Share this page
7 / 10
*STORY* *&* *WRITTEN BY*:✍🏻 *ANTY MAIMOUNATH*πŸ’ž *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page2⃣7⃣~2⃣8⃣ D'aukan ta yayi cak yayi kan gado da ita tana magiya,ko sauraren ta k'inyi yayi,ina ganin YARIMA ya saki hanya,na bazo a guje falo,amma ina fitowa ummu basheer ta tisa keyata wai in koma in samo labari,nidai ba ruwana itaceπŸ™Š IMAAN dai ido ya raina fata,dan sai kusan asuba ya saurara mata shima wai dan saboda d'an babyn shi ne,hmm,bayan ka gama Kenan,cabb....da asuba ya d'auketa cak saΓ― toilet dan yasan yau ya ta6ota bazata iya tsinana komai ba,hmm... A toilet d'in ma saΓ― da suka 6ata lokaci dan cewa tayi bazai mata wanka ba wai kar ya kalle mata jiki,hhhh na nawa kuma wai ance da kuturu Allah ya la'ance ka, Bayan tayi sallah a nan ta 6ingire tana baccin wahala🀣ah to na wahala ne mana,ko da YARIMA ya dawo daga masallaci,ya tadda ta bisa abin sallah tana ta sharar baccin ta,saΓ― da ya tausaya mata dan yasan ta wahala,zuwa yayi ya d'auketa ya kaita bisa gado,ya cire mata hijab d'in duk tana bacci,lallai IMAAN an wahala,shima d'in tu6ewa yayi ya kwanta a bayanta suka cigaba da baccin su.... Basu suka tashi ba sai 12am na rana,wanka suka sakeyi suka shirya tsab dasu sai k'amshin turare ne ke tashi a jikinsu,falo suka nufa,IMAAN kuwa sai kumburi takeyi,sai da suka zauna bisa dinning table ya kalleta yace''baby na yadai na ganki haka,lafiya dai ko?",ta zumburo baki tace''ba kaine ba...kuma sai bata k'arasa maganar ba ta kyale'',murmushi yayi yace''nine nayi me?",tace''ba kaine ka bani wahala ba,kuma sai na had'a ka da mama'',dariya yayi yace''to ai na fad'a miki daman,sai da nace miki muzo 6angaren mu,amma kika k'i Kenan duk yanda nayi miki banyi laifi ba,haba baby na kinsan fa yanda nake amma kika basar kamar baki gane ba,kikayi zamanki a wajen su mama'',shiru tayi tana sauraren shi sai da ya gama ta kalleshi ido cike da hawaye tace''cikina ya kulle kuma inajin amai'', YARIMA yace''cikinki kuma,oh God,tashi to mu tafi kiyi aman sai kisha magani,ko in kira doctor ta duba ki'',ai fa da taji ance doctor sai cewa tayi''ni fa aman ma ya koma,kuma cikin yayi sauqi,hmm,kallon ta YARIMA yayi yace''kinsan banson musu da gaddama ko?",zo ki kwanta tazo ta dubaki,hmm lallai ciki d'an gata tun kafin ya zo duniya Kenan,kwantar da ita yayi,ya d'auki waya ya kira doctor,ce mishi tayi kar ya damu ba wani abu da zai samu cikin,Dole ne mai ciki ta rink'a jin chanji a jikinta ba kamar da ba'',yace''ok to shikenan doctor nagode'',tace''ok ba komai aikina ne ai'', ******* ****** ******* Yau ne za'a kawo sadakin jamila IMAAN tana ta magiyar YARIMA ya barta taje wajen sadaki,daga nan kuma ta lek'a gidansu tunda a unguwar ne su jamila suke,amma fir yak'i,ta marairaice tace''kai ma fa zuwa zakayi sai a bar ni ni kad'ai a gidan'',yace''to baby na me zakiyi a can?",tace''hmm jamila ce fa,k'awata tun muna yara muke tare sai