Share this page
1 / 13
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writings by; Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam 📚✍🏽 Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Ina yi wa Allah godiya da ya bani ikon kammala littafina mai suna DA MAI RAI AKE RIKICIN DUNIYA Littafi ne da ya yi duba akan ƙanne, iyaye da irin yadda suke shigo-shigo ba zurfi na ji daɗin yadda littafin ya samu karɓuwa. Labari guda uku basira uku mahanga uku labarin ba iri ɗaya bane ko wani labari mahangar shi daban don haka ku shirya a sannu zaku gane In da labarin ya dosa a wata mahangar Yanzu ma muna tafe da wani littafi mai suna WATA MAHANGAR ku buɗe kunnen ku zaku sha labari tare da faɗakar wa daga garemu littafi ne da zai haɗa marubuta guda uku, zamani uku, da tunani guda uku. Ina ma'abota karance- karance ku matso kusa don zaman jiran fitowar wannan littafi na marubuta Amina maaji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam. Paid book 400 Kai tsaye zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984 Doka bamu yadda a juya mana labari ta kowace fuska ba yin hakan saɓa doka ce garemu duk mai matsala ko labarin yayi dai dai da rayuwar wasu mafita da gyara a ke nema duk da labarin a cikin kashi ɗari kashi sittin gaskiya ne ,ba munyi dan cin zarafi ko sawa wasu sunji sun tsani soyayya ba kowa da irin tashi ƙaddaran kai tsaye kakira_ kikira ɗaya daga cikin marubutan littafin mungode . LAMBA TA ƊAYA So shine ya ruguza min dukkanin tunanina ya ruguza min dukkanin ƙofofin daƙile wani gurbi na soyayya so ya yi min mungun saran maciji da son JB gara na sha guba lokaci ɗaya na bar duniya ashe maza sun daɗe suna yi mana lahani mai kama da ukuba na shiga garari tare da shiga tsaka mai wuya na tattara dukkan yarda da amana na bawa JB ashe mungu ne azzalumi, kuma mayaudari. ina rokon Allah da ya sakawa duk wacce ta faɗa irin tarkon da na faɗa wannan shine da na sanin da na fara yi na amsa tayin JB .da na barshi ya shiga cikin gararin rayuwa da tashin hankalin na godewa Allah da yasa ba a kan soyayyar shi na fara tsintar kaina da soyayya mai ruɗani ba sai in ce a cikin soyayya ni ce ban dace ba don an cutar dani .anyi mun lahani an sa natsani soyayya gaba ɗaya aguna bata da amfani don tayi mun illa a dalilin so narasa wasu abubuwa masu mahimmanci agareni. Saboda soyayyar da muka yi da sauran ya sha banban da na JB duk da ƙaracin shekarun shi sai da ya yi min wayo yaci zarafina girma na bai amfane ni da komai ba sai cizon yatsa. so bai yi min adalci ba yasa na ruguza irin tarbiyyar da iyayena suka ɗaura ni akai Allah ka saka min. A wani safiyar asabar ne ina cikin zama na na hau yanar gizo misalin ƙarfe bakwai da rabi na safe 7:30am don ganin wani wainar ake toyawa na hau shafin sada zumunta wato wajen da ya haɗa mutane daban-daban wato facebook duk da a yanzu kasuwar shi ta kwanta yanzu yayin TikTok ake yi yawanci yan mata da samari nanne wajen samun nishaɗin su .amma hakan bai dame ni ba don duk in da kayi sabo to nan ne hanyar farin cikin ka. ba da kowa nake mutunci ba bana yawan posting amma mutane da yawa sukan yi min magana kuma muyi mutunci da mutunta junanmu har ma da girmama wa a tsakanin mu. Wani naga ya yi min magana ganin sunan yasa na amsa don kuwa sunan mahaifinmu iri ɗaya da shi mun gaisa sosai sannan na mutunta shi kwana biyu da faruwan hakan ranar Laraba ina zaune misalin ƙarfe tara na safe 9am naga wani baƙon number ya Kira ni da kamar ba zan ɗauka ba kawai wani