sun zo Sannan zakina Shiga duk Bayan 3hrs ki duba idan da dirty ki gyara wajen,sai Kuma idan wani ya nemeki,Kar kiyi nisa.
Wurin da aka tanada na hutawa taje ta zauna tana hutawa Lokacin Meenal ta tashi sai gwarancinta take mata tana saurara suna hirarsu.
Musaf ne ya fara zuwa Office yau sai Manager Ogan kuwa Bai shigo ba yau ya tafi Abuja duba wasu kamfanonin nasa sannan Yana da meeting a Rivers State.
Musaf ne ya nemi ganin Khairat.
Babu ko tsoro a ranta taja Meenal dinta suka tafi,Bata iya Shiga lifter ba tabi steps taje tana knocking sai da ta Dade yace Come in,Auzubillah ta Furta ganin katuwar Plasma dinsa ya Kama tashar XXX Yana ta kalla a nutse Yana Shan tea,ko a jikinsa Volume ma ya karo sai yi suke suna ihu,ganin Haka yasa ta fitar da Meenal waje take karki kiyi kuka tsaya a Nan Zan Shiga na fito,Allah ya kawo Aminu kawai ya dauki Meenal suka tafi Office dinsa ita Kuma Khairat ta Shiga tana matukar Jin tsanar Musaf a ranta,Bata ko kalli TV dinsa ba tace gani fa nazo baka ce komai ba,da yatsa ya Mata alamar ta matso tana matsowa ya mike tare da sharara Mata uban Mari,Fuskar ta tayi jajir sannan yatsunsa rada rada a jiki.
Ta daure ko kwalla Babu kuma Bata ce komai ba,yace sai ta sake shara da wankin Toilet,ba gajiyawa tayi Masa,yace Ina Nan Akan kudira ban Fara daukan mataki ba a kanki,wannan Yar taki da kika fi so zakiga me Zan mata sai kin kwammace Baki haifeta ba,dama daga gani Yar cikin shege ce.
Bata ce komai ba sai ga Aminu ya kawo Mata Meenal tana kuka taki zama a wajensu,Takaici ya Kama Musaf Nan take ya mike tsaye Yana Zubawa Aminu masifa sai na Kore ka daga aiki,u r very stupid Kar ka sake ka ajiye min wannan tsinanniyar yarinyar a Office Dina,Khairat taji haushi tana huci zata Fara masifarta Aminu ya Mata signa da Ido,Musaf Yana kallon abinda sukeyi yace da Aminu na sallameka daga aiki daga yau,Khairat tace jeka Aminu Zan sa Oga Hunaif ya dawo da Kai,Zan sa Wanda ya gaji arziki ya dawo da Kai bakin aikinka,fari me farar aniya Dan Kyakyawa ba kyan kame kame ba,kishin Hunaif ya tasowa Musaf komai shi baza a yabeshi ba sai Hunaif,Mata Hunaif,kudi Hunaif komai Hunaif,Kara Jin Tsanar Hunaif yayi a ransa Jin Khairat tana yabonsa,a fusace ya mike Khairat ta dauki Meenal da sauri zasu gudu ya samu ya tankadasu suka Fadi rijif,Meenal bakinta ya fashe jini na zuba,Aminu kuwa tuni ya bar ma Building Baki daya.
Zuwa Khairat tayi famfon da suke wanke hannu a can baya Garden ta wankewa Meenal bakinta tana Kiyi hakuri kinji,yi Shuru Allah zai saka miki tana jijjigata tayi Shuru kuwa.
Yinin yau Sunyi shi ba Dadi Khairat ji take ma ta tsani aikin,Amma ba yanda ta iya Haka zata hakura dole karfe biyar na yamma tayi tafiyarta gida ta dafa musu abinci suka ci sukayi Wanka sannan ta kwanta tana huce gajiya ita kuma Meenal tana Wasanta a tsakar daki.
Tunanin rayuwarta takeyi kawai musamman Meenal da take riketa ganganci tayi ta karbi yarinyar gashi ta Shiga ranta baza ta iya Kai ta gidan Raino ba.
