ai kuma aiki ya sameni baby rigimar ta motsa, da Sauri ya isa wajenta ya tasheta zaune yace''baby na lafiya kike kwance a k'asa kuma kina kuka,me ya faru?",cikin kuka tace''ba kaine nayi tafiyarka ba sai ni kad'ai a gida,kun tafiyarku wajen 'yan matan ku'',ya salam yarima ya fad'a,yace''baby na wane irin 'yan mata kuma,inda muke ko matan ma babu,kuma ko da akwai ma me zanyi dasu'',ita dai kukanta takeyi,ya tasheta tayi tsaye,janta yayi suka je bakin gado suka zauna yace''baby na kalleni'',juya kanta gefe tayi ya juyo da ita yace''please just look at me'',kallon shi tayi cikin ido yace''baki yadda dani bane ko me?",bata yi magana ba,yace''karki manta a k'asar waje na zauna inda ga mata sai wacce nakeso zan za6a,amma ko kallo basu isheni ba,ni mace bata isheni kallo ba harkar gabana nakeyi kawai,shine ban bi mata a can ba sai a nan kuma inada matata'',tace''to ba kaji abinda naseer ya fad'a ba,mata suyi ta kallonka,ai shiyasa nace mû tafi tare'',murmushi yarima yayi ya lak'uce mata hanci yace''kai baby na akwai kishi,ki daina shakku a kaina, babu wata bayan ke,hmm uhm uhm yarima mû dai ba ruwan mû ko sis....
Yace''tashi kiyi wanka duk kin 6ata kwalliyarki please ki daina kuka kunji?",kai ta d'aga mishi yace''good girl,bari nima inyi wanka sai muci abinci dan na tabbata kema bakici ba,ana nan ana kukan kishin miji ya fita fuska ta rufe tace''banso fa tam'',dariya yayi yace''baby na rigima sannan ya fice........
*'YAR MUTAN KAZAY CE💞*
*ANTY MAIMOUNATH😘*
*+22969164943*
[02/11, 22:18] Yar Niger Frd Husaini: 🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*KHADIJATUL*
*IMAAN*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY:*✍🏻
*ANTY MAIMOUNATH*💞
*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA,KAI HAR DA MA MAK'IYANA😜😜*
*DEDICATED TO:*
*MAMAN AHMAD(ANTY MARDIYYA KA'OJE)*
*MAMAN FAIRUZA*
Page4⃣3⃣~4⃣4⃣
Ana gobe d'aurin aure IMAAN ta rok'i yarima da tanason zuwa wajen amarya,kallon ta yayi yace''baby na ki bari mana gobe ba sai kije ba"shagwa6e mishi tayi tace''haba dan Allah duk k'awayen mû a can fa,saï ni kad'ai kuma ni ce babbar k'awarta idan ban je ba ai bazata ji dad'i ba'',yace''ai ita kanta tasan cewa yanxu aure ne a kanki so dan me zata zarge ki da k'in zuwa,ai ba zaman kanki kikeyi'',kyaleshi tayi ta koma kan gado ta kwanta,murmushi yayi dan yasan fushi ne tayi,yace''fushi ne kikayi baby na,sorry tashi ki shirya in muka saukeki zan wuce wajensu naseer suna jirana,saï kira yake yi min a waya'',dad'i taji tace''Allah da gaske kakeyi?",kai kawai ya d'aga mata,sannan yace''ina falo kiyi Sauri,ai bata d'auki lokaci ba wajen shirin,ta fito cikin shigarta na wani tissu coton blue mai kyau ta d'auki jakar ta da takalmi su kuma farare ne mayafin ma fari ne,tazo tace''to mu tafi na gama'',yarima ya kalleta sama da k'asa,yace''amma bakiso zuwa ba ko?",tace''why?,inason zuwa mana,me ka gani?",yace''da wannan shigar haka zaki tafi,kalli mayafin da kika saka'',tace''basu yi bane ko kuwa?",yace''eh mana,ina fa sukayi kinsan kuwa yanda nake da kishi,kinzo kinyi kwalliya kamar kece amaryar,kije ki saka hijab,in zamuje party tare kin saka mayafin shima babba zaki sa'',komawa tayi ta sanya hijab d'in duk dan ta samu tafiyar ne,ta gane take taken shi duk dan ya hanata ne,tace''to yanxu fa?",yace''yauwa ko ke fa mu tafi'',
