jikina Yana karkarwa mummy ta damu sosai hakan yasa nace
"Doctor tsoro ne Kawai Amma nasan da na huta zan dena ko?"kai ya gyad'a yayimin umarni na kwanta kan gadon duba marasa lafiya yayimin allura ya jona min wasu abubuwa a hannuna da gefen kaina,cikin minti biyar Naji bacci na d'ibana cikin baccin Naji maganar doctor Yana cewa mummy
"Zatayi bacci ne na kusan awa gomahar yanzu zuciyarta Nada rauni shiyasa ta kasa controlling tsoron da takeji,baccin zaisa kwakwalwarta ta huta zata dena jin tsoron idan ta farka insha Allah Amma ba wata matsala yanda kike gani gashi heart rate d'inta Yana gudu sosai Amma zai fara sauka yayin da take bacci,zanyi mata allura idan yai stable daga nan Tana farkawa Sai kuje gida ga wannan......"ban qarasa ji ba bacci y kwasheni.
Farkawa nayi na sameni a d'akin asbiti mommy na kan kujera Tana bacci,agogo na duba naga biyu na dare,ya salam Banyi sallar magriba ba da sauri na tashi nayi sallar magriba da Isha nayi nafila raka'a hudu na koma na kwanta,Naji dad'in jikina sosai domin na saba na tashi kaina yayimin nauyi Amma yanzu babu,kwanciya nayi Ina tunanin school har bacci ya qara d'ibana
"Munaya tashi kiyi sallah"mummy ta tasheni,murmushi nayi mata nace "kin Kwana lafiya mummy?"
"Lafiya Lau na Kwana da tunaninki dai"
"Na Saki damuwa ko?"
Bata amsamin ba tace"kiyi sallah mu tafi da wuri saboda school"
* * *
7:30 Ina school Amma fa nasha wahala Dan mummy ta azalzaleni,Bayan assembly muka wuce class Ina tafiya Ina tunani Naji anyimin sallama,Juyawa nayi da murmushi na amsa ganin Nabila na miqa mata hannu muka gaisa
Ba Wanda ya qara magana har muka ISA class muka zauna na d'auko jakata na ciro littafinta na miqa mata
"Ban samu damar qarasa kwafa ba Banjin dad'I YAU zan qarasa"
Murmushi Kawai tayi ta kar'ba a haka period uku suka wuce ta hud'u na shigowa na sauke ajiyar zuciya,na gaji banda ma anan school d'in Wa yake had'a physics da maths da english a farko?gashi yau nasha tea duk jikina ya mutu Sai bin table nakeyi
"Sisters Dan Allah me two pen??"wata ta fad'a daga seat d'in gefenmu ta 'bangaren Nabila,miqawa Nabila nayi ta miqa mata Nabila na tashi na janyota da sauri ta zauna,kallona tayi cikin mamaki nace
"Karki tashi sister kinyi staining kayanki"
Kiran waccan nayi Dan na lura class d'innan kowa sister CE Dan haka sunan kad'an na Sani,cikin sauri Nabila ke bincika Jakarta saida ta zazzage tas ta aje jakar ta sunkuya kan table,nasan me take dubawa kuma nasan Nima banida,domin Kwana 5 da Gama period d'Ina bansan me zanyi da pad ba shiyasa ma ban d'auko ba,gaba d'Aya kunya takaici da baqin ciki sun had'ar ma Nabila ta tashi hankalinta sosai nace
"Bari na tambayar Miki Hafsa"
Gyad'a kai tayi,mata fa munashan wuya Allah Dai ya saka ma iyayenmu,ta'bo Hafsa nayi nace"sister kinada pad pls?"
Bud'e Jakarta tayi ta miqomin Nikam da na kalli Nabila ta bani tsoro domin ta canza gaba d'Aya pencil take riqe dashi ya rabe biyu ranta a 'bace saidai na fahimci duk a cikin wannan yanayi ne dafata nayu nace
"Kwantar da hankalinki sister na samo Miki kar wani ya ganki yace laifi na Miki"
"Ban damu da Wanda ze ganni ba bakya gani ne ta Yaya zan fita!!!?"
