dumin tagudanarda wannan babban kes din"" duk inda zakije zankasance atare dake saboda tsarooo""
dariya tayi tace kai ya haydar saboda kishi dai"" karan hancinta yaja yace koda hakanne aibanyi laifiba menene amfanin mijinda bayakishin matarsa??? Ni aganina duk mutuminda baya kishin matarsa bayasontaa wlh ilham da dayanda zanyi"" hmmm dababuwani wani mahalukinda zaiga ko suturarda kike sakawa ballana takaiga yagankiii
Yanzun ma daurewa kawai nakeyii danbazan hanaki yin jahadiiba kamar yanda kikai alkawari duk Wanda akaci zalinsa akasarnan zakizama lauyansa me karesa akullum kuma kisani haydar yana kusadake zanyi komai akan hakan """ konawa za akashe nizandinga bayarwa musamman yayan talakawa da akeyiwa fyade basada gata sai Allah duk wani Dan shugaban kasa kodan majalisa kokuwa hamshakin maikudi yanemi ya lalata yar mutane zamu nema masu hakkinsu """ zamutsaya kaidafata danganin wannan abun yarage akasarmu""
Ilham tarungumeshi nagode sosai baban arfar" yace tashi muje dan fa inkika biyemun anan zamukwana "" mikewa tayi tadauko hijab dinta da nikaf suka wuce""
. dama arfat sunbarshi gidan momma dayanbiyu dansosai sunayarda da kakus tunda itah kawai sukasani sosai"" dasukaje cen basu sha wata wahalaba saboda sunsamu izinin ganinsa da ilham tanunamasu katinta nashaidar ganinsa
Akafito dashi ansaka masa sarka karkuso kuganshi gwanin tausayii suk yarame yafita kamanninsa"" yana ganinsu yashaida haydar dakuma wannan mai nikaf din""
Wajensu yakaraso yazauna"" police dinyace mintii talatinne gareki"" tajinjina kai"" ok"" tamaida kallonta wajen sa tace kawu ina wuni"" dakyar ya iyah cewa Amman kai kamar nasanka????
Haydar yayi murmushi yace bakamabane kashaidani"" yace hakane"" wannan kanwarkace ??? Ko matarka??? Yasakeyin murmushi yace autar ammie ce""
Dasauri yakalleta yace kana nufin ilham dinmu tawajen kanina??? Haydar yagyada kai "" Allahu Akbar Allah maigirma"" hawaye ne suka zubomasaa yace hakika komai dalokacinsa"" mahakurci mawadaciii duk yanda kaso kacutarda mutum inhar Allah yakaddara bazai cutuba babu abunda zaisameshi"""
Yafashe dakuka ilham ina mamanki Dan Allah kinemamun yafiyarta ninasan daman Allah bazai barniba
Ilham race.kawu kadaina wannan kukan"" komai yawuce ni awajena har ammei"" fatanmu Allah yayimana gafara bakidaya"" yace Ameen ameeen nagode sosai""
Ilham tace kawu gashi harmunci mintuna biyar"" kuma bamuyi maganar datakawo muba"" tagyara zama tana fuskantarsa tace"" kawu kozaka iyah sanardani gaskiyar abunda kasani