Saï da suka sauketa a gida sannan suka wuce,daman direba ne yake tuk'in motar,IMAAN gaishe da su umman ta kawai tayi ta fice gidansu Jamila,na shiga inda na iske wasu k'awayen mu,suna gani na waje ya d'au shewa,wai ga imaan,mun gaisa suke cewa hmm kaji manya ba'a ganinku saï da dalili,nace''baku je inda nake ba ai'',na kalli jamila na fara mata''amaryar naseer daga yau shikenan 'yar baiwar Allah kwana saï gidan naseer'',jamila tace''naji dai dan ki sani kuka ne kuma bazanyi ba'',imaan tace''hmm zaki fad'awa 'yan garinku,dan wlhy da ganin mijin nan naki ba wasa'',dariya suka yi su duka,jamila tace''oho dai,wato dan ke kin tsallake shiyasa kike min iskanci ko?",imaan tace''yes,ni kam yanxu na huta,dan wannan abu kam ba'a magana dai,in kinje kin bani labari,hhhhh,kuma in nine naseer bazan d'aga miki k'afa ba har safe,hhhhh...jamila dukan wasa ta kai mata tace''wai yaushe kikayi baki haka'',imaan tace''oho''.....nan na wuni saï wajen 5 na yamma na koma gida dan in taya umma aiki,gashi daman maryam bata nan taje k'unshi da kitso,nidai yarima ya hana inyi k'unshi yace wai indai dan auren ne bai amince ba,ban jima da shiga gidan ba yarima ya bugo min waya wai za'a zo d'aukana,nace mishi ka bari mana bayan sallah magrib,yace''in nak'i fa,ki shirya kawai ki jirashi yana nan zuwa'',kashe wayar nayi ina gunguni,umma ta kalleni tace''mijin baki kikeyi wa gunguni?",zumburo baki tayi tace''umma to ya bari mana zuwa bayan sallah ba saï in tafi ba'',umma tace''to yak'i bazai bari d'in ba,kin ganki ko banson sakarci'',zama nayi har direba yazo muka tafi...
Na iske an kar6o min anko(uniforme) na daga wajen dunki,na tambayi harira ko har yarima ya iso ne,tace min''a,a bai zo ba'',a raina nace shine ni zai sa ni inzo gida wato shi yana can yana shak'atawar shi ko,hmm,na kalleta nace''OK shikenan kun gama abinci ne?",tace''eh mun gama gashi can mun jera su a dinning'',imaan tace''ok,ta d'auki ankon ta ta haura saman d'akinta,tayi wanka aka kira sallah tayi sallah ta,tana zaune tana addu'o'inta har aka kira isha'i,saï da ta gama komai tayi simple kwalliyar ta ta fito falo ta zauna,ita da su harira,yarima kuwa saï k'arfe 9pm na dare ya shigo,sannu da zuwa tayi mishi shima d'in dan tana ganin su harira ne da bazata mishi ba,hmm kumullon mata Kenan,wato kishin ne ya motsa,su harira suka gaishe shi ya amsa tare da wucewa,su harira ma saï da safe suka min suka fice,ina kallon t.v tazo ya zauna yace''baby na kallo akeyi?'',nace''uhm kawai'',wayarshi ta shiga ruri,ban bi ta kanshi ba,ya shiga amsa wayoyinsa,tashi ma nayi na bar mishi falon na tafi d'akina nayi shirin kwanciya,can saï gashi ya shigo,yace''baby na har kwanciya ne zakiyi?",nace''uhm,inaso ne in tashi da wuri'',yace''dan yin me?",nace''dan zuwa wajen d'aurin aure mana'',yace''ba zakije ba'',tace''dan me kuma'',yace''kawai meye na zuwa d'aurin aure kuma saï kace wata tsohuwa,da rana zan aiko a d'aukeki dai'',kyaleshi tayi,ta kwanta,yace''yau nan kike sha'awar mu kwana kenan?",bata amsa mishi ba,zuwa yayi ya sauya kaya zuwa na bacci ya dawo d'akin.....
