Share this page
2 / 7
tafi gidan ki bana San shashanci dama mijin ki ke ta Kira kika k'i d'auka"? "Umma dan Allah ki bari na Kira Ahmad nasan bazai hana ni jiran Abba ba" Sai da na ga ta kira mijin ta ya amince ta jira Abban ta kafin na yarda ta zauna duk da har a kasan raina ba gajiya nayi da ganin ta ba gani nake kamar jiya na haifeta sai gashi cikin ikon Allah da ran mu ta girma tayi, aure duk Wanda ya ganta yasan tana d'auke da karamin ciki,a tunanin da nake na tuna halin da mahaifinta ya bijiromin dashi,take da girmana da komai nabi sauran kannenta da kallo da duk sun ma fi Nusrah girma Annur da Fahad ne kawai basu fita girma ba,mutane da yawa sun d'auka saifullahi yayanta ne da yake girman yazo da zamani har wani saje da gemu ya ajiye, ba Mai yarda ta girme shi, Shigowar Larai da sallama yasa Mu ka mai da hankalin mu wajen k'ofar tare da amsa sallamar da tayi,Larai yar aiki ce a wani gida dake bayan layin mu na riga da nasan da zuwan ta tunda hajiyar ta kirani akan zata turo ta ta kawo min kayan aiki. Buhun hannun ta ta fara ajiyewa kafin ta sauke kayan dake Kan Almajirin dake biye da ita a baya ta zauna muka gaisa Tana "ga kayan nan Hajiya tace ki duba abinda babu sai na karbo" Kayan na duba naga duk abinda na bada list Ina bukata akwai hakane yasa na dago Ina "Karfe uku ne taron ko? "I karfe uku ne idan Allah ya kaimu" "Toh ba damuwa gobe karfe daya da rabi kizo da kulolin zuwa lokacin na gama in sha Allah" Mik'ewa tayi ta min sallama ta tafi, "Umma dan Allah ki daina wanan aikin wahalar wlh har ga Allah bana so sabida ke nake so na nemi kudi ki huta" Cewar Faisal yana hade rai. Saifullahi ya karba da "Abin nan na cimin tuwo a kwarya wlh nima bana san aikatau dinan da take karba kudin ma ba wani Mai yawa ba a gaskiya lokaci yayi da Zaki daina wanan aikin umma" Murmushi na saki Ina "Ina ga tunda kuka taso kuka same ni da sana'ar nan, ni kadai nasan kalar rufin asirin da wanan sana'ar yamin bani kadai ba har daku tunda kunsan aikin baban naku ba wani mai kwari bane idan na daina ku kan ku zaku Sha wahala a yanzu idan ta biyani kudi na gobe shine zan samu kudin registration din jamb din ka" Yana k'ok'arin magana Abban Nusrah ya shigo da sallama hannun sa d'auke da ledoji niki niki. Tuni yaran Suka mimike Nusrah ta riga su isa wajen sa tana "Abba oyoyo tun dazu nake jiran dawowar ka sannu da zuwa" Washe baki yayi Yana "Kin dade da zuwane" "Kana fita nazo Abba" "Ai da kin kirani a waya ai da na dawo da wuri ya kike ya maigidan naki" A kunyace Nusrah ta ringa amsawa Bayan ta ajiye ledojin. Daya bayan daya suka ringa Masa sannu da zuwa fuska a washe ya ringa amsawa sai da ya juyo muka hada ido ban kawo zai min kallon arziki ba naga ya sakar min murmushi take na saki murmushi Ina Jin dadi a raina na Masa sannu da zuwa a daidai lokacin da Yesmeen ta d'auko masa ruwa ta ajiye a gabansa. Ganin su Saifullahi na k'ok'arin mik'ewa yasa yayi saurin dakatar dasu sai da suka zauna ya kalli Saifullahi Yana "Ni nawane ma kudin registration din ka" Washe baki Saifullahi yayi Yana "Abba na dan yi aikin lebura