Share this page
4 / 8
takaici Shigowa ummama tayi tace"ya kikeji?" "Ummama qirjina"na fad`a cikin kuka "Sannu,ungo shafa wannan,ga dankali nan na had`a Miki da shayi,Ki shirya Sai kici" Zazza`Bine sosai ya rufeni ga kasala man da ummama ta banj ma na kasa shafawa haka abincin da ta kawomjn na kasa ci, shigowa tayi ta sameni na nad`e Ina karkarwa ta d`agoni ta ta`ba jikina "Nabila Sannu,kanki Yana ciwo Bayan Zazza`bin?" Kai na gyad`a alamar eh,ta d`auko magani ta ajiye gefen gadon "Tashi kici abinci sAI kisha" Ita ta dinga bani abincin a bakina ba abinda nakeji Sai d`aci haka na daure naci nasha magani,Kaya ta d`aukomin tace"tashi Kisa" Jiki a mace na tashi Amma karkarwa ta hanani saka kayan,ita ta janye Zanin jikina ta kalli nonona da ya canza kala daga fatar jikina tsabar jajir d`in da yayi "Ai Sai kin gasa nonon Dan ya kumbura",ta fad`a Tana zuromin Riga ta kaina,Tana sakamin rigar na kwanta ta fita, cikin mintina biyar bacci ya d`aukeni,ban farkaba Sai Bayan azahar jikina ya danyi daidai zazzabin ma ya sauka Sai tsakanin qafafuna da qirjina da sukemin zugi Ranar Babu abinda nayi daga bacci Sai kwanciya duk abinda ya kamata ummama tayimin shi har na farajin Dama Dama a jikina,saidao Abin mamaki batayi maganar mutuminnan ba haka nima na kasa tambayarta Ranar lahadi da dare ta sakani a gaba ta fad`amin abinda yasa na tsaneta abunuwan da suka lalata rayuwata, ta fad`amin qaddarar da zata gudana kaina a wannan gida,ta fad`amin abinda kunnuwana da shekaruna a lokacin bazasu d`auka ba,Kinsan me CE?.... MUNAYA: KASA ko da motsa kai nayi kafin ta qarasa Naji horn d`in motar mummy,tashi mukayi tace "Da alamu labarina YAU ya katse Sai kuma mun qara had`Uwa" Hugging d`ina tayi tace"dukda nasan bazaki fad`awa kowa matsalata ba Amma Ina qara jaddada Miki Ki riqemin sirrina Dan Allah ko da mahaifiyarki karta Sani" "Nayi Miki alqawari bazan fad`awa kowa ba"na fad`a Ina qoqarin maida hawayen dake leqowa,sakina tayi mukayi sallama na Shiga mota Ina qaqalowa mummy murmushi,Ina zama na fad`a kogin tunani Tabbas Nabila taga masifa a rayuwa,saida na zauna da ita YAU na qare mata kallo na lura da duk abubuwan da ta fad`a,duk inda mace takai mace to Nabila taje,fara CE qal kalar `yan kamaru,fatarta har wani sheqi take saboda kyau,duk goshinta gashine a kwance luf,kalar idanuwanta light brown ne sosai kalarsu Tana d`aukan ido,hancinta dogone bakimta madaidaici lebenta pink ne Yawancin mazan class dinmu har ma matan na cewa tanada girman kai Dan taga tanada kyau Bata kula kowa basusan dalilin ware kanta da takeba "Lafiya munaya Ina ta Miki magana kinmin shiru?" Firgigit na juyo nace "babu komai kaina ke ciwo"kuma hakan ne wannan maganar tasa kaina ciwo "Dole kanki yayi ciwo kina sawa kanki tunani,indai akan Mahaifinki ne bazan qara Miki magana a kansa ba na lura tun zuwansa kin canza MUNAYA har rama kikeyi Dan Allah karki sanyawa kanki ciwo" "Mummy nagode kuma insha Allah nadena damuwa kiyi haquri" Hira muka fara sama Sama da ta lura banason hirar ta ajiyeta,nikuwa tunanin Nabila ne yayimin katutu, inaso Naji me ya faru Bayan wannan abin, zan iya hasko zafin da takeji Dan na samu makamantanshi Amma bazan ta`ba Sanin yanda takeji ba Muna zuwa gida na wuce d`aki nayi wanka na kwanta