Share this page
Sam,Kuma ba boye boye kawai zata Fadi gaskiyarta. Tunani ta katse Masa tace Sir ai mu inda kasan a kauye muka taso Haka muke I'm serious ban taba ganin wannan abubuwan ba sai anan,sannan Ni Tea ma idan bana kaninfari da citta ba ban iya hada komai ba sai dai kawai ka kwankwadi barasarka daka Saba sha zunubi kuwa kayi ta Tarawa kanka ba ruwana. Ko ka Kira arniyarka ta hada maka amma Ni Nan da kake gani na banza ce ba wayewa nayi ba,Naga Alama ya Furta sabo da magana sai Dole yake yinta. Ta gaji da tsaiwa tace to nidai Zan tafi gida Naga yarana,Wani yaron kika Samu again? Kai ta daga Masa tace rannan ne ya bace an rasa iyayensa shima na karbe na hada da Meenal nake rike su, Bai ce komai ba da biro ya nuna mata kofa Wai ta tafi,Aiko tace sai Gobe Sarkin kirki Allah ya biya bukata Dan Aljanna. Tana fita ya saki Murmushi dimple dinsa ya loba,shi Kam tana bashi dariya wannan yarinyar wacce ko sunanta Bai sani ba,tana fita gefen titi Mararta ta rike again ta rike Mararta tana zaga wurin tayi gabas ta dawo yamma ga Napep Bai samu ba,da gudunta ta Kara yin gaba tana ta falfala gudu gudu hannunta dafe a cikinta, wani katafaren Hotel ta gani ta shige ciki da gudu,su kansu maaikatan sun tsorata wani Namiji yace lfy madam? Tace Dan Allah ku taimakeni ku bani aron Toilet da daki daya Zan Dan huta,Baki bude suka ce Kudi kwana daya dubu Hamsim da biyar,Baki bude tace bani da ko kwandala sadaqa zaku taimakeni,ta sake rike ciki tana kara, Kamar Aljani taga Hunaif Driver dinsa ya kawo shi Hotel din Wai Yana da Meeting a nan da wasu turawa. Bai gane Khairat bace sai da yaji rokonta tana Dan turancinta data iya wani ma Shirme take fada,Tana joyowa taga Hunaif yasha wani wankan daban ba irin na dazu ba,kamshi kawai yakeyi,Magana yayi da Maaikatan da su Bata abinda ta bukata zai biya,da gudu ta shige tana murna,Bayan sun Bata dakin tayi abinda zatayi ta fito tana tafiya a hankali tana rike da mararta,Hunaif a ransa yace sabun Shiga Yan mata an fara period sai iyayi harda Shiga Hotel Wai a Bata toilet. Baki ya tabe an kawo Masa fruit salad ya Mika Mata ta karbe tana godiya ta shanye tace Kai wannan yanzu Zan warke idan har Zan shanye Kofi uku,Wai wayo tayiwa Hunaif Dan ya Kara Mata,Murmushi yayi a ransa yace a karo Mata tana tsaye taki tafiya,Ana kawowa ta karbe tana Murmushi ta shanye kwat kwat tace har na Fara Jin sauki da Zan Kara Kofi daya shike Nan na warke ma,dariya kamar zata kwace Masa yasa aka Miko Mata wani ta shanye,tace yawwa naji Ras Ras yanzu Amma da ace zansha Mango juice to gobe aikin da zanyi a Office Allah ne kadai ya sani. Mamaki ya Kama Hunaif Bata koshi tana ta durawa cikinta ruwa,yace a kawo Mata fresh mango juice, aka kawo Mata a wani Dan Glass cup ta karbe tare da Furta ku dinga cika mudu bayin Allah ba kyau wlh,ku sa Babban Kofi sai Kuna saka irin wannan karamin ai salon cuta ne Abu kadan sai tsada ta shanye,Hunaif Yana gefe Yana kallonta tace yawwa yanzu