yana Neman abunda zairufamana asiri inkawo masa tawa bukatar
.gwaggo tunfarko kece kika kashe zuciyarki bakya neman komai saidai kizauna anemo maki
Niyanzu natuba wlh banajin zansake kwatanta abunda Na aikata bayaa kitashi kiyi sana a kikashewa kanki takaicii
Nibazanyi maki karyar zankawomaki kudiba dannima mijina nemansu yake""
Larai tace Zainabu nizakicewa intashi inyi sana a??? Tundanake bantabayin tallar komaibaa da arzikinki zainabu aike abunkunyane agareki ace anganni rariya rariya ina tallah""
Zainab tace kinatsu gwaggo kisaurareni magana ta gaskiya zaid bashida kudiii kawai yayimun hakanne danya aureni"" kuma Alhamdulillah tunda mijina yanasona nima inasonsa kuma yanajidani yarikeni tamkar zinariya nikudi basa gabana yanzu
Larai ta nainayo ashar tace gadebabben albarka yanzudaman kajine bashida ko sisin kwabo Amman yazoyaliliya mana karya ya aureki
Toke wacce tsiyar kikeyi agidansa haryanzun baki dawoba"" tace dakata gwaggo nidai kidaina zagarmun miji aishi karashi bayada matattar zuciya tunda yana nema kekumafa dakikazama cimakwance saidai kizauna anemo abaki
Menene amfanin zama babu sana a"" gwaggo wlh tunfarko kece kikabata kankiii"" nikam natuba gwaggo"" kerufemun baki karnasakejin kinsake kirana da gwaggonki bayan kingama kwancemun zani akasuwa
Nagode zainab kici mijin naki sainagani idan danamiji saikashe maki takaiciii takashe wayarta "" baki zainab tamere saidaifa kiyi hakuriii bazansake daukar wata mugunyar shawarrkiba dabaya taso tungurtani yanzukan bazan sauraraba
Larai sunagama wayar tace yaunaji tsinanna nizatacewa inada matattar zuciyaa watoyanzu tafiiison mijinta akaina""
Tayi shiru kumafa gaskiya tafada dantunda tataso itah ce mairike dagidan bansaba dasiyarda komaiba lallai natabbata mai matattar zuciyaa dolene intashi innemi nakaina inhuta dagoriii innemi halalina intsayada kafafuwana""
Zaid yashigo gidan bayan gama wayarta da gwaggo yanda taga yanayinsa yasa tasan balafiyaba""
Dayake wajenta yake saman kujerar yazauna yadafe kansaa"" tace sannu dazuwa yace yauwaa""
Tayishiru tasassauto murya meyake damunka zaid??? Tsaki yadanyi yanakallonta yace daga gidan major nake""
.tace mekuma yafaru agidan?? Yanisa naje ganin haydar ne"" tanazaune saida tamike tace meyake damunsa????
Yagirgiza kai yace wlh bakiga yanda yakomaba"" tunjiya akenemansa kafafen yada labarai saiyanzu akaganshi Ashe yanagida
Zee hartafara kuka tace katashi muje Dan Allah"" yanda take kuka tamkarma zaid dinne bailafiyaa"" mikewa yayi yace dauko mayafinki muje""
Garin dauko mayafi tadauko zani"" saida yakarbaa yamiyar yadaukomata hijab takarba tasaka sukasanarda fauzyy zasuje ganin wani Dan uwan Zainab tace haba anty nimezaihana kujirani nadubosaa
Zaid yace dauko mayafinki mujeto haka sukafito zeelash tazauna baya tace Amarya tashiga gaba dama yaune fitarsu tafarko""
Itah ma tace bazata zaunaba suka zauna baya tare yaja motor din saigidan major
Zaid bakin kofa yatsaya sukuma suka shiga ciki"" mom ce kawai cikin falon kakus da Haneefa sunadakinda haydar yake
Suka gaidaa itah sukaimata yamaijiki Sam batagane zeelash ba tace sukarasa dakin tanuna masu jiki sanyaye suka karasa fauzyy ce gaba sannan zainab
Kakus tana ganinta tamike tana rabka salatiiii tace menake shirin gani zainab wayakawoki wajen jikana
Jin sunanda ta ambata yasaka hadar dago fuska yace Kanwata kece karaso mana kizaunaa bakibude kakus takebin haydar da kallo da murmushi tana kuka takarasa tazauna. Yace wannan kumafa??? Ko abokiyar zamankice
Tadaga masa kaii nansuka gaisheshi sukaimasa yajiki yace yajisauki sosaiii
