wannan abin kafin videon nan da Audio su fita waje wallahi kashin mu ta bushe."
"Abban Zuhura ya ce "Idan na fito yanzu zargi zai shiga tsakanina da Balkisu, dole muyi haƙuri har zuwa gobe da safe." Haka sukayi sallma da juna amma ko wanensu ya kasa komawa bacci sai safa da marwa sukeyi, Abban Zuhura har parlo ƙasa yake yana yawo saiga Hajiya Balkisu ta fito, kallonsa takeyi ganin gaba ɗaya baya cikin natsuwarsa,
saita ɗauka rashin Zuhura ne ya saka shi wannan hali saboda irin so da ƙaunar da yake mata wacce ko kanta ke ciyo ranar baya fita ko ina dafa ƙafaɗarsa tayi cikin sanyin murya ta ce "Abban Zuhura kayi haƙuri kaje ka kwanta Zuhura bata cikin mugun yanayi nayi istihara tun ɗazu abinda na gani kenan addu'a zamu dage dayi Allah ya bayyana ta,
duk inda take." Ajiyar zuciya ya sauke! kana ya ce "Shikenan Balkisu zan kwanta amma bana tunanin zan ita bacci baki san kalar tashin hankalin da nike ciki bane har na matsu gari bai waye ba naje neman Ƴata da kaina." Balkisu ta ce "Kayi addu'a in sha Allah zaka samu bacci." Da ƙyar ta lallaɓa shi sukaje ya kwanta,
addu'a tayi mai har ya yi bacci tana zaune tana kallonsa tayi nisa cikin tunani sai gashi ya zabura yana kiran Zuhura Karkiyi min nifa Mahaifinki ne ina sonki fiye da kowa dan Allah...... Ya sai kuma ya koma bacci, gaba ɗaya taisayinsa ya gama ratsa zuciyar Balkisu, washegari da safe ko sallar a suna gida ya yi ta bai fita Masallaci ba,
Wayarsa ta soma ruri, Alhaji ILIYA ne yana ɗagawa ya ce "Gani nan zuwa yanzu." Ya kashe wayar kallon Hajiya Balkisu ya yi kana ya ce "Zamu fita nida Alhaji ILIYA wurin neman Zuhura kega har zuwa yanzu babu wani abu da aka samu ɓangaren ƴan sanda." Ta ce "To adawo lafiya Allah ya bayyana ta." Ya ce "Amin." Tare da ɗaukar Key ɗin Motarsa ya fita,
Ita kuwa wuri ta samu ta zauna tana tunanin inda Zuhura take, kamar wacce aka tsikara bedroom ɗin Zuhura ta shiga ta soma bincike amma bata ga komai ba, haka ta fito, laptop ɗinta ta janyo tana son duba wani abu saboda ta saka Cc Tv camera a gidan har ta manta maybe ta ga lokacin da Zuhura ta fita,
ta soma dubawa kenan, taji hayaniyar ƴan aiki a bayan gidan suna ihun wuta "Wayyo Allah Jama'a gobara a taimaka muna!." Ta gudu ta fito, wutar gas ce ta kama gaba ɗaya ta mamaye kitchen, nan fa masu gadi suka fara zuba ruwa amma a banza wutar sai hauka takeyi, har ta shiga cikin part ɗin gidan,
ai da sauri suka fito, Hajiya Balkisu ta ɗauko wayarta tana kiran Abban Zuhura amma bai ɗaya gaba ɗaya wutar ta soma mamaye gidan da gudu suka fito wajen gidan nan fa wani maƙocinsu ya kira motar kashe gobara, koda motar ta iso gaba ɗaya wutar ta kama gidan babu wurin shiga, idan aka zuba ruwa har wani zillo takeyi,
tana ƙara kamawa kar an saka mata fetur, nan da nan labarin wannan gobara ya zagaye gari gidan shahararren ɗan kasuwa Alhaji Haruna ya kama da wuta kuma an kasa kashe wannan gobara, Abban Zuhura kuwa sunyi ta kiran number da aka turo musu saƙo amma a kashe take, sun rasa gane ko waye ya akayi haka ta faru,
saƙo ne ya shigo wayar Abban Zuhura "Kaje gidanka gobara ta kama ta cinye komai har ɗakin tsafinka." Wani ihu ya kurma tare da fita mota ya kwasa da gudu Alhaji ILIYA ya bi bayansa yana kiransa amma ina har ya kai bakin titi, karaf wata ƙatuwar Mota ta buge shi, bata tsaya ba ta gudu, da yake babban titi ne,
Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY
Happy iftar Mubarak ☕🥂 My lovely friends
💀 * FATALWA* ☠️
*Love and romantic* 💋
*Story and Writer Bey*
*PINKY DARLING MRS JAY*
Masu neman fatalwa daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran liltafai
https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e
Following this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD🌍
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_______________________________________
*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝
Bismillah Rahamanin Raheem💫
🆓 BOOK PAGE 4️⃣7️⃣▶️4️⃣8️⃣
Ihu Alhaji ILIYA ya saka ganin kan Abban Zuhura ya rabu da gangar jikinsa, wasu suratai ya soma yi kamar mai taɓin hankali, "Haruna ka tashi mana muje zuwa wurin mitin kasan yaune zamu cika ma Dodon kuɗi alƙawarin da muka ɗauka kayi sauri ka tashi." Haka ILIYA ke faɗi,
Tare da ɗauke kan Abban Zuhura da ya cire ya ɗorawa a gangar jikinsa, Mutane ne suka fara tasowa dake chan tsallake titi saboda wasu sunga lokacin da wannan motar ta kaɗe Abban Zuhura, har suka iso wurin Alhaji ILIYA na wannan surutu, nan suka fahimci ƴan ƙungiyar asiri ne ai kuwa suka shiga dukansa,
yana Ihu amma ya kasa guduwa sai sunan dodon kuɗi ya ke kira , sai da suka sumar da shi kana suka rabu da shi, wani ya kira jami'an tsaro suka zo nan fa suka soma bincike, wurin motar Abban Zuhura sukaje a nan suka samu wayarsa aka kira Matarsa, suka sanar da ita halin da ake ciki,
Lokacin kuwa gidansa wuta ta cinye komai da kanta ta mutu, kowa ya cika da al'ajabin wannan gobara, Hajiya Balkisu kuwa yanke jiki tayi ta faɗi ƙasa a sume, maƙociyarsu da ƴan aikin gidan suka kaita cikin gida aka fara zuba mata afuwa da ƙyar ta farfaɗo,
tana kiran Zuhura ki dawo gidan Abbanki ya mutu saboda rashinki wayyo Allah na wannan masifar dame tayi kama Allah mun tuba." Haka take ta maganganu, kamar zautatciya,sai haƙuri ake bata, Alhaji ILIYA kuwa jami'an tsaro sun tafi da shi, kana aka ɗauko gawar Abban Zuhura zuwa gida, a motarsa Hajiya Balkisu ta ɗauke Key ɗin ɗaya daga cikin gidajensa aka wuce da gawarsa chan,
Ɓangaren Zuhura kuwa sai ƙarfe goma na safe ta falka da sauri ta zabura tana kiran "Wayyo Allah na shiga uku, za..... Ta zube ƙasa a sume saboda tunowa da abinda ta gani cikin ɗakin Abbanta, lokacin Abbey ya shigo paroln, saboda ihun ta da yaji,
ruwan sanyi ya ɗauko a firij, ya zuba mata ajiyar zuciya ta sauke! tare da buɗe idanunta, dishi-dishi take gani saboda yunwa takeji zaune ya tayar da ita, yana faɗin "Ki kwatar da hankalinki, babu abinda zai sameki ina tare dake." Kitchen ya shiga ya haɗa mata shayi mai kauri ya kawo mata
da kansa yake bata tas ta shanye kana ta zuba mai idanu saboda yanzu ta ganesa Abbeeyn Pinky ne ganin kallon da takeyi mai mai cike da ayar tambaya, ya ce "Nasan keyi mamaki sosai ya akayi nike tare da ke dalili kuwa shine Mahaifinki abokin Mahaifin Matata Khadijah ne,
Mahaifiyarta da Mahaifiyata uwarsu ɗaya Ubansu ɗaya Ummana ce Babba, Umman Khadijah ƙarama ranar da aka haife Khadijah Ummanta tace ta bani ita a matsayin Mata lokacin ma dawo London wurin karatu haka rainon Khadijah ya dawo Hannuna, ni na yayeta da kaina,