Da ya dawo d'akin shima gadon ya hau tare da juyota ya fara bata hot kisses,kwace bakinta tayi tace''ni bacci nakeji'',yace''ai kuwa baki isa ba,kwana biyu ban kusanceki ba,yanxu kuma ina buqatar hakk'ina ne'',bata yi magana ba ya cire mata rigar jikinta ya cire tashi,ya shiga murza kkirjinta yanda yakeso,saï kuma ya kai bakinshi ya kama....saï da tayi d'an k'ara yace''yadai?",tace''ciwo nakeji'',yace''sorry a hankali zanyi,tsotsa yake cikin kwarewa,kai yarima d'an duniya ne,a haka ya samu ta bada kai bori ya hau,hmm,na kyale dai sis ta hanani magana🙊
Tunda safiya yarima ya fita saboda d'aurin auren,mutane sun hallara sosai ta kowane 6angare,masha Allah jama'a sun taru kasancewar abbansu jamila shima d'an kasuwa ne, k'arfe 9am na safiyar asabar aka d'aura auren *jamila da Dr.Nasser*,miyetty Allah.....6angaren su feenat na shiga,tana zaune a falo,nace mata ya nake ganinki a zaune baki shirya ba,kuma nasan ki da nawar shiri'',tace''yanxu nake cewa inje in gani ko kin shirya'',imaan tace''ni nawa ba wahala ba wata kwalliya sosai zanyi ba kinsan halin mutumen nawa'',dariya feenat tayi tace''sosai ma kuwa,bari in tashi in shirya to'',imaan tace''ina mama?",tace''tana d'akin abba'',imaan tace''lafiya har yanxu bai fita fada ba?",tace''lafiya klau kawai hutawar shi yake yi'',tace''ok bari in tafi muyi Sauri kar ya kira ni bamu ida ba'',
Basu jima da shiryawa ba yarima ya kirata yace''su fito ga direba nan tana jiransu,tace''to'',dukansu anko ne a jikinsu saï kuma wasu kaya da suka d'auka dan sawa da dare lokacin party.....a gidansu ya saukesu,da suka shiga maryam tana shirin fita ita ma,tace''lah anty imaan Ashe zakizo'',imaan tace''to me zai hanani zuwa bikin babbar k'awa,ina umma?",tana can gidansu Jamila,tace''ok to mu tafi, abba ma yana wajen maza ko?",maryam tace''eh yana can'',muka rangaya mu uku muka tafi gidansu Jamila, da shigar mu suka fara min shak'iyanci wai saï yanxu yarima ya barni nazo,banza nayi dasu na wuce wajensu umma na gaishe su ita da maman su Jamila duk na iske su waje d'aya,sannan na dawo wajen amare,imaan tace''armaryar naseer wai k'arfe nawa ne partyn dan ni ban ma ga katin ba'',Jamila tace'k'arfe 9 zuwa 11pm na dare'',imaan tace''ah amaryar zamani har kinsan lokacin ko,haba kin fad'a musu idan kuka shiga hannun Nasser yau'',Jamila tace''ai honey na mai tausayi ne kamili ba ruwanshi'',hmm inji imaan,wato idan ana sallah ba'a magana dai....saï lokacin magrib muka watse saboda kowa yaje yayi shirin shi na party.....
Saï da naji gabana ya fad'i ganin motar yarima a k'ofar gidan mu,muna isowa shi ma yana fitowa daga bayan motar,feenat da maryam gaishe shi kawai sukayi suka shige gida dan sun ga fuskar shi ba annuri,hmm...ina wuni imaan tace dashi'',yace''lafiya,ina ta kiranki a waya baki d'aga ba why?",ina kika shiga?",imaan tace''ina gidansu Jamila mana ba gashi daga can ne Muka fito ba,kuma ni wallahi wayar ma banji k'aran ta ba'',tace''ok yayi kyau'',ki shirya ni da ke zamuje wajen partyn'',tace''da ka tafi kawai ni saï mu tafi dasu feenat'',yace''haka nayi niyya sunje da k'awayen amarya,ki zauna cikin shiru zanzo da time yayi'',yana kaiwa nan ya shige mota,tsayawa tayi yake kallon shi,hmm yau 'yan ikon sun motsa Kenan......