Hannu NASA na rufe mata baki domin kusan kowa ya kallo inda muke na riqe hannunta da ta damqe gam nace "zan samo Mana hanyar fita"
"Ta Yaya?"ta fad'a Tana kallon qasa,"wasu lokutan na tsani kasancewata mace domin zama na a mace baida amfani Sam,daga wannan masifa Sai wannan I am really embarrassed of my self(Naji matuqar kunya)"
Da sauri ta rufe bakinta domin ita kanta batasan ta furta haka ba,menene dalilinta menene bala'in da take furtawa kanta haka,bud'e baki nayi zan mata magana.....
Kuyi haquri da mistakes ban samu nayi editing ba Ina Fatan kunji dadin wannan chapter Ku fadamin abnda kuke tunanin kan littafina
[12/7, 00:52] Maryam?: *MUNAYA*
Maryam?
Wattpad @mamsuhaimerh
03
Da sauri ta rufe bakinta domin ita kanta batasan ta furta hakan ba,menene dalilinta menene bala`in da take furtawa kanta?bud`e baki nayi zanyi mata magana Amma nayi shiru Dan naga babu amfani,shawara ce ta fad`omin na nemi excuse na nufi wajen headmistress
Bayani nayi mata ta banI spare Hijab cikin uniforms d`in da ake ajewa na qudunduno na dawo na baiwa Nabila,kar`ba tayi ta saka kasancewar babba ne ya rufe stain d`in rigarta
Tana fita na zauna Ina tunani,Nabila Tana bani tsoro Tana bani mamaki,a Kwana biyunnan da nayi da ita na lura da abubuwa da yawa,Bata magana idan ta sunkuyar da kanta ta fara Zane ko wasa da pencil har Sai teacher ya shigo,haka idan ta sunkuya Tana tunani Sai kiyi magana Goma bataji ba,dukda class d`inmu 32 students ne Amma idan ana surutu Sai kaina yayi ciwo ita kuwa Sam kaman bataji,ga idonta kullum tamkar Bata bacci,idonta ya mutu babu haske cikinsa,tamkar idona a lokacin da nake cikin depression, na lura da safennan le`benta ya kumbura kaman ta bige,yanda take tafiya daban ne,mu`amalarta daban CE.........meyasa nake wannan tunani ne?ya Allah Nima Naji da kaina Mana
"Can you explain to us what dessert means"da sauri na d`ago naga teacher na kallona da alama dani take,nema nayi ta maimaita tambayar ta maimaita sannan na amsa mata
"It is the snacks or beverage taken at the end of a meal like cakes,ice creams and others"
Yatsine fuska tayi ta juya Hafsa ta juyo ta kalleni"kinci sa`a da ta wulaqantaki yanzu gara Ki maida hankali kafin ta fita"Tana Gama maganar ta juya Nima naci gaba da note
"Nagode sosai"ta fad`a lokacin da ta zauna,kai Kawai na gyad`a domin na lura na fara sa kaina a abinda ba ruwana,bamu qara magana ba har lokacin break Bana Sha`awar cin komai haka nayita binsu a baya Muna tafiya,Bayan sun sayi abinci na tafi toilet Dan nayi fitsari,matsalar lokacin break mutane sun cika toilet din haka na haqura na juyo,banaso na koma na zauna sunacin abinci Ina kallonsu Kawai na fara zagaya makarantar,na tsaya na sayi bounty naci gaba da kewayena a haka har nazo wani wuri da babu mutane ga hantsi,ko da na matsa Dan na zauna qasan bishiya Kawai na hango Nabila can gefe ta had`a kanta da bango ta had`e qafafunta,matsawa kusa da ita nayi na lura da hawaye a fuskarta
Tsayawa nayi Ina kallonta na lura Sam batasan da tsayuwata ba Kawai na zauna gefenta na fara maganata ko taji ko bataji ba Nima Ina buqatar hakan
"Duk lokacin da na zubda hawayena nakanji sanyi a Raina yayin da nake zubar da hawayen kuma nakanji zafi cikin Raina,rayuwa Tana buqatar hutu da kwanciyar hankali da kuma tawakkali,Ki Sani duk abinda zai Saki kuka to bai cancanci Ki zubar masa da hawaye ba,idan har zaki janyo damuwarki Ki taho da ita makaranta to kin d`auko hanyar wargaza future d`inki haka idan zaki dinga buya kina zubar da hawaye ba tareda kin furta abinda ke ranki ba,to zaki mutu da damuwa silar damuwar taki kima basuda asara"