wata soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu, ana haka har na kaita makarnta lokacin na koma ƙasar US domin ƙaro karatu, tun tafiyata sau ɗaya na dawo Najeriya lokacin Mahaifin Khadijah ya ɗan fara samun arziki saboda bashi da hali sosai ya buƙace Khadijah ta koma gida har zuwa lokacin da zan dawo,
satina ɗaya na koma lokacin tana gaf da kammala makarantar piramare, ban sake dawowa ba sai lokacin da ta kammala sakandare, saboda bayan na kammala karatun da naje ƙarowa kasuwanci na fara har na buɗe babban Company, chan muna waya da juna har video Call mukeyi bayan na dawo gida aka fara shirye-shiryen bikinmu,
Zuwa wannan lokaci arziki ya tasowa Abban Khadijah, har ya sauya gida ya siyi manyan gidaje da motoci, ya buɗe manyan shaguna, a kasuwa, haka akayi bikinmu lafiya muka tare a sabon gidanmu, haka muka fara rayuwa cikin farin ciki da ƙaunar juna bayan wata biyar da aurenmu,
Khadijah fara laulayi mai matukar wahala, haka mukayi ta rainon cikin har yayi ƙwari, tafiya ta kamani zuwa Ingila naso tafiya da ita amma Umma tace na barta a nan zatafi samun kulawa kafin na dawo, bayan tafiyata Khadijah taje gidansu tayi kwana biyu ta dawo gidanmu tun ranar ta soma rashin lafiyar da ba'a gane ma kanta ba,
sunyita yawon Hospital ba'a gane komai, har na dawo natafi da ita wani babban hospital dake ƙasar Dubai, nan ma babu wani ci gaba, haka muka dawo gidan kullum abin cigaba yakeyi har cikinta ya kai watan haihuwa, a ranar kunga tashin hankali Khadijah na haihuwa Allah ya karɓe abarsa,
muna Hospital aka kira Umma Mahaifiyar Khadijah ta haukace, ranar da akayi addu'ar kwana uku na mutuwar Khadijah ranar Mahaifiyarta ta rasu, nayi rashin lafiya kamar bazan tashi ba bayan wata biyar da rasuwar Khadijah ina zaune bedroom ɗinta ina duba wasu abubuwan ta,naga wani liltafi
Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY....
💀 *FATALWA* ☠️
*Love and romantic* 💋
*Story and Writer Bey*
*PINKY DARLING MRS JAY*
Masu neman fatalwa daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran liltafai
https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e
Following this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD🌍
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_______________________________________
*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝
Bismillah Rahamanin Raheem💫
🆓 BOOK PAGE 4️⃣9️⃣▶️5️⃣0️⃣
Tayi rubutu Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shekaran jiya naje gidanmu nayi kwana biyu, ranar da zan dawo kunnuwana sunyi min mummunan ji wanda ko a mafalki banyi tsammani ba ashe abinda wasu mutane ke faɗa akan dukiyar Mahaifina gaskiya ne bata hanyar Allah ya sameta ba,
shida abokinsa Alhaji Haruna sun bayarda ƴaƴan su ne saboda abin duniya ina matuƙar ƙaunar Mahaifina bazan iya tona masa asiri inason na sanar da kai Mijina da kunnena naji Abbana na waya da Abokinsa cewa ya bayar dani dana haihuwa zasu shanye jinina, shi kuma Alhaji Haruna ya bayarda auren ƴarsa ga dodon kuɗi,
wannan ya sa na tattara kayana na koma wurin Umma saboda kar Mahaifiyata gano halinda nike ciki, ka duba dirowata ma ajiye wayata a cikin akwai Audion maganar su dana ɗauka inason ko bayan raina ka samu wannan saƙon la dakatar da su da abinda suke aikatawa, ka taimake wannan yarinya, daga mugun halin da Mahaifinta zai jefata
