Share this page
6 / 8
"Haba doctor kana tunanin zan iya kashe kaina ne?Wai meyasa babu mai fahimtata Nifa lafiya nake,Dan Allah kabar wannan maganar"na fad`a Ina goge hawayena Chocolate ya miqomin naqi kar`ba ya bud`e ya gutsuri kad`an ya miqomin"na miki alqawarin idan batai miki dad`i ba zan shanye abata" Kar`ba nayi NASA a baki na koma kafad`ar mummy na kwanta,Wai waiwai...wannan cakulet akwai dad`i, cikin sauri nace"a Ina ka siyota?ya sunanta?" "Takanas nasa aka taho miki da ita daga qasar waje abokina ya dawo nace ya siyo miki" Hannu na miqa na kar`ba tuni na manta kaina a duniyar cakuleti,haushin abinda ya fad`a ma ya fara raguwa Wato cakulet Nada wata baiwa da ni kad`ai zan iya sanar muku,zaqinta Yana kauda damuwa,haka idan na sanyata a bakina wani sanyi nakeji a Raina,Nutella da mummy ta siyo roba guda kwanaki zamuyi cake da ita ni na shanye Bana iya barin cakulet domin na zama addicted da ita,idan nayi Sati bansha cakulet ba to banajin dad`i cakulet abokiyar rayiwata Kenan "To dawo daga duniyar cakulet d`in haka"ya fad`a Yana tafa hannu Bud`e idon da na lumshe nayi nace"indai bazaka hanani shan cakulet ba ka fad`I duk abinda ya kamata nayi," "Kinashan pills d`inki ko?" "Ina sha,ya kusa qarewa ma" "Idan kikasha kina minti nawa bakiyi bacci ba?" "Farko idan na Sha Bana minti Goma,Amma yanzu Ina fin minti talatin Banyi bacci ba" Kallon mummy yayi yace"zamu had`ata da anti depressants,sannan zamuyi mata psychotherapy, ma`ana talking therapy,zamu ga abinda Hali yayi kafin kuma muyi tunanin had`ata da electroconvulsive theraphy" Ina jinsa sunata magana Nikam na bar musu ragamar rayuwata,bazanyi musu ba wannan maganin rayuwar da aka had`ani dashi ma ya isheni wahala,inaji mummy tace zata dinga min talking therapy Dan babu Wanda zan iya fiddawa damuwata kuma Gaskiya ta fad`a Bana tunanin Bayan ita babu Wanda zan fiddawa damuwata Kafin mu tafi ya qaramin wannan hadaddiyar cakuletin guda biyu Wayyo kaman na rungumoshi saboda dad`i ya bani shawarwari da wasu magunguna muka tafi "Baki sanar dani abinda ya faru ba da yasa kikai fainting"ta fad`a tareda qwace ledar cakulet d`Ina"idan kina wannan shan alawan zaki qarawa kanki wani ciwon,ko tsananin ciwon maran da kikeyi AI yasa Ki rage shan zaqi Amma bakya jin lafiyar kanki,wannan likitan bansan meyasa yake d`aure Miki g.....i wajen shan alawa ba" "Ai Yana Sona ne,Nifa wasu abubuwan Dan shi nakeyi,Yana da mutunci,Wlh Mummy banda doctor jafar ne likitana da anga taurin kai,Amma ya iya magana da lalla`ba da Kwantar da hankali,Uwa uba yasan qaunata da cakulet" "Ba wannan na tambayeki ba" "Abunda ya faru shine mahaifina,ya zama silar shigar mutum uku damuwa,ni,ke,da Nabila" "Wacece Nabila" "Wata CE qawata, tunda tazo Bata kula kowa tayita ware kanta da nayi kusa da ita ganin kusan damuwarmu Daya Sai take sanarmin cewa she`s sexually abused,wadda take wurinta Tana saidata ga masu kud`i Wanda a cikin mjtanen da aka saidata garesu mahaifina shi ya fara sayenta,shine ya......ya Allah mummy he took her virginity, nazo da ita gida Ku gaisa ta ganshi anan ta tabbatarmin shine,Ina Shiga gida naga Anty suwaiba na naquda stress ne ya sanyani na