Dan bazanyi sallah ba,Ina kwance mummy ta shigo ta kirani naci abinci,Banyi mata musu ba Dan inajin yunwa Amma tunani bai barni naci yanda ya kamata ba,tunani nake dani da Nabila Wa yafi wani Shiga damuwa?duk yanda na auna damuwoyinmu saidai naga kowa da hanyar da damuwarsa tayi,tamkar na janyo Gobe nakeji Dan Naji sauran labarin Nabila Ku fad`amin ra`ayinku kan labarina karku manta ra`ayinku zai taimakamin matuqa,Taku a kullum baby maryam [12/11, 10:01] Maryam?: *MUNAYA* Maryam? Wattpad@mamsuhaimerh 07 Raba dare nayi Ina karatu da tunani, lissafi baya bani wuya Amma fa chemistry Bana qaunarsa,ayita zana layuka Dan mugunta ace kayi musu sunaye da ana musu fuska ne ma Sai kace da sauqi Amma banda lanqwasa ba abinda ake canzawa kuma ace kayi musu Suna Sai 12 na haqura na ajiye na kwanta bacci,da wuri na fita domin test biyu garemu yau,Sam bamu samu lokaci ba ana fitowa kuma Nabila tayimin sallama tace zataje wani wuri "Yau akwai Abin mamaki a gida,Amma tunda kinqi fad`amin meke damunki zan kautar da Abin mamakin" "Sorry mummy karatu ya fara bani tsoro ne,Sam kaina baya d`auka gani nake bazanyi Abin kirki ba" "Kinsan dalilim da yasa na zama sananniyar lawyer kuma na zama lauyan tun farko?to Ki Sani duk abinda na fara Ina saka hope Akai zanyj nasara ko menene shi komai dadi ko wahalarsa,Kema Ki sanyawa ranki haka kinji?" "Nagode mummy idan babu ke bazan iya rayuwa ba bansan ya zanyk ba idan na rasaki" wani kallo tayimin lokacin da takeyin parking Bata tankani ba ta shige gida na bita a baya Ina d`akina naji ana qwalamin kira,towel ne Kawai jikina na fito daga wanka na leqo kaina,wani tsalle nayi na nufeta zan rungumota Kawai na dakata ganin titsitsin cikin dake jikinta "Amma Anty suwaiba baki cika alqawari ba kince fa dani zamu raini babynki Amma saida ya tsifa zakizo" "Au bazaki min Oyoyo din ba Kenan" "Wannan kayan zai barni ne?ni na fara Kishi dashi ma"na chono baki Matsowa tayi ta rungumoni muka qara gaisawa cikin murna na karbi kayanta na shigar Daki na dauko kayana na fito parlour "Me nake gani?anan zakI shirya?Wai ke baki canza Hali bane?" "Haba antyna Dan na shirya a parlour AI ba wani Abu daga ke fa Sai mummy" "Oh ni Allah ya nunamin randa zaki girma,ko ruwa baki bani ba" Da sauri na d`auko mata ruwa da kayan marmari na zauna Ina matsa mata qafarta da ta kumbura "Antyna Amma bakizo da wuri ba,yanzi a haka kikai Zaman mota?" "Munaya ba yanda Banyi dashi ya kawoni tun watanni biyu da suka wuce ba Amma yace na JIRA Sai lokacin da zai koma aikinsa shiyasa"ta fad`a Tana cije baki "Saura Kwana nawa yanzu" "Bazan kai wata guda ba Insha Allahu" "Amma kuwa suwaiba kinyi ganganci da tsohon ciki zaki taho wannan Uwar tafiya tun daga Minna,da kin haihu a hanya fa?"mummy ta fad`a Tana duba system d`inta "Yaya AI motar gida CE kuma ban takura ba na gaji Dai da zama ne Kawai" "Anty suwaiba anya Bakyajin ciwo nidai naga kaman kinajin ciwo"na fad`a Ina kallon yanda take cije baki "Marata ke ciwo saboda zama Ina hutawa zan sake" "To kije kiyi wanka Ki kwanta idan kin tashi Sai mu qarasa hiran" Ba musu ta ja tulelen cikinta ta nufi d`akina ni kuma na koma wurin mummy "Mummy case d`in menene wannan?naga Sai aiki kike" "Wani mutumi ne ya cinye kudin marayu `ya`yan qaninsa kuma