tun daga wannan lokaci nike bibiyar Surukina da Abbanki dake kanki sai gashi tafiya ta kama ni ina dawowa na tarar keyi aure ba kya ƙasar nan kina Pakistan, haka na cigaba da bibiyarsu, har zuwa lokacin da kika dawo, ƙasar nan, Mahaifinki shine ya kashe miki aure saboda yasan duk kina tare da Arman bazai taɓa cin galaba akanki ba,
Wannan shine dalilin da yasa bayason kiyi alaƙa da kowane namiji lokacin da kika shiga wannan ɗaki yaji alamar haka." Nan ya kwashe komai ya gayama Zuhura har yadda akayi ya taimaketa saboda Dr da suke zuwa wurinsa abokinsa ne shine suka hada kai yayi mata allurar bacci matsyin ta hauka,
Tun da ya fara bata labari hawaye ke zuba a kan fuskarta har ya ƙarasa, sai yanzu take tuna wasu abubuwa da suka faru, lokacin da ta haɗu da Arman ƙasa mai tsalki har suka ƙulla soyayya mai ƙarfi ƙarshe ya biyota Najeriya, babu kalar walaƙacin da Abbanta bai yi mai ba Mommy ce kawai ke sakar mai fuska,
itama haka kawai ta dinga yi mai walaƙanci lokaci ɗaya kuma ta dena, da ƙyar dai akayi auren nan Abuja suka fara zama bayan wata biyu suka wuce Pakistan, share hawayen tayi kana tace"Na gode sosai Allah ya saka da alkhayri, Allah ya jiƙin Aunty Khadija ya raya muna Pinky." "Amin." Kawai ya faɗa,
shiru ya biyo baya kafin ya ce "kiyi wanka kizo na maida ki gida." "To kawai ta ce kana ta shiga ciki wanka tayi kana tayi sallar asuba ta fito, suka fita, kai tsaye Unguwar Area 11 suka nufa ta ce "Ai ba nan Unguwarmu ba." "Eh na sani yanzu dai nan ku ka dawo, saboda gobara ta cinye wancen gidan!."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Wayyo Allah Mommyna fa.?" Ya ce "kega karki cika min kunne idan munje ai zaki ganta." Shiru tayi ganin lokaci ɗaya ya sauya kamar ba shi ba, suna isa bakin Get suka tarar da jama'a suna alwala, da gudu ta shiga gidan parlo ta tarar da. Mommy sanye da hijab duk fuskarta ta kumbure saboda kuka,
rungumeta Mommy tayi, suka fashe da kuka, Mommy ta ce "saboda rashinki Mahaifinki ya zauce gaba ɗaya ya fita hayyacinsa shine mota ta kaɗe sa Allah ya karɓe abinsa." Girgiza kai Zuhura ta shiga yi tana wani iri. Kuka haka aka fito da gawarsa waje sallah akayi mai kana suka wuce maƙabarta,
Da yamma bayan jama'a sun rage Zuhura taja Mommy bedroom take sanar da ita duk abinda ya faru har labarin da Abbeey ya bata, Mommy ta ce "duk da ina zarginsa amma ban taɓa tunanin sonda yake miki zai bar Zuciyarsa ta cutar dake ba, ai kuwa dai yaga sakayya saboda Motar data kaɗesa saida kansa ya cire,
jama'an tsaro sun tafi da Alhaji ILIYA, ashe wannan ne dalili, to Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu." Zuhura ta ce "Amin Mommy." Washegari Umman Abbeey da Pinky sunzo gidan wurin ta'aziya, sai yamma suka tafi a nan aka bar pinky saboda har kwanciya tayi ƙasa tana birgima anan zata zauna bazata bisu ba,
dole suka barta akan direba zaizo ya kawo kayanta na makaranta, bayan addu'ar uku Abbeey yazo don tafiya da Pinky, da ƙyar ta yarda ya tafi da ita, bayan wata uku da shaƙuwa ta ƙara shiga tsakanin Pinky da Zuhura Abbeey ya ɗan saki jiki da ita idan ya kawo pinky yana ɗan tsayawa su hira,
