Share this page
7 / 8
haka Arman ya tunkaro wannan Masarautar, kasan waye Mahaufinsa waye Kakansa, suna da alaƙa mai ƙarfi da Aljanu, saboda kakar Arman wacce ta haife Ubansa Aljana, ce, A halin yanzu Arman ya kasance ruwa biyu ne, shi, shi ba mutum ba shi ba aljan ba, yana samu matuƙar ƙarfin iko irin na Sarkin Aljanu, shi ya sa cikin jikinta ya kasance mai matuƙar ƙarfin gaske, yanzu abu ɗaya ya rage ma, wanda zaka gama da su shine ka yanka, kan Ɗanka, ka shinye wannan jini, ka wanke fuskarka da shi, idan kayi haka ko aljani bazai iya karawa da kai ba." Sarki Raka ya ce "Ba ɗana ba kowa zan iya kashewa in dai zan tabbata akan wannan kujerar mulikin." Ya fashe da wata mahaukaciyar dariya dai dai lokacin, Arman ya bayyana, wurin da aka ɗaure Anaya kwance mata sarƙoƙin ya yi, kana ya bata wasu ruwa cikin wata kalba, ta shanye tas, waziri ne ya ahamo da zuwan Arman gashi an fito da Amrita, da siffar Arman, dai dai lokacin sandar dake hannun Boka ta kama da wuta, nan fa wata guguwa ta taso daga sama wani baƙin hadari ya kama, kamar ruwan sama zasu sauko, To ka ya zata kaya tsakanin Sarki Raka da Arman ? Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY kuyi haƙuri da rashin Update kwana biyu bana jin ƙarfin jikina wallahi kuyi haƙuri da wannan 😩 💀 *FATALWA* ☠️ *Love and romantic* 💋 *Story and Writer Bey* *PINKY DARLING MRS JAY* Masu neman fatalwa daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran liltafai https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e Following this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD🌍 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _______________________________________ *DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️* (*we stand together*) 🤝🤝🤝 Bismillah Rahamanin Raheem💫 🆓 BOOK PAGE3️⃣7️⃣▶️3️⃣8️⃣ Amrita na tozali da Arman tayi wata irin girgiza, kawai ta ɓace sai barin dakarun tayi riƙe da sarƙar da suka ɗaureta, nan masarautar ta fara girgiza kamar ginin zai rushe, ɗaya daga cikin kuyangen da ke yiwa Matar Sarki hidima, ta bar filin masarauta da gudu ta shiga ciki, part ɗin Sarauniya ta shiga a bakin ƙofa suka ci karo, wannan lokaci ko durƙusawa batayi ba ta ce "Ranki ya daɗe, kiyi gaugswar ɓoye Yarima Charam, domin Boka ya baiwa Sarki izanin yanka kan Yarima saboda ya samu ƙarfin yaƙar su Arman, saboda haka yanzu zaɓi ya rage naki." Sarauniya kuwa ƙitjinta ne ya yi dukan uku uku, girgiza kai tayi bakinta na rawa ta ce "Ina hakan bazai taɓa yuwa ba, ɗan nawa guda ɗaya dana mallka, nafison sa fiye da komai." Ta juya da sauri ta shiga part ɗin Yarima ya na gaban mirror ya na fesa turare saboda fita kallon gwabzar da za'ayi da su Arman, ganin Mahaifiyarsa ta shigo, hankali a tashe ya ce "Mom lafiya meke faruwa ne.?" Cikin da firgici ta ce "Charam ma za ka bi hanyar baya ka fita cikin garin nan gaba ɗaya, saboda Boka ya gayawa Sarki ya zo ya yanka kanka ya sha jinin idan har ya yi haka to zai samu nasara akansu Arman, kuma ya amince zai kwar da kai, akan mulki, saboda haka kayi saurin barin cikin Masarauta, zan sanar da Sarki, Rusman, ya turo manyan dakarunsa su tafi da kai chan masarauta nima zan biyoka daga baya." "Mom