blue and black color,Haka takalmi da jaka ma same color Wanda Hunaif ya kawo,Ladi tana ta kodata gaskiya kinyi kyau Khairat karfa ki zautar da yaro,dariya tayi kawai sukayi sallama da Ladi ta Shiga rantsatsiyar motar Hunaif da Driver yazo daukanta.
Tana zuwa Airport ta hango Hunaif da ruwa Eva Yana Sha Yana Danna waya,gefensa Yar karamar Jakar maza ce ta manyan Yara ya hade cikin Shadda light blue da takalmi Baki agogonsa Baki dama Bai fiye sa wata hula ba,Suma taci kudi sai sheki yakeyi,Khairat wani nishadi take ji sai wani fara'a takeyi,ji take kamar tafi ko wacce mace duniya,Nan kanta ya Kara girma,ta Fara yanga da gadara tana taku dai dai kamar wacce zata tafi England,tun kafin ta karaso wajensa da kyar ya gane Khairat sabo da tsananin kyan data yi, kamar balarabiya,sai yaji ta Kara birgeshi Bai taba ganinta da kwalliya Haka ba sai yau.
Murmushi yake saki shi kadai tana karasowa ya sunkuyo tare da leka Fuskarta Yana dariya yace kwalliya Kika yi min? Gaskiya na iya zaben Kaya,Khairat tayi Murmushi tace ai wacce tasa kayan ita ce me kyan ba kayan ba,dadina dake kuri da yabon Kai cewar Hunaif,yarinya kinyi dacen miji Dan Umminsa, kafin ya rufe Baki tace kaima kayi dacen mace Khairat marainiyar Allah zankadedediya son kowa kin Wanda ya rasa,Murmushi ya saki suka tafi aka musu Screening tare da shigewa jirgi,Khairat gata ga Hunaif sit dinsu su kadai,Kamshi kawai suke musamman Hunaif sarkin kamshi,Khairat an Shiga jirgi yau harda zaro Qurani a jaka ta Fara karance karancen adduoi Allah ya saukesu lfy,Hunaif ya kalleta ta birgeshi Yana son mutum me addini da yawan addua.
Mintuna kadan sai gasu a Taraba,Ashe tuni Hunaif yasa an shirya Masa lafiyayyar mota tare da driver Dan garin Taraba Wanda yasan lungu da sako a garin, Khairat ta kalleshi a ranta tace kudi masu gidan nara,ko me kake so indai da kudi an Gama, ita kanta abar motar abar kallo ce,baya ta shige kusa Da Hunaif sabo da kamshi da sanyin dake motar a fili Khairat tace Naira maganin masifa da Jarabar duniya,Naira masu gidan nara.
Hannu ya Mika ta tare da Furta bani Address note din naki uwar surutu.
Yar takardar data rubuta Address din da Kawu ya Basu ta Mika Masa shi Kuma ya mikawa Driver,Ido Driver ya zaro yace tab Kauye ne sosai kafin muje kauyen sai munyi kusan 4hrs,nisa ne da garin,idan zaku ci Abinci ma ya kamata kuci tun muna cikin gari,Hunaif yace muje kawai bama Jin yunwa, a'a nifa bana jure yunwa Allah ya gani sai naci na koshi nake iya tafiya cewar Khairat, Dole aka tsaya a wani eatery na manyan yara suka yi take away sannan suka dauki hanya.
Daji ne sosai suka Shiga abin tsoro,Khairat tsoro ma takeyi Kar matsala ta samesu a Dajin,suna tafiya Sunyi rabi Motar tasu Haka kawai ta mutu a Dajin,Karfen nasara ba tabbas,Tsoro ya Kama Khairat Amma Driver da Hunaif ko a jikinsu,anyi anyi motar ta tashi Taki,Hunaif Yana fita Khairat ta fice da gudu ta makale kusa dashi kafa ya motsa sai ta motsa,Driver yace mota sabuwa dal kawai ta mutu karfen nasara,suna ta gyara Driver da Hunaif Amma taki ko motsi har Magrib ta wuce,a wurin sukayi Alwala da salloli sannan suka ci take away nasu.