fad`i, "Maganganunku da Abba suka dinga dawomin kaina,abinda ya faru dani da kuma Abu mafi muni da na gani ga mahaifina ya dawomin, tamkar a lokacin komai yake faruwa Kawai Naji kaina yayimin nauyi" "Ita nabilan a Ina take?kuma tun yaushe take cikin wannan matsala?" "Tana nan kabuga,shekara uku Kenan tun Tana shekara Goma Sha uku" "Ya Allah wasu marasa imanin ne zasu qinga amfani da qaramar yarinya haka?ai ko a yanzu shekarunta basukai ta fuskanci irin wannan matsalar ba,zan kai matsalarnan qungiyarmu Muga abinda za`ayi" "Mummy tanajin tsoro fa,da qyar ta amince na fad`a miki domin idon Matar a kanta yake zata iya Shiga matsala idan Matar tasan wani yasani" "Matsala AI ta Gama shigarta,dole na taimaka mata domin Kema kin kusa fad`awa irin wannan matsalar bazakisan yanda mahaifiyarta zataji bane kan hakan" "Iyayenta sun rasu da duk Yan uwanta a hatsarin mota Wanda ita kad`ai ta rayu" Shiru mummy tayi Bata qara magana ba har mukaje gida,nan ta bani magunguna nasha na nufi d`akina,nayi mamakin nutuswata Bayan Sanin cutar dake damuna,tunanina hankalina zai tashi Amma jin bazan warke gaba Daya ba ya sanya hankalina kwanciya,gara Sanin ciwo da zama da rashin saninsa Bayan na sanya kayan bacci na sauko aunty suwaiba na Zaune Suna hira da Mummy, jaririnta mu`azzam na kar`ba inata kallonsa,Ina matuqar San yara lokacin da mummy ta haifi khairat a hannuna take wuni,Gashinan wannan mutumin sanadinsa ta rasu Kuka ya fara na tashi Ina jijjigashi,yaron akwai rigima Tubarkallah, Ina jijjigashi ta tashi ta had`o masa Madara ta miqomin na zauna na fara bashi Ko da zuqi madarar danya canyara wani ihu saida na rasa yanda zanyi,haka na qara samu daqyar na Tura masa feeder a baki Amma yaqi shan madarar Kar`barshi tayi ta fara bashi nono tuni yayi shiru "Lallai yaronnan na lura bayason Madara Kwana biyu"na fad`a Ina goge jikina da ya `batamin da Madara "Tunda ya ganema nono ya fara Qin Madara aikuwa yaro ka fara qirgawa kanka ranakun yaye" "Haba antyna kwananshi nawa?" "Sai Ki yayeshi da wuri mugani,kefa San jikinki yayi yawa,tunda kika haifi yaromnan Sai complain"mummy ta fad`a Tana rubutu "Yaya ba complain nake ba ai Wlh Kema Kinsan feeding d`in namiji akwai wahala Haba,15 minutes yaro na tsotsonka ba dole nayi Mita ba" "Tom karki bashi kiga idan bazai zamar miki kayaba" "Gashinan Kuna fad`a a kanshi shi baccinsa ma yake,kawoshi na Kwantar dashi"na fad`a Ina miqa mata hannu,Bayan na kaishi na dawo magani ya fara d`aukata,na kasa zama Sai faman layi nake,kaina yayi nauyi "Tashi kije Ki kwanta" "Ba musu na d`au hanya da dafe dafe na qarasa Ina kwanciya na Lula duniyar mutuwa,Dan bazan kira wannan bacci ba,da qyar na tashi Yau zan koma school gaba d`Aya dad`i ya cikani,harda tsararbar kilishi na yiwa Yan class d`inmu Makaranta ta tafi yanda ya kamata sannan test d`in da nayi missing za'amin makeup,na gaji sosai haka yasa na d'auki maganin baccina nasha na kwanta Tunanin rayuwata na fara ta baya da yanda lokaci guda komai ya sauyamin Ina tsoron abinda na koma Ina matuqar kewar rayuwata ta da,hawaye ne ya tsoyayomin da na tuna irin rayuwsr carefree din da nayi a baya,kafin mahaifina da ya zama dukkan gatana a lokacin