yanzu "Daddy ya amince zai kasheni akan mulki kema bazai barki ba kizo kawai mu gudu." Ya ja hannun Sarauniya, suka bi wata ƙofa, suka fita, kai tsaye bayan Masarauta ƙofar ta fito da su, suka nausa cikin daji, fitarsu keda wuya Sarki Raka ya shigo part ɗin Yarima amma bai gansa, fita ya yi zuwa part ɗin Sarauniya, nan ma shiru har ita bata nan masu gidan part ɗinta ne ya tambaya, ko sunga fitarta, ɗaya daga cikin su ya ce "Sunga lokacin da ta shiga part ɗin Yarima, amma basu ga dawowarta ba, nan fa Sarki ta fahimci ta samu labarin abinda ke shirin faruwa shine ta gudu ita da yaronta, a fusace ya fito, tare da ba dakarunsa dama su fita a nemo mai Sarauniya da Yarima duk inda suke, Arman kuwa yaƙi ne ya kacame tsakaninsa da dakarun Sarki, saiga Amrita ta bayyana ita da wasu dakarun Aljanu, cikin shigar yaƙ iya shigar da sukayi kaɗai ta isa firgita Mutane, nan fa yaƙi ya dawo sabo Boka ya ce ma Sarki babu makawa sai ya shiga wannan yaƙin zai yi galaba akansu Arman, ya sadaukar da sandarsa, a madaɗin kan Yarima Charam, aikuwa nan rigima ta kacame tsakaninsu, duk inda Sarki Raka ya shiga cikin dakarun Aljanu sai dai kaga kanunsu a ƙasa, ɓangaren Arman kuwa kaɗan ya rage ya kawar da dakarun Sarki Raka, duk yawan da suke da shi, Najeriya ɓangaren ZUHURA bayan Zuhura sun koma gida, wanka tayi ta kwanta, ta re da janyo wayarta ta hau WhatsApp Wanda rabun da ta shiga cikin sa tun tana Pakistan, message ta gani da sabuwar number dpn number ta duba nan ta ga hoton pinky ne akai, murmushi tayi tare da duba saƙon voice ne ta kunna muyar Pinky ce, "Aunty barka da yamma ya kike fatan ke koma gida lafiya Abbey ya ce na gaya miki ya na godiya sosai sai na kawo miki ziyara." Murmushi Zuhura ta yi kana ta mayar da martani"Barka dai ma Baby fatan kina lafiya,ki gayamai ba komai, nima na gode zanji daɗi sosai idan kika kawo min ziyara." Kashe datar ta yi saboda kanta ta ji ya na sarawa, kusan kwana uku haka take fama da ciwon kan, idan ta fara jin haka, sai wani bacci ya ɗauke ta, wannan lokacin ma haka ta faru, ba'a yi awa ɗaya ba ta falka a firgice, tayi gumi sharkaf, kamar ba'a cikin sanyi. Ac take ba, dai dai lokacin Hajiya Balkisu ta shigo, ɗakin saboda daga wurin aiki ta fito ta biya ta shagon Zuhura bata nan tana so ta wanke mata kaine, shine ta shigo ta duba ta saboda ƙarfe shida take dawowa shagon amma gashi yanzu akayi sallar la'asar, ganin yanayin da Zuhura take ciki ne ta zauna gefen gadon ta ce "Ke lafiya meke damunki ne.?" Rungumeta Zuhura ta yi kana ta fashe da kuka mai ban tausayi, bata hanata ba, sai da tayi mai isarta kana ta shafa bayanta alamar ya isa haka ta ce "Mommy kwana biyu zuwa uku, kaina ke masifar ciyo idan ya fara ciyo sai bacci ya ɗauke ni, a cikin baccin nike wani mugun mafalki, wani mutum ya ja hannuna da ƙarfe fuskarsa, a rufe muna tafiya cikin wani daji, mai mutuƙar duhu har ya muka isa wurin wani ƙatun gida, wasu mutane ne, sanye da baƙaken kaya, muna shiga aka fara rera min waƙa, wai ni ce amayar dodon kuɗi!." Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY 💀 * FATALWA* ☠️ *Love and romantic* 💋 *Story and Writer Bey* *PINKY DARLING MRS JAY* Masu neman fatalwa daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran liltafai https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e Following this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD🌍 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _______________________________________ *DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️* (*we stand together*) 🤝🤝🤝 Bismillah Rahamanin Raheem💫 🆓 BOOK PAGE 3️⃣9️⃣▶️4️⃣0️⃣ Zuhura ta ƙarasa faɗa tana kallon Mommy, ajiyar zuciya! Mommyn ta sauke kana ta ce "Zuhura ke yanzu kika fara wannan mafalki ni na jima ina yinsa amma tun bayan aurenki da Arman, na dena sai kuma ranar da kika dawo Najeriya, yanzu gashi kema abin ya fara damunki fiye da ni, tabbas akwai matsala akwai abinda ke shirin faruwa, amma in Allah ya yarda babu abinda zai sameki, abinda nikeso da ke, shine ki mayar da hankali sosai wurin ibada saboda ki ƙara samun kusanci da Ubangiji, saboda shi kaɗai ne zai taimakonki akan komai, amma ina so ki kama bakinki duk hirar da zakuyi keda Abbanki, karki yarda ki sanar da shi komai, duk abinda ya faɗa miki ki nuna mai ke ɗauka ke amince zakiyi mai duk abinda yake so, akwai abinda nike bincike, daga baya zan sanar da ke." Ɗaga kai tayi alamar to kana Mommy ta jata zuwa bedroom ɗinta, wasu adduo'i ta bata na safe da yamma,dana kwanciya bacci sai addu'ar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya kowayar da mu idan kayi mugun mafalki, bayan ka karanta addu'ar kai sauya kwanciya, kana ta koma bedroom ɗinta, lokacin har an fara kiran sallar magrib, wanka tayi kana ta ɗora alwala bayan ta idar da salla, ta janyo chalbi tana azkar, wayarta ce ta shiga ringing, bata ɗauka ba sai da ta kammala, kana ta duba wayar number ce ba suna saboda haka ta mayar da wayar, Unguwar Maitama Gidan Minista Alhaji Abubakar M Bello, Pinky ce a tsakiyar ƙatun gidan tana wasa, ita kaɗai sai ga wata dattijowar Mata ta fito ƙofar paroln gidan tana kiran "Takwara kina ina ne zo ga Abbeey ya kira.?" Pinky dake zaune tana wasa jin Abbeeyn ta ne ya kira da gudu ta ƙarasa wurin matar, tana faɗin "Har Abbeey ya isa gida kenan." Ganin ba waya hannun matar Pinky ta ɓata fuska ta ce "Haba Kaka ya zakiyi min haka, ƙarya fa ba kyau.?" Dariya Matar ta yi kana ta ce "Da gaske ya kira na duba ki ba kya parlo shine ya kashe wayar, na fito na duba ki." "Okey to muje na kirasa, ai ya ce zai siya min waya na huta da ɗaukar wayarki kina yi min yanga." Murmushi Matar ta koma yi kana ta ce "Ai kuwa da wayata ta huta da masifarki ." suka shiga cikin paroln, wani babban Mutum ne na hango ya na saukowa daga kan bene, Alhaji Abubakar M Bello kenan, wurinsa Pinky taje da gudu ya buɗe mata hannu ya na faɗin"Oyoyo Amaryata, har kun dawo wurin gyaran gashin.?" Ta ce "Eh mun dawo muje ka gani ya yi kyau sosai." Zama sukayi kan kujera kana ya ce "Wow you are so beautiful, my dear, wacece wannan mai gyaran gashin.?" Cikin zumuɗi Pinky ta bashi labarin har abinda bai tambaye ta ba, murmushi ya yi kana ya ce "Nima zan bata kyauta muje tare ki kai mata." Pinky ta ce "Ai kuwa zataji daɗi kaga gobe ba school sai muje gidansu." Ya ce mata "Eh zasu je." Kana ya ce "Hajiya Maryam ki bata waya tayi