nan fa Abbansa ya tasa shi gaba akan neman Auren Zuhura, da ƙyar ya yi ma Zuhura magana yana son ya aureta, batayi musu ba aka tsaida lokacin aure wata biyu, nan fa Mommy ta kira ƙawarta ƴar Maiduguri tazo aka fara gyaran Zuhura ciki da waje, koda akayi sati ɗaya idan kaga Zuhura bazaka ganeta ba,
India ɓangaren Arman da Sarki Raka
Arman ya samu nasarar yankan sarki Raka a gadon bayansa Anaya kuwa a kafaɗa ta yanke sa, masifa ta kai masifa Anaya da Amrita sun koma gefe suna kallon yadda Arman ke gabzar Sarki Raka, wannan karon falfalowa sukayi da guda cikin mugun nufi aikuwa Arman charaf ya sarewa Sarki Raka kai,
sai ganin gangar jikinsa akayi ƙasa, wani fito Amrita tayi ita Anaya Wannan bawan Allah kuwa sujada ya yiwa Allah kana ya rungume Arman, nan fa gari ya ɗauka Arman ya kawo ƙarshen Sarki Raka, jama'ar gari kowa ta cika da murna, bayan sati ɗaya aka fara ginin sabuwar masarauta ta zamani,
koda akwayi wata biyu an kammala an gyra gari komai ya dawo yadda akeso, kana aka fara hidimar naɗin Sarki Arman, lokacin Kakansa ya dawo aka sha shagali na ban mamaki, sarakunan ƙasashen duniya babu wanda bai hallaci wannan biki ba, anyi komai lafiya
lokacin cikin Anaya ya girma, sosai ta ƙara wani kyau soyayya kawai suke zubawa ita da Arman akwana a tashi ba wuya a wurin Allah cikin Anaya ya shiga watan haihuwa ta santalo ƙatun ɗanta Namiji mai kama da Arman, ranar suna aka sakawa yaron Muhammad suna kiransa da Arif,
haka suka ci-gaba da gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali, jama'a na farin ciki da zaman Arman matsayin Sarki Anaya Gimbiya ga Yarima Arif, ya yi wayo sosai ga wasu abubuwan ban al'ajabi a tare da shi,
Gida Najeriya ɓangare su Zuhura,
ranar shagalin buki yazo an ɗaura auren Zuhura da Muhammad Abbeey, akan sadaki miliyan biyar, anci an sha anyi walima ta gani ta faɗa, idan ku kaga Zuhura zaku ɗauka balarabiya ce akan tsabar gyaran jikin da ta sha, bayan sallar isha'i aka ɗauki Amarya zuwa gidan Mijinta Abbeey,
ranar bai ɗagawa Zuhura ƙafa ba saida ya lallasa kayansa yadda yake so kunsan anjima ba haɗu da kayan marmari ba, ranar Zuhura ta gane Allah ɗaya ne, bayan wata uku ta fara laulayin ciki ya ɗauke abarsa suka wuce London wurin rainon ciki aka bar pinky wurin Umma,
chan Zuhura ta haihu, ta samu ƴan biyu mace da Namiji kana suka dawo gida aka sha shagalin suna yarinyar taci suna Nana Khadijah, Namijin kuma Abdullahi suna kiransa da Abulkhairy
Story and Writer Bey Zainab Abdullah Usman Ubandoma Elharm PINKY DARLING MRS JAY
Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!
anan na kawo ƙarshen wannan Liltafi mai Suna Muguwar fatalwa, fatan kun ilmantu kun waza'ntu da wannan labari kuma ya baku nishaɗi fatan zaku ɗauke halaye masu kyau ki zubar da na banza Allah ya sa mudace Amin! Abinda nayi kuskure Allah ya yafe muna nida duk wanda ya karanta wannan Liltafi,
Ina mika sakon Godiya ta ga daukacin masoyana a duk inda suke a faɗin duniya, ina godiya sosai da addu'oin ku a gareni Allah ya bar ƙauna Much love All my lovely fans 😍😍😍
Ina yi muka albishir da sabon Liltafin da zan fara sakar muku bayan sallah mai Suna
1 MIJIN KARUWA
2 BA ƊAYA BANE
3 SARKI NE SHI
4 BARIKI DA KUD'I
5 SA'ADATU
6 NAYHA
Waɗannan Liltafai zasu baku citta kai har sa sugar duk wanda ke karanta Liltafi na ya san waɗannan Books zasu tashe kanku,
Bey.................
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels