Share this page
2 / 8
ya gaya miki." Zuhura tace "Wallahi Mommy tun bayan tafiyarmu Pakistan, na fara ganin wasu abubuwa masu masifar ban tsoro da firgici." nan ta kwashe komai ta gayama Mommy tas tas kakeji Mommy ta wanke Zuhura da mari, kana tace "Wallahi keyi asara Zuhura duk wannan abin da ya faru, laifin waye idan ba naki, gashi da kanki ke faɗa, ba kya karatun Alkur'ani, ba kya kunnawa ki saurara idan bazaki iya karatu ba, sallah sai kega dama kike yinta baki da aiki sai kallon horor Film da sauraren waƙoƙin banza ai dole kiga abinda yafi Fatalwa, kuma ta tsorata ki, Allah keci amanar Arman don haka ba ruwana kijira Abbanki ya dawo shi zakiyi ma wannan bayani, dama shi ya lalata ki yanzu sai ji illar gatan da ya yi miki." Mommy na gama faɗar haka, ta haura sama ta shige bedroom ɗinta, Zuhura kuwa sai yanzu wata nadama marr amfani ta ziyarce ta, tabbas gaskiya Mommy ta faɗa, yanzu ina zata samu miji ko wanda bai kai Arman ba, tayi sake wannan Muguwar Fatalwa ta cuceta, gajiya tayi da zama parlon ta nufi bedroom ɗinta yana nan kamar yadda yake, da gani kullum sai an gyara sa, wanka tayi, kana ta kwanta tana jiran dowawar Abbanta, Pakistan bangaren Arman! Company ya wuce saboda yana da mitin da wasu ƴan Chaina, bayan sun kammala ya wuce wurin hutawa, bakin ruwa ya zauna, yana tunanin Zuhura lokacin da suka zo wurin, suna wasa tana watsa mai ruwa, har ya goyata, suka rinƙa zagaye bakin Tekun, jin ya yi an dafa kafaɗarsa, "Arman tunani ba naka bane neman wannan yarinya shin yafi dacewa da kai Zuhura ta fita rayuwarka har abada ba zaku sake ganin juna ba ita tamkar iskan gaguwa ce duk abinda ta ɗauka bazata mayar da shi ba, to kamar haka ne ya faru tsakaninku da ita, haɗuwarka da ita rubutacciyar ƙaddara ce." Shiru yaji maganar ta tsaya waigawa ya yi amma ba kowa, ta shi ya yi zuwa gidansa, saboda ya gaji gaba ɗaya wurin beyi mai daɗi ba, yana kan hanya, ne sam bai kula da matashiyar dake ɗaga mai hannu ba alamar ya dakata zata tsallaka titi karaf kakeji ya kaɗeta ba shiri ya fito cikin motar kwance ya ganta gashin kanta duk ya rufe mata fuska, hannu ya kai zai ɗauke ta zuwa hospital, zobon hannunsa ne ya yi wani haske, yana wani kyalli, jikinsa ya fara karkarwa, jiri na fisgarsa, ja ya yi da baya, ya jin gina jikinsa motarsa, ya jima haka kafin ya dena jin komai, ya ɗauke matshiyar budurwar ya saka ta mota kana ya nufe hanyar hospital wata zuciyar tace"Karka manta kaima Dr ne kaje da ita gidanka ka duba ta, da wannan shawara ya juya motarsa zuwa gidansa, yana isa ya ɗauko ta zuwa parlo yana sauketa kan kujera, tana buɗe idanunta, da sauri ta zabura ya riƙe ta, yana faɗin "Ki natsu ke samu rauni a ƙafa nine na kaɗe ki da Mota Please kiyi haƙuri idan na duba ki zan mai daki gida...sauran maganar ce ta maƙale mai, ganin kyakkyawar fuskar yarinayr itace wadda yake mafalki tare da ita! Itama kallonsa takeyi kamar tasan wannan fuskar amma a ina ta santa, kanta ne ya shiga juyawa ta rufe idanunta tare da kwantawa kan kujera, Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY more comment More typing please share fisabilillah https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD 🌍 Not Editing ❎ 💀 *FATALWA* ☠️ (Horror💀story) love and