magana da Abbanta, ki sameni a paroln sama." Ya na gama faɗar haka ya haura sama bawa pinky wayar tayi kana tabi bayan Mijinta zaune ta same shi, kusa da shi ta zauna kana ta ce "Yallaɓai gani." Zama ya gyara kana ya ce "Maryam me kika fahimta game da Takwararki, da wannan yarinya Zuhura.?" Lumfashi Hajiya Maryam ta sauke! kana ta ce, Maganar da zanyi da kai kenan saboda tun bayan dawowarsu ta dameni da zancen Aunty Zuhura, kamar ba yau suka san juna ba, ƙarshe dai cema Abbeey tayi dan Allah ya aure Zuhura ta rinƙa yi mata gyaran gashi, data matsa mai da zancen shine ya mareta, ya bar gidan gaba ɗaya baya son zance aure, ai ko don saboda ƴarsa ya kamata ace ta samu mata, gashi Takwara bata taɓa cewa ya yi aure ba ko tayi zance wata mace bayan Mamanta sai wannan duk da ban taɓa ganin yarinyar ba amma yadda Takwara ke zancen ta sai naji ta shiga raina, shine yanzu ya kira waya ya gama fushi, da ƴarsa." Alhaji ya ce ai ina ganin wannan lamari zai zo muna da sauƙi saboda na fahimci itama Yarinyar tana ƙaunar Pinky, da wannan zamu lauye sa dole ya je neman soyayyar ta ko yaƙi ko ya so, yanzu abinda ya kamata zuwa gobe kuje tare gidansu yarinyar domin ke ƙara gane mana yadda take idan ba wata matsala, shikenan." Dariya Hajiya Maryam ta yi kana ta ce "Haba Yallaɓai yanzu sai kawai muje tare da Takwara.?" "Eh mana miye aciki, ke san yadda zakiyi dabarun nan naku na mata." "To shikenan Allah ya kaimu gobe lafiya." "Amin." Ya amsa tare sauya akalar zancen , pinky kuwa Abbeey ta dannawa kira, katse kiran ya yi kana ya kira, ɗagawa tayi bata ce komai, shiru sukayi na wani lokaci, kafin ya ce "Pinky fushi kikeyi dani.?" "Hamm." Shine kawai abinda pinky ta yi, ajiyar zuciya ya sauke! saboda ya san halin ƴar tasa akwai zuciya, ya ce "I'm sorry my Angel bazan sake dukan ki ba, a yafewa Abbeey." sai lokacin Pinky tayi magana ta ce "Idan har kana so na yafe ma sai ka yimin alƙawarin zaka aure Aunty Zuhura ta dinka gyara min gashi." Be tsaya wani tunani ba saboda bai ɗauke maganar da mahimmanci ba, ya ce "Na yarda, yanzu dai kiyi min dariya idan ke haƙura." Dariya tayi mai sauti kana ta ce "Thank you my Dad love you." "Me too my Angel." ta kashe wayar da gudu ta haura sama tana kiran "Takwara Daddyn Abbeey kuzo muyi rawa Abbeey zai aure Aunty Zuhura." Ta shiga parlon tana faɗawa jikin Alhaji, Hajiya Maryam ta ce "Ke Takwara bana son ƙarya fa shi Abeey ya yarda zaiyi aure.?" Pinky ta ce "Na taɓa yi miki ƙarya ne bara na kira shi kiji." Ta dannawa Abbeey kira ɗagawa ya yi ta ce "Dad ba ka yarda zaka aure Aunty Zuhura ba.?" "Eh ya akayi.?" Ƙis ya ji ta kashe wayar, tana kallon Hajiya Maryam, ta ce "To yanzu kinji ai." Alhaji, ya ce "Oh wannan yarinyar baki da dama, akwai rigima, to Allah ya sa da gaske ya ke." Hajiya ta ce "Amin." Pinky kuwa tsalle tsalle kawai takeyi Abeeyn ta zaiyi aure, India ɓangaren Arman da Sarki Raka, Wani azababben yaƙi ne ta kacame da, banda gumurzu da kaima junansu mugun farmaki babu abinda sukeyi, kusan awa biyu suna abu ɗaya babu wanda ya samu nasarar cutarda ɗan uwansa, ganin haka Arman ya sauya salon yaƙi suka zubar da makamai suka zage damtsi, nan fa Sarki Raka ya fara raina kansa