Ina,Bayan sun Gama da cikin garin sai suka koma wajen gari, katsam suka Shiga Suleja Khairat na ta siyar da katinta,A cikin yaran guda Daya ya gane Khairat yace wannan ce,Khairat Bata sani ba suka dauketa hotuna da video tana ta faman bin motoci tana tallan katin waya sai tsalle tsalle takeyi sabo da kuruciya ko gajiya batayi.
Yaron Hunaif ne yayi parking da motar ya siye Katin wayar Khairat gaba daya ragowar na dubu Bakwai ne a hannunta,Khairat sai Murna takeyi an siye Mata Kati.
Da murna yaran Hunaif suka sameshi a katafaren Office dinsa dake birnin tarayya,Yaron ya dakko katuwar wayarsa yace Sir ga yarinyar nasan wannan itace,Video na Khairat tana tsalle tsalle ya nunawa Hunaif shi kanshi Bai San sanda yayi Murmushi ba ganin yanda take tsalle tsalle Akan siyar da kati,Pics dinta yayi zoomin tabbas itace Nan take ya jika yaran nasa da kukade yace ya za ayi tazo inda nake Ina so muyi fada da ita na gani ko Zan iya tunawa again I think Memory na zai iya ajiyeta .
Babban yaronsa Usman yace ai Zuwa zamuyi muce muna bukatar Kati na dubu dari oganmu Yana nema Amma idan ta Saro tazo da kanta ta kawo maka sai mu Bata Address da Number wayarka Kuna magana.
Murmushi yayi cikin Isa da Izza Yana wani juyawa a kujera sanye cikin hadaddun kana Nan Kaya Yana rike da biro a hannunsa yace Good Idea aje ayi hakan Ina son ganinta gobe.
An Gama sir cewar Usman suka fita suna Jin Dadi yau sunsha kudade duk da cewar Yana musu kyauta ko yaushe Bayan albashinsu Amma na yau yafi na kullum,Nan take suka koma Suleja lokacin Khairat tana cin abinci a runfar Ladi,Usman ya Karasa har gabanta inda suke zaune tare da Ladi,Khairat taga wanda ya Mata ciniki yau ta washe Baki tace Ina yini? Yace lfy tare da gaisar da Ladi sannan yace Ogana ne yake bukatar Kati na dubu dari idan har zaku siyar Masa,da sauri Khairat tace me? Yace Kati na dubu dari Kinga idan kika Saro sai ki siyar Masa ki samu riba,dazu na siyi katinki naji dadi shi yasa na kawo Miki hanyar Karuwa,Khairat tace dubu dari fa kace,Ladi tace to yaro siyarwa shima zaiyi? Usman yace a waya zai sa ko kudin Sunyi kadan a Kara dubu dari biyu? Khairat tace Sunyi yawa sai Gobe idan na siyo Taya zaka Karba to? Number ya Bata yace gashi number Ogana ce ki nemi number sai ya Baki Address ki Kai Masa,Khairat taji kudi Bata ji tsoron komai ba ta karbi Number sannan ta Basu Tata number din suka tafi.
Ladi murna takeyi tace Bari anjima naje banki na Ciro kudin gobe da wuri zamuje mu Saro katin sai a Kai masa.
Washe gari kuwa 11am Khairat ta Kira Number Hunaif,Wanda tuni yaransa sun bashi number Khairat yayi Saving,Yana Office ya ga kiranta sai da yayi Murmushi sannan ya daga ba tare da yace komai ba,tace Hlo Good day Sir, me siyar da kati ce, katin ko a maka Transfer kawai a waya? Murya ya canja yace no Haka nake sonsa a takarda Yan 1k a kawo min inda nake,Khairat tace to sai ka tura min Address naka, Alright ya Furta tare da datse Kiran, Khairat tace wannan wanne irin mutum ne da baya Jin kudi? Ta bawa kanta amsa da Maybe wani shugabane a kasar nan.
