Share this page
8 / 10
sai k'asa,YARIMA yana cewa kiyi a hankali fa karki fad'i,ina ta tafi,tana sauka taje da gudu ta rungume ummu aymana tace''kai anty na shine kuka yi mana surprise'',tace''kiyi a hankali irin wannan gudu haka ai sai ki jima kanki ciwo'',a kunyace ta koma ta zauna suka gaisa da Mustapha,sannan tace''anty ina haneefah kuma ban ganta ba?",tace''na bar ta a gida wajen mai reno yanxu zamu wuce ai,saidai in mun dawo musha hirar mu'',daidai nan YARIMA ya iso ya zauna IMAAN ta kalleshi tace''kanajin anty wai tafiya zasuyi'',tace''haba dai tun yanxu'', Mustapha yace''ai ba hira mukazo ba,mun fito daga wani wajen ne nace mu biyo,amma zamu kawo muku wuni wata rana,amma bani number wayar ka zan kiraka in zamu zo'',yace''ok to kawo in sa maka,nan dai sukayi musanyar number IMAAN ma ta d'auki ta ummu aymana,sun d'an ta6a hira sannan suka fice,har ummu take tambayar IMAAN ya ta ganta babu cikin,IMAAN ta zayyane mata komai,ummu tace''ayya srry bakomai Allah ya kawo mai albarka'',dukansu suka amsa da ameen..... ******** **** Bayan sallah magrib ne IMAAN taje 6angaren su mama,wajen nafeesat,ta iske su a falo suna zaune ta shiga tare da yin sallama,zuwa tayi har k'asa ta durk'usa ta gaishe da mama,mama ta kalleta tace''yata lafiya naga kin rame kinyi fari haka?",IMAAN ta sunkuyar da kai tace''lafiya lau mama'', Mama tace''a,a fad'a min gaskiya kodai baki da lafiya ne,ko shureim yana miki wani abin ne?",girgiza kai tayi tace''ba komai mama'',tace''a,a ban yadda ba akwai wani Abu'',bari in kira mijin naki,d'aukan waya tayi ta kira YARIMA yana d'auka tace''kazo ina kiranka....... *'YAR MUTAN KAZAY CE*💞 *ANTY MAIMOUNATH*😘 *+22969164943* [27/10, 21:45] Yar Niger Frd Husaini: 🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *KHADIJATUL* *IMAAN* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *STORY* *&* *WRITTEN BY*:✍🏻 *ANTY MAIMOUNATH*💞 *Wannan shafi na sadaukar dashi ne ga 'yan grp din:* *Alk'awari fan's,khadijatul Imaan fan's,nuriyya fan's,inajin dadin addu'o'inku,mi yenty......* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page3⃣7⃣~3⃣8⃣ YARIMA ne ya shigo tare da yin sallama, yazo kusa da k'afafuwan mama ya zauna,mama ta kalleshi tace''shureim'',yace''na'am mama'',tace''me yake damun yarinyar nan naga duk ta rame,kalleta ka gani da kyau kamar marar lafiya ko bata cin abinci ne da kyau?",ya d'ago yace''mama lafiyar ta lau,kuma tana cin abinci'',tace''yanxu mai lafiya haka yake,ita tak'i ta fad'a min abinda yake damunta,kaima gashi nan kana 6oye min'', Yace''wly mama ba komai'',mama tace''to bakomai amma ta rame haka,kodai damunta kakeyi ne?",nan take kunya ta lullu6e YARIMA dan ya gane tambayar inda ta dosa,Sosa keya yayi yace''a,a mama'',tace''haba d'an nan me ka d'aukeni na tabbata haka ne,kunyar fad'a min takeyi shiyasa tace ba komai, to bari kaji ba haka ake zaman aure ba,ya kamata ka rink'a kyale musu yarinya tana hutawa,in duk mazan duniya kamar kai suke da ba kowace mace bace zata jure zaman auren,itama