yanxu kace bazanje ba,kayi hak'kuri in tafi daman nayi missing su umma'',yace''ohk naji,amma da sharad'i'',tace''wane iri'',yace''banson kije ki shiga cikin k'awayen ku kuyi ta shirme da wani raye raye,karki manta ke matar aure ce,idan naji labari ranki zai 6ace kinji na fad'a miki,ki kula da kanki,saboda zuwa gida kawai zan barki'',ta kalleshi yace''to naji na yadda'',yace''ok jeki ki shirya har da ni zamuje in na gaishe su sai in wuce office akwai abinda zanyi a can,monday zan fara zuwa wajen aiki'',IMAAN kuwa sai zumud'in zuwa gida akeyi.... Sun fito a jere suke tafiya gwanin ban sha'awa,sunyi shar dasu sai k'amshin turare sukeyi,6angaren su mama suka nufa....shiga sukayi tare da yin sallama,mama bata falo YARIMA ne yaje har d'akin ta ya kira ta,da ta fito IMAAN ta durk'usa har k'asa ta gaishe ta,mama tace''tashi 'yata kinji,ya kuka kwana da fatan jikin da sauqi ko?",a kunyace IMAAN tace''eh mama naji sauqi'',yace''to alhmdllh'',YARIMA ya kalli mama yace''zamu fita mama,yau akeyin sadakin k'awar ta jamila,naseer ne angon ai ranar ma na fad'a miki ko?",eh ka fad'a min,Allah sarki yau da yamma ne za'ayi Kenan?",YARIMA yace''insha Allah,to zan kaita gida ta wuni da yamma bayan anyi sadakin sai a d'auko ta'',yace''to shikenan ku tafi Allah ya kiyaye hanya,'yata ki kula da kanki kinji'',to mama kawai tace'',amma a k'asan zuciyar ta tambaya take wai meyasa ake ta cewa ta kula da kanta?oho kema baki sani ba Bare kuma mΓ»...... ******* ***** A gidan su IMAAN sai murnar zuwan ta akeyi,zuwa tayi ta kwanta a jikin umman su tace''umma nayi kewar ku sosai wallahi,kamar nayi shekara ban ganku ba,umma tace''to ai haka auren yake,ba gashi yanxu kinzo kin gan mΓ» ba,ai YARIMA akwai k'ok'ari yazo ya kawo mana abin arziki wai tsaraba ce'',da Sauri ta tashi zaune tace''umma Kenan shi yazo,shine ni yak'i kawoni sai yau'',shima sai da na rok'eshi nace sadakin jamila ai Dole in zo sannan ne fa yace to muzo ta k'arashe maganar a shagwa6e'',ummu tace''ai ke da shi duk d'aya ne tunda yazo ba shikenan ba'',hmm to umma ina tsarabar da ya kawo muku, nima na kawo'',tace''bazan nuna miki ba ina ruwanki ne da abinda ya kawo'',uhum kawai IMAAN tace sannan ta basu na ta tsarabar,a gidan babu Wanda bai samu ba har abba shima anyi mishi tashi tsarabar,tace''umma bari inje in ga shirye shiryen me ake mana na tarben 'yan kawo sadaki'',umma tace''duk ne ai za'ayi har lefe gaba d'aya'',IMAAN tace''shine jamila bata fad'a min ba?",umma tace''a,a itama sai daga baya sunce suna son ayi gaba d'aya a huta kawai'',to umma bari dai inje gidan nasu ina zuwa'',umma tace''kin fad'a wa mijinki dai ko?",to umma ai yasan zanje d'in,eh duk da haka dai ki fad'a mishi yafi,6ata fuska tayi ta 6ude jakar ta ta fiddo wayar ta,Kiran YARIMA tayi,umma tace''to ki saki ranki mana ko a haka zaki mishi magana,kai yau naga wata irin 'ya, Daga can YARIMA ya kashe Kiran sai ya kirata yace''baby na