ya dawo Babban duhun rayuwata,Ina wannan tunanin kaina ya fara nauyi,maganinnan Yana wahalar dani kafin na samu bacci haka kuma idan na farka tamkar wadda akayiwa duka,idanuwana kaman Wanda tayi shaye shaye,da qudurin sanar masa da wahalar da maganin ke bani na kwanta bacci *bari mud'au complete 180 turn muje Muga rayuwar MUNAYA ta baya,nasan kowa zai tausayawa yanda ta koma* ```Shekara biyu baya``` Saukowa nayi da gudu daga bene da earpiece a kunnena"mummy gani" "Kira nawa na miki kafin Ki amsa min?" "Biyu ne Wallahi kuma na amsa kafin na sauko kin kuma kirana" "Bani wayarnan Ki tattare kwanukan dining Ki kaisu kitchen Ki wanke" "Wayyo mummy tunda adama ta koma gida nakeshan wuyar wanke wanke,Dan Allah Ki kawo wata Mana,bari na canza Kaya na dawo na fara" `Daki na koma n cire rigar jikina na sanya qaramar vest da underwear na fito,wani irin kallo mummy tamin tace "Yanzu Kaya ne haka a jikinki?kalli vest d`in da kikasa cibiyarki a waje ga wannan underwear da duk pant dinki a waje,koma Ki nemi zani" "Allah bazan canza ba Mummy nauyi Kaya sukemin idan zanyi aiki,kiyi haquri idan na Shiga kitchen bazan fito ba Sai na gama,idan Anyi Baqo Kawai Ki kawomin hijabi kitchen I lobe you"na mata kiss na shige kitchen Ina rawa Wanke wanke nake Ina juya quguna Ina waqa "Every night when I would go to sleep I couldn't stop dreaming about you Ur love has gotten me feel kinda we I really can't see me without you And now ure running around inmmy head I`m never gonna let you slip away again,again... Its real love that u don't know bout oooohhh Everynow and then when I watch you I wish that I could tell you I want you...." "Akin kike ko waqa?" "Mummy gashi har na Gama inayi Ina waqata" Tattara kwanukan nayi na fita parlour Ina waqar "Ku Girgiza kwankwaso"inayi Ina Girgiza abina Sai ga khairat ma ta miqe "Bambasho,bambasho"ta farayi Tana rawa Haka muka had`e nida khairat Muna waqar girgiza kwankwaso Muna rawa saida Mummy ta taso kaman zata dakeni sannan nayi d`Aki da gudu khairat ta biyoni "Yana jacice abba ya ciyamin baby ko?Nima jance ya ciya mishi baya" "Waya CE ba baya ba,zan fad`a masa Kema Ki fad`a kinji?" Wayata CE ta fara ringing da gudu na sauka na kar`bo wajen mummy "`Yan mata ya Akai?"na tambaya _kinsan fa YAU girls day out,Ki shirya Ki fito da wur"i_ "Haba bintu AI saidai na tuna miki, mu had`u 3:00 a gidanmu dan bazan fito ba" _To er rainin hankali,ya muka iya dake bari na sanarma sauran_ Ina katsewa na koma na d`auko zani na dawo wurin mummy da take Zaune a parlour "Mummy Kinsan YAU Friday d`in qarshen wata,zamuje shopping" "Ya Allah banason yawonnan Naku fa," "Mummy Kinsan Bana yawo banda school ba inda nake zuwa Sai wannan outing d`in Dan Allah Ki barni naje" "To ya zanyi dake Dama kin bawa kanki go ahead AI tunda kin d`auko mutane na ISA na hana?Ki Dai JIRA abbanku ya dawo" Tana rufe baki Sai ga Abba ya shigo da murna na tareshi"Oyoyo abbana na kaina abbana yafi na kowa kai naketa JIRA" "Nima auta ta tafi ta kowa ya akayi" "Nishe fa auta"khairat ta fad`a Tana ta`be baki Dagata Abba yayi Yana mata wasa yace"ai ke autar mummy CE MUNAYA kuma autata,sannan ke autar munaya da Yaya ce" Dariya