romantic, story 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _______________________________________ *DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️* (*we stand together*) 🤝🤝🤝 Bismillah Rahamanin Raheem💫 🆓 BOOK PAGE 6️⃣ Gaba ɗaya jikinsa ne ya yi sanyi ya shiga tunanin itama yarinyar tana ganinsa a famalki, idan har tana ganinsa shikenan girmansa ya zube saboda har kuka yakeyi mata idan tana romantic ɗinsa, tanayi mai shorking, Dick, motsinta ne ya dawo da shi, daga tunanin da ya shiga, a hannu ta samu rauni ya wanke wurin kana ya ɗora hannunsa dake sanye da wannan zoben, wani shorking ne yaji, sai da ya rufe idanunsa, yana buɗewa, yaga raunin dake hannunta ya ɓata gaba ɗaya shiru ya yi, wannan murya yaji tana faɗar"Kada kayi mamaki Sarkin sarakai, Sarkin Mutane da aljanu, wannan kaɗan daga cikin sirri da baiwar dake tattare da kai ne, wannan yarinya, ka karɓeta hannu biyu itace Ayanar ka ita tamkar inuwarka ce." Shiru yaji, tashi ya yi kana ya mayar da akwatin kayan magani, ya shige bedroom ɗinsa ya yi wanka ya shirya cikin kayan hutawa, parlo ya dawo, har zuwa lokacin yarinyar na kwance ga alama bacci takeyi, Tv ya kunna yana kallon ball, ƙarar Tv ce ta tayar da yarinyar kallon Arman takeyi, kafin ta Ƙawar da kanta saboda taga alamar zai juyo, kada ya kamata tana kallonsa, Arman kuwa sarai ya san kallonsa takeyi sai da ya ɗauke mintuna goma kafin yace" Ya jikin zan iya maida ki gida.?" Shiru tayi idanunta na cikowa da kwallah, jin shiru ya ɗago fuskarsa yana kallonta da narkakkun idanunsa, yace "kejifa abinda na faɗa." Cikin muryarta mai sanyi, tace " Naji mutafi." Tashi ya yi zuwa bedroom ya sauya kayan jikinsa, kana ya fito, yana gaba tana bayansa har suka paroln, harabar inda yake ajiye motoci ya nufa wata ƙaramar mota ya buɗe fara, mai baƙin gilashi, itama ta zagaya ta shiga gaban motar, Get Man ya wangele mai, get suka fita, sai da suka bar layin Unguwar yace "Bani address." Tace "Duk inda ka samu ka sauke ni kawai." bai ce mata komai ba ya cigaba da tuƙi sai da ya isa hanyar da ya kaɗeta kana ya tsaya, yana buɗe gaban murfin motar ya ciro mata rafar kuɗi, yace "Ga wannan." Yana ɗora mata a hannu, batace mai komai ba ta buɗe motar ta fita kana ta ajiye mai kuɗinsa, tace "Bana buƙata na gode." Ta juya ta bar wurin, tafiya takeyi batasan inda ta dosa ba, sai ga wasu ƴan iska sun tare mata hanya, suka zageye ta gaba ɗaya Arman kuwa juya motarsa ya yi kawai ya bar gurin, mazan da suka zagayeta kuwa, ɗaya daga cikin su yace "Ke ina kika fito ina zakije.?" Tace "Miye dumuwarku da inda zanje bazan faɗa ba." Ɗayan yace "Kaga Ashfa muyi mata fyaɗe kawai, mu ƙara gaba, miye matsalar mu da inda zataje." Sauran suka ce "Haka ne fa Nikil muyi mata Fyaɗe kawai, waye zai fara cikin mu uku." Ashfa yace "Nikil zai fara fasa muna ita, ni zanyi zagaye na biyu, kai kuma Kasim, kayi na ƙarshe." Ƙasim yace "Ba laifi na jima inason lasar zumarki Anaya amma yanzu na samu bagas." Shiru tayi tana kallonsa, har Nikil ya soma matasawa inda take, ya zura hannunsa ya janyo ta, nanfa suka soma kokowar cire mata kaya, amma ta hana sai zabga mata mari yakeyi,Ashfa ne yace "Riƙeta kawai bari na cire mata kaya karta ɓata muna lokaci." Hannu ya ɗora ya fara