Share this page
su cinye kudin,ganin Haka Ummi ta matsa Masa kullum sai yayi rubutun abinda ya faru kafin yayi bacci, yayi iya yinsa Kan ya samu ya tuna ko wani abune ya kasa,Haka Yana so ko bacci ya kwanta ya tashi yaga ya tuna wani abin Amma ko kadan Baya tunawa,sabo da Haka sai gaba daya Hunaif Rayuwarsa ta canja ya koma so silent sosai baya Magana,Bai son a takura Masa,Ya Zama Masifaffe me bacin Rai da kunci baya faraa ko kadan yanzu. Tunda Allah yasa Mus'af ya gano shike Nan ya nacewa Zuwa Abuja wurin Hunaif ko yaushe sai ya shato kudi Wanda zasu Kai million goma sai yace Hunaif ya ranta Masa zai biya, shi Kuma Hunaif ganin Mus'af ne sai yace ka tabbatar ka biyani bashin sai suyi dariya sai shi Kuma Hunaif ganin Mus'af ne Frnd nasa sai yaki rubutawa tuna ninsa zai bashi Kuma baya biyansa shi Kuma baya iya tuna komai. Ummi Bata da sukuni ko kadan kullum tana dawainiya da Hunaif ya zata yi taga ya warke burinta kenan.ta manta Kuma Sunan budurwarsa da zai aura tunda Hunaif sau daya ya taba fada Mata Sunan Khairat,Ga yaran tuni Yar uwarta Amina tace ita a bar Mata su sun shaku hakan yasa Ummi ta barwa Yar uwarta su Hajiya Amina kuma tana rike dasu Meenal lfy a garin Katsina da take auren wani me kudi. Ummi da kanta ta Nemo Mus'af Kan ya fada Mata Sunan budurwar Hunaif tunda tasan abokinsa ne Dole zai sani, Mus'af yace Ummi wlh ban San Yana da wata budurwa ba Ni,kin San Hunaif da zurfin ciki ba komai yake fada ba,Ummi tace Ni na manta sunanta Amma ya fada min sau daya ko Khausar ko Karimatu tsakanin dai haka,Mus'af sai yayi zargin ko to Khairat ce a ransa,a fili sai yace Babu wata me suna Haka da Hunaif ke muamula da ita,Ummi tace wayyo Ina ma nasanta da Haka za'a daurawa Hunaif aure da ita ko zai samu kwanciyar hankali,bana Jin dadin ganin Hunaif a Haka kullum cikin kunci. Harara Hunaif ya watsawa Ummi a boye,a fili kuma ya kwantar Mata da hankali da kalamai masu dadi,kwanansa days suna tare da Hunaif ya tafi Kano abinsa, Farouq kuwa Allah sarki mutumin kirki kullum Yana Kan hanyar Abuja duba lafiyar Hunaif,Har ganin Likita kusan idan lokaci yayi da shi ake tafiya. Farouq ganin irin Su Musaf suna ta cutar Hunaif sai bawa Ummi Shawara kan Karawa Hunaif matakan tsaro duk inda zaije da masu take Masa baya gudun matsala,in kaga Hunaif ba karamin kyau da haduwa ya Kara ba sabo da yanda yake samun hutu da kulawa. Su Meenal kuwa gani Ummi ta sama musu matsugunni gurin Yar uwarta ba ta damu ta dakko su ba,Ummi sai takaici takeji Bata San wacce Hunaif zai Aura ba bare ta wuce gaba ayi musu auren haka. Ummi tana zaune watarana katsam ta tuna Sunan Budurwar da Hunaif yace zai Aura Khairat,tace kwarai sunanta Khairat. A waya ta Nemi Musaf ko yasan wata Khairat? Musaf ya sani sarai Amma sai yace Mata Bai sani ba ko daya, Ummi ta gama bincikenta Babu labari sai ta hakura taje ta karbo su Meenal suke zamansu wajenta,tace baza ta bawa Yar uwarta ba ta fasa tunda ita tana da Yara da yawa, Koda Hunaif yaga Ummi tare da Meenal da Mohd Sam Bai sansu ba sai ma tambaya da yayi Ina ta samo Yara? Tace