na tara dubu goma yanzu ciko nake nema" "Nawane cikon" "Dubu goma Sha biyar ne" Hannu yasa a Aljihu ya d'auko wrapper Dari biyar biyar,na gwallo Ido Ina kallon sa tamkar yanda duka yaran suma suka zaro ido suna kallon kudin,ya kirgo Dubu ashirin dan dani aka kirga kudin ya mikawa Saifullahi Yana "gashi nan kaje kayi registration din" "Na gode Abba Allah ya Kara arziki" "Ameen" Ya kalli Faisal yana "nawane kudin jamb din naka" Shima baki a washe ya fada masa ya kirga ya bashi zuwa lokacin farinciki da mamakin Inda ya samu kudi Mai yawa hakane ya cikani dan iya sanina yanzu ba lokacin samun kudin sa bane Dan aikin nasa sai lokacin zafi sosai idan ya samu su gyaran freezer haka Ac franker da sauran su. Mamaki bai Kara kasheni ba sai da naga daidai da Annur sai da ya tambaye shi matsalarsa ya kirgo kudi ya bashi ko Nusrah bai bari a baya ba ya kirgo Dubu goma ya bata har ga Allah kasa motsi nayi dan a lissafin da nayi ya bada wajen dubu sabain,Ina ya samu irin wanan kudin mai yawa haka yadda ya bawa Nusrah dubu goma haka ya bawa Yesmeen da bakin su ke washe suna ta zuba Mai godiya da Addu'a sai amsawa yake bakin sa shi ma a washe. Sai a lokacin yacewa Yesmeen ta d'auki ledar kajine a ciki ta wanke ta dora sai yarana suka Kara haukacewa da murna har Nusrah na wlh sai ta tsaya an gama ta tafi dashi. Sai da duk Suka watse ya juyo ya kalleni yana "Hajajju yau nima na dan yi abin kwarai rabon da na yiwa yaran nan abu da kaina har na manta baki ji dadin da naji dana ga farin ciki a fuskarsu ba" Murmushi na saki Ina "Allah ya Kara arziki ya Kara budi ni da adashe na ma Zan dauka na bawa Saifullahi yayi registration din sai Kuma Allah yayi ikon sa ka samu kudi" "I Allah kuwa yayi Ikon sa Alhamdulillah ke ma ai ga naki siyayyan nan na miki" Ya turo min daya ledar gabana Baki a sake na bud'e ledar naga less ne guda biyu sai atamfa da wani bakin mayafi duk da ba wani sanin kaya masu tsada nayi da gani kayan masu tsada ne" "Abban Nusrah a Ina ka samu kudi mai uban yawa haka" Kabiru gyada kansa yayi dan yasan zaa rina indai Sajeedar daya sani ne sai ta tambaya "Haduwa nayi da wani tsohon abokina ya zama mugun mai kudi,shi yamin kyautar kudin nan bai tsaya iya nan ba yace zai taimaka min na samu aiki" "Wane abokin naka ne dan Kamar duk nasan abokanan ka"? "Aa baki san wanan ba primary Mu ka yi tare" "Allah sarki Allah ya saka Masa da alheri ya biya Masa bukatunsa na alheri yadda ya faranta mana Allah ya faranta masa" "Ameen ya Allah" A ranar tare duk Muka ci abinci cikin tsananin farin ciki su Annur a kudin da aka basu har da siyo sababin takalma. Abban Nusrah ma zan iya cewa rabon da naga farin ciki haka a fuskarsa har na manta. Bayan sallah isha mijin Nusrah yazo Suka tafi. Addua kawai nake a raina Allah yasa Abban Nusrah ya cire wanan mumunan abin a zuciyar sa har ga Allah naji dadi da naga baya fushi dani bana san abinda zai Kara sawa na mu yi fada. Ko da muka kwanta a ranar bai neme ni ta baya ba ta hanyar da Allah ya hallasta miji ya nemi matar sa ya neme ni bayan ya samu nutsuwa ya bani hakuri akan na kwantar da hankalina bazai Kara tunanin nemana ta baya ba sai a yanzu ma ya ringa nadama da yayi tunanin gwadawa. Har ga Allah naji Dadi rumgume da juna muka yi Bacci. 