ƙoƙarin janye mata riga, saukar duka kawai yaji a gadon bayansa, sai da ya saki wani ihun azaba, yana waigawa don ganin wanda ya yi masa wannan mugun duka naushi ɗaya amma kamar an karya mai gadon bayansa baya tunanin zai iya tashi tsaye dai-dai ba kowa bane fa ce Arman lokacin da ya bar gurin haka kawai ƙirjinsa ke bugawa, ya ji gaba ɗaya, bai yarda da tafiya ya barta a gurin ba gashi dareni komai zai iya faruwa da ita, dole ya juyo kan motarsa ya dawo, shine ya ganta cikin wannan halin, zuciyarsa har ta farfasa takeyi, launin idanunsa har ya sauya zuwa red color Nikil dake riƙe da ita, Arman ya janyo tare da karya hannun, sai ƙarar karyewar ƙasusuwan hannunsa ka ke ji! wani wawan naushi ya kaiwa Kasim a gefen wuya sai jini kawai ya faru zubo mai ta hanci da baki, gaba ɗaya saida Arman ya karya musu ƙasusuwan jiki, ya naka sa su, Anaya kuwa zubewa tayi ƙasa saboda jirin da ya ɗebeta, kamar jaririya haka Arman ya ɗauke ta cikin Motarsa ya saka kana ya shiga mazaunin Direba ya ja motar gidansa ya wuce da ita, bedroom ɗin Zuhura ta kaita ya shiga bathroom ya haɗa mata ruwan zafi ta shiga tayi wanka, wadroub ɗin Zuhura ya duba yasan bazata iya kwashe kayanta gaba ɗaya ba, ai kuwa ya yi sa'a akwai sauran kayanta a ciki sunfi kala hamsin, wata rigar bacci ya ɗauko mata mai dogon hannu, da pant, kana ya fita ɗakin kitchen ya shiga indomi ya dafa mata da kwai, sai ruwan tea masu kauri, kana ya fito, bedroom ɗin ya koma lokacin har ta fito, tana gaban mirror tana shafa mai, face ɗinta duk ta kumbura, idanunsa ne suka sauka akan ƙirjinta, da tawol ya zame suka fito kaɗan masu kyau da ɗaukar idanu, gaba ɗaya bearst ɗinta ya tafi da shi, ita kuwa Anaya bata kula ba lokacin ta gama shafa mai ta bar gaban mirror, dole ya ɗauke idanunsa kar ta gane abinda yake kallo, ajiye mata pilet ɗin ya yi cup ɗin tea ya juya zai fita, tace "Thank you." "Uhm." Kawai yace kana ya fita, zuwa bedroom ɗinsa da ke gefen nata, wanka ya yi kana ya saka kayan bacci, ya kwanta, idanunsa na hasko mai bearst ɗinta, da ya gani, Dick ɗinsa yaji tana motsi alamar tana buƙatar, wurin sauke nauyi, juwa kwanciyarsa ya yi, yana rufe idanunsa, Anaya kuwa bata saka rigar baccin ba wadroub ta buɗe ta ɗauko wata red ɗin riga iya cinyarta rigar ta tsaya shara-shara rigar take, ana ganin komai dake jikinta, indomi ta fara ci ta sha tea, kana ta wanke bakinta ta fashe jikinta da turaruka, kana ta ɗauke pilet ɗin da cup ta fito tana waige-waige inda zata hango kitchen, parlon ƙasa ta sauka ta fara dubawa a nan ta samu kitchen ta ajiye kayan kana ta fito, ji tayi kamar ana bibiyarta a idan ta waiga bata ganin kowa sai da ta kusa hawa bene taji an dafa kafaɗarta juyowar da zatayi, hannu kawai ta gani ba saurayn gangar jiki, wani ihu ta saka, tare da faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ya Allah na shiga ukuna FATALWA!." Arman kuwa yana jin ihunta ya fito da sauri, gaba ɗaya Anaya ta gama firgita, Arman kuwa yana fitowa wannan hannun ya ɓace, Anaya kuwa batasan lokacin da ta shige jikinsa ba, tana maƙalesa, sam taƙi yarda ya cireta jikinsa, haka suka haura sama, bedroom ɗinta ya nufa zai ajiyeta ai kuwa tace batasan zancen ba, ta tsorata sosai dole bedroom ɗinsa ya tafi da ita