Share this page
5 / 13
duniya ne Nusaiba kin shayar dani wani zuma mai daɗin gaske amma kiyi haƙuri ki yafe mun a kullum ce miki nakeyi in kin samu miji kiyi ƙoƙarin ki manta dani ,a rayuwar ki kiyi, auren ki. Maganganun baya yake ta maimai tamun amma ido na ya rufe in gane baya sona yaudara ce kawai ke damun JB a duk lokacin da zai nemi in tura mishi surar jiki na kalaman shi daban ne agareni bana son fishin JB haka zan tura mishi matsalan ɗaya ce a duk lokacin da natura mishi bana iya samun nutsuwa a rai na.,haka Ibrahim yayi sallama na ajiye wayar Ibrahim ɗan uwa nane yazama tamkar jinina ɗaukar shi nake a matsayin yayana Abubakar shiyasa bana sa komai a rai na barin shi kawai nakeyi"kina charting ne?e ya hanya ina fatan ka,kawo mun Farana yana gun Hajiya na,isa in zo garin nan batare da na kawo miki fara ba ya jikin "da sauƙi sosai " inna tace a gaishe ki"ina amsa wa". Sai kusan mangari ba kafun ya fita daga ɗaki na Ibrahim duk lokacin da yazo ɗaki na to ɗaga mun, labulai zai yi sama duk wanda zai wuce yana kallon mu,ko kulashi banayi . Kwanan sa uku bai iya shawo kai na ba duk wani hanya da zai bi dan mallakar nawa zuciyar a banza ne don nawa zuciyar gaba ɗaya na miƙawa JB ban taɓa tsan manin zan so wani ba bayan Muhammad sai gashi nasamu wani amma yazo mun a wata mahangar.iyayen mu so ,suke su haɗamu aure da shi amma zuciya ta bata sonshi babban ma,aikaci ne ,a CBN a cikin barno amma bañsan a wani ɓangare ya keba a salin su Ibrahim Usman Garba yan damaturu ne aiki ne yakai mahaifin shi cikin garin barno a cen duk a ka haife su su bakwai a ka haifa shine na farko maza hudu mata uku sannan a cikin zuriyar mu ,shine jika na farko a ɓangaren mahaifiya ta daga mahaifin shi sai Hajiya na yana da kuɗi sosai ga kyau ga ilimin boko da na,addini amma duk wannan basu bane a gaba na da,a ce shine yafara sona kafun JB zan so shi so mafi inganci a duk lokacin da yazo shike ƙaramun karatu kafun ya tafi duka sai na bashi hadda .ranshi ya ɓaci ne ya tafi da wuri sati biyu yake yi ma na in yazo ga miskili ne bana kaɗan ba irin su doctor da Ibrahim da Alhaji Sani sune zan iya nunawa duniya ga zaɓi na ,amma in har na nuna JB sai na samu wanda zai wanke ni da mari . Washe gari Tun safe nake kiran JB bai ɗauka ba nata kiran shi shiru nayi mishi magana shiru tura mishi saƙo shiru,har dare shima shiru sai danayi kwana biyu baya ɗaukar waya ta ina zaune nace bari na jarraba cikin ikon Allah ya ɗauka tambayan shi nayi lafiya kuwa ina ta kiran ka shiru ? a bun da ya ce mun "karki ƙara kiran number nan don an riga da an karɓe wayar Babana ya karɓa yanzu ma dabara nayi mishi ya bani ki bari sai komai ya lafa zan kira ki. Tinani nadin gayi me ya faru ko dai iyayen shi sunga wani ,abu a wayar shine kodai wani matsalan ne.daure wa nayi na ƙiyi mishi magana sai da yayi kwana biyu kafun yayi mun magana shiru nayi yata sharara mun ƙarya wai duk a kan auren shine iyayen shi suke fishi da shi kar,in ta kira ya gaya mun magana in ya ɗauka .babu abun da nace sai Allah ya rufa asiri nasan ƙarya ne a yaran zamanin nan a ce iyaye zasu karɓe maka waya kamar ɗan secondary school nasan ya shirya mun ƙarya ne kawai walakanci ne yake damun shi . Yanayi na ya cenza ,abun haushi yake bani .da ina yawan kiran shi ,amma yanzu missed call ɗaya zanyi mishi nam ma sai da yayi ƙorafi da,ina yawan kiran