Da dare Khairat Bata iya wani baccin kirki ba sabo da tunanin wulakanci da Musaf ya Mata, washe gari ma Haka suka shirya cikin kayansu na gwanjo,Khairat Bata yi wani baccin kirki ba suka tafi Company ta Fara aikinta tana Office din karshe na Musaf bacci ya takura Mata,ita Kuma tun farko Haka take daga taji bacci a wajen zata kwanta,Meenal tana Wasanta Khairat ta kwanta a kasan tiles ta fara baccinta,ko minti goma Bata yi ba Musaf ya shigo ya dau shegen wanka,mamaki da takaicin Khairat ya kamashi ya watsa Mata ruwan Robar dake hannunsa gaba daya ya juye Mata a jikinta,Amma ko a jikinta baccinta takeyi,Baki bude yake kallonta,Meenal Kuma tana dariya ta Kama rigarsa tana Mika Masa hannu ya dauketa,Babu Imani Wai ta Bata Masa Kaya Sunyi Dirty,yayi ball da Yarinyar ta Fadi goshinta ya fashe,lebenta na sama ya tsage kadan Yana jini,ta kwala uban kuka,ba shiri Khairat ta farka taga abinda yake faruwa,itama Khairat sai ta dauki Meenal ta fashe da kuka suka zauna a wajen suna ta yin abinsu,Musaf ko a gefen rigarsa sai ma takaici da ya sani Bai sa Hunaif ya Bata aiki ba zasu kashe Masa dodon kunne,Khairat Kuma tunani tayi da wani banza ya ci ma mutunci gwara Dan uwa,Gidan Kawu Sabiu ya fiye Mata wannan wulakancin,A tsawace Musaf ya koresu daga Office dinsa,jiki na rawa Khairat ta fito Meenal tana kafadarta suka Shiga lifter Bata kula ba ta fada ciki,wani kamshi ya ratsasu na musamman,garam tayi Karo da Hunaif a lifter zai je Office nasa,yasha kana Nan Kaya kamar a England yayi kyau ya gaji,duk macen data ganshi sai ta zauce.
Da sauri Khairat tace Morning sir ita a Dole maaikaciya,Hannu kawai ya daga musu ya kallesu yasan aikin Musaf ne ko a jikinsa,da sauri Khairat tace Sir Dan Allah Ni dai a cire min aikina zuwa Office din Musaf ko kudina na albashi na yarda ka rage,Dariya ce ta kusa kwace masa sabo da yanda a farko ta dinga kuri sai gashi just 2days tayi laushi,a fili ko kala Bai ce ba ya fita abinsa ya bar lifter zuwa Office dinsa.
Khairat tace Kai kaga mutum Lallai sai na gyara musu Zama Naga Alama,tana zaune wurin 12pm Bayan ta Kai Meenal chemist ta dawo bakin aikinta,Aminu yazo yace kije Sir Hunaif na nemanki, yace Kinga Alhmdllh Hunaif yace Kar na tafi ya barni nayi aikina, murna Khairat tayi tace Alhmdllh Musaf sai ya mutu, da sauri ta mike da Meenal dinta a kafada ta tafi Office,tana yin knocking yace Shigo,Yana Shan tea Yana rubuce rubucensa tace gani Sir, ba tare da ya Dago kansa ba yace ke Ina iyayenki suke? Tace sun rasu Sir Baki daya,wannan Makahon fa da kuke tallan magani? Kanin Baba nane same father and Mother,Blood daya,wannan yarinyar kuma fa?tace 'yata ce,cikin shege kikayi ko aure? a'a ko daya tsintarta nayi sabo da ita ma nake wannan aikin Zan kaita schl tunda ta fara wayo kaf ta bashi labarin tsintar yarinyar,wayarta ce tayi Kara kirrrrr....ta daukota da Sauri taga Baba Isyaku,tana dagawa yace an kawo Miki yaron Nan daya Bata ba a ga iyayensa ba,anyi bincike an gaji nace musu nine mijinki nayi signing da komai yaro gashi a wajena idan kin dawo kizo ki tafi dashi,Ok to ya Sunan yaron? Hmm yaron da baya wata magana kawai ki rada Masa Mohd, Khairat tace to ba damuwa.