hak'uri ne da ita,amma nasan abinyi duk laifin mai martaba ne da yasa waziri yake baka abinda bai kamata ba,IMAAN da YARIMA dai kansu a k'asa dan kunya,tace''ku tashi ku tafi zanga wazirin gobe insha Allah, Tashi sukayi suka nufi 6angaren su,da shigar su ya janyota ya rungume ture shi tayi tace''ka manta akwai su harira ne",yace''ban manta ba,dan suna nan saï in k'i rungume my wife'',tace''nidai ka daina salon su fito su gan mu ko'',yace''so what dan sun gani,mu da gidan mu sai a hana mu shak'atawa,suzo ma su fice tunda sun gama girkin'', Kiransu yayi sukazo yace''kun gama aikin ko?",harira tace''eh har mun kai dinning'',yace''good,to ku fice ku tafi sai da safe kuma'',tashi sukayi suka d'auki abincin su suka fice.... Zuwa yayi ya kulle k'ofar falon ya dawo,suka nufi dinning table,da kanshi ya zuba mata abincin,ta kalleshi tace''wannan duka ina zan iya cinye shi gaskiya yayi min yawa'',yace''bakiji abinda mama tace bane yanxu,cewa tayi kin rame kamar marar lafiya, nima sai yanxu naga hakan so ki cinyeshi duk ko inyi miki dura'', Baki ta zumburo amma batace komai ba ta fara cin abincin,suna tsakar cin ne ya kalleta yace''baby na kinsan me mama take nufi da ina damunki?",tace''a,a'',ido d'aya ya kashe mata yace''wai nufinta ina damunki wajen kwanciya'',take IMAAN ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya tace''ka daina ni banso'',yace''an gama gimbiya matar yarima'', ********* ***** Cikin dare IMAAN ta farka tana murk'ususu har YARIMA ya tashi,ganinta a zaune yasa ya tashi da sauri ya kama ta yace''baby na meye'',da k'yar tace''marata take ciwo duk sanyin A.C da ke d'akin amma ita zufa takeyi dan wuya,ya rungume ta yace''oh my God,sannu baby na kinji,zai daina bari in miki dubara kafin safe in kira doctor'',shimfid'eta yayi ya tashi ya nemo ruwan zafi da d'an karamin tawul yazo ya cire mata Riga tana k'i ma yace''meye kuma ki bari magani ne zan miki dan ki samu bacci'',y'a barta daga ita sai pant,yana tsoma tawul a ruwan zafi yana d'an dadanna mata a marar yana kawo sauqin rad'ad'in ciwon, Da haka ya samu tayi bacci bayan tayi ta mishi kukan shagwa6a,ya kwantar da ita ya mayar da abin ruwan zafin ya shiga toilet ya shanya tawul d'in tare da d'auro alwala yazo ya fara nafilfilin shi sai 3:30pm na koma bacci tare da rungume babyn shi,kai YARIMA akwai son yaji shi jikin mace hmm, Da asuba ya kusa makara zuwa masallaci dan yana zuwa ana tayar da sallah,sakamakon a da kuwa yana can ake tayarwa, Ko da ya dawo har yanxu tana bacci,da alama kuma taji sauqi,shiyasa ma bai tashe ta ba, tunda ba sallah take ba,zuwa yayi ya kwanta a bayanta har bacci yayi awon gaba dashi,sai 10am na safe IMAAN ta tashi,d'akinta taje daga nan ma toilet ta shige tayo wanka ta shirya,bata koma d'akin YARIMA ba,k'asa ta sauka,daga nan tayi kitchen dan yau tanaso tayi musu break fast da kanta,tea ta had'a Wanda yasha kayan k'amshi su citta da kanumfari ta duk ta had'a dasu,ta dawo ta sulala dankalin turawa ta fasa Kwaï tasa maggi, onga,da dai