haƙura zan wuni haka tunda yau babu in da zanje sannan da yamma ki shirya zaki rakani unguwa kinji da to na bishi abincin shi na kawo mishi kaɗan yaci yace ya ƙoshi
Da yamma misalin ƙarfe hudu muka fita unguwar su JB naga ya nufa har kusan bakin shagon shi ,da yake motar ba lalle ne ka gane waye a cikin taba fita yayi suka ɗan matsa ya fara yi mishi magana a kan yana so a sa,pop a ɗakin baƙi yau she zasuyi ban san me suka yi ba kawai kallon JB nake tayi hawaye kuma daga zuciya na ,take zubo wa bada ga ido na ba ban san me hakan ya ke nufi ba ya Ibrahim so yake yace ya fahimci a kwai soyayya ,a tsakanin mu ,shine zai yi mishi haka ko dai cin mutunci zai yi mishi ya na so ya ce yaron bai kai ya Soni ba ko yaya ina kuka ina tinani har ya Ibrahim ya ƙariso bai kula da yanayin da nake ciki ba jan motar yayi .
Ina zamuje ko dai in kaiki gidan abokina ku gaisa matar sa tana sonki kullum labarin ki ,take yi "ba na so mu wuce gida shine kaje ka jima gun waye ma ,kazo ne? "baki gane shi bane ko yaya yaron da ya kiraki ne fa a ,waya shine akwai aikin da zai yi mun "ya Ibrahim kenan yau she ka koyi cin zarafin mutane ,yau she zaka ɗauki talaka a kan matsayin ku ɗaya kayi hakan ne dan Kaci mishi mutunci ko dai ka ɓata mishi rai na gaya maka babu komai a tsakanin mu, mutunci ne sannan girman ka zai zube nida na gaya maka dole sai shine zai yi maka aikin ka nemi wasu,mana taya zaka zo ka ɗauke ni ka ,kaini gunshi wallahi muddin ka nuna mishi ka sanni bazai ƙarbi kuɗin aikin ba sannan zai yi maka biyayya don nima daraja wa ne da karamci tsakanin mu.
"Ba komai Nusaiba baki san meke zuciya na ba naso in kyautata mishi ne ta,wani hanyar amma tunda kin ce hakan zan kiyaye bazan bari ya gane ke mata na bace kin yadda bana son ganin ki cikin ɓacin rai banajin daɗi gaskiya ".
Naƙi zuwa gidan abokin na shi siyayya yayi da yawa muka wuce gida muna zuwa a na kiran sallah masallaci ya wuce nima alwala nayi na shige ɗaki don gabatar da sallah.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: *
[11/5, 21:39] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam
Zaki sanya kuɗin ki ɗari huɗu 400 ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984
Laifin daɗi ƙarewa a nan muka kawo ƙarshen labarin JB a cikin littafi na ɗaya duk mesón ci gaba ya biya kuɗi kafun ya karanta sannan ya duba number waya kafun ya mana magana gudun kar a samu matsala littafi na biyu yana nan tafe.
Wani darasi kuka ɗauka ,a labarin JB ?
Wani a bu kuka koya a labarin JB
Wa kuka fi so tsakanin JB da Nusaiba?
Wa yafi burge ku tsakanin JB Ya Ibrahim doctor?.
LAMBA NA ASHIRIN DA TARA
__________Karma ka fara wannan gangancin JB aure tsakanin mu da kai ka,ajiye shi gefe yadda baka bayyana musu a farko nikake so ba rashin yin maganar ka shine ya jawo maka komai koda na rasa mijin aure bana jin zan zauna da mayaudari sannan maƙaryaci kasani da na soka yanzu gara na haƙura da auran. tsanar ka tafi yawa a gareni bana son kallon fuskar ka ka barshi a zuciyar ka bayyana musu koni waye ce hakan zai rage maka kima da daraja a tsakanin ka da iyayen ka. sanin kanka ne natsani ƙarya da yaudara sannan kai mungu ne JB .
"Karkiyi mun haka kibarni inji da,azabar rabuwa da ke kawai ina son ki sani nafi kowa sonki " ka gyara kalaman ka don babu komai a idon ka sai tsanata da yaudara da haƙinci ". tafiya na farayi ko wai _wayo wa banyi ba da muryar shi wanda ba fitowa take ba yata kirana sosai ko wai wayo wa banyi ba gida na wuce Hajiya ta tambaye ni ya maijikin nace da sauƙi "yauwa mahaifiyar yaron tananan ko dai ta koma in kuwa bata tafiba zanje in dubo ta kawai don kartaga rashin zumunci ,agaremu shiru kawai nayi cen taƙara tambaya na ko munyi waya da Ibrahim nace mata bamuyi ba ce mun tayi gobe yana hanya zaizo wani abu ne nace Allah ya kaimu na shige ɗakina .