Sallaya Hunaif ya dakko tare da Shimfida musu shida Khairat a gindin bishiya ko Ina koren ciyayi luf luf fresh air na kadawa,Driver Yana can jikin mota Yana fama ta tashi taki.
Dare yayi 8pm Bayan Sunyi sallar Isha Tsoro da bacci ya Kama Khairat tana gyangyadi Hunaif na gefenta Yana latsa waya sai ji yayi ta Fado jikinsa,dama ya Santa da bacci duk inda ya kamata a Nan zatayi,Murmushi yayi Yana karewa kyakyawar Fuskarta kallo,kwanciyarta ya gyara Mata tayi matashi da cinyarsa baccinta takeyi sosai sai da ya gaji yaga Allah ba Wasa ba Driver ya shige mota yayi kwanciyarsa Yana bacci,shi kanshi Hunaif yanzu tsoron Dajin ne ya kamashi,ba shiri ya zame Kan Khairat daga cinyarsa a hankali,ya Dan matsa can karshen katuwar carpet din ya kwanta Yana so shima yayi bacci,idonsa ya rufe ruf.
Cinnaka ne ya sadado ya ciji Khairat ta mike a firgice tana Sosa wajen,Daji ga duhu ko Ina Tsoron Aljanu ya Kama Khairat ta Matsa jikin Hunaif ta kwakwume shi,Yana jinta shima tsoron yake ji baya so ya bude idonsa.
Kukan wani Abu sukaji Khairat tace wayyo namun daji ne ga kukan Damusa can,Hunaif da sauri yace Allah? Wani Abu yayi wani Gurnani,Hunaif ya juyo tare da rungume Khairat sosai itama ta shige jikinsa tana cewa fada sukeyi da Zaki da Damusa wancan kukan Zaki ne,Innalillahi cewar Hunaif mu koma cikin mota,da sauri suka tashi suka tafi wurin motar da sauri,Driver ya farka a tsorace shima yace lfy? Hunaif yace Dabbobin daji ne harda su Damusa gasu can suna ta kuka,Driver ya koma gaba da sauri,Khairat da Hunaif suna Bayan mota,Abin mamaki Driver na gwada tashin mota sai kawai sukaji mota ta tashi lafiya Lau,farin ciki ya kamasu,yaja mota suka ci gaba da tafiya,Khairat da Hunaif bacci sukeyi sosai,har Allah ya taimakesu suka kusa zuwa garin daga Nan suka dauki Hanyar kauyen,lokacin 12am, Saida Driver ya kawosu lfy cikin garin sannan ya samu wuri yayi parking motar ganin darene Bai tashi Hunaif ba,shima sai ya gyara kwanciya ya fara baccinsa.
Basu farka ba sai Asuba Kiran sallah ya tashesu, da ruwansu Na roba sukayi Alwala sannan Hunaif da Driver suka tafi masallaci,Khairat ta Shimfida sallaya jikin mota tayi Sallah da azkhar sannan ta koma motar taci gaba da baccinta, Hunaif ma dawowa yayi yaci gaba da bacci,Driver kuwa ya bazama garin abinsa.
Tunda suke bacci sai sha daya suka tashi,Lokacin Driver tuni yaje table din me shayi yayi hadin kauri ya karya abinsa.
Khairat ta Kalli Hunaif,shima ya kalleta suka sakarwa juna Murmushi,Driver yace Hajiya ki fito tuni na tambayi gidajen da kuka bani Address an samu kuma.
Khairat ta fito ta Dan gyara Fuskarta da jikinta,Suka tafi,Gidan me Unguwar Garin shine Dan yayan Baban Khairat.