sauransu,sai da ta had'a komai ta shirya a dinning,ta hau sama,d'akin YARIMA ta nufa,da ta shiga bata ganshi ba,amma taji k'aran ruwa a toilet,wannan ya tabbatar mata cewa yana wa ka Kenan... Tana zaune ya fito daga shi sai tawul,kauda fuskar ta tayi,dan bata son ganin shi ba kaya tsoro yake bata,hhhhh IMAAN Kenan, Tace''the food is ready fa kai nake jira'',yace''banji ba,sai kin juyo kin kalleni sannan zanji'',tace''to sai ka sanya kaya tukun'',bata sani ba yayi sand'a yazo yace''to juyo ki kalleni na saka'',tana juyowa taga har yanxu bai sa kayan ba,ta saki ihu,saurin rufe mata bakinta yayi da nashi bakin sai da ya tsotse bakin tas sannan ya saketa,su duka suna maida numfashi,tashi tayi ta gudu dan ma kar yace zai sake mata,a falon ya isketa suka nufi wajen cin abinci, kallonta yayi ya ce''baby na kece da kanki kikayi mana break yau?",tace''eh mana ni ce nayi'',yace''to ya ciwon cikin ya daina ko?",tace''eh da sauk'i amma ina ji kad'an kad'an'',waya ya d'auka ya kira doctor mata ta gidansu, Bayan ta d'auka ne yace''morning doctor ya kike?",tace''morning YARIMA lafiya klau,ya madam'',yace''tana lafiya,plx magani nakeso ki aiko min na killer pain,ni babu a nan gida saboda na manta ne wlhy kuma sai gobe zanje asibiti'',tace''ok ba matsala ko ni da kaina zan iya kawo maka'',yace''ok thank u,sai kinzo d'in'', Suna zaune a falo doctor tayi sallama ta shigo,bayan sun gaisa ne ta fiddo magani a jakar ta,ta bashi yace''nagode,wlhy jiya bamuyi bacci da wuri ba saboda ciwon cikin nata ne ya tashi,tace''ayya sorry madam,zai daina insha Allah daga ta haihu shikenan'',yace''insha Allah muna sa ran hakan,ai yanxu bai mata kamar na farko'', Doctor bata jima ba tayi musu sallama ta tafi,ya kalli IMAAN yace''tashi d'auko ruwa kisha maganin,baki ta fiddo tace''nifa na warke'',yace''wane irin kin warke,to wlhy ko kisha ko inyi miki allura yanxun nan'',ai ba shiri ta tashi ta d'auko ruwan tasha'',dariya yayi yace''baby na akwai tsoron allura'', Tace''akwai ciwo ne wlhy,ni ko sunanta banson ji'',janyota yayi ya rungume ya rad'a mata a kunne''kina tsoron allura idan kika zo haihuwa kuma fa?",kanta ta cusa a k'irjinshi tace''banso ka daina'',to naji na daina idan time yayi kinyi min bayani ai,hhhh....... *'YAR MUTAN KAZAY CE*💞 *ANTY MAIMOUNATH*😘 *+22969164943* [02/11, 22:18] Yar Niger Frd Husaini: 🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *KHADIJATUL* *IMAAN* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *STORY* *&* *WRITTEN BY:*✍🏻 *ANTY MAIMOUNATH*💞 *DEDICATED TO:MY LUVLY FAMILY,I MISS U SO...SO MUCH...