Sanye take cikin doguwar Riga red and Golden da Dan Hijab dinta me hannu madaidaici ta yiwa Ladi Sallama ta Shiga taxi tana bin Address din Office dinsa daya bata har ta je katafaren Building dinsa dake Asokoro,ta kirashi a waya gani a Office din naka,yace ki shigo ga yarona zai Miki Iso,Ok tace ta kashe wayar ta Shiga sai kuwa ga Usman ya fito da fara'a yace Hajiya me Kati biyoni a baya,Khairat tayi Murmushi ta bishi suka Shiga lifter sai gasu a bakin Office din Hunaif.
Knocking Usman yayi daga ciki suka ji yace Come in,Usman yana bude Office din wani kamshi da sanyi ya daki Khairat ta lumshe Ido tana kallon katafaren Office din kayan Alatu da gani kasan na Yan gayu ne.
Sanye Hunaif yake cikin farar shadda Kal Tasha dinki me azabar kyau na Yan zamani,sheki da kyalli kawai yakeyi ya Kara wani Masifar kyau.
Juyowa yayi lokacin tuni Usman ya fita,Khairat kawai sai taga Hunaif ne Ashe,Haushinsa take ji baya tunawa da ita ya yaudareta,yanzu Kuma me yake Shirin Yi Mata,Fuska ta hade ta Mika Masa katin da yawa a wata Yar jaka,kallonta yayi Yana mamaki to wannan a Ina ta sanshi ne? ga katin ka karba Zan tafi Ni ta Furta da Shagwaba,Murmushi yayi tare da kallon katin yace Kije dashi kawai,Khairat ta kalleshi ban gane ba? Dama rannan Ina Jin haushinka ka fasa min Powder me tsada yanzu kasa na kawo maka Kati baka biya kudin ba,kudin Powder nawa ne? ya Furta tare da Mikewa tsaye ya matso kusa da ita, tana turo Baki tace dubu biyu ce ehe Nan take ya zaro Bundle na 1k da dubu Ashirin a Kai yace gashi har kudin Powder da kudin mota 5k,Khairat mamaki ya kamata baya Jin kashe kudi dama tasan shi tuntuni,Katin ta Mika Masa yace Kije ki bayar kyauta ko ki siyar ko ki zubar duk abinda kike so kiyi dasu,Khairat ranta ya baci ya sata wahala a banza a wofi, kamar zatayi kuka tace amma ka sani wahala nazo har cikin gari? A fusace ta fita ta bar Office din tana goge kwallarta wani son Hunaif ya Kara taso Mata,ace Wai baya iya ko nuna alamar yasanta ma.
Hunaif Kam yace to fushin me takeyi? Baki ya tabe yaci gaba da aikinsa, Khairat Kuma tana komawa Gida ta sanarwa Ladi me ya faru ta cire dubu Ashirin dinta kudin mota Dana Powder ta bawa Ladi dubu darinta sannan suka siyar da katinsu riba biyu Ladi taji dadin wannan harka.
Tunda Khairat ta bar Office din Hunaif ya kasa komai sai tunaninta yanda ta Bata Rai tana Masa masifa da Shagwaba,har Murmushi yakeyi shi kadai,Haka daya koma gida ma,Ummi taga canji yau Yana farin ciki taji dadin hakan domin ta Dade Bata ga ko Murmushin Danta ba,ta tambayeshi me ya faru yaki sanar Mata yace ba komai kawai.
Washe gari daya tashi daga bacci kawai sai ya sake tuna Khairat kaf abinda ya faru dashi jiya tare da Khairat ya tuna Amma baya tuna na komai sai na Khairat,Haka yaje wurin Doctor ya sanar Masa,Likitan ya sake gwaje gwaje yace yarin Yar Nan Zata taimaka kwarai wajen dawowar memory naka.
Tunda Zainab taji Khairat tace su Talatu sun kusa tashi zuwa kasa me tsarki kullum ta damu Khairat da waya yaushe zasu tashi, Khairat ita kanta taji Zainab ta dameta kawai sai yau tana ganin Kiran Zainab tace Su Talatu su shirya su tafi Airport yau jirginsu zai tashi.