Hunaif Yana ji Yana aikinsa yace bazan iya hanaki aiki a Office din Musaf ba,sabo dashi ma na Baki aikin Nan domin shi yace na Baki yana da nufinsa,,Amma Kai dolo ne Sir, Baki bude Hunaif ya kalleta, gaka a Haka kamar Namiji tsayayye Ashe ba Haka bane wlh Mijin tace za ayi a Nan.
AsmaBaffa
[9/19, 3:27 PM] Aysha Galadima: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚
5-10
Official
By
AsmaBaffa
Hadin Kai fans and AsmaBaffa fans wannan page dinku ne ku kadai.
Hunaif Mahmood Kuwait cikakken sunansa,Mahaifinsa Dan Asalin Kuwait ne Wanda ke kasuwanci a garin Makkah,Mahmood Attajiri ne na gaske,Wanda shi kadai iyayensa suka Haifa Wanda sun Dade da Rasuwa, Hajiya Fatima itace Mahaifiyar Hunaif wacce Bafulatana ce yar Jigawa state can kauyen fulani,Babanta shima ya rasu sai Mahaifiyarta wacce har yanzu tana Raye Kuma tana Makkah tana auren wani Dattijo Dan Sudan, tun Farko da Fatima ta tafi Saudiya acan take zaune suna kasuwanci Har ta auri Dan Sudan,lokacin ita kuma Fatima Bata son zaman Makkah tafi son Nigeria,Wanda acan Kuma ta samu mijin aure balarabe Mahmood Dan kasar Kuwait,tana sonsa ta aureshi ta zauna dashi a garin Makkah,Danginsa ne suka takura basa kaunarta su saidai ya auri Balarabiya Yar uwarsu,hakan yasa suka dinga samun matsala har Allah yasa ta Haifi Hunaif lokacin sun koma kuwait da Zama,Bayan Hunaif Yana da Shekara biyar Mahmood ya saki Fatima Allah yasa ta dakko danta Hunaif ta gudo Nigeria,Mahmood Bai so hakan ba.
Amma Dole ya hakura ya kyaleta gashi Yana son dansa,sabo da yasan yanda Nigeria take sai ya siyawa Fatima gida a Kano state me kyau ta zauna da dansa Kar yasha wahala,duk watan Allah zai turo Mata da kudi masu yawa Kan ta kula da rayuwar dansa,sannan idan ya samu time Yana zuwa yaga dansa jefi jefi ya koma kasarsu Haka kuma Yana daukansa suje yayi hutu ya dawo dashi Nigeria,Sosai Hunaif ya taso cikin gata,Naira da Hutu ga kyau,Bayan ya Gama Primary Maman Fatima dake auren Dan Sudan ta Mata waya Lallai tayi aure.
Bayan wata Uku Fatima ta auri wani Alhaji Umar Wanda yayi aure aure da dama Amma baya Haihuwa matansa duk gudunsa sukayi suka auri wasu,sai Bayan auren Fatima ta gano baya Haihuwa sannan baya son Haihuwa Kuma Allah yasa ma baya haihuwar, Alhaji Umar rikakken Dan boko ne,baya kaunar Haihuwa baya son Yara ko kadan,sannan yayi Dace Allah yasa baya Haihuwa,aiki yake a ministry of education,tun sanda Hunaif yana yaro ya tsaneshi sai yayi ta hararsa,Yana zaginsa,ya takura Masa sannan baya son ci gabansa,ganin hakan yana secondary masu tsada a Nigeria sai Fatima ta yiwa Mahmood magana ya kai Hunaif karatu London inda zai karanci kasuwanci,Unguwarsu daya da Musaf a Kano,tare suka taso shi da Musaf talakawa ne sosai,Haka Hunaif yasa Babansa Dole ya biyawa Musaf makaranta me tsada sukeyi tare tun daga Primary har University a london,Ita Kuma Maman Musaf sabo da taimakonsu da Hunaif yakeyi take mugun kaunarsa Haka ma Baban Musaf,abinda Hunaif yake so take dafa Masa idan yaje gidan kamar zata goyashi,shima Baban Musaf Haka abin gwanin Sha'awa.