yake bamu wahala duk wata shaida da zata nuna ya cinye dukiyad ya danqwafar da ita shine na samunakamin hacking email dinsa nake dubawa" "Allah ya taimaka"d`aura kaina nayi a cinyarta har bacci ya kwasneni Lokaci guda muka farka mukaci abinci munata hira,Naji dadin zuwan aunty suwaiba rabona da ita tun Bayan na gudo daga wurin Wanda ya saceni Sai yanzu,qanwar mummy CE Uwa d`Aya uba Daya Shinfid`a nayi Mana na gyara ko Ina dukda ban Tara datti ba da wuri muka Shiga Tana zancen zata kwanta da wuri Nima zan kwanta saboda school "Ance anajin motsin babies ko antyna?" "Sosai ma kuwa wani lokacin har alamun qafa ko hannu zaki gani saidai da na fad`awa Mahmud yace ni kad`AI ke gani" "Zanso Naji motsin babynmu kuwa,Wai ance har murya Suna ganewa idan ana magana su motsa" "To Allah masani Amma zata yiwu hakan ne" Muna zama muka kafa hirar Bayan tahowata daga gidanta,Tana kwanciya tayI sauri ta miqe tace"yanzunnan kuwa ya motsa kawo hannunki kiji" "Kaman me jiran wahayi haka na kasa kunne Ina jiran motsin Baby hannuna na kan cikinta Amma Dan rainin hankali yaqI motsawa,har na haqura zan kwanta Kawai Naji alamun motsi na zare ido "Anty Wlh da gaske anaji,Lah ya qara motsawa,kai aunty Bakyajin zafi?" "Idan ma inaji AI saidai na gode Allah lafiya kesa ya motsa,yanzu Dai kwanta saboda makaranta Nima kwanciya zanyi" Saida na qaro mata pillow kusan a Zaune tayi baccin ta bani tausayi iyaye na shan wuya sosai akanmu Ba Dan naso ba haka na fita da sassafe na bar antyna a gida Tun 10 muka fito daga test muka kama wuri muka zauna ni da Nabila,domin Bana jin Ina cin abincin kirki tun farkon jin labarinta burina ta Gama Kawai "Na hanaki sukuni da abinda na fad`a Miki ko Hafsa?nikuwa tunda na fad`a Naji wani nauyi ya sauka daga qirjina kaman nauyin wannan Abin da na `boye Yana hanani numfashi" "Ai haka magana take nidai na qage Naji qarashen labarinki" _cigaban labarin Nabila_ Tana bud`ar bakinta Sai tace dani "Nabila kin kawo girman da d`awainiyarki tayimin yawa,kina gani Dai ba aiki nakeba kame kame ne da dabaru Dan haka dole Ki tsaya da qafafuwanki Ki ne!awa kanki mafita,abinda ya faru dake ba Wai zalinci bane wannan shine budewar qofar rayuwar da zaki Shiga, Ke macece me tsada Allah ya baki jiki mai kyau na tabbatar zakiyk Arziqi da wannan surar taki,daga yanzu Ki Sani na Sama Miki sana`a kuma baki ISA kice a`a ba ko kimin musu,wannan kyan naki bazai tafI a banza ba, "Ke tamkar haja kike a kasuwa Wanda yafi Bada kud`I shi zai d`auka,zaki fara biyama mazaje buqatarsu akan kud`ad`e masu yawa da alkhairaI,kuma......" "Ummama bansan inda maganarki ta dosa ba,Dama da saninki akamin fyad`e?ummama jikina zan dinga saidawa maza akan kud`i?bazan iyaba ummama ko talla ne Ki bani Amma bazanyI karuwanci ba Allah bai haliccsni Dan na baiwa maza jikina ba,yayi ni Dan na bauta masa na kima Kare mutuncina ummama ke zaki bani shawarar na fara karuwanci?" Mari biyu ta saukemin tace"ke ni har zaki gayawa Allah,duk abubuwan da nakeyi Miki kin d`auka a banza ne?to Wallahi tallahi abinda nace zakiyi Sai kinyi baki ISA kimin taurin kai ba,wani irin gata ne ban Miki ba?kina sahun farko na Yan matan unguwannan masu sanya kayan ado da na alfarma kowa nunaki yake ana fad`ar tsadar kayan da kike sawa a banza