Maimakon tayi shiru Sai ta qara fashewa da kuka Abin mamaki Kawai Naji ta bud`e baki ta faramin magana
"Meyasa rayuwa Bata yiwa wasu adalci,meyasa haka ke faruwa dani?na rasa amfanin rayuwata ana cewa rayuwa duk d`acinta tafi mutuwa dad`I Nikam da zan mutu da Nafi kowa godiya ga Allah,na gaji da rayuwa na gaji"
Hannunta na riqe nace"ba`a yiwa rayuwa tambaya domin Allah shi yake sane da duk halin da kike ciki,ba Dan baya sonmu yake jarrabarmu ba,tsabar Yana sonmu fiye da wasu daga cikin bayinsa yasa yake jarrabarmu Dan ya gwada imaninmu ya bamu mafificin Lada,idan kina yiwa rayuwarki wannan kallo to bazakici ribar komai ba Amma Ki dinga tunawa Allah na Sama Yana kallonki Yana sane dake kuma so yake Ki masa godiya ki jure kisani Allah Yana tare damu duk wuya duk dad`i
Kallona tayi cikin sauri da mamaki Kawai ta fizge hannunta ta goge fuskarta ta tashi ta barni a wurin
* * *
Sati uku Kenan babu abinda ya qara had`ani da Nabila banda gaisuwa,tamkar `buya take daga gareni Nima na Bata space d`in da take buqata saidai na matsu Naji damuwarta
Yau Friday Muna hanya mummy ke fad`amin zatayi tafiya sunada case a magistrate court Abuja zataje YAU Monday ta dawo,kaman zanyi kuka duk yanda nayi ta d`aukeni muje tare taqi cewa take ta barmin surprise a gida a nan mukai sallama ta wuce
School ba dad`I inata tunanin zanyi weekend babu mummy inata saqa gidan da zani na zauna lokaci da gudu ya wuce,Ina zuwa gida na bud`e shiru babu kowa na rufe na jingina jikin qofar parlour Ina takaici,dad`Ina d`aya qaramin gidane parlour da d`akuna uku da kitchen da toilet a kowane d`Aki Sai wurin parking d`in mota d`Aya,leda na gani kan kujera na bud`e naga snacks da lemu da paper an rubuta"dont miss this my baby"
Daki na nufa na Shiga na rufo Kawai naga qafafuwa na motsi a kan gado,numfashi naja na fara qoqarin fita Ina bud`e qofar Naji ance "Ina zaki je?dawo nan"
Ban waiwaya ba na ranta a na Kare kafin naje gate an cafkoni,a tsorace na juyo cikin sauri na sauke ajiyar zuciya
"Nuriyya kin tsorata ni sosai Wlh"
Rungumeta nayi nace"nayi kewarku Ina su ruqayya"
"Suna ciki,ba wani missing na tabbatar ko tunaninmu bakyayi munaya banda munkai zuciya nesa ba abinda zamuzo muyi Kawai kinci darajar mummy Wlh kuma mun d`an yi Miki uzuri Amma ya zaki mant a damu ba waya ba komai......"nidai Jana take kaman wata Kaya Tana zuba Uwar Mita Muna Shiga ruqayya da Jamila Suna parlour wani kallo suka wurga min kunya ta kamani,Tabbas ban kyauta musu ba rabona dasu tun sallah qarama Ina tsaye Kawai Naji sunyi tsalle kaina na fad`I gaba d`aya muka d`au dariya
"Guys Kuyi haquri Dan Allah nasan nayi muku laifi Amma bazan kuma ba kunji"
Maimakon su haqura Sai suka rufeni da duka Ina ganin En matana fa sunada matsala,da qyar na ceci kaina na shige d`Aki da gudu,da gudu suka biyoni Sai kuma suka tsaya
"Duk lokcinnda kikai Sati baki nememu ba to haka zamuyi Miki"inji Jamila
"Wlh kin `batamin rai da ko magana banaso nayi Miki"inji ruqayya
"Ya isa yanzu Dai shirya musan me zamuyi"
Zama sukai Suna danna waya na cire uniform na saka Riga nayi sallah na Shiga wanka,fitowa nayI da towel Ina cewa
"Me kuka shirya Mana.......WHAT!!!MENENE HAKAN!!!"kayana na gani sun baje a tsakar d`Aki na roqe qugu Ina kallonsu
