Share this page
6 / 7
mai kyau a gidan ba har ta manta,jininta da zaa auna zaa ga yayi mugun Hawa saboda fargabar da take fama dashi,kalar tsanar da take hango Kabiru na mata wata rana zai iya kashe ta din" Kafin a Kai ga haka gwara ta tsira da ranta ta gudu ta bar gidan ta Shiga duniya bazaa rasa na Allah da zasu taimaka mata ba,dan bazata je wajen dangin mahaifiyar ta ko mahaifinta ba ballantana a Nemo ta. Tana rubuta wasikar tana kuka har sai da ta gama ta ninke takardar ta kwanta lamo tana jiran dare yayi ta fice daga gidan. A kwancen da take kuka kawai take tana tunanin Ina zata dosa ya Sajeeda zata ji idan ta ga wasikar. Tana nan a kwance bacci ya fara k'ok'arin sace ta sai k'ok'ari take ta hana kanta baccin har sai da baccin ya saceta ta k'arfi. Mafarki Shigowar Sajeeda d'akin ta da Sunan ta da ta Kira yasa ta bud'e idonta. Ganin Sajeeda a tsaye ta kura Mata ido hawaye na zubo Mata yasa ta mik'e zaune da sauri tana Umma "Kar ki tafi ki barni Yesmeen,Mai na miki da Zaki tafi ki taimaka min karki tafi Yesmeen"......... 2nd to the last free pages Biya 500 ta wanan acct din 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko katin mtn ta wanan lambar 08033719070 sai a turo da shaidar biya ta layin nan 08033719070 ko wanan layin 08068484400 Mutanen Niger Kuma ku tuntubi wanan lambar +227 96 82 89 84 karku yarda a Baku labari dan rufaffen sirri labarine mai Abubuwan ban mamaki da alajabi akwai Kuma darusa Mai yawa MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4k Mg's beauty kit 14k Herbal whitening soap Body cream Face cream Scrub Cleanser Glow oil Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Team glow😍 *RUFAFFEN SIRRI* *NA SADNAF* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *Page 9* "Yesmeen Kar ki tafi ki barni Yesmeen" Sajeeda ke ta maimaitawa a mafarkin ta har sai da ta tashi a firgice bakin ta d'auke da sallati. Dan sai taga kamar a gaske ba mafarki ba. Sai da ta ga k'ofar d'akin ta a rufe yake ta tabbatar da mafarki take tabi ta hada gumi,ta kalli hannun ta da ta rik'e wasikar da ta rubutawa Sajeeda,ta dago ta kalli agogo taga karfe Sha biyu na dare ta mik'e tsaye da sauri dan har ga Allah so take ta gudu ta bar gidan,dan rayuwarta a cikin hatsari take tunda har Kabiru ya fara mata Barazana akan zai kasheta idan bata gudu ba watarana zai kasheta din. Jakar da ta zuba kayan ta ta d'auko bayan ta ajiye takardar a karkarshin pillo a hankali ta fara karewa dakin kallo hawaye na zubo mata hakika Sajeeda ta rik'e ta tamkar Yar cikin ta bata tab'a barin ta tayi maraici ba duk da dangin mahaifinta sun watsar da ita,mahaifinta ma gani take ya manta da Yana da ita dan bai tab'a Neman ta ba. A yanzu bata san hannun wa zata fada ba Tafi minti talatin a tsaye tana zubar da hawaye tana tunanin halin da ta tsinci kanta a ciki tayi matukar nadamar leka Kabiru,dan da bata leka shi ba da duk haka bata faru ba. A hankali ta murda k'ofar d'akin ta fita palo kirjinta na dukan uku uku fitilar palon ma a kashe take ko Ina shiru sai karar fanka. Cikin Sand'a ta nufi k'ofar fita daga palon ta murda a hankali ta fice tare da rufo