zanyi Miki wannan?a banza nayi kiwonki kika zama Cikakkiyar mace da zakimin musu?to abinda na fad`a ba gudu babu ja da baya dole kiyi idan bazaki iyaba ga hanya nan Ki fice Ki barmin gidana Amma kafin Ki fita saikin biyani duk wani sule da na kashe miki mutuniyar banza mai baqin ciki ana nuna Miki arziqi kina qunshe kai kud`ine Sai kin NEMA Wallahi ko ta Yaya ne" Anan ta wuce ta barnI Ina sharar kukana har na gaji na nufi d`aki, bata tankamin ba Sai safiyar Monday tayimin kashedi mai tsayi ta kuma sanar dani Tana da ido a kaina Sati biyu Babu abnda ya faru saida na cika satI biyu wani matashin saurayi yazo ya sayeni, nasha wahala wurinsa Hafsa,ya ganamin azaba,kwanana uku a wurinsa,Yana sakina na gudu na d`au hanyar da ban Sani ba tafiya nake Ina hutawa har dare Irin abinda nake gani a fina finai shi nayj tsammanin zai faru dani,wani Dan arziqin ya tsaya a mota ya daukeni ya kaini gidansa matarsa ta riqenI,saidai mutumin da ya fara d`aukata bai taimaka min ba Sai ma amfani da yayi dani ya bani kud`in mota yace na koma gida Ina komawa ummama ko ta kaina batai ba ta Shiga harkarta,saidai na lira cewa duk abinda zai faru dani a gidan ummama ba kaman abinda zai faru dani a titi ba,ko ba komai inada wurin fakewa a matsayim gida Bayan wannan guduwar sau uku Ina yunqurin guduwa Amma Abu d`Aya ke faruwa dani,za`a d`aukeni wani lokacin ma ta qarfi ayi amfani dani a bani kud`i Daga nan na saduda nasan qaddarata Kenan na zama sex toy wadda kowane qazami zai fuskanta idan yanada buqata,Amma daga baya na gano ummama CE ke turawa ayimin hakan domin ta fad`amin da bakinta matuqar zan guje mata to zan hadu da masifar da Sai na dawo,ko Ina tanada ido a kaina Daga lokacin na saduda,tun Ina kolawa da qoqarin qwatar kaina idan za`a cutar dani har na haqura,tun Ina kuka idan ana s*x dani har na dena rabona da zubada hawaye Sama da shekara biyu Sai ranar da kika taimakamin Bazan iya qiyasin mutanen da suka kwanta dani ba domin da wuya naga fuskar mutum sau biyu,tun ana amfani dani barkatai har ta kafa dokar sau hud`u za`azo wurina a Sati,akwai lokacin da na samu ciki ta zubar,nasha wuya har likita yace na kula mahaifata batada qwari idan na qara shan magani dam zubar da ciki zan iya dena haihuwa gaba d`aya Daga lokacin ta koyamin amfani da protection equipments, sannan wasu lokutan anamin wasu allurai karatuna ya fara tabuwa Dama ba qqari ne dani ba haka yasa ta canzamin makaranfa har sau biyu Kullim cikin qyanqyamin kaina nake saboda Hakane nake nisanta kaina da mutane gani nake tamkar kowa ya kalleni ya gane,na samu kyaututtuka da Dama a wannan qazantacciyar hanyar Waya sabuwar yayi na shigowa zan riqeta,inada system,duk daga mazajen dake zuwa wurina,d`akina bazakice a gidanmu yake ba,fridge d`Ina shaqe yake da kayan zaqi...... [12/11, 12:29] Maryam?: *MUNAYA* , Maryam? Wattpad@mamsuhaimerh 08 Kud`i ba abinda ya fishi sauqi a gareni,account d`ina inada Sama da 200,000 bayan kud`ad`En da nake samu a hannuna Wanda nake amfani dasu,Hafsa Ina sanya sutura mai tsada mayika da turarrurruka na duk masu tsada ne kuma ban taba fidda kud`I na Saya ba,gadona kansa kyauta na samu a wannan qazantacciyar sana`a karatuna kamfanin da suka kad`e iyayena su suke d`aukan nauyina,haka lokaci lokaci