😘😘😘😘😘* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page3⃣9⃣~4⃣0⃣ Wuni sukayi suna shan soyayyar su kasancewar babu aiki,da wannan ne yarima yake amfani wajen cusa ma IMAAN son shi,dan yanxu ta fara sakewa dashi ba kamar da ba,hmm yarima na daban ne cikin maza... Tun k'arfe 7:00am na safe yarima ya tafi asibiti sakamakon aikin da gareshi sosai a can...yana zaune a office a lokacin k'arfe 11am ne,wata nos ce tayi knocking ta shigo office d'in,zuwa tayi ta tsaya batayi magana ba,yarima ya d'ago kanshi ya cire glass d'in da ke fuskar shi,yace mata''ya dai,lafiya kikazo kika tsare ni da idanu?",kanta a k'asa tace''uhm...daman..ina neman wata alfarma ne'',fuska d'aure yace''alfarmar me?",tace''daman kirana akayi daga gida mahaifiyata ce ba lafiya inaso in tafi gida'',yace''ok no problem kina iya zuwa,Allah ya bata lafiya'',tace''ameen na gode sir,ficewa tayi tanajin dad'i yau sunyi magana da yarima,kasancewar sun sani bai basu fuska ko kad'an, Yarima kuwa binta yayi da ido,ya girgiza kai,yace wai me yake damun matan nan ne,dan ya tabbata ba wannan kawai ne ya kawo ta ba,tsoron fad'a ne tayi,murmushi yayi da ya tuna IMAAN d'inshi,yace my sweet baby kenan, ai ni ita kad'ai ta isheni rayuwa,she is my life,i can't survive without her,hhhhh ni kuwa nace yarima ya zauce kan imaan, abinda bai tab'a tunani ba,wai shine yau yake nunawa mace so,hmm rayuwar Kenan ai... Ba yarima ne ya koma gida ba saï wajen 8:00pm na dare,a lokacin kuma 'yar rigimar tashi ta cika dan ganin bai dawo gida da wuri ba,hmm su imaan an san dad'in soyayya Kenan,ko da ya shigo da sallama da k'yar ta amsa gami da tashi tayi d'akin ta,hmm,murmushi yarima yayi dan ya gano laifin shi,binta yayi har d'akin nata,ya isketa a zaune bakin gado tana danna wayar ta,game takeyi,zuwa yayi ya zauna kusan ta yace''baby na yau babu sannu da zuwa ne?",tace''ka koma inda ka fito saï ayi maka a can'',yarima rungumo ta yayi yace''haba baby na kinsan fa daga asibiti nake,ina kuma zanje?",tace''oho wa ya sani dai'',yace''is ok,am so sorry baby na wlhy aiki ne yau nasha duk na gaji tashi mu tafi ki taimaka min inyi wanka saï muci abinci dan har yunwa na kawo'',zatayi magana ya d'ora hannunshi a bakinta yace''ya isa haka tashi mu tafi ko kuma inyi miki allura dan yau da kayan aiki nazo ban manta komai ba'',tace''ai na warke ban tsoro'',yace''are u serious kin warke,kina nufin bak'on ki ya tafi?",tace''wane bak'o kuma?",yace''bak'o mai hanani sakewa da baby na man,saï a nan ne ta gane nufinshi,rufe fuska tayi tace''a,a fa ban warke ba gaskiya'',yace''ok muje to'', Tana zaune har ya gama wanka yasa k'ananan kaya sannan suka nufi k'asa dan cin abinci,bayan sun gama ne suna zaune a falo suna kallon t.v,wayar imaan tayi k'ara,tana dubawa saï taga ashe k'awarta jamila ce,d'auka tayi bayan sun gaisa jamila tace''yarima ya fad'a miki an sanya ranar auren mû?",ihu imaan tayi Wanda saï da yarima yace''ke lafiya kike ihi?",tace''ba komai,sannan ta cigaba da cewa''wai dan Allah da gaske kike an sanya ranar biki?",jamila tace''ke wallahi da gaske nake miki nan da two weeks aka sa'',imaan tace''wayyo Ashe zamu sha biki budiri,to yaushe zakizo mû shirya yanda za'ayi dan kinga ba isasshen lokaci'',jamila tace''gobe ina nan zuwa insha Allah'',tace''OK Allah ya kaimu saï kinzo bye,bayan sun gama wayar ne ta juyo ta kalli yarima Wanda shi hankalin shi ma yana kan t.v,tace''shine baka fad'a min an sanya ranar bikin su naseer