Share this page
a ranta tana yawwa saura na gobe Kuma zanyi maganinki. Khairat ta Gama shiryawa su Talatu Mugunta tunda ta gano cewar Karuwanci suka kawo ta,Sai cikin dare ta dauki waya ta Kira Number Zainab,Zainab tana dagawa Suka gaisa da Khairat tace Dan Allah bawa Ummanki waya,Talatu tana kusa Jin Khairat ce tace Alo...Alo Kharait tawa Talatu ce mene ne Khairat wani abin Alheri ne ya samu? Khairat tayi Murmushi tace Umma ki fadawa Kawu Allah ya kiraku bana,Talatu tace Allah ya Kira mu Ina Khairat? Umma Ashe Kiran da Allah ya muku da wuri zai tabbata, Nifa ban gane ba cewar Talatu, Khairat ta Furta Makkah fa nake nufi Umma Allah ya kiraku bana,wani mashahurin me kudi ne ya bani Kujerar Makkah guda uku shine nace na baki daya na bawa Kawu guda Daya kawai kuje kuyi International passport Zan zo mu tafi tare mu uku. Haukacewa Talatu tayi da ihu da murna ta gigice,da gudu ta fada Dakin Kawu tana bashi labari,ya fara murna,su Zainab Nan suka Kara Kiran Khairat tana dagawa Zainab tace Hajiya Khairat Dan Allah Nan gaba ko Umrah ce muma ki samo Mana kujerar Makkah ko ni da Rahinatu ce muje Makkah muma, Khairat tace karki damu Ni nake sa Alhazawa masu kudi damun Kujerar Makkah wajena ba komai bace,Allahu Akbar mashaallahu cewar Zainab. Suna Gama waya Khairat ta dinga sheka dariya a dakinta,Hajiya Baturiya ta samu a bedroom tace Hajiya Dan Allah ki ranta min dubu Hamsin kiyi min transfer ta accnt Dina kafin zuwa gobe Inshallah idan naje wajen Alhajin da Zaki hadani dashi Zan biyaki, Hajiya Baturiya Dadi ya kamata Khairat ta dauki Darasi zata Fara samun kudi da ita,sabo da Khairat taji dadin Yi Mata aiki sai tace tsakanina dake yanzu babu Rance Zan Baki kyauta ma,burina kawai ki taimaka ki Nemo mana kudi masu yawa yanda kike me kyau Haka Babu Wanda bazai so ki ba,kin ganki kuwa Khairat,ko Na hada ki da Mata ne masu bukatar irinki Nan ma mu samu kudi? Khairat a ranta ta dinga tsinewa Hali irin na Hajiya Baturiya a fili Kuma tace Ina so Hajiyata ai Ni duk inda kika ce Haka za ayi,Hajiya tayi dariya tace an Gama yata,nan take Baturiya tayiwa Khairat Transfer,Khairat tana ganin Alert itama sai tayiwa Zainab transfer ta kirata a waya tace kudin International passport ne ki bawa Kawu da Talatu suje suyi Passport kwana Nan zasu tafi,Nan suka Kara tabbatarwa Khairat abin nata da gaske ne,murna ba a magana Kawu harda kukan murna. Alhaji Mudassiru kuwa Yana farkawa daga baccin kwayar da Khairat ta Sa Masa a lemo ihu ya saki ganin Kirjinsa a tsatsage ko Ina jini ya dankare har ya fara bushewa,Bai Gama firgita ba sai da ya shafa kansa yaji wayam sai toliyar gashi a tsakiyar kansa,a fili ya Furta na tabbatar yau Aljanna Hajiya ta hadani da ita,Nan take ya nemi wayar Hajiya Baturiya tana dagawa ya ci Mata mutunci yace kinzo kin hadani da Aljanna zata dauki raina,Hajiya na bashi Hakuri yace wlh Dan kina min abin arziki ne kadai yasa na daga Miki kafa Amma da wlh sai naga gatanki a kasar Nan,kamar Ni Senator ki kawo min yarinya Yar iska duk ta keta min kirji ta Mai dashi kamar atamfa ko yadi,yanzu da