Hawaye yashare yace "" ilham wannan shariar ninasan saigaban Allah danbanada hujjar dazan kare kaina dadare ne ina kwance cikin daki sainaji kamar ihu cikin gidan" harnakyale saikuma naji ihun ya tsananta yanacewa sunkasheni"" dagudu nafito waje"" sainaji ihun adakin muftahu yake fitowa"" dasauri nazagaya nafita zuwa bangaren dakinsa kulle nasamu kofar" naturah dakarfii nashiga sainasameshi rubda ciki dasauri nakarasa nasa hannu najuyoshi
Jini duk yabatamun hannu""" gabana yayanke yafadi sakamakon wannan abun danagani"" saina zagee masa wukar""
Alokacin baikarasa mutuwaba"" ina tambayarsa waye yamasa haka??? Daidai shigowar hajara kanwarsa saita kwatsa ihu saiga hajiyar tashigo"" tanashigowa yana mutuwaa idanuwansa suna kantaa""
Ihutayi kawai takama dukana wainakashe mata yaro"" nayita batahakuri tajirah naimata bayanie Amman takiko saurarena""
Wayarta tadauko takirah yansanda"'sunazuwa sukasamu gawar wukar nagefe gahannuwana dajini tanunawa dansandan cewa nine nakashemata yaro
Shine sukasamun ankwa sukatafi dani"" yanisa wannan shine kawai abunda nasani wlh ilham ninasan saidai acekawai inada fitina Amman kisa dakaina nakashe mutum wane irin rashin imanine haka""
Ilham tanisa tace kawu kuma bakutaba samun sabani da matarba??? Yace kodaya nidanake tsoronta tayama zan iyah musayar bakida itah tunda Na aureta idona danata basutaba haduwa ba yanda kikasan yaro da ubangidan sa""
Duk fitinata akan huwaila sainayi sanyi komai zatamun banajin zan iyah musawa kona nuna bacinraina"" ilham tace to alokacin da abun yafaru karfe nawa??? Yace wajajen daya darabine nadare""
Ilham tace to kawu ya akai dashidin yayi ihu. Ace kaine kawai kaji ihun itah kanwarsa dakuma hajiyar suna ina???
Yace Allahu wa alam Amman basagidan lokacin kuma bawairanarne tasababa daman batazama gidan dadare"" saidarana kawai takezama dadare nikawai akebari ninake gadin gidan""
Shikanshi muftahun baicika kwana gidan ba sai idan yadibo yammatansa"" ilham tace zaka iyah sanin yanmatan nasa????
Yace ah to zan iyah tunadaya danyataba aikena insiyomasu ruwan sanyi naganta Amman bansan sunantaba"""
Daidai shigowar Dan sandan yace lokacinki yakare"" takalleshi tajinjina kai tace shikenan kawu sainasake dawowa""
Yace to ilham kisake nemamun gafara wajen mamanki"" suna tsaye akawucedashi dakyarma yakedaga kafa saboda sarkokinda aka samasa""
Ilham harda yan gallah tayi"" ta share hawayen tana kallon haydar tace mujeko baban arfat"" dama tsaye yake yawuce sukafita tunda sukashiga motar ilham tayi shiru tana kallon motocinda suke wulgawa dasaurii dasaurii
Gentle Ladyππ½
[10/01 1:30 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 25
By
Aeesha Ibraheem
Dedicated 2
Hafsat M Shareef
&
Haneefa Usman"ππ
Haydar yarage gudun motarsa yana kallontaa"" yace yadai barrister kan yadauki chajine??? Murmushi tasakar masa shima yamiyarmata da martani"" tace baban arfat mekafuskanta akan wannan maganar???