kawai a gidan Raino ta karbo su zata rikesu. Khairat kuwa su Talatu sun Fara ganeta,musamman ramar da tayi kullum kuka ne aikinta,gashi an wuce 3mnths Hunaif Shuru kawai sai Talatu ta Fara kokarin dawo da halayyarsu ta Baya Kan azabtar da Khairat,Khairat tana daki a kwance zazzabi me zafi ya Kama ta,Wata kawar Talatu ce tazo daga Abuja suna Hira kawar Talatu Hajiya Abu tace Wai Talatu Ina yarinyar da kuke rikewa ne wannan kyakyawar? Talatu ta tabe Baki tare da cewa tana Nan da ta samo wani attajirin Matashi balarabe Amma munji Shuru. Hajiya Abu tace kina zuba Mata Ido ke Kuma yarinya me kyau Haka Talatu ai jarice a wajenki,da kin min magana ai da tuni kin Zama me kudi,Talatu tace Dan manzon Allah?, Kwarai kuwa cewar Abu,ki bani ita na tafi da ita Abuja na kaita gidan wata Hajiya uwar Karuwai ce,Kinga manyan sanatoci,Yan majalisu da manyan masu fada aji ake kaiwa su suna biyan kudi,idan ta samo kudin Rabi naki ne,Uwar dakinsu tana da quarter itama yarinyar tana da Quarter. Shewa Talatu tayi tace na yarda,Abu ta ce ai ke kawata bugu da Kari sai dai kiga Kuna zuwa Makkah,motoci sai kun zaba,to yarinyar taurin Kai gareta da kyar zata yarda,Hmm ai karya za ayi Mata kice aiki za a kaita birni tana kula da wata yarinya albashinta dubu Hamsim Kinga taji kudi sannan Bata son Zama daku Kinga zata Amince. Hmmm Abu yarinyar Nan addini gareta ko an kaita baza tayi karuwanci ba,ke irin wannan sunfi kowa iskanci ki Bari a kaita ki gani Bayan Haka ma idan Bata son maza akwai Matan Alhazawa da suke neman Mata kyawawa suna amfani dasu Zaki Zama me kudi Ni Nan duk wata Zan karbo miki kudin na kawo Miki ko na Aiko Miki dasu wlh,ki lallaba ta Sigar dabara mu samu kudi ta hanyar wannan zukekiyar budurwar,samun irin Khairat sai an tona kowa sai ya sota. Talatu tace an Gama Dole ma ta biki zanyi duk yadda zanyi Dole ki tafi da ita Nima na Zama me kudi,ai yanda take da kyau sai dai kiga Gomnoni na binta cewar Abu,Talatu tace shegiya sai kugu kamar na babbar mace ga kirji me kyau. Bayan sun Gama maganganun su Khairat Bata San me suke cewa ba taji dai kawai suna ta faman shewa, washe gari Talatu har daki ta samu Khairat,ita kanta Khairat tayi mamakin Talatu yanda take wani Magana a hankali da lumana,tace Khairat ba wani Abu ne ya kawo Ni ba face Hanyar arziki da Zan Miki,me zai Hana kibi Hajiya Abu zuwa Abuja Zaki samu aikatau Yan share share da kula da Yara a gidan Attajirai Kuma suna biyan kudi me tsoka ko ya kika gani? Baki Khairat ta tabe tace me yasa Baki tura Zainab ko Rahinatu ba ai kinfi sonsu a kaina sannan kinfi son ci gabansu Dani. Baki bude Talatu tace ai gani nayi kinfi Zainab da Rahinatu nutsuwa da hankali,gaki da hakuri Zaki jure ko wanne aiki,Khairat tunaninta baza ta sake ganin Hunaif ba kawai mayaudari ne,sannan idan ta zauna dasu Talatu tabbas sai ta koma Tallan magani,gwara ma taje aikin share sharenta ya fiye Mata,gashi ko banza zata zauna a Abuja capital city,Murmushi Khairat tayi tace na Amince yaushe Abu zata koma Zan bita,Farin ciki ya Kama Talatu zatayi kudi taje Makkah itama a