shi zai ga missed call goma biyar amma yanzu kaman wani maye guda ɗaya in ba zan kira shi ba in haƙura da kiran kawai. na rasa dalili ina da zuciya amma ta ɓangaren JB nazama lusura ta,ajin gaske har mamakin kaina nakeyi na daina yi mishi magana sai in yayi mun daya ke shi tinanin shi irin na yaran ce ko ganewa bai yi ba ko yayi mun magana ta Whatsapp bana kula shi daman nice ke yawan kiran shi sau uku a rana ko sau hudu nakan bashi lokaci na muta hira ko zuciya irin na sauran mazan nan babu .ina cikin zamana a ɗaki yaya na Abubakar ya shigo na gaishe shi ce mun yayi Abban mu yana kirana yana falon ƙasa cemishi nayi ina zuwa jin kiran Abba sai da zuciya ta ya,tsinke ban san mezanje in tarar ba da sauri na sanya hijabi na ,nanufi ɓangaren Abba bakina ɗauke da sallama ganin yanayin mahaifina ya ɗaga mun hankali bana kaɗan ba gaishe shi nayi ya amsa hannun shi ɗauke da jarida bayan shiru da ya biyo baya sai jinayi yayi gyaran murya"Nusaiba bafa zan zuba miki ido kina abun da zuciyar ki take so ba me Ibrahim yayi Miki kikayi mishi korar kare mekike nufi Muhammad ya riga mu gidan gaskiya in da kece kika mutu wallahi aure zai yi muddin kuwa ya samu matar da take kulawa da shi mantawa zai yi dake haba Nusaiba to ke wakike so tunda bake son Alhaji Sani bake son Ibrahim kigaya mun sannan kice mishi na bashi kwana goma sha biyar . Juyawa yayi yaci gaba da karatun jaridar dake hannun shi ban taɓa riskar kaina a tashin hankali ba irin ranan na ɗinga maima tawa kwana sha biyar a take zufa ta karyo ,mun ya zanyi kaina a sunkuye yake tun da naje falon Abba zanyi magana ya ɗaga mun hannu "ki tashi ki fice mun daganan sannan nasan halin ki yanzu zakije ne kita tunani sannan ni kai na,ban taɓa ganin ki da kowa ba tun bayan rasuwar Muhammad " Jan ƙafana nayi nawuce cikin ɗakina ina zuwa hijabi na nacire na rushe da kuka ya zanyi nima zanso in yi auren kodan shekaruna da suka ja ina yiwa JB mungun so ga duk abun da yayi mun bana ganin laifin shi taya zan fuskan ce shi bayan shima, yana da nashi matsalan duk da ƙarya shi ya keyi mun haka nata tinani har bacci yayi awun gaba dani sai kusan ƙarfe biyar na yamma na tashi jikina duk yayi nauyi . Yau da wuri JB ya tashi ban san kome ya faru ba nidai ya ce mun yana gida hirar ma sama sama ,mukayi yayi mun sallama.abun mamaki da safe da na hau Whatsapp naga har ƙarfe uku bai rufe datar shi ba sannan ya ɗaura status ƙarfe ɗaya na dare . JB munafikin na miji ne sannan ya cika son kanshi dayawa bai damu da damuwar wani ba nashi ya sani . [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam 📚✍🏽 *Wasu mazan musamman samarin zamanin nan har ma da matan sai a hankali basuda imani sun ɗauka babu gida babba ne ko sun ɗauka babu wani shari,a da zata biyo bayan zalinci ina tausaya miki Nusaiba Allah ka shiryar da mu badan halin muba so makaho ne bashi da ido* ```Muna godiya sosai da karɓuwar littafin nan wata mahangar ina yawan samun kira dayawa da ɓangarori da dama da kuma addu,a garemu mu samman yan mata da samari mungode sosai zan sanya number ɗayan marubucin in an Kirani bai shiga ,ba a kira shi ``` LAMBA NA GOMA Ikon Allah ! mamaki ne ya kamani taya JB ya nuna mun bacci yake ji a she ƙarya ne ba baccin yake ji ba ,ban biyo ta kanshi ba naci gaba da aiki na ko in kula shi .har ƙarfe biyu na rana kafun naga yayi mun magana nima sai da