naji dai dai tace na gode na tafi gida Sir fatan dai kasha man mota da yawa yau? Sabo da wahalar Mai akeyi gomnatin kasa ta karawa man petrol kudi,gaba daya Babu motoci ba Napep na haya. Ya gano wayonta Wai Dan ya rage Mata hanya take sharara Masa karya haka,yace Ashe yau Zaki kwana a hanya kenan ko ki tafi a kafa,Ganin ya ganota sai taji kunya ta tafi da sauri ta bar wajen sai gida. Soja kuwa Yana Nan Yana neman Khairat Amma hutunsu ya Kare ya koma schl. Hunaif Yana komawa Gida Ya kwantar da kansa saman Cinyar Umminsa suna Hira,Ummi tace Hunaif bana son ganinka baka da aure,burina na ganka da iyalinka,yaro matashi da kudi Haka irinka matsala ce Zama ba mace,kaga har yanzu nasan fa kana Shan giyar Nan taka kana Shan Shayin wiwi,nema nake Allah ya hadaka da mace ta gari wacce zata gyara min Kai ka nutsu tunda Ni baka Jin maganata,Shagwaba Hunaif ya fara kamar yaron yaye Ummi zanfa daina inshallah kwana Nan,kin San na tsani aure da Matan Nan Baki daya Amma tunda kin damu Zan samo mace ko da bana wani sonta Zan aureta tunda kina so,farin cikinki shine nawa. Ummi ta fadada faraarta tace ko kaifa ta Haifa min jikoki na Tara Family na, wlh I'm serious Hunaif sabo da rashin aurenka ko baccin kirki bana iya yi sai tunane tunane,bana so na Mutu Banga ka samu mace ta gari ba me kaunarka, tsoro abin ya bashi Jin Ummi na ambaton mutuwa Kar yazo itam ta tafi ta barshi,sannan Yana son ganin Umminsa a farin ciki,Nan take a ransa ya yanke hukunci zaiyi aure ko baya son matar ko bazai iya hada jini da ita ba zai aure ta inshallah kawai Dan Umminsa tayi farin ciki. Alhaji Umar Abba Mijin Ummi ne ya dawo daga Office ya tsani yaga Hunaif Yana rabar Matarsa duk da cewar danta ne shi ya tsani Hunaif,Ransa a murtuke ya karaso yace ke kullum Fatima Baki da hankali Kai kuma katon banza kazo ka Haye min Cinyar Mata Dan Uwarka ce ko? Ni na gaji da irin tsarinku na turawa abin ya isheni,Fatima kije na Sakeki saki daya,kije ki auri danki gashin nan,dama Ita Ummi ta gaji da wannan auren na rashin ci gaba,murna ma tayi,shima Hunaif Haka,Alhaji Umar yace Gida na danki ne shi ya Gina Akan Haka kike min abinda kika ga dama to ga gidanku Nan Allah yasa Nima me kudi ne da gidana ba a matsiyaci na aureki ba,Nan take ya kwaso kayansa kaf ya bar musu gidansu. Hunaif yace Alhmdllh mun huta muma,Kaci gidanku cewar Ummi tana murmushi. Sunday Ba aiki Khairat tana cikin gida ta Gama girkinta Sunyi wanka ga Wutar Nepa su Meenal suna Wasa sanye cikin wando da vest na Shan iska suna tsakar gida gaba dayansu,Khairat tana sanye da wata doguwar Riga Yar kanti rubber ta Mata masifar kyau me hannun shimi,ta baje dogon gashinta data wanke Yana Shan iska,taji Ana buga Mata kofa tasan Baba Isyaku ne ya siyowa Yaranta sweets data bashi sautu kasuwa,ta bude da Sauri gabanta ya bada dam dam sau Uku.. AsmaBaffa [9/19, 3:27 PM] Aysha Galadima: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚 11-15 Official By AsmaBaffa Mom