*Luv u all fan's....*
*'YAR MUTAN KAZAY CE💞*
*ANTY MAIMOUNATH😘*
*+22969164943*
*
[02/11, 22:18] Yar Niger Frd Husaini: 🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*KHADIJATUL*
*IMAAN*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY:*✍🏻
*ANTY MAIMOUNATH💞*
*SAK'ON TA'AZIYYA ZUWA GAREKI KAWATA KHALEESERT ALLAH YAJIQAN ABBA DA RAHAMA YASA YA HUTA,KU KUMA ALLAH YA BAKU HAK'URIN JURE RASHIN SA....*
*MU DA MUKAYI SAURA IN TAMU TAZO ALLAH YASA MU CIKI DA KALMAR SHAHADA..AMEEN!!!*
*RAYUWAR KENAN,WANDA YAJE BAI YI GAGGAWA BA,KAI DA KK NAN BAKAYI JINK'IRI BA.....KAICO DUNIYA😭😭😭*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page4⃣5⃣~4⃣6⃣
K'arfe 9pm na dare tana bugawa yarima yana isowa a ya kirata a waya yace ta fito yana k'ofar gida,bai sauko ba daga motar kasancewar babu kowa a gidan duk suna gidansu jamila.....cikin shirinta na wani material mai shegen kyau da tsada,anyi mata ado a gaban rigar,dunkun riga da skirt ne,yayi mata kyau sosai, ko da ta fito yana zaune cikin mota a gidan baya,da Sauri wani ya bud'e mata sharin guda ta shiga kusa da yarima,shima ya d'au wanka kamar shine angon,IMAAN ta kalleshi ta 6ata fuska tace''wannan shigar irin ta angwaye ce Kayi,saï kace kai ne mai amaryar'',murmushi yarima yayi tare da shafa fuskar ta yace''nima ango ne ai'',IMAAN ta kalleshi fuskar ta da alamar tambaya,yace''yes ba gaki nan ba,ai kece amaryata ko?",6oye fuskar ta tayi a jikinshi,hmm wato IMAAN an fara cire kunyar yarima ko....motocin su jere suke da na ango da amarya har zuwa inda aka shirya partyn,fitowa sukayi suka jera,ango da amaryar shi IMAAN da prince d'inta,zuwa sukayi suka zauna inda aka tanadar dan ango da amarya,imaan tana gefen amarya,shi kuma yarima yana gefen ango,
Kid'a kawai yake tashi a wajen inda k'awayen amarya suke cashewa,har da su maryam da feenat,can aka buqaci ango da amarya su fito fili,kid'a ya canza a lokacin da suka fito akace suma su taka,su IMAAN dai 'yan kallo ne,dan yarima yace bbu wata rawa da zasuyi salon a rainashi cikin yara,hmm yarima akwai son girma....bayan sun sha raye raye kowa ya nemi waje ya zauna akaci gaba da shagulgulla,yarima ya bada tarihin naseer hk IMAAN itama ta bada na jamila,an raba abinci da abin sha,yarima wayarshi tayi k'ara ya tashi ya fita saboda wajen akwai hayaniya..IMAAN ma tashi tayi tace ma jamila''k'awata ina zuwa'',ta nufi inda ta hangi su feenat,tana zuwa tace''hmm wato ko nemana bakuyi ko?",feenat tace''me zamu baki ai mun san kina tare da mijinki ne,kuma k'awar amarya'',ya bamuga kinyi rawa ba?",IMAAN ta kai ma feenat dukan wasa tace''banson zolaya fa,kinsan dai yayanki bazai ta6a barina inyi rawa ba'',dariya suka mata feenat da maryam sukace''kai amma an baroki a baya gaskiya,mû dai mun cashewar mû sosai'',IMAAN tace''oho muku dai'',suna cikin hirar ne saï ga yayan jamila nan yazo suna gaisawa da imaan,yake tambayar ta ya kwana biyu,tace mishi lafiya klau,ya hidima?",yace''alhamdulillah'',basu Ankara ba saï ganin yarima sukayi a tsaya yana kallonsu,imaan gabanta ne ya fad'i ras,yayan jamila ya mik'a mishi hannu dan su gaisa,amma yarima ya k'i,d'aga mishi hannu kawai yayi,yace''sa'ar ka d'aya kai yayan jamila ne da