Fara kiranta da Hajiya Talatu. Da sauri tace gobe goben Nan Zata tafi sai ku tafi kawai ki shirya kayanki. tun dare Khairat ta Gama shirinta tsaf da Sanyin safiya Abu tazo tace Khairat ta fito Su tafi,Zainab,Rahinatu da Talatu dariyar mugunta kawai suke wa Khairat,Kawu ma tunda yaji kudi za a samu yace Allah bada sa'a. Khairat ansa Doguwar Riga dark blue and white cikin kayan da Hunaif ya siya Mata masu kyau da tsada Allah sarki sai Murna Khairat takeyi Bata san Karuwanci za a kaita ba. Tasha suka je Khairat da katuwar wayarta da Dan ragowar kudinta dubu biyar tasa a jaka,Abu ta kalleta kawai tana dariyar mugunta a ranta,Khairat anyi tsuru a mota Ana kallon Hanya a zuciyarta Kuma in Banda tunanin Hunaif ba abinda take yi, har sukayi nisa tafiya ake ba tsayawa Ana zarara gudu. Wani nishadi Khairat takeyi Bata taba tafiya me nisa ba sai yau, har Waka Khairat take rerawa sabo da Jin dadin hanya tafiya mabudin Ilmi duk ta takurawa mutane a motar tana Danna waya tana wakarta Kuma ba a hankali ba,akwai wata Yar sanda a motar a dauketa zata koma wajen Aiki a Abuja take aiki Masifaffiya ce ta kalli Khairat da katuwar Muryarta tace Dan Allah yarinya ki Mana Shuru kin hana mu sakewa,sauri muke zamu koma aikinmu ke Kuma kin addabi mutane da wake wake a Haka kamar Yar birni,Khairat ta kalli Yar sanda tace yo Kya fada Mana aikin yi,tunda sauri kike wa yace ki fito yanzu ai da Asuba Zaki fito shine Zaki nuna kin San darajar aikinki, Dan kina Yar sanda sai kice baza muyi abinda muke so ba. Yar sanda ta Fara masifa kaga yarinya marar mutunci,da Alama Yar kwaya ce ki kalli Uniform ne jikina zanyi maganinki,Khairat tayi banza da ita ta canja salon wakarta ma yi take ba ji ba gani,Haka Yar Sanda ta hakura ta kyaleta,Driver Kuma dama Dan Gulf ne kawai ya kunna wakar Yan Wiwi Khairat ta iya da yawa,Driver har dukan sitiyari yake sabo da dadin wakarsa da yake ji shi da Khairat sun takurawa kowa ita kanta Abu yau tasan Khairat data dakko za a Sha fama da ita. Sun Shiga garin Abuja Wani katafaren gida taxi ta tsaya gidan ya Hadu katon gaske part-part ne fadin tsaruwar gidan Bata Baki ne,Khairat Yar kauye ta koma tana kalle kalle,sai da suka Shiga gidan Khairat tun daga bakin gate taga motoci wannan tana wane wannan da Alama tunanin Khairat gidan siyar da motocine Amma sai taga Yan Mata tsala tsala cikin Shiga kusan tsirara suna Fitowa ko wacce tana Hawa motarta suna fita,akwai Wanda Kuma Alhazawa ke saukesu. Khairat tun tana yin Shuru ta gaji da gani tace Abu wannan Amma gidan yawa ne Naga mutane Kuma kamar Yan bariki, Abu ta kalleta kawai tayi Murmushi tace Family House ne. Me gadi ne ya musu Iso har babban Palon Uwar Karuwai Hajiya Baturiya,Palon ma Yan Mata ne da Shiga tsaraici a waje,Shekeke suke kallon Khairat da Abu,wasu cikinsu har toshe hanci sukeyi,Hajiya Baturiya ta sakko daga sama cikin Shiga ta Alfarma,Dattijuwa ce ta Gama kwarzane fatarta da Mai farin har yayi yawa ba kyan gani,tattijuwa da ita Amma Tasha kitson attach ta Dame sosai tana faman tauna chewgum Fuskarta kwayar kwarjinin musulunci