yace ku Shiga,ga mutane Nan a ciki cike da mota, sai dai Kamar kiftawar Ido sai sukaji Driver ya tsaya wani yace a Nan Zan sauka,Driver ya juyo da kansa Yana kallon su Talatu yace daga nan baza mu sake tsayawa ba sai a birnin sin,Baki Talatu ta bude tace Birnin sin can kasar China karshen duniya? Driver yace ae, da sauri tace a Nan zamu sauka,da Sauri taja Kawu suka sauka,sai taga motar ta Bace bat ba ita ba alamarta,Ashe dai Talatu motar aljanu ta suka shiga hhh.
Mutane suka gani kalarsu daban,Ana ta wani yare da Basu sani ba,Talatu ta samu wata mace Allah yasa tana Dan tsintar turanci Jin su Zainab suna yi,Talatu ta Fara turancinta na gwari gwari tace Me..From...Nigeria....where? Tana gwadawa da hannu tana turancinta na Yan koyo,Da kyar wani mutum ya gane me take nufi,yace You are In Kenya,Talatu ta fashe da kuka tace Sabiu motar Aljanu muka Shiga kamar kiftawar Ido har sun kawo mu Kenya, Kawu Hawaye ya kwararo Masa yace shike Nan sai gawar mu,Talatu Kenya fa kikace?
Kawu yace Kai Khairat Allah ya kwashe Miki albarka,yanzu ya zamuyi? Talatu tace wasu zamu nema a sanarwa hukuma sai a dawo Damu gida,Haka suka Fara garari a cikin kasar Kenya gashi a Kenya dinma can Kauye aka sauke su ba cikin birni ba sai wahala suke Sha,Har ga Allah Khairat Bata San su Talatu Haka zata kasance dasu ba,tana da tausayi baza ta so hakan ba,sannan ba kowa yasan Ana Shiga motar Aljanu ba,Khairat tayi tunanin Dan Niger ai zasu iya dawowa.
Hunaif da Ummi suna Dining sai tuna abubuwan da suka faru tsakaninsu da Khairat yakeyi,wayarsa ta Fara ruri Mus'af ne ke kiransa,dagawa yayi suna gaisawa irin ta abokai, Mus'af yace Hunaif akwai matsala a Company dake Rivers State jiya naje kudade da dama ban san ya akayi ba sun bace naje na Gama bincike na ban San ya akayi ba,Hunaif yace kudin masu yawa ne? Mus'af yace zasu Kai 90millions na yanke shawarar korar maaikatan baki daya matukar kudaden Basu fito ba,Hunaif yace Amma Taya za ace kudi Haka sun bace dare daya? Ummi tana jinsu tasan Mus'af ne ya shirya komai makaryaci ya sace kudade, me yasa su sauran masu Amana ba a asarar sisi Amma shi komai matsala a jikinsa ta Kare,daga yace wannan sai yace wancan, Bayan Hunaif ya Gama waya Ummi tace a rufe Company din kawai,Hunaif yace to Musaf din Kuma Ina zai samu kudin da zai inganta rayuwarsa Dana danginsa? Ummi ta kalli Hunaif kawai tace shi ya sani sai ya nemi aiki a wajen wasu Amma ka sani bazan Rufe Company din ba Amma Zan Dora sabon Manager both har na Kano.
Hunaif Ummi yake roka data bar Mus'af Amma Ummi tuni ta canja Shugaban Company daga na Kano har na Rivers, Mus'af Yana Office Sai takarda yagani an Mika Masa cewar an saukeshi daga matsayinsa an maida shi karkashin wani Wanda Ummi ta kawo,yasan ba Hunaif bane Aikin Ummi ne,bakin ciki da Tsanar Ummi ya Kara darsuwa a ransa,a fili ya Furta Dole nayi maganin wannan uwar Banzar, sake Sake Musaf yakeyi kawai yanda zai kassara rayuwar Ummi wacce ta shige Masa hanci da kudundune.