tunani nayi na ɗauka can! sai naji ya yi sallama ta ɓangaren shi na amsa "kin san da waye kike magana?"cewa nayi gaskiya ban sani ba . "JB ne kin gane ni" waye haka kenan?" wanda sunan mahaifinmu iri ɗaya "na gane amma waye ya baka number ta kuma waye ya baka izinin kira na? "Ki yi haƙuri babu wanda ya bani kawai nine na samu ki yi haƙuri don Allah "shikenan yaya na ba komai na gode Ka ci darajar suna "godiya nake sosai gimbiya ta sarauniyar raina. Murmushi nayi don gaskiya ya yi matuƙar bani dariya da Hausar shi irin ta Barebari. Bayan mun gaisa shikenan ban ƙara jin labarin shi ko da na minti ɗaya ba a ranan haka ban sa komai a raina ba don ni ba komai a raina sannan nasan mutunci ne yasa ya ƙira ni ban san in da ya samu number ta ba tunda ni wajen shekaru hudu ban yi soyayya ba naso ganin hoton shi amma ba shi bane a kan dpn shi na Whatsapp ba, bayan Kwana biyu naji ya yi min magana ya ƙira ni da sunan da ni kaina muddin a ka kira ni da sunan bana jin daɗin shi wato a kira ni da baby, a dama bai yi min amfani ba balle yanzu. "Me yasa zaka Kira ni da wani sunan da gara guba ma da shi? '' subhanallahi! me yasa kika ce haka?"e babu wani suna da zai burge ni indai ta shafi soyayya ce "ki yi haƙuri nima da soyayya na zo miki sannan da maganar aure". Aure kuma? "bana jin soyayya a raina ka bar ni inyi rayuwa ta ba tare da wani ɓangare na jiki na ya samu matsala ba, don kuwa maza duk halinku ɗaya duk da sunan ku daban ne, amma hali kam duk ɗaya ne,"ka yi haƙuri na daina soyayya"ki taimaka mun ki karɓi tayin soyayya ta ba zan taɓa gudun ki ba zan kula dake da baki dukkan kulawa daga gare ni". dogon numfashi naja saboda abun ya dame ni wallahi ko kalmar so bana son ji ko kaɗan saboda yana matuƙar ɗaga min hankali ba na kaɗan ba, na rasa dalili, a ranar ya kira ni yafi sau goma yace min sai mun yi video call ni kuma na kafe, bani da ra'ayin shi tunda ni ba ma'abociyar yin shi bane da safe ina buɗe waya ta da saƙon shi zan fara cin karo tun bana yarda har na fara sakin jiki da shi in ya kira mu zage mu yi ta hira da shi sosai A nan ne nake sanar mishi nifa ba yarinya bace ya kamata ya gane nayi mishi bayanin yadda shekaru na shima ya gayamun na shi duk da ba a nan gizo ke saƙar ba don na ba shi shekaru kusan biyar ma'ana na girme shi kalman da yace min "wallahi shekaru ba za su taɓa ruguza mana soyayyar mu ba ko dai su hana mu auren junanmu ba. ''tura min hoton ki' don Allah' ba musu na tura mishi shima ya turamun nashi tabbas yaro ne sosai don wani zubin a hoton kaya ne ke sawa a ganshi kamar mai yawan shekaru da yawa tun daga nan muka yarda da juna har muka amince da juna ya yi min dukkan bayani a cikin Borno yake ni kuma cikin Damaturu nake ban ɓoye masa komai ba kamar na ƙara masa wutar so na a ranshi amma na sanar masa da irin lalurar da nake fama da ita na ciwon zuciya ya yi min fatan samun sauƙi. Akwai wani ranar da ya tambaye ni me ya raba ni da tsofin samari na a yadda ya ganni bazai iyu a ce banida samari ba . Numfashi naja sosai " Na farko mun rabu ne sakamakon shaye-shaye na biyu mun rabu saboda na kama shi yana soyayya da ƙanwata a ɓoye na uku saura sati biyu auren shi ban sani ba sai na ƙarshe Muhammad wanda har in koma ga wanda ya halicce ni ba zan samu madadin shi ba " Muhammad ya So ni ya ƙauna ce ni, in kuwa abubuwa zai yi wan da ya shafi jin daɗi tabbas baya barina a baya koda sutura ce ko da shadda zai ɗin ka to kala ɗaya zai ɗinka mana in anyi musu albashi zuwa yake garin mu