Share this page
5 / 8
takuramin na sanar mata naqi,haka na Kwana duk Suna Fushi dani musamman mummy da ko kallon kirki batayimin ba da damuwa FAL na Kwana Da safe ma a hanyar school babu abnda mummy tacemin har ta saukeni ko addu'a batai min ba ta juya,haka na had'iye hawayena na Shiga class Bayan mun Gama Muna Zaune Nabila Sai fad'a takemin Tana cewa Dama Bata sanarmin ba Gashinan na hana kaina sukuni,kuma naqi fad'a mata meke damuna "Da wuri zaki koma gida?"na tambayeta "A' a YAU ummama batanan banason komawa gida ma za'a takuramin Jiya ma Banyi baccin kirki ba,zan zauna nayi karatu wajen 3 haka Sai na tafi" "Haba Dai 12 fa batai ba,kawai Kizo muje gidanmu mummyna batanan nima Sai antyna tazo haihuwa Kizo muje Ku gaisa Sai Ki zauna la'asar Sai Ki tafi" Kafin tace a'a na fara mata magiya Baku sanni ba na iya magiya dole kayi abinda nace,haka ta bini gida a mota babu wanda yayi magana,nayi shiru saboda tsananin ciwon kai da nake ita kuma ta takura saboda rashin sabo Tukur Yana ajiyemu muka nufi cikin gida,Sai ji nayi Nabila ta damqo hannuna da qarfi,a tsorace na kalleta jikinta na rawa tace "Hafsa Kinsan wannan mutumin?"ta nuna mahaifina dake tsaye a gefen qofar parlour ban ma hangeshi ba saida ta nunamin shi Tsoratar da tayi CE tasa nace mata"a'a family friend ne me ya faru" Muryarta na rawa tace"Hafsa shine" "Shine Wa?"na fada Nima da rawar murya Ina tsoron abnda zai fito daga bakinta "Hafsa Wallahi shine bazan ta'ba mantawa da fuskarsa ba,shine mutumin da ya sayi budurcina, shine mutum na farko da ya....." Dakatawa tayi Tana kallon idona da suka rine da hawaye, cikin takaici da qunar rai na kalleta da jiqaqqiyar fuskata nace "Nabila wannan mutumin.....mahaifina ne....." *ga double post na Baku saboda murna da nakeyi sosaj da sosai Ina cikin farin ciki Ina muku Fatan akhairi Ku sanarmin da abnda kuke tunani a kan littafina* [12/12, 21:21] Maryam?: *MUNAYA* Maryam? Wattpad@mamsuhaimerh 09 Sunkuyar da kanta tayi qasa da alamu Tana nadamar sanarmin da hakan,na goge hawayena nace"Bakomai Sai mun had`u Gobe kinji?" Muka rabu ta juya na shige ko kallonsa Banyi ba.Ina Shiga na qara had`Uwa da wani tashin hankalin Aunty suwaiba ce a parlour Tana ta had`a gumi tana murqususu,da gudu naje na d`auko wayata Dan na kira mummy babu chaji,gefenta na zauna cikin tsoro da kid`ima nace "Auntyna Ina wayarki?" Ko nuni ta kasa yimin ciwo yaci qarfinta da gudu na fita na kira driver ya kaimu asbiti mummy ta samemu a can,Ina fita Naji qaran horn alamun ta dawo Cikin sauri ta shigo Tana tambayata "Ina auntyn taki?" Nuni Kawai nayi mata da d`aki muka Shiga,a sume muka sameta hankalina yayi bala`in tashi mummy ta shafa mata ruwa ta farfad`o da qyar muka kamata muka kaita mota Gudu mummy take sosai Amma haka bai hanamu Dakatawa holdoff ba "Na Shiga uku mummy kingani bleeding take" "Wayyo Allah na mummy Bata motsawa" "Mummy muyi sauri kar wani Abu ya sameta" "Mummy....." "WOULD YOU SHUT UPP!!!!?"Ta dakamin tsawa ba shiri nayi shiru har muka qarasa asbitin,ana dubata akace aiki za`a mata nan mummy ta kira mijinta ya amince mummy tasa hannu Muna Zaune mummy na ta Kiran dangi Tana fad`a musu Naji kaina ya Sara,na fara ganin biyu biyu,rintse ido nayi na dafe kaina har Naji