Gentle ladyyππ½
[10/01 1:28 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 012
By
Aeesha Ibraheem
Dedicated 2
Hafsat M Shareef
&
Haneefa Usmanππ
Yace Amman waike wayafadamaki banda lafiya??? Tashere hawaye tace zaid mana"" baijima dabarin gidan nan ba"" yace ke manta qalau fa nake "" kawaifa ciwona ilham ce kuma tunda bazasu nemomun itah ba mezaisa suyita tallana kafafen yada labaraiii
Tace banganeba ina ilham dinne tashiga??? Kayan ilham dayake rungume dasu yasake kankamesu yace tagudu tabarni dantaga nakamu dasontaa kingafa tabarni darungumar tsumma""
Zainab tace ilham din??? Yace wlh kalleni Kanwata nakoma abun tausayii Amman itah matar gidan nan cewatake inmutu wayayi hasaraaa
Ninasan idan namutu ilham ce mai hasaraa tunda batada kowa saini sukuma sunada Haneefa""
Maganganunda yakeyi tamkar bacikin hankalinsa yakeyiba haka yakeyi da dare yayita sanbatu shikadaiii""" yace waifa ina kukabar maigidan naku????
Fauzy tace yana waje"" yace tokuce yashigo mana kunsan yanzu mutane bata sukeyi kar shima anemeshi arasa "" yalangwashe kansaa kamar karamin yaro yace nima kunga ilham dina narasataa""
Har fauzyy saida tazubar masa da kwallah zeelash tatashi tashigo da zaid"" yagaida mom sannan yakarasa ciki yagaida kakus wacce take tsaye tanabinsu da ido""
Haydar yakalleta yace kakus kinga mijin Kanwata"" namanta banfadamaki ba tayi aure"" yanzun itah kanwatace danhaka banason kinamata gani ganie""
Yasake makale kayan ilham ajikinsa yalumshe ido"" saiyafara wakaae "" a m in love"" yanda yakeyin wakar tamkar shine yayitaa ahankali yakeyin wakar yana gyadaa"" kaii
Rayuwa kenan haydar yazama tamkar bashiba akan soyayya bamaganar zuwa asibitiii kowa yazo ganinsa saiyazubarda kwallah Amman Sam bayayin komai namarasa hankali major saida yasaka akabinciki kwakwalwarsa koyasamu matsalane wajen hadarinda sukayi ganewane ba ayi ba saiyanzu Amman likitocin basuga komaibaa
Kusan duk bayan kwana biyu sai zaid yakawo zainab kakus matasaki ganin haydar bayajin dadin abunda takewa zainab din
Kwana biyu tsakani""" haydar yana kwance mom tashiga"" tana kallonsa "" yanda yakankame kayan ilham motsi yayi hartajuya yace momma""" tajuyo dasauriii tana murmushii tace haydar""
Saman gadon takarasa hannunsa tarike tace sannu"" saman cinyarta yakwanta yace ilham tace indaina fushidake Amman meyasa momma kikace inmutu bakyajin tausayin halinda ilham zatashiga idan taji labarin namutu????
Tana dariya hadeda hawaye tace haydar kasan inasonka sosai bansan yazanyiba ganin kana neman halaka kanka akan mace shiyasa kawai nafurta hakan Amman baharcikin raina hakan yake nufiba""
Amman kayi hakuriii kaji Dana ainima banason katafiii kabar ilham dinkaa"" kakwantarda hankalinka ilham zata dawo gareka
Yayi murmushi yace nasani ai kullumfa sainaga ilham shiyasama kikaga nadaina damuwaa yanzun ma da itah nakefirah tacemun intashi gakinan kinshigoo
Mom tace waini haydar inakataba ganin anyi hakan magana dawani acikin barciii"" yace soyayya kenan "" momma zuciyoyi guda biyu sukanhadu suyi magana tamkarma atare suke "" ilham dina tana nan"" yayi nuni dasaitin zuciyarsa""
Mom tace Allah sarki Allah yabarka da ilham dinkaa yace Ameen momma dat why love u muaah"" kinsan me momma waishi dad saidai yayita banihakuriii nikuwa duk Wanda zaibani hakuriii inhakurah da farincikina haushi yakebaniii
Yalumshe ido wayyo ilham dina ranarda zakidawo gareniii nikawai nasan irin dunbin farincikinda zanyiiii yayi shiruuu natsayin lokaciii yace momma laifinane ko?..