muyi kusan kashe kuɗin in zai koma yabar min kuɗin kashewa . kasancewar jinyar mu ta ciwon iri ɗaya ce ba ya ɓata min rai, bai taɓa gaya min abun da zan ji raina ya ɓaci ba yakan baro garinsu don kulawa da tawa lafiyar, mahaifiyar shi da sauran danginsa, suna mutunta ni a ganin su, haɗuwa dani yasa ya samu sauƙi don baya yawan kwanciya rashin lafiya a kan da, su biyu iyayen su suka haifa duk da suna da kuɗi amma baya garesu ni yake so yakan iya baro garin su yazo guna ya kama hotel don ya kula dani a gidan mu muke wuni Gani yake yi kamar za a sace ni ko wani ya kwace mishi ni shekarun mu uku da shi an yi mana baiko kenan komai na akwati tare muka siya ina makaranta zaije department ɗin mu ya jirani na samu gata sosai, ban taɓa jin wani abu zai raba mu ba, ashe muna namu ne Allah na nashi wannan rana ta zame min wani ɓangare na jiki na da duk lokacin da na tuna sai na zubar da hawaye . Kuka ne ya kuɓuce min sosai nai ta kuka na gagara daina kukan har yakai ga JB ya tambaye ni ki dai na kuka me ya samu Muhammed? tuna min da ya yi shine ji nake kamar zuciya ta zata fashe don fargaba da ruɗani . "JB Muhammad ya rasu ciwon ciki ne sanadi ciwon zuciya bata zama ajalin sa ba duk da ita ce jinyar sa sanadin rabuwar mu ,ta har abadan don ranar Laraba shine ranar da Muhammad ya amsa kiran mahaliccin sa ,wajen misalin ƙarfe takwas ya kira ni mun sha hira sosai da shi wani kalmar da ta tasar min hankali da ya gayamun "yau ba kya son mu yi hira ki kasan ko mutuwa zan yi? "ya Muhammad to sai me Allah ya jiƙan ka" ya dame ni da surutu gashi bacci nake ji yana yi min magana kamar wasiyya wajen ƙarfe tara yace min cikin shi na ciwo nace yasha magani yace babu nace ya kira maman shi yace ba kati a wayarsa dole na kira ta nace babanta cikin shi ciwo yake yi mishi a aika mishi magani zai sha ta bayar a ka kai mishi bayan wasu lokutan na kira shi don tabbatar da ya sha maganin, a daren mun yi hira sosai sai cewa ya yi "muddin nabar duniya ban yarda a ɗauki kayana a bawa Kowa ba don kayan auren mu da sunan ki na siya bada wata ba sannan ban san wa zai riƙemin ke amana ba ,ba lalle bane wanda zai soki ya kulamun da ke yadda ya kamata ke macece mai sauƙin kai naso mu rayu tare mu gina rayuwa kash zanyi tafiya gari mai nisa wanda ba lalle ne ki zoba ko da kinzo .a matar wani zaki zo in sha Allahu in dai baki cenza hali ba zaki samu mai irin halina ."kai dai Allah ya baka lafiya "Amin ya rabbi". Har sha ɗaya kafin nayi bacci na barshi jin waya ta na ƙara neman agaji shine ya farkar da ni"ya Muhammad ka kwanta kayi bacci mana kaji "shikenan zan kwanta amma muddin kika ga ban tashi da wuri ba ki tasar dani kinji da to na bishi saboda bacci da nakeji sosai . Washe gari Shine ke zuwa ya tasar da iyayen shi sallah amma sunji shiru har kusan goma na safe aka aiki yaro yaje ya dubo shi yace yana bacci, "bacci kuma kodai bai samu yayi bacci da dare ba in ji mahaifiyar shi kabar shi zuwa anjima sai ka tasar da shi, yayan shi ne ya shigo don tambayar shi a na neman shi a office a kwai signature (saka hannu) ɗin da zai yi " ba shida lafiya kaje zan gaya mishi' in ji mahaifiyar shi da sauri ta wuce ɓangaren shi ta dinga kira babana ka tashi mana ayya kayi sallah kuwa jin shiru bai motsa ba ashe rai yayi halin shi ɗaga hannun shi ta yi ta duba saitin zuciyarshi ashe zuciyar ba lalle ne tayi aiki ba, ba a son yaushe ya rasu ba, addu'a ta yi mishi tare da hawayen da suka biyo kuncinta masu zafi yana ta zuba, ta gagara fitowa