Yadaga kafadarsa yace nikuma menene alakar aikina danaku wannan zafin wajen bincike aisaiku"" kinsan Allah nibangane komaiba kawaidai natausaya masa
Amman wannan hukuncin sai ikon Allah Amman taya za agano gaskiyar"" ilham tace gobedai zamuje unguwar itah matar meyuyuwane. Asamu wani haske"" yace hakane Allah yakaimu Allah kumayasa adace ilham tace ammen""
Sundan taba tafiya yace zakisha ice cream "" tace ah ah" yana kallonta yace waiyanzu bansan meyasaba bakyason shan ice cream keda kobarci kikeyi idankikaji kamshinsa saikin tashi
Baki tarike la baban arfat yaushene kaga inabarcin nafarka dankazoda ice cream"" yace ranarda ahmad yakawo wa yanbiyu"" kintunaa tace au aisaudayane"" kawai
Yace gaskiyadai tafito"" dariya tayi tace ainikam nagatakaina shiyasama ainadaina shan sa adaina cewa yara nisuka biyo dashan zakiii"" baki tamurgudaa
Haydar yace nikike murgudawa bakiii ba"" kinci bashi danyau saina karbiii abunaa"" bakinta tadafe tana dariya wlh mantawa nayi baban arfat bazan sakeba""
Yamurmusa saifa kinkarbii nayau sai nangaba ki kiyaye"" tace please my"" takasan ido yakalleta yace. Kinsan me wannan kashe muryan dakikeyi sake tsumani takeyi wlh"" tace toya kakeson inyi nagana??? Akoda yaushe muryan mace kasatake gata mijintaa
Banason Maryana tadara taka hawa kokadan"" hamma tayi tace bannakwanta wlh barci nakeji"" ido yazaro ganin tayi matashin kai da cinyarsa""murmushi yayi yacigaba da
tafiyaa""
Barcinta takeyi hankali kwance"" koda yayi pkng baifitoba saboda bayaso yatasheta tana barcii"" zaune yayi cikin motar" har akasoma kiran sallah "" zatagyara kwanci tajita atakure tabude idon ahankali tuni tatashi zaune"" hasbinallahu wa ni imal wakil "" baban arfat"" yaushe muka kawo""
Yana kallonta yace aimunyi awadaya anandin"" tashagwabe murya kai my lov shine kokatasheni""
Hannunta yarike yana kallon cikin idonta yace nalurah kinajin dadin barcinne nikuma bazan iyah tashinkiba zanragemaki wani jindadin"""murmushi"" tayi tace nagode muje kajifa ansamo kirah"" yace yauwa kodai saina daukekine"" bakitarike tace laa baba fa zaiganmu"" yace idan yaganie saiyarufe idonsa"" ai yakanne mata ido daya"" ganin yafito yazagayo kofar tasan zai iyah dasauri tatashi tana dariya baban arfat anhutardakai wannan karon"" cikin gidan suka karasa yana dariya
Washe gari haka sukaje gidan yakubun sukadauki rahane zuwa gidan huwaila a unguwar suka tsaya suna tambaya Amman Sam babuwani haske haka sukadawo gida"" rahane saikuka takeyi Dan itah sosai tanason mijintaa
Anasauran kwana biyu akoma kotun sukasake komawa wajen yakubun iyah rayuwar wahalarda yakeyiwa huwaila kawai yafada danshi baisan wani wanda muftahu yake fada dasuba hasalima baisan abokansaba
Haka sukadawo gida jiki bakwari dadare suna kwance haydar yace anya weety chest dinnan bazakibari abaiwa wanishiba nidai Sam banga alamar akwai haske acikinsaba
Jibinefa zamu koma kotun kuma alkali yace kizoda gamsasshiyar hujjarda zata tabbatar dacewa bashine ya aikata kisanba"" kumani kokadan banga wata hanyar dazaki ganoba nisam lissafina ya kwance
Ilham tamurmusa tace insha Allah bazasuci galaba akainaba inhar kawu yanada gaskiya totabbas gaskiya saitafito kawaidai katayani da addua"
Yace kumafa kinyi magana to Allah yataimaka"" tace Ameen"" tagyara kwanciya "" haydar yace weety kwanciya zakiyi??? Tace ah ko akwai wani abune??? Yace ah ah nidai tunda an sallameni aibanida wata magana nagakinada wannan rigimar agabanki indanine aiko gyangyadi bazan iyah ba
Ilham tayi dariya baban arfat bakada dama"" nagadai duk katsure akan wannan chest din"" nibazan hana idona barciba"" idan nakwanta ainatsuwa zatazomun kafin goben Amman idan nazauna natirsasa kaina akan tunani nayizurfi cikin tunanin komai zaichakudemun inrasa ta inama zankama"