take tace"na yadda,Abba Yana jataje yawo yau" Kallona yayi yace"Ina zakije?" "Abba ka manta Friday d`in qarshen wata yau?" "To ya akayi" "Abba ka Tina,Abba ka Tina Mana"na fad`a da shagwa`ba Ina bubbuga qafata a qasa "A`a sorry autar Abba fad`amin Mana Kinsan na fara tsufa Sai mantuwa" "Ka manta zamu fita da qawayena shopping?" "Au Hakane fa,shikenan Sai mummynki ta baki nata saqon duk Ki had`o ta huta fita,yanzu nawa kikeso" "Abba kawak ka dumbuzo ka bani" "Tunda zakiyiwa mummynki shopping ga 20,000 nan" Caraf Mummy tace"Haba abban Salim ya zaka Bata kud`i dayawa haka,Gaskiya yayi yawa ko me zata siyo,nawa take da zata riqe wannan kud`in" "Mummy kinsan Dai Bana wasa da kud`i kuma ba Wai sasu zanyi gaba na kashe ba kiyomin list na kayan cefanenki mayo miki" Komawa tayi ta zauna Tana list ni kuma na shige d`aki domin na shirya Rigace Arabian gown baby blue na saka doguwace daga Sama ta zauna qasa kuma ra bud`e sosai,kwalliyar silver ce a jikin gaban rigar gaba d`aya, Sai dogon hannu da rabinsa Anyi kwalliyar silver, mayafin kayan nayi rolling na saka pink d`in jambaki nayi Gira na d`auko baqin glass na saka? Juyi nake gaban mudubi Ina kallon kaina saida na tabbatar nayi daidai na d`auko farin agogo na saka na fesa turare na fara Jan Selfie, babu inda Banyi pic ba harda su toilet,Ina gamawa na kira khairat muka dinga posing Muna hotuna,duk wani style da nayi saita kwaikwaya haka mukasha pics da wankan juma`a 3:30 duk mun Gama had`Uwa mu shida,Nuriyya,ruqayya, Jamila,A'isha da mariya my trouble makers Sai ni,d`akin Yaya na kwankwasa nace "Yaya mun shirya" "To Ganinan 5mins" , cikin qanqanin lokaci ya fito muka d`au hanyar zuwa yawon juma`a inda ya Saki waqa a motar Muna tafe Muna bi Muna tsalle tsalle _sorry guys,ba anan naso na tsaya ba Amma naga nayi rubuti da yawa sannan Bana mood din typing abinda nayi niyya,Sai min hadu next love you all,Ku fad`amin da wannan munayan da waccan Wacce tafi burgeku?_ *MUNAYA* Maryam? Wattpad@mamsuhaimerh 12 Bayan na Gama bin list d`in mummy na tabbatar. Na siyo mata komai Sai na koma kan khairat,idan ban kai mata Abu ba ba Zaman lafiya da qyar na samu babydoll mai sauqin kud`i kuma mai kyau Daga nan muka wuce namu shopping d`in neman magana muka cika wurin da hayaniya kafin mu sayi abinda zamu Saya mu fita Ana Kiran magariba Muna kusa d gidanmu,a bakin titi aka saukeni ga Kaya niqi niqi,inata mitar takawar da zanyi Naji ana tsaidani "`Yan mata d`an tsaya mana" Juyowa Nai naga ko na yarda wani Abin naga ban Yar da komai ba, "Tun daga titi nake qwala Miki kira Amma kinqi tsayawa" Juyawa nayi na hango gida sannan na kalleshi nace "Amma bawan Allah ai bai kamata ka dinga kirana a titi haka ba,kayi haquri zuwa wani lokacin"na fad`a tareda qara gaba,hannuna ya janyo kayan hannuna suka zube na kusa fad`awa kansa,fizge hannuna nayi Ina qoqarin guduwa amma yayimin riqon da har zafi hannuna yake Tuni idona ya ciko da hawaye nace"Dan Allah ka sakeni Mana" Hannu yasa ya rufemin baki ya jani wani lungu inata qoqarin qwace kaina,layin babu kowa ga duhu ya fara Shiga Hannu boyu yasa ya kafeni jikin bango,qoqarin kufcewa nake yace"Haba `Yan mata ya zaki gudu?d`an