Hakan yasa suka Zama frnds da Fatima Ummin Hunaif suke zumunci me karfi,Ummi Fatima mutuniyar arziki ce Haka Umman Musaf ma,sabo da wannan zumincin yasa Bayan Hunaif ya Gama Masters tare da Musaf suka dawo Nigeria,Lokacin Kuma Mahmood Baban Hunaif tsufa ya kamashi kuma bashi da aure tun Bayan rabuwarsu da Fatima Bai sake aure ba,sai ya damkawa Hunaif dansa Dukiyarsa Baki daya ya koya Masa business kasa kasa.
Cikin sa'a Hunaif ya fara aikin kasuwanci kasa kasa lokaci kankani ya Zama Hamshakin Attajiri Wanda lokacin tuni ya dankarawa Alhaji Umar Mijin Umminsa gida na Allatsine uwar me karya a GRA suka koma ciki da Zama daga shi Sai Ummi tare da Alhaji Umar mijin Ummi,hakan Kuma ya ginawa Baban Musaf gida na gaske a kusa dasu Nan layi daya.
Bayan Haka ya bawa Baban Musaf Jari me yawa yaci gaba da kasuwancinsa na gwanjo sannan ya bawa Musaf Babban matsayi a Company nasa guda biyu Dana Kano shine Secretary Wanda Khairat ke aiki,sai Kuma na Rivers State Musaf ne Manager,kafin kace me Musaf ya Zama me kudi shima Wanda dama burinsa kenan,ya siyi manya manyan motoci ya siya Babansa ma da Ummansa ga Driver da Yan aiki,ya Kai iyayensa Makkah da daukan nauyin kannensa, yayin da zumunci me karfi ya karu tsakanin Fatima Ummin Hunaif da Umman Musaf,Alhaji Umar mijin Fatima shi harkar aikinsa yakeyi sannan baya kaunar Hunaif Haka kawai,shi ko abokinsa ne indai ya haihu to ya daina kulashi,baya kaunar Haihuwa,Fatima Kuma tana son Haihuwa kawai Dan ta aureshi ne ta hakura Haka tunda tana da danta Hunaif,kuma tayi dacen yaro,duk da cewar Bata son abinda Mijinta ke nunawa Hunaif tsana karara Bayan Shi Hunaif Yana mugun girmamashi Yana daraja shi ya daukeshi uba sannan Yana Masa duk abinda yake so Amma Abban nasa Mijin Mamansa baya gani Kuma baya yabawa,hasali ma Kullum Kara Jin Tsanar Hunaif yakeyi.
Sabo da hakan ya jawo Fatima ta rage kaunar Mijin nata Bata damu dashi ba,sabo da tafi son Hunaif da komai a duniya.
Bayan Shekara daya Allah yayiwa Mahmood Baban Hunaif Rasuwa,sunsha kuka har Fatima.bayan sunje taaziyya komai ya lafa sai Fatima ta gano danta Hunaif Yana Shan giya da Shayin wiwi.
Tayi Masa fada har ta gaji Haka Maman Musaf ma tayi musu fada ta gaji,ganin hakan yasa Fatima ta takurawa Hunaif Dole yayi aure tunda taga ya Zama Attajiri kudi Kar su jawo danta ya lalace.
Sabo da Hunaif ya samu tarbiya,ilmin addini Dana zamani,shi dai kyaleshi da iyayi,ga son ya auri wayayyar mace,katuwa,sannan ace Yar gayu ce,baya wulakanta mutane baya Shiga harkar kowa,ga taimakon talakawa,sadaqa,sannan shi ko yasan cutarsa kakeyi bazai fasa yi maka abin Alheri ba idan yayi niyya sai dai fa akwai Iyayin tsiya.
Musaf kuwa Baban sa Alhaji Salis Yan Asalin kebbi state ne,Shi da Matarsa Hajiya Lubabatu suna da dangi da yawa a kebbi Amma duk talakawa ne,Babansu cirani ne ya kawoshi Kano state Yana dako a kasuwanni,har Allah ya hadasu da Hunaif a fillin ball na Yara suka Zama frnds da Musaf sosai,Musaf Yana da kanne Najmin da Najma mace da Namiji sai Autarsu Haneefa.