Dama dama barkata da mummy Bata gane ba "Bari naje na d`auko Kaya a gida ke Ki zauna anan"mummy ta fad`a tanamin kallon tuhuma? "A`a Mummy idan aka Gama AI za`a buqaci babba,kuma za`ayi ta kiranki,zanfi sauri bari naje" "Bazan barki Ki tafi ke kad`ai ba Kinsan haka ko?" "Dan Allah mummy Ki bari naje kafin ta fito,zan cire uniform kinga fa dole a buqaci abubuwa bamuzo da komai ba,kuma yanzu Anyi minti 5 da shigar da ita,Ki yarda dani Mummy " "Bazaki tafi a wannan halin ba,dubi idanuwanki haka zaki fita titi?" "Mummy...." "Kudai kaman yara kullum cikin musu kuke kaman ba Uwa da `ya ba,MUNAYA duk kukan tausayin ne haka?"yayar mummy ta fad`a Tana zama gefena "Hm yaya Wallahi taurin kai gareta ne Wai a haka zata fita ta koma gida" "Munaya AI bakya fita a haka ba,yanzu tunda nazo kubar musun Ku tafi tare,ba shikenan ba?" Fita mukayi kaina na saramin ga nauyi da yayimin,riqe kaina nayi mummy tace"Wai ciwon kannan har yanzu?idan mun dawo zakiga likita" Gaba d`Aya Naji kaina ya fara Juyawa ko me na kalla Juyawa yake,a hankali ganina ya fara dishashewa,Sai abunuwan da suka faru dani suka fara dawowa _Haba `Yan mata ya zaki gudu Ina zakije?d`an tsaya Mana......Wayyo Allah na ka rabu dani.....mummyyy!!!!!!na Shiga uku_ _na gaji da zama dakai abdallah,ta dalilinka na rasa d`ana Ina kallonsa aka qulle ba yadda zanyi,abinda yafimin ciwo nice lauyan Wanda ya kaishi qara,ka lalatawa d`ana tarbiyya bazan zauna ka lalata tarbiyyar MUNAYA ba,macece ita abinda kake zai iya samunta...._ _abdallah wannan Wace irin masifa CE,munaya fa `yarka CE ta cikinka,abdallah lalacewar takai ka nemi `yarka Bayan `Yan aikin da ka kora da wadda kayima ciki?_ _abdallah Zamanmu yazo qarshe halayyarka ta fara ta`ba `yata na Gama Daurewa,ka fad`amin mene Bana Maka a Zaman aurenmu,zakayi watanni Baka waiwayeni ba Amma kullum kana wajen matan banza,kaCE zaka canza amma Babu alamun canji tare da kai,karka fita ka dawo ka bani takardata_ _ka gani abinda na fad`a Maka ko?a qofar gidanka ana neman molesting `yarka,abdallah yaushe zaka canza `ya`yanka fa mata biyu ne abdallah Baka tausayina?_ _na Gama zama dakai abdallah har takai ka kawo karuwa cikin gidana?da ninna ganka da sauqi Amma bazan zauna dakai a haka ba,Bayan ka nemi `yarka ta cikinka sannan ta ganka kana tarayya da wata?ka sakeni yanzunnan ko kuwa duk Duniya taji abinda ka aikata Wallahi_ _yarinya Kenan,MUNAYA kke ko?karki damu zaki mutu Kema kaman yanda larai qanwata ta mutu,amma saina d`and`ana Miki azabar da ta d`and`ana_ _mummy na kashe mutum,mummy ya mutu....na Shiga uku da hannuna na kasheshi mummy..._ _Hafsa shine,Wallahi shine bazan ta`ba mantawa da fuskarsa ba shine mutumin da ya sayi budurcina,shine mutun na FARKO da ya...._ "Innalillahi Wa inna ilaihi raji`un,meke faruwa?munaya!munaya!!MUNAYA menene haka!!!MUNAYAAA!!!" Qoqarin bud`e baki nayi saidai babu kalmar da ta fito,a hankali na fara ganin duhu,mutanen dake zagaye dani suka fara ja baya,babu abinda nakeji Sai muryar mummy Tana Kiran sunana kafin na fad`a cikin duhu..... Farkawa nayi da azababben ciwon kai na kalli wurin da nake,d`aki ne na asbiti ga monitor a gefe Tana bugawa,roba CE a hancina da cannula a hannuna,a hankali na d`aga kaina na kalli drip d`in dake