saboda Arman nayi mai naushe biyar kafin ya kai masa naushi ɗaya, nan fa ya fara haɗawa da tsafi, da wannan ya fara cutar da Arman Anaya kuwa ganin yana neman halaka mata miji, ta diro tsakiyar filin ita da Amrita, suka fara gwabzawa, yanzu gaba ɗaya suna samun sa'ar juna, sun jigata sosai, amma sai gumurzu sukeyi, Sarki Raka na kaiwa Arman suka da wuƙa Anaya ta kara ya daɓa mata ita ga ciki take ta zube ƙasa, wani ihu Arman ya saka tare da yi kan Anaya, nan sarki Raka ya chaka mai wuƙa a gadon bayansa, take ya zube kan gauwoyinsa wani yanka ya kaima Arman ya kafaɗa take ya zuɓe ƙasa, idanunsa na kallon Anaya dake dafe da cikinta, jini na zuba, saboda takobin ta shigeta sosai hannu take miƙowa Arman shima ya na miƙa mata nashi amma basa cinma juna, cikin mugunta Sarki Raka ya take hannun Arman, Amrita kuwa tana ganin haka, ta daka wani tsalle tayi sama, Sarki Raka ya bi bayanta, Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY Idan kunyi comments kuga Update yadda kuke so idan ku ka yi shiru zaku ga shiru 💀 *FATALWA* ☠️ *Love and romantic* 💋 *Story and Writer Bey* *PINKY DARLING MRS JAY* Masu neman fatalwa daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran liltafai https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e ____________ Following this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD🌍 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _______________________________________ *DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️* (*we stand together*) 🤝🤝🤝 Bismillah Rahamanin Raheem💫 🆓 BOOK PAGE4️⃣1️⃣▶️4️⃣2️⃣ Haka Sarki Raka ya bi bayan Amrita kamar wani tsuntsu, suka ringa shawagi, a sama, da ƙyar ya samu damar cinma Amrita, suka fara gabza bala'i, ko wane na ji da iya tsafi, da ƙarfi, Boka kuwa, da ganin Sarki Raka ya bi Amrita da sauri ya isa wurin Arman, ya tayar da shi, tare da bashi sauran ruwan da ya baiwa Anaya tasha, jin ginar da Arman ya yi kana ya je wurin Anaya, itama ya bata, ɗaukar ta ya yi kusa da Arman ya ajiyeta, tare da ɗaukar hannun, Arman ya ɗora a cikin Anaya, take wurin da Sarki Raka ya chaka mata wuƙar, ya soma haɗewa, sai lokacin Arman ya buɗe idanunsa da suka rikiɗe i zuwa ja kamar wuta, ganin Anaya kusa da shi, ga boka zaune gefensa, ya ɗan zabura, zai tashi Boka ya dakatar da shi ya ce "Zauna Yaro ba cutar da ku zanyi ba, ka tsayi kaji dama ni bana tare da Sarki Raka, kawai ina biye masa ne saboda idan na fito fili na gaya mai gaskiya kasheni zaiyi, asali ne ba Boka bane, musulmi ne, sunana Kabir, dama wannan ranar nike jira tazo asamu Jarumin da zai kawar muna da shi, wannan mulkin zalunci da yake yi, yanzu lokacin da zan ɗauke fansa ya cika saboda ya kashe iyayenka har Matata ya kashe tana ɗauke da tsohon ciki ita ke yima Mahaifiyarka hidima wannan shine dalilin da ya sa nayi ɓadda kama tsawon shekaru ina zaune a matsayin Boka, shi ya sa na saka, shi kashe ɗansa a matsayin, hakan zai bashi ƙarfin ikon da zai iya halaka ku, ita Aljana Amrita ta san komai wannan ne ya sa taja shi i zuwa sama saboda na farfaɗo daku kafin ya dawo, ya tarar daku, ya ida nufinsa." Shiru Arman ya yi saboda duk yadda yake jin zalunci irin na Sarki Raka