lafiya ko?",eh daman inaso zan leqa gidansu jamila in ga shirin da akeyi in akwai aiki sai muyi tunda umma tace har da lefe baki d'aya zasu kawo'',yace''no baby na kije amma ban ce kiyi aiki ba ok'',tace''to dan me sai inje in zauna manya suna aiki ina kallonsu ai da kunya ko'', Yace''to wallahi sai in ce ki zauna ma,nidai banso kuma kar in ji labarin kinyi aiki'',to shikenan'',sukayi sallama ta saka wayar a jakar ta tashi tsaye ta shiga d'aki ta aje jakar tace''umma yace inje na tafi sai kunzo,tace''to kin d'auki wayar ki ko?",a,a umma in maryam tazo ta kai min can,tace''a,a dan me d'auki kayanki in aka kira ki fa'',IMAAN tace''to bari na d'auka, d'auka tayi ta fice,umma kallon ta takeyi a zuciyar tace Allah sarki khadija na,yarinta na damunki baki ma san kinada ciki ba,hmm in ta sani ko ya zatayi?oho ****** ***** Bayan sallah magrib,IMAAN ce ta shigo da kuka umma ta rikice tace''ke lafiya kika shigowa mutane da kuka",cikin kuka tace''umma wai da gaske ciki ne gareni?",murmushi umma tayi tace''shine ya saki kuka wa yace miki ciki gareni?",tace''ba a gidansu jamila bane suke cewa masha Allah IMAAN Allah ya raba lafiya,da farko ban gane nufinsu ba sai da wata a cikinsu tace muna nufin cikin da ke jikinki,tana kaiwa nan ta k'ara fashewa da kuka'',umma tace''ke banson hauka da shirme kinji ko,ciki ne gareki ai ba shege bane da ubanshi sai me'',ai fa IMAAN ta fara birgima kamar k'aramar yarinya 'yar goye, Umma tace''ai kuma sai kiyi,ki cigaba da kukan har abbanku yazo ya tardaki a haka,wallahi sai ranki ya 6ace na gaya miki'', Tsagaita kukan tayi sakamakon muryar abba da taji a tsakar gida,yana cewa ina IMAAN d'in ta fito direban ya zo,ras gabanta ya fad'i a ranta tace babu inda Zani badai yaudara ta akayi ba,inada ciki ake 6oye min,hhhh IMAAN mai shirme kenan..... Maryam ce taje ta fad'a wa abba cewa IMAAN tak'i fitowa wuri ma ta samu tayi kwanciyar ta,hmm Abban da kanshi yazo,tsawa ya daka mata yace''ki tashi maza ku tafi waye sa'an ki a nan,anayi miki magana kin nemi waje kin kwanta ba jiran ki akeyi ba a k'ofa'',tashi tayi sumi sumi ko jakar bata d'auka ba,sai maryam ce ta biyo mata da ita,ta shiga baya ta zauna,direba yaja suka tafi... Da suka isa ma bata tsaya an 6ude mata k'ofar mota ba,ta 6ude ta fita,cikin gidan ta nufa,kai tsaya 6angaren su tayi,ko sallama batayi ba ta shiga,babu kowa a falo,amma taji motsin mutum a kitchen da alama su harira ne,bata bi ta kansu ba ta shige bedroom d'inta,jefar da jakar tayi ta fad'a bisa gado tayi rub da ciki ta bud'e sabon kuka... Tana cikin kukan ne ta jiyo motsin mutum kamar an shigo d'akin,k'amshin turaren da taji ne ya bata tabbacin YARIMA ne,isowa yayi yace''baby na lafiya kike kuka,kuma kikayi irin kwanciyar da na hanaki'',tashi tayi zaune ta kalleshi tace''daman ciki gareni shine kuke 6oye min?",YARIMA yayi shiru ya rasa abin fad'a...toh fa sai ka nemi hujjar ka ta 6oye mata,hhhh mudai 