Khairat tace to kaji Ashe ma jinin sarauta zaka aura,dariya Hunaif yayi kawai suka Shiga gidan,da Sallama matar gidan ta amsa tana kallon Khairat,tace shigo,Khairat tace da bako nazo,haba gidan ai gidan jama'a ne ce Masa shima ya shigo,Ganin Hunaif ya shigo Dattijuwar wata juwa ta kwasheta don tunaninta Bature ne yazo,sai taji yayi Sallama Kuma ya gaisheta,ta amsa da fara'a sannan ta Shimfida musu tabarma katuwa,ga gidan ko Ina tsaf, Me Unguwa ta kirawo a dakinsa tace kazo kayi Baki,Tunda yaga Khairat yasan jininsu ce,Bayan sun gaisa da me Gari Khairat tayi Masa bayanin ko wace ita,Me unguwa yace Allahu Akbar dama Sabiu na Raye,Munje Munje baya zuwa karshe ma idan Munje Kano akace ya canja gida sannu Khairat,Allah yaji kan Mahaifinki Dan uwanmu,Khairat tace wannan Zan aura shine nazo na sanar muku,Ina shi Sabiun? Khairat tace Yana Kano tace Nasha wahala a hannunsa Nan ta kwashe labari ta bawa me Unguwa.
Me Gari yace ai tun Sabiu na yaro Haka Halinsa yake, ba mutumin kirki bane Allah Yana sane zai saka miki,yanzu ku huta kuyi wanka sai a rakaku wurin dangi kaf,Gidan Mamanki Yana can gaba damu,Khairat tana ta murna aka bawa Hunaif wani daki simintine aka sa carpet da katuwar Katifa yasha gyara,me kyau ko Ina fes,ita Kuma Khairat ta Shiga dakin Matar gidan me suna Adama.
Sai ga Babbar Yar Adama me Suna Suwaiba16yrs,Tunda taga Khairat ta manne Mata.
Adama ta Fara dafawa Hunaif ruwan wanka,yayi wanka da Brush,Khairat ma Haka,ga gida ya dau kamshin soye soye duk da cewa kauyene,Sai ga Adama dauke da katon tire ta kawo musu kayan Kari,Flask din Kunun gyada ne,ga chips,sai soyayyar doya da kwai,wani plate kuma cike da Naman zabi.
Khairat ta shirya cikin doguwar Riga black and red ta dauki tire din ta Shiga dakin Hunaif ta ajiye musu suka zauna suna ta ci magana kasa kasa kamar munafukai,Khairat tayi Muryar rada tace kaga a kauye harda Chips,Hunaif shima kasa da murya yace Kuma ta iya girkin Yar tsohuwa Haka,harda Kunun gyada cewar Khairat,Hunaif yace Dan Naga tana da Tsafta ne da bazan Ci ba,Nima Haka Khairat ta Furta.
Me Unguwa ne ya shigo suka ci gaba da Hira sosai suna cin abinci kamar sun Shekara da sanin juna.
Sai da suka huta sannan da Yamma Me Unguwa da kansa yace kuzo muje Khairat a rakaki wurin Dagacin garin Nan shine Yayan Mamanki uwarsu daya ubansu daya dake auren zumunci akayi shi yasa Kika gaji sarauta ta fannin uwa da uba,Khairat tanaji ta kalli Hunaif tana murmushi suka hada ido,kasa da Murya tayi tare da rada Masa kaji fa jinin sarauta ce Ni Dole kayi biyayya,Haba shi yasa a jikina nake tunanin Anya ba jinin sarauta bace Ni,sabo da Haka kawai Me Unguwa sai kaga Ina gadara da takama,na rasa Dalilin hakan Ashe ma ga inda nayi gado.
Me Unguwa ya washe Baki yace ai Dole kiyi domin Ummanki da Abbanki jinin sarauta ne,Khairat tace ai Kawu komai nawa sai naji kullum kaina Yana Kara girma,ga Isa ga mulki watarana idan abin ya motsa min ko magana bana yi,Me Unguwa shima kamar yaro biyewa Khairat yakeyi sabo da yanda yake Jin kansa Me Unguwa ne ka rantse sarkin Kano ne, Hunaif Yana jinsu dariya suke Bashi Akan me Unguwa da Dagaci irin na kauye sai Alfahari sukeyi.