Nakiyarda da soyayyar ilham bayankuma nadade inasontaa aganina kodana fadamata bazata yardaba zatace akan wani dalilinane kawaiii
Amman yanzu zanfadamata babu ruwana koda zatayi gunduwa gunduwa danie"" ina nan inataramata shinki shinkin kalamai"""
Yauwa mom kisanarda dad gidana "" dazaran ilham tadawo acen zamutare nagaji dazama tsohon gidansa acen zamuyita soyayyarmu da ilham""
Lambon bayaa asare bishiyoyi huduu ashukamun furanni farare dakuma jajaye""" asamu masu banruwa dakuma kulada su"" kullum arikayi masu askiii inason ranarda zanfallasawa ilham sirrin zuciyata yakasance wajene mai cikeda ni ima"" da kyawawan furanni masu fitarda sihirtaccen kamshiiii
Yakasance akwai korama daga gefe ruwa masu kyau suna "" gudana tareda kukan tsuntsaye tamkar suna rera wakaa yasake rungume kayanta yace bansan yazanji aranarba wane irin yanayi zanshiga Wanda bantabajin irin yanayinbaa
Yafitarda sihirtatten murmushiii aranar zanfikowa murna zankasance danlele awajen ilham
Please ilham come to mee!!!! Am weetin......π£π£
Gentle Ladyππ½
[10/01 1:28 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 013
By
Aeesha Ibraheem
Dedicated 2
Hafsat M Shareef
&
Haneefa Usmanππ
Dakarfi yayi maganar "" mom tace haba haydar waime yakesawa kana yin Abu kamar Wanda baiyarda da kaddaraba ina ilham zatajika yanzu kasan awacce duniyar take???
Yatashi daga kan cinyarta yace momma yakikeso inyi wlh nayarda da kaddara wannan abun shi akekirah jarrabawar so
Kowane Dan adam(RUFAIDA) yakan fuskanci tashi saidai tawanin zataadara tawani karkiji tausayina dannine najawa kainaa
Gashi yanzu ina nemanta alokacinda ganinta yamun wuyaa inasonjin muryanta yayinda samuwar hakan yayimun wuyaa inason ganin kyakkyawar fuskarta ma abociya murmushi Amman bansamu damar hakanba
Allah sarkii weety ashekema hakan kikeji lokacinda kike rokona harkasa infurta maki inasonki koda bahakanne azuciyataba Amman nacire kafata nabar kasar "" gashiyaΓ±z u inasoΓ± sanardake inasonki amman kinyimun nisaa yashare sirarun hawaye danasan hakan kike azabtuwa da soyayyata dabanyi watsi da damataba gashi ke kinyi jinyar sona natsayin shekara shida Amman ni nakwana biyar jibi yanda na lalace
Kowaye yace yanasonka baidace kaki karba tayin soyayyarsa ba wannan karatun bansanshiba saiyanzu
Yakalleta yace momma hakika soyayyar ilham tsabtatacciyace zuciyata tana karyata soyayyar kowa daga karshe kuma sainaga karyarce
Amman haryanzu zuciyata takasa karyata soyayyar ilham menene ranar soyayyar da za ayimaka tadan wani lokaciii ni inabukatar soyayyace wacce zata dore nadade ina kokonto kohakan zaifaruuu
Momma ayanzu mafiyawancin soyayya basaboda Allah bane zakaga mutane suna baibayeka kokai dansiyane sunaso idan kaci kadaurasu akan wanni mukamiii kokuma kabasu kwangilaa toduk ranarda kasauka daga mulkiin bazakaga kodayaba karen layinsuma yafika daraja haka zasu juyaa akan wani maimulkin wannan soyayyar karyace
Momma wani yakance mawakine yanayin wakarsa anasonsa sosai kawai danyadaina waka saikiga andaina yidashi Allah yawadaran irin wannan soyayyar
Waishinku aladole saiwanda yake damawa shikukeso??? Meyasa bazakuso mutum Dan Allah ba "" idan har kunason mutum tokoda saboda wani dalilinne dagabaya babu dalilin kusosi ahaka wannan itace soyayya koda kamutu bazai manta dakaiba inaso masu karatu kunatsu kugane inda maganata tadosa wlh mafiyawan wanda suke zagaye dakai basonka sukeyiba
Ni inason masoyane wadanda kobayan raina zasu tunadani suyimun addua bawai wayanda nake rayenba sukamanta dani to inagakuma nakwanta damana wannan soyayyar banzace wannan soyayyar banyarda da itah baπ
πΌ
Yasakeyin murmushi momma ilham taci jarabawa kuma wlh bana shakka akan soyyyarta akan ilham nayarda da soyayya ashe bakowane bayason gaskiyaba akwai masu soyayyar gaskiya dafari bugudaya nayiwa kowa harnake karyata soyayya""
Hmmm anan zanyiwa HAFSAT M SHAREEF jinjina kafin asamu kamarki abune mai wahalaaa ninayarda dahakan""
Momma tayi murmushi tace haydar aini nayarda da abunda kakefada batun yaubaa Amman kadaure kadaina surutunnan haka wlh hankalina tashi yakeyi sosai banason kazauce akan soyayya
Hnmm momma kema kinasona ko??? Bakyason kirasani????
Tagyada kai sosai"" yace kinajin haka ballanta ilham yanzu bansan metakejiba nine kawai nataa kekuma kinadani ga haneefa gakuma mamanki ga babanki "" gakuma dadyna
Kinraba soyayyarki gida biyar Amman itah ilham duka soyayyarta akaina take yakike tunanin takeji awannan yanayi ninasan tasan halinda nakeciki Amman yaushe zakazo gareni
Yajuyo da fuskarsa sosai yace momma please kitaimaki rayuwata wlh jinakeyi tamkar bazankai wayewar garin gobeba idan bansakata a idonaba
Yayi shiru nasan yazanyi zankai kukana wajen mahaliccina nasan zaisharemun hawaye zaiyimun abunda babuwanda zai iyah yimun"" mikewa yayi yashiga toilet mom tabishi da kallo gwanin tausayi hakika yaronta yana wahala da soyayyar ilham Amman kuma shine daidai tundahar yaki yasanarda itah tanabinsa yanawani gwaletaa
Haydar ne yafitoo yadauro alwala yasake bude labule yana kallon zanensa yayi murmushi sannan yaje yashinfida darduma yafara sallah""
Mom takurawa zanen ido bata tabaganinsaba kenan daman wannan zanen ne ilham takeyi ta iyah sosai
Haydar tunda yafara sallah saida mom tagaji tabarmasa dakin""
Tundaga ranar saikuma haydar yadaina surutai kullum kashigo dakin zakasameshi yana sallah ko addua dazaran yagamakuma zaisake tada ikama
Badare barana barci kuwa saidai idan yasaceshi kuma dayafarka zaisake dauro alwala yasake cigaba
Azumikuma litinin da alhamis yanakai kukansa Allah yasa ilham tadawo gareshi duk indatake
Gentle Ladyππ½
[10/01 1:28 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 014
By
Aeesha Ibraheem
dedicated 2
Hafsat M Shareef
&
Haneefa Usmanππ
4 Months letter
Abubuwa sunfaru dayawa farincikin gidan major duk yagushe saboda danlelensa yakoma kalar tausayiii gabagaya suma tabata masa fuska shiya manta yanda akeyin aski ballantana kwalliya wankane kawai yazama dole yayi""
Yayi rama sosai kuma yayi haske har izuwa yanzu bayan masallaci bayazuwa ko ina"" Haneefa takoma kano dancikinta yadan taso koshi dakyar akasamu takoma "" saida mom taso nunamata bacin rantaa""
Haneefa tace wlh mom ya haydar tausayi yakebani nibansan waye yabawa ilham shawarar guduwa tabarshiba !"mom idan kinsan inda take Dan Allah kisanardani nizanje indawomasa da itah ninasan ilham bazata taba barin ya haydar ba koda bayasontaa
Mom tace shawara takeyi dani kokuma sanda tatafi tasanardani"" karnasakejin kinyimun wannan maganar kuma kidau kayanki kikoma wajen mijinki da yaronki dankwae kinsamu miji mai hakurii ace wata daya kina zaune anan saidai yazo yaganki toyau kafarki kafarshi kokuma inhadaki da haydar kinsan kullum saiyace miki kikoma wajen mijinki kicemasa bakyajin dadi""
Tace naji nidai mom zankoma Amman Dan Allah kifadamun inda ilham taje "" tatsuke fuska wainikam yaushe nazama abokiyar wasarki??? Bacemun daganie"