Inteesar, Hadiza muktar and Flower. Page naku asha shagali. Gabantane yayi mugun bugawa Dam Dam har sau Uku ganin Hunaif tsaye a bakin kofar ta ya gaji da Haduwa cikin kana Nan Kaya wando pencil white da Riga irin ta kamar mawaka doguwa ta sauka cinya silver color da tof a sama Yar pencil dai dai shi me dogon hannu marar nauyi Fara,sumar Tasha kyau ya gaji da haduwa, askinsa kawai da aka yiwa sumarsa abin kallo ne. Ko baza ki bani hanya bane ya Furta a nutse? Da sauri Khairat ta gigice tace Uhm...ahm...wuce ...sannu da zuwa Sir,Allah Sa dai ba laifi nayi ba, Baki ya tabe ya kalli gashinta Yana mamakin tsayinsa dama Yan Nigeria na da Natural gashi Haka,Ba tare da ya kalleta ba yace da Daren Nan gashinki a bude a wannan kangon gidan naki me cike da aljanu,kallonsa tayi tace Ni dai Dan Allah Kar kasa na kasa bacci Gidana ba Aljanu,Meenal da Mohd sun ganeshi suka zo wajensa ta janyesu da sauri tace ga abincinku ke Meenal wanne iskanci ne wannan nasa Miki Riga ki tube ki jefar kunki cin Abinci sai magana kuke sani,idan Baku ci ba yanzu wlh bazan tashi cikin dare na Baku komai ba. Ta kalli Mohd tace Kai zo Nan Kaci naka Baki bude take kallon Mohd ya kwaso Vaseline dinta a hannunsa da yawa Yana ci,bakin ciki da rashin sabo da rainon Yara kawai Khairat ta Fara Hawaye,tace Ni dai na Shiga uku,na Shiga Uku da wannan Yara kasheni zasuyi kawai su huta. Dariya tayi mugun bawa Hunaif ya harde Hannayensa Yana kallon Ikon Allah, Sai ga Meenal ta fito da gudu ta karyewa Khairat Kan janbaki tayi kaca kaca da jikinta. Idon Khairat jage jage da hawaye tace ku kashe Ni ki huta kawai,ta jawo hannun Meenal tasa a wuyanta tace shakeni kasheni ki huta,Meenal tunaninta Wasa Khairat take Mata sai ta Fara goga Mata jambakin a jikinta,Khairat ta Dago ta kalli Hunaif tace ka gani ko ka gani ko yanzu Ni ya zanyi dasu ta fashe da kuka tana Yan yaran Nan Basu da mutunci ko kadan so suke su sa min Hawan jini. Kallonsu kawai yakeyi suna bashi dariya Kujera ya jawo ya zauna,ita Kuma Khairat tace Haka zaku yi bacci Ni bazan sake muku wanka ba Dazu Nan nayi muku Dan kuji dadin bacci, Bedroom ta turasu tare da kullesu sabo da Kar su fito,dawowa tayi tace Sannu fa na kyaleka,plate din dake hannunta na danwake yake ta faman kallo har ya kasa daurewa ya kalleta kadan yace wannan abin kika yi? Kai ta daga Masa dazu naji Ina Shaawarsa ko kana ci ne na kawo maka? Da sauri yace ae Amma idan da Egg da tumatir zanci,Allah ya taimaki Khairat tana da kwai guda goma da ta siyo yau zata dinga soyawa su Meenal da safe,tace akwai sai ka Dan jira kadan na dafa Kwan,Ok ya Furta Mata kawai yana zaune Yana latsa wayarsa ta daura a karamar Gas dinta data siya irin Wanda Yan Hostel suke tafiya da ita,minti kadan ta yanka Masa tumatir da kwai a wani Dan karamin Plate na roba,ta zuba Masa danwaken a plate daban me yawa kuwa ta kawo Masa Yajinta me shegen Dadi da Mai har Maggi ta ajiye a gabansa tace gashi Nan, tnx ya Furta Da kansa ya zuba