suka kwanta, gaba ɗaya ta hanawa Arman saƙat duk ta shige mai cikin jiki, kamar zata haɗiye sa, shi kaɗai yasan yanayin da ta saka shi, da ƙyar ta bari ya rage hasken ɗakin, ta rungumesa sosai dole Arman ya saka hannu ya rungumeta, hakan ya saka su cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa, wani lumfashi Arman ke sauke dick ɗinsa sai huci takeyi, tana neman hanayr shiga, Anaya kuwa haka kawai ta samu kanta da sha gashin ƙirjinsa da ya kwanta luf, da shi gwanin burgewa, haka take yawo da hannunta kan ƙirjinsa har zuwa kan nonosa, wani irin shorking Arman keji yana fisgarsa kasa riƙe kansa ya yi, ya damuƙo bearst ɗinta, ya fara wasa dasu cikin salo mai rikitarwa, bakinsa ya kafa kan ɗaya ya fara sha, Anaya kuwa gaba ɗaya ta ɗauke wuta, shafa jikinsa takeyi ta ko ina batare da tasan me takeyi ba, batsan lokacin da hannunta ya sauka akan dick ɗinsa ba, ta fara shafata har zuwa ƙasar sa, romantic ɗin juna sukayi Sosai har suka samu natsuwa, batare da sex ya shiga tsakaninsu ba, wani bacci mai daɗi ya yi awon gaba dasu, Writer Bey PINKY DARLING MRS more comment more typing please share fisabilillah my dear friends 😍🙏 💀 *FATALWA* ☠️ *Love and romantic* 💋 *Story and Writer Bey* *PINKY DARLING MRS JAY* 🌼🌺🌼🌺🌼🌺🌼🌺🌼🌺 Masu neman fatalwa daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran liltafai https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e Following this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD🌍 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _______________________________________ *DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️* (*we stand together*) 🤝🤝🤝 Bismillah Rahamanin Raheem💫 🆓 BOOK PAGE *PAGE* 7️⃣▶️8️⃣ Kiran sallar asuba ne ya tayar da Arman ya janye ta cikin jikinsa kana ya shiga bathroom, ya yi wanka kana ya fita Masallaci, Anaya kuwa kunya ce ta hana ta tashi sai da ta tabbatar ya fita kana ta shiga wanka tayi sallah,abinda ya faru daren jiya na dawo mata, ta lula duniyar tunani, har Arman ya dawo, masjid, ya shigo bedroom, bata jishi ba, kwanciya ya yi kan bed yana jan bargo, ya rufe jikinsa, saboda bacci yake ji sosai,tarin da ya yi ne ya ankarar da ita, ta dawo cikin hayyacinta, Arman kuwa bacci ya yi awon gaba da shi, Anaya kuwa komawa tayi, bedroom ɗinta, wata dogowar riga ta saka blue kana ta fito Kitchen, doya ta soma ferewa kana ta kunna gas ta fara tafasa doyar ta kaɗa kwai sauran kayan buƙata, ta soma soya doyar bayan ta Kammala, ta ɗora ruwan tea ta cika filas ferfeson naman kaza tayi yaji kayan yaji kana ta ɗora komai kan teburin cin abinci, ta koma kitchen ta gyra komai, Kamar batayi aiki a ciki ba, paroln ta soma gyarawa, duk da bashi da wani datti, kana ta feshe sa da turarakan gida, lokacin ƙarfe 11:00 na safe, bedroom ɗinsa ta koma ya shiga bathroom wurin wanka gyra gadon tayi tare da sauya bedsheet, ta gyra komai ya fito net, sai ƙamshi bedroom ɗin keyi, jin alamar zai fito wanka da sauri ta fita, ta shige bedroom ɗinta, wanka tayi kana ta shirya cikin dogowar rigar abaya Black corlo, anyi mata ado da folawowi masu kyau, ta fito paroln ƙasa, ta kunna Tv tana kallo sai ga Arman ya sauko ƙasa, wani fitinannen ƙamshi ne ke tashi a jikinsa, ya yi masifar kyau, sanye