Haneefa tawuce tana gunguni ranar tabi mujaheed suka koma kano saidai tarikayimasa wayaa
Nomber ilham kuwa duk safiyar Allah sai haydar yayi train din ta sama dasau hamsin kozata shigaa tex Kuwa na soyayya yaturasu babu adadi koda zatabude tagansu
Amman shiru babu amsa """ kullum yanasaran jinkiranta awaya Amman shiru
Zeelash ce zaune adaki tabuga tagumie hawaye sunabin wasu tana sharewa "" tunranarda fauzyy tafara rashin lafiya akace tanadauke dajuna biyu hankalin zeelash yatashi kullum saitashige daki tayita kuka itah kadai
Tasan ta aikata kuskure gashi yanzun itah ma tanason ganin jininta sosai fauzyy take burgeta ganin yanda zaid yakeyin nan nan da itah"" bayason yajitayi koda dogon motsi dukda yanadan daurewa yanuna rashin ko inkula yadaina rawar kafaa ganin zainab kamar batajin dadin hakan""
Zeelash tashare hawayenta zaid wanda yake tsaye bakin kofa yana kallonta jiki sanyaye yakaraso inda take"" saman kujerar yazauna yajawota jikinsa saitasake fashewa dakuka tashige jikinsa
Bayanta yakeshafawa ahankali yana rarrashinta yace haba zainab ninarasa gane abunda yake sakaki kuka "" kukan nan nakiyana konamun rayuwa""
Inajin kamar banrike amanarda haydar yabaniba kullum naje gidan saiya tambayeni kinacikin jindadi duk dashidin bayacikinsa
Kenan karya nakemasa bayankuma kullum saikin zubarda kwallah kuma nayitambayarki harnagaji Amman kinki kisanardani damuwarki
Kifadamun mekikeso zainab komenene shi indai inada halinyinsa nizanyimaki"" tadago takalleshi kai tagirgiza tace bakadashi zaid wlh bakadashi "" aduniyar nan babu wani mahalukinda yakeda abunda nakeso kudi mulki sarauta duk bazata samamun abunda nakesoba
Katayani da addua Allah shine kawai yasan maganin kukana"" ninasan bazan daina kukaba har abada dankomai yasameni laifinane!!!! Kuma wannan yakasance izna kuma ishara gamasu irin halinaa
Tashare hawaye zaid karka tambayeni menene musabbabin kukana danbazan iyah fadaba fatana kacigaba dasona harnakoma ga mahaliccina karwani abu danarasa atattare dani yasa kajuyamun baya kanuna halinko inkula agareni
Soyayyarka kawai takan ragemun radadin abunda yakedamuna idan nawayi gari kaidanake tinkaho dakai kajuyan baya yakake tunanin zanyi ???kuma mezanji
Yanisa zainab haryanzu kina kokonto akan soyayyarda nakemaki???? Wlh ni duniya banga abunda zai karkare sonki arainaba "" ruwa ko iska dakwai ko babu "" lafiya ko akasin haka arxiki ko talauci "" sanyi dazafiii rani da damina babu abunda zai kwantarda guguwar sonki acikin raina haryanzu banga watamace wacce tafimun kebaa kecedai arainaa haryanzuuu idankuma kina tantama da soyayyata kigwadani kiganie
Tarungumeshi ah ah zaid nayarda dakai kuma nima inasonka sosai"" yasake rungumeta yana murmushi
Mom ce tashigo dakin yanxu zuwanta na uku kenan tanasamun sa yana sallah bai sallameba"" tayi tsaye tana kallonsa ganin yanayin tahiyaa "" yana sallamewa yafara addua
Waje tasamu taxauna haryashafa zaikuma tayarwa tace dakata haka malam liman wajenka nazo zamuyi magana"" yajuyo yakalleta saiyakoma yazauna yace inawuni"" tace qlau yace wacce maganace momma inafatardai maganar dazakimun wacce tashafiii ilham ce ???? Idankuma batasha fetaba
nidai banasonjinta"" mom tace to sannu ubana nishikenan banda ikonyin magana dakai dole sai idan akan ilham ne ??? Card tamika masaa tareda kudiii yakalleta batareda yakarbaba yabi hannunta da kallo sannan yace wannan kumafa???