Babu ko digo. Zama tayi saman kujera ta Kalli Hajiya Abu sannan tace da Yan Matan dake palonta suna ta faman dannan waya tace ku bani waje,ficewa sukayi Baki daya,Abu tace Hajiya ga wata maaikaciyar na kawo Miki,wannan da kike gani sai kin Sha fama Bata iya komai ba,Murmushi Baturiya tayi tace gaskiya tunda ake kawo min Maaikata ba a taba kawo me kyan wannan ba gata yarinya sannan duk gidan Nan Babu wacce ta Kama kafarta a kyau da cikar zati,Fara Kuma natural wow gaskiya Abu kin kawo min hanya Babba kudin Sallamarki dubu dari Zan Baki cash,Abu tayi guda ayyiriri nanaye tace na gode Hajiya ai yarinyar akwai Shiga Rai mata da maza kaunar ta zasuyi. Khairat tana zaune ta kasa gane me suke nufi da maganganunsu,rafar Yan dubu ta mikawa Hajiya Abu,sannan ta kawo dubu Talatin tace ki kaiwa uwar yarinyar,Yarinyar Dole tayi tsada Mata da maza zasu so ta cewar Baturiya a zuciyarta. Hajiya Abu da murna tayiwa Khairat sallama tace ta tafi gida sannan ta bawa Baturiya Accnt number din Zainab Wanda za a dinga turawa Talatu kasonta duk wata,tace dubu Talatin din Nan ma gashi Hajiya ki tura musu kawai ta accnt din Zainab yayar Khairat ce,Nan take Hajiya Baturiya tayi transfer Yana Shiga Hajiya Abu Nan take ta Kira Talatu da Zainab suna ta ihun murna kudi sun Shiga,sannan Abu ta tafi abinta ya rage daga Hajiya Baturiya sai Khairat wacce tayi mutuwar zaune ta kasa gane me suke nufi da ita,Fuska Khairat ta kwabe zata saka kuka,Hajiya Baturiya tace No..no..Kar kiji tsoro fa ba abinda za muyi Miki ba cutar dake zamuyi ba,ki saki jikinki,Khairat tace wlh indai kuka min abinda zai cutar Dani na gane sai na Kone gidan Nan Baki daya,Talatu ta zaro Ido waje tace Kone mu zakiyi? Khairat tace da gudu ma kuwa. Sama taja Khairat suka tafi,nanfa Baturiya tasa aka kawowa Khairat lafiyayyun abinci taci ta koshi Tasha ruwa da lemo,bacci ya kwashe ta a nan,. Washe gari da safe da wuri Khairat ta farka tayi Alwala da sallah cikin dakin da aka Bata a matsayin nata ne,Sabo da Hajiya tana son samun kudi da Khairat sai ta Bata daki kusa da nata Wanda ko part Bata hadawa da sauran Yaran nata sai Khairat. Da Asuba Khairat ta Ware Murya tana rera Karatun Qurani ka rantse a radio aka kunna,Hajiya kasa bacci tayi Khairat ta dameta,har dakin Khairat tazo tace Dan Allah ki rage Murya Mana wanne iskanci ne wannan kin hanani bacci,a Nan gidan ba a wannan karatun,Hajiya ai sai kice ku arna ne ba Wai kizo kina min tsawa ba cewar Khairat,Baki bude Hajiya take kallon Khairat, Khairat tace kiyi hakuri Hajiya na manta Ashe Baku da addini gidan Maguzawa ne na kiraki da Christain, duk yaranta Babu wacce ke iya Kallon ta ma bare ya iya Mata musu sai Khairat ma bakaken magana take fada mata. Hajiya tace ke karki yi tunanin Wai ke wata ce da har Zaki fada min bakar magana wlh zanyi maganinki Naga waye ubanki a kasar nan,bani da mutunci ki kiyayeni Ina da Marasa mutuncin da Zan turo su Gyara min ke. Qur'ani Khairat ta rufe tare da ajiyewa gefe tace Hajiya kija mutuncinki Ina girmamaki ne a matsayin ke Babba ce,Marasa mutuncin naki ki