Share this page
7 / 8
"Ya akeyin godiyar?" "Ai ni na iya Dama,idan aka Baka Abu she kace"tanchu"idan kanasho a Baka kace"piyis" "Good girl Sai kuma me" "She kuma aka Mana Wa`a akashe mu dinga gaishuwa,cinshan ya aceyi" "A`a" "Gummoyin" Dariya nayi nace"Amma fa babyna akwai qwaqwalwa" Dariya tayi tace"idan jami fi`ayi cinshan me muce shewa?Anty an go an wiwi" Dariya nayi nace"lallai kuWa nan da kwanaki kad`an kin dena Hausa,kinci abincinki?" "Yesh" Kafin na qara cewa komai mummy tazo naja hannun khairat muka Shiga mota "Mummy khairat fa ta iya turanci sosai,nidai nafiso a kaina makarantar da ake Islamic da Boko a had`e" "Naje yau AI shiyasa ma na jima,za`a d`auketa da zaran na Gama processing komai" Muna ISA gida mummy tayi parking ta fara laluben keys Amma Bata Gansu ba "Mummy inaga fa kin Barsu a ciki" "Aikuwa inaga Suna ciki saboda abbanku ne ya rufe gidan,bari na kirashi ko baiyi nisa ba" Tana kira ya tafi voicemail "Inaga ya tafi,yanzu yanda za`ayi muje can guest house d`inshi nasan inda yake ajiye spare keys d`insa,idan akwai na nan Sai mu d`auko idan babu saimu zauna a can Gobe idan Allah ya kaimu Sai a zo a yanka Mana wani Saida muka biya muka sayi kayan da zamu saka sannan muka wuce munyi sa`a kuwa a Bayan gidan inda yake `boye spare key munsamu na gidan Amma babu na gidanmu Shiga mukayi da abincin da muka siyo mukaci mukayi wanka Mummy nata gwada number Abba taqi Shiga `dakunan duk a gyare suke d`akina Banu fitila haka yasa khairat ta gudu wajen Mummy ta barni ni kad`ai, Mummy taso duk mu Kwana wuri d`Aya Amma ni nafison jina ni kad`ai Bayan na Gama jimamin wayata da na bari a gida na kwanta bacci cikin baccin Naji an riqoni ta baya Anyi kissing wuyana Ina bud`e ido Naji Ashe ba a bacci bane a farkene a tsoraCE na fara qoqarin qwacewa "Shhhhhhh nine fa nasan zakizo ai shine da zakimin hawo da hankali kice bazaki samu damar zuwaba?" Ture hannunsa dake bakina nayi na fara qoqarin cire hannun dake riqe da cikina Ina qoqarin kautar da tunanina,kaman muryan Abba nakeji "Ba inda zakije sweetheart, na gane wayonki"Kawai na jishi a kaina,ihu na fara Ina Kiran Mummy,shigowarta yayi daidai da saukan da yayi daga kaina a rud`e Cikin firgici na kalli Abba na kalli mummy a take na Saki kukana mai sauti "Innalillahi Wa inna ilaihi raji`un"abinda mummy ta fad`a Kenan Tana riqe kanta,Abba da kunya ta hanashi motsawa ya sunkuyar da kansa qasa yaqi d`agowa Qudundune bedsheet d`in nayi a jikina Ina kuka na kasa d`agowa ma na kalleshi "Abdallah wannan Wace irin masifa ce?MUNAYA fa. `yarka ce, lalacewar har takai ka nemi `yarka Bayan `Yan aikin da ka kora da wadda kayima ciki?abdallah....ya salam,fita daga nan!" Baice komai ba ya fita ta dawo gefena ta zauna Tana rarrashina ba tareda tace komai ba,baccin da ban koma ba Kenan na kasa gasgata abinda ya faru,abbana?abbana da nakeji dashi yakeji dani?yanzu Abba na ne yayimin haka Da safe Mummy ta d`aukemi muka koma gida jikina babu qwari Sam banason ganin Abba a yanzu.daga ni har ita jikinmu a sanyaye yake dad`Ina d`Aya Yaya Yana wudil yaje wani project Banje school ba haka na zauna a d`akina Ina kuka,duk lallashin khairat yau bai hanani kuka ba haka ta zauna Tana tayani ganin naqi denawa Ban qara ganin Abba ba a wannan satin nasan dai Yana shigwa