Tace saika karba sannan "" hannu yamika yakarbo"" yace ticket??? Mekuma zanyi da ticket??? Tace Dubai zakaje"" idanuwa yazaro yace nidin momma mekuma zanje inyi a Dubai niko kadan wlh banason fitaa ko ina
Tace to kaji nanemeka shawarane??? Umurni nakebaka"" aikenka zanyi cen"" sannan kuma kafin kaje kasamu ka aske wannan mugunyar sumarda katara afurkarka kamar Wanda yayi shukaa
Hannu yasaka yashafo fuskarsa yana kallonta yace aski kuma ??? Menene alakar tafiyana dakuma sumar fuskataa??? Tace saboda inda zanturaka yar Kawata nakeso idan taganka taga kayimata saikudaidaita kafin kadawo
Yace what??? Yanzu fisabilillahi momma sainaje Dubai dole??? Amman kinsandai bakiyiwa ilham adalciba
Gentle Ladyππ½
[10/01 1:28 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 015
By
Aeesha Ibraheem
dedicated 2
Hafsat M Shareef
&
Haneefa Usmanππ
Tace saikuma Kayi Amman zuwa Dubai dole danbansan wanda zan aikaba kaine kawai Dana idankuma niban isah dakaiba sainaji""
Yace bancefa hakaba momma Amman zancen yarinyar nan abarshi"" mom tace bazan barshiba nisonake kakoma kamar yanda nasanka ada haydar inda nasani maiyawan kwalliyane mai tsaftane kuma Dan gayune
Wanda magana bata shamasa kaibaa natsattsene "" ma aboci murmushine akullum zakasamu fuskarsa kumshe da murmushi Amman sabanin yanzu haydar duk kasauya zuwa wani haydar din daban inason samun chanjii daga gareka
Momma bazantaba komawa haydar inda kikasaniba wannan haydar in na ilham ne komai zanyi xanyine Dan ilham tagani tayaba toyanzun inatake babu amfanin nayi murmushi saboda wacce nakeyin murmushin saboda itah batakusa dani
Babu amfanin yin fara a"" duhune nakegani hasken fuskata bata taredani"" zandawo kamar yanda kikasanni Amman sairanarda idona yayi tozalida zinariya ma abociya haske acikin kowanne irin haske
Saikunnuwana sunji dadddar muryanta maikoremun damuwa arainaa
Sai gangar jikina taji dimin jikinta alokacin zandawo cikakken mutum "" zanje kamar yanda kikeso Amman bazan iyah sonwata yaba aduniya bayan ilham
Mom tace saidai idan bakagantaba wlh yarinyar tahadu kaman mamanta"" baki yatabe bandamuba niba haduwa nake nemaba momma wlh duk yammatan duniyar nan tamkar maza nake ganinsu inhar akahadasu da ilham diina"" kuma nibabu askin dazanyi
Mom tace kaikasani "" kajedin ahakan ammanfa idan hartace kayimataa tokanadawo wa saibukiii"" kaje kayi wankaa kuma kashirya kayanka Dan jirgin safeee zakabiii yace babu bukatar sainaje dakaya dan goben zandawo komai dare""
Tace waikai zumudin me kakeyi idankuma yanayin garin dakuma yanmatan garin sunyimaka kaji kana bukatar sake zama kona kwana biyune takenan kuma bakaje dakomaiba""
Yace banajin yanayin garin zaiyimun tunda ba ilham ce acenba "" goben zandawo menene address din gidan???