Shiga jikina,ga mummy Zaune kan kujera tayi tagumi,Bana gani sosai haka yasa na runtse idona na qara bud`ewa "Mummy"na fad`a da muryar da ko ni kaina banji sosai ba,tunanin abnda ya kawoni nan nake,Bata lura dani ba ta Shiga kogin tunani,ina qoqarin zama kaina ya saramin,a take na tuna yanda Akai nazo Hannu biyu NASA na riqe kaina saboda tsananin ciwo hawaye ke zuba daga idona numfashina ya fara cijewa Cikin sauri mommy ta taso ta riqe hannuna "Nurse!!!yi sauri Kizo zata jima kanta ciwo!" Juyo nake Ina riqe kaina saboda yanda yake bugawa,a hankali Naji monitor d`in ta fara alarming kafin nurses biyu da doctor suzo Qoqarin riqeni sumin allura suke saidai azabar da nakeji ta hanani sukuni ni kad`ai nasan abinda nakeji,cikin zafin nama likitan ya kar`bi allurar ya riqe hannuna ya dannata ta cikin cannula,cikin mintina qalilan na qara komawa cikin duhu Ko da na farka na samu sauqin ciwon kai sosai,mummy Tana kan kujerar da na ganta wancan farkawar da nayi,saidai na lura ta canza Kaya,Nima kayan asbiti ne a jikina "Mummy" A hankali ta juyo ta kalleni da idanuwanta da suka nuna rashin bacci"bari na kira likita" Kai kawainna gyad`a mata ta d`au waya ta kira sannan ta kalleni "Ya kikeji yanzu?" "Da sauqi,me Anty suwaiba ta Haifa?" "Namiji?" "Tana nan?" "Ta koma gida an sallameta" Zare ido nayi nace"Mummy kwanana nawa anan?" "Hud`u" Shiru nayi na fara tunanin ya akayi nayi Kwana hud'u?anya ba da wasa mummy take ba? "Kinyi Kwana d'Aya sannan kika farka kika qara komawa,YAU kwananki uku Kenan Bayan wancan" Tana Gama fad'ar haka likita ya shigo da murmushinsa yace "Munaya da sauqi Kenan" Kai na gyad'a Dan na tuna komai,duddubani yayi yace"ya kike ji?" "Inajin kaina empty doctor ba kuwa qwaqwalwata kuka cire ba?" Dariya yayi yace"family d'inki sun damu da yawa qa'ida babu mai shigowa wurinki Sai kin samu sauqi sosai Amma yanzu zasu shigo,daga nan zan miki allura Ki qara komawa bacci kin zama 'Yar gatan bacci" "Doctor Yusuf kaidai kanaso na dinga bacci ne kawai" "Kina buqatar baccin ne,yanzu zaki aramin mummynki na d'an mintina?" Girgiza kai nayi alaman a'a,murmushi yayi yace "Saboda me?kin fa liqe mata da yawa" "Saboda zakayi mata maganata,nidai a fad'a anan Gaskiya"na chuna baki "Munaya Kenan sarkin rigima,Haba babynmu Ki d'an aramin ita Mana nayi alqarin zan biya da chocolate" "Ka fanshi kanka,na Baka ita all day,Amma inajin yunwa da qishirwa ko bazanci abinci bane" "Zakici Mana,nurse zatazo yanzu," "A`a mummy nakeso ta bani" "Shikenan yanzu zamu dawo,ga baqinki nan shigowa" Suna fita Anty suwaiba,sumayya Nuriyya, da sauran iyaye suka shigo" "Sorry my dear"Nuriyya ta fad`a tareda kissing goshina,murmushi nayi na kalli Anty suwaiba "Anty suwaiba ya Akai kika zo Kema" "Takura musu nayi hankalina yaqi kwanciya" "Muga babyn" "Sumayya ta miqawa babyn ta riqemin Dan hannuna rawa yake da qyar ma na zauna "Aikuwa kamarmu d`aya dashi tubarkalla,Naji haushin banj na fara ganinsa ba,gashi yanzu ma bazan iya daukarsa ba" "Mudai fatanmu Allah ya baki lafiya"babbar yayarsu mummy ta fad`a Shigowa Mummy tayi Muna hira na kalleta da kyau nace"Mummy kuka kikayi?me likitan yace?" Numfashi taja ta zauna,saida mama ta qara mata magana"duk hankalinmu Yana kanki surayya