Yace hakane barrister"" toyanzu wanne guri yaragemana muje??? Tanisa bako ina bansan abokanan saba ballantana wadanda mamansa takehulda dasu "" basuda mutane agidan ballantana inje intitsesu da tambaya""
Allah daiyashige mana gaba"" haydar yace Ameen mudai kam zamuga yanda weety zata karkare"" murmushi tayi tashige jikinsa tace idan banyi Wener ba"" aikai za ayiwa dariya""yace bama zasu kadakeba babyna muyi barcin mu
Yasake sagalo matarsa suka kwantaa fuskokinsu kumshe cikin nishadii
Kotu tacika makill wajen wucewa ma saikayi dakyar wasu tsaitsayema suke banda kujerun kotun da akacika bamasauka tsintsiya
Yakubu ne akashigo dashi zuwa inda masu laifi suke tsayawa"" tunda akashigo dashi huwaila takebinshi dasakon harara rana kunkuni"
Aduniya idan akwai Wanda tatsana to yakubune daza abata wuka ace takashe mutum daya wanda batasonsa toba shakka yakubu zata kashe
Tayita tsinewa wannan shegiyar ilham din datazo darana tsaka tahana ayankewa azzalumi hukunci
Tasan baida kudin daukar lauya Amman tayimamaki a inakuma yasamu wannan lauyan??? Duk da lauyanta yace takwantarda hankalinta babu makawa sai anyankewa yakubu hukuncin kisa "" tundahar ankamashi dumu dumu wajen aikata kisan
Wannan shari ar maisaukice inbadan sunason hawalda shari a ba"" Amman tasan alkali dayagaji da tangariri aidole ayankemasa hukunci
Alkali yakatse mata tunani tahanyar buga gudumarsa kotun tayi tsit"" kasancewar tunda akashigoda "" yakubu kache nache akafarayi wadansu sunacewa aizai iyah wadansu sunacewa mudaizuba idomuga yanda zatafitardashi badai ance yautaxoda hujjojin taba""
Maga takarda yatashi yarabtaho bayanai akan dalilin karar dakuma hujjojinda barrister lawal yagabatar dakuma aune aune dalikitoci sukayi nashatin hannun yakubu
Bayan yagama alkali yakalli barrister lawal yace kokazoda wasu hojjoji bayan wadan nan???? Mikewa yayi yace babu yamaigirma maisharia hujjojinda nabayar sun isah sugamsarda kotu cewa yakubu shine yakashewa wannan baiwar Allah danta "" yakamata ajitausayinta domin shine kawai danta aduniya nagode yamaigirma maisharia yakoma yazauna
Gentle Ladyππ½
[10/01 1:30 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 026
By
Aeesha Ibraheem
Dedicated 2
Hafsat M Shareef
&
Haneefa Usmanππ
Alkali yajinjina kai sannan yakalli ilham yace barrister fateema kotu tanaso kigabatar mata da hujjojinda kika zodasu""
Ilham tamike tasake gyara tsayuwar rigartaa"" yau doguwar rigace tayadiii saikaramin hijab datasaka saita dorah rigar asama
Haryau tanasanye da nikaf dintaa"" tajuya takalli haydar yasakar mata murmushi "" tajuya wajen alkali tace yamai girma maisharia inaso agabatarmun da mahaifiyar mamacin akwai tambayoyinda nakeso zanyimata"""
Alkali yace idan mahaifiyar wannan yaron tanakusa tafito gaban kotu anason ganintaa"" hajiya huwaila tafito daga cikin taro inda mutane dayawa sukajuya suna kallonta wadanda basuma santaba yaune suka samu shariar wasunsu kuma sunsanta Amman saida suka sake juyawa sukaganta
Wajenda masu shaidu suke tsayuwa tatsaya ilham tataka ahankali zuwa gabanta"" tace baiwar Allah kotu tanason taji sunanki""
Tanisa sunana hajiya huwaila"" ilham tajinjina kai tace hajiya huwaila kozamu iyah sanin sa na arki??? Tace ah nakan siyo hajane ina bayarda sarii hakan ina siyarda kayandaki dadai sauran abubuwan saye da siyarwa"
Ilham tace yakike da wannan bawan Allah tayi nuni dayakubun"" huwaila tamere baki tace mijinane"" ilham tagyada kaitace hajiya huwaila tsayin shekaru nawa kukayi da aurenku??? Tace za ayi shekara Tara " ilham tace shekararku Tara"" Amman auren soyayya kukayi dashi???