3am Kabiru a hankali ya leka fuskar Sajeeda yaga tayi nisa a bacci. Ya zare jikinsa daga nata ya sauko a hankali sabida Kar ya tasheta daga bacci. Gefen gadon ya duba a hankali ya d'auko pant din ta ya kudundune a hannun sa cikin sanda ya fice daga d'akin yayi waje. Yana zuwa yayi bayan gida ya d'auko tukunyar kasar da ya shigo dashi da ba Wanda yasan ya shigo dashi,ya saka pant din a ciki ya fara surutan da aka ce yayi a hankali Yana waige waige duk da Yana da tabbacin ba Mai ganin sa dan a sharrudan ance Kar ya sake ya yarda a gan shi. Yesmeen. Bata da nauyin bacci ko kad'an ko ya taji motsi sai ta farka. Motsin k'ofa yasa ta bude idonta. Kafin taji Kamar takun tafiya a ta Bayan dakinta Inda ta mik'e zaune tare da dafe kirjinta cike da tsoro. A hankali ta Mike ta leka ta window.......... MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4k Mg's beauty kit 14k Herbal whitening soap Body cream Face cream Scrub Cleanser Glow oil Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Team glow😍 *RUFAFFEN SIRRI* *NA SADNAF* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *Page 3* Ba abinda take iya hangowa sabida duhu,amma dai kamar mutum take hango wa tunanin ta kila barawone ya shigo gidan hakane yasa tayi sauri ta bar jikin window ta nufi k'ofar d'akin cikin sand'a ta bud'e a hankali dan so take ta je k'ofar d'akin Umman ta sanar musu,tana fitowa Kabiru ya shigo shi ma cikin sand'a,ganin Yesmeen yasa gabansa mugun faduwa dan daga shi sai gajeran wando,itama jikinta ne ya dau rawa cikin rawar baki tace "Abba motsi naji a bayan dakina Ina tunanin barawone ya shigo shine na fito na fada muku" Sai a lokacin Kabiru ya dan saki ajiyar zuciya dan duk tunanin sa ta gan shi "Ki koma nima motsin naji shi yasa na fito ba kowa Ina ga b'eraye ne" Da sauri ta juya ta koma ciki ta rufe kofar ta ta saka sakata ta kulle ta Kara gyara labulen window ko da ta kwanta sai ta kasa komawa bacci dan zuciyar ta cike take da tsoro tunda Nusrah tayi aure take jin tsoron kwana ita kadai. Kabiru kuwa Yana shiga d'akin yayi sauri ya kwanta a gefen Sajeeda yayi rigingine Yana kallon ceiling sai murmushi yake shi kadai dan a yau kawai da ya rabawa yayan sa kudi ya sauke hakkin da ya Kamata ace shi yake saukewa ba Sajeeda ba sai yaji wani irin farin ciki da ya dade bai ji irin sa ba,yana bakin ciki yaga yaran sun tsallake shi idan suna zaune sun tafi wajen Sajeeda suna Yar murya ta basu kudi har Kuma suka girman kallon babu suke masa dan sau tari zai ji suna mun san Abba bashi da kudi,abun na matukar Kona masa rai zai iya cewa tunda yaran Suka dai girma ba Wanda ya tab'a tunkarar sa yace Abba ina san kaza kayi min kaza duk wajen Sajeeda suke zuwa,Wanda yasan sabida bashi dashi shi yasa basa tunkarar sa abin arzikin da zai ce yayi shine a lokacin Auren Nusrah ya dan tab'a abin arziki,amma komai dai Sajeeda ke yi Kuma bata tab'a nuna gajiyawarta ko damuwa ba dan