menene?" "Mama.....munaya......" Ohhhh kumin haquri banda duka Sai mun hadu Gobe luv u all [12/13, 16:52] Maryam?: *MUNAYA* Maryam? Wattpad@mamsuhaimerh 10 "Mummy Dan Allah kiyi magana,mutuwa zanyi?" "Ina ganin muje waje muyi maganarnan"mama ta fad`a Tana kallona,kafin na maida martani duk sun fice sun barmin d`akin cikin qanqanin lokaci mummy ta dawo ta bani abinci ban tambayeta ba itama Bata sanarmin ba haka muka zauna shiru Ina tunanin abinda aka fad`a da ya maida mummy haka,allura aka qaramin na koma bacci Ban jima ba na farka daidai lokacin likita ya shigo,murmushi yayi yace"ga alqawarin da nayi nan na taho dashi Amma bazaki iya CI yanzu ba saikin koma gida" "Doctor me kacewa mummy d`azu" Kallona yayi ya kalli Mummy yace"zan fad`a miki idan kinji sauqi" Had`e rai nayi nace "shikenan jeka da chocolate d`inka banaso" "Munaya!"mummy ta fad`a cikjn tsawatarwa "Mummy indai abinda ya shafeni ne Ku fad`amin Mana tunda ko ba yanzu ba zan Sani" "Haba er baby idan aka fad`a miki yanzu zaki iya qara kwanaki a nan,indai kinaso Ki fita da wuri Ki bari saikin warke,na miki alqawari da kaina zan sanar miki" Juyawa nayi na dena kallonsu Dan Banga amfanin `boyemin ko ma menene ba indai ya shafi lafiyata,menene banji ba akan ciwona d`an abinda suka `boye bazai rage komai ba "Haba hafsatuna,YAU banida aiki fa takanas nazo kawo miki uwargidan taki amma kika juya?shikenan bari na koma da abata ko ma na zauna na shanye" Nayi qoqarin sharewa Amma inajin qaran leda alamun ya bud`e nayi saurin juyowa "Bani abata,AI cewa nayi banaso ba Bana Sha ba" Dariya yayi ya miqomin na bud`e ROXY na fara Sha,"Gaskiya doctor kasan kan chocolate, Wai ma a Ina ka siyosu" "A wani wuri mai nisa,takanas naje na siyosu Dan na kawo miki" "My pleasure"na fad`a tareda sunkuyawa Dariya yayi yace"da alamu kin samu sauqi sosai zuwa jibi dai kin koma gida" "Gobe dai bafa najin ciwon komai ni yanzu,au kace fa bazanci kayan zaqi ba Sai na koma gida" "Na manta...kawosu nan" "Ai sunzo hannu kuma" Fizgewa yayi da sauri na tabe baki cikin shagwa`ba"Mummy kin ganshi ko?kice ya bani" "Doctor idan Baka rabu da yarinyarnan ba bazata barka kayi aikinka ba,gara ka qyaleta kayi tafiyarka" Tashi yayi da ledar chocolates d`in na kwa qwalla qara na fara buga qafa"Allah ka bani abuna" Maimakon ya bani Sai ya tsaya ya hard`e hannu Yana kallona Yana murmushi "Na ma dena kulaka"na fad`a tareda jingina jikin pillow na ta`be baki "Sorry princess,ga abinki nan na baiwa mummy Amma bazaki Sha ba Sai kin koma gida okay?" Kai Kawai na gyad`a tareda murmushi,saida yaje qofa ya juyo yayi kissing hannunsa ya huro wurina alamun flying kiss Cafewa nayi na cukwuikwiye na saka a shara duk mukayi dariya ya fita,mummy Kawai kallonmu take daga ni har shi batace komai ba ta maida hankalinta kan system, Tana dannawa wayarta tayi qara ta d`auka "Assalamu alaikum.....eh na dubashi da kyau na kuma samu suspect d`in dukkansu basa da niyyar magana,banajin Gaskiya zan d`au wannan case d`in,mutuminnan akwai abinda yake `boyewa,last time cewa yayi zai Bada ko nawane shi Dai burinsa ayi Shari`arnan da wuri......a`a banaso ne.....to shikenan.....jiki da sauqi sosai.....to Allah ya kaimu zataji" Kallonta nake Dan tayimin magana Amma Kawai ta