sake sake da bacci barawo kuwa ya daukeni na hau Mafarki
da Kabiru da abokin sa
Mafarki........
MG'S SKINCARE
Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?
Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar
fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,
Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara
a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin
hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo
bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,
Ga product din kamar hka,
Sabulu 4k
Mg's beauty kit 14k
Herbal whitening soap
Body cream
Face cream
Scrub
Cleanser
Glow oil
Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k
Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,
Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Team glow😍
*RUFAFFEN SIRRI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*Page 4*
Mafarki
A kwancen da nake naji motsin bud'e k'ofar dakina hakane yasa na bud'e idona sai naga abokin
Abban Nusrah ya shigo da Jan zani daure a kugun sa hannun sa rik'e da tukunyar kasa,sai na
Mik'e da sauri cikin tsananin tsoro na fara kwallawa Abban Nusrah Kira akan ya tashi,dan ba iya
abokin nasa ne ya shigo ba har da wasu a bayan sa suma da tukunyar kasa a hannun su,ihu
nake iya karfina na kasa d'auke idona daga kansu na Kai hannu na dan na tashi Abban Nusrah
sai na ji baya gefe na har suka zagaye gadon da na ke kwance na cigaba da ihu Abokin Abban
Nusrah ya fusgoni da k'arfi ya Kai hannun sa wajen zani na, na saka ihu!"
A daidai lokacin da naji an rik'e ni ana girgiza ni na bud'e ido na da sauri tare da mik'ewa zaune
kirjina na dukan uku uku a lokacin da na farka na ga ashe mafarki nake duk na jike da gumi,na
Kankame Abban Nusrah da ya rik'e ni gam yana "lafiyarki kuwa"?
"Mafarki nayi Abban Nusrah innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"
Na cigaba da sallati Ina kallon k'ofar dakin mu dake rufe dan sai nake ganin kamar ba mafarki
nake ba
"Kiyi Addu'a ki koma ki kwanta"
"Abban Nusrah mafarkin abokin ka nayi"
"Gwara da ki ka ce mafarki ba gaske ba ki koma bacci dan Allah"
Ya fara k'ok'arin cire ni daga jikin sa na Kara Kankame shi mu ka kwanta ahaka.
Mafarkin da nayi na nan daram a idona,ko kad'an ban runtsa ba dan gani nake ko Yaya na rufe
ido zan ga sun shigo bansan Mai yasa nayi mafarki da abokin Abban Nusrah ba,Mai ma'anar
wanan mafarkin da nayi.
Idona biyu har aka Kira sallah Asuba na tashi na daura alwala Abban Nusrah kuwa sai sakin
munshari yake,a yanzu baya sallah akan lokaci sai nayi ta tashin sa kafin ya tafi massallaci.
Duk tashin da na masa bai tashi ba da na dame shi ma tsawa ya daka min hakane yasa na
rabu dashi nayi Sallah ta ina ta mamakin canjin da nake gani a tare dashi,sai Kuma na tuna wai
abokinsa yace zamu bar gidanan take naji wani irin tsoro da fargaba ya rufeni da na tuna
mafarkin da nayi dashi,jikina na gaya min mutumin nan baa a banza zai taimake mu ba bansan
mai yasa jinina bai d'auke shi ba ko dan na saka shi a raina shi ya sa nayi irin wanan mafarkin
dashi.
Har na fito Muka hada abincin karyawa da Yesmeen zuciyata cike take da tunani har sai da
Yesmeen tayi ta tambaya ta mai ke damuna nace mata ba komai.
Karfe tara da rabi su Saifullahi suka shigo dan su karya fuskar su a washe,Annur kuwa ya
zauna a gefe na bayan duk sun gaisheni yace "Umma nifa yanzu kullum sai nayi mafarki Abba
yayi kudi"
Da sauri na daga masa hannu Ina "ka ringa mana Addu'ar idan alheri ne kudin Allah ya tabbatar
mana"
"Ai yama tabbatar in Sha Allah yaro babban ka ya zama Mai kudi,Umman ka ke so mu cigaba
da zama a talauce ba cigaba"
Naji maganar Abban Nusrah a baya na na waiga Ina kallon sa a daidai lokacin da ya iso gefena
ya zauna fuskar sa d'auke da murmushi Yana amsa gaisuwar da suke Masa.