ba'',ya janyota ta fad'a k'irjinshi,yace''sorry mantawa nayi d'azu naseer ya kirani a waya ya fad'a min,kuma daga zuwa na kin tarbeni da fushi shiyasa na manta ai'',hmm su baby har an iya kishi,tace''ni ba kishi nake ba'',yace''to meye, cewa fa kikayi in koma inda na fito'',kyalewa tayi,yace''tashi mu tafi mû kwanta yau bacci nakeji da wuri,na gaji sosai, Kashe kayan kallon yayi yake ya rufe k'ofar falo sannan ya jata sukayi bedroom d'inshi,tana ganin ya shiga toilet ta tashi taje d'akinta dan sauya kata zuwa rigar bacci, ta shafa turaren humran ta mai shegen,ta rufo d'akin ta goma bedroom d'in yarima,a daidai lokacin ya fito daga toilet yana goge jikinshi da tawul,dan Jan magana yace''baby na zo ki goge min jikina mana'',wucewa tayi ta hau gado ba tare da ta kalli inda yake ba,murmushi yayi,saï da ya feshe jikinshi da turare mai dad'i sannan ya fesa Air freshner a d'akin ya kunna A.C haba nan da nan d'aki ya d'ume da k'amshi zuwa yayi ya hau gadon tare da kashe wutar d'akin saï duhu ne ya mamaye ko ina ya shige blanket d'in shima,ya lalube ta yace''baby na juyo kiji wata magana,a rashin wayo na imaan saï ta juyo,bakinsu ya had'e waje d'aya ya tura hannu cikin rigar ta,wasa ya fara da k'irjinta,mutsu mutsun kwatar kanta ta shiga yi,a hankali ya rad'a mata yace''kinsan dai ba wani Abu zanyi ba,just inason in samu nutsuwa ne,wlhy a matse nake'',kyaleshi tayi saï da ya gaji dan kanshi ya kyaleta tayi bacci.... ********* **** Da safe,yau imaan ce da kanta ta shiga kitchen dan tayi musu break,dankalin turawa ta d'ora a wuta dan ta sulala shi,ta fasa Kwaï tasa Maggi,onga,da dai sauransu,ta kad'a kwan sosai,ta fere sulalanlan dankalin nan,ta d'ora mai a wuta da yayi zafi saï ta d'auki dankalin nan ta tsoma a ruwanKwaï saï ta zuba a kwaskon tuyar,haka takeyi har ta gama,saï kuma ta had'a ruwan tea mai kayan k'amshi citta da kanumfari,saï da ta jera komai a dinning table sannan taje ta tashi yarima a bacci,ya shirya ya zo sukayi break ya kalleta yace''kai baby na amma gaskiya kin iya dahuwa''tace''da gaske kakeyi tayi dad'i?",yace''of course,i'm serious yayi dad'i'',tace''thank u dear'',yace''me kikace?inda d'an k'ara fad'a inji'',rufe ido tayi,yace''kai baby na ba dai kunya ba,yaushe ne za'a daina dan ni take cuta'',to ni zan tafi asibiti,inaso in biya in gaishe da su mama tukun,tace''nima zanje,kafin Jamila tazo'',yace''ok mû tafi to'', Nafeesat kawai suka iske a falon tana kallon t.v,yarima yace''ke yau baki zuwa skull ne kika zauna kuna kallon t.v?",feenat tace''a,a saï da gamma'',yace''ina mama?",tace''bata fito ba tana d'akinta'',yace''ok zan kira ta in na isa asibiti,juyowa yayi ya ma imaan pick a goshi yace''baby na na wuce saï da yamma ko?",a kunyace tace''to Allah ya kiyaye hanya'',yace''ameen my nurul qalb,sannan ya fice... Imaan zuwa tayi ta zauna kusan feenat tace''wai me kike kallo da safiyar nan?",tace''uhmm wato saï da kuka gama soyayyar ku sannan kika ganni ko'',imaan tayi mata dukan wasa tace''kai feenat banda