Me unguwa ne ya katse Masa tunani da cewa ai Dole ki Zama me Gadara da Izza ai jinin sarauta ce ke gaba da baya,kwana Nan za a bawa Kanin Mamanki Me Unguwa again,Khairat tana murna tace ehem ai a Nan zan zauna har ayi bikina,Harara Hunaif ya watsa Mata tare da cewa gobe zamu tafi kima shirya.
Gidan Dagaci suka Fara zuwa,sunsha mamakin yanda Khairat ta girma Haka,Sunyi murna tare da Allah wadai da Jin labarin Kawu da Talatu,Karrama su Khairat akeyi sosai shi Kuma Hunaif Yana musu bulala da Kudade masu nauyi.
Har dare suna aikin Zaga dangi har suka Gama suka koma masaukinsu wajen Me Unguwa.
Me Unguwa kuwa da daren ya zauna tare da Khairat da Hunaif sai Matarsa Adama tare da Dagacin garin yace zai musu Nasiha tunda aure zasuyi.
Me Unguwa ya fara Nasiha sosai me ratsa jiki sannan karshe yace Khairat bamu gaji tsokana da wulakanci ba,karki yi tsokana Amma duk wanda ya tabaki ki taba shi ko waye,karki Bari a taka ki,kaf danginmu bama daukan raini,ki tabbatar kinyi gado,Mamaki ya Kama Khairat da Hunaif, Dagaci ya amshe yace ice ko a makaranta bakya ragawa kowa? Ko yatsa mutum ya nunaki to ki balla yatsan ko uban waye,Nan da kika ganmu kaf ba a taka mu a zauna lfy,kema karki sake sannan ki rike mijinki Gam karki Zama shashasha wata ta kwace Miki shi,Adama tace ato kinji dai da kike mace ki tsaya ki Zama mace sosai wurin me gida yaran yanzu ba wuya sun kwace Miki miji,ko kishiya za a Miki karki kulata da fada Amma tana tabaki ki wanketa da soso da sabulu,Khairat tace ai Kawu Sam bana ragawa duk Wanda ya Shiga gonata,nifa duk inda naje idan aka cuceni sai na bar musu lesson,Me Unguwa yace Mene lessin (lesson) Kuma?
Darasi cewar Dagaci sabo da Yana da ilmi shi yayi Nce.
Me Unguwa yace Madalla kinyi dai dai yanzu nasan ke jininmu ce,ai Me Unguwa gashi Nan ka tambayeshi shi kanshi ba kyaleshi nakeyi ba cewar Khairat tana Nuna Hunaif, shi Kam Hunaif dariya ma suke bashi abin nasu kamar wasan Yara.
Talatu a jirgin ruwa Kato tare da Kawu duk jirgin bata Gari sunfi yawa a ciki,sabo da Haka Ana bada abinci,Talatu ga cin masifa tace wannan abinci baifi na turashi a hanci ba aikin banza,ta tafi tace a Karo Mata suka ce sai dai ta siya,Talatu ta zaro Yar Doller darinta zata siya wasu Majiya karfi Maza masu kalar Yan China suka zo tare da zare Mata wuka,Dole ta Mika musu kudin suka fisge sukayi tafiyarsu abinsu.
Talatu ba abinci ba kudi,salab salab ta dawo kusa da Kawu ta zauna tare da yin tagumi.
Jirgin ruwa dai Yana ta tafiya abinsu lfy har Allah ya taimakesu suka kwashe kwanaki a cikin ruwa ba dare ba Rana har suka tsaya a lagos,Talatu tana Fitowa ta dinga murna tana godewa Allah sannan Kawu yace saura mu tafi Kano a Ina zamu samu kudin komawa ki Bari muyi Bara ko ta kwana biyarce mu samu kudin mota,ba da son ran Talatu ba Amma ya zasuyi Dole su hakura sabo da sun San baza a daukesu kyauta ba.