Barrister lawal ne yamike yace yamaigirma mai sharia baikamata barrister fateema tarika yiwa wannan baiwar Allah tambayoyi narashin da aba""
Alkali yace barrister kikiyaye"" ilham ta jinjina kai"" tace hajiya huwaila aganina baidace kinazargin mijinkiba kodai azamanki dashi kintaba kamashi dawasu dabiun marasa kyau
Koyana shaye shaye dasauransu"" tace bayayin kodaya kumani bantaba saninsa damugun dabia ba Amman kinsan yanzu bakashaidar mutum kodankane zai iyah sauyawa
Dawanine yafadamun zankaryata hakan Amman da idanuwana naganshi akan gawar dana gawuka ahannunshi""
Ilham tace lallai natausaya maki"" Amman hajiya huwaila lokacinda abun yakasance ke kina ina??? Dahar dannaki yayikuwa bakijiba
Tace ah gaskiya bana gidan"" ilham tace yahausar bakyagidan "" amatsayinki na matar aure"" ace karfe daya darabi bakyagidan mijinki
Duk wata mata aiyakamata zuwa lokacin tana tareda iyalinta kodai akwai wata boyayyar sana a dakikeyi wacce bakyaso kowa yasani???
Barrister lawal yace yamaigirma maisharia barrister fateema tana nema tawuce huruminta menene alakar kisan danta dakuma wannan sharkafaffun tambayoyinda takeyiwa hajiya huwaila""
Alkali yace korafiii bai karbuba"" cigaba barrister fateema tadan dukarda kai tana murmushi tace nagode"" tasake kallonta tace lokacinda akai kisan bakya gida"" tagyada kai ah banagida"" ilham tace mijinki yace idan kikabar gida tun bakwai namarece bakya dawowa sai safe hakane????
Tace kwarai hakane"" ilham tace to aranarda akayi kisan menene dalilin dawowarki bayankuma bakitaba dawowaba dole saida safe kodai kinasane dacewa ankashe dannaki""
Tayi shiru"" ilham tace hajiya huwaila bakibani amsaba"" tace ah gaskiya banadawowa sai safe ranarkuma dana dawo hajarace takirani dawaya tace inzo gida nayi baki""
Ilham tace bakikuma dakarfe 1;30am ??? Wadanne irin bakine kamar na aljanu dabasakai ziyara saida tsakar dare""
Tace lokacinda takirani kaitsaye nashiga motane zuwa gidan dantacemun inyi sauri"" bayan nakawo kofar gidan nasameta saimuka shiga ciki danbakin kofa nabar motana
Munashiga sainasamu kofar dakin babangida abude"" kuma bansaba ganinta ahakanba shine nacewa hajara tadubo meyakeyi haryanzu bairufe kofaba
Dashigarta sainaji takwallah ihu tanacewa ya kasheshi daguduna nayarda jakata da makulan motah inah cewa wanene aka kashe dashigata dakin nayi turus ganin wannan azzalumin saman gawar dana inashiga ransa yanafita""
Tafashe dakuka Allah ya isah tsakanina dakai yakubu wlh sai anyanke maka hukuncin kisa kamar yanda karabani da Dana kaima haka zakabar duniyar nan "" tafyace majina""
Ilham tace Allah yajikanshi"" tace Ameen"" ilham tace Amman hajiya huwaila kince hajarace takiraki cewa kinyi baki shindakikaje gidan kinsamu bakin???