k'ofar duk abinda take yi jikin ta rawa kawai yake. Taku uku tayi taji motsin bud'e k'ofa. Cikin zafin nama ta shige cikin fulawowi dake kewaye da jikin bangon runtse idon ta tayi da k'arfi dan ji tayi abu ya soketa a baya ta d'auke numfashin ta a lokacin da Kabiru ya fito Yana dube dube. Ganin bai ga kowa ba yasa yayi bayan gidan dan ya duba lafiyar karen sa kasan dan Kamar motsi yaji Yana yin bayan gidan Yesmeen ta fito daga fulawowi ta shige cikin gidan da gudu ta bud'e kofar ta ta shige tana sauke ajiyar zuciya dan ta balain tsorata ta d'auka Kabiru zai ganta. Ba haka taso ba taso ta gudu a yau dan ta balain tsorata da Kabiru amma ko bata gudu yau ba sai ta gudu gobe. Tana Jin motsin sa a bayan gidan sai da ya jima kafin ya koma ciki. Sajeeda A firgice ta tashi daga baccin da take ta hau kalle kalle,ganin Kabiru a gefen ta yasa ta hau tashin sa tana cigaba da kallon bakin k'ofar jikinta na rawa Karen da Kabiru ya kawo cikin gidan tayi mafarki ya shigo Yana kokawa da ita Yana jan zanin ta tana ja Kabiru bude idonsa yayi yana "Sajeeda zan bar Miki d'akin nan na koma dakina kawai dan bakya barina nayi bacci na gaji" Kuka Sajeeda ta fashe dashi tana "Kabiru dan girman Allah ka fitar da Karen nan da ga gidanan rabon da nayi bacci cikin dadin rai har na manta tun muna tsohon gida rabona da samun bacci Mai nustuwa kullum sai nayi mafarki da Karen nan na gaji Wallahi na gaji Kabiru idan har ba za ka fitar da Karen nan daga gidanan ba wlh zan bar gidanan kullum cikin fargaba nake dare yayi ban da mugayen mafarkai da nake fama dasu. Ido Kabiru ya zuba mata cikin mamaki dan ya d'auka aikin da shugaba yayi a kanta zai saka duk abinda ta gani bazata iya magana ba. Ya za'ayi ya barta ta bar gidan bayan yazo dab da cimma burinsa Dole yasan dabarar da zai mata nan da kwana uku yasan ya samu cikar burin sa tashi yayi ya zauna Yana "Ya isa Sajeeda tsaya ki saurareni" Sajeeda tsagaita kukan da take tayi Kabiru ya fara magana Yana "Ki kwantar da hankalin ki zan maida karen wajen Wanda ya bani amma baya gari sai ranar alhamis zai dawo na Miki alkawari Yana dawowa zan maida karen akwai barayi sosai a unguwar nan shi ya sa na karbo Karen dan na san idan barayi najin haushinsa zasu ji tsoron shigowa amma tunda kin saka tsoro a ranki ran alhamis zan maida Karen shikenan"? Gyada Kai Sajeeda tayi Kabiru ya saki murmushi Yana ta koma ta kwanta. Sajeeda tashi tayi tana bari tayi sallah raka'a biyu. Kamar kullum dai tana raka'a biyu bacci ya kwasheta akan sallaya. Kabiru kuwa na ganin haka ya fito daga d'akin yayi waje. Yesmeen tuni ta ajiye batun guduwa a gefe dan sau uku tana mafarkin idan zata gudu sai Sajeeda tazo tayi ta rokonta Bata san Mai yasa take yawan mafarkin ba. Yau har suka gama karyawa bata ga Sajeeda ta fito daga daki ba taga dai Kabiru ya fita ganin har Sha daya Sajeeda bata fito daga d'akin ba yasa ta nufi d'akin Sajeedan dan ta dubata. Koda ta tura k'ofar d'akin Sajeedan a kwance ta ganta tana ta mutsu mutsu tana girgiza ita kadai idon ta a rufe ta hada gumi,. Da sauri ta Isa bakin gadon ta fara girgiza ta tana "Umma umma ki tashi" Sai dai