Yana fita amma da Naji sallamarsa zan gudu. A adaidaota sahu muka dawo gida kasancewar lokaci yaja Mummy ko Abba basizo d`aukarmu ba,suk yanda qawayena sukaso jin meke damuna naqi fad`a musu na sanya kowa a damuwa cikin week d`in Daga qofa Naji hayaniyar mummy na tashiabdallah zamanmu yazo qarshe halayyarka ta fara ta`ba yata na Gama Daurewa,ka fad`amin menene Bana Maka a Zaman aurenmu zakayi watanni Baka waiwayeni ba Amma kullum kana wajen matan banza,kace zaka canza Amma Babh alamun canji tareda kai,karka fita ka dawo ka bani takardata Ina qoqarin shigowa muka gwari juna da gudu na tafi d`akina na fara sana`ar kuka,tun ranar da Abin ya faru Abba da Mummy basa Zaman lafiya,kullum saita nemi Saki shi kima haka zai fice ya qyaleta basu ta`ba Sanin Ina jinsu ba Sai YAU. Damuwata tayi yawa hakan yasa mummy ta fita damu wajen shaqatawa,Muna Zaune khairat nata zagaye Tana wasa da wasu yara,nayi mamakin yanda ta Saki jiki dasu Mummy tace "Munaya Ki fad`amin abinda ke da!munki ko da na Sani Ki qara sanarmin ko kya rage damuwarnan,zata iya janyo miki matsala Hawaye na share nace"Mummy zamanku da Abba bayamin dad`i Sam,sannan Bana San ganin abba idan na kalleshi wannan kwarjinin na uba Sam Bana ganinsa,wani mutum nake gani daban" "Kiyi haquri MUNAYA insha Allah komai ya kusa zama da sauqi,jibi birthday d`inki banaso Ki Shiga 16 kina damuwa okay?Ki ajiye komai a gefe insha Allahu ni zan Mana maganin matsalarmu "Mummy Dama Abba neman mata yakeyi" "Karna qara jin kin ambaci haka kan Abbanki,babu ruwanki da rayuwarsa kinji ko?" Daidai lokacin khairat ta dawo Tana mitsistika ido alamun bacci,d`aukanta nayi a hannuna nace "Mummy muje gida kafin tayi bacci" Sam banason komawa gida YAU Kawai banajin dad`in Zaman gidan,Muna zuwa khairat tayi bacci na d`auketa a kafad`a nayi d`akin mummy da ita,Ina bud`Ewa nayi tozali da abinda har mutuwata bazai ta`ba ggewa ba Abba ne wata mace kan gadon Mummy a nan qafafuuwana sukamin nauyi na kasa motsi na runtse idona na sauka da gudu,kafin na sauka nayi missing step na fad`I qasa dani da khairat,qara ta Saki na firgici,kuka sosai nakeyi a tsorace mummy ta hau don taga menene ya tsoratani haka _a kad`an daga rayuwar munaya Kenan na tsakuro muku,karku manta Ku kuke qarfafamin gwiwa,fatana zakuci gaba da karanta munaya Kuna fad`amin ra`ayoyinku_ *MUNAYA* Maryam? Wattpad@mamsuhaimerh 13 Jiki a sanyaye ta sauko Ina Zaune bakin benen riqe da khairat da banda kuka da qanqameni ba abinda takeyi,bayana da kaina sun bugu sosai Amma Sam banajin zafin abinda na gani ne kemin yawo a kaina Hannu mummy tasa ta kar`bi khairat da babu abinda ya sameta domin na Qanqameta jikina kuma kasancewar a Zaune na fad`i Kawai tsorata tayi taketa faman ihu Ajiyeta tayi kan kujera ta kamo hannuna da qyar na miqe Nima na zauna kan kujerar.had`a kaina nayi da jikin kujerar Ina hawaye tareda runtse idona,ya Allah ka ciremin wannan Abin daga rai na,wannan shine Abu mafi munin gani ko da ba mahaifina bane Mummy dake gefe ta samu ta lallashi khairat Wanda ta dena qara Amma kuka take Tana qoqarin zuwa wurina Mummy ta riqeta Muna wannan yanayi karuwar ta sauko,ba qaramin tashin hankali na Shiga ba ganin computer studies teacher d`inmu ce, d`auke kai nayi tunanina zata fice Amma Sai ta tsaya ta