Ya janyo faranti ya fara zuba dankali yana cigaba da magana "Saifullahi Kai da Faisal yanzu
idan muka gama karyawa zamu je ku rakani gidan da abokina ya bar min kyauta nasan zaku ga
kwana biyu na dan samu kudi,wani aminina ne tun muna primary Allah ya hada ni dashi Mai
kudine sosai hakane yasa yace zai taimaka min yanzu haka jiya nida mahaifiyar ku mun je jiya
ta masa godiya ba iya kyautar gida kawai yace zai min ba har aiki zai bani a companyn sa zaa
ringa biyana miliyan daya duk wata"
Ihu Suka saka gabad'aya suka hau murna har da tsalle Yesmeen itama sai murna take
"Abba yanzu kana nufin sabon gida zamu koma Wanda yafi wanan"?
Saifullahi yace cikin tsananin murna da farinciki
"Sabon gida zamu koma ai zamuje kuga gidan daga nan ma sai muje ku masa godiya"
Murna kawai suke Yesmeen kuwa jiki na rawa ta d'auko wayarta ta Kira Nusrah ta hau labarta
mata naji itama ta saki ihu ta cikin waya tana zata zo gidan.
Nidai da ido kawai na ringa bin su banji Ina murna ba na rasa dalili hakika cigaba ne yazo mana
Wanda ban tab'a tunani ko mafarkin sa ba amma na rasa mai yasa naji a madadin naji ni cikin
Farin ciki nake Jin akasin haka har ga Allah bana san mu bar gidanan abokin Abban Nusrah
sam bai kwanta min ba Ina addua Allah yasa tarayyar su ya zame Mana alheri.
Yaran ko ta kaina basu Kara bi ba suka yi waje duuu dan Abban Nusrah ma cewa yayi duk suzo
su tafi suga gidan.
Basu dawo gidan ba sai wajen laasar bakin su Kamar gonar auduga sai labarta mun kyaun
gidan suke da haduwar sa ,suka d'auko Dubu hamsin suka bani akan abokin Abban su ne ya
basu kyauta,sai fadar kirkin shi suke suna murna wai Abban su ya zama Mai kudi nidai ban iya
ce komai ba sai dai sake sake a zuciya dan ban samu fuskar ma da zanyi wata magana ba.
Sai da muka zo kwanciya Naga na kasa jurewa dan Abban Nusrah cemin yayi a gobe goben
nan zamu tashi mu bar gidan Kuma baza mu dau komai ba dan akwai komai a gidan
Duk da nasan magana ta zata b'ata masa rai haka na daure na fara magana Ina "Abban Nusrah
daga haduwar ka da abokin nan naka ina ga ko sati ba'ayi ba har a cikin Yan kwanakin nan ya
maka irin wanan alherin har dasu kyautar gida Abban Nusrah Kar idon mu ya rufe ya Kamata
muyi bincike a kansa kafin mu koma gidan da ya bamu,ya Kamata mu tabbatar da irin sana'ar
da yake yi saboda mu samu kwanciyar hankali wlh zuciyata bata dauki wanan abokin naka ba
tsoro nake ji Kar ya zama bata hanyar halak yake samun kudin sa ba Abban Nusrah"
"Ya isa haka Sajeeda na fada miki Mai kudine Yana harkar Mai Kuma babban dan kasuwane
bansan sau nawa kike so na fada Miki ba, ya za'ayi cigaba ya zo mana har gida ki tsaya kina
wani kananan zance an gaya Miki banyi bincike akan sa ba Mai kudine na fada miki dan haka
idan Zaki saki jikinki mu ci arziki toh idan bazaki saki ba wanan matsalar ki ce"
Yaja dogon tsaki ya kwanta tare da juya min baya
"Allah ya baka hakuri Abban Nusrah ai bansan kayi bincike akan sa ba Allah yasa mu koma
gidan a saa"
"Ameen"
Kawai yace ya Kara Jan bargon saman kansa.