bata bude idon ta ba ta cigaba girgiza hakan kuwa ya Kara dagawa Sajeeda hankali tayi waje da sauri taga ko su Saifullahi na nan" Ganin su Saifullahi basa nan da ta duba dakinsu yasa tayi d'akin ta dan ta d'auko wayarta ta Kira Kabiru ta fada Masa halin da Sajeeda ke ciki. Jikinta rawa kawai yake a lokacin da ta d'auko wayarta akan gado ta d'auko wayar kenan kamar ance ta kalli windon dakinta taga Karen a kwance Yana girgiza Kuma a ringingine Yana wani gurnani Sakin baki tayi tana kallon Karen dan bata tab'a ganin Kare a kwance kamar mutum ba sai wanan,kamar an mitsineta tayi d'akin Sajeeda da gudu,Koda ta Shiga girgiza da mutsu mutsun ta cigaba da yi ta Kara fitowa da gudu tayi dakin ta ta tsaya a bakin windo shima mutsu mutsun taga Karen nayi,sai ta fara k'ok'arin ta hada tunanin ta waje daya tunanin daya darsan mata a zuciya yasa tayi waje da gudu zuciyarta cike da tsoro da fargaba tayi bayan gidan ta tsaya nesa da wajen da Karen yake har lokacin Yana ta girgiza dube dube ta fara yi idon ta ya sauka akan wani katon dutse bata tsaya bata lokaci ba ta d'auki dutsen ta jefa wa Karen ya kuwa mirgina ya fara haushi Yayo kanta ta kwasa da gudu ta koma ciki tare da rufo k'ofar Jikinta karkarwa kawai yake dan saura kiris ya kawowa kafarta Cafka. D'akin Sajeeda ta koma ta kuwa ganta a zaune tana sauke ajiyar zuciya ta bi ta hada gumi yesmeen kuwa tuni ta daskare a tsaye dan a yanzu abinda take zargi ya tabbata. Sajeeda kawai take kallo zanin da ke jikinta ma a yau tayi mafarkin ta dashi Ganin Sajeeda ta kallota yasa ta nufi wajenta tana "Sannu umma na shigo na duba ki ne da naga har sha daya baki fito ba" Sajeeda bata iya ce Mata komai ba dan gabanta zugi kawai yake mata. Mik'ewa tayi tana "Bari na shiga bandaki Ina zuwa" Tana shigewa Yesmeen ta fito jikinta na rawa dan boye tashin hankali da take ciki tayi dama tunda aka kawo Karen nan tasan da akwai manufar da ya saka Kabiru ya kawo karen, Yanzu Kabiru ya rasa wa zai cutar sai Sajeeda mai ta masa haka da ta cancanci irin wanan zaluncin daga wajensa a iya sanin ta da zaman da tayi a gidan,Sajeeda kullum k'ok'ari take ta kyautata masa amma sakayar sa zai yiwa Sajeeda kenan,kuka kawai take na tsananin tausayin Sajeeda bata san Mai ma'anar abinda ta gani ba bata san wane cutarwa Karen zai yiwa Sajeeda ba,ta riga da tasan sirrin Kabiru a yau Allah ya haska mata abinda Kabiru ke nufi da kawo Kare cikin gidan zata yi iya k'ok'arin ta dan ta taimakawa Sajeeda Koda kuwa nata rayuwar zai zama a cikin hatsari. Sake sake kawai take a zuciyarta Motsin Sajeeda da taji a palon yasa ta goge hawayen ta ta fita waje. Ta tarar da Sajeeda a zaune tayi fayau da ita kamar mara lafiya. Kitchen ta shige ta d'auko flask din da ta zuba Mata kunnun gyada da Kofi ta Kai Mata palon ta fara k'ok'arin zubawa Sajeedan sai Sajeeda ta daga Mata hannu tana "Bazan iya sha ba yesmeen bana Jin dadi bani da lafiya bansan Mai yake damuna ba ba daidai nake ba" Sajeeda ta karashe kwalla na zubo Mata Yesmeen kuwa ta zuba mata ido itama idonta ya ciciko da kwallan tausayin Sajeeda kila ma jininta ake zukewa. Cikin rawar murya Yesmeen ta