riqe qugu Tana kallon Mummy "Kar fa kiga laifina,laifinki ne da bazaki iya riqe mijinki kisan Meye buqatunsa ba,Sai yanzu kike nadamar sakinsa da kikai Yana walagigi?hm indai haka zakiyi to kad`an ma kika gani domin wannan gidan idan na shigoshi Wallahi Sai ya zamar Miki masifa,oh nayi mantuwa ur husband is sooooo sweet ai ban ta`ba Sanin haka yake sambatu ba kodayake Kema bazaki Sani ba Dan bakya masa abubuwan da zai....." Kafin ta qarasa na Dakatar da ita"ya isheki haka,Ki fita Ki bar mana gida karuwar banza karuwar wofi,har kina taqama kin aikata Haram?Ki iya Bakinki Dan bazan zauna kina zagin mahaifiyata Ina kallo ba" "Ohhhh my hafsat,Ashe wannan jahilar Matar uwarki ce, karkiga laifina Ina koya mata riqe miji ne kuma Ki dakata haka ko kuwa kiji abinda yafi Wanda kikaji muni" Bansan lokacin da na d`aga hannu na tsinka mata mari ba,daga ita har Mummy har khairat saida suka tsaya cak,inda khairat tuni ta Saki kuka mummy kuma ta taso Tana qoqarin janyeni daga gareta Kafin Mummy ta samu damar janyeni tuni ta tsinkamin mari Wanda yayi daidai da saukowar Abba daga bene "Meye haka?me kikeyi anan?"ya tambaya Yana kallon karuwar da ko sunanta bazan iya kiraba "Baka ganewa idonka ba?yarka CE takemin rashin kunya harda marina na tsaya ne na maida martani" "Ke MUNAYA sa`aerki ce da zaki mareta?" Tsayawa nayi Ina lkallonsa cikin mamaki,babu abinda nake gani daga gareshi na uba,kallon da nake masa abubuwan da suka faru ne suke dawomin tuni na ajiye matsayinsa na uba a gefe nace "Abinda ma zaka ce Kenan?Abba bakaji kunyar abinda kayi ba zaka tambayi dalilin marinta da nayi?" "Munaya karki qara magana"mummy ta fada cikin rawar murya,banbi ta kanta ba naci gaba "Ka nunawa karuwar ka cewa tafi matarka muhimmancin da har zata zo Tana fad`a mata magana,instead of ka kori karuwarka ta fita zaka tambayi dalilina na marinta?Abba Nifa erka CE Mummy matarka CE,qazantacciyar halayyarka da na gani bai isheni ba Sai ka qaramin da wani Abin?" "Kayiwa erka kashedin ta dena kirana da karuwa" "Karki qara kiranta....." "Whaaattt!!au karuwarka tafi iyalinka Kenan na kirata da karuwan akwai abinda zaka iyamin ne,na fad`a karuwa KARUWA!!" Saukar MarI CE ta hanani qarasa ambatar karuwar na kalli Abba cikin tsananin takaici nace "Abba akan wannan ka mareni?nayi Dana Sanin zama erka gara na tashi babu uba da na tashi a matsayin erka daga YAU nadena kallonka a matsayin uba sai a matsayin ma....." "Ya ISA haka munaya!!!"mummy ta fad`a idonta cike da hawaye"ya isa, na Miki umarnin karki qara bud`e Bakinki anan" Matsawa Anty haulat tayi jikin Abba tace"Uhm Sai yanzu zaki zama Uwa Kenan?Ashe erki batada tarbiyya"kallona tayi wani irin kallo kafin ta juya ta fara kissing Abba Wani qara khairat ta Saki ta buya jikin Mummy haka na runtse idona cike da takaici,wannan baqar rayuwa da na fad`a Allah ne kadai zai fiddani daga cikinta Bansan lokacin fitarsu ba ko takun takalminsu banji ba kasancewar na toshe kunnuwana inata sharbar kuka,mummy Naji ta rungumeni na koma jikinta naci gaba da sana`ar kuka,Tabbas Allah yayimin arahar hawaye qaramin Abu ma kuka nake masa balle babba Munfi minti talatin a haka kowa yayi shiru hatta khairat wadda ta dawo jikina ta manne lokaci lokaci Tana d`agowa ta gogemin hawaye,duk lokacinnan kuka