Share this page
6 / 13
dariya yana zuwar mini dole na danne shi don gudun ɓacin rai yaya Sa'eed. Gyaran murya yaya Sufyan ya yi, yana kallon yaya Sa'eed da yake juya cokalin kawai a cikin abincin ya ce"malam ka ci abinci da don wallahi yunwa ba ta da hankali, kuma ba ƙanwar su Abba ba c...". Bai ƙarisa ba sakamakon cokalin da ya jefa masa ya kauce da sauri yana dariya. Tsam ya tashi yana huci"Hajiya na gaya miki yaron nan ya gama raina ni, gidan Momma zan koma". Yana gamawa ya fice daga falon gabaɗaya. Duk dariya muka tuntsire dashi ni kam har da riƙe ciki Hajiya ke tambayan yaya Sufyan abin da ya faru. "Wata yarinya yake so tun da daɗewa ya kasa faɗa mata. Sun daɗe suna alaƙa a matsayin aboka ashe shi ba haka ya ɗauka ba, sai da yau da na raka shi wajen ta muka iske ta da wani da ya tambayi wanene sai take sanar damu cewar wanda zata aura ne. Shine fa duk ya birkice yake ta wannan ƙuncin, bayan shi ya tsaya ganin ruwa kwaɗo ya yi masa ƙafa". Jijjiga kansa kawai Hajiya tayi ta cigaba da cin abincinta, ni da Anty Sadiya kuwa sai da muka ji ƙwaƙwaf don har hotonta ya nuna mana 'yar guntuwa da ita a gefensa. Na sha dariya sai da na ji cikina ya fara ƙullewa sannan na tsagaita. Muna gamawa na haɗe kwanukan na kai kicin, nake naji cikina ya bada sautin ƙululu tunawa da nayi da aikin gidan da malam Suraj ya bayar da ban yi ba. Na fita da sauri zan wuce na yi kiciɓus da yaya Sufyan ya tsare ni da ido kafin ya furta"meye kika birkice haka?". Take ƙwalla ya ciko mini koramar idona, muryarta tana rawa na furta"aikin gida aka bamu kuma ban iya ba". Taƙaitaccen murmushi ya yi"to shikenan ki je ki jira ni na kaiwa Sa'eed abinci, sai nazo na taya ki ko?". Kaina na ɗaga masa cike da jin daɗi, na ware idona akan fuskarsa da har yanzu yake sakin murmushi na ce"baka taɓa fushi da yaya Sa'eed ". Rausayar da kai ya yi yana shafi ƙeyarsa kana ya ce"shima baya iya fushi da ni na gudun lokaci, na tabbatar yanzu yana can yana tunanina". Murmushi kawai na yi na matsa na bashi waje ni kuma na fita izuwa ɗaki. Sai da na yi wanka na yi sallan isha'i sannan na ɗauko takardan ina ƙara dubawa, a saki sakekken ajiyar zuciya gani na saka gane komai a ciki. Ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan fuskarsa yaya Sufyan da yake tsaye a ƙofar ɗakin ya naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa. Na kwaɓe fuska na ce"kai fa nake ta jira". Ya saki murmushin da ya zamo ɗabi'arsa kana ya tako a hankali ya zauna a ƙasa a gabana. Na yi saurin dirowa daga kan kujera da nake na dawo ƙasa nima na zauna, dariya kawai ya yi ya jijjiga kansa ya umarce ni da na miƙo masa takardan na miƙa masa da rawar jiki. Ya karɓa yana dubawa sai ya ya kalla sosai sannan ya ce na miƙa masa biro na bashi, ya fara solving ɗin tambayoyin sai da ya gama tas ya ɗaura mini takardan a bisa cinya. Cike da tsantsar farin ciki na zari takardar ina kallo na mai da idona gare shi na furta"na gode sosai ka ceci rayuwata". "Na gode sosai ka ceci rayuwata". Ya furta cikin kwaikwayon muryata na yi kasa da kaina ina yin dariya, ya miƙe tare da faɗin"bari na wuce gobe ina da class ɗin safe". Nima tashi tsaye na yi"kuna ƙoƙari fa bi kam gani nake kamar ba zan iya koyarwa ba". Ya galla mini harara"ai kuwa koyarwa ba ƙaramin aiki bane sai dai lecturing da sauƙi. Mafi yawan lokuta guiding ɗin su kawai za ka yi". Jinjina kaina na yi alamar gamsuwa da zancen na san, na rako shi har wajen motarsa ina masa addu'ar sauƙa