Yau Ladi ta bawa Khairat dubu Ashirin kyauta Kan taje ta siyi kayan kwalliya,Yau Bata yi tallan Kati ba,Da yamma kwalliya tayi sosai tayi Masifar kyau cikin ready made Doguwar Riga light blue da baki, takalmi da jaka duk Black ta shirya ta Shiga Taxi sai cikin garin Abuja,ta shiga katon Mall na gani na fada na manyan masu hannu da shuni Amma Iyayin Khairat da Dan kudinta tace Nima na masu kudi Zan Shiga Kar a barni a baya, komai ta daga sai taga tsadar masifa, tunda ta Shiga ta kasa ko zabar Abu daya komai tsada,sai zaga wurin takeyi,karshe taje layin cosmetic ta dauki wani jambaki maroon taga an rubuta dubu Bakwai,ta hangame Baki tana kallon jambakin, Hunaif ne ya shigo Mall din shima zaiyi siyayyar da kayansu na maza.
Khairat ya gani tana ta daukar Kaya idan ta kalla sai ta mayar ta kasa daukan Abu ko daya,ta dauki wata powder 15k Yar karama da ita,Khairat tace kai Ana tsada a kasar Nan,ba Imani ba tsoron Allah,Yar wannan Powder har 15k to baza a siya ba din aikin banza barayin mutane,Hunaif Yana gefe Yana kallonta Yana dariyar maganganunta ita kadai,karshe yaji tace an fasa siyayyar ma,tana fita ya fito,duk abinda yaga ta dauka sai da ya siya Mata har ma da Wanda Bata duba ba,Kaya sosai ya siya Mata iri iri masu tsada,yaransa suka zuba a motarsa ya karbi Key yace zai je shi kadai,sauran motocin suka koma gida dasu shi Kuma ya nufi garin Suleja wurin Khairat.
Yayi nisa a Hanyarsa wayarsa tayi Kara Farouq ke kiransa Yana dagawa yace Ina Abuja gani a palonka Ummi tace ka fita kana Ina? Wani wuri zanje can Suleja wurin yarinyar da na baka labari Ina iya tuna ta ita kadai,Farouq yayi Murmushi yace ko dai so ne ya kamaka? Tsaki Hunaif yaja tare da cewa Allah ya kiyaye wannan Yar yarinyar karama ko 19yrd Bata Kai ba, Dariya Farouq yakeyi yace wait for me zanzo muje na ganta,Hunaif yace ok Bari nayi Parking sa Driver ya kawoka petrol station na Total, 10mnt sai ga Farouq Driver ya saukeshi ya shige motar Hunaif suka tafi,Hunaif ya Shiga bashi labarin Khairat ga kida na tashi a motar tasu,Yace Wato Farouq Ina fada maka yarinyar baiwa gareta,Farouq dariya kawai yake kwasa,Yana biyewa Hunaif yace Allah mutumina ai tunda naji kana iya ajiyeta a memory naka nasan Yar baiwa ce,Hunaif ya karo Sautin kidansa Yana wani nishadi har kada kai yakeyi Yana Murmushi yaci gaba da cewa Farouq yarinyar Nan gata Masifaffiya ce fa kullum idan muka hadu fada mukeyi,gata tana da kyau shegen iya Shagwaba ne da ita,Farouq ya sheke da dariya yace tab Lallai ta hadu to, Hunaif ya Dan kalli Farouq sannan yace Kai fa Dan iska ne Ina baka labari Kuma kana min Dariya,Farouq ya matse dariyarsa yace na daina to.
Hunaif yace baka ga Dan bakinta ba idan tana masifa Ni kaina ta rainani,idonta idan tana Harara har wani spark sukeyi,sai naji zuciyata ta Fara wani Das..Das...Das..sai kuma tace Dit...Karshe sai dai naji zirrr...a cikin jini na,Farouq kasa danne Dariyarsa yayi ya dinga Kyakyatawa har Hunaif yayi Fushi yace ya daina bashi labarin ma.
Lokacin da suka shigo Unguwar su Khairat ta talakawa Me Dawa Hunaif ya fara gani suna tsaye tare da Khairat,Me Dawa Kiran Khairat yayi Kan shifa da gaske son Khairat yakeyi,ganin ta kulasu sunje gidan Hajiya Baturiya shine yake tunanin zata so shi,Khairat ta Kalli me Dawa tace Dan Allah kayi hakuri wlh Ina da Wanda nake so,idan kudin Wiwi kake bukata Zan na San maka watarana.