turo su mana ai Ni irinsu nake nema, bana son zaman lfy Ni Nan da kika ganni,abin ya ba Hajiya mamaki Wai duk rashin kunyar da yarinyar tayi Mata Ashe Nan girmamata tayi,Ashe za ayita cewar Hajiya tace to mu zuba, ta fita sai kitchen tace Kar a sake a bawa sabuwar bakuwarta ko ruwa. Khairat Misalin 11am yunwa ta Fara damunta ta fito tana neman Hajiya ta ganta a Palo,tace Hajiya Ina kwana ko kallonta Baturiya batayi ba,Khairat tace Hajiya a nuna min aikin da Zan Miki su goge goge da share share me zanyi a ciki? Dariya Hajiya tayi da wasu Yan Matan Dan sun San aikin Khairat,Hajiya tace jeki huta sai zuwa dare Zaki ga aikinki. Khairat tace to yunwa fa nake ji ya kamata a bani naci na koshi Zan Fi Jin karfin aikin, Nayi me kyau,Hajiya Baturiya tayi Murmushin mugunta tace ai Nan gidan kowa ci da kansa yakeyi,idan kina da kudi ki kawo a siyar Miki da binci plate daya dubu biyu,Ido Khairat ta zaro Ni da Zan Miki aiki Kuma Ni Zan siyi Abinci?. Hajiya tace ga Yan Mata Nan tambayesu kiji komai a gidan Nan na kudi ne,ai ko sai Khairat taga Yan Mata suna ta bada kudin Abinci idan kin biya kudi sai ki Fadi me kike so Sai Hajiya tasa Yan aikin Abinci su dafa Miki a Baki. Khairat tace ban fa gane ba Hajiya ya kuke rayuwa kamar ba bil'adama ba? Baturiya ta kalli Khairat kawai ta dauke Kai,Wata budurwa Yar kwallisa tace in Zaki kawo kudin Abinci yarinya ki kawo ba a aikin banza a nan Yar kauye kawai,jahilar Ina ce ke baza ki gane ba,ko iyayen naki Basu sanar Miki me ya kawoki Nan ba? Khairat tace Ni Marainiya ce ku taimaka min,Yar budurwar tace wannan jaka ce gaba daya Bata ganewa, Khairat tace nice Jakar? Ae da mece ai ke kinfi jaka jakanci ma,Tasss kake ji Khairat ta kwashe Yar budurwa me ji da kanta da mari tare da cin kwalarta ta makata da bango ta shaketa Kam. Hajiya Baturiya ta fara tafi raf raf...tace Wannan kin dace da gidan Nan wlh irin wacce nake nema ce. Nan take Hajiya tace a bawa Khairat abinda takeso taci kyauta,me aiki ta tambayi Khairat me za a kawo Miki,Khairat tace soyayyen kwai,chips,bread,shayi hadin kauri. 5mnt aka kawowa Khairat taci ta koshi tace Kwan da aka soya yayi kadan ta shige kitchen da kanta ta soya kwai wani me Fadi fakaka ta karo bread taci abinta ta tafi dakinta tayi wanka,Hajiya ta fito tace Khairat tazo zasu je Shopping,Kamar me Hada Lefe haka Hajiya ta hadowa Khairat kaya na gani na fada readymade ba abinda Babu ga kayan kwalliya,wasu Kuma laces,atamfofi da shadda masu tsada suka tsaya aka bada dinki. Tunda Khairat tazo gidan ba a Zama lfy da ita kullum sai anyi fada da ita,cikin kwana Uku kacal ta buwayi kowa sabo da Babu wacce ta Isa ko kallon banza tayi mata sai ta Rama Har Hajiya Baturiya tasan Khairat ta Gama sabawa da masifa da rashin son Zaman lfy ga karfi, Amma Kuma duk yawancin Karuwan gidan daga kauye suke Khairat kuwa daga birni take idonta a bude Kar yake,Dan ma yarinyace shi yasa wani abin Dole ake Mata wayo. Bayan kwana Uku Hajiya Baturiya da kanta ta karbowa Khairat kayan sawarta wurin tela,Murna Khairat take kamar me,tunaninta a banza aka siya