daga ɗakin ana cikin haka ne ya yi daidai da lokacin dana ke kiran wayar . Mum ce ta ɗaga a take zuciyata ta tsinke jin kalmar haƙuri da take bani da kuma yi min nasiha, sunana ta kira Nusaiba nasihar da tayi min shine ya tabbatar min akwai babban matsala sosai . Sai da taga na samu nutsuwa kafin ta gaya min rasuwar Muhammad na shiga fargaba tare da ruɗani, a lokacin muka haɗa kayan mu sai Bauchi mutane da ke zuwa yawanci a ni ake yiwa ta'aziyya, na rame sosai, so bala'i ne! akwai wata kalma da mom ta gaya min , akan in yi haƙuri Allah zai bani wani a madadin shi kwanan mu shida kafin muka dawo nasha wahala muna dawowa na kwanta jinya kamar ba zan yi rai ba don har aman jini nake yi sai da nayi wata biyu a asibiti kafin na dawo dai dai na sha fama da addu'a na fara mantawa . "Ka ji waye mahaƙurci wanda yayi so tsakani da Allah babu algus a cikin ta ko". jikin shi yayi sanyi sosai haka ya daure ban taɓa jin labarin da ya tarwatsa tunani na ba, hakika na tausaya miki, Allah ya mishi rahama kin bani tausayi labarin akwai tausayi a cikin ta Allah ya bamu ikon yin gyara kuskuren mu Amin ya rabbi "Nusaiba zan riƙe ki tamkar jinina zan nuna miki gata sosai in sha Allahu zan kwatanta irin abun da Muhammad yake miki koda bai kai nashi ba kisa a ranki kin samu miji shekara huɗu da kika yi ba tare da soyayyar wani a ranki ba rabona ne ya tsaida ke daga kula kowa 'ki bani zuciyar ki zan mallaka miki ruhina da tawa zuciyar ". Godiya nayi mi shi na kamu da son JB a kwanaki kaɗan a raina saboda kulawa da yake nuna min har jina nake na tafi wata duniyar sauran rayuwa ko, in ce na buɗe wata rayuwa mai tare da jindadi, JB ya So ni ya ƙauna ce ni sannan yana kulawa da ni amma ba zan taɓa haɗa soyayyar Muhammad da ta JB ba don shi Muhammad so mai tsafta yake min don ko ya tsana bai taɓa riƙewa ba. JB kuwa sai yasa in tura mishi suran jiki na in naƙi turawa ya yi fushi sosai ya daina kula ni duk da yawan shekaru na soyayyar JB ta yi min kamu amma abun da na lura da shi shine. Suran jiki na yake so amma son bata da yawa gare shi son da nake mishi yafi nashi yawa nayi tafiya ya ce dole sai na tura mishi hoton ƙirjina naƙi kasancewar ina gidan biki shine yayi min fushi ya daina kula ni, duk hankalina ya tashi ba na kaɗan ba gashi na kamu da son shi wanda, raba mu zai yi mun illa tabbas . Wajen sati ɗaya bai kula ni ba can dai na shiga fargaba sai da natura mishi' kafin yayi murmushi muka shirya... Takun farko [11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam 📚✍🏽 Paid book 400 zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068758984 LAMBA NA BIYU *Masu karatu ku shirya wajen yin comments da sharhi marubuta guda uku zamani uku tunani uku karku sake ayi babu ku ,zaku sha karatu cikin aminci fatan alkairi gareku*. Yanzu kenan na fuskanci bana ranshi wata ɗaya muka yi da shi wanda bai nemi komai daga gare ni ba yawan tura mishi hotuna na da nake yi cikin kaya masu daraja wanda kaman doka ne ya bani zan tura mishi guda uku a kowace rana da farko ya nuna min shi na Allah ne don baya son yawan sa gyalen da nake yi ko fita zan yi tabbas kamar mijina sai na tambaye shi . a bu ɗaya na ɓoye mishi aiki da nakeyi amma shi kanshi ganin walwalan da nakeyi sannan ban taɓa roƙon shi ko mai ba ,bashida arzikin da zan roƙeshi ko mai wannan, ya samo a saline da irin kulawa dana ke samu daga iyaye na.yace kar in jima nace to, in kuwa ya kai awa ɗaya zai ta kira na ya dame ni in koma gida ya zo mun a kan shi na Allah