"Bakya gani ne?gyara mukeyi Mana,Wai me kika zama ne eh?Kaya yanda aka kawo daga dry cleaning haka kika ajesu,Ki duba Wai wannan underwear kike sakawa Wai ke me kika zama ne munaya?"ruqayya ta fad`I kaman zata rufeni da duka
Wani kallo sukemin nace"Dan Allah Ku bari banaso kunamin wannan kallon ni Banga laifin kayana ba,haka nakeson abuna"
"Ki shirya zamu fita yanzu,lingerie shopping"
"Ba inda zani bazan manta last fitarmu ba haka Jamila ta bani kunya ta dinga d`auko bra Tana karamin jikina wani qato na tsaue Yana qaremin kallo,ban komawa kudai kuje"
"Wallahi Sai kinje an Gama magana"
Rabuwa nayi dasu sun fara isata Nikam ba inda zan je ina gida,Hijab na d`auko na saka na sanya underwear na cire hijabin Ina shafa mai,Kawai Naji an fizge towel d`in
"Me zaki `boye Mana tun kina qwailarki kike shiryawa gabanmu Sai yau zaki wani maqale towel
Dariya Kawai nayi na juya musu baya na Gama shafa maina na d`auko Kaya zan saka
"Kisa Wanda zakifi sakewa Dan zamu dad`e
Doguwar Riga na saka ba yanda zanyi sunja ra`ayina dole na bisu
Account d`Ina na duba na samu 32000,Ina na samu wannan kud`i?oh ashe fa tsoho yana turomin kud`I qarshen wata nayi alqawarin bazanci kud`insa ba Amman dole wad`Annan jarababbun zasu sa na ta`ba
A hanya muka tsaya gidajensu duk suka kar`bo kud`I sannan muka wuce,ya Allah nasan yau Sai sunyimin mugunta,
Muna zuwa 'bangaren lingerie a cikin store d'in nidai na fara ja baya Dan nasan Hali,saidai fa abinda na shirya sun fini shiri Dan munja 'Yan kallo saboda dariya,haka muka dinga kara underwear Muna hotuna Muna tsokanar juna,Bayan mun Gama na biya kud'in Jamila ta nemi musha ice cream haka muka biya ice cream parlour,Wayyo Kano tayi Allah Dai ya qarawa annabi Daraja tunda na fara shan cookies and cream ice cream Naji na bar Nigeria na koma wata Duniya daban,lumshe ido nake Ina uhmmmm Kawai Suna min dariya,daga nan muka biya muka sayi kayan cake da lemu mundai kashe kud'ad'e Amma na samu walwala da farin cikin da na jima ban sameshi ba,Sai Bayan magriba muka koma sallah mukai muka d'auko katifu biyu da filallika muka shinfid'e a parlour qyuya ta hanamu girki Sai cocopops muka Sha ana sallar Isha muka fara kallo Bayan mun sanya sabbin kayan baccin da muka siyo iri d'aya
Cartoon muka fara kallo 'FROZEN'Sai naga tamkar a kaina labarin yake,idan kana gujewa tsoronka Sai yayita binka duk inda kake ka kasa controlling d'insa Amma idan ka fuskanci tsoronka Sai kaga yafi komai sauqi
Bayan nasha maganin baccina mun d'an qara hira 9 muka kwanta bacci,wannan juma'a na d'Aya daga ranakun da zan nemi Allah ya maimaitamin su nayi bacci cikin farin ciki ko Sau d'Aya ban farka ba har asuba
Munayin sallah muka koma bacci Sai 9 muka had`a breakfast plantain zalla da Kwai 8,mukayI scrambling d`insa yasha attaruhu tumatir da sweet pepper,12 muka had`a cup cake Dama ance hannu da yawa......yayi dad`i sosai sannan muka wuni Muna hira cikin hirar aka sako wajen da kemin qaiqaiy
"Ke kuwa munaya Ina ganin abinda kikewa Abbanki bakya kyautawa,lokacin da abbana Yana Raye ba irin kyautata masa da banayi Yana Sona Yana fifitani kan `Yan uwana Amma da ya rasu saida nayi nadamar wasu qananan laifuka da nayi masa Wanda basu taka kara sun karya ba Amma inajin rashin dad`I tun Yana Raye Ki gyara mu`amalarku kafin kizo kina Dana Sani"ruqayya ta fad`a Tana kallona
"Ruqayya bakisan me mutuminnan yayi bane,nayi niyyar haqura na yafe masa Amma bazan iya ba,inama ba shine mahaifina ba Dan Ina kunyar kiransa uba Dan babu uban kirki da zaiyiwa `yarsa haka har ya fifita......"