yajinsa Mai da magi sannan ya zuba egg da Tumatir Yana ci,Dadi kamar ya cire Masa kunne Yana kaunar danwake. Bai taba jin danwake me dadin na Khairat ba,a hankali yace da me kika yi danwaken dashi? Tace Flour da Garin rogo sai kuka da Kanwa Amma in kana so yafi Dadi to garin Rogon yafi flour yawa. Kai ya jinjina yace Zan fadawa Ummi na,Khairat mamakinsa da Dadi ya Gama kasheta Bai kyankyameta ba,har yake cin abincinta duk kudinsa Kuma yazo har gidanta gaskiya Bai da girman kai. sai da ya cinye abinsa tas tana gefe a zaune tana kallonsa farin ciki kawai take ji mutum kamar Hunaif yaci abincinta tana ganin ita ba kowa bace,Bayan ya Gama ci tace mu Pure water muke Sha na kawo maka? Kai ya girgiza Mata baya bukata,dama tasan shi sai ruwan roba. A hankali yace kin San me ya kawo Ni gidanki? Kai ta girgiza masa Bata sani ba,Zaki Aureni taji Maganar ta wani dake ta dam, tsoro ya kamata ta firgita,karki ji tsoro,Ummi ta ne ta damu nayi aure Ni Kuma bani da Budurwa kuma Ina son na faranta mata ne,Kinga bana son kowa Ni yanzu,bazan iya son mace ba,Maimakon na zauna Ina neman mace da Zan biya ta kudi ta aureni sai kawai na tuno da ke, Zan biyaki kudi masu yawa ki aureni ko Room daya baza mu kwana ba bare bed daya,kawai Kinga idan kin yarda kudi Zan biya Miki kudin ko mene,rayuwarki Zata canja Baki daya. A hankali Khairat tace Ni dai tsoro nake ji Kar Bayan aure ka kaini gidan Yan mafiya,Amma irinka ai ba ajina bane,talaka Dani marar gata ko a wasan Yara ai kafi karfina bare a aure ba Wasa bane,idan ba kaini zaka Yi a yanke min Kai ba me zakayi Dani? Murmushi yayi yace ki kwantar da hankalinki ki daina zargina wlh ba cutar dake zanyi ba,kawai Zan farantawa Ummi na rai ne ba Wai sonki nake ba,ai Ni nafi karfin soyayya dake ba type Dina bace. Da sauri Khairat tace au ci min fuska kazo Yi kenan, to kaje ka auri type dinka ba Ni ba,kawai zaka zo kana ci min mutunci,Ni nace Ina sonka ne. Calm Down ba Wai fada bane kawai ki taima ka min Ummi na tayi farin ciki pls. Khairat da har ta fara murna a ranta Jin zai aureta Amma sai taji Wai shi Baya son ko wacce mace a duniya,kawai kudi zai biyata ta aureshi to yaranta data ke rikewa Ya zatayi dasu, a hankali taji muryarsa ya Kuma cewa Kinga dama ba mutunci bane mace ta dinga zaman kanta ita kadai zarginki za ayi etc Amma idan da aurenki kina da daraja da mutunci a idon kowa, Khairat taja ajiyar zuciya tace Ni dai ba ruwana,Kuma Ni bana bukatar ko sisinka,Haka kawai Ni Dana ke burin aure me inganci wanda Zan auri me Sona,wannan yaran Kuma Ina Zan kaisu? Ummi na tana son Yara sai ki Bata su ta rike su Dama naji tana cewa zata je gidan Raino ta dauki yaro ta rike Kinga ta samu kawai kema kin huta. Ni dai gaskiya tsoro nake ji kaje ka aureni baka so na ka wulakanta Ni,sannan Su Kawu ma baza su daura min auren ba Tunda guduwa nayi na barsu,wannan ba ruwanki nasan yanda zanyi na Samu a danginki a daura auren,sannan lokacin Zaki San inda dangin Ummanki