kalleni ta maida kanta kan system,tasan Tana fara magana zata fad`i abinda batason fad`a,Nima tanamin magana zan fad`a mata abinda banaso ta Sani Na gaji da zama shiru nace"mummy a ciremin wannan Abin nayi sallah" "Toh"waya ta d`auka ta kira nurse,na rasa nurses d`in asbitinnan me sukeyi kullum Sai an kirasu su da ya kamata ace Suna gefen Mara lafiya "Gobe class mates d`inki zasuzo dubiya na sanarwa school d`inku" "Okay" Ko da aka ciremin drip d`in kasa takawa nayi saida mummy ta riqeni,Kwana hud`u a kwance ba wasa ba,a Zaune na gabatar da sallolin da zan iya na haqura sauran Sai na qara hutawa Ina Zaune yau ras nake jina Sai cin abinci nake Muna hira `Yan Uwa Sai zuwa suke,suwaiba ma munyi waya da ita tanata complain an hanata zuwa Bayan tafiyarsu da mintina Naji hayaniya a waje,Sai kuma Naji Anyi shiru a hankali suka fara shigowa,`Yan class d`inmu ne mata suka shigo bansan lokacin da Hafsa ta cukwuikwiye ni ba "We miss you so much Wallahi" "Hafsa karki qarasata Mana" "Munaya Sannu" "Ya jikin" "Da aka fad`a Mana kina asbiti Wlh duk jikinmu yayi sanyi" "Tun yaushe kike nan" "Meke damunki" "Kin rame Amma kinyi kyau" HAka suka dinga zuba magana na rasa ma Wanda zanyiwa reply Sai murmushi Kawai nakeyi "Kinganta nan tunda kika tafi ta koma kaman Mara lafiya tare ma Dai kuke cutarnan"Hafsa ta fad`a Tana nuna Nabila dake gefe Tana kallona Murmushi nayi nace"na kusa dawowa insha Allah" Muna haka Naji muryar doctor zai shigo"kwankwan Kwan princess SSS kin huce zan jya shigowa?" Kallona Hafsa tai ta zare ido tarefa rufe baki,harararta nayi nace"zaka iya Amma inada baqi" Leqowa yayi Abin mamaki Sai naga fuskarsa ta canza ya zama serious "Bata son hayaniya sosai,so...karku mata hayaniya"ya juya ya fice Zare ido Hafsa tayi ta bud`e baki Tana kallona Tana qifta ido,Sai can tace"OHHHH MY GOD!!!" Gaba Daya suka d`au dariya wata da nake kira mummyna tace"oh Ashe Dai zanga auren d`iyata kafin na mutu,Wayyo diyata zata auri likita" "Qawalliya kimin alqawari babynku ta farko sunana zakisa kinji?kodayake inda SOYAYYA tayi zurfi sunan mata miji yake mayarwa Dan haka nasan ma kaman ansa sunana an gama"Hafsa ta fad`a Tana juyi a gabana,hannu NASA na maketa nan ma suka d`au dariya,cikin murmushi Nabila tace"kun manta mun bar maza a waje fa" Mayafi na yafa akace su shigo "Oh my Babe what happens to you"drama boy Kenan,shine ya taimaka min da test d`innan tun lokacin muka saba Murmushi nayi nace"Naji sauqi" "Ban yarda ba lemme see"ya kawo hannu zai ta`ba goshina Hafsa ta makeshi "Do not touch the doctor's property, yanzu yazo Yana hello my princess, muma da ya ganmu saida ya Mana kashedi ka sake ka tabata Sai ya cire Maka kwakwalwa" "Wayyo zuciyata, bazan iya rabuwa da MUNAYA ba u are the love of my life,bari Kawai nayi ta Romeo na kashe kaina"ya janyo biro ya caka a rigarsa kaman irin mutuwa a film Sai ga mutum a qasa "Zan farfad`o kina furta you love me" "Idan kika furta masa baki fara furtamin ba,Nima zan mutu"mujahid ya fad`a "Amma AI Kinsan duk na fiku Santa ko?"auwal ya fad`a Yana kashemin ido "Wait, Nima fa Ina sonta Kawai lokaci nake JIRA na furta"Khalil ya fad`a Kafin wanimya qara magana nace"guys I love you all,idan na dawo school Sai ayi competition Wanda yaci