Talatu ta gigice ta Shiga makwafta tace to jama'a a yafi juna mu Allah ya kawo tashinmu,abinda Kuka yi min na yafe muku Kuma ku yafe min,Su Rahinatu harda kuka za a rabu da iyaye,Talatu an Nemo Taxi sun shirya da jakarsu Kawu ya fashe da kuka ya rike Hannun Rahinatu yace to Rahinatu ko mu dawo a raye ko ba mu dawo ba ku rike zumunci,ku kaunaci junanku,Talatu tana goge Hawaye yace ke Zainab ki rungumi kannanku kafin mu dawo,Bayan Sunyi Sallama da juna suka wuce airport, Bayan sunje Airport sai Talatu ta Kira Khairat ta sanar Mata,Khairat tana ta dariya tace yanzu za a zo a daukeku za a kaiku wurin Screening,Aiko sai ga wani mutum me Gulf yazo duk cikin aikin Khairat ne,yace Kune Talatu da Kawu?,da Sauri Talatu tace ae mune,yace ku Shiga Mota mu tafi inji Khairat,Sai da Talatu ta shigar da Kawu sannan itama ta Shiga mota suka tafi,kawai Bawan Allah ya mike hanyar Niger,gudu yake tsalawa tun su Talatu na tunanin an kusa zuwa suka ji Shuru.
Kawu yace Kai yaro ko Makkah zamu a mota ai sai Haka wannan irin nisa Haka,Driver yayi banza dasu gudu yake shekawa kawai har suka Isa Katsina suka wuce katsina state suka dauki Hanyar Niger.
Sai da sukayi tafiyar 5hrs lokacin sun Shiga kauyukan Niger can yankin Sahara,ba gida gaba ba gida baya,sai tarin Sahara da Rana kwal ba ko ruwa kusa Babu bishiyu ko wani koren gayye Babu,Talatu ta fashe da kuka,Kawu yace lfy a Ina muke? Talatu tana kuka tace Bangon duniya ya kawo mu,Malam ka taimakemu,cikin Dajin ya gangara sannan ya fito ya kwace wayar Talatu da Kawu ya jefar musu da jakarsu yace ku fice min a mota, Bayan sun fita yaja motar Sa yayi tafiyarsa ya bar Talatu da Kawu Makaho a wajen,Talatu tace ya zamuyi? Kawu yace kwadayi mabudin wahala Yi min jagora mu tafi ko zamu ga wani kauye sai muje a samu a hanya mu koma Nigeria, Talatu ta Fara tsinewa Khairat,Kawu yace wannan yarinya Allah wadaran Halinta,wlh idan muka koma gida sai nasa Soja ya harbe ta.
Talatu taja Hannun Kawu suka Kara nausawa cikin Dajin Sahara suna tafiya,yunwa da kishirwa kamar zasu mutu.Talatu ta rushe da kuka Kawu Kam ya rasa abin cewa ta kansa yakeyi kawai.
Khairat kuwa tace Nayi maganinku Talatu kafin ku dawo sai kunyi nadamar halayenku.
Hunaif ya gaji da tunanin Khairat, kawai ya Umarci Usman Daya binciko Masa gidan da Khairat take sannan wanne time suke komawa Gida Bayan sun Gama sanaarsu.
Usman ya sanar Masa da Address din gidan sannan yace sai 5pm suke komawa Gida, ba tare da Hunaif ya nemi Driver ba da kansa yake Driving ya tafi gidan su Khairat 7pm na dare,so yake yasan Taya ta sanshi,sannan me yasa indai sun hadu sai ya tunata da safe,baya tuna kowa sai ita,me yasa Memory dinsa yake tuna Khairat kadai.
Lokacin Khairat ta fito siyen Maltina a wani kanti ta tafi gida wani Dan wiwi marar mutunci ya tare Khairat a hanya yace ke marar kunya ke wato kinfi karfin kowa ko Akan ance Ana sonki har wani Shan kamshi kike Mana ke Wai Dan kina da kyau ko? Harda wani siyo Maltina guda biyu Zaki Sha ke ba maaikaciyar Gomnati ba ba komai ba,ke ba Yar kowan kowa ba harda wani Zaki Sha Maltina,karuwar banza ai duk mun San irinku Sumi Sumi a hijab, shekeke Khairat ta kalleshi ita dariya ma ya Bata Wai Maltinar ma da zata Sha bakin ciki yake mata,tace to bana sonka ko Dole ne,duk mazan duniya na rasa wa zan so sai irinka Dan wiwi,Kuma Ni ba Karuwa bace Kaine babban Karuwi tunda Ni Karuwa ce Kai kuma fa Karuwi ne?