saï na hukuntaka,yanxu ba da bane,yanxu ita matar aure ce,dan haka ka fita harkar matata'',yace mishi''kayi hak'uri gaisawa kawai mukeyi walhy ko a da ma babu komai a tsakanin mu'',yarima yace''gaiduwa da izinin wa?",ya juyo ya kalli imaan yace''da izinin wa kika zo nan har kuke gaisawa?",shiru tayi,tsawa ya daka mata yace''ba dake nake ba?",su feenat kuwa tuni sun fice dan kar a had'a dasu..nace''nifa wajensu feenat ne nazo shine da ya ganni yazo muka gaisa,bbu komai a tsakanin mû dashi'',ficewa yayi yaje ya zauna,imaan kuwa har idonta ya ciko da ruwa dan ta gama tsorata da yanayin shi,imaan cikin d'ari d'ari haka nan ma taje ta zauna kusan shi,tace''kayi hak.....a zuciye yace''enough,yana huci kamar mayunwacin zaki'',naseer ya kalleshi yace''friend meye haka ne wai,meyasa ka cika zafin rai ne?",d'aga ma naseer hannu yayi yace''kaima excuz me dan Allah'',tuni idanuwanshi sun rine dan fitina,hmm,waya ya d'auka ya kira direba,yace''ka jira a waje za'a maidata gida'',da Sauri imaan ta d'ago ta kalleshi tace''ba'a tashi zan tafi,kuma ai saï mun kai amarya'',yace''ba zakije ba,gida zaki in kuma kina musu dani bismillah'',Jan bakinta tayi shiru dan gudun kar tayi magana kuma ya k'ara mata tsawa,naseer ne yace''haba ya zaka mata haka ranar auren k'awarta ta kace ta tafi gida tun yanxu'',yace''eh haka nayi niyya,tashi yayi yaja hannunta bai tsaya ko ina ba saï a waje,yace ma direba kai ta gida....
Da suka isa gida,imaan tana shiga kai tsaye d'akinta ta nufa zuwa tayi ta kwanta a gado tayi ta kuka har ta gode Allah,saï 12pm saura yarima ya shigo gidan,saï da yaje tayi wanka ya ida komai nashi sannan ya nufi d'akinta,yana shiga da imaan ta ganshi saï ta koma can k'arshen gado ta fara sana'ar tata,wato kuka,ita a zaton ta dukanta zaiyi,hmm duka kuma cabb....,zama yayi yake sauraron ta,can saï yace''me aka miki kikewa mutane kuka,ko kawai niyya,Kenan kinsan kinyi laifi ko?",imaan tace''kayi hak'uri wlhy gaisuwa ce kawai'',yace''banson ji,ba laifinki bane,laifina ne da na barki kikaje,toh fa yau naji iko ita da bikin k'awarta guda...tashi yayi ya fita daga d'akin,
Da safe tana falo a zaune ya fito cikin shirin fita saï k'amshin turare yakeyi,imaan tace''ina kwana?",yace''lafiya,ki had'a min breakfast ana jirana'',imaan tace''in shirya mû tafi?",ba tare da ya kalleta ba yace''ina Kenan?",tace''gidan amarya mana'',yace''ba can zanje ba,gaisuwar surukai zamu kuma ba gidan naseer d'in ne za'a had'u ba'',tace''to direba ya kaini mana'',yace''no gobe zan kaiki da kaina'',bata saké cewa komai ba ta tashi take ta had'a mishi break fast,da ya gama yazo yayi mata kiss a kunci yace''sai na dawo by'',hmm Ashe ma zaka sauko ai ko dan ka samu....🙊yana ficewa ta d'auki wayarta ta kira jamila taji a rufe,a ranta tace hmm wato su k'awata an ji jiki kenan, ita kad'ai take dariya,ni kuwa nace dariyar mugunta...maryam ta kira tace mata''kina gida ko kina ina?",tace''gamu nan ni da feenat a gidan amarya'',imaan ta zaro ido tace''yaushe feenat ta fita har kuka tafi?",dariya maryam tayi tace''ai daman a nan gida muka kwana bata koma ba'',imaan tace''shine kukayi musu saukon zuwa gida ko'',feenat ta kar6i wayar tana zolayar ta