tsaya Mana"ya sa hannayensa biyu ya riqo bayana "Wayyo Allah ka rabu dani" Hannu yasa daga bayana ya zuge zipper din rigata,gaba d`Aya tsigar jikina ta tashi jin hannunsa a Gadan Bayan,hannu yasa ya rufe bakina hannunsa d`Aya na roaming jikina daga bayana zuwa cikina Hawayene ke kwarara a idona da qyar na samu na Ciji hannunsa ya janye saboda zafi na kurma ihu "Mummyyyyy!!!!!!na Shiga uku"kafin na bar wurin ya qara riqoni haka na dinga ihu Ina doke hannunsa a jikina Naushi aka kawo masa yayi tangal tangal ya fad`i gefe,a tsorace naja baya kafin na lura da yayana dake kai masa duka ta ko`ina.ganin baya motsi yasa nayi saurin janye yayana daga kansa Amma na kasa "Yaya karka kasheshi ka qyaleshi haka Dan Allah YAYA!!!!" saida ya masa jina jina sannan ya taho gareniya fara dubani "Yaya"na fad`a jikinsa Ina kuka.zip d`ina ya zugemin yaja hannuna ya kaini gida tareda tattare kayan da na siyo Da gudu na fad`a jikin Mummy Ina kuka ta kalleni a tsorace "Lafiya?menene?Ina kayan?" "Mummy wanine"na fad`a Ina kuka" "Subhanallahi me wanin ya miki" "Ta`bani yayi mummy" "Ya salam,bai Miki komai ba Dai ko?"ta d`agoni Tana kallon fuskata" "Yayane yazo ya dakeshi" "Sorry yi shiru kinji?indai ya gane fuskarsa shikenan zamu d`au mataki" "Mummy Wallahi qazami har wari yake yasa hannu ya ta`ba jikina,na fad`a tareda face hancina" "Yana ciy ha`uyi CI dena kuka"khairat ta fad`a Tana ta`be baki alamar zatayi kuka Share hawayena nayi nace"karkiyi kuka nadena Nima kinji?ga babynki na siyo miki"na janyo leda Ina bincikawa Miqa mata doll d`in nayi ta kar`ba ta rungumeta ta kwanta a jikina har tayi bacci `Daki na kaita sannan na Shiga wanka na dinga dirje jikina Ina mita "Shege insha Allahu sai anyiwa `yarka ko qanwarka Wanda baisan darajar mutane ba,qazamin banza qazamin wofi" A haka na Gama wankan na fito na shirya nayi sallah,Ina idarwa Naji wayata tayi qara "Hello A'isha kunje gida lafiya?" _lafiya Lau Kema kinje lafiya_ "Hmm lafiya ba Lau ba,Kinsan Kuna saukeni wani qazami ya biyoni?" _Huhuhu,`Yan matana tayi kasuwa,tell me everything_ "Dalla can ba wata kasuwa he molested me,yanzu na Gama shan kukana" _kutumar uba....kin ganeshi?wait Ina zuwa yi holding_ Conference call ta had`a Mana mu shida nan na sanar musu duk abinda ya faru tun daga farko har yanxu da nake sallah _Amma wannan ya cika Dan iska_:Jamila _Amma yaya yayimin daidai da ya dakeshi Wallahi da nice saina bari ya sumar dashi_ mariya _sorry sister da mun kaiki qofar gida da duk haka Bata faru ba_ sumayya _Wallahi ya sake na kamashi Sai na kusa kasheshi,kunji tsinanne?baisan ke ba irin wad`Annan matan bane?_ A'isha _wait....tell me how does it feel_ Nuriyya Gaba d`Aya suka hau mata hayaniya ni kaina saida na janye wayar daga kunnena,na tabbatar da Muna tare da tasha duka yanzunnan _karki damu kinji munaya, indai Muna nan ba Wanda ya ISA yaqara ta`baki,mu kanmu mun isheshi_ nuriyya Haka muka qare wayar Suna kwantarmin da hankali daga baya muka d`Anyi jokes muka kashe * * * "Abba next week birthday d`ina fa" "To munaya gashi lokacin Bana nan,me kikeso a present" "Abba waya tacesho"khairat tayi Caraf ta fad`a "To na baki za`bi uku Wacce kikeso?" "Abba