Idan kaje zakasamu Wanda yaje tarboka dannafada mata zuwanka zata turah adaukoka kalurah dakyau kakarewa yartata kallo kyakkyaawace sosai inayimaka fatan Alkhairi akan soyayyarku
Yace ba ameenba"" ni wlh batayimunba "" haba momma yanzu banda tallana dakukai kafafen yada labarai tamkar yadin sakawa shine har wata kasar kuma kika aika da tallana""
Mom tamike ah nayihakan danfarincikin Dana yadawo""" yace baburana momma nidai da dayanda zanyi wlh dabanjeba Amman bakomai Allah yamayarmun da alkhairii ninazama gwanjo tunda ilham takini sai akoma tallana""
Mom fitah tayi tana dariyar maganarsa"" babukuwa abunda yayi washe gariii sha daya sukaje airport din abuja harda major da kakus yanrakiyaa
Kakus tace nidai maigida kaduba yarinyar dakyau yanda naji hafsatuuu tanacewa nasan yar mutuncice tsaki yayi yajuya wajen major yace dad karfe bakwai katuro driver yadaukeni anan anjima """ yawuce baisake cemasu komaibaa"" sunatsaye suna kallonsu harsuka shiga jirgi saida yadaga sannan sukajuya gidaa
Haydar tunda sukashiga jirgi yaji wani Abu aransa saitsaki yakeyi yana ganin antakurashiii ""
Biyar daidai suka sauka felin jirgi !""Dubai Yasauko yana raba ido ina zaiga kuma wanda yake nemansa"" wanine yakaraso da pic ahannunsa yana waya yace ah naganshiii yakaraso yabawa haydar hannu suka gaisaa""
Yace nine nazo daukarka ur welcome"" yace tnx Amman Dan Allah zan iyah samun ticket nakomawa Nigeria yaudin nan???
Yace mezaihana Amman saida cuwa cuwa"" kasan komai saida kudiii yace tomuje kakaini danyau nakeson komawa yace toshikenan"" cikin sa akuwa yasamu amman jirgin saikarfe bakwai zaitashi yace babu matsala tunda har bazaikwana garinba takwana cikin saukii
Saida yabiya masallaci yarama sallar da akebinsa azahar da la asar sannan yacewa mutumen suje""
Sun soma tafiya yace kayi hakuri natsaidakai ko??? Yayi murmushi don't worry its my work"" haydar yace nagode sosai""
Yace nima haka"" nakanso tarbar irinku masu fara a"" koba komai zanji nishadiii kafin murabu"""
Haydar ya jinjina kaii daidai kofar wani Dan madaidaicin gida mai kyau mutumen yayi pkng""
Yafito yacewa haydar bisimillah yaturah kofar get din yashiga gidan mai kyaune akwai yalwatattun shuke shuke gasunan tsanwaye sharr gwanin sha awa
Gidan tsitt yake saikukan tsuntsaye haydar yalumshe idonsa yabude sanyi yaji yana ratsashi tako ina"" aransa yace inama zanga ilham irin wannan wajen"" muna gudu cikin nishadii ingoyata abayana inatafiya cikin farinciki
Yasake lumshe idonsa iska takadomasa mai matukar sanyiii inasonki ilham wannan yanayin yasa naji gidan nan yaburgeni""
Mutumen ne yakatsemasa tunaniyace yallabai munkawo saika karasa nizan koma"" yabashi hannu suka gaisa sannan yajuyaa
haydar yadade tsaye wajen yana kallon wasu tsuntsaye guda biyu daganinsu masoyane suna wani kuka tamkar masu rera waka"" ahankali yataka zuwa karamar kofar gidan yadanna kararrawa""
Sam yadaina wani murmushi dankarma yarinyar taganshi taga damarsa saida yasake knock sannan yaji alamun mutum dauke kansaa yayi yana kallon shuke shuken wajen"" akabude kofar dakarfi yaji ance ya haydar!!!!!