Tunda Musaf ya fara girma yaga Hunaif ya fishi ta ko Ina sai yake Jin haushinsa,duk abinda Hunaif ke musu kishi yake da bakin ciki,shi a rayuwarsa Hassada Ce dashi me karfi baya son wani ya fishi,baya kauna yaga wani Yana ci gaba,hakanma Dan talauci ya musu yawa ne da tuni ya daina kula Hunaif,shi ko abokinsa ne indai yaga ya fishi kudi ko kyau etc to sai ya daina kula mutum tsakaninsu Harara,bashi da burin da ya wuce yaga Hunaif ya talauce shi Musaf ya koma me kudin Yana tallafawa Hunaif.
Amma bacin ransa sai yaga kullum Hunaif Kara ci gaba yakeyi,Kuma yazo ya samu zukekiyar budurwa wayayyiya Yar boko Yar kwalliya Sultana zai Aura,
Tunda Musaf yaga Hunaif ya samu Mata irin Sultana yaji shine ya Dace ya auri Sultana ba Hunaif ba,daga Nan ya Hana kansa sakewa ya tashi hankalinsa,Amma Yana gani aka daurawa Hunaif aure da Sultana,Dole ya danne zuciyarsa suka Sha shagalin bikin da akayi Bari da Naira.
Bayan wata shida Lokacin Ango Hunaif ya kasa gane Kan Sultana da muguwar kazantarta shi Kuma baya son kazanta,ba abinda ta iya sai chatting a waya,ko girki batayi,kullum burinta ta Masa rashin kunya,a boye Kuma Musaf ke zuga Sultana har watarana taje har gida ta karewa Ummin Hunaif zagi tatas,Hunaif Yana gidan Yana ji ya saketa saki biyu ta tafi,dama Bata da tarbiya Yar gidan minister na tsaron kasa ce,Bayan tayi Idda sai katsam Hunaif yaga soyayya ta barke tsakaninsu da Musaf yayi mamaki,Amma sai Musaf ya shiryawa iyayensa karya da Hunaif Wai itace ta nace Masa tana rokonsa ya aureta sabo da Idan tana ganinshi kamar Hunaif ne,tana son Hunaif Amma ya sake ta,Haka ya dinga karya iri iri har ya cirewa kowa shakku aka daura Masa aure Da Sultana,a ranar yace yawwa Nima sai naji abinda Hunaif yaji a jikinki.
Bayan wata Shidda Ummi ta nemowa Hunaif matar aure Yar gidan Gomnan Sokoto Kyakyawa da ita Amma Kuma Yar lezbian ce Ummi Bata sani ba,aka daura auren Hunaif da Zeenatu ko Shekara ba ayi ba ya kamata suna lez da kawayenta sannan dama shi Baya sonta Bata Masa ba,Yana sakinta Musaf ya saki Matarsa Sultana,ya sake shige da fice Zeenatu na yin Idda yayi yanda yayi ya aureta Nan ma Wai sai yaji dole me Hunaif yaji a jikin Zeenatu.
Lokacin Ummi ta Fara gano halayen Musaf Amma data fadawa Hunaif yayi hankali dashi sai yace Allah ya rubuta dama shima sai ya auri Matan daya saki,ita kuwa Ummi tayi Baya baya dashi, Haka Yana ji ance Hunaif ya samu sabuwar budurwa Ameera zai Aura sai ya saki Zeenatunsa, duk Kuma Matan Allah yasa Babu wacce ta samu ciki da kowa a cikinsu, Hunaif Yana son Ameera sabo da tarbiyarta iyayenta ba wasu masu kudi bane Amma akwai tarbiya Ummi ma tana sonsa Bayan an daura Auren Hunaif da Ameera suna zaune lfy cikin Jin Dadi iyayen Ameera ma sun Zama masu kudi sabo da yarsu ta auri Hunaif, kasa kasa suke zagawa da Ameera suna holewarsu,shi kuwa Musaf kamar ya mutu Haka yake ji,hakan yasa ya koma neman Mata ko zai samo me kalar Ameera ko wacce tafi Ameera matar Hunaif,ya dinga bin Mata kamar bunsuru,Hunaif kuwa Bai San me yakeyi ba,sabo da a gaban Hunaif baya nuna Masa komai a boye yakeyi.