Wlh a ranar sai naji na kasa bacci kallon dakina dana kwashe shekaru a ciki kawai nake sau
uku Abban Nusrah na farkawa ya leka fuskata idan yaga idona biyu sai ya koma ya kwanta yaja
tsaki ana hud'u da ya leka fuskata muka hada ido sai ya Kara Jan tsaki Yana "Wai me kike yi
baki yi bacci ba"?
"Bana Jin baccin ne Abban Nusrah Ina ta jimamin yadda zamu tashi mu bar gidanan Mai tarin
tarihi"
Tsaki yaja Ya juya min baya ya hau magana kasa kasa ban ji Mai yake cewa ba.
Tun bai zama mai kudin ba ya canja hali Abban Nusrah ya zama wani iri sai na tsinci Kaina da
Addu'ar ina ma abokin Abban Nusrah yace ya fasa ba mu gidan.
Ana Kiran sallah asuba na tashi nayi alwala duk tashin da na masa akan yayi sallah bai tashi ba
har yanzu mamaki yake bani,dan Ina Jin karar bude gidan wanda nasan su Saifullahi ne suka
tafi massallaci.
Koda na iddar barin dakin nayi dan wani zazzabi zazzabi naji Yana Neman rufeni na kwanta a
dogon kujerar dake Palo.
Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani,Kamar dai mafarkin da nayi jiya haka na sake mafarki
da abokin Abban Nusrah ihu kawai nake a mafarki dan Jana kawai ya ringayi Abban Nusrah na
tsaye Yana kallona bai motsa ba girgizani da aka yi da k'arfi ana ummaa!!
Yasa na bud'e idona da sauri na Mik'e zaune Ina waige waige
"Umma lafiya kuwa"?
Yesmeen ta kara rikeni
Na dafe kirjina da hannu biyu Ina sallati a raina ya zaayi nayi mafarki iri daya sau biyu
Sai da na dan samu nutsuwa na mik'e na nufi dakina.
A zaune na tarar dashi a gefen gado na zauna a gefensa Ina "Abban Nusrah wlh yau na sake
mafarki da abokin ka sau biyu kenan Ina mugun mafarki dashi Abban Nusrah bana jin mutumin
nan akwai alheri a tare dashi dan Allah ka Kara bincike a kansa.
"Tunda kin ringa kin dasa mugun nufi a zuciyarki ai dole kiyi ta kananan mafarki ban taba ganin
matar da take bakin ciki da ci gaban mijinta ba sai ke,wato kin fi so mu cigaba da zama a gidan
haya kinfi so kiga na cigaba da yawo a machine da karfuna Ina bin mutane Ina musu gyara kinfi
so yarana su cigaba da zuwa suna neman abu a wajen ki ni Kuma na cigaba da zama
hoto,Sajeeda baki isa ba sabida wani banzan tunanin ki bazan k'i karbar arzikin da Allah ya nufa
zan samu ba idan Kin ga ke ba za ki iya ba za ki iya cigaba da zama a gidan nan amma ni da
yara na a yau za mu bar gidan nan ba fashi"
Ya fice daga d'akin a fusace.
A takaice Ina ji Ina ga ni muka bar gidan ba dan raina na so ba yara na kuwa murna kawai su
ke.
Ban tsorata ba sai da na ga tafkaken gidan da abokin Abban Nusrah ya ba mu kyauta,gidane
katon gaske da wawakeken fili komai na gidan sabo ne, da ido kawai nake bin gidan yarana
kuwa cikin murna suka ringa zagaye gidan su fito daga wanan d'akin su fada wanan,tuni suka
rabawa kansu daki, daki daya mutum biyu Nusrah kuwa ta dage kwana zata yi sai murna take
tana zabgawa abokin Abban Nusrah godiya.
Yesmeen itama katon daki ta zaba.
Abban Nusrah kuwa sai washe baki yake shima Yana nuna min dakinsa na can karshe yace na
d'auka shine d'akina.