wanne idon Zan kalli yarana, da Kyar ya karbi tuban Hajiya Baturiya sannan ya Kira babban yaronsa ya kawo Masa kayan sawa da Shaver gashin data bar Masa a tsakiyar Kai ya Karasa askeshi,sannan yayi wanka tare da gasa Kirjinsa da ruwan zafi Yana kwala ihun zafi Toilet. Hajiya Baturiya ta samu Khairat tace ke Dan ubanki me kika yiwa Senator Mudassiru? Khairat gabanta ya Fadi ta daure tace Ni ban sani ba yace min kawai Yana da Meeting zai tafi Dubai,Ni ban San abinda akayi Masa ba,Baturiya tace wlh kika sake na bincika na gano gaskiya wlh sai na sa an kusa halaka ki a gidan Nan,Khairat tace yo Ni kawai kyaga laifina ni ba ruwana, kwafa Hajiya taja tare da ficewa a fusace,Khairat taja tsaki tayi kwanciyarta tana tunanin Hunaif dinta. Da wuri Talatu da Kawu suka je Office din Immigration aka musu Passport na tafiya aikin Hajji,suna ta murna ba ruwansu da tunanin Khairat ko kudin Bata hanyar Halak bane kawai su dai suje Makkah. Ummi da Hunaif suna zaune lfy sai dai rayuwar Hunaif yanda ta canja kawai abin baya yiwa Ummi Dadi,kullum cikin kunci yake,Masu aiki a karkashinsa ma yanzu basa Jin dadinsa gaba daya ya canja ba mutunci ba ko Murmushi,frnds Dinsa baya muamula dasu sai kawai dai Musaf sai Farouq dake kula dashi sosai. Ummi na zaune da yamma ta gama shiryawa Danta Abinci lafiyayye sai ga Musaf ya zo daga Kano,Ummi tana ganin Musaf yazo ranta ya baci Amma Bata nuna Masa ba suka gaisa yace Ummi Ina Hunaif? Yana samansa,yanzu kazo? Ina su Mama fa?suna Nan lfy sunce a gaida ki,jeka wajensa sai kuzo kuci abinci. Part din Hunaif ya nufa,Yana zuwa ya iske Hunaif a palonsa Yana kallon News ya Kara wani azababben kyau da Yar kiba sabo da hutu, Mus'af bakin ciki ya kamashi ganin kullum Hunaif ci gaba yake Kara yi,Harara ya watsawa Hunaif ba tare da ya gani ba,suka tafa yace mutumina kyau kake karawa,Allah ya baka lfy dai ka warke, Hunaif yace Ameen Ni mamaki nake Musaf Wanda ta ya bana tuna abinda ya faru na last year sannan ba abinda zai faru yau gobe idan na tashi komai bazan tuna ba Musaf,yanzu kaga dai muna tare to Wlh gobe Ina tashi a bacci Zan manta komai, Farin ciki ya Kama Mus'af a fili Kuma ya nuna kalar tausayawa harda hawayen Kuka yace kayi Hakuri in Allah ya yarda zaka dawo Normal,naso ace Naga uban waye ya kadeka a mota ya gudu wlh da sai na daureshi har abada,Ni ban yarda da mutumin ba turoshi akayi ko dama haushinka yake ji ko waye ma. Murmushi Hunaif yayi tare da cewa kaddara ce kawai Allah ya saukar bana zargin kowa,nanfa suka barke da hirarsu ta abokai daga Nan suka ci abinci tare suka je masallaci tare,washe gari Mus'af yace jirgin karfe biyar zai bi ya koma Kano,Hunaif yace me ya kawoka Abuja ne naji kace China zaka je a week din Nan,Musaf yace wlh kuwa Hunaif kudi ne Banda su Kuma Ina so Na Fara shigo da Kaya kasar Nan Ina Kara fadada Business dina, Hunaif ya manta da Yana ta rantawa Musaf kudi different time kawai yace million nawa zata maka? Yace Million Bakwai ma ta isheni,Nan take Hunaif ya Masa transfer sannan ya rakashi har Airport ya dawo gida,Ummi Bata San me suke