zasu zo duba lafiyata su kawomin akhairi nayi qoqarin sanar dasu banida matsalar komai na rayuwa Amma sunce dokarsu Kenan Duk wad`annan abubuwa da nake samu Bana iya amfani dasu a kwanciyar hankali,Bana iya cin Abin ci, na marmari ko zaqi,na tsani nama qyanqyaminsa nake,idan na sanya sutura ko nayi amfani da kayan shafawa Sai Naji tamkar na aminta na miqa kaina ga wannan qazantacciyar sana`a Maganar fatar baki Sama da shekara biyu Bata had`ani da ummama,maganar da nayi da ita ta qarshe na nuna banason abnda take sakani saboda Ina shan wahala sosai a shekaruna wasu Suna fansar kud`in da suka kashe ne a kaina ta hanyar maidani tamkar dabba Amsamin tayi da to ta kuma CE ta yanke alaqa dani,nayi zaton wasa ne saida rana tayi ta hanani abinci,ta hanani wanka da canza sutura,ta hanani Kwana a d`akinta da dare,washegari ma haka ta hanani abinci Shiga d`aki da sanya sutura,da wanka A rana ta uku na Gama galabaita da yunwa ga daud`a ko makaranta banje ba,da sassafe period yazomin na roqeta ta barni na canza kayana na gyara jikina ko kallona batayi ba,Ina ciwon mara mai tsanani a lokacin haka na dinga juyi a tsakar gida na kuma yi rashin sa`a yazo da yawa Kafin 11 na safe duk na `baci da jini dole na roqeta tayi haquri na amince da duk abnda takeso nayi ko menene,a take ta haqura ta had`amin ruwan zafi ta bani magani ta gyaramin gado kayan da nayi staining da kanta ta wanke daga nan ta fad`amin illar yi mata taurin kai Ban qara mata taurin kai ba tsakanina da ita eh,a`a,to,da sauransu,daga baya na gano sana`arta dukda zargi nake Amma akwai alamun Tura Yaya mata qasashen waje,kinji rayuwar da na tsinci kaina" *MUNAYA* Kallon Nabila nake baki bud`e idanuwana kuwa zasu iya ta`bo kaina tsabar wangalesu danayi,ta Gama Bada wannan mummunan labarin Amma idonta ko d`igon hawaye babu?Wai kun ma fahimCI me nake nufi? Nabila batayi kuka ba Ta Gama Bada labarin Rayuwarta batayi kuka ba Labarin ba mai dadi ba Amma batayi kuka ba Jama`a da gaske Bata kuka Nabila Bata kuka ```Nabila Bata kuka``` *Nabila Bata kuka* JAMA`A NABILA BATA KUKA..... "lafiya kike kallona haka Hafsa kina bani tsoro fa" "Dan mintsineni Naji ko mafarki nayi?" Babu musu ta gantsaramin mintsini saida nayi ihu,na "Wannan AI mugunta ce"na fad`a Ina Sosa hannun" "Umarni nabi ai"ta fad`a Tana murmushi "But seriously Nabila bakida lafiya,Tabbas akwai matsala tare dake,Ki Gama fad`ar abinda kikai shekara uku kina boyewa Amma idonki Babu qwalla?" "Hafsa zuciyata ta Gama bushewa,karki manta mutum 5 sun mutu a gabana,Anyi amfani dani lokutan da bazan iya qirgawa ba,a cikin gida,d`akina kuma kan gadona,banida Wanda zanje gareshi ba,babu Wanda nake yiwa magana na njsanta kaina da kowa Kalaman da nakeji na yaudara ne wad`Anda suke nuna irin rashin sa`ar da nayi a rayuwata, jikina zan iya CE Miki babu zuciya,domin amfaninta aika jini ga sassan jikina Amma banida expression A baya duk lokacin da wani ya daukeni ko ya ziyarceni nakan ji wani Abu a zuciyata tamkar yanamin haqa,a yanzi ramin dake haquWa a zuciyata yayi girman da Bana jinsa Bana tunanin cikeshi domin ta gama bushewa" Hawaye na share daga fuskata nace"ya kike kallon mutane" "Ina Kishi akam duk wata mace musamman Irinku da kuka fini sa`ar rayuwa,Ina da mummunar tsana