yake cikin sut blue, da takamli sawu ciki Black, sai agogon diamond dake ɗaure a tsintsinyar hannunsa, sajen fuskarsa ya kwanta sosai sai kyalli yakeyi, ga farin gilas ne manne a face ɗinsa, sumar kansa ta sha gyra, kamar jarumin Filim ɗin India Ram Charam, Anaya kuwa baki da hanci ta saki wurin kallonsa wannan kyau haka kamar wani ɗan Aljanu ba mutum ba, ɓangaren Arman kuwa tas ya ƙarewa Anaya kallo kyakkyawa ce ajin farko, saboda duk kyaun Zuhura bata kama ƙafar Anaya ba, kwayar idonta iri ɗaya da nasa blue corlo, sai ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke pink lips, ga dogon hancinta, sumar kanta har ta kusa haɗewa girarta, bata da jiki sosai amma baza'a kirta siririya ba, ta ko ina Anaya ta haɗu, har yanayi sukeyi da Arman shi lips ɗinsa red color, ne, hanyar fita ya nufa Anaya tace "Barka da safiya Yallaɓai." "Barka." Tace "Amm ga break fast na haɗa." Kamar zai tafi sai ya dawo wurin cin abinci ya nufa, tabi bayansa, da ganta ta zuba mai komai ta haɗa mai tea,ta koma gefe ta zauna sai da ya kammala a ransa yake yaba girkin ba laifi komai ya yi, tashi ya yi kana yace "Zan fita akwai abinda kike buƙata.?" Tace "A'a adawo lafiya Allah ya tsare." Ya fita, kana ta zauna tayi break, ta kwashe kayan ta wanke tas, kana ta zauna parlo tana tunanin wannan rayuwa data shiga yanzu, kamar a mafalki, Gida Najeriya ɓangare Zuhura kuwa Daddynta ya dawo, Mommy take sanar da shi, Zuhura ta dawo fa shine yace ta kirata, jikinta a mace ta fito paroln, "Daddy barka da dare." "Yauwa Mamana barka ya kike.?" "Alhamdulillah." Ta bashi amsa kana yace "Mommy ki ta sanar dani ke dawo hope dai lafiya.?" sunkuyar da kai tayi, batace komai ba, Daddy yace"Haba Mamana kiyimin magana ki gayamin abinda ya faru." Mommy tace "Ai bazata faɗa marar kunya, rashin hankali da hauka tayiwa mijinta tsaresa tayi sai da ya saketa har saki uku fa, ta kwaso kaya ta dawo to wallahi bazan zauna da ita ba aure kawai zakayi mata, haka kawai ta zauna min a gida kamar wata kishiyata, ko da yake ai duk abinda ya faru laifinka ne kaine ka lalata Zuhura wallahi duk abinda tayi baka bari a tsawatar mata sai......"Dakata Bilkisu, ya isa haka aure dai ya riga ya mutu Shikenan ai babu dole sai ta zauna da shi, idan ta samu wani mijin sai tayi aure idan kuma bata son auren gaba ɗaya, shikenan." Daddy ya faɗa yana janyo Zuhura jikinsa kamar yarinya ƙarama, Mommy kuwa ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci, tashi tayi kawai ta bar parlon, saboda taikaci, saboda ita yanzu zargin Daddy takeyi, da farko lokacin da Zuhura ta kawo Arman a gidan ya yarda zai aura mata shi daga baya ya sauya, babu kalar abtarwa da bai saka akayiwa Arman ba da ƙyar ya tsira amma yace shi sam bai saka kowa ya kama Arman ba, yanzu kuma ta kula da wani farin ciki data hango cikin ƙwayar idanunsa, tabbas akwai abinda yake ɓoyewa, amma komai nesan jifa ƙasa zai dawo, Daddy kuwa lallaɓa Zuhura ya yi har ta saki jiki kana ya shige ɗakinsa, ƙarfe biyu na dare ya shirya cikin wata dogowar riga baƙa har ƙasa da jar hula, sai wata sanda kana ya buga sandar a ƙasa sau uku sai gashi ya bayyana cikin wani ƙaton daji tafiya ya soma yi sai da ya kai tsakiyar dajin kana ya koma buga sandar sau uku, yana