Mata Kaya kamar lefe komai akwai har akwati Uku,ga gyaran jiki kullum yanzu Sai Hajiya Baturiya ta kaita kamar Amarya,Gashinta yasha gyara,skin dinta kamar daga engine aka fito da ita,sai kamshi take ta ko Ina,Nan fa Yan Matan gidan suka Fara kishi da Khairat sun San zata kwace musu Customers. Khairat Kuma ta Fara zargin ba sanaar arziki akeyi a gidan Hajiya Baturiya ba,da dare sai taga Yan Matan gaba daya suna ta fita a motoci wasu Kuma Ana zuwa daukansu manyan masu kudi,duk kusan basa kwana a gidan,wasu ma idan suka tafi basa dawowa sai Bayan 1wk,Sannan ko wacce ta dawo zata kawowa Hajiya Baturiya naka kason makudan kudaden,ga maza Alhazawa suna sintiri a gidan Nan ma suna bawa Hajiya kudi,sannan kullum ba a zaman lfy a gidan Yan Matan fada sukeyi harda wukake da kwalabe kamar zasu kashe kansu,ga shaye shaye na kayan maye. Hajiya Baturiya tunaninta Khairat Bata da wayo Bata San Khairat tayi sanaar tallan maganin gargajiya ba har da maganin Mata,sai ta kawowa Khairat maganin tsumi na Mata Wanda zai sa Khairat Sha'awa da son maza tace ta shanye,tana fita sai Khairat ta juyeshi a toilet ta Kora ruwa ya tafi,sai ta koma tace gaskiya Hajiya maganin Nan da Zaki a Kara min, Hajiya Baturiya sai Dadi take ji tana bawa Khairat tana zubarwa ita Kuma. Yau Kuma Saturday Hajiya Baturiya sun Gama Magana da wani Senator yau akwai budurwa sabuwa dal me tsada zata tayashi kwana su Sha weekend me Dadi da Khairat,Hajiya Baturiya tace yarinyar me tsada ce Haka Senator ya biya Hajiya makudan kudade yace yaronsa zaizo ya dakko Masa Khairat zuwa Katafaren Hotel din da zaiyi weekend. Da dare misalin 9pm Hajiya tace Khairat taso maza ga me kwalliya tazo Zaki fita aikinki yau zai Fara,Khairat Ita dai wanka tayi kawai ta Gama gane nufin Hajiya Baturiya,me kwalliya tazo ta shirya Khairat kamar zataje gasar sarauniyar Kyau,wata Gown me Masifar kyau aka sa Khairat tasa,kowa ya ganta sai yaji kamar ya hadiyeta gashin Nan yasha gyara,ga takalmi me tsinin gaske da Yar pose hadaddiyar gaske,su kansu Yan Matan gidan sakin Baki suka yi suna kallon Khairat. Yaron Senator Yana gidan Yana jiran Khairat,Har mota Hajiya ta raka Khairat ta Shiga arniyar motar yaron yaja Khairat sai Hotel,a hanya Khairat tace ya tsaya zata siyi paracetamol a chemist,Wani katafaren Chemist Khairat ta Shiga,duk Wanda yaga Khairat sai ya rantse ko jini Bata hada da musulmi ba,a sirri ta siyi Magunguna wurin me Chemist ko na mene oho Sannan ta fito ta Shiga motar suka tafi Hotel. AsmaBaffa [9/23, 8:03 AM] Aysha B Galadima: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚 26-30 Official By AsmaBaffa INNARO,INDON BIRNI,and MAMAN SAMHA. Ga page naku Ina ganin Sharhinku na gode. Fans zaku ga kwana biyu bana muku reply ban samu time bane, ayi min Afwa fans Katafaren Hotel din suka tsaya,yaron Senator sai wani yabon Khairat yake, Yana wlh kin Hadu Hajiya,irinki Ogana yake nema,komai yaji Har Room din Alhaji Senator ya raka Khairat yace Hajiya asha weekend Lfy a fito lfy,bana dake Alhaji zai tafi aikin Hajji. Khairat ta Shiga daki sai taga