Washe gari
da kaina na shiga kitchen na haɗa wasu JB abinci na bayar a direban mu ya kai musu na ɗaura wanda ya Ibrahim zaici in ya iso tun sha ɗaya na gama nayi wanka na shiga ɗaki na dau jarida a hannuna ina ta aikin karatu yau ta kama asabar Abba na yana gida tashi nayi dana ga azahar yayi nayi sallah na kwanta sai ƙarfe hudu na tashi daga bacci yunwa naji nafito ina tafiya nací karo da mutum a gabana ɗaga idon da zanyi naga ya Ibrahim ya ƙuramun ido sosai "yaushe ka zo ?tun ƙarfe sha ɗaya na shigo gidan "shine baka nemeni ba meyasa haka? "bana son in raɓi in da kike taya zan nemeki kice na takura miki a duk yadda kika zo a haka zan biki yadda kike so Nusaiba ".
Kaci abinci kuwa?
Nací tun da nazo meye na tambaya na kin damu da rayuwa nane don Allah kibarni karki ɓatamun rai don Allah "nasan baka Ciba kafaɗa ne kawai kaida cin abinci bai da meka ba taya zakace Kaci abinci don Allah ka daina faɗa tun safe na dafa maka abun da kafi so "waya gayyace ki bana so ki cinye na ƙoshi ".
Jan rigar shi nayi na kaishi ɗaki na wuce kitchen na ɗauko abincin na kawo,naje na ɗauko ruwa nazuba mana abincin har nafara ci banga yana da niya ba danna wayar shi kawai bata rai nayi nací gaba da cin abinci na aiko Fatima Abba yayi a kan ya na son ganin mu nace mishi zanzo kafun nabar cin abinci naga ya jawo ya fara ci loma uku yayi sai gashi ya tashi ɓangaren Abba ya nufa bayan ya shiga na bishi a baya da sallama dukkan mu,muka shiga waje na samu muka gaisa da Abba naji yace ya mai jikin nace da sauƙi sosai .
"Ibrahim ina son zan yanke lokacin auren ku da Nusaiba nan da wata ɗaya nasan ka gama shiri in baka gama ba to ka bari in taje gidan ka zaka ƙarisa komai a ,hankali".
Da Sauri na ɗago
Aure Aure kuma Abba!
e auren bake sone ko dai ke baki shirya ba ku tashi kubani waje muddin kuka furta wasu magana zan bata muku rai in bakwa son junan ku ,in kunje ku kashe kanku .
Kallon ya Ibrahim nayi shima kallona ya keyi ya zuba mun ido duk tausayi na ya kama shi ya rasa ya zai yi muddin zan samu farin ciki ya haƙura da auren har abadan duk kanmu hawaye mukeyi mun gagara tashi daga wajen kowa yasan ma,anar kukan shi na ya Ibrahim tausayi nane ya sashi kuka nikuwa bañsan ya zan yi ba bana son tarayya ta da shi in badan ba zan so in auri JB ko don shine mutum na farko da yasan daraja ta zanso mu zauna tare da shi ina son nunawa JB shi ba komai bane taya zan auri ya Ibrahim bayan nasan ni fanko ce nasan ɗan uwana ne zai rufa mun asiri amma in har kuma yana da zafin kishi fa .
Kiyi haƙuri ba na son Abba yayi fushi da mu ki taimake mu ,mugama da iyayen mu lafiya, ki shirya muje asibiti don ance kina da mara lafiya "ba zanje ba kuje kayan ku nafasa zuwan "Hajiya ne fa tace ki shirya zan kaiku don Allah kar ki bari wasu mutane su gane bama son junan mu ki taimake ni don Allah musamman Hajiya .
Bayan nayi sallar mangari ba muka tafi asibiti har da Hajiya da Aliyu da Hibba da Fatima da mahaifiyar JB muka fara haduwa nikuma na ƙarisa cikin ɗakin nabar ya Ibrahim yana waya da ganina ya tashi "daman zakizo na ɗauka kinyi fushi shiyasa don Allah ki shigo rayuwa ta mugina rayuwa mai ɗaɗi ina son kisawa ranki ruwan sanyi ni nakine wallahi ina ƙaunar ki zan baki duk wata kulawa zan kula da lafiyar ki zan tarairayi duk wani matsalan ki".