iPhone nakeso" "Anya zaki iya riqon iPhone?tanada wuyar Sha`ani fa a matsayinki na student Ki samu mai sauqin cin kud`i "Too bari Muga?Yauwa Abba Samsung" "To shikenan Wace iri?Amma Kinsan battery na Samsung Yana saurin mutuwa" Yaya ne ya shigo yace"Dalla can kice infinix" "Abba infinix" "Angama ranki ya dad`e,wayarki na nan zuwa ranar da kika cika 16" "Aba Nagode Allah ya qara Arziqi"na fad`a Ina tsalle"Amma Abba,inaso nakai cake class dinmu" "Haba qanwata wannan AI Aikina ne,shine nawa present d`in" Murna nake bakina har qeya mummy na Saukowa nace "Mummy Abba zai sayamin waya Yaya zaimin cake,ke me zakimin?" Murmushi tayi ta zauna gefen Abba tace"wato saboda birthday dinmu lokaci guda ne ni ba Wanda yake ta taWa ko?" "Mummy ni nisan me zan miki nidai me zaki bani?" "Nima na barshi surprise" "Khairat me zaki bani?" Hannu ta miqo na d`auketa ta mannamin kiss"wow kyautar babyna ta fi ta kowa"na fad`a tareda kissing d_inta Murmushi Mummy tayi tace"ni baza`amin ba?" Sauka khairat tayi ta bisu duka da kiss sannan ta dawo ta riqe qafata "Yana janci abinci" "Allah ya nunamin ranar da zaki kirani da munaya babyna" "Amin"ta fad`a Tana murmushi Wanda ya bayyanar da fararen haqoranta da dimples d`inta Wanda suke matuqar birgeni,ana cewa auta na muni tamu Kam duk ta fimu kyau Tanada yawan murmushi dukda batada yawan wasa ita Dai ta kwanta jikina ko tayita yimin surutu Ina biye mata,siririya CE sosai bazaka CE tayi shekara uku ba Bata yiwa kowa magana banda mu na gida gata da kunya Kitchen muka nufa na zuba mata abinci na zauna na fara bata saida ta qoshi sannan na d`auketa muka koma d`akina "Yana kansha Uwa"ta fad`a Tana Tashina daga bacci,dubawa nayi naga ban shigo mata da ruwa ba ga dare yayi haka na kunna fitila na fita Dan dauko mata ruwa anan Naji hayaniyar mummy da Abba "Ka gani abinda nake fad`a Maka ko?a qpfar gidanka ana neman molesting `yarka,abdallah yaushe zaka canza `ya`yanka fa mata biyjne abdallah Baka tausayina?" "Ki dena d`aga murya mana idan sukaji fa?" "Au `ya`yanka kake tsoron Susan halayyarka?meyasa kakemin haka abdallah?meyasa ni bazaka saukemin haqqinka na aure ba Sai matan banza a waje?meyasa kake wulaqantani abdallah meyasa?" Alamun kuka da rarrashi Naji cikin sanyin jiki na d`auki ruwa na koma ba tareda sunji takuna ba,Abba ne ke magana Amma Bana buqatar ji da sauri na koma d`aki na rufe Khairat na shan ruwan ta dawo jikina ta kwanta,a qirjina na d`aurata na lullu`beta har tayi bacci saidai bacci yayi qaura a idona,Ashe akwai matsala a gidanmu?Tabbas abinda zaisa Mummy kuka ba qaramin Abu bane,haka nayita tunani har bacci ya d`aukeni Safiya cikin walwala naga Mummy ta Gama had`a Mana Abin kari muka fita school. A kindergarten ta ajiye khairat ta kaini makaranta tace"YAU abbanku yayi tafiya zanzo na d`aukeku Amma Ki biya Ki d`auko khairat Sai na d`aukeku a can" Amsa mata nayi da to na shige,Bayan an tashi na nufi makarantar su khairat Tana Zaune tareda auntynsu aai magana Take mata Amma kanta qasa murmushi Kawai takeyi.Ina sallama ta taho da gudu na d`auketa na gaida antynsu na mata sallama muka koma gate Muna jiran Mummy "Me aka koya muku YAU" "Godiya"

Chapter 6 of 8