Ba abinda ya burgeni a gidan duk da kyau da haduwar sa ko dan murnar da na ga yarana na yi
na so na saki raina amma sai naji na kasa haka dai nayita yake har lokacin kwanciyar mu yayi
muka kwanta.
KABIRU
Ya kasa yarda da canjin rayuwar da ya fara tsintar kansa a ciki da Rabiu yace masa somin
tabi ne wanan iya farinciki kawai da yaga yaran sa a ciki yasa ya Kara daura damarar yin koma
mene ne dan ya samu kudi,a yanzu sai ya daina jin wani tsoro zuciyar sa a dake take da yake
Jin zai iya komai indai zai zama Mai kudi,kananan surutan da Sajeeda keyi kuwa haushi kawai
take bashi abinda ma aka ce yayi jiya bai samu yayi ba saboda tak'i tayi bacci ko a yanzu da
yake kwance lek'a ta kawai ya ke ya ga ko tayi zurfi a bacci dan Rabiu na ta Kiran sa akan ya
tabbata yayi abinda aka ce yayi.
Karfe biyu na dare yaji saukar numfashin ta alamar tayi zurfi a bacci sai da ya lekata yaga
baccin ta take shara.
Ya sauko daga kan gadon a hankali ya bud'e k'ofa ya fice cikin sand'a.
Yesmeen.
Motsin da taji yasa ta bud'e idon ta a hankali ta ji takun tafiya ta bayan d'akin nata dan d'akin
nata Yana ta wajen bayan gidan.
Wani irin tsoro ne ya rufe ta kirjinta na bugawa dan Sajeeda korar Nusrah tayi akan bazata
kwana ba.
Jikinta na karkarwa ta mik'e zaune ta nufi wajen window dake ta bayan d'akinta dan fitilar d'akin
a kashe take.
A hankali ta daga labulen d'akin ta hango Kabiru a zigidir Yana zagaya tukunyar kasar da
tsakiyar sa ke ci da wutar kyandir.
Kirjinta kamar ya fado ta gwalo ido tana cigaba da kallon Kabiru dake ta surutai yana zagaya
tukunyar kasa.
Jikin ta rawa kawai yake a san ta dafa window saboda rawar da jikinta keyi, abin karfen labulen
dake Kan windown ya fado.
Kabiru yayi sauri ya juyo hankalinsa a tashe......
Novel din RUFAFFEN SIRRI na kudine biya 500 zuwa acct din nan 2029764071 first bank
nafisa sai ku turo da shaidar biya ta Wanan layin 08068484400 ko katin mtn ta layin Nan
08033719070
: Assalamu alaikum wa rahmatullah.
Na ce bara in tunasar daku cewar na shirya aji tsaf don ci gaban mata iyayen gida,A wannan
lokacin da sanyi yayiwa mata yawa a matsayin ki na mace yaya kike kula da kanki don kariya
daga ɗaukar cutar sanyi ko da mai gida ya na ɗauke da shi?
: Shin kinada labarin sai kin isa ake tafiya dake? Aure nawa ke suke mutuwa saboda mazaje
sun gaji da rashin damun isashiyar gamsuwa awurin matayensu?
Da yawan mata basuda labari game da kansu ma bare su nemi maganin matsalar su abu ɗaya
suka sani sanyi ko dryness
Kina zaune kinashan maganin da ba shine matsalar taki ba
Kiyi ƙoƙarin shiga wannan ajin da naira dubu ɗaya jal, inda zaki mallaki ilimin da babu mai
ƙwace miki shi har abada; A wannan ajin namu zamu baki ilimi akan sanin wace kalar macece
ke acikin mata, menene matsalar ki a ɓangaren jikinki, yanda zaki kula da kanki a lokacin
saduea da bayan saduwa, dabarun samun gamsuwa yayin jima'a musamman da ragon namiji.
Hanyoyi inganta tukunyar gidan ki, zamu kawo daɗaɗan abubuwan da zasj taimakawa mai gida
idan kin mishi ya dawo da ƙarfinsa. Bamu tsaya anan ba zamu koyar da ke yanda zaki haɗa
kayan mata 'yan gaske da hannunki, kama daga dahuwar kazar amarya da uwagida, dahuwar
'yan shila, haɗin tsumi kala lala kai abin dai ba'a magana.