Me Dawa ya Hasala dake shima Saurin fushi ne dashi,Haka Khairat ma akwai Saurin fushi sannan basa son rainin hankali,Me Dawa ya daga Murya Dole ki Soni Wai ke Baki da Imani ne Ana miki magana aikin banza,Khairat tace kaci darajar yau Birthday na, ba komai na yafe maka, ta juya ta bar Me Dawa a tsaye,tsaki shima yaja ya juya ya tafi,Hunaif Yana kallonsu sai yaji ransa ya baci ganin Khairat tare da wani, Farouq kuwa Bai ma kula da komai ba,har Khairat tazo ta jikin motarsu ta wuce,Ashar Farouq ya saki tare da cewa Hunaif kaga wata hadaddiya kuwa? Gaba daya ta haske unguwar Nan,Talliya Sunan wata Kai ban taba ganin me kyan wannan ba.
Hunaif yace itace yarinyar Dana ke fada maka to,Lallai ta hadu,Hunaif ya balle murfin mota ya fita yabi Khairat a baya, yace Ke..da sauri ta juyo Jin Muryar Hunaif,Farouq Yana kallonsu dake haske ya wadaci layin,Cike da masifa ta dawo baya zuwa wurin Hunaif tace nifa tsakani da Allah ka dameni kuma,Tunda baza ka iya tunawa Dani wace ba ka Sarara min,ka sakar min Mara nayi Fitsari, na Sakar Miki mararki tsula fitsarinki cewar Hunaif,Shuru tayi sai data gaji tace to Mene? Shuru yayi Mata Dan Bai San Me zai Mata ba face ya tsokane ta suyi fada,Yace mamaki nakeyi da kika ce nasanki kina mummuna Haka kamar Ni Zan ko kula irinki? Fada min" Haka dama muke soyayya dake kullum fada? Ga Yan Mata Nan hadaddun Taya Zan kula irinki,Jin cin fuskar da yayi Mata sai zuciyarta ta baci Amma ta danne,Sai baya ta juya Masa da sauri tana goge hawayenta ance Bata da kyau,irin son da take Masa Amma muninta yake gani Taya zai so ta.
Juyowa tayi ta kalleshi idonta yayi jajir ta rasa me zata Masa kawai sai tace ka cuceni maye kawai,Wai Dan shima ta bashi haushi.
Dariya ta bashi ma.
Kallonsa tayi tace Maye me farin zabiya,tsoho kawai Dattijo, Ni sai Dan yaro Dan Shila,Farouq Yana gefe Yana kallonsu Yana dariya,Baki Hunaif ya tabe yace to Ni me zanyi da ke kin min yarinya,Hannunta ya rike tare da shafa tafin hannunta yace Kai yanzu wannan ace hanun mace ne,hannu duk kaushi kamar Bayan crocodile,Ba shiri Khairat tayi dariya tace wannan Kuma ko hassidin bazai ce min Haka ba,yaro anji hannu kamar auduga Kai fa? fa dogo zankala koki kafi kowa tsayi zamarke ,ta nuna Farouq tace frnd naka ya fika kyau shi nake so,Murmushin dake Kara Masa kyau ya saki,Khairat tayi dagalolo tana kallonsa a duniya tana kaunar Hunaif.
Manyan Ledoji ya fito Mata dasu yace gashi Nan yau kinje Shopping kin kasa siyen komai talaka dake kawai,Mamaki Khairat tayi yaushe ya ganta ita bata sani ba,Amma taji dadin kyautar tasa,ba Bata lokaci ta karba tace nagode badan halinka ba,Kuma Dan na Isa aka siyo min sai ni Khairat me sa mutum yayi kyautar dole ba tare daya shirya ba.
Mota Hunaif ya Shiga Yana Dariya,Farouq suka gaisa da Khairat sannan taje jikin motar saitin window Hunaif dake mazaunin Driver ta Dan matsa da kanta ciki ta kalli Hunaif tace Yaro na Dolenka ka siyo min, kwanan Nan zaka Fara kirana da Aunty ta dole.
Dariya yake kawai yayi sama da glass dinsa yaja mota suka tafi Yana wani nishadi,Khairat ma ta kwashi kayanta tayi Gida tana murna Dadi ya Gama rufeta.
Farouq ya kalli Hunaif Akan hanyarsu ta dawowa yace Kai Hunaif wannan love Haka da kuke Sha,tsaki Hunaif yaja ku fa Hausawa komai naku kuce soyayya,kawai Ina Jin dadin yanda muke fada Memoryna Yana ajiyewa that's all.
Mus'af ganin yanzu baya wani samun kudi kawai sai ya tattara ya koma gida ya daina zuwa Office kudin daya Tara su ya zauna ya Sa agaba ya bude duniya yana tsikararta da tsinke,Ummansa da Babansa Sunyi Masa fada da Nasiha har sun gaji sun kyaleshi, aikinsa ya kwashi Mata su tafi Hutawa Yana kashe musu kudade,daga wannan budurwa sai waccan,Shine wajen Aisha,Badriyya,Salima etc har Aikin Hajji ya biyawa wasu Yan Matan nasa,shine siyawa Budurwa wayoyi masu tsada etc anan kudinsa suke karewa sai shaye shaye da ya karu Akan da, yanzu yaci uwar uban da a shaye shaye,yanda yake bulbular hayaki ka rantse salansar mota ce.
Sabo da shaye shaye duk sai ramewa yakeyi Yana karmashewa sai Dan wuya,Umman Mus'af musamman ta Kira Hunaif ta karanta Masa halin da Mus'af ya sake canjawa tace dan Allah yayi Masa fada,sannan ta Kira Ummi tace danki ya dakko hanyar lalacewa Dan Allah ki Masa fada.
Ummi Bata ji Dadi ba sai kawai ta tausayawa Mus'af tasan zarginsa take da rashin gaskiya Amma Bata kamashi da kanta ba sai kawai ta maida shi matsayinsa na da yanda yake a Company din,yaji Dadi sosai,Haka Hunaif ya dinga Murna abinda Ummi tayi yaji Dadi ko ba komai Mus'af din nasa zai gyara halayensa idan Yana samun kudi sosai.
Shi kanshi Mus'af yaji Dadi sosai sai dai ya kullaci Ummi a ransa Yana Nan ya rantse sai ya dau fansa,sannan Kuma har yau Hassadarsa tana Nan Akan Hunaif ya tsani yaji Hunaif ya fishi,burinsa ya kassara Arzikin Hunaif kowa ya rasa,ko zai talauce yafi son Haka matukar Hunaif ma zai talauce.
Khairat Kuma murna takeyi ta Rama abinda su Talatu suka Mata ko ba komai ta nuna musu iyakarsu,Sannan Hajiya Baturiya ma Haka sannan tana so Nan gaba Dole ta tashi gidan Baturiya sabo da sabon Allah da akeyi yayi yawa,sai Kuma Musa'af Wanda tafi tsana a duniya hanya take nema da za tayi maganinsa irin abinda ya mata.
Rokon Allah take Hunaif ya aureta ta samu Mus'af a banza tayi maganinsa kowa ya huta.
Mus'af kuwa sabo da yasan ta Ina zai bullowa Ummi sai yace ya dauki hutu a Office zai zo Abuja gidan su Hunaif zaiyi 2mnths,Ummi Bata damu ba,Hunaif Kuma har da Jin Dadi ma.
Yau Sunday Hunaif Yana guest House nasa tare da Musaf Wanda ya sauka a Abuja jiya,suna Hutawa suna ta buga game,Sai Mus'af yace Wai Ina Yan aikin gidan Nan ne? Gidan ya min Dirty Kuma yunwa nake ji ya kamata kasa a Mana abinci,Hunaif yace me abincin ta tafi ganin gida Amma Bari na Kira wata yarinya na biyata kudi tayi mana ko nasa Ummi ta bayar a kawo Mana? Mus'af ya tabe Baki kawai ka kyale Ummi ta huta, Kira mana yarinyar.
Hunaif ya nemi waya tare da Kiran Recharge card Sunan da ya sawa Khairat kenan.
Tana dagawa yace Guesthouse Dina Zaki zo ki dafa mana Abinci Zan biyaki bako nayi,Ladi ta kalla sannan tace tsaya na fadawa Anty ko zata Amince,Ladi ta sanarwa,Ladi tayi shewa tace Kai yaron Nan akwai iyayi wlh,kudi ne suka Masa yawa yaro da kudi,tunda biya zaiyi maza jeki ga harkar Karuwa,Amma dai ki kula ki tsare mutuncinki kina gamawa ki dawo,sannan ki kiyaye kadaicewa da Namiji baligi a gida daya,Dan ma yaron Naga me hankali ne da Dan iska ne baza kije ba,Khairat tace ai na sanshi tun a Kano,Ladi tace ok sai kin dawo.
Khairat ta shirya tasa Riga da skert na lace tayi kyau da mayafinta tasa flat shoe ba Wanda zai ce batayi kyau ba duk da cewa ba kwalliya tayi ba.
Tana zuwa gidan taji kida na tashi ya cika gidan tun a Compound Ana ji, Door bell ta danna,Hunaif ne ya bude Mata sanye yake da jallabiya Fara fitted ta Masa kyau matuka ta tsangale Masa Balarabe sak,kamshi ke tashi kawai,Yaki Bata hanya ta wuce Yana Kare Mata kallo,kawai ya tuno da rannan da Bra dinta ta dawo cikinta Bai San sanda ya kwashe da dariya ba,Khairat ta harareshi ta shige ciki sai ko sukayi Ido Hudu da Mus'af, ba karamin Mamakin ganin Khairat Musa'af yayi ba,yasan Hunaif baya tuna baya to me ya sake hadashi da Khairat,Khairat kuwa dama tasan abokin Hunaif ne Bata yi mamaki ba.
Ganin yanda Khairat ta Kara kyau ,Nan take yaji shaawarta ta taso Masa,gata me kyau Wai me yasa kullum Hunaif ke da sa'a ne a rayuwarsa,samun mace irin Khairat ai sai an tona Amma ga Hunaif a banza ya samu,Wani bakin ciki ya Kama Mus'af Ina ma shine Khairat ke kulawa.
Ita kuwa Khairat Harara ta watsawa Mus'af ganin kallon da yake mata,Amma dake munafuki ne bai nunawa Hunaif ya santa ba ko tayi aiki a karkashinsa ba,sai ma cewa yayi a Ina ka samo wannan Yar kauyen kuma,? Khairat tace bashi kaci a ranta,Hunaif baiji dadin Furucin Mus'af ba sai ya share shi kawai suka ci gaba da buga game,Khairat Kuma ta Shiga kitchen tana girkinta,tana gamawa Hunaif ya sata gyara gida Nan ma tayi sosai ko Ina ya fito neat.
Suna ta game tana sani ganin Mus'af Yana ta hararar Hunaif a boye sai ta zauna kusa da Hunaif,tace ranka ya Dade an Gama komai? Wani tsaki Mus'af yaja,Hunaif ya kalli Khairat yace kin rainani fa,Murmushi tayi tace dan Allah kafin na tafi koya min game din Nan Zan na Yi a gida,tun rannan nake so na koya na kasa,Hunaif yace Ok Mus'af Bata Handle naka minti kadan, hararar Khairat yayi tare da jefar da handle din ya mike ya koma Dining ya Shiga cin abincin Khairat me shegen Dadi Wanda shi kadai sai Santi yake a ransa,da niyyar cin kadan yaje sai gashi Yana ta ci.
Game suka Fara da Hunaif Yana koya Mata suna ta faman dariya,Khairat idan taci sai Murna,wata suka sake sai Hunaif yake ta cinye ta Bata iya ba,yace bafa Haka akeyi ba ya ajiye Handle nasa ya daura hannayensa saman nata dake rike da Handle ya fara koya Mata kin gani,wannan idan kika danna sai kiyi pressing wannan,hannayensu ya Hadu wani shock suke ji a jikinsu,Kasa Kallon Computer Hunaif yayi ya koma kallon Fuskar Khairat gasu gaf da juna,tana shakar kamshinsa Wanda ke kashe Mata jiki,. Mukus tayi ta sandare a Haka sabo da abinda take ji a jikinta,Hunaif ma Haka gashi sai magana yake mata a hankali cikin kunnenta,Wai koya Mata game yakeyi a Haka,dukkansu Babu Wanda ke Fahimta sun manta ma game sukeyi jikinsu kawai wani shock suke ji Wanda Basu taba ji ba Tunda suke.
Mus'af bakin ciki ya Masa yawa Yama rasa me zaiyi kamar ya hadiyi zuciya,karaji ya kwarara kamar zai kashe musu dodon kunne Wanda ba shiri suka dawo daga duniyar da suka Lula,Khairat ta mike da Sauri tace Zan tafi,Hunaif ya Mika Mata dubu Hamsim rafar yan dari biyar, Musa'af yayi tsalle ya cafki Hannun Khairat tare da fisge kudin Yace Akan Dan wannan abin da tayi shine za a Bata har kudi Haka,wannan karuwar Banzar matsiyaciy.....tas..tas kakeji Khairat ta wanke Mus'af da Mari har biyu tace uwarka ce Karuwa,Kai ka Isa ka taba min ko hannu kazami da kai,Musaf ya mutu a tsaye Ya rasa na Yi Khairat ta fisge kudinta a hannunsa ta kwasa da gudu tasan idan ya dawo hayyacinsa sai ya kusa Halaka ta,Shi Kuma Hunaif shi kanshi Khairat ta bashi haushi ta Mari abokinsa duk da yasan Laifin Mus'af ne amma baiji dadin Marin Mus'af da tayi ba,Bai San Khairat tun tuni da wata a tsakaninsu da Musaf ba, Bai San dama hanya take nema ba,shima Mus'af dama burinsa ya tozarta Khairat tun tuni sai gashi ta rigashi daukan mataki.
Har zai zauna ya fasa yayi Kan Hunaif da masifa wlh kaje ka kamota na Rama tun wuri,Dariya Hunaif yayi kaji kunya Kato da Kai ka tsaya 18yrs girl ta Mareka Haka Kuma ka kasa komai,ai da nine sai na ballata.
Tunda Khairat ta fita da gudu Ashe ba tafiya tayi ba,ta glass din window take lekensu tana jinsu,tana kallonsu farin ciki ya isheta sai Muryarta suka ji ta window ta zuro hannu ta dage labilen tace Musa'af in ka Isa Kai Kaine ka Rama,kalli yanda na zabga maka Mari, in Allah ya yarda sai fuskarka ta kumbura tayi ruwa, wullu ta Masa gwalo Dan bakin ciki kalli kudina a hannu,Kai baka sanni bane Nan gaba sai na zubar maka da hakora,Wai Kai me kudi har da wani gadara kana wani kashe kala kana Shiga shadda Kai me kudi, kallonta Mus'af yake galala,tace hum hum Dalla can daina kallona Ido kamar na zakara.
Tana ta surutunta Bata San Hunaif ya bar Palon ya fito wajenta ba sai ji tayi caraf an kama Mata hannu Kam,Tayi matukar tsorata ta Fara Dan Allah ka sakeni,in kanawa Allah,wlh na tuba,bazan sake ba,wayyo uwata wayyo ubana,Kokawar kwacewa take ta kasa ta tsuguna tana Jan hannunta dake cikin nasa, Amma ta kasa kwacewa tana ji yace Mus'af fito gata sai ta rushe da kuka,wlh bazan Kara ba, Mus'af Kam da murna ya fito da belt a hannunsa ya kusa karasowa sai Hunaif ya saki Khairat yace ki gudu,ai ko ta arce a guje tana dariya tace wullu na Mari banza.
Takaici yasa Mus'af ya dauki key din mota kawai ya bar gidan Hunaif a fusace sabo da yaga Lallai Hunaif son Khairat yakeyi,ya daina damuwa dashi,Kuma duk ranar daya Kama Khairat shi kadai yasan me zai Mata,Khairat Kuma tuni ta shige taxi ta gudu Garinsu Suleja.
Tnx fans.
AsmaBaffa
[9/25, 9:41 PM] +234 906 331 4694: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚
41-45
Official
By
AsmaBaffa
Wannan page naku ne Yan albarka:
Fulani Gal
Hajara
Faheemah,Uss,Hamnah,s.y.sagagi,Jeeddah luv,Bintu Rasul,Maman Fatima yobe,Nana Mahmud,Me kubewa da Kuka,Mmn Sajida and Halima,Aisha Idris Abdullahi.
Fans Wanda ban ba page ba afwa Ina sane daku Zan baku inshallah daya Bayan daya.
Mus'af Bayan ya bar wurin Hunaif Hotel ya wuce ya Kama room ya kwanta sai Kuma ya Shiga tunanin Khairat,ya kasa mantawa da ita sai tunana Abinda ta Masa yake,maimakon yaji haushinta sai ma yaji ta birgeshi, tunawa yayi yanda ta leko ta window tana Masa rashin kunya sai ko ya fashe da dariya Yana tunawa,ya Dade Yana tunanin Khairat ya kasa mantawa da ita Yana so ya daina tunanin Khairat Amma ya kasa,ya tabbatar son Khairat ne ya Masa shigar sauri,Tunawa yayi da Hunaif na sonta,zumbur ya mike a fili yace Ashe za ayi bala'i Hunaif bazan taba Bari ka rigani auren Khairat ba,na fika sonta,Dani ta Dace,idan na sameta na more duniya na Gama amsa kaddarorina na duniya.
Hunaif Kam da Mus'af ya tafi yasan zai dawo Bai damu ba yayi wanka ya shirya yaci abincin da Khairat ta dafa sannan ya tafi gida abinsa wurin Umminsa, a Bedroom ya Iske Ummi ya zauna a gefen bed dinta suna ta hirarsu irin ta uwa da danta,Ummi tace Hunaif yanzu baza kayi aure ba? Murmushi yayi yace na kusa Ummi ki Kara min time kadan Zaki Sha mamaki,Murmushi tayi tare da Furta ko Kai fa Allah ya shige Mana gaba,karka manta da adduar bacci,ok ya Furta ya nufi part dinsa.
Khairat tana komawa Gida ta mikawa Ladi kudin gaba daya,Ladi sabo da itama Mayyar kudi ce Dubu biyar kacal ta bawa Khairat ta rike sauran Akan ta bawa Khairat wurin kwana,itama Khairat Bata damu ba Tunda Ana bata Abinci da wurin kwana an Gama Mata komai,wanka ta fesa tayi Shirin bacci ta kwanta tunanin Hunaif ya lullubeta,Bata iya komai sai tunaninsa kala kala musamman yau Yanda yake koya Mata Game.
Murmushi takeyi harda Shure Shure sabo da Jin dadin tunaninta, Ladi ce ta shigo dauke da Farfesun kifi a plate ta iske abinda Khairat takeyi,Ikon Allah ke lafiya kike kuwa Khairat? Firgigit ta nutsu tana kame kame,Ladi tace ga farfesun Nan naki kici kafin ki kwanta,Godiya Khairat tayi ta mike tana ci.
Kirit... wayarta tayi kara tana dubawa taga Message ne na Hunaif da sauri ta dauki wayarta ta bude ta karanta sakon Haka: thanks for today, How u?
Murmushi Khairat ta saki tare da Masa reply da I'm Good,baka yi bacci ba?
Yeah! Gobe Zaki zo? kin iya Danwake? Khairat ta tuna sanda yaci danwakenta a Kano Amma yanzu Wai Bai ma sani ba,gaskiya yana Raina Mata hankali Wai ta iya Danwake yake tambaya,Murmushi tayi tace na iya,yace to pls gobe Zaki min? Khairat ta Masa reply da sai da yamma,yace ba damuwa Good night,ta tura Masa da sweet Dreams.
Bayan ta Gama cin farfesunta hannu da bakinta ta wanke ta dawo ta kwanta cike da nishadi Bacci ya saceta.
Talatu mutanen Kenya ga Kawu ya zame Mata Kaya ko Ina tana rike dashi suyi fada su Shirya sun kwashe sati biyu a Kenya ga Basu da kudin kashewa,Abinci ma ya gagaresu,sun rame,Sunyi baki,ganin ba Mafita sai talatu ta koma bara tana Jan Kawu suna bi titi cikin Tasha suna bara,Kawu yace Ina ma a kasar Hausa ne ai da tallan maganinmu zamuyi mu samu Kudi,Talatu bakin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 13