sharri a yaushe mukayi soyayya a nan'',tace''hmm ba wani sharri gaskiya na fad'a'',tace''to naji dai,an Sanya ranar bikin k'awata jamila,nan da two weeks'',feenat tace''haba dai?kai amma zamu sha biki,ko dan wannan an bar mû mû shak'ata'',imaan dariya tayi tace''kai duk murnar bikin ne haka saï kace ke za'ayi wa auren'',saï da mama ta fito suka gaisa sannan imaan ta koma 6angaren ta,ta iske su harira suna zaune,bata jima da zama ba saï ga jamila,sun sha hira Wanda rabin hirar duka ta shirye shiryen biki ce.... *BAYAN KWANA BIYU* IMAAN yau ta fara sallah amma bata son yarima ya gane saï dai kash tana sallah magrib yarima ya isko ta wani dad'i ne ya ziyarci zuciyar shi,d'akinshi ya wuce dan gabatar da wanka,imaan kuwa bataso haka ba,saboda tasan yau yarima bazai barta tayi baccin dare ba....... *'YAR MUTAN KAZAY CE*💞 *ANTY MAIMOUNATH*😘 *+22969164943* [02/11, 22:18] Yar Niger Frd Husaini: 🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *KHADIJATUL* *IMAAN* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *STORY* *&* *WRITTEN BY:*✍🏻 *ANTY MAIMOUNATH💞* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page4⃣1⃣~4⃣2⃣ Bayan sallah isha'i,suna zaune a falo yarima ya kalli IMAAN yace''baby tashi mu tafi d'aki'',cikin zokana IMAAN tace''tun yanxu,gaskiya ni banjin bacci kallo zanyi,amma kaje ka kwanta mana,ni saï na ida kallo tukun'',kallon ta yayi yace''baby na banson zolaya fa,kinsan abinda nake nufi ai,please tashi mû tafi'',nok'ewa tayi,kashe t.v d'in yayi cak ya d'auketa,tace''ni ka saukeni zan tafi da k'afafuna'',yace''no bari dai in kaiki da kaina,saï tsoro kamar wata sabuwar amarya'',rufe fuska tayi,bai direta ko ina ba saï bisa gadon baccin shi,yace''ina zuwa ya shiga toilet,tashi tayi ta cire zanen da ta d'aura bisa rigar baccin ta,ta shige blanket tayi baccin k'arya,ko da ya fito bai tsaya wani b'ata lokaci ba,direct gado ya nufa,kiss yayi mata a baya yace''nasan ba bacci kikeyi ba'',kyaleshi tayi,hannu yasa ya juyo ta yace''baby na meyasa har yanxu kike tsoron in kusanceki?",ya k'ara cewa''ko har yanxu ciwo kikeji?",kai ta gyad'a mishi,yace''dan kina tsoro ne yasa kikejin ciwon ai,so please ki daina tsorona,ni ne fa prince d'inki,babu abinda zai faru,wannan tsoron ko sabuwar Amaya bazata yi ba ai'',murmushi tayi ta cusa kanta a k'irjinshi Wanda yake d'auke da yalwataccen gashi mai santsi,kissing d'inta ta shiga yi yana wasa da ita duk dan ta saki jikinta,a hankali yake isar da sak'onshi zuwa gareta Wanda a halin yanxu ta fara kar6ar sak'on dan yaji alamu,duk ta saki,da haka ya samu ya cire mata rigar jikinta,ya gangara k'asa saï ta kama hannunshi,a hankali ya rad'a mata''please baby na kiyi hak'uri a matse nake kuma ke kanki kinsan da haka'',a haka dai har ya samu kanta,amma fa taji jiki dan in tak'aice muku labari saï da yarima yayi round biyu kafin safiya kuma ko wanne saï ya gamsu yake kyaleta,hmm amma yarima yanason kashe 'yar mutane,amma kuma yasa shagwa6ar babyn tashi dan kuka take mishi yanda kukasan sabuwar Amaya haka ta koma mishi saï raki takeyi bayan,k'ugunta,k'irjinta haka dai take fad'a har safe, ********* **** Da asuba yarima da kanshi yayi wa IMAAN d'inshi wanka sannan tayi na tsarki ta d'auro alwala,da ta fito yarima ya tafi masallaci,d'akinta ta nufa a can tayi sallah ta koma bisa gado tayi kwanciyar ta dan bacci ne a idonta,da yarima ya dawo bai isketa a d'akin ba murmushi yayi ya wuce zuwa d'akinta ya isketa a kwance hawa gadon yayi tare da rungumar ta,gabanta ya fad'i ras,dan tana tsoron yace zai k'ara dan kad'an ne daga cikin aikin yarima,marar ta ya shafa yace''Allah yasa na samu baby a daren jiya'',lub tayi ta kyaleshi har bacci ya d'auketa, Ko da ya shirya zuwa asibiti bai tashe ta ba dan yasan baccin gajiya ne takeyi,Allah sarki baby na saidai ki rink'a hak'uri da buqatata,nasan kina da k'ok'ari da juriya,hmm....imaan kuwa sai k'arfe 12am na rana ta tashi a lokacin har su harira sun ida abincin rana,da ta sauko taci abincin suna zauna a falo ita da su suna bata labari mai dad'i suna ta dariyarsu,wayarta ne tayi ringing d'auka tayi dan tasan mai kiran, ringing d'inshi na musamman ne,hmm masoya Kenan....tace''shine baka tasheni ba kayi tafiyarka'',yace''sorry baby gani nayi kinajin dad'in baccin ne,kuma nasan kin gaji jiya shiyasa'',a shagwa6e tace''banso ka daina'',yace''an gama ranki ya dad'e gimbiya matar yarima'',tace''uhm zolaya ko,to ya aiki?",yace''lafiya klau saï kewarki'',tace''kai dear duk ma yaushe ne muka rabu'',yace''da safe mana yanxu kuma wajen awa nawa nayi ban ganki ba'',tace''to ka dawo mana ba saï ka ganin ba'',yace''idan na dawo akwai abinda zaki bani?",tace''eh ga abinci an gama'',yace''haba dai me zanyi da wani abinci ni ke nakeso'',tace''ai ni daman taka ce'',yarima mamaki yakeyi wai yau IMAAN ce take mishi wannan maganganu ko dan ba a gabanshi take ba,yace''da gaske kike baby na'',ita kanta saï da yace haka sannan taji kunya,ba tare da tayi mishi sallama ba ta kashe wayar tana murmushi,su harira ma murmushin suke kansu a k'asa,ta kallesu tace''na gan ku shine kuke min dariya ko'',sukace a,a ranki ya dad'e,6ata fuska tayi tace''zamu 6ata da ku fa,ban ce muku karku sake ce min ranki ya dad'e ba?",harira tace''au mantawa mukeyi ne wlhy kiyi hak'uri'',IMAAN tace''to shikenan ya wuce,inaso ku d'aukeni tamkar k'awarku kunji ko'',sukace to, Lokacin bikin jamila sai k'aratowa yake yanxu yayi saura sati d'aya ranar muna zaune ni da yarima a gida kasancewar week-end ne,naseer yayi sallama ya shigo,nayi mishi sannu da zuwa,muka gaisa ina zolayarshi ina ce mishi ango ya shirye shirye kuma?",dariya yayi yace''alhamdulillah muna cikin yi'',yarima ya bashi hannu suka gaisa yace mishi to bismillah sai ka zauna ko wato an Sosa maka inda yake maka k'aik'aiyi ko'',dariya yayi ya zauna yace''har na kaika,karka manta a lokacin naka ko baccin dare bakayi'',dariya sukayi su duka,yarima yace''kai friend banda sharri fa'',yace''ah to ai gaskiya ce ba wani sharri malam'',IMAAN tashi tayi ta kawo mishi ruwa da