ashe ya wuce haka, lokacin Anaya ta farfaɗo wurin sa ya chaka mata wuƙar ya haɗe gaba ɗaya kamar babu abinda ya sameta a wurin, rungume juna sukayi sun jima a haka kafin suka sake juna Arman ya tashi, tare da fasa wani ihu yana girgiza jikinsa, take takobinsa ta zo da gudu, sai cikin hannunsa, take kayan jikinsa suka sauya zuwa cikin wata shigar yaƙi irin ta mayan sadaukai, masu jini ajiki da basu san tsoro ba, Anaya ma haka ta cire wani zube dake hannunta tana juya shi, sai ga shi ta dawo cikin shigar yaƙi dai dai lokacin Sarki Raka ya sauko ƙasa tare da Amrita saboda masifa, ya na ganin Arman ya yo kansa ai kuwa su Anaya sukayo kan sarki Raka suka kacame da azababben yaƙi, har wani tsalle sukayi zuwa sama suna masifa kana su dawo, ƙasa, kamar wasu tsuntsaye, har wuta takobin Arman ke fitarwa, wannan lokacin sun samu sa'ar Sarki Raka sai gabzar juna sukeyi, sukeyi, kamar ba jini da tsoka a jikinsu, Abuja Najeriya ɓangaren ZUHURA Washegari da safe bata fita shago ba kwnace kawai take har Mommy ta fita wurin aiki, Abbanta ya fito ya ce "Mamana lafiya yau bazaki fita bane.?" Ta ce "Abba yau bazan fita ba sai gobe idan Allah ya kaimu kaina ke ciyo." "Ayya Mamana ke sha magani.?" "Eh Mommy ta bani." "Okey ni zan fita saina dawo ina da mitin da wasu turawa." "Adawo lafiya Abbana." "Amin Mamana." Ya fita ta raka shi da idanu, sai da ta tabbatar ya fita haka kawai taji tana son shiga part ɗinsa, ta zagayawa, shiga tayi, ta soma yawo ciki ƙatun paroln, tana yawo ta shiga bedroom ta fito wurin wani ƙaton hoton Abbanta ta nufa, da ke gefen paroln shi kaɗai tana fara dosar wurin ta ji kamar ana bibiyarta a baya, a tsorace ta juya bataga kowa ba, ta cigaba da tafiya jin tayi an cigaba da bibiyarta, addu'a ta somayi shiru taji andena biyarta, tana isa wurin hoton ta saka hannu ta ɗauke hoton tana faɗin"Kai duk ya yi ƙura ina ganin kamar ba'a taɓa gogesa ba." Idanunta ne suka sauka kan wata ƴar ƙaramar ƙofa ta gilas wurin da ta janye hoton, cike da mamaki take kallon ƙofar tun da suka tare a gidan tsawon shekaru bata taɓa sanin akwai wannan ƙofa ba, haka kawai taji zuciyarta na ingizata ta shiga ciki, ai kuwa ta buɗe ƙofar tana shiga, taji ƙofar ta rufe da ita, Abbanta kuwa bayan ya fita, ya na cikin mota ya ji totsar dake kunnensa ta fara motsi zata fito ya saka hannu ya dafe kunnensa, alamar ta koma, ya ce "Direba juya da sauri ka mayar dani gida." haka suka juya zuwa gida yana shiga parlo ya duba bega Zuhura ba kana be ga Motar Hajiya Balkisu ba, da sauri ya haura sama zuwa parolnsa, turus ya tsaya! ganin Zuhura ta shige cikin wannan ƙofa da sauri ya rufeta ta waje ya mayar da hoton ya zauna gefen bed wani gumi na keto masa gaba ɗaya jikinsa har rawa yake yi, Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY more comments more typing please share 💀 * FATALWA* ☠️ *Love and romantic* 💋 *Story and Writer Bey* *PINKY DARLING MRS JAY* Masu neman fatalwa daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran liltafai https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e Following this link to join PINKY🌺DARLING 👄HAUSA NOVELS📚 WORLD🌍 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _______________________________________ *DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️* (*we stand together*) 🤝🤝🤝 Bismillah Rahamanin Raheem💫 🆓 BOOK PAGE 4️⃣5▶️️⃣4️⃣6️⃣ Motar data ɗauke Zuhura kuwa tafiya ya yi mai nisan gaske har ya isa wata Unguwa da babu wadatatcin jama'a dai dai wani ƙatun get ya danna horn Get Man ya wangele mai ƙofa ya danna hancin motar ciki, yana gama parking ya fito ya zagaya baya ya ɗauko Zuhura, ya shiga da ita cikin gidan parol ya ajiyata kan kujera, kana ya wuce ciki bathroom ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin kayan bacci, kana ya dawo paroln ya zauna tare da ƙorawa Zuhura idanu, wayarsa ya ɗauko ya kunna tare da kiran wata number, "Hello Dr Ali tsawon awa nawa allurar zata ɗauka kafin ta saketa.?" "Tawon awa shida haka zuwa 7 idan jininta bashi da ƙarfe sai da safe zata iya sakinta." "Okey thanks." Ya kashe wayar tare da saka hannunsa cikin sumar kansa, wayarsa ce tayi ringing ya na dubawa ya ga sunan Umma ɗagawa ya yi tare da sallama, "Assalamu alaikum." Wa'alaika salam Abbeey wai ina ka shiga? ne tun da safe Pinky sai rigima takeyi da ƙyar tayi bacci saita ganka anyita kiran number ka bata shiga har gidanka Mai gadi yaje baka nan." Lumfashi ya sauke! ya ce "Wani aiki ne ya riƙe ni inda nike ba network amma in sha Allah zan shigo da safe." "Okey to sai ka shigo saboda har mun shirya zuwa gidansu Zuhura amma ba'a samun number ta kashe take." "Maybe ta kashe wayar ne a bar zancen zuwa gidansu har nan da kwana biyu." "To naji saika shigo da safe." Ya ce "Okey Allah ya kaimu lafiya." "Amin." Ta kashe wayar, idanunsa ya maida kan Zuhura da sai bacci takeyi, a fali ya furta, "Ke dai bakiyi sa'ar Uba nagari ba amma ba komai ƙarshen su yazo lokacin da nike jira ya zo zan shafe labarinsu, a doron ƙasa." Wani murmushin ya yi kana ya bar parlo zuwa bedroom ɗinsa ya kwanta, Zuhura kuwa na nan parlo tana bacci, ƙarfe uku na dare wayar Alhaji ILIYA ta soma ringing, cikin maganin bacci ya ɗaga wayar batare da ya duba mai kirinsa ba, "Hello." Ya faɗa ɗaya ɓangaren akace "Kai la'ananne daga yau baccin dare ya ƙare maka, ƙarshen ka ya zo daga yau zaka fara girbar abinda ka shuka." Ɗif yaji an katse kiran dubawa ya yi an ɓoye number da aka kirasa, message ne ya shigo ka duba Wahtsapp ɗinka da sauri ya kunna data shiga saƙo ya shigo da wata number, video ne ya buɗe yana kallo shida Abban Zuhura ne lokacin da suka ajiye ta suka bar wurin sai Audio wayar da sukayi kafin a ɗauko Zuhura, wani gumi ne ya rinƙa karyo mai, gaba ɗaya hankalinsa ya tashi, be ida shiga tashin hankali ba sai da aka Tura mai wani Audio, lokacin yana magana da Abban Zuhura akan bada ƴarsa Khadijah da ya yi ga dodon kuɗi, da matarsa ta gano ita kuma ya haukatar da ita, gaba ɗaya ya faɗa cikin wani yanayi Number Abban Zuhura ya kira lokacin shima Abban Zuhura na zaune an turo mai duk abinda aka turama ILIYA, Yana ɗauka ya ce "Alhaji Haruna wallahi muna cikin babbar matsala ya za'ayi mu haɗu yanzu." Abban Zuhura ya ce "Kaga abinda aka turomin kuwa.?" ILIYA ya ce "Duk abinda aka turoma nima haka saboda haka ya kamata muyi gaggawar ɗaukar mataki mu gano ko wanene ya yi muna

Chapter 7 of 8