naja lokaci kafun na mayar mishi da amsa ya bani haushi daman duk lokacin da zamuyi hira shiyake nuna wa bacci yake ji nikuma ganin tun safe yake aiki a shago sai in tausaya mishi in ce ya kwanta kawai shagon JB bawani abun kirki gare shiba dan nagani in har muna video call a hakan ko yau she fatan alheri nakeyi mishi maza . !maza !! Ya lura da yanayi na yaga raina ya ɓaci shine yayi mun magana ya ,yaga raina a ɓace ce mishi nayi ba komai ya hauni da masifa wai nafara yawan tinani so nake ciwo na yatashi bana tausayin irin kuɗin da ake kashewa ne ko uffan bance ba na barshi har ce mun yayi inyi bacci ko kaɗan ne zaifi .nace to na gagara baccin tinanin matsalar da yake bani ce tafara gundura na. ni ma,abociyar son kasance wa ita kaɗai ce sai in wuni ina ɗaki in ta karanta jarida. a ranan yana tashi daga shago ya Kirani bayan mun gaisa sai ce mun yayi ɗazu naga ranki a ɓace to meyafaru mata na ki gayamun ɗan Allah karki barni a cikin duhu ko dai har yanzu a kan maganar Alhaji Sani ne? Nunawa nayi ba shi bane tambayan shi nayi jiya da yau she yayi bacci "na gane fishin ki dan kinga lokacin da na sauƙa kiyi haƙuri wallahi babu wanda nake so fiye da ke sannan ban taɓa soyayya da wata ba bayan ke da A'isha to meye na ɓacin ran ina bacci ne naji baccin ya,ishe ni shine na kunna data na naso in tashe ki amma nayi tinanin kina bacci banaso in katse miki jin daɗin ki haba mata na kece fa wanda nake tattalin ki. a ranan sai da yasani farin ciki muka ta faranta wa junan mu rai da kalamai masu daɗi daga ƙarshe ya fake da cewa ina kayan sa ,nayi mamaki daya ke tambayan ina kayan sa a she yana tambayan abubuwan jiki nane murmushi nayi nace suna gaishe ka wani murmushi yayi mun daga ƙarshe sai cewa yayi ɗauka mun hoton su in gansu mu gaisa ina neman su . Ko kulashi banyi ba na kashe waya ta kawai na kwanta nayi bacci washe gari ban buɗe wayar da wuri ba sai ƙarfe goma na safe naga yayi mun magana ta Whatsapp a kan cewa "jiya muna magana najiki shiru ?"nima Hajiya nane ta karɓe wayar dan taga menakeyi "me yasa kin kasa yadda dani a kan babana ya karɓe mun waya ta kwanaki "tsiya nifa ba haka nake nufi ba baka yadda ba kenan" tun ranan kullum sai kin gayamun magana a kan mekenan babu yadda a tsakanin mu kina zargina wannan ya nuna koda munyi aure zargi zai shiga tsakanin mu kenan. Zargi ! "In har munka sance mata da mijin kenan ko,ka manta zaɓin iyayen naka ne karfa ka manta auren mu bamai iyuwa bane nida kai taya zaka gayamun abun da zai faranta mun rai bayan kasan ba haka bane meyasa kake son wasa da hankali na nifa macece mai rauni " yaga bashida abun faɗa sai yafake da cewa "ina zuwa minti goma ". a jiye wayar nayi na nufi ɓangaren mahaifiya ta baki na ɗauke da sallama ƙanwata Hibba ce ta amsa shigowa nayi nasamu guna zauna mahaifiya tane da tazame mun kamar Sirika zan iya cewa sirikar ce tunda ni, mai sunan umma ce maman Abba na "yau kuma ziyaran safe ,muka samu ne ? Murmushi nayi nace e Hajiya haɗa shayi nayi nasha na ƙarya daman nasame su ,suna karyawa shiru nayi ta ga yanayin da nake tambaya ta tayi "lafiya kuwa Nusaiba meyafaru "? babu komai Hajiya kawai ina son kasancewa a cikin kune shine nazo gareku karkiji komai babu komai. Hibba ce tada meni da surutu ita da Fatima har da Aliyu sai naji sun ishe nida surutu Aliyu ne yayi magana"Anty Nusaiba ranan nashiga ɗakin