ciki ba,yau tayi sauri tun kafin Hunaif yayi bacci ta sameshi tare da tambayarsa me Musaf yazo yi? Ummi ba komai fa,Bata Rai Ummi tayi tace wlh idan baka fada min ba Hunaif sai na Saba maka, kiyi Hakuri Ummi kudi yace na ranta Masa million Bakwai,Baki bude Ummi ke kallonsa,tace Hunaif rannan fa naji ka bashi million goma,Hunaif yace yaushe? Ni bani bane kin San bana iya tunawa,Ummi tace bani wayarka Hunaif, Mika Mata yayi ta canja Masa sabuwa da sabon layi tayi Masa copying numbers na layikansa ta bashi gashi Nan kayi amfani da wannan Babu wani rancen da zaka sake bawa kowa,Kuma daga yau ko nawa zaka karba Ni Zan na baka da kaina tunda Kai Mus'af yafi kowa a wajenka, Saman Cinyar Ummi ya kwantar da kansa ya Mata shuru, ta Gama fadanta ta kyale shi ta koma lallashin abinta Kuma. Hajiya Baturiya yau tasa aka tsantsarawa Khairat kwalliya cikin wani danyen Material me azabar kyau da tsada,Riga da skert Tasha kyau Amma sun fito da surarta Haka tasa Driver tace ka kaita gidan Hajiya Bara'atu matar Ambassador Safiyanu Maharez, Khairat tace Hajiya an fasa Dan majalisar ne? Harara Hajiya ta watsawa Khairat tace ae Bara'atu ce ta bani kudi me yawan da yafi na Dan majalisar yawa shi yasa nace kin fasa zuwa wajensa yau sai Gobe yanzu wajen Bara'atu za a kaiki ki tayata kwana saura kuma kiyi Mata wani abin wlh sai kin gane kurenki idan Baki Bata hadin Kai ba. Khairat tayi Murmushi ta kalli Hajiya tace ko Dabbobi Hajiya basa neman jinsinsu sai Dan Adam da Allah ya musu daraja,kalli fa Duk abinda nake dashi tana da shi,iri daya ne fa idan ba kwakwalata zata yi ba me zata iya min ta gamsar Dani? Rankwashi Hajiya ta zubawa Khairat tace kije haka ai Business ne,Driver ya Kai Khairat hadadden Guest House din Hajiya Bara'atu Wata me aiki ce tazo tayiwa Khairat iso har cikin gidan,katafaren gida ne na gani na fada,Ga bedrooms na Alfarma ko Ina Yan Mata a cikin gidan tsala tsala ko wanne room free to enter ne Mata suke cin karensu Babu babbaka. Ko wace taga Khairat sai ta hadiyi yawu suna kallonta kamar mayu,Hajiya Bara'atu taga Khairat tun kafin ta karaso ta Fara Lashe Baki ganin irin budurwar da Bata taba samun ko shigenta ba. Na take ta Kira Hajiya Baturiya ta Kara Mata dubu dari biyar kyauta sabo da Jin dadin kalar budurwa irin Khairat da aka Bata,Hajiya Baturiya sai Murna takeyi. Khairat ta zauna a kujera tana tauna chewgum Hajiya tace sannu da isowa Babyna. Khairat ta kalleta kawai fuska ba rahma tayi kas kas da Chewgum tace yawwa sannu Iya,Iyata barka da hutawa,Ido Bara'atu ta zaro Iya fa kika kirani yanzu ki kalleni Sweetheart kice min Iya nayi Kama da tsohuwa? Khairat tace to da mece Gododo dake tsofai tsofai ki bar mijinki kina neman Yara Mata ai gwara ki nemi Maza,tunda Haka kike so ai shike Nan Ni ba ruwana iyaka ci na Miki abinda kike so na tafi. Hajiya Bara'atu tayi Murmushi tace indai Zaki min yanda nake so ai ba damuwa wlh ko nawa ne Zan iya biyanki matukar Kika bani farin ciki an Gama,Khairat tace a kawo Abinci naci yanda Zan Fi Jin dadi,Hajiya tana wani fari da Ido tana yiwa Khairat