ne tunda nake ban taɓa soyayya marar tsafta da kishin kaina kamar na JB ba, samarin da nayi duk sun girme Ni daga wanda ya bani shekara biyar sai shida Muhammad shekara biyar ya bani.a haka ban taɓa kallon shi a zahiri ba har muka yi kusan wata biyu. Kamar wani ubana, ni nake fara kiran shi in ce mishi ina kwana mu gaisa baya aiki shago ne da shi na siyar da kayan ɗinki, ƙarfe tara yake fita na safe ni kuma muddin na tashi to tabbas zan tashe shi wajen kiran number shi dole ya tashi har zai ce min . "wato ke in kin tashi sai kin tashe ni ko me zan yi miki ne kike yawan tashi na? "In kuwa baka son in tashe ka to ya zama dole ka rufe wayarka amma yau ina son muyi magana ". A kan me kenan! A haka ya yarda muka yi ta charting ina tambayar shi "don Allah ka gaya min baka taɓa soyayya bane sai a kaina naga kana yawan zumuɗi na sosai a ranka ? Numfashi ya ja kamun ya fara yi mun magana kamar haka "nayi soyayya a baya wanda na so faɗawa cikin tashin hankali na so ta sosai,tunda muke da ita nine na fi damuwa da ita akan ita, yar unguwar muce sunan ta A'isha da farko ta So ni daga baya kuwa ta shiga yi min wulaƙanci in ban kira ta ba ba zata taɓa kira na ba in kuwa ta kira ni wani maganar ce kawai zata gaya min daga baya wulaƙancin yayi yawa na haƙura". Amma yanzu kam ba kwa tare ko don gaskiya ni kishi ne dani? amsa ya bani da basa tare amma yana ganin status in ta ɗaura shima haka, "haba Noor ina so ka goge number ta daga wayarka don tunda bata son ka ni kam ina son ka, ya tabbatar min da ya goge sannan ya tura min number ta nace me zan yi da shi? anan ne na gane tabbas soyayya da yaro yarintar zai yi ta maka na nunawa JB tsantsar soyayya nasan zan samu matsala a gun iyayena don koda giya suka sha ba zasu taɓa yarda in auri yaron nan da sa'an ƙanina na uku ba amma babu ruwa na don shi nake so shine mahadin dukkan rayuwa ta, suna muka sawa junan mu Noor shi kuma Hayat tsabagen kunyar shi da nake ji ban taba kiran shi da sunan shi ba nasan duk wata soyayya da ba'a gina ta ta fuska mai kyau ba an dinga samun matsala farkon abun da ya ɓata mun rai kullum nine ke yawar kiran shi amma shi sai ya wuni bai Kira ni ba ina zaune naje gidan ƙawata kenan nayi' mishi' sallama ya amsa a WhatsApp bayan mun gaisa shine nace mi shi kai kullum nine ke yawan kiran ka amma ba komai kamar daman jira yake yi ya fara gaya min magana . Ke nifa ba za ki takura min ba taya kinsan ina da shago sannan mutane zasu zo siyan kaya a guna in ƙi kulasu in biye Miki mu yi hira nifa kina takura min gaskiya wato ke dai burinki, kiji murya ta ko, gaskiya ki canja tunani " duk yasa jikina yayi sanyi a hanyar dawowa gida ne na kira shi nayi mishi' tas . Ina da zuciya in raina ya ɓaci nayi mishi magana "Kaci sa'a don na kira ka don na cire ka cikin samari ka sani in na jure maka mai ƙarancin shekaru ba zata jure ba sannan ya kake mai da ni kamar wata marar gata sai kace soyayyar dole . ka sani banyi banzan da wani bazai ganni da daraja ba yawan faranta maka da nake yi baya bayyana maka na rasa masu sona ba kaji da kyau . Yaga raina ya ɓaci yayi shiru ko kulani bai yi ba kwana uku na daina yi mishi magana don in karɓawa kaina yanci tun daga nan ban ƙara shiga wani ruɗani na rashin mutuncin saba. Naƙara da cewa muddin kawuce kwana uku baka zo in da nake ba wallahi ka nemi wata bani ba sannan in har kana tunanin ba zaka zo guna ba saboda mahaifiyar ka bata gari ka zauna sai ta dawo kace an bar maka kannen ka nono suke Sha

Chapter 1 of 13