Tace banga kowaba kuma hankalina yatashi tayama zanlura dasu"" ilham tace hakane yanzu ke aganinki taya mutum zaikashe wani kuma yazauna akan gawarsa aidazaran yayikisan neman wajen guduwa danasa ran zaiyi kar akamashi Amman kuma kikasameshi zaune kuma rungume dayaronki""
Tayi shiru ilham tajuya wajen alkali tace yamaigirma maisharia inason kotu ta gabatarmun da hajara akwai tambayoyinda zanyimata
Alkali yace idan tanakusa tafitoo"" hajara tanacikin mutane"" tataso akabudemata hanya tagabata kusa da hajiya huwaila
Huwaila takoma gefe"" ilham tace toku tanason taji sunanki"tace sunana hajara"salis" tajinjina kai tace yakikeda wanda aka kashe??? Tace yayanane'' ilham tace ma ana uwadaya ubadaya koya abunyake""
Tace ah ah nayan uwa " ilham tace kenan akwai aure tsakaninku""tayi shiru "" ilham tamurmusa"" tace hajiya huwaila tace kinkirata cewa tayi baki alokacin dataje gidan kuma batasamesuba
Inasukaje??? Tace uhum eyem" dama dama"" gidan zanshiga kumani tsoro nakeji inshiga nidaya saikuma najikamar motsi shine nakirata nafadamata anyibaki Dan inbahakan naceba baxata zoba"
Ilham tace tsarinki yayi hajara tunyaushe kike gidan"" tace anan natashi kusanma anan akarikeni tun inakarama"" ilham tace arikeki agida kuma matar gidan batazama dadare saida rana Amman ahakan kikeshiga gidan saikawai ranarne kikaji tsoron shiga kika kirah hajiya huwaila""
Hajara karki wahalarda hukuma"" kisanardasu abunda yafaru kuma dole kinsan Wanda yayi wannan kisan"" tace wlh nibansan komaiba iyah gaskiyata nafada
Ilham tajuya tace nizanbaki labarin abunda yafaru hajara takasance tanason miftahu kamar ranta"" shikuma yakasance yanada wata budurwa daban kokadan baya nunawa hajara so itah kuma takasance tanason sa"
Ranar ne muftahu yazo da budurwarsa shine hajara takudurah aranta saita kashe yarinyar shine tashiga gida tadauro wuka taboyeta abayanta
Tashiga dakin muftahu yace meyakawoki dakina????
Tace nazone inkashe wannan tsinannar yarinyar dame tafini dazakafisonta akaina nida nake yar uwarka
Yace banason sakarcii kifita daganan"" hajara tace wlh bazan fitaba sainaga bayanta"" tayikukan kurah cikinta garin muftahu yakarbe wukar taluma masa aciki shine da itah da budurwar suka ruga kowa yayi waje lokacinne yayi ihu yanacewa sun kasheni
Shikuma wannan bawan Allah yanacikin gida yaji ihunsa yana Neman taimako kafin yazagaya hajara tayisauri tafure kofar saita fita takirah hajiya huwaila tacemata tayibaki tazo dasauri
Dantasan tabbas zatazodin"" shikuma yanazuwa yaballe kofar yashiga yasamu yakife"" yajuyodashi yazaremasa wukar shine sukasameshi dawukar ahannunsa""
Barrister lawal yafara tafiiii raf raf raf"" angaisheki barrister gaskiya kin iyah bada labari" yanzu muna zaune harkin lauye magana "" tokisani nandin bagidan redio bane kuma basauraren labarai mukazoyiba ke idan bakida aikinyi mu munada abunyi""
Alkaline yakatsamasa tsawa yace barrister lawal kashiga taitayinka karnasakejin kayi magana indai banine nabaka izinin maganaba"" kasani kotu tana iyah sake mailaifi Amman babban laifine ahukunta Wanda bashida laifi danhaka ka kiyaye"
