana mai zafi ba da takai ya mun irin wannan tijaran ba .har zai rufeni daga ko mai na shi ayya JB yana da hankali kuwa ga shi yayi karatu da, ace bai yi karatu tuba zance a kwai rashin ilimi a tattare da shi .
Ta howa ta barno yayi mun rana in da a damaturu nake yanzu ina ɗaki duk tunani ya dameni nan kuwa ina cikin yan uwa na ,babu abun da basa mun tun ranan da muka je ban ƙara sa ya Ibrahim a ido na ba ,da wuri yake fita yau dai takama Jumma,a naga A'isha sai washe baki ta ketayi
"Lafiya kuwa indo sai wani fara,a kike tayi"?
"Anty Nusaiba yau na tashi bani da kuɗi ga shi yau ne ya Ibrahim yake mana rabo na kuɗi ko wani jumma,kinga kuwa dole in yi murna da kasance war wannan ranan " gaskiyar ki kice mutumin ya nason lada kenan miƙomun jakata in fara baki kafun ya tashi daga bacci miƙo mun jakar tayi na ɗauki dubu goma na bata tsalle tayi tariƙeni sai murna take tayi tun da ga cen naga ya Ibrahim yana ta hararan ta "ki cika ta so kike ki karya ta baki ga ita ba lafiya ne da ,ita ba haba A'isha ina ganin ki kamar mai hankali ",kayi haƙuri ba zan ƙara ba zan kiyaye "
Ya dai fi miki kyau ki kiyaye zaifi ƙariso wa in da nake yayi "Madam a nema mun abun da zanci yunwa na keji gaskiya ko dai in yi miki kuka" kayi kayan ka meyasa kake son ka dinga bani wahala ne ina huta wana zaka takura mun . na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 13