fara magana tana "Umma Allah ya baki lafiya Wai me yake damun ki haka"? Sajeeda share hawayen daya zubo mata tayi tana "Bansani ba Yesmeen idan har Zan kwanta sai nayi mugun mafarki da Karen da Abban ku ya kawo na rasa dalili jikina ba kwari Ina Jin ciwo a jikina bansan Wanda Zan fadawa ya gane Mai nake ji ba,na fadawa Abban ku yace ran Alhamis zai fitar da Karen Kinga jibi kenan rabona da bacci mai Dadi har na manta har tsoron rufe idona nake yi" "Umma daga mafarkin nan da kike yi da Karen nan da Abba ya kawo Zaki san ba kalau ba kinsan wasu karnukan fa mayune Dan Allah umma ki dage da Addu'a ki daina ma bacci,idan za ki yi Addu'ar ki fito Palo kiyi saboda kiyi a nutse" "Ina yi Yesmeen sai dai Ina fara yi bacci zai daukeni ni gidanan gabadaya nake so ma mu bari nidai haduwar Abbanku da wanan abokin nasa bai zame min alheri ba dan sai da suka hadu nayi bankwana da kwanciyar hankali Ina ta so na nusar da Abban ku ya kasa gane kiga fa daga zuwa gidanan Annur dina ya kurmance wallahi banga alheri a tarayyar Abban ku da abokin nan nasa ba na dai cewa Abban ku ya maida Karen nan Inda ya d'auko yace jibi zai maida Karen" "Umma ki dai cigaba da Addu'a kafin kiyi bacci kiringa karatun Qur'ani" Kiringa kwanciya da alwala ni tunda na fara mugayen mafarkai na dage da Addu'a na rage mafarkin dan biyun dare nayi nake tashi nayi ta Addu'a" "Zan saita alarm a wayata in sha Allahu zan ringa tashi biyun daren So nake ma na Kira Abban ku nace masa zanje asibiti bana Jin dadin jikina zanje likita ya dubani" "Sannu umma ki daure ki sha kunun Kinga da zafin sa" Dak'yar Sajeeda ta sha kunun kamar wacce aka yiwa duka haka take jin jikinta. Daga sallahr asuba ta koma bacci,a cikin baccin ta taji Kamar ana zungura mata abu a gabanta ta rasa wane irin masifa ne wanan" Wajen biyar na yamma su Saifullahi suka shigo gidan a guje suna ihun murna Sajeeda dake can daki ta fito da sauri Yesmeen dake kitchen itama ta fito daga kitchen din tana kallon su Faisal ne ya fara magana cikin murna Yana "Abba ya siyo sabuwar mota dalelliya yana waje yanzu zai shigo" "Umma ke Kinga kyaun motar"? Cewar Saifullahi Yana washe baki Sajeeda Da ido kawai nake bin su dan ban ji digon farin ciki a zuciyata na siyan motar da suka ce Abban su yayi ba,ni a yanzu ma tsoron yadda Abban su ke kashe kudi yake dan naji Wai Yana shirye shirye tura Saifullahi kasar waje yayi karatu,a kasa da wata hudu Abban Nusrah yayi irin wanan kudin,anya kudin nan nasa na halal ne kuwa. Bakin sa a washe ya shigo palon Yana kada mukulli ya nufo wajen da nake tsaye Yana "Sajeeda na Miki sabuwar amarya fito waje kiganta" So nake na mishi tambayoyi amma na kasa Kamar wacce aka likewa baki haka nabi bayansa,na ga dalaleliyar motar a tsakar gidan,bansan kudin motar ba amma nasan masu kudi ke hawa irin motar nan Wanda ya isa ya tadda Kai" Yake kawai nake Ina Masa Allah ya sanya alheri cikin murmushi ya Miko mun mukulin Yana "Ke na siyawa Sajeeda babban burina dama na samu kudi kiji Dadi na faranta miki ba kaina na siyawa ba ke na siyawa" Sakin baki nayi ina kallon sa ya gyada min kai "Ni Kuma Abban Nusrah baka siyawa