kallon so tasa aka cikawa Khairat gabanta da kayan alatu iri iri,Khairat taci ta koshi ta kalli Hajiya tace ya kike kallona ne kamar mayya ne? Idan ban kalleki ba wa Zan kalla kin hadu da yawa khairat, dare ne yayi Khairat duk tayi sallolinta har Isha sannan tace Hajiya ki kwanta sai tsakiyar dare zamu yi harka,Hajiya taci kwalliya ta hade cikin kayan bacci,tayi tayi Khairat ta Sa kayan bacci taki yarda. Khairat ta Haye Saman bed ta kwanta tayi lambo kamar me bacci,Hajiya ta yi tunanin Khairat bacci take ta tube tayi tsirara sannan ta haura saman bed kusa da Khairat ta makalkale Khairat a jikinta,Khairat tace Wai mene Haka nake Jin Kirji kamar Slifas Wanda akayi da fatar Giwa a jikina,gefe ta matsa tace Abu kamar gugan Danko na ebo ruwa a rijiya,Hajiya dai Hankalinta ya tashi sai ta ja Hannun Khairat ta daura a kirjinta,takaici ya Kama Khairat tace Wai mene Haka kina yakushi na, ganin za a samu matsala sai Khairat tace Darling Bari dai na Miki kiji Dadi,kamar gaske Hajiya ta fara Murna Khairat tace kwanta ki baje,Hajiya tayi dai dai a saman bed,Da dabara Khairat ta dakko dakakken Yaji ta zuba ya Kai Rabin spoon a farjin Hajiya Bara'atu,Mai makon Hajiya taji Dadi sai Balai ya biyo baya,Ihu ta kwarara Wanda ya gigita Yan iskan gidan Baki daya,sai ko Khairat ta dire a kasa ta kwashi takalmanta da Jakarta da komai nata ta rike a hannu ta fice da gudun tsiya. Hajiya tana ihu da birgima a kasa ta fito tsirara tana ku Kama min shegiyar yarinyar can ta kasheni,wuka ta caka min a kasana na,wayyo karfe ta zurkuda min,Nan fa Hajiya ta Fadi tana ihu tana neman agaji,da kyar Yan aiki suka jata toilet suka hada Mata ruwan sanyi a baho ta zauna a ciki,Haka suka dinga canja ruwa Hajiya na Zama,har yajin zafin ya ragu ta samu sauki ta kwanta ta wangale ta kunna fanka da ac tayi shanya tana tsinewa Khairat kwando Kwando sannan tace wlh sai taci uban Hajiya Baturiya ta biyata kudin data kashe Akan Khairat. Khairat kuwa da gudu ta bar gidan ta mike titi tana gudu saida tayi nisa ta tsaya ta huta tare da da gyara kanta tana tafiya a hankali tana jiran ko zata samu taxi Amma ba Taxi dare yayi titi ba kowa wurin 11pm har 12am na dare Bata samu taxi ba sai mazan banza masu tsayawa a titi daukan Mata. Khairat tasan idan ta koma Gidan Baturiya ta Shiga uku sai kawai ta Nemi wani asibiti katafaren gaske ta Shiga ciki da niyyar Wai tazo Yar zaman jinya ce,tana ta zagaye zagayenta a asibitin kawai tana tafiya da baya da baya a tsorace tayi Karo da mutum Jakarta ta Fadi kayan suka watse a kasa, wani turarene me azabar Dadi ya daki hancinta rabon taji mutum me kamshi Haka tun suna tare da Hunaif. Wayarta ya take da arnen takalminsa me kyau da tsaya ya wuce abinsa,Khairat ta mike a masifance tace Malam mene Haka wannan ai wulakanci ne,yaransa da suke take Masa baya Suka yi shuru,a hankali ya juyo sukayi Ido Hudu da Hunaif da Khairat. A hankali yace malama kina rike kayanki da kyau kina Bata min lokaci,Jin Muryar me Maganar ce yasa ta dago da sauri a firgice ta kalleshi,Mutuwar tsaye tayi ganin Hunaif ya Kara wani