Hannu ya daga da niyyar zabgawa Khairat Mari saiko wani zukeken hannu me laushi ya rike Hannun Dan Wiwi Wanda ake kiransa da Me Dawa,Khairat ganin Hunaif ne sai ta Fara kuri ai da ka kyaleshi ya taba fuskata ya tabowa kansa bala'i da Jarabar duniya,da ka barshi ya jawa kansa barin Suleja ba tare da ya shirya ba,Da yatsa ta nuna Me Dawa tace ka kiyayeni nafi karfin Wanda ya fika ma,ba a ja dani,Baki Hunaif ya bige Mata tayi sauri ta rufe bakin ta tsuguna a kasa tana Yar Kara taji zafi, Kudi ya zaro Wanda Bai San ko nawa Bane ya mikawa Me Dawa,Me Dawa ya samu kudin wiwi ya dinga murna Yana sai Oga Allah bar Mana Oga,wannan kanwarka ce? Hunaif yace ae,shike Nan na kyaleta Amma ayi Mata fada Bata da kunya Zan iya take Mata wuya watarana,Khairat day sauri ta dago da kanta tace ka take Mana.....kafin ta rufe Baki Hunaif ya rankwasheta,Kara ta saki da salon Muryar Shagwaba tace Wai me na maka ne? Ka daina takura min,me ya kawoka gidanmu ka daina Bina Hawaye ne ya zubo Mata na tunanin irin son da takewa Hunaif.
Fuskarta ya leka ta matsa baya tana boyewa Dan kar ya gani,kuka kikeyi? Tace a'a Ni ba kuka nakeyi ba,Akan me zanyi kuka tana magana tana goge Hawaye,Murmushi yayi kawai yace a Ina kika sanni ya akayi kika sanni?Mene a tsakaninmu da?
Takaici ya Kama Khairat Yana Raina Mata hankali duk yanda ya santa ya nuna wani Bai taba ganinta ba,shi Kuma Hunaif ya kasa fada Mata Accident din da yayi,ita Kuma Bata sani ba,ganin Yana Raina Mata hankali kawai sai ta dauki ledarta tayi gaba,Yana binta a baya suna tafiya har cikin gidansu.
Ladi taga Mutum kawai a gidanta,a mutunce suka gaisa,tace Malam lfy? Hunaif yace wurin yarki nazo Taki tsayawa ta saurareni,Ladi ganin me kudi Haka tace Khairat jeki Mana ki saurareshi,Maltina ta ajiye ta fito a fusace ta bude Masa Kofa Malam fitar Mana a gida,ganin Yanda yarinya karama take Raina Masa hankali sai ya fita kawai,Khairat ta rufe kofa sannan ta zauna tana hawayen son Hunaif,sai da ta gaji sannan ta Shiga ciki ta kwanta bacci ya kwashe ta.
Hunaif kuwa Bai San ya akayi ba idan yaga Khairat sai yayi ta faman tunaninta sannan Yana Jin nishadi da farin ciki a zuciyarsa,Haka washe gari ma gidan su Khairat da yaje Yana tashi a bacci ya tuna,memory nasa ya ajiye Masa.
Khairat Kam harkan gaban ta takeyi,yau ma sai ga wayarta ya Kira cewar ta kawo Masa Kati na dubu Dari zai siya,ya tura Mata Address na guest House nasa,Yana son ganin fadanta da masifarta tare da Saurin fushinta,Khairat Kuma Ladi ta fadawa Anty kinji Wai a sake Kai Masa Kati Wanda ya siyi Kati rannan,Ladi ta washe Baki tace Wanda ya biyoki gida jiya Zaki ce,mu Ina ruwanmu tunda riba muke ci ai shi yaga duhu maza jeki Saro ki Kai Masa,idan Bai karba ba ya biya kudi mu siyar da abinmu riba biyu kenan.
Sanin Hunaif ne mutumin kirki ne sai Khairat ta siyo Kati ba ko kwalliya ta tafi inda yace taje Guest House nasa.