nakeyi ba abinda nake gani Sai abubuwa uku idan na tuna abbana Abbana tareda wata mace Abbana ya nemi aikata Haram dani Abbana manemin mata ne Jiki babu qwari na tashi na koma d`akina na wanke fuskata somin na gaji da kukan,haka na kwanta Ina jiran bacci yayi awon gaba dani da qyar na samu nayi bacci Mugayen mafarke mafarke na fara kan abbana dole na farka na kasa komawa saboda tsoro da firgici saidai kuskurena maimakon na tashi na miqawa Allah lamurana Sai na nad`e cike da tsoro Sati guda Kenan da faruwar wad`Annan alamura na canza gaba d`aya, a school,a gida a Karan kaina ma na canza,mummy kuwa kasamcewarta Uwa ta koma kaman babu abinda ya faru,yayana tunda ya dawo yaga yanda gida yake ya fice ya koma bansan inda yayi ba,bansan me yakeyi ba duk wani bala`i ni kad`ai nake kwasa "Wani gidan kake kira gidanka?kuma Wa kake kira iyalinka?ai abdallah ka rasa iyali tun lokacin da ka nunamin ni sharace a wurinka,ka aikata Abu mafi muni da kunya a gaban erka,saboda haka ka fice ka bamu wuri,Wlh karka qara tako gidannan,kuma bari Kaji,idan bazaka sakeni ta lallami ba,inada hanyoyin da zasusa dole ka sakeni,karka `batamin rai yanda zan kai qararka Duniya tasan Abin kunyar da ka aikata Abdallah meyasa kake amfani da haqurina kana cutar dani?ko iyayenka bazasuyi haqurin da nayi dakai ba Wallahi, Amma ka sakeni ta lallami bazaka sakeni ba?idan har kana qaunar `ya`yanka zaka sakeni ko Dan tarbiyyarsu,saboda wannan Abu runutacce ne,idan kana aikata zina ko ayiwa matarka ko erka ko mahifiyarka,abdallah bazan ta`ba yafe Maka ba idan wani Abu ya samu _yata ka sakeni Kawai" "Wai ni surayya sau nawa zan sanar Miki ni bazan iya sakinki ba kiyi haquri muci gaba da zama haka na Miki alqawarin wata rana zan canza nima ai banaso haka ya ta`ba yarana" "Iya abinda zaka fad`a Kenan?to ka Sani a YAU rabuwata dakai tazo,zanje na sanar da iyayenka duk abinda kakeyi kuma na roqesu susaka ka sakeni Dan na Gama zama dakai,abdallah idan nace zanci gaba da zama dakai yaudarar kaina zanyi,Wallahi a yanzu abdallah Bana sonka,Bana son ganinka abdallah ka zama qazanta a idona bazan ta`ba qara iya amince Maka a matsayin miji ba,kar kasa Allah ya rubutamin zunubi idan har kana Sona ka sakeni Kawai" Ina leqowa na tarar ya fice ya barta a nan parlour, numfashi naja Dan ban shirya ganin wannan takaici da sassafe ba.shiryawa nayi muka tafi makaranta khairat nata d`ebemin kewa da surutunta Sam ban fahimci komai ba a darussan yau, tuni nadena fahimtar komi a wannan lokacin sai tunani. Na nisanta kaina daga qawayena Wanda nakeda tabbacin zasu iya sanyani Naji Dama Dama,Amma banason ganin kowa balle magana ta had`ani da wani,Mummy ma duk yanda taso nayi magana naqi,idan na bud`e bakina kalma Daya zuwa biyu ke fitowa Ana tashi cikin sauri na ISA parking lot amma Banga motar Mummy ba,inata hange Naji an kira sunana,Sam ban amsaba saida Naji an qara kira,Ina Juyawa naga wani na d`agomin hannu alamun na tsaya "Hajiya CE ta turoni na d`aukeki, saboda bazata samu damar zuwaba tace na kaiki gida"ya fad`a yayin da ya ISO inda nake Kallonsa nayi Tabbas yayi kama da direba,Amma Bata ta`ba turomin shi ya daukeni ba "Amma ai ba kai kake zuwa ba idan bazata zo ba,Ina lawal d`in yake?" "Ai lawal baya gari tacemin ma na kaiki gidan antynki