tace''gamu nan muna shak'atawar mû a gidan amarya'',imaan tace''naji dai ku bani jamila dan na kira wayar ta a kashe'',tace''ok to gata nan'',ta mik'a ma jamila wayar,imaan ta shiga mata shak'iyanci tana cewa''k'awata ya jiki,shine har da kashe waya wato dan ma kar a dameku ko?",jamila tace''ke ni lafiya ta klau kiji ma,babu abinda ya faru'',imaan tace''k'aryane wannan mijin naki mai rawar kai'',jamila tace wlhy nake gaya miki,kedai bayani saï kinzo'',tace''ok to yace wai saï gobe sannan zai kaini,kinsan halin mutumen nawa'',tace''ok Allah ya kaimu saï kunzo......
*'YAR MUTAN KAZAI CE💞*
*ANTY MAIMOUNATH😘*
*+22969164943*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*KHADIJATUL*
*IMAAN*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY:*✍🏻
*ANTY MAIMOUNATH*💞
*OH ALLAH!*
*SHOW US WAY*
*TO THE JANNAH*
*AMEEN!!!*
*JUMA'AH MUBARAQ*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page4⃣7⃣~4⃣8⃣
Saï da yamma yarima ya dawo gida a gajiye,bayan yayi wanka yaci abinci yace ma imaan muje kiyi min tausa duk jikina ciwo yake,imaan ta kalleshi tace''ka bari mana zuwa dare'',yace''no yanxu nakeso'',tashi muje'',jan hannunta yayi saï d'akinshi,
Tausa take mishi yana wani lumshe idanuwa,hannu yasa yana shafo cinyar ta,yanayin yanda take mishi tausar ya saka shi cikin wani irin yanayi sakamakon lallausan hannunta da ke sauka bisa gadon bayanshi....kyaleshi tayi a haka har bacci y'a d'aukeshi,hmm lallai yarima an gaji,auren aboki ba wasa ba....tashi tayi ta fita daga d'akin ta koma falo ta kunna t.v tana kallo....
Feenat ce tayi sallama ta shigo,zuwa tayi ta zauna bisa kujera sannan ta kalli imaan saï ta fashe da dariya,imaan tace''ke Kuma fa lafiya daga zuwa kin sani gaba kina dariya?",tace''wlhy jiya na tuna,amma gsky yaya bai kyauta miki ba,bikin babbar k'awa guda ace mutum ya dawo gida'',imaan ce ta jefe ta da filon kujera tace''eh d'in naji dai,Allah yasa wani ustaz ya aureki ki zama matar kulle gaba d'aya'',
Feenat cikin dariya tace''wlhy a,a ba ameen ba gsky karkiyi min baki'',dariya imaan tayi tace''hmm yayi kyau mudai a kawo mana na kirki'',tace''insha Allah,ke jiya na samo wani handsome fa'',
Imaan tace''ke haba dai bani labari'',tace''hmm kin ganshi kuwa mai bala'in kyau,abokin naseer ne a can wajen party muka had'u sunanshi Affan'',imaan tace''ba wani kyau ai duk kyan shi bai kai mijina ba ah to'',feenat tace''cabb lallai ma anty imaan d'in nan to ya fi yaya shureim kyau'',
Imaan ta zaburo takai mata dukan wasa tace''ke wlhy k'aryane ba dai mijina ba,ai shi cikin maza saï an tona kiji ma da kyau'',feenat tace''hhh mai da wuk'ar anty na kowa nashi dai ya sani,bari wata rana zan kawo muku shi'',imaan tace''to Allah ya kaimu'',feenat tace''ameen,wai ina yayan ne?",imaan tace''yana bacci'',feenat tace''cabb bacci Kuma a yanxu da goshin magrub d'in nan?",tace''tun d'azu ya kwanta wai ya gaji yace'',
Feenat tace''hmm kedai aiki ya sameki Allah ya k'ara miki hak'urin zama dashi'',imaan tace''kamar ya?",tace''zafin zuciyar wannan nashi mana'',imaan tace''hakan ma ni yayi min tunda babu damar wata mace da zata shigo min gida ah to'',dariya feenat tayi tace''hhh su anty iyayen kishi lallai'',.......