ki zan baki kati Abba yace in baki nasamu kina kuka shine nadawo da shi bana son katse miki kukan ki ban san ko zai sakaki farin ciki ko dai yasa damuwar taragu ba shi yasa" Aliyu kenan bani Katina shine banyiwa Abba godiya ba haba da Kabani .kallon mahaifiya tanayi,ita ma nitake kallo nasan ta karanci meke da muna a kan fuska ta batayi mun magana ba nima haka iyayen mu basu cika jawo mu,a jiki ba koda muna da matsala a wasu zamu faɗa wa ko dai a ƙawayen mu ,damuwa sai tayi mana yawa fiye da komai koda wani abu yana damun mu ba lalle ne su tambaye muba. iyayen yanzu kuwa yaran su sun zame musu tamkar ƙawaye koda kaya ne zasuyi anko kamar ƙawaye shine banbancin mu da yaran yanzu. nada sunfi kunya yaran yanzu suna kan cinyar iyayen su zasu amsa wayar samarin su ganin su,abun burgewa ce agaresu . Ganin zama daƙin Hajiya bazai kaini ko ina ba tashi nayi nashiga kitchen a ranan nine na ɗaura mana abincin rana tun da nabar ɗakina ban koma ba sai da na kammala komai kafun nayi alwala na shiga ɗakin danyin sallah na daɗe a kan sallaya ina zaune waya tane tafara ya neman agaji tashi nayi na ɗauko nacire daga key ina buɗe wa naga missed call goma ganin kiran JB guda takwas da sauri nabi ta kanshi bayan nayi sallama ya amsa sai ce mun yayi ina kikabar wayar ki tun ɗazu ina ta kiranki ko dai kintafi kina cin amana ta ne bansani ba,a nawa tinanin ban taɓa jin kin anbaci sunan wani ba. ce mishi nayi niban iya cin amana ba in kaga an samu matsala daga gareka ne bada gani ba "nagaya maka a tsari na bana haɗa soyayya guda biyu a lokaci ɗaya kaima ya na,iya da fitinar ka balle kun haɗu ku biyu kitchen na shiga_shiyasa kaji shiru ban tafi da waya ta ba . Hira mukayi cen nace lokacin da kazo ka samun number mama na gwada jiya wanine ya ɗauka kodai ka cenza number ne ba shi kasamun ba."wani irin magana kike yi haka Hayat taya zan saka miki number da ba ,dai dai ba mekike nufi kenan kin gwada kuwa dan naduba shine nasa miki. " da mutumin da na kira da wanda na rage wasu nombobin na saka wasu na gwada nakira wata ce tana Kaduna duk nayi recoding din na tura mishi ya turo mun da number iri ɗaya dana guna nasan ƙarya ne kawai yayi haka ne dan kar wataran in kirata in wani abu ya faru bana son jayayya kawai barin shi nayi da halin shi. Ban ƙarayi mishi zancen wani abu da ya shafi mahaifiyar shi ba tunda naga in har naci gaba da magana zamu samu babban matsala na rage yawan kiran shi da nakeyi ,badan komai ba sai don in samu sauƙi a zuciya ta a hakan zan iya cewa Ma sha Allah .ganin nayi kwana biyu ban fita ba shirya wa nayi kusan ƙarfe biyar zanje in duba ƙawata maman Sadiq tambayan JB nayi ce mun yayi kar in kai mangari ba in dawo da wuri da to na bishi . naje munata hira da,ita har ƙarfe bakwai na dare ko sallah bamuyi ba ganin kar in tsaya Sallah dare yayi sallama mukayi ,na dawo gida ina zuwa alwala nayi sai da nayi sallah kafun na kira JB yana ɗauka sheda mishi nayi kaina ciwo yake yi sannu ya ce mun tambaya na yayi yaushe nadawo cemishi nayi kusan ƙarfe takwas ya dinga masifa banace karki kai mangari ba ,ba gashi kin dawo da ciwon kai zaki dameni surutu yatayi haƙuri na bashi na sha magani na kwanta. Ƙwana biyu ina kwance ciwon kai ya takura mun ko waya bana,iya ɗauka wayar ma,a hannun Aliyu yake a she JB ya kira shi kuma Aliyu ya ɗauka jin muryan shi yaɗinga yiwa Aliyu