bilki a can zata d`aukeki" "Okayyyyy to khairat fa?" "Ai tun d`azu na d`auketa na kaita nayi sa_a Ina zuwa Suna tashi" Turus na tsaya Dan Sam zuciyata Bata amince masa ba,maganarsa CE ta dawo dani daga tunanin na bishi ko a`ah "Wai ba hafsat Abdullahi bace?wadda ake kira munaya?barrister surayya itace mahaifiyarki, Alhaji Abdullahi Abdullahi kuma Mahaifinki,ai Ina cikin yaran shagonsa,kuma Ki duba wannan number Bata mahaifiyarki bace?yanzu muka Gama waya da ita" "Itace"na fad`a Ina duba wayar Haka yauita min dad`in baki har na amince na bishi,Bayan mun Shiga motar yace"saidai fa zaki kwatanta min gidan antyn taki Dan bansani ba" "Idan mukaje Sharad`a ja`En daidai gidan mai sai muyi Kwana,kaga muje in nuna maka" Tafiya ta d`au nisa cemin yake zaibi ta hanya mai sauqi Amma sai naga Yana kauce hanya,kafin na Ankara ya tsaya wasu mutane biyu sun shigo motar sun rufe,a tsakiya suka Sani tuni na rud`e na kasa Koda motsi Duk glass a rufe yake kuma babu tints Amma hanyar babu mai ganinmu domin babu mutane,d`aya daga cikinsu ya qullemin hannuwana a bayana d`Aya yasa qyalle ya qullemin idona,wani Abu suka turamin a abakina sannan suka qulle,bansan inda muke bi ba haka Naji mun tsaya an d`aukeni cak an canzamin mota Tafiya mukeyi babu tsayawa bakina ya gaji,qafaduwana da aka qulle nake Zaune kansu sunyi tsami,hannuna ya gaji haka wuyana,ba damar kuka babu damar ihu ba damar fad`a haka na zauna cikin wannan wahalar na iya tsawon lokacin da bazan iya qirgawa ba kafin Naji motarmu ta dakata.... _Kuyi haquro da wannan,dawowata Kenan daga anguwa na rubuta Fatan Zaku dauke kai ga duk kuskurena Nagode kuci gaba da bibiyar MUNAYA Dan jin yanda zata Kaya,Taku a koyaushs,baby maryam *MUNAYA* Maryam? Wattpad@mamsuhaimerh 14 , nan ma cak aka d`aukeni aka kaini wani wuri inda aka kuncemin bakina Amma qafafuna,hannayen da idanuwana duk a rufe,bayana tuni ya fara amsawa ga ciwon fad`Uwa daga bene Wanda Jiya na fara shan magani ga zama a takure Banji muryar kowa ba banji motsin kowaba,har wasu En mintina Dan haka na fara neman taimako "Dan Allah akwai Wanda yake jina?jama`a Ku taimakamin Dan Allah Ku taimakeni!!!Dan Allah a taimakamin!!!bayin Allah......" "KE!!!"wata razananniyar tsawa ta Dakatar dani"nan yayi miki kama da wurin taimako?kiyiwa mutane shiru idan ba haka ba na lahira sai ya fiki jin dad`i" Ai tamkar ya tunzurani na qara ware muryata tunanina wani zai jiyoni"a taimakamin!!!!Dan Allah a taimakeni na Shiga uku!!!!Ku taimakamin zasu kasheni!!!" Saukar wani mari mai kama da saukar wuta ne ya Dakatar dani babu shiri cikin gigicewa nayi shiru hawaye na kwarara daga idona saboda azabar wannan Marin,gaba d`aya jikina ya d`au rawa tsorona ya qaru Su Waye wad`annan? Me yasa suka saceni? Me zasuyimin? A Ina nake? Menene yasa suka d`aukeni? Ina mummyna? "Idan kika sake na qara jin muryarki ko?....."duka ya sakarmin a kafad`a Wanda Allah kadai yasan dame ya dakeni,babu shiri nayi tsit da bakina domin azabar ta isheni haka, Qafafuna sun kumbura domin nadena jinsu a jikina saboda taruwar jini,domin tunda muka taho a kansu nake Zaune,da qyar na matsar dasu gefe nan bayana ya kar`bi nashi kason tamkar zai rabe biyu,ga hannuwana da kafad`una da suke azabar ciwo,ga zafin mari ga qulallen ido A haka na zauna cikin