Yadan gurfana agafarceni yamaigirma maisharia"" alkali yakalli ilham yayi murmushi yace cigaba barrister
Tace nagode takalli haydar tana murmushi shima yamiyar mata yadagamata babban danyatsa"π
Gentle Ladyππ½
[10/01 1:30 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 027
By
Aeesha Ibraheem
Dedicated 2
Hafsat M Shareef
&
Haneefa Usmanππ
Murmushi tayi sannan tajuya wajen hajara tace"" bakyaso budurwar muftahu tatona maki asiri shine kikabata kudi kikace kartazo koda taji ana maganar anyi kisan""
Hajara tace wlh bani nakasheshiba""ilham tace idan bakebace towaye??? Hajara karki wahalda hukuma kisani idan kikafadi gaskiya cikin sauki batareda kin wahalda hukumaba"" za amaki sassauci wajen yanke hukuncii
Shiru tayi tana kuka" ilham tajuya wajen alkali tace yamai girma maisharia tabbas wannan tasan wanda yayi kisan kokuma itah ce tayi kisan
Inaso kotu tasa atuhumeta danbazata fada cikin saukiba"" yamaigirma mai sharia iyakar abunda zan iyah cewΓ kenan"" takoma tazauna""
Alkali yayi yan rubuce rubucensa yadago yakalli barrister lawal yace barrister kokanada. Abun fada??? Mikewa yayi yace babu yamaigirma mai sharia""
Alkali yasake yan rubuce rubucensa yace bisaga hujjojinda muka saurara lallai kotu tanabada izinin akame hajara atuhumeta "" sannan kuma kar abada belinta
Sannan acigaba datsare yakubu harzuwa zama nagaba kuma nakarshe""
Yansanda sukazo kamataa tace kudakata wlh zanfadi gaskiya danaje gidan yari kwara nafadi gaskiya!!! Gabadaya hankalin kowa yakoma kantaa"" alkali ya umurci yansanda dasu saketaa yagyara zamanshi yace munajinki""
Tashare hawaye tace wlh banice nakasheshiba teema ce!!!"" Alkali yace wacece teema??? Hajara tadago jajayen idanuwanta tace budurwar ya mufty""
Kamar yanda lauyan nan tabada labari agaskiya inasonsa sosai nakanji haushi idan naga yanakula wasu matan duk da mahaifiyarsa batasan hakanbΓ hasalima batasan abunda yake aikatawaba danbata zama gidan indai bada ranabane
Takan barni cikin gidan tunkafin tayi aure taje wajen haskokinta"" nataso bansan dadin uwaba danni bansan ma iyayenaba idan natambayeta zatacemun niyar kanintace daga kauye tadaukoni
Bansan sana arda takeyiba saidai wacce nasani tahajace nima takanturani karbomata kudi"" tashare hawaye watarana ne dadare ina dakina saiga ya mufty yashigomun abuge alokacin banfi shekara sha biyar ba""
Cikin barcina naji ana lalubana koda nabude idona sainaganshi zanyi ihu yarufemun baki yace karnayi ihu"" alokacin ma natuna koda nayi ihu abanzane danbakowa nice kawai agidan
Aranar ne yaso yayi lalata dani duk da natsorata abunda bansababa aikuwa takarfi yayimun saida yabiya bukatarsa yatsallakeni yawuce""
Washe gari koda hajiya tazo tasameni akwance cikin jini"" tataimakamun tagyarani saitake tambayana waye yayimun haka??? Nafadamata ya mufty ne shine tadaukeni da mari tace wai nalakawa yaronta kazafi inama danta yasan wata aba mace dazaiyi mata fyade""
Cikin kuka nacemata wlh shine"" tasake daukeni dawani marin tace kul tasakejin nadanganta yaronta da iskanci asheni bansan mutunciba tarikeni tabanici tabani sha Amman da abunda xansaka mata kenan ""