Bayan Shekara daya Ameera ta samu cikin Hunaif Yana ta murna lokacin Musaf ya nace wa gidansa Yana ta hurewa Ameera kunne Kar ta Haihu zata tsufa,Ashe dake Ameera ma Imaninta baiyi nisa ba sai ta yarda a boye Tasha kwaya ta zubar da cikin Hunaif,Haka ya hakura Bai san dalili ba,Bayan Yan watanni ta Kara samun ciki,Nan ma ta zubar,na Ukun Hunaif ya kamata da kanta da kwayar a saman bed din dakinta.
Ummi ya sanarwa da komai itama Ummi Bata ji Dadi ba,ta shirya taje gidan Hunaif ta Fara yiwa Ameera fada Amma sai Ameera ta rufe Ido ta gayawa Ummi bakar magana a gaban Hunaif,shi Kuma Hunaif indai kika taba Masa Umminsa to sai ya sakeki Haka ya saki Ameera badan baya sonta ba.
Iyayen Ameera har gida suka sake zuwa tare da karewa Ummi tanaji tas danta me auri saki ne sabo da Basu San me yasa yake saki Matan nasa ba.
Bayan ta Gama Idda Musaf yaje ya dinga faman kyautatawa Iyayen Ameera ya nuna musu na gari ne ya dinga langabewa,Ita kanta Ameera tace Lallai Musaf yafi Hunaif mutunci da hankali har ta yarda suka Fara soyayya,Har aka sa ranar aure, wannan Karon Umman Musaf ma ta Fara ganin halin danta har kuka tayi akan bazai auri matar da Hunaif ya saki ba sun gaji.
Haka ya dinga karya da karairayi iri iri har suka Amince,Ummin Hunaif batayi mamaki ba sabo da ta Gama gane Musaf,shi Kam Hunaif da gaske Bai gane ba,gani yake dama Allah ya rubuta Mata daya zasu dinga aure,sannan shi ba wani son Matan daya aura yakeyi ba,Dan Musaf ya auresu Bai damu ba,sai yaga ai shima Musaf suna Masa abinda suka yi Masa shi yasa shima yake sakinsu Bayan aure da kankanin lokaci.
Haka Musaf ya auri Ameera Hunaif dashi akayi komai.
Bayan Aure da wata biyar Ameera ta samu ciki,Musaf baya son Haihuwa Kuma shima ya tsani Yara,yayi yayi da Ameera ta zubar taki yarda tace shi ya kashe Mata aure a gidan Hunaif shine yanzu Bayan ta gane kuskurenta taki zubarwa,tayi yaji ta koma gidansu da Zama har ta haihu tayi arbain,bayan wata Uku Yarta tayi wayo ya dawo bikon Ameera iyayenta suka ce baza ta koma ba baya son Haihuwa,sabo da ko Yar aka nuna Masa baya ko kallonta,ganin Haka ya kyale su ya banzar tar dasu,har aka kwashe shekara guda.
Watarana Musaf ya fita yawon shakatawa yaga yanda Ameera ta Kara kyau ta goge sai yace shifa bai saketa ba,ya koma ya dinga hure Mata kunne,Amma kuma yaki yarda ko yarsa ya kalleta ya tsani Yara,Haka ya lallabasu da Sa bakin Hunaif aka maida Auren Musaf da Ameera.
Sai ya dawo yace baza ta tare a gidansa ba yanzu sabon gini yakeyi a Bari sai ya Gama, a Haka ya dinga daukan Ameera matarsa suna zuwa Hotel suna Shan Duniyarsu da tsinke,katsam ta Kara samun cikinsa Nan dai sukayi baram baram da Ameera ya saketa saki biyu yayi tafiyarsa,Ameera kuma iyayenta suka tattara ta tare da yarta daya da cikinta suka kaita Abuja gidan kanwar babarta taci gaba da Zama acan,anan ta Karasa degree dinta da service ta samu aikin Gomnati tanayi.
Tun daga haka Hunaif ya tsani Mata da aure,Ummi ma ta Goya Masa baya tace baza ta Kara sashi yayi aure ba,sanda Allah ya fito Masa data gari dai dai dashi me Amana,yaji dadin hakan tun daga Haka ya daina ko neman aure ba ruwansa,Yaga yaro dashi 32yrs har yayi aure uku a Dan kankanin lokaci.