Kyau da Haske,shekeke ya kalleta ya bi takan wayar ta ya wuce Yana Jan tsaki. Khairat da sauri ta mike tsaye tare da kwala Masa Kira Hunaif ganin ya juyo da mamaki Yana kallonta Ina ta sanshi ita Kuma shi da baya hurda da Mata,ganin Yana Mata kallon banza yasa Khairat ta gano ko dama can yaudararta yayi Bata san yayi accident ya samu matsala ba,sai tace Kai Malam ya zaka watsar min da Kaya Amma ko Sannu ko tunaninka irin Yan matanka ne daka Saba yaudara? Mayaudari kawai,Da mamaki Hunaif yake kallonta yanda take Masa tsiwa,yace a Ina kika sanni ko kin sanni ne? Baki Khairat ta tabe tace Dole kace Haka Mana tunda Kai babban mayaudari ne,sannan ka fasa min waya da kayan kwalliyata me tsada,Abin ya daurewa Hunaif Kai da take ce Masa Mayaudari ko budurwarsa ce gashi tana kiransa da Mayaudari,dama Ummi tace ya taba soyayya to ko itace,a ransa yace karya ne yaja tsaki ba wani Bata lokaci yayi gaban abinsa,Khairat Baki bude take kallonsa har ya bacewa ganinta. Hawaye ne suka wanke Mata fuska sabo da tana Masifar son Hunaif Amma ya ganta ya nuna Bai ma santa ba,wani haushinsa taji ta kwashe kayanta tana mamaki Wai Bai nuna ko alamar ya santa ba,wurin Zama ta samu a Hospital din ta zauna ka rantse jinyar wani takeyi,a zaune a wurin bacci ya kwasheta Bata farka ba sai da gari ya washe yayi tangararan,Ana ta zirga zirga Ana wuceta,pampo ta nema a can Bayan Compound tayi Alwala tare da gabatar da Sallah sannan ta fita ta Shiga taxi ta wuce gidan Hajiya Baturiya. Hunaif tunda ya koma gida yake ta faman tunanin Khairat da abinda ya faru tsakaninsu,tunda cutar Nan ta sameshi Abu Bai taba faruwa ya tuna ba sai Akan Khairat,Koda dare yayi ya kwanta bacci Mafarkin lokacin kuruciyarsa shi da Mus'af yayi suna yara,Sannan Yana farkawa daga bacci sai gashi ya tuna abinda ya faru tsakaninsu da Khairat jiya,ya tuna yafi sau a irga abin ya bashi mamaki da yake tuna Abinda ya faru dashi jiya da Khairat,sannan rabon da yayi mafarki ma ya manta sai gashi a Dalilin Khairat yayi Mafarki jiya,farin ciki ya kamashi,ko wanka baiyi ba ya fito da sauri Yana kwalawa Ummi Kira,tana kitchen ya fada ciki yace Ummi na tuna abinda ya faru jiya Ni da wata,wlh nayi mafarki jiya ma lokacin muna Yara da Mus'af,sannan Ina farkawa a bacci jiya naga wata Yarinya munyi fada Kinga yau na tuna komai,Ummi farin ciki ya kamata tace da gaske yace yafi Sau goma ma na tunata,Kinga yanzu Ina ganinta a kwakwalwata Memory na ya ajiyeta. Ummi tana dariya tace wannan wacce yarinya ce Haka wacce ta samin yarona farin ciki Nima ta sani ya kamata a nemota ko a Ina take,Hunaif yace Zan Kara nemota muyi fada na gani ko Zan sake tunawa, Good cewar Ummi,Waya Hunaif ya dauka ya Kira Farouq ya bashi labari,Zai Kira Mus'af Ummi tace ka Bari tukun a samo Kan lamarin kawai kayi Shuru shi Farouq kadai zaka sanarwa tunda shi ya damu da lafiyarka, jeka yi wanka muyi Breakfast sai mu tafi wurin Doctor a sanar Masa an samu chanji. Koda Hunaif ya fara wanka in Banda tunanin Khairat da maganganunta jiya ba abinda yakeyi Yana Jin wani Nishadi, Haka suna Break ma,Hospital sukaje Doctor ya Gama Jin Bayaninsu kaf sai yace Hunaif You are In love with her tun tuni,sonta ya Dade da kamaka Wanda Brain naka bazai iya mantawa da ita ba. Ummi tace to Dr yanzu mene shawara,? Lallai a Nemo yarinyar ita zata taimaka ya iya dawowa Normal,Hunaif ya tabe Baki yace wannan Yar Baby din Zan zubar da mutuncina Ni wlh bazan nemota ba,Babu yanda Ummi batayi da Hunaif ba Amma yace Sam baza a Nemo yarinyar ba zai warke a Haka. Kwana biyu tsakani ya kasa mantawa da yarinyar kullum tunanin Khairat yakeyi maganganunsu tana kiransa da Mayaudari,Cikin securities dinsa ya nemi Wanda suka yi escorting Nasa zuwa Hospital yace Lallai a Nemo Masa yarinyar da suka hadu da ita a Hospital ya bangajeta. Yaronsa yace an Gama sir,Nan suka bazama neman Khairat. Godiya da Jinjina gareki UMMI GARKUWA. AsmaBaffa [9/23, 10:47 PM] Aysha B Galadima: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚 31-35 Official By AsmaBaffa Hadiza Hussain,Khady Chafe,Hassana Usman,Aisha Ad,Nomah Zinatu,Jameelah Abdullahi,Zinatu Aliyu,Rukayyatu,Ummu Hanan,Mmn Tasleem,Mmn Labyb. Ina ganin sharhinku,jinjina nake muku mutanena ga page naku. Yaran Hunaif ke aikin neman Khairat lungu da sako, Khairat kullum sai anyi fada Da ita a gidan Hajiya Baturiya kowa rashin mutunci take musu ba abinda ya dameta,Suna Zaune a Palo Khairat ta fito cikin zaratan Yan Matan Nan dankwali ta tsigoshi gaba sannan ta kallesu daya Bayan daya ta tabe baki tare da Jan tsaki, jira kawai take wata tayi magana suyi fada, sabo da sun San Masifar Khairat Babu wacce tayi ko tari,Hajiya Baturiya ce ta fito da sauri dauke da akwatunan Khairat ta watso su waje tana huci ta nuna Khairat da yatsa .. Tashi ki fitar min a gidana tunda Kika zo ban a Karuwa dake sai asarar Customers da kike min,kina hadani Fada da manyan masu kudi Dan ubanki Dan Uwarki bar min gida, dariya Khairat tayi tace an fada Miki Ni Karuwa ce? Ina tsoron Allah Baki Isa kisa na sabawa Allah ba,Kuma Dan na bar gidan Nan sai me,gidanki din banza an fada Miki Allah bazai tallafa min ba, Ni har Ina neman yabawar Dan Adam ne. Hajiya Baturiya kallon Khairat kawai takeyi har ta Gama sannan ta kwashi akwatinanta da Babba da karama ta kalli Baturiya tace gidan da aka Gina da Haram,ake ci da Sha da Haram me zanyi da Zama a cikinsa, taja tsaki tayi ficewarta ta bar gidan Hajiya Baturiya Baki bude suke jinjina Rashin kunya irin ta Khairat. Khairat tunani takeyi Ina zata je,idan ta koma Gidan Kawu wata Masifar ce,tana zaune jikin Wata bishiya sai wayarta tayi Kara kirrrr..tana dubawa taga Zainab,dagawa tayi tace Zainab ya akayi? Umma ce da Kawu suka ce na tambayeki yaushe zasu tashi zuwa kasa me tsarki? Khairat a ranta tayi dariya a fili tace sai an fara iban Alhazai Nan da sati Uku kice su shirya. Zainab ta fadawa Talatu me Khairat tace ai kuwa suka fadawa Yan uwa da abokan arziki zasu tafi Makkah kwana nan,Ana musu Allah Sanya Alheri,Talatu harda shiri taje gidansu ta sanar bana dasu za a tafi aikin Hajji. Bayan tafiyar Khairat Talatu ta Fara abincin siyarwa Amma tunda taji