Gidane na Alfarma wani me gadi ne ya Mata Iso har ciki,tana kallon yanda gidan ya tsaru,a Palo yake daga shi sai 3qtr da Riga t-shirt me azabar kyau,remote a hannunsa ga Magazine Yana karantawa,ya harde kafa daya Kan daya,ga wata katuwar tv plasma a jikin bango Yana kallon wani American film.
Kamshi da sanyi ne kawai ke tashi ta ko Ina,Juice dake glass cup ya dauka tare da kurba Yana kallon Khairat dai dai,tana tsaye a kansa daga shi sai ita,katin ta Mika Masa a wata Yar wallet tace gashi,yace Ok Yana kallonta kasa kasa Yana so ya gano Ina ta sanshi,sai yace bazan biya ba sai kin gyara min Palon nan, Dan karamin bakinta ta turo tace ba abinda ya kawoni ba kenan ka bani kudina Zan tafi,Zaki kwana anan Ashe matukar Baki min abinda na saki ba,Harara Khairat ta watsa Masa,yayi Murmushi kadan,ta juya a Shagwabe tana tafiya irin ta sangartattun Nan, ya nuna Mata inda kayan aikin suke tsintsiya,Mopper etc,Khairat aiki yasa ta cire Hijab T-shirt ce a jikinta Fara ta kamata daf Bata da wani kauri rigar, sai skert din atamfa sai dankwali a kanta Baki karami ta daura,Hijab Kuma Yana saman kujera Ana ta aiki,duk ta gaji,Bra dinta ta goce ta koma cikinta,shi Kuma kirjin gashi Nan Ana kallon komai har nipple dinta,Abu dagwas dagwas, Hunaif ya mike zai Shiga kitchen tayi sauri ta tareshi tace na Gama Ni ka bani kudina na tafi,juyowa yayi ya kalleta karaf idonsa ya Kai Kan kirjinta,gabansa ya Fadi,yarinya da abubuwa haka, ganin bra dinta ta koma cikinta abin ya bashi dariya,ya daure da kyar,baya so Kuma yace ta gyara taji kunya ko ta fassarashi, Khairat ta Kara matsowa tana gyara tsaiwarta tace Dan Allah Zan tafi, kirjinta ya kurawa Ido kadan ya dauke Kai yace ga kwaro Nan a cikinki,da sauri ta kalli cikinta da kirjinta.
Kara ta kwalla tare da durkushewa a kasa ta kankame jikinta,kunya ta kamata,ganin yanda tayi ya bashi dariya ya dinga dariya da kyar ya danne wata,ya juya bayansa yace gyara to,da sauri ta mike ta gyara kanta ta jawo Hijab dinta tasa sannan ya juyo tare da Bata kudinta da katinta tayi tafiyarta da saur ga kunya ya kalle Mata kirji.
Har tayi Nisa taji Muryarsa yace Dan tsaya,Ashe Yana biyota a baya,sai da ta tsaya ba tare data juyo ba,yace Pls a Ina kika sanni? Wani bakin ciki ya Kara rufe Khairat Wai Dan rainin wayo ita zai ce Bai gane ba,mutumin da yace zai aure ta,Yama raina Mata hankali, Hunaif har yayi tunanin fada Mata rashin lafiyar dake damunsa sai Kuma ya fasa yaji bazai iya fada Mata ba sirrinsa ne,Yana tsaye yaga tayi tafiyarta a fusace Bata ko saurareshi ba.
Ina matukar Godiya gareku masu Sharhi da masu kirana a waya,da masu min magana,Novel din Nan Yana da masoya.
Masu Sharhi Ina gani Ina Kuma karantawa,kwana biyu bana Yi muku reply aiki ne ya min yawa ga typing Ina so na Baku kullum ba Delay ,ayi min afwa Zan gyara Inshallah Zan na kokarin reply. Rashin replying yasa ma ko wacce Ina ganin Sharhinta sai na Bata page kyauta.
duk wacce taga sunanta to tabbas tana min Sharhi domin Ina karantawa Ina ganin kowa.