kanka ba sai ni"? "Kin cancanci na siya Miki Sajeeda" Girgiza kaina nayi na maida Masa mukullin Ina "bazan karba ba Abban Nusrah dan duk Wanda ya tambayeni Ina na samu motar Nan bansan mai zance Masa ba" Take ya hade rai ya hau masifa kamar zai kawo min duka Wai so nake nace sata yakeyi bata hanyar halal yake samun kudinsa ba" Nidai shiru nayi bance Masa komai ba. Sai gashi a ranar yayi fushi yak'i kwana a dakina duk hakurin da na bashi yaki ya saurareni. Washegari ma ko ta kan Sajeeda bai bi ba yana tashi ya Shiga kitchen ya dafa abinci dayaji namomi ya zuba a plate din da yake kaiwa Kare abinci dan da kansa yake hadawa Karen abincin da yake ci. Zuciyarsa cike take da farinciki dan a yau zai samu cikar burinsa dan idan komai ya tafar Masa yadda yake so ya zama multi millionaire Har ya d'auki abincin zai yi waje ya ajiye saboda fitsarin daya mugun matsar sa. Sai ya nufi bandaki dan yayi fitsarin. Yesmeen dake labe tana lekansa da tun jiya take Addu'a Allah ya bata saa da nassara. Ganin ya ajiye abincin yasa ta fito da balain sauri hannunta dauke da shinkafar beran da ta Nemo tun a jiya. Tana zuwa ta juye shinkafar beran gabanta na mugun faduwa. Ta fito daga kitchen kenan taci Karo da Kabiru cikin mugun faduwar gaba ta ja da baya ya shige yana watsa Mata mumunan kallo tayi waje da gudu. Ya d'auki abincin yayi bayan gida. Yana zuwa ya tsugunna a gaban Karen ya ajiye abincin a gabansa. Da sauri Karen ya fara cin abincin Yana kada jelarsa. Kabiru kuwa sai shafa Masa baya yake Yana tunanin yadda zaiyi a Daren yau dan abinda akace yayi wanan da zaiyi yafi kowane wuya da hatsari Ganin Karen ya daina cin abincin ya sa ya daina shafa shi yaraf Karen ya zub'e a kasa bakinsa na fitar da kumfaa hankali a tashe Kabiru ya mik'e tsaye Yana kallon Karen tun Karen na motsi har sai da ya daina. Hankalinsa a mugun tashe ya girgiza Karen Yaga ko motsi baya yi babu ma alamar rai a jikinsa wani irin ja da baya yi cikin azabar tashin hankali ko baa fada Masa ba Karen dai mutuwa yayi. Wani irin ihuuu ya saka yana "Yesmeen kin kashenii............. Hmmm Yanzu aka fara labari ku biya 500 zuwa acct dinan 2029764071 ko katin mtn zuwa lambar Nan 08033719070 ku turo da shaidar biya ta layin Nan 08033719070 ko wanan layin 08064484400 Mutanen Niger ku tuntubi lambar Nan +227 96 82 89 84 Dan kuyi payment ku more karatu.. MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4k Mg's beauty kit 14k Herbal whitening soap Body cream Face cream Scrub Cleanser Glow oil Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Team glow😍 *RUFAFFEN SIRRI* *NA SADNAF* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *Page 10* A haukace Kabiru ya ringa girgia Karen Yana kuka wiwi,shi kadai yasan wahalar da ya sha kafin a iya hada masa abinda zaiyi ya samu cikar burin sa,sai a yau da zai samu cikar burin sa Yesmeen ta kashe masa arzikin sa. Ya dauki abincin ya kurawa plate din ido, zuciyarsa kamar tayi bindiga saboda bakin ciki,ba Mai Masa aika aikan nan sai Yesmeen ba wacce ta saka masa ido sai ita daga fita yayi fitsari shine ta Shiga kitchen taje ta masa wanan aika aikan. Shikenan