macece ita Mai zafin nema,a yau da yaga ya Sanya yayansa farin ciki yaji ya Kara kwadaituwa da ya samu kudin. Abu daya ke damun sa a cikin dokokin da aka shimfida masa,na kin sallah na tsawon sati daya,yaso ya nuna bazai iya ba Rabiu ya dage Masa. Haka yayi ta sake sake har aka Kira sallah Asuba Sajeeda ta mik'e zaune cikin hamma da adduar tashi daga bacci,shi kuwa yayi saurin rufe idon sa kamar Bacci yake. Sai da ta sauka daga gadon ta hau neman pant din ta dan zani kawai ta rufe jikinta dashi. Ganin ta duduba wajen da ta kwanta bata gani ba sai tayi tunanin ko wajen da Kabiru ke kwance ya danne,hakane yasa ta hau tashin sa akan ya tashi yayi wanka Kar ya makara sallah asuba. Kabiru kuwa kamar mai baccin ya mike Yana mitsitsika ido,ya mik'e tsaye ta janye bargon ta hau duduba Inda ya kwanta bata gani ba sai gashi har zanin gadon ta cire,Kabiru kuwa ya San mai take nema Sarai hakane yasa ya shareta ya shige bandaki yayi wanka ya fito ko alwala bai yi ba ya nufi wajen kayan sa. Sajeeda kuwa cikin mamakin rashin ganin wandon ta tace "Abban Nusrah kaga ban ga pant dina ba sai dubawa nake" "Toh tsayawa Neman pant zakiyi ko Kuma wanka zaki Shiga sabida kar ki makara sallah asuba,kin wani daddage da nema kamar baki da wani" "Ba haka bane Abban Nusrah kasan yesmeen na shigowa d'akin tayi gyara Kar nazo taga pant akan gado Ko a wani wajen kaga da kunya ko" ""Umm ni dai na tafi massallaci sai ki dage da nema" Yayi waje. Sajeeda Kuma ta shige bandaki dan tayi wanka ta yanke idan ta iddar da Sallah sai ta gyara d'akin ko zata gani. Kabiru kuwa yana fita ya labe daga waje Yana kallon lokacin da su Saifullahi suka fito daga gidan suka nufi massallacin. Sai Kuma yaji kirjin sa ya masa nauyi Mai bambanci Arne da musulmi sallah ce fa, yanzu haka zai yi sati kenan ba saka goshin sa a kasa ba? tuna irin kudin da zai yi yasa ya ture tunanin a ransa dan a wanan yanayin da yake ciki kudi kawai shi ne burin sa dan Rabiu yace masa Rabin masu kudin garin nan duk ta haka suka yi kudin su. Sai da ya ga yaran sun dawo sun shige ciki shima ya fito daga lungun da ya b'uya ya Shiga gidan. Koda ya Shiga daki Sajeeda ya Tarar ta daddage da neman pant da hijabin da tayi sallah a jikinta har zanin gadon ta canza sabida Neman da take shi kuwa ya hade rai dan ko da wasa baya so ya bata fuskaar da zata ishe shi da maganar pant din ta. "Abban Nusrah kaga har daga katitar nan nayi wlh Babu pant ba dalilin sa" "Mtsss kina da matsala wlh Tom mai Kika daddage kina nema daya ne dake"? "Aa ba dayane dani ba Ina ta mamakin yanda zan kwana da abu a gefena yanzu na duba ko sama ko kasa bangani ba" "Baki da abin yi ne Sajeeda ki cigaba da nema idan Kuma ba barawone ya shigo ya rasa mai zai dauka sai wandon ki" Kabiru yace tare da Jan siririn tsaki,ya kwanta Yana zai koma bacci karfe goma ta tashe shi daga bacci zai je wajen abokinsa da ya bashi kyautar kudi yace masa yaje Yana san ganin sa. Da toh ta bishi ta fito daga dakin tana tunanin kila wani wajen ma pant din yayi ta tsaya wahalar da kanta. Tare suka yi abincin karyawa da Yesmeen dake bata