wahala da gajiya ga qishirwa ga yunwa ga tsoro ga fargaba,ga takaici ga nadama ga fitsari ga rashin wanka,bansan adadin dad`ewata a haka ba Amma Tabbas zanyi Kwana guda ko yini domin na zama makauniya an rufemin ido da qyalle Ina cikin wannan yanayi Naji alamun an bude qofa da alamun an shigo an rufe,bugun zuciyata ya qaru,tsorona da fargabat sun ninku,ahikenan mutuwata tazo,Ashe ganin qarshe nayiwa Mummy da khairat,Ashe bazan qara ganin yayana da Abba ba, A hankali aka kuncemin abinda ya rufemin ido gaba d`Aya na kasa gani sosai saboda haske yayimin yawa,Ina rufe idona Ina bud`Ewa a haka har d`akin ya zamarmin daidai na kalli Wanda ya kunceni,shine direban da ya d`aukoni cikin kuka nace "Dan Allah me nayi Maka zaka saceni ka kawoni nan?" "`Yan mata aro ai ba Sata bace,nasan bazaki zauna Ki dad`e ba a lissafina,dan haka na bud`eki kiga gari Ki kalleni Ki qaremin kallo,Dan duk wurinnan Babu mai imani kamar ni" "Dan Allah ka sakeni na koma Wallahi bazan fad`awa kowa ba nayi Maka alqawari ka qyaleni Kawai na koma ga iyayena Dan Allah" "Munaya ko?Suna mai dad`i kisani zaki koma gida Amma AI bazai yiwu mutum yayi tafiya mai nisa haka ba tareda tsaraba ba,zaki koma gida Amma kan sharudda,yanzu kiduba inda kike, zan kunceki Ki huta na awa d`aya zamu auna hankalinki mu gani" Kunceni yayi ya fita ya rufeni a d`akin,d`Aki ne babba Amma banda katifa da Zanin gado babu komai cikinsa sai wata qofa alamun band`aki ne,babu murfi babu komai Qofar na nufa nayi alwala kukana sannan nayi alwala na fito na fara tunanin sallah nawa zan gabatar. Leqowa yayi yace"saiki fara da azahar d`in Jiya lokacin da na d`aukoki Kenan zuwa azahar d`in YAU wannan lokaci da muke ciki,Ki hanzarta karki `batamin lokaci Ina sallah Ina kuka tareda gayawa Allah matsalata Ina roqonsa ya fiddani daga hannun wad`Annan azzalumai Bayan na idar da sallolin ya shigomin da abinci Wanda Sam banbi ta kansa ba Mummy khairat da Yaya ne Kawai a Raina Ina tunanin halin da suke ciki,tuna maganarmu ta qarshe nayi da Mummy _munaya kicemin wani Abu Mana,tunda abunnan ya faru kin denamin magana ko Nima Fushi kike dani kamar mahaifin naki?_ _Mummy Banyi niyyar CE Miki komi ba,Amma har ga Allah banason ganin Abba a gidannan banason maganganun da kukeyi,nasan laifinsa ne Amma bai kamata Kuna fad`ar wani Abin ta yanda zan jiyo ba,Mummy Ki dena biye masa idan kukaci gaba da irin wannan hayaniyar watarana Zaku wayi gari Ku nemeni Ku rasa na bar muku gidan gaba d`Aya daga nan na bar duniyar ma ni na huta kuma Ku huta_ Kuka na fara da tunanin Mummy na nan Tana baiwa kanta laifi Tana nadama Tana roqon a Nemo mata ni duk inda nake,Tana tunanin gudiwa Nai saboda abinda ke faruwa Khairat na hango Tana kuka Tana yiwa Mummy birgimar ta kawo mata ni,ya Allah nasan duk dangina zuwa yanzj hankalinsu ya tashi "Idan kinaso Ki fita da wuri ga sharudda na idan kikabi ko Sati bazaki rufa anan ba zaki fita" Maganarsa CE ta katsemin tunanina na share hawaye nace"me kakeso" "`daukar fansa" "Kamar Yaya?saboda me zaka d`au fansa dani?" "Wannan ba huruminki bane Ki tambaya da kaina zan sanar miki,kin shirya kar`bar sharudda na?" Shiru nayi Tabbas inaso na fita kuma naga babu kalan cuta a tare dashi,Amma kuma Ina tsoron abinda zai fad`a "Na lura baki

Chapter 7 of 8