masifa . Ina bacci a ka kawo mun wayar tashina Aliyu yayi ya bani ya juya shima bai ce an Kirani ba ranshi ya ɓaci sai ƙarfe goma na dare kafun ya Kirani ,ko sallama bai yi ba ya dinga masifa "a waye kika bada wayar ki yayi mun rashin kunya ko dai a saurayin ki ne wannan cin mutunci ne taya zaki ɗauki waya kibawa wani". Ka tsaya mana ya kake yi mun masifa kamar wani wanda zai dokeni ka tsaya in yi maka magana ka gagara tsayuwa jinayi ya kashe wayar nace zancen banza daman an daɗe ba,ayi faɗa da kai ba ,daga ciwon kai tsintar kai na ,nayi a asibiti an samun dirif juyawa nayi naga guda biyu sun ƙare a lama ya nuna na daɗe a asibiti na uku ne a jiki na a she tun da na kwanta numfashi na yafara sarƙewa ciwo na ya tashi cewa nayi Hajiya ta bani waya ta miƙa mun tayi . Buɗewa nayi cin karo nayi da saƙon JB "kin zaɓi farin cikin mutane da nawa kina ganin kin rufa mun asiri kin soni, ina yaro ƙarami to nima haka ban kula yara sa,annun aure na ba natsaya kulaki ,kema haka manyan masu kuɗi suna sonki kinƙi su ,dan Allah mu haƙura da juna zaifi kawai bana so ki rasa ranki ta dalili na nasan yanzu a kwance kike bakida lafiya ina yi miki fatan alkairi . Jinayi hawaye suna bin ƙunci na ba kalaman JB ne suke damu na,ba yawan damuwa da nayi da shi gani nake in babu shi ba zan ,iya rayuwa ba sau daya wa yawan nunawa samari tsantsan so har su gane son da muke yi musu yafi nasu yawa to nanne hanyar basu daman cin zarafin mu,ko dan na daɗe ban yi soyayya ba sai a kanshi ban sani ba ace masoyin gaskiya ba zai ganni a kwance ya cimun mutunci ba. juyawar da zanyi muka haɗa ido hudu da doctor Ibrahim Sulaiman.... [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA GOMA SHA DAYA Na sha jin ana cewar zuciya tana son mai kyautata mata sai dai na rasa wacce irin zuciya ce a cikin tawa ƙirjin. Da ta kasa amsar yaya Sufyan a matsayin masoyi. Dafe kaina nayi da nake jin kamar zai tarwatse gida biyu don ciwon da yake mini, zuciyata tana harbawa da sauri da sauri. Sai da aka ɗauki mintina biyu kafin ya maido mini da amsa da kalmar innalilahi wa inna ilahir raji'un, sannan ya yi mini saƙon murya da farko na zargi kunnuwa da rashin jiyo mini abin da yake faɗi. Sai da na ƙara saurara a karo na biyu na tabbatar da cewa kuka yake yi bilhaƙƙi, yana shaida mini ba zai iya aiwatar da komai a rayuwarsa ba tare da ina kusa dashi ba ko guje mini da ya yi a baya ya zabga babban da na-sa-ni. Take na ji jikina ya ƙara yin la'asar idanuna ya daina gano mini komai sai baƙin duhu. Rayuwar da muka yi da Suraj ya fara dawo mini sabo fil. Ya kasance malamin mu lokacin muna aji uku a babban sakandiri. Yana ɗaya daga cikin malaman da suka kasance abin tsoro ga ɗalibai, baya dariya ko bisa kuskure yayin da yake koyarwa sannan ba ya ƙarban uzuri balle ɗaga ƙafa. Darasin lissafi yake mana na fi kowa tsoronsa a kaf ajin mu hakan ya sanya ko darasin da yake koyar damu bana fahimta, duk gwajin da ya yi mana sai na faɗi domin ko sahun waɗanda suka haye maki biyar bana kai wa. Hakan ya sanya shi tsaurarawa da sanya ido a kaina fiye da kowa, ko sunansa naji an ambata zuciyata sai ta tsinke balle tozali da fuskarsa da babu rahama a tattare da ita. Tun da ya shigo bugun ƙirjina ya tsananta saboda fargaban kar sunana ya faɗo cikin waɗanda basu haye gwajin da yake mana a duk lokacin da ya kammala darasi ba. Sakina dake