labari taji motsi jiya a bayan windonta,ko baccin arziki bata yi ba Dariya Sajeeda ta saka mata ta ringa ce mata matsoraciya yanzu haka b'eraye ne. Sajeeda Tare muka ci abinci da Abban Nusrah da yazo fita ya bani Dubu biyar Wai nayi cefane har ga Allah daga jiya zuwa yau bansan kalar Farin ciki da Addu'ar da nayi wa Abban Nusrah ba, hakika ya kyautata wa nida yarana,dan ko da Abban su ya fita suka shigo hirar kyautar da aka musu kawai suke Annur kuwa ya hau cewa "Nayi mafarki Abba ya Zama mugun Mai kudi Wai ya gina wani gidan bene duk muna ta murna amma ban ga umma a gidan ba" Murmushi na saki Ina "idan baka gani a gidan ba wata Abban ku ya auro kenan,a lailai auta kyautar da aka ma ya maka dadi irin wanan mafarki haka. Tare muka yi aikin abincin da aka kawo min da Yesmeen dan Kamar na mayar nima na dan huta tunda na samu Yan canji,dan daidaikun Rana ne baa kawo min aikatau Kuma har ya zame min jiki. Da yamma Ina d'aki sai ga Abban Nusrah ya shigo gidan da sallama fuskar sa Kamar gonar auduga ba kowa a gidan sai ni kadai dan duka yaran sun tafi islamiya. Nima ganin fuskarsa a washe yasa nima na washe bakina Ina "Abban Nusrah Mai muka samu ne naga fuskar ka d'auke da Annuri haka" Zama yayi a gefena Yana "Sajeeda Ina ga mun kusa zama masu kudi" "Allah Abban Nusrah abokin naka ya nemo ma aikin ne"? "Daga wajen sa nake yanzu haka ai yanzu ma zama bai Kama ki ba tashi Zaki yi mu tafi ki tayani yi masa godiya Kinga yau ma kudin daya bani kyauta Sajeeda" Gwalo ido nayi a lokacin daya bud'e ledar dake hannun sa wrapper Dubu Dubu ne guda biyar,mik'ewa nayi na dafe kirjina Ina "Abban Nusrah duka wanan kudin ya baka aikin me yake yi haka"? "Ke kinsan kudin sa kuwa wanan ai ba komai ne ma a wajen sa ke baki ga alkawarukan da yamin ba a ciki kuwa har da kyautar gida yace bazai manta alherin da na masa muna Yara ba" Kudin daya dora a cinyata kawai nake juyawa har ga Allah sai najini a tsorace tambayoyi nake so na yiwa Abban Nusrah amma bana so na rusa Farin ciki da yake ciki,a wanan zamanin har wane irin kudine da shi haka jiya ya bashi kyautar dubu dari biyu yau Kuma ya d'auko dari biyar ya bashi. "Wai ya na ga ba kya farinciki ne Sajeeda Allah ne ya turo min shi ya taimaka min fa Allah yasan tsawon shekarun da na dauka Ina aikin wahala" Murmushi yak'e nayi Ina "ba haka bane Abban Nusrah Mai zai hana ni murna kawai Ina ta mamakin yanda daga jiya zuwa yau ya iya baka kyautar dubu dari bakwai zugudum a wanan zamani ko dan uwan ka ke da wanan kudin ba lailai ya iya baka irin wanan kyautar ba" "A wajen masu kudi kyautar dubu dari bakwai ba komai bane Sajeeda sabida dai bamu da kudin ne shi yasa kike ganin yawan kudin, ba za ki gane abinda na ke fada ba sai anjima idan mun je gidan Zaki tabbatar da ko miliyan daya ya bada kyautarsa ba zai ji komai ba" "Allah ya saka masa da alheri" "Ameen Ameen ai idan ya samo min aikin nan sai na siya miki tsalallen mota,su Saifullahi ma sai na bi su da motoci" "Allah ya yarda yasa arzikin na alheri ne a gare mu Abban Nusrah kasan wani arzikin masifa ne,ni wlh a rayuwata rufin