dana Abbanki suke idan kin yarda Ni Kuma Zan nuna Miki su Kuma Kawun da kansa Zan karbi Address wurinsa. Tunani Khairat ta tsaya yi yace ki aureni Ummi na nake so na cikawa burinta Amma idan Kinga baza ki iya ba bazan takura ki ba,Khairat tace Zanyi tunani zuwa jibi Zan fada maka a Office,No ki bani Number dinki Zan neme ki,Number ta bashi ya kirata tayi Saving Number dinsa da Sir sannan ya mike yace Good Night yayi waje a binsa ya bar Khairat tana tunani iri iri a ranta. Kwanciya Khairat tayi tana faman tunane tunane iri iri sai Kuma ta fashe da dariya kadan tace wlh Aurensa zanyi ba ruwana ko banza na daina wahala,ga yaran Nan Umminsa zata rike su shike Nan na huta,Kuma ma ai bashi da wulakanci tun a Daren Ranar Khairat ta Gama tunaninta zata aureshi Haka,sai Murna takeyi ita kadai idan ta tuna ba sonta yake ba sai ta hade fuska,da kyar tayi bacci. Washe gari da safe tace nayi miji Hunaif yau bazan je wajen aiki ba kamar Hunaif Ina da dashi Zan Aureshi ai nafi karfin aiki yanzu sai na ga dama,yau Monday Amma Khairat taki zuwa,Hunaif da wuri yaje Office Yana so tazo Office ya tambayeta tayi tunanin,Amma Shuru Bai ganta ba. Musaf kuwa kullum Kara Jin haushin dukiyar Hunaif yakeyi,so yake yaga ya raba Hunaif da Dukiyarsa,duk inda Hunaif yasa kafa Yasa Yaransa suna binsa,Bayan kullum Kuma kusan suna tare da Hunaif suna zumincinsu Inda Allah ya taimaki Hunaif bashi da surutu ko duk abinda zaiyi sai ya fada Sam ba Halinsa bane,Yau Ma da yamma Musaf yana gidansu Hunaif. Suna tare suna ta Hira abinsu Wanda Ummi ita Sam hankalinta Bai kwanta da Musaf ba kawai alkunya take Masa. Musaf ne ya kalli Hunaif yace Man ya kamata da muyi aure Dan ya bugi cikin Hunaif sabo da Yaransa da suke Masa aiki sun fada Masa Hunaif yaje gidan wasu talakawa,Baki Hunaif ya tabe kana yace ba yanzu ba Ni bani da kowa,sai in Kai zaka Nemo Musha biki, kamar gaske Musaf ya saki Murmushi tare da cewa Ni sai Nan da wani lokaci kadan very soon,Ummi tace Allah ya nuna Mana,sun Dade suna Hira Kafin Musaf ya musu Sallama ya tafi gida. Cikin dare Hunaif ya Kira Khairat tana dagawa yace kiyi tuna nin nan fa gobe Zaki bani amsa ta,ya datse Kiran,Wayar take bi da kallo tana murmushi. Washe gari ma Hunaif Bai ga Khairat tazo aiki ba,gashi Yana so yaji amsar ta,Yana Office har 5pm ya tabbatar baza ta zo ba yauma ko lfy oho. Wayarsa ya dauka tare da latso number dinta ya kirata kirrrrr lokacin Khairat tana girki wayar na gefenta a kitchen su Meenal suna can suna wasansu a tsakar gida,ganin Sir ne yake kiranta sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga Wai ita Jan aji,Sallama tayi Masa ya amsa cikin muryarsa me Dadi, Me ya hanaki Zuwa aiki yau 2days ko sanarwa bakiyi ba? Sannan Kuma yace hope dai kinyi tunanin? Da farko dai rashin zuwana aiki ya Isa ya baka amsar cewar na yarda da auren sabo da Ina matsayin wacce zan aure ka ai na Fi karfin Shara da Mopping,Dariya ta bashi sosai ita Nan Ashe har ta fara mulkin