zaune kusa da ni ta riƙe hannuna saboda rawar da jikina ya ɗauka kamar mazari, zubar hawayen idanuna ya yi dai dai da sanda ya ƙwala ƙiran sunana. Na ƙara daburcewa. Tsawar da ya daka mini ya tursasa mini runtsun idanuna da har yanzu yake tsiyayar da ƙwalla tamkar burɗaɗɗen famfo. Kaina a ƙasa na iso gabansa na zube akan gwiwoyina, bai ce da ni komai ba sai ma cigaba da ƙiran waɗanda basu haye ba yake yi. Sai da duk suka fito ya ce"ku je ku zauna yau nayi muku alfarmata da ba kullum ake yin katari da shi ba". Abin da ya tokare mini ƙirji ne naji ya wuce na miƙe da sauri zan wuce, ya dakatar dani da faɗin"Madam ban da ke". Na koma da baya duk suka koma suka zauna ban da ni. Bai ce dani uffan ba har sai da ya ƙare darasin tsaf ya bada aikin gida, sannan ya dube Ni fuskarsa tamkar magribar ɗinya haɗi da furta"ke kuma za ki zauna a nan har sai wani malamin ya shigo". Yana dasa aya nan ya fice kukan na cigaba da shi saboda sanyin da duk gaɓoɓin ƙafata ya yi, Sakina ce ke ta jeranta mini sannu wani na bin wani. Shigowar Malam Saminu ya sanya ni jin wani sanyi ya ziyarci sashin ruhina. Ko gaisuwar da 'yan ajin suka miƙe suke yi masa bai amsa ba ya fara da tambaya ta me nake yi a wajen. Na sanar dashi bai ce komai ba illa jijjiga kansa da ya yi ya fice ransa a matuƙar ɓace. Kafin lokacin tashi zazzaɓi mai zafi ya rufe Ni ko da na isa gida ban iya assala komai ba face kwanciya. Hawayen takaici ne suke gudu a bisa fuskata na rasa dalilin tsanar malam Suraj gare ni da yake yi mini hakan, kamar daga sama naje jin muryar yaya Sufyan da ya sanya ni saurin tashi na fita. Zaune na iske sa da yaya Sa'eed da kuma Hajiya. Ciki ciki nayi sallama kafin na yiwa kaina mazauni. Yaya Sa'eed ya hararo ni tare da faɗin"kafurai kika tarar a wajen shi yasa kika adana sallamarki ko?". Da sauri na zaro ido na ce "wallahi nayi" . Taɓe baki ya yi yana mayar da kansa tare da mayar da hankalinsa a wayarsa da yake latsawa, idona na zube a bisa fuskar yaya Sufyan ina yi masa sannu da zuwa. Fuskarsa tamkar gonar auduga ya amsa mini yana ɗaurawa da"kaga autar Hajiya da Momma". Sunkuyar da kaina nayi ina murza zoben dake saƙale a hannu, ban ɗago ba naji ya cigaba da cewa"ki rabu da Sa'eed yau sai an yi masa uzuri shi kaɗai ya san abin da yake ji". Ya ƙare maganar yana kashe mini ido ɗaya dai dai sanda na ɗago kaina, ƙunshe dariyata nayi da ido nayi masa alamar me ya faru?. Kafin ya yi wata magana yaya Sa'eed ya tare shi da faɗin " wallahi na gaya maka ka kiyaye ni fa bana son raini Sufyan". "To yaya babba meye kuma nayi?, naga dai bani na kar zomon nan ba rataya aka bani". A kufule yaya Sa'eed ya kallo Hajiya da ta maida hankalinta ga TV ya ce" ki yi wa yaron nan kashedi bana son raini ni fa". "Ba ruwana da sha'anin ku". Ƙasa nayi da kaina ina dariya don yanda yaya Sa'eed ya yi kici kici da fuska a dole baya son raini, Anty Sadiya ta shigo da tray tana ajiye wa a dinning tare da furtawa Hajiya cewar komai ya kammala. Sannu tayi mata sannan ta iso ta zauna tana tambayar yaya Sufyan abin da ke faru, ɗage kafaɗa ya yi alamar me sa ni ba yana mata nuni da yaya Sa'eed. Har muka wuce dinning area ɗin babu wanda ya ce ƙalla, tare da Anty Sadiya da lokacin ita ce bata yi aure ba muka yi serving ɗin kowa. Kasancewar ranar Abba baya gari. Muna haɗa ido da yaya Sufyan nake jin wani sabon

Chapter 5 of 13