asiri kawai nake so bani da wanan burikan tashin hankalin indai zanci sau uku a rana yarana su kawo bukatar su na musu ba tare da na gaza ba wlh Alhamdulillah" "Sajeeda kenan yanzu dai tashi kije ki boye mana kudin ki zo ki fada min Abubuwan da ake bukata a gidan" D'aki naje na boye kudin na dawo wajen sa duk jikina a sanyaye bansan mai yasa ban ji Ina mugun Farin ciki ba shi kuwa sai zuba yake yana lissafa yadda idan ya samu kudi zai canja mana rayuwa ko girki da na so dorawa hana ni yayi yace yau bazaa yi girki ba Kuma bai yarda na Kara karbar aikatau ba. Koda Yara suka dawo haka ya tara su Yana tambayar su abinda suke so. Tuni duk suka haukace da murna daga Mai cewa machine yake so sai Mai cewa keke yake so Annur kuwa sai tsalle yake Yana mafarkin sa ya tabbata Abban su ya Zama Mai kudi,Abban Nusrah kuwa sai washe baki yake Yana su Kara saka su a addua ai Yana ganin nan da sati biyu zamu bar gidanan. Ni dai da ido nake bin sa yanda ya hakikance Yana zuba lissafi Taya mutumin da ba shi da ko asi sai ya fita yayi buga buga tashi daya ya ringa wanan lissafe liisafen sai Kuma nayi tunanin Allah Kan iya azurta bawan sa a dare daya zai Kuma iya talauta bawan sa a cikin mintuna. Bayan sallah isha yace na shirya mu tafi gidan abokin na sa na masa godiya na so ya bari zuwa gobe ya dage mu tafi. Haka na shirya cikin dogon hijabina na haye machine din sa mu ka dau hanya. Ni dai ban san wajen da mu kayi ba kalle kalle kawai nake har mu ka iso wani wawakekken gida da aka masa ado da fitilu masu haske kamar ba dare ba. Haka kawai na ji tsoro ya Kara rufe ni na hau sallati a daidai lokacin da ya kashe machine d'in na sauko yayi parking a gefe ya hau buga gate d'in. Wani ne ya bud'e yana ganin Abban Nusrah ya washe baki Ya rusuna ya bashi hanya tare da masa sannu da zuwa, nidai tsayawa nayi daga baya Ina mamakin yanda Mai gadin yasan Abban Nusrah har yake wani rusunawa. Sai da Abban Nusrah ya juyo ya nuna min hanya na Shiga gidan da bismillah dan sai naji Ina karkarwa har Ina Jin sanyi na Shiga na. Abban Nusrah kuwa kamar yasan gidan yayi gaba nayi saurin ruk'o hannun sa ya juyo Yana kallo na. "Abban Nusrah tsoro nake ji ka ga girman gidan fa" Nace Ina kalle kalle Ya janye hannun sa Yana "mai abin tsoro ke dai kawai ki biyoni" Kirjina na dukan uku uku na cigaba da bin sa a baya har Muka karaso wani k'ofar da gabad'ayansa glass ne. Abban Nusrah ya danna wani waje k'ofar ta bud'e da kan ta,ya shige nima nabi bayan sa Ina zare ido,dan tunda nake a rayuwa ta ban tab'a ganin irin Wanan gidan ba. Ba kowa a palon Abban Nusrah kuwa ya samawa kansa wajen Zama ya nuna min kujera akan na zauna. Ni kuwa rawar da jikina yake yasa na zauna a kasa. Abban Nusrah ya d'auko wayar sa daga Aljihu Yana "gamu nan mun zo" Daga haka ya mai da wayar cikin jaka. Ni dai Sam ban ji hankalina ya kwanta ba dan Addu'a kawai nake a zuciya ta. Takun da na jiyo yasa na daga kaina Ina kallon sama. Wata mata ce mai kib'a fuskarta d'auke da murmushi bayan ta Kuma wani ne shi ma da kib'ar sa da Alama shi ne Abokin Abban Nusrah da matar sa sai naji