lafiya da saƙon gaisuwata ga Momma. Washe gari na tashi cikin nishaɗi haka na tafi makaranta, darasi ɗaya muka yi na biyun kuwa Malam Suraj ya shigo. Tsit ajin ya ɗauki shuru tamkar babu wani halitta mai motsi a cikinsa. Ya ce a haɗa masa aikin gidan da ya bayar da zumuɗina na ciro nawa daga cikin jaka na miƙa. A ajin ya zauna yana makawa har ya gama ya fara ƙiran waɗanda basu haye maki biyar ba, kamar daga sama na ji ya ambaci sunana. Cikina ya bada ƙarar ƙululu na miƙe tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki na fita. Bulala uku uku aka yi mana muka dawo muka zauna, tunda na kifa kaina akan benci ina kuka har ya gama darasin ya fice ban ɗago ba. Sai da aka tashi tara sannan na fito na wanke fuskana, Sakina ta zauna kusa da ni tana faɗin"don Allah ki daina wannan kuka tun ɗazu fa kike yin sa". Ban kula ta don yanda nake jin wani zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni. Ta dafa kaɗata"ki yi haƙuri don Allah". Sai a lokacin na yi ƙarfin halin faɗin"ke fa ki haye maki biyar kuma wanda na yi kika kwafa, kawai ni ɗin ya tsane ni me nayi masa?". "Bai tsane ki ba hasalima sonki ne ya yi masa da har ya rasa ta yanda zai fara sanar dake. Takaicin ba zai iya tunkarar ki da zancen ba ya sanya shi yi miki waɗannan abubuwan". Tare muka waiga ni da Sakina don ganin mai maganar, Sabira 'yar ajinmu ce tsaye a bayan mu kafin ta tako ta zauna akan dakalin ƙofar ajin da muke zaune a kai. "Ke Sabira ke kuma yaya aka yi kika san duk wannan, shi ya faɗa miki?". Ta yi mana wani kallon da na gaza gane abinda take nufi kafin ta furta"ba shi ya faɗa mini ba amma kowa dake cikin makarantar nan ya san da wannan abunda na faɗa muku yanzu. Malam Suraj son Surayya take yi so mai tsananin gaske, a cikin biyu nan dole akwai dalilin da ya sanya shi yake nuna kamar ya tsane ta a fili. Ko dai yana tunanin ba zai iya samun soyayyarta ba bisa wasu dalilai nashi na karan kan shi, ko kuma ya na tsoron ya sanar da ita ta ƙi amsar sa hakan ta jawo masa raina daga sauran ɗalibai". Duk shuru muka muna nazarin zantukan bayan daki-daki. Ta katse mana hanzari ta hanyar cewar" kun taɓa lura da cewar duk ranar da ya shigo aji bai ganta ba baya taɓa samun nutsuwa?. Kuma ranar komai cikin sanyin jiki zai aiwatar dashi saɓani in tana cikin ajin. Kullum sai ya ƙira sunanki cikin waɗanda basu haye makin ɗin da yake buƙata a gwajin da yake mana ba, don kawai ya gan ki ko kin yi dai dai fa sai ya ƙira sunanki don kawai ya sama nutsuwa a ransa ya kuma tabbatar da kasantuwarki cikin ajin". Ƙarƙafan ajiyar zuciya na sauƙe ina zabga tagumi da hannu bibbiyu, kaina gabaɗaya ya kulle na rasa ta inda zan fara tantance zantukan na Sabira na yi musu rankaɗe da rairaya na ware aya na watsar da tsakuwa. "Maganarki abun dubawa ne tabbas, da akwai alamar ambayar akan abubuwan nan da Malam Suraj yake aikewa. Amma ta yaya zamu tabbatar da abinda kika faɗa". Sai da ta gyara zaman ta kana ta ce"lokaci ne zai tabbatar da hakan amma ina da tabbacin malam Suraj yana son Surayya. Kuma dole komai daren daɗewa zai furta hakan a gare ta domin ba zai taɓa iya riƙe abin a ransa ba, sannan ko ba ki amshi tayin soyayyar sa ba sai sama nutsuwa domin ta furzar da abinda yake sukar ransa har yake masa zogi a cikin zuciya". Tsam na miƙe tsaye ina cewa"don Allah ku daina wannan hashashen domin ba zai taɓa zama gaskiya ba". Ina dasa aya a nan na koma cikin aji na zauna, sai dai na gaza samun nutsuwa har aka tashi ban dawo dai dai ba. Kwana nayi da tunanin abin a raina ina kwantanta girman bayyanannen tsanar da yake nuni mini a zahiri, babu yanda za'a yi a ce wai akwai soyayyata ko da misƙala zarratin a cikin zuciyarsa. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA GOMA SHA BIYU Tsanar da Malam Suraj yake gwada mini kullum ƙara ƙaruwa yake yi, ko yaushe ina cikin waɗanda suka faɗi a gwajinsa. Hatta 'yan uwansa ragowar malamai zai da suka fahimci hakan . Bana taɓa samun nutsuwa idan yana cikin aji haka nan bana taɓa fahimtar darasinsa, sai dai bayan fitar da Sakina ta koyar da ni ƙalilun abubuwan da ta fahimta. Domin zafi da tsananinsa ya sanya ba kowa yake fahimtar darasinsa ba. A haka lokaci ya cigaba da tafiya, rayuwa ta na juyawa har aka yi bikin Anty Sadiya lokacin muna hutun ƙarshen zangon karatu. Muna komawa babu ɗadewa muka zana jarabawar jamb. Koda aka sake sakamako ina ɗaya daga cikin waɗanda suka ci maki mafi yawa a kaf makarantarmu. Da shugaban makarantar ya gabatar da mu a gaban assembly tare da shawarar raguwar sauran ɗalibai da su yi koyi da mu su zamo jajirtattu kuma masu mai da hankali akan harkan karatun su. Ina sauƙa daga izuwa wajen da sauran ɗaliban suke tsaye na ci karo da Malam Suraj yana nufi wajen. Da hanzari na rusunar da idanuna ƙasa saboda wani kallon da ya jefo mini yana ɗaure fuska tamau tamkar magribar ɗinya. Har aka gama assembly ɗin ba ni da nutsuwa muka koma aji, muna tsaka da gudanar da darasin kusa da na ƙarshe a ranar. Wata yarinya daga ajin bayan mu ta nema izni ta shigo ta na cewar"wai Surayya ta je inji Malam Suraj". Take na annurin dake fuskana ya kau zuciyata ta shiga dakan lugudan tara-tara sau tara. Muka haɗa ido da Sakina ta jinjina mini kai alamar na tashi na je, a sanyaye na miƙe ina taka ƙafata a hankali har na isa cikin ofishin malamai na shi ne na biyu daga gefen hagu. Na kai hannu da nufin bubbugawa na ji saurin janyewa, ina runtse idanuna da ƙarfin gaske. Ina karanta duk wani addu'ar da ya fara zuwar mini a rai har na sama nutsuwa a cikin raina. Na ɗaga hannu zan buda aka buɗe ƙofar. Idanunmu suka sarƙafe a cikin na juna babu shiri na kawar da nawa gefe ina ƙoƙarin danne ruwan da nake jin yana ƙoƙarin zubawa daga koramar idanuna. "Sai yanzu za ki zo?". Ya furta a zafafe na jijjiga kaina da sauri alamar a'a. Ya sa ki tsaki yana juyawa ciki na taka a hankali raina cike maƙil da tsoro na bi bayansa. Na daɗe a tsaye ba tare da ya ce da ni komai ba, sai ma mayar da hankalinsa da ya yi ga making ɗin wasu takardun dake gabansa. Jin ƙafafunsa sun fara rawa su na alamta mini gajiyarwar su na ɗaukar nauyin gangar jikina ya sanya ni cira kai na kalle shi. "Malam muna darasi ne na fito". Sai da na cire rai da samun amsarsa kana ya furta mini"na fi ki sanin hakan ai". Ban kuma cewa komai ba wasu hawaye suka gangaro izuwa kan kuncina. "Na ji wai ance kina ɗaya daga cikin waɗanda suka fi kowa cin jarabawar jamb a makarantar nan ko?". "E". "Ya yi kyau keep up ruwa good work". A sanyaye na furta"na gode". Shuru ya kuma karaɗe ofishin sai can ya ya ce"ki fice min daga ofishin". Da hanzarina na fita na jawo ƙofar na rufe, sai da na koma cikin aji na sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi ina dafe ƙirjina. Haka har muka fara zana jarabawar waec da neco, yaya Sufyan ya cika mini alƙawarin da ya yi mini na cewar matuƙar na yi ƙoƙari a jarabawar jamb zai saya mini waya. Sauranmu kwanaki biyar mun kammala jarabawar aka ce mu