kan mazaje,Ina tsorom mutane kuma Ina jin haushin kowa,duk Wanda yayi qoqarin shaquwa dani Ina saurin tureshi macece ko namiji" "Nabila kina buqatar taimako,bakida lafiya kuma dolene na sanarwa da mummy, kiyi haquri Ki fahimta,kina buqatar taimako ko ba na abinda kikeji ba,na halin da kike ciki bazai yiwu Ki zauna Ki qarar da rayuwarki a haka ba,mutum CE ke ba dabba ba kuma mace,kinada burika a rayuwa" Da sauri ta riqo hannuna tace"Hafsa Dan Allah karki fad`a zaki janyo min matsala" "Amma Nabila...." "Na roqeki Hafsa,Dan girman Allah ya tsaya ni dake akwai abnda nake shiryawa kaina zan sanar miki Amma banaso Ki fad`ama kowa" "Zanyi qoqari amma banyj alqawari ba,Yauwa kikace akwai kayan dad`i a fridge d`inki ko?" "Sosai,wasu har sunyi expire nayi qoqarin Bada su Sai naga kaman zan baiwa yara Haram Kawai na Barsu kayan Haram AI kyawunsu lalacewa" "Ni zansha Haram d`in Kinsan tsadar chocolates kuwa?Dan haka ni Ki kawomin ba ruwana da Haram d`in shan abuna zanyi" "Kema fa akwai kwad`ayi idan kina cycle d`innan Gobe zan kawo Miki masu kyan ciki kisan yanda zakiyi dasu" "Kai amma fa I love u so much ni fa zan iya auren mutum indai zai bani sadakin chocolate" Dariya tayi sosai tace"kice zaki aureni idan na baki chocolate" "Auren zobe ma kuwa babu Saki babu yaji" Dariya mukayi dukkanmu na goge hawayena muka bar wurin Tunda mummy ta d'aukeni take qaremin kallo tuni na fara tsarguwa na kasa zama "Me ya saka Ki kuka" Tambayar tazomin ba zata,cikin rawar murya nace mata"a'a....ni.....ni ba kuka Nai ba....Kawai....Uhmm.....kaina ke ciwo Amma banyu kuka ba" "Munaya meyasa kika fara 'boyemin abubuwa?meyasa kikemin qarya ko kin samu wadda ta fini ne?MUNAYA na damu dake sosai Amma na lura kin fara canzamin,so kike na maida idona kanki?" Wayyo mummyna ta kamani hannu dumu dumu,Bana iya yima mummy qarya Ina kallonta zan fara rawar murya,Amma maganarta ta dakeni jikina yayi sanyi,sunkuyar da kai nayi Ina wasa da hannuna tace "Bazaki fad'amin ba Kenan,Hafsa ko tamtama kikeyi akan kulawar da nake dake ne?akwai abinda nake Miki bakyaso?ko a school ne ake Miki wani abu" "Mummy babu abinda akemin babu abinda kikaimin kiyi haquri da kaina zan fad'a miki Amma Dan Allah Ki dena magana idan kika takurani zanyi ba daidao ba" "Bazan qara wannan gangancin ba,rashin takurakin da nayi a baya ya janyo Maki rashin lafiya,Dan haka ko Ki fad'a ko mu wuce asbiti yanzunnan,inda za'a sanyaki Ki fad'a dole" "Mummy Dan Allah...." "Hafsa karki qara had'ani da Allah Ki fad'amin meke damunki" Fashewa nayi da kuka Dan mummy Bata Kiran sunana Sai Tana nufin Abu serious, haka kuma ranta ya 'baci saidai bazan iya fad'a mata ba banida za'bi ne Ganin ta d'auki hanyar asbiti yasa na dawo hayyacina,idan mukaje asbiti wani Abu sukemin da nake fad'ar komai ban saniba "Dan Allah mum kar muje Wallahi zan fad'a miki da kaina Dan Allah mummy" Qin tsayawa tayi har saida tayi parking a harabar asbitin tace na fito "Mummy zan fad'a Dan Allah muje gida" "Fad'amin anan ko na Shiga dake ciki Wallahi" Rungumota nayi na qara tsananta kukana,tasan illar da kuka yakemin dole ta haqura muka juya Bayan doguwar magiya da alqawari da nayi mata Muna komawa gida Bata bi ta kaina ba ta fad'a aikinta itama Anty suwaiba ta

Chapter 4 of 8