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin
Tallafawa tukunyar azuminki ta hanyar koyar dake ƙayatattun girke girke, shu'umar humrah da
kuma kulacham ga turaren tsugono don zama tauraruwa👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin Saiki tura shaidar
biya ta nan👉🏻 07084161619.
Na gode.
2073065733
UBA BANK
SHA'AWA IBRAHIM
*RUFAFFEN SIRRI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*Page 5*
Hankalin sa a tashe ya kashe kyandir din ya rarumo rigar sa ya saka hankalin sa idan
yayi dubu ya tashi dan a sharadun da aka bashi har da Kar ya sake ya yarda a gan shi idan har
aka gan shi da matsala.
Tukunyar kasar ya d'auka yaje ya ajiye a d'akin da ya ajiye duka Abubuwan da aka bashi akan
yayi amfani dasu,dan kafin su dawo gidan duk Suka kawo Abubuwan su musamman Suka ware
d'akin ta bayan gidan.
Yana rufo k'ofar d'akin.
Ya nufo wajen window cikin sand'a addua kawai yake Allah yasa ba ganin sa Yesmeen tayi ba
dan kamar daga dakin ta ya jiyo karar faduwar abu.
Fuskar sa ya Kara a window ya hau lek'a d'akin sai dai ba abinda yake iya hango wa.
Jiki a sanyaye ya koma ciki sai daya je har k'ofar d'akin Yesmeen ya Kara kunnensa yaji ko zai
ji motsin ta sai dai har ya karaci tsayuwar sa bai ji motsin komai ba.
Addua kawai yake Allah yasa ba ganin sa akayi ba dan yasan da matsala.
Jiki ba kwari ya nufi d'akin su
Yana tura k'ofar d'akin yaci Karo da Sajeeda tana ganin shi ta Kankame shi tana sauke
numfashi.
Ture ta yayi daga jikin sa dan yasan yanzu zata ce mafarki tayi
Kara ruko shi tayi jikinta na rawa ta fara kuka tana "Abban Nusrah akwai matsala wanan
mafarkin da nake ba haka kawai bane Mafarki iri daya sau uku Abban Nusrah wlh wanan
abokin naka bana Jin mutumin arziki ne"
Wani irin tsawa ya daka mata idon sa jawur dan yanzu sam ba'a hayyacin sa yake ba abinda
aka ce yayi a yau har da wankan bai samu yayi ba fada ya rufeta dashi akan daga yau Kar ta
Kara fada masa tayi mafarki ya gaji da halin ta idan ba za ta zauna dashi ta bar masa gida.
Yaja dogon tsaki ya kwanta ya bar Sajeeda da jikin ta ke Karkarwa saboda tsoron mafarkin da
tayi na yau ya da tayi ya munana dan har yanzu zafi take ji a gaban ta kamar a gaske,dan
mafarki tayi abokin Abban Nusrah ya zura mata hannu a gabanta ya Ciro abu tana ta ihu, tsoro
yasa ta kwanta a bayan Kabiru ta Kankame jikinta tare da rufe fuskarta.
Allah yasan Kabiru fin karfin ta kawai yayi amma jikin ta na gaya Mata akwai wani abu game da
Abokin nan nasa ba abanza take mafarki dashi ba daga ranar da ta fara zuwa gidan sa ta ga
Yana ta kura Mata ido ya zama dole ta tashi tsaye da Addu'a.
A haka tayi zuru har aka Kira sallah Asuba da yake tana fashin sallah sai ta Shiga bandaki ta
gyara jikinta ta canja pad dinta ta saka Wanda ta cire a leda da zumar idan gari ya waye sai ta
Kai bola dan haka take yi daga lokacin da take flushing din pad ya toshe pipe din ruwa ya daina
tafiya ta daina sakawa a toilet.
Ko da ta fito daga bandakin kwanciyarta tayi Dan tasan sai Abban Nusrah yaga gari ya kusa
wayewa yake tafiya massallaci abin na matukar bata mamaki.
Tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita dan baccin take ji.