Kasa qarasawa nayi Dan banaso na zubda hawaye ga mutumin da bai d`au iyalinsa da Daraja ba
"Ko me yayi bakida iKon furta haka a kansa har yanzu a mahaifi yake a wajenki ko me yayi kina buqatar albarkarsa zunubi kike d`auka idan kina furta haka kuma Allah Sai ya tambayeki"Jamila ta fad`a
Ita Nuriyya Bata fiye magana ba Amma idan ta bud`e baki Sai jikin kowa yayi sanyi nayi zaton zata fara min dogon Wa`azi Kawai murmushi tayi tace"gaba ake hange ba baya ba,kinje ganin Yaya kuwa?"
"Yaya rabona dashi Nafi shekara tunda aka kamasu suka Gama horo aka kaisu wannan training ko muryarsa ban qara ji ba mummy tace shugabannin nasu ne suka nemI a rabu dasu su dogara da kansu nayi missing d`insa sosai bansan yaishe zai dawoba"
Anan muka dire hirar muka fad`a wata,Sunday kuwa haka suka maida gidannan filin biki suka qure waqa sunata rawa,daga baya Dai na Shiga na tayasu wannan weekend shine na farko Dana samu Bayan shekara guda,nayi dariya da ta taho tun daga zuciyata,na ajiye duk wani tunani na wuni guda,nayi `barna na koma MUNAYA ta da wadda take da qiriniya,surutu,wadda Bata jure kid`a Sai ta taka mai barkwanci,inama zan kasance a haka
[12/9, 00:57] Maryam?: *MUNAYA*
Maryam?
Wattpad@mamsuhaimerh
04
"Tashi malama 7 fa tayi"
"Mtsew Ku qyaleni Dan Allah me zanyi da safennan?"
"Ke yau fa Monday"
Firgigit na tashi na nufi toilet da gudu saida nayi wanka na fito Kawai na Tina Munada maths quiz yau
"Wayyo Allah na I hate you guys saboda Ku Gashinan ba abinda na karanta yau zamuyi quiz second period"
"We love you too baby,Gashinan har munyi Miki breakfast sannan karki damu Dan kin fad`i quiz Dai AI ba test bace"
"Bazanci komai ba ni na tafi bye I love u"na Tura musu flying kiss suka kama na fita da sauri
Sai cin biro nake Ina Fama da paper ta a gabana na rasa ta inda zan fara,hmm zama ma da irin su hadiyya ganganci ne a wannan lokacin,paper na gani a gabana na d`aga kai naga Wanda ya ajiyemin ya nufi wajen submitting Kawai ya kashe ido d`aya, babu wani tunani na kwafe tas nayi submitting
"Ya Allah da wannan bai taimakamin ba da bansan yanda zanyi ba"
"Aikina ne wannan karkiji komai `Yan mata"ya fad`a ya bar wurin,ban San ma Yana tsaye ba, murmushi nayi nayi masa godiya na sunkuya Dan kaina ya fara ciwo,fita teacher d`in yayi ya barmu mu huta Hafsa ta juyo tace "Yaya ne?"
"Hmm Allah ne Kawai ya ceceni Kinsan ko kallon jakata Banyi ba a weekend saboda cousins d`Ina uku sunzo,ba Dan wancan yayimin sneaking paper ba da zero zan ci"
Hira mukai Sama Sama ta juya taci gaba da harkarta,kasancewar Nabila nasan ba kulani zatayi ba na janyo littafina na fara karatu
"Uhmm Hafsa"
Juyowa nayi naga Nabila ke magana nace mata"ni hafsan ko ta gaba?"