Shi kuwa Alhaji Umar mijin Umma Dadi yaji ma shi Baya son yaga Hunaif Yana Jin dadin duniya,Shima Musaf tunda yaga Hunaif ya daina ko Zancen aure shima Bai Kara ba,sai dai shi Baya daure Shaawarsa Yana bin Mata sama sama,sannan yanzu burinsa yaga Arzikin Hunaif ya durkushe,Dukiyarsa ta Kare,yanzu burinsa kenan Yana ta hada target ba tare da Hunaif ya gane hakan ba,domin shi tsakani da Allah yake zaune da Musaf,Musaf shirye shiryensa yake yi a boye.
Kadan daga Halayen Musaf kenan sai Nan gaba zaku ji wasu kalar sababbi kuma,duk abinda yake iyayensa Basu sani ba,ya Gama rufesu ruf yanda baza su gane ba.
Allah ya Kare mu daga sharrin abokai irin Musaf,Haka Mata ma a wannan zamanin Hassada da bakin ciki tayi yawa,cin Amana da yaudara ba a son aga wani yafika ko ta fiki sai Hassada ta shiga,Allah kiyashe mu, ga gasa daga wance ko wane yayi Abu sai kaima ko kema kice sai kinyi,da dama yanzu mutane muna amsa jarabawar da ba tamu ba,kowa Question paper dinsa daban Amma wani ya Gama amsa tasa dai dai ya cinye sai mutum yaje yayi copying Bayan Questions ba iri daya bane Taya zamu ci jarabarmu ta duniya har mu samu Lahira me kyau?
Allah ya kyauta.
Yau Monday yau Ameera tana Office din Hunaif mararta ta Fara ciwo tana murdawa,Hunaif Yana ta aikinsa a Laptop dinsa Yana Shan lemonsa ya ga Khairat ta jefar da Mopper ta rike Mara tare da tsugunawa tana murkususu, tun Yana ganin abin na Wasa ne har yaga ta kwanta a kasa tana wani sankamewa tana kuka sosai, rasa me zaiyi Mata yayi yace mene? Da kyar tace marata ce,Period ne?ya tambaya tace Ni ban sani ba ban taba yi ba Ni,ke da kike Me Magani ai naji a tallanki harda maganin Ciwon Mara sai kiwa kanki magani, ka taimakeni Dan Allah kaifa me taimako ne.
Waya ya bugawa Doctor din Umminsa macece ya sanar Mata komai,tace ya tura Mata Driver dinsa ya karbo Magunguna da komai,yace ki hada Har Always pad tace ok.
Ba afi 15mnt ba sai ga Driver ya shigo ya kawo Masa magungunan,Khairat ya mikawa ya Bata ruwa a wani glass cup me kyau lokacin ma Har Jini ya fara Bata Mata kayanta sai wani babboyewa takeyi,tana Gama Shan magungunan daya Bata ta dinga bin bango nata rike Mara,yace karfa ki Bata min bangon Office ki Shiga Toilet Dina gashi can cikin wani resting room dina,da gudu ta dauki ledar pad din ta shige Wai kunya,ta tsaya ta gyara kanta ta wanke inda ya baci Allah ya taimaketa harda panties masu tsada guda biyar,ta shirya tsaf ta fito da pad dinta a leda taje ta zauna a kujera,Bai kulata ba Yana kallonta ta kwanta zata huta bacci ya kwasheta sarkin bacci.
Sai yamma ta farka tana tashi lokacin sallar laasar yakeyi tace na tafi gida sir,na gode Allah ya Kara budi.
Ta dauki maganinta da ragowar pad dinta zata fita ta tsinci muryarsa yace zo ki gyara min Office dina duk kin Bata shi da dirty naki.
Office din ta kalla tsaf tace Ni dai Banga komai ba jibeshi tsaf, Ina magana kina yi? Ba shiri tace sorry Sir ta dawo haka ta Kara gyara ko Ina zata tafi yace ga kayan tea can hada min,bangaren da aka tanadin dukkan kayan tea ta nufa da wani engine na hada tea,Bata iya Amfani da komai ba ta kalleshi tare da Shagwabe fuska tace Ni ban iya amfanin da komai ba anan,mu kasan kawai dai muna birni ne Amma banbancinmu da Yan kauye kadan ne,kallonta yayi kamar dariya zata kwace Masa tana Masifar birgeshi da Bata da duhun Kai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13