Duk abinda take yi Kabiru na sane rufe idonsa kawai yayi sai da ya tabbatar da tayi nisa a bacci
ya mik'e ya Shiga bandakin ya d'auke pad din dan Yana ta addua ta cire dan zai Kai ayi amfani
dashi Yana d'auka yayi waje da sauri dan so yake yaje ya samu Rabiu,suje yaji ya ko aikin da
aka sa shi yayi.
Yesmeen
Rik'e numfashin ta kawai tayi da rarrafe ta kwanta ta Kankame jikinta dake ta karkarwa
ba abinda take gani a idon ta sai Kabiru da ta hango Zigidir Yana zagaye wuta,gani take kamar
a mafarki tana jin takun tafiyar sa har zuwa lokacin da taji karar bud'e k'ofar da yayi Wanda
hakan ke alamunta Mata da shigowa yayi,Jin motsin sa a bakin k'ofar d'akinta yasa taji Kamar
ta saki fitsari saboda tsananin tsoro,ita dai tasan ba tabin hankali ta samu ba Wanda take yiwa
kallon mahaifinta taga yayi tsirara Yana zagaye wuta,mai hakan nufi?Mai yake yi da tsakar dare
da kowa ke bacci,duk yadda ta so ta gano ma'anar abinda yake yi kwakwalwar ta tak'i bata
had'in kai, dan a iya sanin ta a film take ganin irin wanan tashin hankalin ta Kuma san Abban ba
boka bane ba maye bane.
Baccin da bata koma kenan ba ta Kankame jikinta tana Addu'a a zuciyarta sai take ganin kamar
ma dai idon ta ne ya gane mata Abba amma bashi bane.
Umman ta zata fadawa taga Abba da tsakar dare tsirara ko Saifullahi
Ko dai Aljani ne da siffar Abban,amma dai taji motsin shigowar sa cikin gidan.
Haka ta kwanta bata motsa ba sai da aka Kira sallah Asuba ta mik'e ta daura alwala duk ba'a
nutse tayi sallahr ba sabida tunanin abinda ta gani.
KABIRU
Yana fitowa daga gidan ya hango motar Alhaji Rabiu a nesa da gidan dan dama sun yi
akan za su hadu da sassafe dan shi ma zai je can wajen shugaban nasu.
Yana Shiga cikin motar Rabiu yace "dafatan ka yi abinda shugaba ya saka Kuma ba'a samu
kuskure ba"?
"Jiya na fara yi na ji Kamar motsi ina tsoron ace ganina aka yi ko wankan ban samu nayi ba"
"Ya za'ayi a gan ka ba karfe biyun ka tashi ba"?
"Karfe biyu na tashi wlh motsi naji Wai dole a gida zan yi Abubuwan nan ba zan iya yi a wani
wajen ba"?
"Aikuwa dole a gida zaka yi Kuma indai an gan ka wallahi da matsala ka samo jinin nata"?
"Eee gashi nan a Aljihu na"
"Tom bari mu karasa,tunda tak'i bamu hadin kai ayi ta baya kaga kuwa Dole a biyo mata ta
bayan gida"
"Kasan me ke damuna wai tana yawan mafarki dakai abin na damuna dan har ta fara nuna min
Kamar kudin da kake bani bana halal bane tana da saurin gano abu fa Ina tsoro asirina ya tonu
da Wanan mafarkin da take"
"Ni mai hadina da ita da za ta yi mafarki dani ai da Kai ya Kamata tayi mafarki bani ba"
A haka suka cigaba da hira har Suka karasa wajen.
Ta baya Suka Shiga d'akin da shugaban nasu ke zaune kafin su karasa su zauna shugaban ya
daka musu tsawa Yana "ku dakata!!