je ofishin Malam Suraj domin cike abubuwan da za a sanya mana a cikin photo album. Tare da Sakina da kuma Sabira muka je duk da ni ce gaba dasu a layi amma ya ce na jira sai kowa ya gama sannan ni na yi, haka na zauna sai da kowa ya gama sannan ya ba ni na nawa lambar waya, adireshi da wasu abubuwan. Ina fitowa na iske su tsaye suna jiran fitowata Sakina ta na riƙe da jakata. Ina isa na dafe kaina ina faɗin"wash". Maimakon na tsinci tausayina wahalar da na sha a fuskar Sabira sai ma dariya ta tuntsire dashi tana cewar"Surayyan Malam Suraj". Tunin na wartsake ina jefan ta da harara"Allah ya kiyaye wallahi". "Ke dai ina raba ki wallahi yarinya, ki yarda ko kar ki yarda da bawan Allahn nan son ki yake yi. Shin ba ki lura tunda muka fara jarabawar nan ya ƙara shiga cikin wani hali ba?. Kin san dalili?". A tare muka jijjiga mata kai ni da Sakina, ta gyara tsayiwarta kana ta ɗaura da"saboda mun kusa kammala makaranta, zai dai na ganin ki zai daina jin muryarki. Ta wani ɓangaren kuma cire yake da tsoron kar ya rasa damar sa gabaɗaya akan ki". Taɓe baki na yi ina karɓar jakata na rataya a kafaɗata, muka fara tafiya zamu fice daga cikin makarantar kasancewar duk an fara watsewa daman iya mu da muke zana jarabawar ce muka zo. "Na fara yarda da zantukanki Sabira wataƙila duk abinda kike faɗa ya kasance gaskiya". Ban tanka musu ba na yi kunne uwar shegu har muka isa bakin gate. Bamu yi jiran mintuna goma ƙwarara ba yaya Sufyan ya iso domin ɗaukar mu. Dai-dai sanda Malam Suraj yake fitowa daga cikin makarantar a bisa kuskure idanuna suka gano mini gefen da yake, ban ƙara gigin ƙars kai idanuna wajen ma muka shige cikin motar. Sabira aka fara sauƙewa sannan Sakina muka yi sallama cike da son juna. Gidan Momma na ce ya kai ni, ya kallo ni fuskarsa kamar gonar auduga ya ce"an gama ranki ya daɗe". Murmushi na saka"yaushe zaka koya mini mota?". Ya ɗan zaro ido a lokacin da yake karya kwanar da zata sada shi da unguwar kafin ya furta"so kike Hajiya da Momma su yi min tarin dangi ko?". "Me yasa to?". "Su ce zan tsorita musu ɗiya ma, kin san da har yanzu basa yarda su shiga motana. Kullum ƙorafin su wai na cika gudu". Dariya na saka saboda yanda ya yi maganar har muka isa ban daina ba. Yana gama daidaita parking na fito da guduna na shiga sashin Momma. Shi kuma ya koma makaranta. Nan na wuni sai bayan sallan magrib ya mai da ya ni gida, bai tafi ba sai ƙarfe goman dare na rako shi har jikin motarsa. Sai da na hana shirin kwanciya tsaf na tuna da wayata, na tashi na ɗauko ta a cikin kayana da nake ajiye ta. Na kunna sannan na koma na kwanta ina latsawa. Whatsapp na shigo domin tambayar yaya Sufyan ya isa gida lafiya, na ci karo da saƙo da wani baƙuwar lambar an yi mini sallama cikakkiyar. Ban amsa ba sai da na turawa yaya Sufyan saƙon babu jimawa ya maido mini da amsa. Haka muka cigaba da yiwa juna saƙo har dare kusan sha ɗaya ya yi ya ce na kwanta. Washe garin ranar bayan mun fito tara, wannan yarinyar jiyan ta ƙara dawowa tare da isar mini da saƙon Malam Suraj yana ƙira na. Cikina ya ƙululu muka haɗa ido da Sakina, ta jinjina mini kanka tana ɗaurawa da"ba komai tashi mu je". Tare da ita muka je ofishin yau su biyu ne a ciki shi da Malam Saminu muka haɗe baki wajen yi musu sallama, shi kaɗai ya amsa mana amma shi gogan ko ɗaga ido bai ya mana kallon arziki ba ya cigaba da latsa wayar dake hannunsa. "Surayya Sufyan". Malam Saminu ya furta na amsa masa ina sunkuyar da kaina ƙasa. "Ko