karanta wasu kalmomi kamar na tsafi sai ƙasa ta fara jijjiga, guguwa mai ƙarfi ta cika dajin sai wani ihu da gurnani ke tashi mara daɗin saurare, wani ƙaton gidane ya bayyana, ƙofofin shinga ciki duk wuta ce keci ko wane gefe sama da ƙasa, haka ya ratsa babbar hanya ya shiga ciki, wasu mutane ne sunfi ɗari cikin irin shigarsa, sunbi layi, suna kallon shugaban su, dake zaune kan wata kujera kai da ganinta kasan ta tsafi ce, ga wata ƙatuwar tunkuya kan wuta sai tiriri take fitarwa, da wani ƙamshi marar daɗi, bayan Daddyn Zuhura ya shiga layi shugabansu yace "HARUNA kai muke jira idan ka yarda ka sake makara zuwa mitin, saina kawar da Matarka! na mayar da kai baya saboda haka fito layin baya ka dawo gaba ka faɗa min sakamakon gwajin da na saka ka." Daddyn Zuhura ne ya fito, layin baya ya dawo gaba kana ya sunkuyar da kansa yace "Tuba nikeyi shugabana, wannan ƴar tawa ce ta dawo gida gwajin da ka bani ya yi aiki sosai, saboda nayi aiki da Muguwar fatalwa dake bibiyar Arman na raba aurensu, da Zuhura yanzu umurnin ka kawai nike jira na aiwatar da sauran aiki." Shugaban yace "Shi yasa dodon kuɗi ke sonka saboda baka wasa da duk abinda aka umurce ka, komai wahalarsa zaka aikata, shi, amma fa akwai matsala saboda Matarka ta fara zarginka, dole sai ka kiyaye wasu abubuwa, ka dena nuna mata abinda takeyiwa Gimbiya ba dai-dai bane idan ba haka komai zai iya faruwa, dodon kuɗi yace na sanar da kai ka ƙara bawa Gimbiya kulawa, karka yarda wani ɗa namiji ya koma kusantar mai mata har zuwa lokacin da zai karɓe ta, sai abu na uku an baka baban matsayi a wannan ƙungiya daga yau kaine zaka rinƙa sanar da kowa lokacin mitin da sauran abubuwan ƙungiya saboda haka zan ƙara ma ƙarin tsafi kaje ka ɗibo naman dake dahuwa a cikin waccen tukunyar ka ci." Godiya ya yi sosai kana ya ɗebo naman ya fara ci, bayan ya kammala, aka sauya mai riga zuwa red color da Black ɗin hulu, sai sanda ɓaka mai kan Maciji, haka sauran mutane suka rinƙa zuwa suna aikata abinda aka umurce su wasu sabbin members na ƙungiyar sun kawo abinda aka saka su wani Matarsa wani ubansa wani ƙanwarsa wani Mahaifiyarsa, wani ɗansa ko ƴarsa wurin neman abin duniya, Allah ka tsare muna zukatan mu da aikata aikin dana sani wanda bashida amfani, Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY more comment more typing please share fisabilillah my dear friends 😍🙏 💀 * FATALWA* ☠️ *Love and romantic* 💋 *Story and Writer Bey* *PINKY DARLING MRS JAY* 🌼🌺🌼🌺🌼🌺🌼🌺🌼 Masu neman fatalwa daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran liltafai https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e Following this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD🌍 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 https://chat.whatsapp.com/Gp8lr2dVNhGKHPQjWl4BRP Comments section group 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _______________________________________ *DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️* (*we stand together*) 🤝🤝🤝 Bismillah Rahamanin Raheem💫 🆓 BOOK PAGE 9️⃣▶️1️⃣0️⃣ Anaya kuwa ƙarfe biyu ta shiga kitchen ta haɗa musu abinci, tayi wanka tana gaban mirror tana shafa mai, ta hango kan mutum amma ba sauran jikinsa waiga tayi amma bataga komai, ta cigaba