jus yace''thank u gimbiyar yarima,sunkuyar da kai IMAAN tayi cikin kunya,sannan yace''to daman zuwa nayi inji dame dame ake buqata na shagalin 'yan matan amarya?",yarima yace''kai shine kuma sai wajen matata zakaxo ka tambaya,kaje ka tambayi sauran mana'',naseer yace''saboda gani nayi itace babbar k'awarta shiyasa'',yarima yace''to a cire matata a ciki ah to'',naseer yace''meye nufinka na a cireta,kana nufin bazata je ba ko me?",yace''zataje mana,amma me ya had'ata da wani shagalin 'yan matan amarya ? ",naseer yace''ok daman na tambayi jamila ne amma tak'i ta fad'a min wlhy'',sai a lokacin IMAAN tayi magana tace''to kawai ka basu abinda ya samu,kuma ma ai da abokai zakuyi shawarar abinda ya kamata ku bayar ko?", ya kalli yarima yace''to kai kaji,tashi mu tafi dan Allah kazo ka mak'ale a gida kamar mace'',dariya IMAAN tayi mishi,yarima yace''haba dai mutum a week end d'in ma bazai huta ba'',naseer yace''kai da hutu sai an gama biki kaji ma da kyau,please tashi muje akwai mutanen da ke jirana a gida'',yarima yace''to ai ka bari in yi wanka ko?",yace''naji to amma kayi Sauri'',yarima ya kalleni yace''baby na muje ki shirya ni kar wannan angon mai zumud'i ya cika ni da surutu'',imaan kuwa kunya taji ganin naseer yana wajen,tace''kaje dai ka shirya,ko nima in shirya sai muje ku saukeni a gida,yarima yace''me akeyi a gidan,bazaki ba sai jibi dan bazaki fita yau ba kuma jibi kice wajen saka lalle ko me ma ake cewa,dan haka kiyi zamanki har in dawo,yana gama fad'ar haka ya fice zuwa d'akinshi..... Suna d'an ta6a hira ita d'à naseer,yarima ya sauko,subhanallahi IMAAN ta furta a cikin zuciyarta,tace''wane irin kyau ne Allah yayi wa yarima na,hmm wai fa yariman ta kunji fa jama'a,wato IMAAN an fad'a tarkon so...k'ananan kaya ne yasa bak'in jeans da farar riga mai ratsin ja a jikinta,tamkar wani balarabe haka yarima yake,gashin kan nan nashi sai walk'iya yake idon shi manne da bak'in glass,zuwa yayi yace''to ango mai zumud'i tashi mû tafi,naseer a zolaye yace''kai friend wannan wanka kamar kaine angon,ka ganka kuwa,yau zaka had'a fad'a a duk inda muka wuce'',dukan wasa yarima ya kai mishi yace''kai karka had'ani da baby na mana,kana ganin yanda ta had'e fuska ba'',dariya nasser yayi yace''ah to ai da gaskiyar ta ka fita a haka ai yau mata sai sun kawo maka hari'',IMAAN kuwa ta cika kamar ta fashe,yarima ne yaje kusanta a hankali yace''baby na rabu dashi dan kawai ya tsokane ki ne,ai kinsan ke kad'ai ce a zuciyar prince,prince naki ne ke kad'ai,a haka ya lalla6a ta ya samu suna fita..... Ba yarima ne ya dawo gida ba sai dare saboda shirye shiryen da suke kuma an had'u da abokai aka zauna aka shirya komai kan party da komai,an shiya party ne na ango da abokanshi amarya ma da nata abokan,wannan kuma yarima ne ya d'auki nauyin shi,hmmm biki budiri Kenan...da ya shigo babu kowa ko su harira ma sun tafi 6angarensu,kai tsaye sama yayi d'akin gimbiyar tashi ya nufa,da ya shiga tana kwance a k'asa tana kuka,a ranshi yace toh fa

Chapter 8 of 10