da bayan kun gama nan ki cigaba da maida hankali ga karatunki kamar yanda kika saba, in sha Allah za ki yi nasara". Kaina na jinjina masa ina cewa"in sha Allah ". "Kuma ce maka yi cewar lalle ne in ta gama nan ɗin ta cigaba, wataƙila aure zata yi don jiya har ƙofar makarantar nan saurayi yazo ya ɗauke su". "Saurayi kuma?". Malam Saminu ya furta yana bin mu da kallon mamakin da ya wanzu a fuskarsa. Ban iya furta masa ko kalma ɗaya ba illa Sakina da ta ce"wannan wanda ta dauke mu jiya yayanta ne, kuma mafi yawan lokuta shi yake zuwa ɗaukar ta". "Yauwa sai yanzu na ji batu". Sai a lokacin ya ajiye wayar dake hannunsa ya kafe mu da ido"so yanzu kenan auren ne ko kuma karatun?". "A burina da na Iyayena karatun ne wannan tsarinmu, amma ba mu san yanda Allah ya tsara mana ba. Kuma a ko yaushe zaɓinsa shine daidai". "Madalla! a ko yaushe maganar hankali ta na fitowa ne daga nagartaccen mutum. Shiyasa a ko yaushe nake girmama kaifin basirarsa". Furucin Malam Saminu yana tafa mini, a suƙure na ce"na gode". Malam Suraj ya buga uban tsarkin da ya sanya hankulanmu komawa gare shi. Dosara wayar ya yi ya gabansa yana ɓallawa Malam Saminu harara"aikin banza ko meye wani sabon abu cikin kalamanta da ya burge ka har kake yabonta haka oho?. Kar ka ce min ba ka taɓa jin wani ya yi irin wannan maganar da ta faɗa ba?". Yana kai aya ya miƙe tare da shigewa cikin banɗakin dake cikin ofishin ya maida ƙofar ya rufe da ƙarfin da ya tursasa mini matse idanuna. Murmushi kawai Malam Saminu ya yi ya ce mu koma ajinmu. Sakina ta riƙo hannuna"ke wallahi yau na gaskaka zancen da Sabira take fada mana, shin ba ki hangi tsantsar kishi a cikin idanunsa ba sa'ilin da Malam Saminu yake yabon ki?". "Ban gani ba komai ba zan taba gani ba, kuma da kuke ikirarin cewar kuna gani akwai don kun canfa abun ne". Haka har muka gama rubuta jarabawar kullum na shiga what's app ɗin sai na tarar da an ƙara yi mini sallama da wannan lambar, duk da kuwa bana amsawa saboda kashedin da yaya Sufyan ya yi mini akan takan tsantsan da mutanen yanan gizo. Mun yi walima mun kuma yi ƙwarya ƙwarya party muka cashe da ƙawayen mu. Raina fari ƙal ji nake tamkar babu wanda ya kai ni murnar wannan gamawan da muka yi, domin ko banza na rabu da ganin tsanar Malam Suraj a gare ni. Ranar da muka y partyn a cikin makaranta, malamai da sauran ɗalibai duk suka taya mu murna. Ban sanya Malam Suraj a idanuna ba domin ko wulgawarsa sai ɗaya ban gani ba. A bakin wasu nake jin cewar bai zo makarantar ba a ranar. Tunda muka yi candy na koma gidan Momma da zama. Yaya Sufyan da Yaya Sa'eed suka tafi ƙarin karatu kasashen ƙetare. Watarana tsautsayi da rabon tafka da ba sa ni ya sanya ni shiga saƙon da ake turo mini da wannan lambar domin na kwana biyu ban duba ba. Murnar kammala makaranta aka yi mini tare da fatan alkhairi da addu'a sosai. Haka kawai na tsinci kaina da amsa addu'ar da kalmar amin a bayyane, sannan ya mayar da martanin cewar na gode da manyan baƙaƙe. Ban tashi daga wajen ba aka maido mini da amsa. Tsoro ya kama ni na tambayi da mace nake magana ko namiji?. Emojis dariya aka turo mini haɗi da cewar na kwantar da hankalina shi mai sona ne kuma sona ya yi tasirin da ba zai taɓa iya cutar da ni ba. Na faɗa wasi-wasi ban ja batun da tsayi na na yi bulokin ɗin layin. Sai dai hakan bai hana ni ganin an ƙara turo mini makamancin saƙon da ake turo mini a baya ba, ko wacce safiya da saƙonsa nake fara cinkaro kana nan kafin na kwanta bacci sai