AsmaBaffa
[9/25, 7:40 AM] Aysha B Galadima: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚
36-40
Official
By
AsmaBaffa
FATIMA IG,UMMU HANEEFER,MAMAN SAUBAN,SUMMIS BEB,UMMU MUS'AB,HAFSAH,HAFCY,SILENT QUEEN,MOM SALEEM,SIS NERNAH,MAMAN RUKAYYA,MRS ABUBAKAR.
Ga page naku Yan albarka.
Hakura yayi kawai ya Shiga dalleliyar motarsa ya bar unguwar tasu,Yana komawa Gida Ummi ta tareshi da Ina kaje Hunaif hankalina ya tashi,nasan baka Driving Amma sai yau Kuma kasan baka da lfy Ina escort naka duk baka tafi da ko mutum daya ba?
Murmushi ya saki yace Ummi kamar wani yaro wani Meeting naje shi yasa,Baki Ummi ta tabe tare da cewa to sai ka sakko kaci abincinka kasan bazan wahalar banza ba ka sani na maka Abinci ka fita,Zanci ai Ummi Bari nayi wanka ya Furta Yana haurawa sama.
Tunda Khairat ta bar gidan Hajiya Baturiya take tunanin me zata yiwa Hajiya Baturiya ta gyara Mata Zama sannan ta Rama cin mutuncin da tayi Mata, tunowa tayi da Me Dawa Dan Wiwi ta Gama sake sakenta.
Washe gari Khairat ta Nemi Me Dawa,Tunanin Me Dawa kanwar Hunaif ce Wanda ya jikashi da kudade,yace ya akayi ne marar kunya,Khairat tace haba ai mun shirya dama Kaine kake tsokanata,Me Dawa yace na yafe Miki sabo da Yayanki,me kike nema? Khairat ta kalleshi sannan ta fadawa me Dawa aikin da zasu yi Mata shi da yaransa guda Biyar,Me Dawa yace kawo kudi,Khairat ta Mika Masa Dubu Ashirin din da Hunaif ya Bata da ta Kai Masa Kati a farko.
Me Dawa yace Ki shirya muje dake,Khairat tace an Gama,dare nayi Khairat Tasha katon Hijab da Nikaf suka Shiga Mota tare dasu Me Dawa sai gidan Hajiya Baturiya.
Katanga Me Dawa ya Kama tare da haurawa gidan yaje ya fara daure me gadi ya like Masa Baki sannan ya bude musu gidan suka Shiga har Khairat, tiryan tiryan Khairat tasan ko Ina ta Kaisu part part suka Fara daure Yan Matan gidan kaf suka kullesu a daki daya suka musu daya Kan daya kamar Kifi sadine,Khairat tace ko wacce ayi Mata bulala Talatin Talatin,ai ko su Me Dawa suka zanesu tas sannan Khairat ta bude fuskarta,basuyi mamaki ba sun San zata aikata,tace na Baku 2wks ko wacce ta koma Gidan ubanta sannan ta ja su Me Dawa har part din Hajiya Baturiya.
lokacin wasu Matan sun tafi sanaarsu,Har dakin Hajiya Baturiya suka Shiga Baki daya tare da rufe dakin suka Sa key,Hajiya Baturiya Ana ta kwasar bacci Khairat ta zaro katuwar bulalar Danko ta dage iya karfinta ta Fara Tsulawa Hajiya Baturiya,a firgice ta farka tana ihu jama'a Yan fashi,Khairat ta Shiga Tafkar Hajiya Baturiya kamar Allah ya aikota,idan tayi magana Kuma Me Dawa su daka Mata tsawa,tari ma sun hanata,Me Dawa ya karbi bulalar a hannun Khairat ya Shiga Tafkawa Baturiya,yana Baki da Karfi karfi ai sai maza,tana tsala ihu da birgima,Mutanen gidan duk matane tsorone ya kamasu Babu Wanda ya ceci Hajiyar tasu Suma ta kansu sukeyi jikinsu duk shatin bulala,ga dakin su Khairat su rufe.