zata je Makkah tace ai Sunyi kudi tafi karfin saida Abinci ta kusa Zama Hajiya. Khairat ta yini a jikin bishiya karshe ta mike da kayanta ta Shiga Taxi tace a kaita suleja inda masu karamin karfi ke Zama,Bayan taje Suleja ta dinga zaga Tasha wurin Yan tuwo tuwo tana neman wacce zata na tayasu aiki a Bata wurin kwana,Babu wacce ta saurareta sai wata Bahaushiya Ana kiranta da Ladi,Ladi tace Yan Mata Zan Baki wurin kwana ganin ke Bahaushiya ce Amma Zaki dinga tayani aikin abincina a Tasha shine taimakon da Zan iya,Murna Khairat tayi tana faman godewa Ladi,Ladi tace shigar da akwatinki shagon cin Abinci zuwa dare idan na tashi sai mu tafi Gidana gaba daya. Khairat ta dinga Godiya sannan ta zage ta Shiga Taya Ladi aiki sosai,Ladi taji Dadin Ganin Khairat Bata da kuya ga Tsafta. Wurin Magrib Ladi ta Gama siyar da abincinta ta kulle shagonta suka tafi gidanta tare da Khairat,ba nisa da tashar Khairat taga Dan gidan karami Amma Yana da Dan kyansa ko Ina tiles,Daki biyu da Palo ne sai toilet da kitchen,Khairat tace Aunty Ladi gidanki ne ko na haya? Ladi tayi Murmushi tace Gidana ne na Kaina Kuma da kudin Sana'a ta na siya,Khairat ta jinjina Kai,Ladi tace yanzu tunda muna tare Ina saida katin waya su Mtn,Glo etc sai ki dinga siyar min da shi a gefen titi Ni Kuma sai naci gaba da girkin abincina ko ya kika gani,Khairat tace ba damuwa ki Saro katin da yawa kawai Ni Zan siyar. Daki guda me dauke da Katifa karama Ladi ta bawa Khairat tace ga dakinki,Khairat tayi murna ga Ladi akwai Tsafta har da ta masifa ma. Khairat Bayan tayi wanka suka danyi Hira Da Ladi sannan Suka tafi makwancinsu,Khairat a fili tace wato Ni a talla Zan Kare a rayuwata ba ci gaba,ba yanda ta iya Haka zatayi Dole tunda Allah ya taimaketa ta samu wurin kwana. Washe gari da wuri Ladi ta tashi Khairat sukayi Sallar Asuba,Shayi ta hada musu suka Sha sannan suka kwashi tarkacen kayan aikin Ladi sai Tasha,Ladi ta tambayi tarihin Khairat ta Dan Bata a takaice itama Ladi tace Ni Yar Asalin Kebbi State ce Allah Bai taba bani Haihuwa ba sai tarin Yan uwa,Aure ya kawoni Suleja,Allah yayiwa Mijina Rasuwa,wannan gidan da nake ciki na Mijina nane Allah yasa Ina da zafin nema,Bayan anyi rabon gado yaransa suka ce zasu siyar,Ina da kudi na sai na siya naci gaba da Sanaa ta,da ita nake ci nake Sha. Khairat ta jinjina Kai tace Anty Zan tayaki sanaarki indai Zaki bani wurin kwana,Ladi ta kalleta tace ba damuwa Allah shige Mana gaba abinda nake so dake ki rike mutuncinki Kinga dai a Tasha zamuna siye da siyarwa Dole sai kinyi taka Tsantsan da Bata gari,Khairat tace inshallah ba matsala. Katin waya iri iri Ladi ta bawa Khairat ta siyar Mata,Khairat tana gefen titi tana bin motoci tana mikawa idan ta gaji ta koma inuwa ta zauna ta huta,a Haka ta dinga ciniki sosai, Ladi sai farin ciki takeyi,2pm Bayan Sunyi sallah a tashar sai Ladi tace Khairat ebi abinda kike so kici ki koshi ga ruwa pure water. Washe gari ma Haka Khairat take zabga cinikinta. Har ta kwashe kwana Uku lokacin Kuma yaran Hunaif sun bazama suna ta neman Khairat ko

Chapter 8 of 13