Cak suka tsaya
Cikin wani irin murya shugaban nasu ya taso da kana masa kallo daya sai gaban ka ya Fadi a
d'akin da yake har da kwarangwal din kawunan mutane cikin wani irin murya yace "Rabiu
abokin ka jiya ya bata min aiki dan ya bari an gan shi"
Ido Kabiru ya zaro ba dama yayi sallati cikin tashin hankali yace "Shugaba waye ya gani"
Akwai yarinyar da ta gan ka Kuma kasan ka'idan aikinmu indai wani ya ganmu sai mun d'au
mataki dan bazamu so ta tonawa wani sirrin mu ba"
Gaban Kabiru ne ya yanke ya Fadi dan Yana tsoron matakin da zaa d'auka akan Yesmeen dan
ya gano itace ta gan shi dan ita kadai ce mace a gidan.
"A cikin abu uku dole ayi daya
"Ko mu kasheta
"Ko mu makantar da ita
"Ko mu kurmantar da ita wane za'a mata a ciki"?
Kabiru shiru yayi Yana tunani bai so ayi mata ko daya daga ciki ba amma karambanin ta ya
jawo mata a yanda ya fara dandana zakin arzikin nan duk abinda zai kawo masa cikas a cikar
burin sa zai iya kau da koma waye tunda har ya yarda zai tab'a Sajeeda
Batare da ya wahalar da kan sa yin dogon tunani ba yace "A kurmantar da ita yadda ko da gani
na ta sake yi nasan bata da bakin fadawa kowa"
Gyada kai shugaban nasu yayi ya koma ya zauna sai a lokacin Suka zauna ya fara kafawa
kabiru sababin sharruda dan yace na baya duk ya ruguje dan Yesmeen ta b'ata musu aiki a
cikin Abubuwan da shugaban nasu yace yayi daya ne yayi balain girgiza shi Kuma shine zai yi
na karshe ya samu kudaden.
A haka ya taso bayan ya bashi abinda zai sawa Yesmeen din a abinda zata ci maganar ta ta
d'auke.
Sajeeda
Na Rasa Wanda zan fadawa damuwata na rasa Wanda zai fahimtar da Abban Nusrah
zuwa yanzu wani irin tsoro nake ji.
Ban yarda da abokin Abban Nusrah ba a yau da na sake mafarki dashi na Kara tabbatar wa
kaina abinda nake ji a jikina da gaske ne.
Ko da na farka ban ga Abban Nusrah a d'akin ba hakane yasa nayi tunanin kila ya fita tunda na
dan dade Ina baccin.
Fitsarin da ya matseni yasa na shiga bandaki sai da na gama fitsarin na maida wandona har
zan fito na tuna pad din da na saka a leda hakane yasa na matsar da randar ruwan dan a
bayan randar ruwan na ajiye ledar.
Ga mamakina sai naga ban ga ledar ba,ba inda ban duba a bandakin ba amma ba leda ba
dalilin sa haka ne yasa na fito daga d'akina Ina mamakin waye zai d'auke min ledar pad dana
cire a jikina.
Ina fitowa palo naga su Saifullahi a barbaje suna karyawa ganin ban ga Yesmeen ba yasa na
nufi d'akin ta dan sai nake tunanin kila ita ta Shiga dakina Ina bacci ta shiga bandakin ta d'auke
ledar a kwance na tarar da ita tayi rub da ciki.
"Yesmeen"
Da sauri ta dago tana kallo na sai na ganta kamar a firgice
Hakane yasa na zauna a gefen gadon ban amsa gaisuwar da take min ba nace "Yesmeen
lafiyar ki kuwa"?
Yatsun hannun ta ta hau murzawa tana motsa bakin ta alamar akwai magana a bakin ta hakane
yasa na Kara gyara zamana bana san naga Yesmeen a cikin damuwa ko kad'an
Na ruko hannun ta ina "Yesmeen menene wani abu ne"?
Yesmeen kasa magana tayi tana tunanin yadda zata fadawa Sajeeda abinda ta gani dan abun
ya tsaya mata a rai dan har ta hada abincin karyawa ba'a nutse take ba,bata san taya zata
fadawa Sajeeda abinda taga Abban yayi jiya daddaren ba,dan har ga Allah yanzu tsoron sa
take ji.
"Ina jinki yesmeen menene"?
"Mafarki nayi umma Mara kyau akan Abba mafarkin ya tsaya min a rai"
Da sauri Sajeeda ta gyara zaman ta kirjinta na dukan tara tara Kar dai