duk burikan sa da wahalar da ya Sha ya tashi a banza, Yesmeen ta jawo mai Asara A wani irin haukace yayi cikin gidan jikinsa na wani irin rawa ba abinda zai hana ya raba Yesmeen da ranta a yau. Bugun da yayi wa k'ofar palon yasa Sajeeeda mik'ewa a tsorace tana "Abban Nusrah lafiya"? Ko kallon ta bai yi ba yayi hanyar d'akin yesmen Yesmeen kuwa tunda taga yayi waje ta shige d'akin ta ta kulle wani irin tsoro ne ya shigeta a lokacin da Suka hadu a k'ofar kitchen sai taji ta fara nadamar ma zuba shinkafar beran dan tasan indai Karen ya mutu atake dole Kabiru ya zargeta tunda yaci karo da ita a lokacin da take fitowa daga kitchen, kirjinta kamar ya fado saboda fargaba ta tsaya a window tana kallonsu. A lokacin da Karen ya zub'e a kasa taji Kabiru ya Kira sunanta bandaki tayi a guje dan tasan yau kashinta ya bushe kuka kawai take a jiya tayi mafarkin Karen na ta cizon Sajeeda har sai da Sajeeda ta daina motsi,sau biyu tana mafarki a jere hakane yasa ko da ta tashi,sai taji gabadaya ta kasa samun nutsuwa zuciyarta tayi ta rayya mata da ta zuba wa Karen maganin b'era dan daga mafarkin da take tasan karen su Kabiru ke so ya cutar da Sajeeda,bazata iya zuba ido tana kallo ba, dole tayi wani Abu. Bugun da Kabiru ya fara yiwa kofarta yasa ta saki ihu dan ba k'aramin bugu yake yiwa k'ofar ba ta tuna yadda ya ringa rantsuwar zai kasheta idan ta Kara masa shishigi. Sajeeda kuwa hankalin ta ba karamin tashi yayi ba da ta ga yadda Kabiru ke k'ok'arin balle k'ofar d'akin Yesmeen Yana rantsuwar sai ya kasheta. Cikin tashin hankali ta fara magana tana "Abban Nusrah Mai Yesmeen din ta maka haka dan girman Allah kayi hakuri karka manta marainiya ce ka rufa min asiri mai ta maka haka dan Allah" Cikin jajjayen idonsa ya kalli Sajeeda Yana "Kinsan Allah yarinya nan sai na kasheta sai dai duk abinda zai faru ya faru" ido Sajeeda ta zaro cikin tashin hankali tana " A hayyacin ka kake kuwa Kabiru Mai ta maka da zaka kasheta innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Tace cikin ihu a daidai lokacin da ya buga k'ofar da balain k'arfi ya balle,ya shige yana hucci kamar wani zaki bai yi wata wata ba ya fara buga k'ofar bandakin da karfinsa. Sajeeda ta saki ihu Kamar yadda Yesmeen dake cikin bandakin ke zunduma ihu tana azo a taimaka mata. Sajeeda kuwa ganin da gaske idon Kabiru ya rufe idan har ta bar shi ya shiga bandakin shaidan na iya cin galaba a kansa ya kashe mata Yesmeen. Jan kabirun ta farayi da karfinta tana rokon sa shi kuwa iya karfinsa yake tura k'ofar dan ya balla kofar ita kuwa Sajeeda ta Kankame shi duk yadda yaso ya tureta ya kasa dan ba karamin kankama ta masa tana ihu ba. Kabiru ya runtse idonsa jikinsa na cigaba da rawa hawaye sai zubo masa yake na asarar da Yesmeen ta jawo Masa yanzu duk mafarkin sa na yin kudi ya tafi a banza dan dak'yar idan shugaban zai Kara sauraransa dan Yana ta basu wahala a duk abinda aka ce yayi bai yi ba Sajeeda da zai samu komai yazo masa cikin sauki,ta bijire masa hanyar da ya rage Masa Yesmeen ta ruguje masa Anya Yesmeen dinan mutum ce kuwa"?ko dai tasan dalilin daya saka ya kawo Karen cikin gidan. Hucci