"A`a ke,amm...Dama akan maganar da kika fad`amin ne kwanakin baya.....Uhmm nagode kuma na duba naga Gaskiya kika fad`amin"
"Babu komai,Allah ya taimakemu baki Daya"
Yunwa nakeji sosai lokacin break,Ina bud`e zip d`in baya na jakata na tarar da leda da cake d`in da mukai baking,Amma fa yarannan sun kyautamin,d`aukan abincina nayi da novel na nufi wajen da na tarar da Nabila kwanaki,kusan wajen ya zama wurin zamana indai Bana tare da Hafsa,saidai qawayenta na min abinda Banjin dad`i
Yau ma Tana Zaune saidai ba kuka take ba wasa take da qasa kasancewar yanayi na damina wurin da d`an danshi saidai rana ta fito,zama nayi gefenta ta d`ago tayimin murmushi na bud`e abincina nace
"To ga ruwa wanke hannunki kici abinci"
"Na qoshi"
"Wallahi Sai kinci tunda na rantse Ki taimaka kici"
Hannu Tana tanaci kaman ana Tura mata na takurata saida muka cinye tare,Bayan mun wanke hannu na bud`e novel d`Ina na fara karantawa
"Ranar da nayi Miki magana Sai Naji kaman na sauke wani nauyi daga kaina dukda cewar banso kikaji hakan ta fito daga bakina ba Amma Nagode"
"Ai Nabila barin magana a ciki batada dad`i,ta dalilin ajiye maganganu a Raina saida nayi wata takwas cikin ciwo,na tsani kowa na tsani kaina na zama Abin tsoro na zama abar Qin yarda,inaji Ina gani aka sanar ma mahaifiyata kar a bari na kasance ni kad`AI a wuri zan iya kashe kaina ko na illata kaina,motsi kad`an ido Yana kaina idan aka yimin allura Ina awanni 12_15 Bana hayyacina Ina bacci magunguna nasha har over dose Amma daga lokacin da na furtawa mahaifiyata duk abinda ke Raina na fara samun sauqi,Kema Ki fad`awa mahaifiyarki na tabbatar zata fahimceki ta baki shawara Ki samu sauqi"
"Hafsa,banida Uwa banida uba banida `Yan Uwa banida kowa"
"Ban ganeba,ke kad`ai ce kike rayuwa bakida kowa?"
"Hmm kusan ni kad`AI nake rayuwata domin wadda nake wurinta batada amfani a wurina Sai cutarwa,iyayena duk sun mutu shekara shida da suka wuce a lokacin Ina shekara Goma"
Tana Gama fad`ar haka break ya qare muka nufi class inata tunanin Nabila,to a hannun kishiyar Uwa take Kenan ta na gallaza mata Dama haka akeyi a iya sanina,to idan haka ne da ta fad`a to Wai ma meke damunta ne?menene matsalarta?haka nayita tunani har aka tashi
Muna nufar parking lot naga mummy da kanta tazo d`aukana,bansan sanda nayi tsalle na d`aneta ba Dan jikin mota take ba da duk mun fad`I ban damu da idanuwan dake kanmu ba na Qanqameta
"I miss you mummy"
"Kekam da yarinta kike Kwana uku fa Kawai nayi Shiga muje kowa kallonki yake"
Waiwaya wa nayi naga idon nabila kaina Tana kallonmu ta fad`a kogin tunani,hannu na d`aga mata itama ta d`agomin hannu,tausayinta Naji da na tuna batada iyaye na Shiga mota muka d`au hanya,surutu nake tayi mummy tayi shiru har Dai na gaji
"Mummy lafiya kikai shiru?"
"Lafiya Lau gajiya ce Kawai dawowata Kenan nazo d`aukanki"
Ban qara magana ba har mukaje gida da sauri na nufi parlour Dan na baje na huta Kawai idona yayimin tozali da abinda Bana Fatan qara gani,abinda na roqi Allah yayimin katanga dashi abinda na datse alaqata dashi,ba komai bane Sai Wanda ake kira da mahaifina Alhaji Abdullahi Nasir
Da sauri na nufi qofa Dan bazan iya kallon wannan fuskar ba,Ina Juyawa na tarar da mummy Tana tsaye bakin qofa
"Kije Dan ke yazo"
"Mummy ba abinda zanyi masa Ki qyaleni na fita"
"Ba shawara bace umarnine kafin ranki ya `baci Ki juya Ki zauna zaiyi Miki magana"
"Mummy....."
"Wallahi kika qara magana zaki fuskanci `bacin rai,koma Ki zauna!!"
Bansan sanda hawaye ya kwararomin ba,rabon da mummy tayimin tsawa har na manta,haka naja jiki na zauna can qarshen parlour na qudundune duk yanda naso na `boye hawayena na kasa haka na barsi suka yita kwarara munfi minti biyar sannan ya furta magana
"Ya kike?"
Shiru
"Ya karatu"
Shiru
"Bazaki yimin magana ba?"
Shiru
Haka yayita magana