hankalina ya dan kwanta har suka karaso wajen da mu ke. Matar tace "Haba ya zaki zauna a kasa ki zauna a sama mana" "Aaa nan ma yayi" Duk yanda naso ta barni a kasa ki tayi har sai da na hau saman kujerun na hau gai da abokin Abban Nusrah da ya kura min ido ya na Kare min kallo. Ku sha ruwa Mana"? Matar sa tace dan suna Zama aka cika gaban mu da kayan ciye ciye ni dai tunda na zauna na rasa nutsuwa ta buri na kawai mu bar gidan. Kaina a sunkuye naji Abban Nusrah na fada mi shi kawoni yayi na masa godiyar alherin da ya Masa. A lokacin matar ta koma sama haka ne yasa na sauko daga Kan kujeran na hau Masa godiya cikin murmushi daya bayyana hakoran makkar sa yace "ba komai uwargida baxan iya biyan Kabiru alherin sa a gareni ba dan ya taimaka min sosai sabida ni maraya ne,abincinsa haka zai kawo mu raba dan na taimaka Masa ba wani Abu bane". Godiya na Kara Masa yace ba komai ya Kara da "akwai wani gida da nake so na bar masa kyauta dan yace min gidan da kuke ciki ba naku bane haya ne,dan haka a satin nan ku fara shirye shiryen komawa na bar muku gidan halak malak,sannan zan d'auke shi aiki a company na zaa na biyan sa albashi miliyan daya kowane wata" Tunda ya fara magana na saki baki Ina kallon sa dan gabad'aya ji nayi na girgiza da Abubuwan da yace zai yi mana. Kamar an like min baki haka na ringa kallon sa Abban Nusrah kuwa sai godiya yake zuba Masa Yana ba komai. Sai da Abban Nusrah ya kalleni na iya bud'e bakina Nima na hau masa godiya. Ko da mu ka zo tafiya kudi ya d'auko Mai yawa ya miko min nak'i karba dan wlh wani irin tsoro naji ya Kara rufeni Kuma gabana bai bar fad'uwa ba idan dai na hada ido dashi. Sai da muka fito na daga palon na fara samun nutsuwa nayi gaba na bar su a baya. Kabiru Yana ganin Sajeeda tayi gaba ya kalli Alhaji Rabiu yana "Kasan idan ba haka muka yi ba wlh haka zata tayi min tambayoyi" "Nasan fa irin su haka sakeena ke da wanan taurin Kan,yanzu abinda za'ayi kayi k'ok'ari jibi ku koma gidan sabida ka fara aiwatar da abinda aka saka ka" "Ba zamu wuce jibi ba" Daga haka su ka yi sallama. Sajeeda Har muka isa gida Sam ban ji zuciyata ta kwanta da wanan sauyin rayuwar da muke neman samu ba hakane yasa sai da muka zo kwanciya nace "Abban Nusrah bansan Mai yasa hankali na bai kwanta da wanan canjin da muke neman samu ba,taya haka kawai zai d'auko gida sukutum guda ya mallaka ma dan kawai ka taimaka Masa Kuna Yara Anya mutumin nan ba dan yankan Kai bane?wane irin aiki zaka Masa da zai d'auko har miliyan daya ya baka a wata"a gaskiya!! Wani irin tsawa ya daka min daya tilasta min yin shiru"Sajeeda dama bakya san na cigaba a rayuwata? kinfi so na dawwama a haka a talauci kina jinki kamar mai gidan tunda ke kike yin komai a gidan,kinfi so na zama kamar yaron ki ko? bakya so kiga na samu na kaina Toh bari kiji na fada Miki da hannu biyu Zan karbi arzikin da ya tunkaroni idan Kinga bazaki iya ba sai kisan nayi" Daga haka yaja dogon tsaki ya juya min baya. Ko da na hau bashi hakuri inaso na fahimtar dashi nufina ko ta kaina bai bi ba. A haka na kwanta a gefen sa ina

Chapter 2 of 7