ma,mene kake dariya kawai ka samu kazo naji tsare tsarenka sabo da Kar nayi abinda za a gano ba auren so bane,Yace ae Zan kawo Miki rules din komai a rubuce,kiyi min Danwake da dare zanzo,Nifa tsoro nake ji Ana ganin motar Namiji a kofar Gidana sai ace Karuwa ce Ni,ke kike tsoron Dan Adam ai ba a iyawa Dan Adam yarinya,nice ma yarinyar katuwa Dani zaka ce min yarinya,ko 20yrs kin Kai ne? Amma ai da hakora na talatin da biyu ka ganni,ko zaka girmeni ai da kadan ne,To naji Aunty me yasa kika rage yi min adduarki da kike jerawa? Kana so ne? Sosai ma ya Furta, ai ban sani ba sai kazo kawai aiki nakeyi,Bayan ya kashe wayar ya bar Office zuwa gida cike da nishadi zai yiwa Umminsa abinda take so. Ko da ya koma gida Umminsa ganinsa tayi Yana ta farin ciki,Ummi tace lfy Kai Kuma yau sai wani nishadi kake yi Wanda na Dade rabon Dana ganka cikin irin wannan yanayin, Zama yayi a gefenta tare da kwantar da kansa saman kafadarta Yan aikin gidan sai zirga zirga sukeyi, Ummi guest what? Ba wani fada min naji mene ne? Har na Matsu naji,Ummi na Samu matar aure very soon za a Kira su Abbi suzo neman aure, wani farin ciki ya mamaye Ummi,tace Alhmdllh,Allah yasa tana sonka itama tsakani da Allah,Yar waye a kasar Nan? Hunaif yace Ummi yarinya ce me tarbiya wlh Kuma ba Yar gidan kowa bace talakawa ne sosai da sosai ma,Amma Bata wuce 19yrs ba,Ummi tana Murmushi tace irinsu dama nake fatan ka Aura sunfi yaran masu kudin Tarbiya,yaushe zaka kawo min Yata na ganta? Tace kunyarki take ji Sai Nan gaba Zan kawo ta,Allah ya nuna Mana yau bacci zanyi harda munshari. Allah ya maka Albarka Hunaif ka Gama min komai,ubangiji Allah yasa idan anyi wannan auren ya Zama anyi kenan ba saki,ba matsala,Murmushi yayi yace Ameen ganin yanda Ummi take ta faraa kamar zata tashi sama sabo da Murna. Duk ta rasa ma Ina zata sa kanta sabo da murna. Hunaif yace Ummi jiya fa gidansu naje da kike cewa Ina naje na Dade da dare girki tayi min Danwake me dadin gaske ko ke Baki iya irinsa ba,Dariya Ummi tayi ta daki Hunaif a baya tana Ni din ko zaka sameni ne. Sama ya Haura abinsa Yana Ummi wannan idan za ayi bikin gida daya zamu zauna dake Ina Nan Ina dankara Mana gida a Abuja zamu koma Zan barwa Musaf ya rike Yana kula da wannan companyn nawa sabo da Business Dina yafi karfi a Abuja zuwa state din South sai turai ,Ummi tace Allah nuna Mana Amma nafi Jin dadin Kano tunda kana son Abuja Naga baka son Kano mu koma Abujan Allah yasa Haka ne mafi Alkhairi yace Ameen. Da dare misalin 7:30pm yayi Sallah Isha ya fito Yana kamshi cikin wani arnen yard milk color yasha dinki me kyau fadar kyan da yayi da kamshin da yayi Bata Baki ne,Ummi ta kalleshi tana dariya Lallai wannan wanka Haka wurin Yar tawa zaka je ne Wai ya sunanta ne? Yana Murmushi kadan yace sai na dawo Zan fada Miki sauri nakeyi,Ummi ta Furta a dawo lfy yau baza kaci abincin nawa na dare ba,Ummi ta yi min girki Yana jirana a can Zan ci. Murmushin farin ciki Ummi tayi tace