'yan kallo ne....... *Ku biyoni dan jin yanda zata kasance*πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€ *'YAR MUTAN KAZAY CE*πŸ’ž *ANTY MAIMOUNATH*😘 *+22969164943* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *KHADIJATUL* *IMAAN* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *STORY* *&* *WRITTEN BY*:✍🏻 *ANTY MAIMOUNATH*πŸ’ž *DEDICATED TO*: *YAYA HASSAN ATK*😘 *HUSSAIN ATK*😏 *YAYA PRINCE ABDALLAH*😘 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page3⃣3⃣~3⃣4⃣ YARIMA fa an jima ba'a had'u ba dan wani zaxxafan wasa yake mata har dai ya kai ga cimma abinda yakeso,IMAAN ji tayi kamar ranar farkon su saboda anty khaleesert ta kira ta tace tasha maganin nan,hmm,ai kuwa IMAAN ta gurzu wajen YARIMA dan ba shi ya sarara mata ba sai wajen 3 na dare,cabb,IMAAN har da kukan ta wai ita yaji mata ciwo,rarrashi ya shiga yi,yana bata hak'uri,wai ya kasa control kan shi,hmm wayo ne yake miki kawai IMAAN,hhhh.... Da asuba ma taji taji ana shinshinar wuyanta,YARIMA ne wai tayi hak'uri yayi kad'an kuma,toh yau naga jaraba,tace''wlhy ni na gaji daman ban warke ba ka tashi duk kaji min ciwo ta karashe maganar cikin kuka'',yace''to naji shikenan i'm sorry nayi laifi ko?",am so sorry baby na,wallahi ba laifi na bane in kina kusana ne ban iya wa saΓ― na kusance ki,kuma kinsan fa na kwana biyu shiru'',batayi magana ba,zata tashi tsaya ta kasa,har da 'yar k'ara tayi yace''sorry baby menene?",tace''ka gani ko na kasa tashi ciwo nakeji'',yace''sannu bari in d'aukeki in kaiki toilet d'in,cak ya d'auketa saΓ― toilet,tare sukayi wanka IMAAN dai idon ta a rufe wai dan kar ta ga YARIMA ba kaya,YARIMA kallon ta yayi yace''oh na manta baki shiga ruwan zafi sosai ba,gaskiya koma cikin ruwan ki gasu da kyau'',tace''wlhy zafi nakeji ni ya isa haka saΓ― gobe kuma'',yace''naji karkiyi min kuka,ke mai arhar hawaye, YARIMA ne ya fara fitowa saboda kar ya makara zuwa sallah,saΓ― da taji ya fice sannan ta fito tana d'ingisawa,hmm kai IMAAN akwai son jiki,guduwa tayi d'akinta kafin ya dawo,hhh wa yaga amarya sabon kawo wa Kenan.....da ya dawo yaga bata d'akin,murmushi yayi a ranshi yace baby na Kenan ita dai akwai tsoro,bari in kyaleki ki kwanta ki huta,gado ya hau yayi kwanciyar shi,haka itama IMAAN kwanciya tayi.... Wayar shi ce tayi k'ara firgigit ya tashi zaune daga asibitin su ne,ya kalli agogon da ke manne a bangon d'akin yaga 8am ta gota yayi d'aukan Kiran yayi banji me aka ce musu ba,yace''ok gani nan zuwa'',tashi yayi a gurguje yayi wanka ya shirya cikin suit bak'ak'e sunyi matuk'ar k'arbar shi abinka ga farin mutum, gaskiya nima na yaba auπŸ™Šba ruwana bakina ne ya fad'a Zuwa yayi d'akin IMAAN ya iske tana bacci,ai Dole saboda jiya batayi sosai ba,kuma ga ciwo,zuwa yayi ya gyara mata kwanciyar ta yayi mata kiss a baki ya fice...da ya sauko k'asa ko break fast bai zaya yayi ba ya fice dan yana da patient dayawa a asibiti kuma an ce ana ta