Ƙarya kake yi baka cencenci haka ba daga gareni bana son ka har Hajiya tazo ta duba shi B banga ya Ibrahim ba kardai har yanzu waya yake yi Allah yasa baiga in da na shigo ba kafun JB ya gama kalaman shi wanda a zuciya daɗi kalaman suke mun a zahiri kuwa baƙin ciki nake yi sosai ina son in nuna mishi kuskuren shine ta yadda ko da munrabu zai mutunta, mata yan uwana ba zai walaƙanta suba musamman ya samu wanda yake so duk ƙarya ce irin ta maza mayaudara, kalman su guba ne a garemu yakan dagula mana duk wata kafa ta ɓangaren numfashin mu ,maza yawancin su da kalma ɗaya suke yaudaran mu.
"Kin yi shiru Hayat kiyimun magana so kike in mutu ne ki duba yadda numfashi take yi mun wahala hawaye ne suka ta gangarowa na gagara tsayar da su daga ido na gara na barshi ko zanji sauƙi a bakin gadon na kifa kaina shikuma yana riƙe da gyale na muna ta kuka sosai "yau guduna kike yi nayi laifi kin gagara haƙura kiyi haƙuri don girman Allah so kike kiyi rayuwa da wani , ki yafe mun kinsan gatan da Allah yayi mun bai ɗauki raina ba a lokacin da muka yi hatsari don in gyara kuskuren da na aikata nacutar da ku keda A'isha musamman ke nabar miki tabon da har ki koma ga Allah bazaki manta dani ba ki tausaya mun karki auri wani "ka gyara kalaman ka wanda zan aura yafi ƙarfin wani a gareni don ɗan uwa na ne, sannan yafika sona da tattalin rayuwa ta na rasa Muhammad a duniya wallahi ko kai ka mutu bazan shiga damuwa ba mai amfani a gareni ma narasa balle kai ko wani abu bazan jiba ina son in fige gyale na ,daga hannun shi na gagara duk wanda ya ganmu zai san mu ,masoya ne in da,ace ɗakin da aka bashi ba shi kaɗai bane mai haɗe da mutane ,ne da mun zama yan kallo zamu bawa duk wanda ya kalle mu tausayi babu wanda zai rarrashe mu ko dai wani ya fahimci halin da muke ciki a wani ɓangaren kuma ina tausayin ya Ibrahim sosai " yanzu Nusaiba kenan kanki zaki bawa wani ina alkawarin da muka yi na cewa zamu kasance da juna ko daɗi ko akasin haka riƙe hannu,na yayi kamar za,a gudu dani ɗago kaina nayi ga hannun shi riƙe da hannuna banƙaɗo ƙofar da a kayi juyawa mukayi don ganin waye ne da ,a lama wanda ya bankaɗo ƙofar ya jima yana tsaye ..
Tammat
Gareku masu karatu shin waye ya shigo ɗakin ?
Shin auren Ibrahim da Nusaiba zai,iyu kuwa ?
Ya Hajiya da Abba zasuji in sunji labarin soyayyar JB da Nusaiba gashi yaro mara aji
Tsakanin doctor da Ibrahim da JB waye zai lashe wannan gasar
Duk kan amsoshin ku yana cikin littafi na biyu ki biya kudin ki kisha karatu.
WATA MAHANGAR*
©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam
LAMBA NA TALATIN
Bisa tursasawar yaya Sufyan muka je gidan su Sakina da son raina ba babu ina da za ni. Domin na yi wa kaina alƙawarin ba ta hutu kafin mu daidaita kamar yanda ita ma take share ni. Mahaifiyarta muka iske a falo muka gaishe ta, ta amsa mana fuskarta tamkar gonar auduga tsabar farin ciki ta rasa inda za ta sanya mu, sai nan da nan take yi damu.
"Masha Allah! Allah ya ƙara haɗa kanku ya albarkaci aurenku".
"Amin".
Muka haɗa baki wajen amsawa dashi kafin yaya Sufyan ya furta"ina Sakina fa tun shigowar mu ban gan ta ba".
"Tana ciki yau ta tashi ba ta jin daɗin jikin ta ne, bari a ƙira muku ita". Ta ƙare zancen tana miƙewa dai-dai sanda na haɗo kaina muka haɗa ido da shi. Ta cikin idonsa na fahimci saƙon da yake son aika mini bai wuce irin tarban karamcin da mahaifiyar Sakina ta yi mana ba. Ban bari ya ja da nisa ba na kawar da ido lokacin da sallamar Sakina take ratsa ƙofofin kunnuwana.