da shafa mai, hannu ta saka zata ɗauko cum ta taje gashin kanta, akayi wuff aka ɗauka shi, ya yi sama ya na lilo kamar zai faɗo, shiru Anaya tayi tana kallon ikon Allah, tashi tayi zuwa gurin wadroub, zata ɗauke kaya, idan ta buɗe sai a rufe kusan sau uku ana yi mata haka , ranta ne ya ɓaci ta buɗe tafin hannuwanta tana nuna wadroub ɗin sai gashi ta buɗe bata koma rufewa ba riga da wando ta fitar zata saka, ta ajiyesu kan bed, ta juya zuwan gaban mirror, ai kuwa sai ga kayan sun biyota, a baya tana tafiya suna biyarta, idan ta juya kayan su koma kan bed, dariya abin ya bata, taje gashin kanta ta somayi, charaf aka karɓe matajen gashin waigar da zatayi ne idanunta suka sauka kan wata mummunar hallilta, mai ban firgici, ta tsorota amma sai ta ɓoye tsoronta, saboda ta fahimci FATALWA ce haɗe fuska tayi cikin jarumta tace "Kega wai me nayi miki ne na kula tun lokacin da nazo gidan nan kike bibiyata, na cutar dake ne ko na cutar da wani ɗan uwanki." Anaya ta faɗa tana kallon Fatalwar, cikin murya mai amon sauti tace "Ko ɗaya amma inaso ki tattara ki bar gidan nan saboda gidan Mijina ne ni kaɗai idan ba haka ba, zan illatar dake." Wani kallon sama da ƙasa Anaya tayi mata kana tace "Uhmm ai nida wannan gidan mutu karraba takalmin kaza, idan kega na fita wannan gida to unguwa zanje ko yawon shaƙatawa!." Fatalwar kuwa da jin haka tayi wata girgiza, hallintar jikinta na sauyawa, tayi kan Anaya zata soka mata wani tsinke dake hannunta da sauri Anaya ta guce, nan fa suka soma rigima ta fara jifar Anaya da miyagun tsafi da wasu abubuwa, Anaya na mayar mata duk sun hargitse bedroom ɗin, rigima ta zama babba har suka fito paroln ƙasa, idan ta jefe Anaya da wuta ita kuma Anaya ta jefeta da ƙanƙara, take wutar zata mutu, suna wannan rigimar ne saiga Arman ya dawo, lokacin Fatalwar ta samu damar kai Anaya jikin ginin parlon, tana ƙoƙarin, soka mata, wannan tsinken a wuya da sauri Arman ya miƙa hannunsa sama wani ɗan ƙaramin ice ne yazo cikin tafin hannunsa ya nuna Anaya da shi, ta koma gefe kana ya mayar da wannan icen kan fatalwar, ihu ta soma yi tana faɗin"Haba Masoyina Arman meyasa kakeyi min haka ne? yacce naci galaba akan Zuhura itama wannan saina ci galaba akanta." Tana gama faɗar haka ta ɓace a paroln, ajiyar zuciya Arman ya sauke yana kallon Anaya yadda duk gashin kanta ya hargitse, duk ta jigata, wannan icen ya nuna kan jikinta take sumar kanta ta dawo gwanin burgewa, Anaya kuwa kallonsa kawai takeyi gaba ɗaya ya tafi da ita, icen ne ya sauka kan tawol ɗin dake ɗaure jikinta zai zame ƙasa da sauri ta riƙesa, tana zare idanu, Arman kuwa kawar da kansa ya yi, yana sane ya yi mata haka saboda ta tsaresa da kallo, juyawa ya yi da wannan icen ya soma gyaran paroln komai ya dawo yadda yake, Anaya ta tsaye tana kallonsa har ya kammala kana ya haura sama da sauri tabi bayansa, ta sha gabansa tana faɗin "Please muje ka gyra min ɗakina duk ya hargitse." Wani kallo ya yi mata kana yace "Bazanyi ba." Ya shige bedroom ɗinsa, ya barta nan tsaye, a fili tace "Wannan akawai taurin kai za'a sha wahalar zama da shi." Ta shige bedroom ɗinta zata gyara abin mamaki koda ta shiga komai ya koma yacce yake kaya ta saka kana ta fito, bedroom ɗinsa ta shiga

Chapter 2 of 8