shirgegen Alhaji yaci kudin talakawa ya koshi Yana kwance saman makeken bed Yana kallon News,Tsoro ya Gama Kama Khairat sai karkarwa takeyi,Alhaji ya saki Salati yace Baturiya Bata taba hadani da irin wacce nake mafarkin samu ba irinki,ki saki jikinki Maganar Kudine kin samu an Gama,ko me kike so Zan Miki a duniya ,Fadi me kike so Yan Mata,gida? Mota? Ko kudi Fadi million nawa? Dabara ta fadowa Khairat tace jikina yafi karfin a siya ko ba sisinka Zan baka. Alhaji ya washe Baki yace Amma kina da aji Yan Mata sai kin Fi cin kudina wlh,Khairat ta zauna gefen bed ta tsiyayi lemon data ga Yana Sha ta kurba tace je kayi wanka so nake nayi bacci da wuri. Alhaji ya Gama susucewa ya rude yace nasan Baki sunana ba,nine senator Mudassiru,Khairat tace Mashaallah Ka ganka kuwa kamar yaro Dan 35yrs,Dadi ya Kama Alhaji Mudassiru shi Bai yarda ba yaro ne gashi tsofai tsofai dashi. Yana Shiga wanka Khairat ta zaro maganinta ta zuba a lemon Alhaji Mudassiru ya narke,Bayan ya fito daga Wanka ta Mika Masa yasha lemonsa suna Hira tana ta zugashi Tane kiransa da Baby,Sai bacci ya kama Alhaji ya kwanta sai munshari kwarrrrr kwarrrrr kamar Ana Jan rago za a kaishi kasuwa,Yar karamar wuka Khairat ta zaro ta samu kirjin Alhaji kamar ta samu Kwaryar Yan fulani Haka ta Zane kirjin Alhaji tatas jini na tsatstsafowa a wajen ba kyan gani, ta Haye Saman bed ta dauko Reza sabuwa ta samu gashin Alhaji da yasha gyara da aski me kyau ta zauna ta askeshi tas tayi masa kwal kwal sannan ta bar Masa wata Suma a tsakiyar kansa tayi wani toluwa kamar askin yaran Fulanin daji,kowa yaga Alhaji sai yasha dariya, kwashe kayan sawarsa tayi ta cire Masa ATM card da kudi etc ta ajiye a gefen bed ta zuba kayan sawar Alhaji a bakar Leda sannan ta rubutawa Alhaji short note a paper kamar Haka: Dattijon banza nafi karfinka,Ni ba Fasika bace,jikina yafi karfinka,in kana da duniya baza ka samu budurcina ba,Allah ya shiryeka da masu Hali irin naka, ta ajiye Masa gefensa tayi waje tare da barin Hotel din. Taxi ta Shiga ta koma Gidan Hajiya Baturiya,Hajiya tayi mamakin ganin Khairat ta dawo,tace Lfy na ganki shi da yace weekend zakuyi tare,Khairat tace Kira ya samu na gaggawa zasu je Dubai meeting da shugaban kasa, Number dinsa Hajiya Baturiya ta Kira yafi sau goma Alhaji Yana can yana baccin maganin Khairat data Sa Masa da tsagaggen Kirjinsa. Khairat ta Kalli Hajiya tace ai na fada Miki baza ki sameshi ba,Hajiya tace ya Alhaji zai min Haka,Amma Bari zai sameni gobe akwai wani Danmajalisa Already ya biya kudinsa ma wajensa Zaki tafi gobe, Khairat tace Allah ya kaimu,Kinga kayan Alhajin ma nace Dole sai ya bani sheda na kawo Miki kar kice ko karya nake Miki banje ba,Hajiya ta karba tace tabbas kayansa ne,na yarda dake Khairat,Amma Banda Shirmenki ya Zaki sa Alhaji Dole sai ya Baki kayansa,Khairat ta turo bakinta kadan tace ai sabo da Zaki Fi yarda Dani ba Wai naci amanarki bane ko? Farin ciki ya Kama Hajiya tace Haka nake son mutum me gaskiya da Amana,jeki ki karbi Abinci abinda ranki yake so kici kyauta,Khairat ta tafi

Chapter 7 of 13