Kujerar dake kallona wanda na zauna ta yi wa kanta mazauni tare da gaishe damu cikin jumla guda ɗaya. A sanyaye na amsa tare da yiwa bakina linzami.
"Na kawo ta mun ba ki haƙuri akan abinda ya faru a tsakaninku. Da ke har ita ranku ya ɓaci da ku ka mayarwa juna martani a zafafe, ba domin ɗaya daga cikin ya manta matsayin ɗayan a gare shi sai don rufewan da idanunku suka yi". Daga haka ya dakata tare da sausauta amon muryarsa kana ya ɗaura da"dukkanku ku yi haƙuri a zamantakewa dole wataran a saɓawa juna domin ko harshe da haƙori ma suna saɓawa. Komai ya wuce ku dawo tamkar yanda kuke a da don Allah ".
Take na ji gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalai tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Kalamansa sun bi dukkan sassan jikina sun ɗaure shi tamau. Na kasa cewa komai sai Sakina ce ta furta"la ni kam wallahi ba komai tun lokacin da abin ya faru ma na manta shi. Ban riƙe Surayya a cikin raina ba kawai dai na bata lokaci ne ta huce daga dokin zuciyar da ta hau".
"To Gimbiya kin ji dai da kunnenki ko? Sai ke ma ki zubar da makaman yaƙinki". Ya furta yana kafe ni da idanu, sai da ya furzar da zazzafan iska daga baki kafin na sama sararin faɗin"nima komai ya wuce a wajena ki yi haƙuri da kalaman da na furta miki a cikin fushi". Da walwataccen murmushi akan fuskarta ta ce"ke ma ina mai ba ki haƙuri".
Murmushi nima na sakar mata, muka haɗa ido da yaya Sufyan shima fuskarsa ɗauke da murmushin da ya ƙara fitowa da kyawun sukakkiyar fuskar da sumarsa suka kwanta luf a saman haɓarsa"to Alhamdulillah! Allah ya ƙara haɗa kanku. Zan bar ki a nan sai zuwa anjima na dawo da ɗauke ki". Kaina kawai na gyaɗa masa Sakina ta ƙira Hajiyarta suka yi sallama. Ina ankare da ita ta ke yi mini alama akan na tashi na raka shi na yi kunne uwar shegu da ita.
Ɗakinta muka koma na yaye mayafin kaina na ajiye shi a gefe guda. Ta dire mini kofin ruwa a gabana na bi ta da kallo yayin da take koma gaban madubi tana gyara ɗaurin kallabinta.
Sakakken ajiyar zuciya na sauƙe haɗi da faɗin"me yasa kika zaɓi ki rufa mini asiri a wajen yaya Sufyan?". Sai da ta gama tsaf ta juyo"idan ba ku canza hali ba ko ban sanar dashi ba wataran da idanunsa zai ga ni". Na cije leɓena domin na san magana ta karta mini. Sai da na jim kafin na ce"hmm Sakina kenan na lura ba za ki taɓa ganewa ba. Na gode da halaccin da kika nuna min".
A hankali ta tako ta iso gabana ta tsaya"zan gane Surayya ke ce kawai idanunkin ya makance akan wani banzan da sam bai damu dake ba. Idan ya damu dake me yasa bai tunkari iyayenki an yi maganar aurenku ba? Me yasa zai laɓe ta bayan fege yana farmaƙan ki ba tare da ya bayyana kansa ga kowa ba?. Uhmm a wancan lokacin na zo wucewa gidanku na sanar da Hajiyarku halin da ake ciki. Amma tunin da na yi ki gargaɗe ni akan fita daga abinda ya shafe ki sai nima na shafawa kaina lafiya".
Ta ka aya tana ɗage kafaɗarta alamar babu abinda ya sha mata kai. Musgutawa na yi ina ɗaura idanuna akan ta"shikenan na janye duk kalaman da na yi a baya yanzu ki ba ni shawara".
Ba ta ce da ni komai ba sai da ta zauna kusa da ni tana fuskantana sosai"babu shawaran da zan ba ki face wanda na ba ki a baya kika sanya ƙafa kika shure su. Ki maida hankalinki wajen neman aljannarki ta hanyar farantawa mijinki. Ki cire ƙaddararren soyayyar Suraj daga cikin ranki ko kema za ki sama sallamar rai da ruhi". Sai da na haɗi wani miyau mai ɗaci kafin na ce da ita"shikenan in sha Allah zan yi ƙoƙarin yin hakan".