kawai yake Sajeeda kuwa har lokacin tana Kankame dashi tana bashi hakuri kamar yadda yesmeen dake bandakin ke aukin bashi hakuri tana sharrin shaidan ne ya yafe mata. Baya Jin kwarin jikin sa saboda irin bugun da yayi wa k'ofar d'akin nata murya can kasa da tunanin daya darsar Masa na idan har ya dage zai yiwa Yesmeen wani abu,asirinsa na iya tonuwa a gaban Sajeeda dan Yesmeen na iya fadar wani Abu ko shi zuciya tasa ya Fadi wani abu asirin sa ya tonu. Ki cikani Sajeeda na fasa yi Mata komai Karen da na ce Miki ba nawa bane na abokina ne Yesmeen ta sakawa shinkafar bera baki ga yadda abokina ke ji da Karen nan ba dazu ma sai da muka yi waya na jadadda Masa zan maida Masa gobe yarinyar nan da ta tashi ta zubawa Karen shinkafar bera" Kabiru yace cikin dacin zuciya idonsa na Kara cikowa da ruwa dan dauriya kawai yake shi kadai yasan tashin hankalin da yake ciki da sai da komai yazo masa karshe Yesmeen ta Masa haka, duk saboda cikar burin sa yak'i sallah har tsawon sati daya,yayi wanka da jini,ya Sha jini yaje makabarta karfe biyun dare ya binne abu sai da ya zo matakin karshe Yesmeen ta kashe shi. Hawaye suka Kara zubo masa daya tuna kalar wahalar da ya Sha har ciwo yaji a garin gudu dayaje makabarta binne abu, Sajeeda kuwa cak ta tsaya tana kallon shi a lokacin da taga Wai duk wanan abin saboda Karen da ya kawo ne,tsabar mamaki kasa ma matsowa tayi Saboda yadda taga ya fice a hayyacin sa har da kuka,ko da dan cikinsa ne ya rasu iya tashin hankalin da zai nuna kenan, saboda Karen dama yake kirarin kashe Yesmeen har da kukansa.? Kabiru hanyar waje yayi Yana ji Ina ma mafarki yake yi ya Kara yin bayan gida yana kallon Karen,ko kashe Yesmeen yayi yanzu baya Jin zai hucce,zai so ya azabtar da Yesmeen,zai so yaga Yesmeen ta Sha wahala kafin ma ya kasheta. Da Jan kafa ya juya yayi hanyar waje dan wajen Rabiu zaije ya fada Masa duk Abubuwan da suka faru. Sajeeda kuwa har ya fice mamaki bai saketa ba kanta yayi mugun daurewa da wanan al amari dama duk wanan tashin hankalin akan Karen da Kabiru ya kawo ne tana Jin motsin fitarsa. Ta buga k'ofar toilet din tana "ki bud'e Yesmeen ya fita" Yesmeen bud'e k'ofar tayi har lokacin jikinta rawa yake idonta yayi jajjur saboda kukan da ta Sha. Koda ta fito Sajeeda ido ta zuba mata dan bama tasan tunanin da za tayi ba a yanzu A hankali ta Kira sunan Yesmeen tana "Yesmeen da gaske ne ke Kika kashe Karen da Abban ku ya kawo"? Yesmeen bata iya magana ba dan batasan yadda zata yiwa Sajeeda bayani ba tunda idan har ta fada Mata ita ta kashe Karen sai ta tambayeta dalili. "Yesmeen Mai yasa Kika kashe Karen Wai Mai ke faruwane na kasa gane abinda ke faruwa Mai yasa Kika kashe karen"? "Umma yadda kike mafarki da karen nan haka nake mafarki da Karen ko bacci bana iya yi, haka Zan ta mafarki ya shigo Yana k'ok'awa dani idan kinzo cetona sai ya koma kanki hankalina ya kasa kwanciya da Karen a gidan nan shi yasa na saka masa maganin b'era" Yesmeen ta karashe tana mamakin yadda ta samu tayiwa Sajeeda karya dan bazata iya fitowa ta fadawa Sajeeda gaskiyar abinda ya faru ba dan da ace duk a hirar su ta tab'a

Chapter 6 of 7