shine nawa" Hira sosai mukai kowa na fad`in yanda yayi missing d`ina banda Nabila wadda kallona kawao take Tana murmushi, da zasu tafi suka ajiyemin qatuwar leda da kuma envelope "Nifa Banga son da kuke mata ba"Khalid ya fad`a Yana kallon matan class d`inmu, kafin na fahimci me yake nufi aka fara hugging d`Ina one by one ana kissing goshina,Nabila CE last,Tana hugging d`ina tace "Am sorry,am really sorry" "Ba laifinki bane,Amma bazan iya riqe alqawarinki ba,saboda lafiyata dole na sanarwa mummy" "Babu komai,na yarda dake" "Ohhhh so romantic"mujahid ya fad`a,ta sakeni ta galla masa harara tace "Kaine romantic d`in ai "Yes baby I love you too"ya fad`a Yana taba zuciyarsa Saida nurse ta korasu sannan suka fita wasu teachers suka shigo sukamin Sannu suma,Bayan tafiyarsu ni kad`ai na rage mummy ta fita Bata dawo ba * * * Yau Sati na d`Aya da dawowa gida kuma YAU ta kama zamu koma check up,kuma YAU ne zai sanar dani abinda ya sanarwa mummy, ya Allah ko zan iya riqewa ko bazan iya ba? Haka na tashi duk jiki babu qwari da Abin na kwanta domin maganin da nasha ma yaqi aiki saboda tunani, Ido a kumbure na tashi naci abinci tun mummy na kirana na shirya mu fita har ta gaji,Dan tasan tsoron abinda zanji nakeyi Sai gab da magriba na fito daga d`Aki Bayan dogayen addu`o`1n da na jera Allah yasa na iya d'aukan abinda zanji A asbitin mukai sallah kasancewar ya Shiga theater Sai wajen Isha muka samu ganinshi "Munaya ya jikin?kina zuwa school?" "Bayan ka hanani zuwa?jiki kuma lafiya Qalau,amma nasan Sai ka qara dubani" Bayan dogayen kalamai da gwaje gwaje yace"kaman yanda na fad'a miki barrister dukda cewa suggestions ne amma yanzu na lura dole muyi hakan" "Doctor ni kace zaka sanarwa abinda ke damuna ya kuka sani a tsakiya Bana gane me kuke cewa" "Munaya kin shirya ji Kenan" Hannun mummy na riqe nace"na shirya MNA doctor AI da bazaka ganni a nan ba" "Munaya.....zamu d'auraki a lifetime medication" "Ban ganeba" "Zamu d'auraki a magani har qarshen rayuwarki" "Saboda me doctor?"na fad'a Ina qoqarin danne hawayena *MUNAYA* Maryam? Watrpad@mamsuhaimerh 11 "Saboda kina Fama da ciwon disthymia,ko double depression, dukkan alamun da muka gani a gwaje gwajenmu sun tabbatar da haka,domin ita wannan dysthymia ba`a tabbatar da ita Sai mai dauke da ciwon yayi Sama da shekara da ciwon. Alamun ciwon sun had`a da Difficulty sleeping,(Gaza yim bacci saida taimakon wani magani Canza rayuwa ko Gaza enjoying rayuwar da kake Yawan nadama da ganin kai ba komai bane ko mutane basu damu dakai ba Rashin kuzari ko yawan kasala Kasa maida hankali ko Gaza concentration akan wani abu Change na appetite mutum baison cin abincin da ya kamata Tunanin mutuwa ko kashe kai Babu matsala wajen yin abubuwa Amma koyaushe mutum zai kasanCE cikin rashin walwala da damuwa Sannan mutum zai dinga jin magana ko ganin mutane,ko jin motsin abunda baya wuri,kaman hasashe Kenan Shi wannan ciwon baya tafiya gaba d`Aya Amma Yana raguwa da lokaci,Bayan Wannan matsaloli qwaqwalwarki ta fara ta`buwa shiyasa ya zamar Mana dole mu d`auraki kan magungunan danya kamata kafin a samu matsala,jinin Ki da muka auna ya hau kuma har yanzu bai sauka ba,idan bamu dauki mataki ba zaki iya kamuwa da cieon zuciya"

Chapter 5 of 8