jiranshi,yau ko wajensu mama bai shiga ba,direba yana ganin shi ya zo da Sauri ya amshi kayan hannun shi gami da gaishe shi,sannan yaje ya bud'e ma YARIMA mota ya shiga shima ya shiga mazaunin direba ya tashi motar suka fice,YARIMA yace mishi kai yi sauri ana jirana,yace''to maigida an gama'', Da isar su ma kai office d'in shi ya shiga ya kira wata nos yace''kice ma patient d'in su fara shigowa'',jiki na 6ari tace''to sir'',fita tayi ta fad'a musu sak'on shi,dad'i takeji wai yau YARIMA ya mata magana,dan bai basu fuska ko kad'an,hmm ********** **** Ba YARIMA bane ya samu kanshi ba sai 10am na safe ga yunwa duk ta addabeshi,waya ya d'auka ya kira mama suka gaisa yace mata yayi latti ne shiyasa ya fice bai shiga ba,haka ya kira abba ma,daga nan sai sahibar tashi wato IMAAN,Ashe bata tashi ba sai wayar ne ya tashe ta,d'auka tayi tace''hello'',daga can YARIMA yace''hey!baby na baki tashi ba kenan,nine ma na tasheki ko?",i'm sorry,amma kinsha bacci'',tace''eh,''yace''duk gajiyar jiya ce baby na ya fad'ane dan ya tsokano ta,ta shagwa6e kamar tana gabanshi tace''ni ka daina banso'',yace''to na daina,so ya kike?",tace''lafiya lau,kana asibiti ne?",yace''yes'',tace''shine baka tashe ni ba'',yace''sorry na makara ne ko break fast banyi ba har yanxu duk yunwa ta addabeni,amma ai nayi bankwana da ke ko?",tace''yaushe ni da nake bacci'',yace''nayi miki kiss a baki da zan fita'',kunya taji ta basar sannan tace''yanxu to me zakaci a can?",yace''yanxu na aika za'a kawo min tea'',inaso kafin in dawo a sake min suna,in tashi daga YARIMA in koma wani matsayi,kuma yau abincin ki nkso ki dafa mana da kanki OK?",yace''to naji amma me sunan naka yayi da za'a sauya shi?", Murmushi yayi yace''bakiji mutane suna cewa mazansu sweety ko dear ko darling ko honey ba?",to sai ki za6i wani a ciki ki rink'a kirana dashi,kuma ki tashi kiyi break rana tayi sosai,luv u baby na,yayi mata kiss ta waya sannan ya kashe,duk ya saukar mata da kasala,kai YARIMA k'arshe ne wajen soyayya dan yanda yake magana kad'ai ya isa ya saye zuciyar mace,hmm.... Tashi tayi ta tsala wankan ta sannan ta sauko dan neman abinci,su harira ta gani suna zaune a falon, wajen su tazo ta zauna suka gaisa,dan ta hana su su rink'a sunkuya mata,sannan ne ta tashi ta nufi dinning,zama tayi taci abinda ranta ke so,a ranta tace haba yanxu naji daidai,amma ace mutum duk abinda yaci sai ya amayar,to kodai in ce ma YARIMA ya kawo min maganin hana d'aukar ciki?,cabb ai kuwa ba ruwan mΓ» ko sister Sai 6 na yamma YARIMA ya dawo a lokacin su IMAAN sun gama komai na abinci,har ta tsala wankan ta tayi kwalliya tasha wani less pink mai d'an karen kyau,tayi shar da ita,ko da yayi sallama su harira suka mishi sannu da zuwa suka fice,IMAAN kuwa tashi tayi ta kar6o jakar shi tare da mishi sannu da zuwa, Yace''haka ake yiwa maigida sannu da zuwa ? ",ta kalleshi tace''ban gane ba?", yace''zuwa zakiyi ki min kiss a kunci mana'',tace''muje kayi wanka kafin time d'in sallah'',yace''toh fa baby na ta fara koyon yanda akeyi,hhh..ficewa tayi gaba yana biye da bayanta har d'akinshi....da shigarsu kamota yayi ya shiga kissing d'inta da k'yar ta kwace kanta tace''uhum meye haka lokacin sallah fa'',yace''na sani zo ki cire min kaya'',tace''haba kayan ma bazaka cire ba sai ni'',yace''yes ko kuma in cire da kaina ke kuma ki kar6i hukunci na'',tace''hukunci kuma wane irin?", yace''bari in nuna miki yazo zai kamata ta gudu,dariya yayi ya cire kayanshi ya shiga toilet... ********** ****** Bayan sallah isha'i,suna wajen cin abinci ya kalleta yace''baby na Anya ke kikayi abincin nan kuwa?", tace''Nice mana me ka gani?", yace''ashe kin iya abinci haka kika bari wasu suke mana'',tace''na iya mana'',suka ci abincin su sannan suka dawo falo dan kallon t.v,IMAAN a ranta cewa take ko inyi masa zancen skull d'in ne,YARIMA ya kalleta yace''yadai baby na akwai wani Abu ne?", tace''uhmm...daman zancen skull d'in nawa ne,nace sai yaushe zan koma ne?", jayota yayi ya rungume yace''sai sabuwar shekara zakiyi'',tayi zumbur ta zauna tace''kamar ya me zai hana ni komawa a yanxu?", Yace''baby na banson ki sake samun wani cikin kuma ga zuwa skull kinsan bazan yadda ba ko?,so da muzo muna samun matsala ki bari zakiyi next year kafin nan kin dire min baby na ko twins ma'',tace''haba dai ai yanxu bani da wani ciki'',yace''ina sa rai very soon kinsan fa kina tare da gwarzon miji,jarumi kuma'',hhhhh YARIMA Kenan, IMAAN tace''to me zai hana ka kawo min magani insha har in gama skull d'in tukun'', Wani mugun kallo ya mata yace''what?magani fa kikace,baby na karki kaini mak'ura fa,waye ya koya miki haka?", Batayi magana ba yace''to wlhy in kika sha wani magani ban yafe fa,a shekarunki har kinsan a sha magani'',hak'uri ta fara bashi,tashi yayi ya haye sama ya kyaleta a nan tana hawaye....... *ayi hak'uri da wannan,buzy* *Sister ummu basheer,miyidima bansan*😘😘 *Bizu a mon bΓ©bΓ© Abdul*πŸ’‹πŸ’‹ *'YAR MUTAN KAZAY CE*πŸ’ž *ANTY MAIMOUNATH*😘 *+22969164943* [27/10, 21:45] Yar Niger Frd Husaini: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *KHADIJATUL* *IMAAN* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *STORY* *&* *WRITTEN BY*:✍🏻 *ANTY MAIMOUNATH*πŸ’ž *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page3⃣5⃣~3⃣6⃣ IMAAN ta jima a nan tana da na sanin maganar ta,wasi wasi takeyi taje ta bashi hak'uri ko kuma ta barshi har ya sauko da kanshi,hmm Hawa tayi ta shiga d'akinta tayo wanka tasa wata shed'aniyar rigar bacci Wanda ita da babu duk daya,hmm wannan duk cikin koyarwa ne na anty khaleesert,ta feshe jikinta da turare mai k'amshi bayan ta shafe jikinta da humra wadda anty tasa aka yi mata,d'akinta ta rufe ta nufi bedroom d'in YARIMA gabanta sai fad'uwa yake dan batasan abinda zata iske ba,tana tsoron ya daketa dan kad'an daga aikin shi idan ya zuciya,hmm Knocking tayi ba'a amsa ba,ita kuma ta murd'a k'ofar ta shiga,yana zauna tsakiyar gado yana type a laptop da alama aiki yakeyi,sallama ta mishi ya amsa ba tare da ya d'ago kanshi ba,zuwa tayi kusan gadon ta durk'usa har k'asa ta fara bashi hak'uri, turaren jikinta ne ya fara kai mishi ziyara yaji duk kasala ta saukar mishi,ya kasa katab'us,IMAAN tace''kayi hak'uri bazan sake ba,karka fad'a ma abba na,wlhy har duka zai min in yaji'',kyalewa yayi bai ce da ita komai ba, Kukan kissa ta fara,hmm wai su IMAAN an fara girma har da kissa aka iya,juyowa yayi ya kalleta numfashin shi ne ya kusa d'aukewa dan ganin irin rigar da take cikinta,yaso ya basar, amma ina wane mutum inji mutuwa,zuwa yayi ya kamota ya hau da ta bisa gadon,yasa hannu ya d'ago ha6ar ta yace''baby na menene,ke abu kad'an na kuka ne a wajenki ko?,sai kanki yazo yana miki ciwo'',komawa tayi ta kwanta lub a jikinshi,ya kwantar da ita sannan ya kashe musu wutar d'akin,yaso yabar IMAAN ta huta a yau amma ina ganinta cikin wannan shiga ya sanyashi wani hali marar misaltuwa,a hankali yake shafar ta,har hannun shi ya ta6o na shanun ta,zura hannun shi yayi cikin rigar ta ya kamasu yana wasa dasu,hannu d'aya ya tallabe ta yana tsotsar lips nata,nok'ewa tayi ta juya mishi baya,murya a kasalance yace''me ya faru kuma baby na'',tace''ni na gaji bacci zanyi'',yace''please baby na wane irin bacci kuma,ashe zaki iya barina a cikin wannan yanayin?",shiru tayi,hannu yasa ya juyo ta yace''sorry ki bari in samu nutsuwa,a shagwa6e tace''nidai akwai ciwo in kanayi,kuma kullum sai kayi min wayo kace kad'an zakayi'',yace''naji yau kad'an ne please,mata da miji sai Allah,nan dai ya lalla6e ta suka dulmiya duniyar ma'aurata,hhhhh........ *Asuba ta gari PRINCE ND IMAAN.....* ********** ***** Da asuba bayan sunyi sallah komawa sukayi suka kwanta,kasancewar asabar ce,ranar hutu ce,duk da dai wani lokacin YARIMA Dole sai yaje asibiti in kamar za'ai tiyata ne ko abinda ya gagari sauran likitocin, Kamo IMAAN d'inshi yayi ya rungume suka koma baccin su,sai kusan 12am na rana sannan suka tashi,IMAAN ce ta fara tashi,d'akinta ta nufa tayi wanka ta sa kayanta tayi simple kwalliya,'yar hoda ce da kwalli sai man lips da ta shafa,kayan sun kamata das ta fito,ni kuwa nace kar fa YARIMA yasa ki wankan Dole yanda kika sa wannan kaya haka,atamfa ce dinkin Riga da skirt ne,ta bad'e jikinta da turare,ita daman can mai son tsabta ce,ta nufi d'akin YARIMA har yanxu bacci yake,a hankali taje ta zauna kusa dashi ta shiga kallon shi,yana bacci abinshi cikin nutsuwa babu abinda ke damunshi,a ranta tace kai a gaskiya nayi dace da miji,YARIMA k'arshe ne wajen kyau da iya nuna wa mace soyayya,k'aryane mace ta kalleshi bata kyasa ba,hhhh nidai banda niπŸ™Š Tana cikin kallon shi ne ya motsa tayi sauri zata tashi,taji an rik'o ta ta fad'a jikin shi,a kunne yake rad'a mata cewa''me kike kallo,YARIMAN ki ko?da fatan babu wata makusa a jikin shi'',kasa magana tayi duk kunya ta lullu6e ta ashe ya ganta,hmm,to sai me ba mijinki bane inji ummu basheer dan ni bansan komai ba.. YARIMA yace''baby na kinyi kyau ashe dai kin iya kwalliya shine bakya yi min in gani'',ya shafa wajen marar ta yace''Allah yasa nayi ajiya a nan'',IMAAN kanta ta cusa a k'irjin shi sbd kunyar da taji,shi fa ba ruwanshi YARIMA d'an rayuwa ne saboda zaman da yayi a turai,amma duk da haka ya rik'e addinin shi,bai yin shaye shaye da neman mata irin na sauran mutane, Yace''baby na tashi a sama na kina sani wani yanayi gashi ke kuma da nace zanyi sai ki fara min raki'',ai kuwa firgigit ta tashi,kauda kanta tayi sannan tace''ka tashi ka shirya muyi break fast rana fa tayi har 12 ta wuce'',a zolaye yace''to ba ke bace kika hanamu bacci jiya'',ta rufe fuska da hannayen ta tace''ni ba ruwana kai ne dai'',murmushi yayi bai ce komai ba ya yaye blanket d'in daga shi sai gajeren wando,IMAAN ido ta zaro,subhanallahi,gaskiya YARIMA irin sadaukan mazan nan ne jarumai kuma,jiki duk a murd'e,yes namiji Kenan,kallon ta yayi yace''lafiya meye?",idonta a rufe ta nuna shi,ya gane ta,sai yayi murmushi yace''bud'e idon ki kalleni,meyasa kike kunya ta,nifa mijinki ne,yanxu babu zancen kunya,muje ma kiyi min wanka'',tace''a,a ni nayi in na shiga zan 6ata jikina'',yace''hmm baby na wayo ko?",to jirani yanxu zan fito......bai jima ba ya fito ya saka k'ananan kaya,suka sauka k'asa,wajen dinning suka nufa,suna tsakar yin break d'in ne akayi knocking k'ofar falon,YARIMA ne ya tashi yaje ya bud'e,harira ce ta sunkuya ta gaishe shi yace''lafiya?",tace''wasu ne suka zo suna k'ofar gida mai gadi yace sai an sanar daku zai barsu su shigo'',yace''ok gani nan zuwa da kaina'',tace''to ranka ya dad'e sannan ta shiga cikin falon ta iske IMAAN,shi kuma ya fice....da zuwan shi k'ofar gidan ya hango MUSTAPHA daga cikin motar,ya zaro ido ya isa da sauri yace''what?wa nake gani kamar abokina?",MUSTAPHA yayi dariya yace''surprise ne muka muku'',UMMU AYMANA ta gaishe shi, sannan yace a bud'e get su shiga,shiga sukayi yayi parking d'in motar sannan suka fito mai gadi kam yasha fad'a a wajen YARIMA sai da Mustapha yace mishi ya barshi ai bai san mu bane kaga Kenan yanada gaskiya,fada suka fara zuwa YARIMA ya gabatar dasu wajen mai martaba aka gaggaisa sannan suka shiga ciki nan ma sai da ya kaisu wajen hajiyar shi,wato mama kenan, daga 6angarensu yayi dasu,ita dai UMMU AYMANA mamakin irin girman gidan take,gida ne cikin gida,Wanda bai san kanshi ba zai iya 6ata,sallama sukayi sannan suka shiga cikin falon ba kowa sai su harira suna kai kawo a falo zuwa kitchen,YARIMA yace bismillah ku zauna ke harira kawo musu abin sha,ya kallesu yace''i'm coming,sannan ya hau sama,zuwa yayi yace''baby na albishirinki'',tace''goro''yace''kinsan bak'in namu kuwa?",tace''a,a'',yace''k'awarki ta malaysia UMMU AYMANA sune sukazo'',IMAAN tayi k'ara ai kuwa ta warci hijab tasa

Chapter 7 of 10