Saï da imaan taga an kusa Kiran sallah magrib sannan ta nufi d'akin yarima ta iske ya tashi yana toilet,fita tayi taje d'akinta dan ta gabatar da sallah itama.....
********* *****
Da dare suna zaune a palo wayar imaan tayi k'ara tana dubawa taga jamila ta d'auka tace''assalamu alaiki amarya ina kika bar angon naki ne?",cikin d'ar d'ar jamila tace''ke ni ba wannan ba,ya fita wai sayen kaza,wlhy na tsorata me yake nufi da sayo kasar ne?",
Ai kuwa me imaan zatayi in ba dariya ba,har saï da ta kular da jamila,ta kashe wayar ma,hhhhhh,
Yarima ya kalleta yace''ke da wa haka kike dariya?",tace''jamila ce'',yace''to me tayi kike mata dariya?",imaan tace''sirrin mû ne na k'awaye'',yarima yace''hmm yayi kyau,tashi muje nima akwai sirrin da zamuyi dake'',ta mak'ale kafad'a tace''nak'i wayo ko,ni kallo zanyi'',yace''ai kuwa baki isa ba saï munje'',tashi muje kawai'',tashi tayi shi Kuma ya kashe t.v d'in tare da kama hannunta suka nufi sama....
*KASHE GARI*
Su imaan suna break fast yarima yanaso zai fita wajen aiki,wayarshi tayi ringing ya ciro ta a aljihun wandon shi,ya kara a kunne yayi sallama yace''friend ya akayi ne?",naseer yace''please ka bani imaan in tana kusa'',yarima yace''lafiya dai ko?",yace''da sauk'i dai bani ita dan Allah'',yarima yace''ok gata nan ya mik'a ma imaan wayar bayan sun gaisa ne yace''dan Allah taimako nkso kiyi min'',imaan tace''wane irin taimako Kenan?",
Dr.naseer yace''please kizo ki tayani ba k'awarki hak'uri wlhy akasi ne aka samu banyi da niyya ba,amma saï kuka take tak'i ma in taimaka mata wai ita gida zata'',nan take imaan ta harbo jirgin inda zancen ya dosa,wata irin kunya ce ta kama ta,tace''to gamu nan zuwa karka damu'',yace''ok nagode ba ma prince wayar'',ta mik'a mishi wayar tare da zama a kujera ta dafe kai,amma kuma cikinta cike yake da dariya,bayan yarima ya gama wayar ne yace''d'auko hijab d'inki mu tafi in na saukeki saï in wuce'',tace''ok to.....
A lokacin da suka isa gidan naseer yana palo dafe da kai,yarima ya mik'a mishi hannu suka gaisa,imaan ma ta gaishe shi,yace''tana d'aki ta rufe daga ciki kiyi knocking idan taji muryar ki ta bud'e'',
Imaan zuwa tayi tayi mata knocking kyalewa tayi jamila,a zaton ta naseer ne,saï da imaan tayi magana sannan ta tako da k'yar tazo ta bud'e mata tare da fad'awa jikinta ta fashe da kuka........
*YAR MUTAN KAZAY CE*💞
*ANTY MAIMOUNATH😘*
*+22969164943*
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or