a gaisheta ta Mika Masa wata Leda me kyau turaruka ne masu kyau da tsada kala hudu tace a kaiwa Surukata. Murmushi yayi a ransa Yana jimami yasan shi Baya son Khairat,ba type din macen da yake so bace,shi da yake son Yar boko,wayayya,Kuma me iyayi sannan kuma ta Kai 25-27yrs wacce ta mallaki hankalinta,Amma irin su Khairat in Banda Shirme me suka iya. Yau ma shi da kansa ya yi Driving zuwa gidan Khairat,layin nasu ba mutane ko kadan Allah ya taimakeshi bare mutane su sa Masa Ido,Baba Isyaku ma ba Zama yake ba da dare Yana can majalisarsu a Zooroad. Knocking yayi lokacin Khairat an Gama Danwake da kwai yanda yake bukata,harda siyo Masa ruwan Roba Faro da juice na kwali da fresh yo an shirya komai gidan Nan ta gyarashi sai kamshi ko Ina yake,su Meenal sunci Abinci yau da wuri ma suka yi bacci,tayi wanka tasa sabuwar doguwar rigarta ta gwanjo me kyau kamar sabuwa black da adon Golden a jiki tayi rolling gyalen a kanta ga acuci anyi,Maroon jambaki ta shafa,sai Powder tasa kwalli a idonta abinka da fara sai tayi kyau sosai. Sai faman kallon mudubi takeyi tana yabon kanta taji knocking sai da tayi yanga sannan taje ta bude, tabarma ta Shimfida Masa ya zauna sai kunya take ji. Abincinsa ta kawo ta jere a gabansa da kayan Sha,a ransa ya yaba Mata kwarai yanda tana cikin talauci ta iya kashe Dan kudin nata,yace zauna muyi magana,duk kwalliyar da tayi taga ko kallonta baya yi bare har tasa ran tayi kyau ko ta birge,labarinki Zaki bani kaf,sannan Nima Zan Baki nawa,Khairat ba Bata lokaci ta bashi tarihinta tas,yaji tausayinta matuka sannan yayi Allah wadai da halin Kawu da iyalansa,shima Ya Bata tarihinsa har Dana Musaf Amma a yanda ya fada Mata Sam Bai gane Tuggun Musaf ba,sannan baya zarginsa,gashi duk matar daya aura sai Musaf ya aureta,to Allah ya kawo karshensa a ranta tace sai tayi maganin Musaf zata gano ko ma mene, tunda itama Bata San da wacce zuciyar yake zaune da Hunaif ba,Amma taji tausayin Hunaif tabbas Musaf ke Masa zagon kasa Amma Bai gane ba sabo da bashi da zargi. Abincinsa ya fara ci,tace to ya za ayi da Kawu? Ki barshi zanje gareshi Dole kafin auren Sai kin koma gidansa da Zama kinyi hakuri har ayi biki a Gama,karki nunawa kowa ba auren so zamuyi ba,kawai ya Zama sirrinmu daga Ni sai ke.nan da ranar Sunday Zan kaiki wurin Ummi na zaku gaisa,Khairat tace Allah ya kaimu,Danwaken yayi Dadi kuwa? Kallonta yayi kadan yaga Ashe dai tana da kyau matuka,yayi Dadi Mana,da baiyi Dadi ba ai bazan ci ba yarinya. Dan lips dinta ta turo ka gani kullum kana ce min yarinya katuwa dani,ba tare da ya kalleta ba yace mike tsaye Naga tsayinki idan har katuwar ce,Mikewa tayi kalla fa kamar Ni ga tsayi kallonta yayi yaga baiwa iya baiwa yace zauna to yarinya ce ke Banga girman ba Ni, ya Saba da ac sai zufa yake hadawa,Mufici ta Mika Masa ba tare da ya karba ba yace ki min fifita Zaki bani da wanne hannun zanyi kina gani daya waya nake Amfani da ita daya Ina cin abinci ya

Chapter 5 of 13