A Lagos suka zauna tare da Fara bara,lungu da sako suna ta Tara kudi,gashi kwana a kasan gada aikinsu ne.
Sun kwashe Kwana Uku ba karamin kudi suka Tara ba dake Kudu ne,Amma wahala ta ishesu, a kusa da shagon wani Yoruba suka zauna,Ranar Kuma wasu suka sacewa bayaraben sabuwar wayarsa me tsada,sai kawai ya kalawa su Talatu sata, yace Wai sune suka satar Masa waya,Nan fa rigima ta kacame,Yan uwansa Yoruba suka ratayawa Kawu Taya a wuya da Talayu zasu konesu,Kawu ya rushe da kuka Haka Talatu ma,Da kyar Allah ya kawo wasu Hausawa suka fanshi su Talatu da kyar kafin a konesu,ana sakinsu Talatu tace Ni da Lagos har a bada Nan taja Kawu sai Tasha, kudinsu Bai Gama cika ba Babu Wanda ya kulasu ,sai suka nemi trailer wacce ake eban shanu Ana kaiwa kudu,Kudi kalilan suka bayar Talatu ta daka tsalle ta fada Bayan motar Shanu,sannan masu motar suka daga Kawu sama tare da jefashi shima ciki,mutane da yawa Yan cirani suka cika motar Shanu tab sannan suka dauki Hanyar Kano.
Suna Tafiya Sunyi nisa sosai Yan fashi suka tare motar su Kawu Dan abinda ke hannun kowa sai da Yan fashi suka kwace,Sannan suka samu suka musu dukan tsiya duk jikinsu a farfashe gashi Sunyi tumurmusu a kasa sai suka dawo kamar an tono su daga cikin Toka kowa yagansu sai ya tausayawa su Talatu kamar Mahaukata Haka suka dawo suna doyi da tsami,a Motar shanun ma Babu Wanda ke matsawa kusa dasu.Talatu kuwa tana can karshen Motar ta time karfe idan ta bude Baki da niyyar yin magana Wanda yake farkon Motar sai yajiyo Doyin bakinta,hakora sun dafe, Sunyi yellow har gansa kuka suke,Gwara Kawu Yana wanka sannan Yana yin aswaki kullum da itace.
Wata Yare Igbo ce tana kusa daTalatu,sannan tana Jin Hausa Talatu tayi Hamma, kai.....matar ta Furta da karfi sannan tace me kana ci Haka? Cikinka na buso wari ohhh I can see Naga baki naka baka Brush?,pls Ajiya Kana wanka da Brush ka goge baki naka,Sai ki kashe mutum da wari.
Talatu na fada Miki bakya jin magana, zan iya sakinki fa kina cin darajar yaranki kawai Amma kazantar Taki tayi yawa cewar Kawu shima.
Talatu tace wahalar duniya ce kawai Amma Zan gyara halayena kayi hakuri.
Duk bake Kika jawo min ba, bakya bani shawarar arziki,naci Amanar Dan Uwana na jini,na cuci marainiyar Allah,na nuna son kai,bazan yafe Miki ba,Talatu Hawaye ya zubo Mata tace naga darasi ka yafe min,zan gyara halayena mu hadu mu gyara halinmu.
Yayin Da Zainab su Kuma damuwa ta musu yawa,wahalar yau daban ta jibi daban,ta gobe daban itama,ga rashin iyaye,sun Kara Masifar lalacewa komai ya tabarbare musu,gashi Mijin aure ma suke nema Amma ya gagara,Soja kuwa kullum bashi da aiki sai tunanin Khairat.