Ciikin kidima yajuyo yaga wacce take kiransa muryarda ko acikin mafarki zai iyah banbance me wannan muryar bakinsa yana sassarfa yace il il ilham"" kece hannu yasaka yamurza idonsa yabude yakuma gantaa kuka tafashe dashi tafada jikinsaa"""
Tace ya haydar nayi kewarka sosaiii "really miss you yadade yana gasgaza wannan al amarin ganin yakeyi tamkar amafarkine hannuwansa yamiyar yarungumeta tsam yace miss u more weety
Gentle Ladyππ½
[10/01 1:28 am] Banyarda da SO ba: π₯BANYARDA DASO π₯BA!!π
π»ββπ
π»ββπ
π»ββ
π₯
π₯ π₯π₯π₯π₯
PAGE 016
By
Aeesha Ibraheem
dedicated 2
hafsat M Shareef
&
Haneefa Usmanππ
Sosai jiyakeyi tamkar yamaidata cikin jikinsaa"" ilham mahaka kuka takeyi sosai"". Dagota yayi daga rungumarda yaimataa yasa danyatsansa yana sharemata hawaye murmushine kwance akan fuskarsa itah ma haka""
.
Yace weety daina yimun hasarar hawayenki bagashi nazoba"" saiyanzu taduba bayansa tace tare dawa kake??? Yaduba bayansa yace bakowa
Hannunsa taja suka karasa cikin falon"" shikanshi yahadu sosai ga fulawoyinan masu kyau"" saman kujerah ta zaunar dashi tace bari nakawo maka ruwa"" harzata wuce yarike hannunta""" zamewa yayi daga kan kujerar yarage tsayinsa akan guiwarsa """ dasauri ilham tace please ya haydar katashi yatsanshi yadorah akan labbanta yace karkice komai ilham
Nadauki akawarin cewa zan fallasa maki sirrin zuciyata duk ranarda idona yayi tozali dake"" cikin kasalallar murya yakirah sunanta ta amsa "" ahankali yace I love u"" cen kasan makoshinsa kalmar tafitoo"" tamkar maiyin rada wani irin sanyi ilham taji tsikar jikintaa tatashi yarrrr tundaga danyatsanta hartsakiyar kantaa
Wani abuutaji taji yana gudana cikin jininta idanuwanta talumshe wasu hawaye masu sanyiii suka sauko akan kumatunta farincikine marar misaltuwa yaziyarceta"""
zamewa tayi itah mataduka """" tace ban ban fahimci maganarkaba kasani arudani kana nufin wai kana sona ya haydar??
Ya lumshe idonsa yabude yace sosai ilham bawai bane inasonki ni haydar nadade inasonki ilham tunranarda ammie tazodake hospital
Inasonki ilham wannan kalma bantaba furtawa wani mahaluki irintaba face ke "" kuma dagakanki bazan sake furtawa wata makamanciyar wannan kalmarba""
Ilham rayuwata zuciyata murmushina walwalata duka nakine"" dawani bawa yanada ikon cire zuciyarsa daga jikinsa yabawa wani babu shakka nine zanzamo mutum nafarko dazaifarayin hakan""
Ilham Dan Allah kijitausayina karkisake gujemun wlh nashiga tashin hankali ranarda nawayi gari banjiki akusadaniba "" nashiga rudani lokacinda nayi arba da takardarki"" komai kikeso zanyimaki inhar zaki yarda da soyayyata"" hawayene suka sauko akan fuskarsa
Hannunsa tadamke tana girgiza kai tace ya haydar menene makomar soyayyata idan harnagujeka ??? Menene ribar soyayyata inhar zanga kana kuka batareda nawanke maka damuwarkaba
Bantabajin haushinkaba kodaya "" bantabayin danasani akan sonda nakeyimakaba yatsanta tasaka tana sharemasa hawaye tace ya haydar inasonka fiye dayanda nakeson rayuwata karkaso kaji farincikinda nakeji yanzu dakafurtamun cewa kanasona
Sake rungumeta yayi yace nagode sosai weety nagode"" sunbatarta yafarayi"" akan wuyantaa"" ilham tasamu kanta damiyar masa da martanie"" hmmm masu karatu kuna ganin akwai abunda zaidakatarda haydar da ilham wajen nunawa junansu yanda sukayi missing din junansu banajin akwai koda nice nafito nace banyardaba hhhhhhhπ
Tsananin yanda jikin haydar yake