"Da kin ga alfanun hakan a gare ki kuwa ba ɗan kaɗan ba".
Mun tattauna sosai da ita ta inda ta dunga bani shawarwarin yanda zan sanya Yaya Sufyan a cikin raina. Har wasu addu'o'i ta ba ni ta ce na dunga yi a cewar ta wai ba ta yarda Suraj haka banza ya bar ni ba.
Sai bayan sallan Asr yaya Sufyan ya zo ya ɗauke ni muka tafi cike da sanyawar albarkan majaifiyar Sakina.
A cikin kwanakin nan na yi ƙoƙarin ganin na yi duk wani mai yiyuwa wajen ganin na samarwa yaya Sufyan matsuguni a cikin zuciyata amma lamarin ya garare ni wankin hula yana neman kai ni dare.
Dukkanin wani kyautatawa ina yi masa haka nan duk wani saƙon da Suraj zai turo mini sai dai na karanta na shafe amma ba na mayar masa da amsa. Na rungume mijina da kuma aurena hannu bibiyu ina bautar Ubangiji, kullum soyayyar da yaya Sufyan yake nuna mini hauhawa take yi kwatankwacin yanda farashin man fetur ke hawa a ƙasata. Bai da burin da ya wuce kyautata mini da yin silar wanzuwar annuri akan fuskata.
Mun shirya da Sakina mun dawo tamkar yanda kowa ya san mu. A na cikin haka Sultan ya nuna yana sonta, ni kam na yi murna sosai tare da yin mata gargaɗin har ta ja wa ɗan uwana aji akwai ta bada kai bori ya hau.
Suraj ya zame mini ƙadangaren bakin tulu na bar shi ya lalata ruwa na kashe shi na fasa tulu. Har yanzun bai daina bibiyata da nuna mini soyayyarsa a gare ni. Bana mance wani yammaci da ya aiko mini da saƙon murya ta wasof.
Yana yi mini roƙo da magiya akan ko sau ɗaya ne na dawo masa da amsar tarin maganganun da ya yi mini. Babu kalmar da ta sanya mini a raina kamar ƙayar kifi a maƙwoƙwaro kamar faɗin da ya yi ya yarda ko da auren wani a kaina shi dai kawai na amshi soyayyarsa.
Na ci kuka tamkar raina zai fita a lokacin na goge dukkan lambarsa daga wayata. Duk da har yanzu soyayyarsa tana nan a cikin zuciyata amma ba zan iya aikata abinda yake so daga gare ni ba a wannan lokacin. Ba zan iya cin amanar aurena, mijina da kuma iyayena ba.
Na gwammace na kashe auren na fito kana mu yi soyayyar amma ba dai ina cikin gidan wani ba. Duk wata hanyar da zai iya turo mini da saƙon na bi na toshe ta ko ƙirana aka yi da baƙuwar lamba bana ɗagawa.
Wani ranar da ba zan taɓa mancewa da ita ba a cikin tarihin rayuwata saboda muninta da kuma zama sanadin datsewar igiyoyin farin cikin rayuwata. Na dawo daga makaranta na shiga kitchen domin ɗaura girki a lokacin yaya Sufyan ya fita masallaci, wayata dake kan firiji ta yi ruri alamar shigowar saƙo ban bi ta kan ta ba sai da na gama yanda albasan da nake yi sannan na ɗauko ta. Baƙuwar lambar ce na shiga saƙon da sauri.
"Ki fito ina ƙofar gidanki idan kuma kin yi biris da zancena, babu shakka zan shigo har cikin gidan na sanar da mijinki abinda ke tsakanin mu".
Mutuwar tsaye na yi bayan na gama karanta saƙon tare da dulmiyawa kogin tunanin wanene wannan?. Kafin na kai ga cimma amsar aka ƙara turo wani saƙon sunan da na ga an rubuta da manyan harrufa suka sanya hancin cikina haɗawa, na maimaita sunan a bayyane.
"Su-su-su-suraj".
Kamar mahaukaciya sabon kamu haka na fito daga kitchen na ɗauko mayafina na banko ƙofar falon na fito waje. Rarraba ido na soma yi akan shimfiɗanɗan titin dake ƙofar gidan, na yi turus saboda ganin yaya Sufyan da Suraj suna tsaye suna gaisa. Wani jiri ya soma deɓe na, na ƙara ware girman idona akan su daidai sanda duk suka juyo suna kallona. Suraj yana jifa na da wani shu'umin kallo.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 13