Nace tayi hakuri Amman banyimata karyaba"" shine tace dama amfanina kenan kuma tanajin tausayina medankawai ina karama''
Tundaga ranar bansake sakashi a idonaba"" itah kuma bata kotambayeshiba dama saitayi sati biyu batasakashi a idontaba"" rana tabiyu hakan yasake zomun saidai yabani wani Abu nasha saigashi dakainama nayarda yatara danie
Tundaga lokancin naketare daya mufty tare muke kwana yini ne kawai bamayi atare "" cikin hakanne hajiya tayi aure da yakubu
Auren ta kokadan baihanamu sheke ayarmuba hartakaima idan zaibar kasar taremuke tafiya itah kuma koda bataganniba baxata taba tambayar ina najeba""
Ana hakane yahadu dawata budurwa fateema Amman anakiranta teema" tana mutuwar sonsa sannan kuma gata damugun kishi"" ranar da abun yafaru"' ina dakinsa kwance saman cinyarsa"" wuka nahannunsa yana yanka kankana yanasamun abakina saiga teema takirashi
Nibansan ma sunyi fadaba ashe saboda sunyifadane yadawo wajena kwana biyu"" tayita kiransa yaki dagawa"" natambayeshi waye yake kiransa yacemun teema ce kaitsaye
Zanyi magana yace banason yawan tambayoyi"" Muna nan zaune saigata tafado dakin kamar dagasama"" kusan tare muka mike"" tace dakyau yanzu babyna akan wannan banzar kaki daukar wayana??? Kafadamun mewannan tafini dashi??? Tafara juya jikinta tace kaima kasan nafita komai banda jaraba irintaka tamkar wani bunsuru kabi waccen kabi waccen "" cindanko kuma hardasu kaxa"" mezaka tsinta ajikin wannan tsohuwar kilakin??? Hajara abun yabata haushi tace abunda yaketsinta ajikinki nizaki nunawa bariki diyar alatsine"" to wlh kishiga taitayinki kona narkamaki shegen duka agidan nan""
Damara taci da gyalenta tahauni da dambe"" ya mufty yana rabamu takibari saiya wanketa da marii"" tarike kuncinta yanzu baby akan wannan jakar zaka mareni??? Yace anmarekin kuma karnasakejin kincemata jaka akwai wata jakar bayan ke nace banasonki banasonki toko dolene sainayi tarayya dake""
Tanarike dakuncinta tace nikamara baby??? Yace idanma kikai wasa saina karamaki wani"" tacije baki nagode Amman kasani marinka baxaisa inkyaletaba wlh tunda kamareni sainayi sanadin halakarta
Hakan datafada yasa yasake dauketa dawani marin yace idan zaki halakata kihada danie"" ke idanma bakisaniba auren ta zanyi""
Nikaina bansan sanda nakalleshiba dankuwa baitaba fadamun zai aureniba kodama nayimasa maganar aure saiyakamayimun dadin baki""
Alokacin nasan inada cikinsa wata biyu banyi niyar sanardashiba harsaina haihu hakan zaisa dole ya aureni
Wukarda take gefenmu tadauka tace wlh yausaita kasheni inyaso itah akasheta"" tayo cikina dawukar nikuma naboye bayansa"" garin yakwace wukar itah kuma tasaita tasokamun saitasameshi aciki
Ihunda yayi yace sunkasheni dagani har itah muntsorata"!!!
Gentle Ladyππ½
[10/01 1:30 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 028
By
Aeesha Ibraheem
Dedicated 2
Hafsat M Shareef
&
Haneefa Usmanππ
Dani da itah har rigengen fitah mukeyi"" waje"" zatagudu nariketa nace inazakije ai wlh babu inda zakije sai nakirah mahaifiyarsa yazaki kasheshi kigudu kibarni cikin balai""
Tace dan Allah kirufamun