Hakuri Hajiya ta fara basu,Khairat tace ki tabbatar gidan Nan kin tashi daga shi kafin Nan kafin sati daya,sannan ko wacce Karuwa ki maidata gidan Ubanta,idan muka samu Baki aikata hakan ba sai mun harbeki,Baturiya a gigice tace wlh zanyi Bazan fasa ba,sabo da zafin dukan sun farfasa Mata jiki ko gane Muryar Khairat Bata yi ba har suka Gama karshe Khairat ta bude fuskarta, Baturiya tace Khairat dama kece? Zaki aikata Allah ya Isa tsinanniya, Dariya Khairat tayi tare da Furta zagi da cin mutuncin da kika min na rama,Kika dinga zagin iyayena Kika wahalar Dani wurin zuwa Hotel da gidajen Mata Dan ki gurbata min rayuwa,Kuma Ina Nan dawowa idan Baki gyara halayenki ba zamu dawo,Khairat tace dasu Me Dawa muje kafin sati biyu mu dawo.
suka bar gidan Baki daya,Khairat ta koma gida tana Jin dadin cin Uban Hajiya Baturiya da tayi dama haushinta take ji yanda ta tozarta ta tana Zagar mata iyayenta da suke Lahira.
Zainab Ana gida tare da Soja da sauran kannensu duk tunaninsu su Talatu Ana Kasa me tsarki,abinda ya damesu shine rashin samun wayar Iyayen nasu,Sannan Shuru Basu nemesu ba har an kwashe kwana Uku,gaba daya sun Shiga damuwa.
Talatu da Kawu kuwa Tafiya suke cikin Sahara wahala ta ishesu tun suna magana har bakinsu ya mutu Babu me magana,Talatu Hannun Kawu kawai take ja,Kawu yace Dan Allah ki Jani a hankali kawai Dan Allah yayoni bana gani sai ki dinga min abinda kika ga dama,Da fada itama ta hayayyako Masa Duk abinda nake maka baka gani wlh sai na sakeka na kyaleka kabi ka isheni,Tsaki Kawu yaja yace karki jawo na Sakeki Talatu,to Ka sakeni Mana sai me aikin banza tsoho kabi ka gallabeni,zagi Kawu ya kundumawa Talatu Nan Fada ya kaure a tsakaninsu,Talatu tace Hanci kamar an taka Kashi,ai gwara Ni dake matsiyaciya an cuceni daga ji an San Talatu ke ba kyaune dake ba cewar Kawu,Baki Babu hakoran gaba,Yarka ce tsinanniya ta cire min su,Khairat tsakaninmu dake Allahumma Tafatsinini cewar Talatu,Kawu ya amsa da Ameen.
Suna Tafiya da kyar suka Karasa wata Yar rugar Fulani,Talatu ta rokesu da su sanmata ruwan Sha,Rijiya suka nuna Mata Talatu ta jawo ruwa Tasha ta cika cikinta jinin jikinta ya dawo sannan ta ebo ta bawa Kawu ya koshi sannan suka koma jikin wata bishiya suka zauna,Bayan sun Huta suka roki Fulanin da su San musu Abinci, Haka aka kawo musu tuwo suka ci hayam hayam kamar Mayu Bayan sun koshi suka sake Shan ruwa sannan aka nuna musu hanyar da Zata kaisu babban titin kwalta suka tafi,Tafiya me nisa wahala ta ishesu.
Zainab kuwa Khairat ta Kira tace su Talatu Shuru ba labarinsu,Khairat tayi dariya a ranta,a fili tace zasu kiraku ai Ni jiya ma na Kira Amirul Hajj nasu ya hada Ni dasu,suna Nan lfy cikin Jin Dadi sunce na gaida ku har Sunyi Umrah saura aikin Hajji, Wayar Talatu ce ta fadi Amma zuwa jibi tace zata siyi sabuwa ta neme ku,Zainab da murna ta fadawa Yan Uwanta abinda Khairat tace sai Murna sukeyi, Khairat tace ai Ummanki Tasha zam zam ta koshi tace shinkafa kaza ma ta gaji da ita,su Zainab sai Ihu Ana dariya,Rahinatu tace nasan Umma wlh sai tayi kauyanci.
Bayan Talatu sunje Bakin titi sai ga wata mota katuwa zata wuce,da sauri suka tsaidata suka ce Kano,Me mota
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13