Yanzu Masifar son Khairat yakeyi,ya Kira wayarta har ya gaji Bata Shiga,damuwa ta Masa yawa, Zainab tana zaune tayi tagumi ga yaran kannenta na Kuka basa jure yunwa,sanaar wankin ma Bata
Samu ba,Rahinatu ce ta shigo futu futu da ita sabo da Babu Sabulun wanki da wanka,Leda ta ajiye tace Aunty ga garrin kwaki da sugar da kyar na Samu Dennis ya bani bashi, mu samu mu jika musha kafin dare muga abinda Allah zaiyi,Zainab ta kalli Soja ya kamata ka nemi sana'ar hannu ga wurin Uba carpenter can tunda mutumin kirki ne ya koya maka kana Zama kana samo mana ko na abinci ne,a Haka Khairat zata aure ka? kana zaune ba Sana'a gaka lafiyayyen Namiji Amma mu Mata mu muke Rika gida, mazan zamani matasa Musamman Hausawa burin kowa sai yayi kudi, sai Kuna Raina sana'a, matasa lafiyayyu Amma zuciyarsu ta mutu.
Soja Jin ance Khairat baza ta aure shi ba matukar Babu sana'a,sannan komai kankantar Sana'a yafi Zama Haka musamman a wajen Namiji,Nan take ya mike ya tafi wurin Uba Carpenter ya rokeshi Allah Annabi suka Fara aiki tare,sai gashi kullum Soja idan suka tashi Yana samo dari biyar dubu daya,watarana ma har dubu biyu Uba yake bashi, sai gashi basa rasa na cefane da sabulun wanki da wanka harda na Omon wankya wanke,gashi yanzu sun dage da Tsafta sosai suke gyara gidansu fes.
Soja shima yanzu yafi Jin dadin rayuwarsa,sannan ya tabbatar da shi Namiji ne Yana rike kannensa.
Mus'af Kwance yake a Hotel Room dinsa Bai San Hunaif yayi tafiya ba,sabo da Sam Hunaif yanzu ba komai yake fadawa Mus'af ba,Ummi ma kanta ce Mata yayi ya tafi Meeting Kwara state,Bata San me ya tafi Yi ba bare wani Mus'af,Tunanin Khairat ya hanashi Sakat idan Kuma ya tuno Hunaif na sonta shima a fili sai ya Furta sai naga bayanka Hunaif,baka Isa ba,baza ka auri Khairat ba nine nake sonta Dani ta Dace.
Washe gari Hunaif yayi Shirin komawa Abuja sannan Fafur yaki yarda Khairat ta zauna wurin danginta har ayi bikinsu,Dole ta hakura zata bishi su Koma in yaso idan an kusa Bikin saura sati daya sai tazo har ayi komai a Gama a kai Amarya.
Bayan Sun dawo Abuja da Sati daya,Hunaif ya sanarwa Ummi da Yanzu Yana tuna Khairat wacce yace zai aura Nan ya bawa Ummi labarin komai Haka suka ga Dr yace a hankali ma zai tuna komai,zai dawo normal,farin ciki ya cika Ummi,ba tare da Bata lokaci ba ta sanarwa dangin Uban Hunaif Kan suzo nemawa dansu Aure.
Bayan sati Guda sai ga bakin Larabawa sun sauka a Nigeria,da Hunaif suka tafi Kauyen su Khairat suka Kai dukiyar aure da komai ,Ladi ta Hana Khairat komawa wurin danginta,tace can Kauye ne Babu kayan gyara Amarya,Ladi tace kawai suje can kauyen a dauro aure ke Kuma ayi shagalin biki a gidana Dangin naki duk suzo Abuja asha shagali Bayan an daura auren.
Haka suka shirya komai da Ladi duk da cewar ba shagali za ayi ba sai Kamu kawai za ayi sannan a daura aure a Kai Amarya.,su Kuma Dangin Khairat suka ce sai dai Khairat taje can ko Ana gobe Daurin aure ne,idan an daura sai a kawo Amarya a mutunce,Hunaif ya dauki nauyin komai na biki.sannan Ummi tasa ya bawa Khairat kudi masu nauyi na gyaran jiki,Ladi Kuma tare da kawarta me Hada Amare sun Fara aikinsu Akan Khairat.