ya turo mini. Tun daga lokacin da ya mayar masa da martani ban ƙara kula sa ba, sai dai nakan buɗe duk wani saƙon da yake turo mini na karanta wani lokacin na yi dariya wani lokacin kuma takaici ya ishe ni. Sai da aka ɗebi tsawon makonnai uku babu ranar da ya taɓa fashin turo mini wannan saƙonnin. Har ya zama na riƙe lokacin da yake turawa da na ga lokacin ya yi komai nake yi zan bari na shiga what'sapp ɗina ina jira. Da ya turo zan tsinci kaina ina sakin murmushin da ban san ina yi ba ina gama karantawa zan ajiye wayar. A haka yi kwana uku ban ga saƙonsa ko ɗaya ba, tun bana mayar da hankali har na fara shiga damuwar rashin ji daga gare sa. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki ta 400 wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984 LAMBA NA GOMA SHA HUDA ________Murmushi naga yayi mun ya fara ta kowa in da gado na yake a hankali idon shi a kai na ƙura mun ido yayi bakin shi yana son furta wasu a bubuwan amma irin yadda na haɗe rai bai bashi daman magana ba sai da ya jima a kai na kafun naji yace"ya jikin naki dafatan kin fara samun lafiya in baki dage ba da kulawa da kanki da bawa zuciyar ki hutu ta samu sauƙi ba zan tura ki barno a cen zaki dinga kallon likita yanzu me yasaki kuka ?. Kallon shi nakeyi bana son wata kalma daga gareshi ko da ta farin ciki ne don zuciya ta tafara rashin yadda da wasu mazan na gagara sai ta kaina sannan nayi hawayen ya daina gangarowa daga ƙunci na amma hawayen ba,daga ido na yake zuba ba daga zuciya ta ce ban ,isa in hana shi zuba ba ko yaya ne . natafi duniyar tinani a karo na biyu kenan da naji zuciya ta tafara ƙarye wa daga samun JB in kuwa halaccin da nayi Wa JB bai sa yayi mun uzuri ba lalle so bai samu matsugu ni a gareni ba . Jin doctor nayi ya fara magana "me yasa kike son jefa kanki cikin tashin hankali meyasa kike son ki kasa jurewa a kan ƙaddaran ki, soyayya ,itace ke sawa zuciya matsaloli masu tarin yawa ,a da zuciyar ki bata samu raunin da yanzu yake samu ba ,na tambaye ki ,kin fara soyayya ne a lokacin da ,a ka kawo ki na duba ki kin ce a'a to yanzu nagane wannan wanda yake saki damu wa,amma bashi da yan uwa ko bashi da ƙanwa ko dai a zuriyar su babu mai irin jinyar ki . "Wa Yagaya maka a irin wannan matsalar nake yin kuka kawai dai bansan yaushe ,a ka kawo ni nan ba shine kawai na shiga damuwa a kai " ƙarya bata da ce da fuskar ki ba wannan ya nuna wanda ya fara sanya ki damuwa a lamu ya nuna maƙaryaci ne zai koya miki a bun da ba ɗabi,ar ki ba ce ". So yake ya ƙureni ga shi ya zauna yaƙi tafiya sai ɗan na wayar shi yake yi cen wayar tafara neman ,a gaji sanya wayar yayi a kunnen shi jinayi yace ganinan zuwa bani minti goma tashi yayi yace zai je asibiti yana zuwa zaije General hospital an kawo wata mara lafiya an nemi jijiyar ta dan a sanya mata drip ba,a samu ba in taya shi da addu,a Allah yasa yayi nasara dan ance tana shan wahala . da to na bishi Allah ya bata lafiya Amin ya ce mun ya fice kafun ya fita ya cire mun drip ɗin don ya ƙare . Hajiya ce ta shigo da su Inna mahaifiyar Ibrahim "sannu uwa ta Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne Ibrahim yace a gaishe ki ɗazu ya kira waya kina bacci bamu tashe kiba duk ya shiga da muwa a jhkan halin da kike "ayya inna ina ji da shi nima ko aure yayi matar shi bata kaini son shi ba "ke ce matar Ibrahim in har ina raye babu wanda zakiaura sama da shi yana sonki ga shi ɗan uwan ki ne, zai kula da ke to meye abun

Chapter 6 of 13