Hunaif a waya ya Kira Khairat Kan ta fito Yana kofar gidansu,lokacin da yamma ne,Khairat ta kalleshi tace muje yawo a kafa mu Dan zaga layin Nan,Hunaif Bai San manufar Khairat ba ya biye Mata suka jera suna tafiya tare gwanin Sha'awa, farin ciki ya mamaye musu zuciya,suna Jin wani nishadi da shauki,Hannunta ya rike ta fisge abinta tare da cewa sai ka Bari sai an daura Auren tukun,Oh Dan na rike hannunki wannan Hannun naki ma duk tauri ba laushi,Tafiya suke suna Hira Khairat tana ta zage unguwar da Hunaif Ana ta kallonsu,Hunaif yace Wai Ina zamuje ne sai zaga unguwarku mukeyi har Tasha da kasuwa kin kaini,Murmushi tayi tace so nake nayi yanga da gadarata kowa yasan Ina da saurayi me kudi Kuma balarabe kalli yanda na birge mutane sai kallonmu ake kowa Yana Jin dama shine,Dariya Hunaif yayi suna tafiya duk Majalisa sai Khairat tace musu Salamualaykum idan tasan wani a ciki ma sai ta Kira sunansa sun gaisa dan a gane Khairat ce da Alhaji Hunaif.
Majalisar su Me Dawa suka zo wucewa ta wajen suna ta Shan wiwi, Khairat ta musu Sallama suka amsa tace Me Dawa a huta lfy, kishi da takaici ya mamaye Me Dawa, Khairat ta Kalli Hunaif cike da Shagwaba tace Ni ka bani Kudi a Dan Yi musu kyauta,Hunaif ya zaro Yan dubu dubu ya Bata Yana Murmushi,ta mikawa Me Dawa tace gashi ku raba inji Alhajina, Murna ta kamasu suka Fara yiwa Khairat kirari sai Khairat ta Hunaif,Khairat tace Alhaji Hunaif Naira cikakken sunansa Haka ake ce Masa,Kiri Kiri ta karfi a Unguwar Nan Khairat sai tace sunansa Alhaji Hunaif Naira,Mata kuwa sai Sha'awa suke da kishi Ina ma sune suka samu Hunaif balarabe.
Khairat abin nata Bai tsaya a Nan ba sai da ta shiga da Hunaif gidan Makwafta da suke mutunci,tayi ta Sa Hunaif Yana Kyautar kudi,Kafin kace me an San da zaman Khairat a Unguwar tare da Alhaji Hunaif Naira,sai girmama Khairat akeyi,Hunaif ya gaji ta rokoshi mota tace Alhmdllh na kankaro mutunci na Dama yan unguwar Nan suna min kallon talaka Yar tuwo tuwo me Saida Kati Basu daukeni komai ba,kowanne gara sai yazo wajena,to yau na Gama dasu,Burina ya cika kayi hakuri na wahalar dakai Naira tayi kuka. Murmushinsa Mai tsada yayi yace ba damuwa,shi Hunaif baida zafi babu ruwansa,hakan ma yasan yarinta da kuruciya ce ke damun Khairat dinsa birgeshi takeyi,komai tayi sai ta birgeshi Bata laifi.
Bayan Sunyi Sallama tace Kai me Kudi Ni jinin sarauta ce karka Fara girman Kai Kaga yau Ina cewa me kudi to Nima Ina takama da sarauta.
Dariya Hunaif yayi tare da riko Hannunta zai Mata Kiss ta fisge hannunta ta gudu gida tana daga Masa hannu.
Murmushi kawai yayi sannan ya ja motarsa ya tafi gida.
Biki naje kwana biyu kunji Shuru fans afwan.
AsmaBaffa
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that -
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 13